Showing 102001 words to 105000 words out of 226732 words
mishi addu'a sannan ta faɗa wanka.
***
WASHEGARI...I just published "BABI NA TALATIN DA UKU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/JH0s4CH5Wab
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
33)
Tunda ta ji kira daga sama wai kuma daga Chairman Aliyu Dikko ta ji kanta ya yi ringingin, ma'aikata dai sun fi dubu a ƙasan bawan Allahnan, ta ina har ya ganeta da har zai turo Oganta ya kirata? Sai kuma da ta tuna Oga ya nema kafin ita ne yasa ta gane bakin zaren.
Kai tsaye tare da Oga suka shiga wurin Chairman. Matar da ta gani zaune yasa ta shan jinin jikinta. Sanadin aikinta dai Hajiya Zeenatu za ta yi mata. Sai cika take tana batsewa, kallon da take watsamata tun shigarta ofis din ya sanya Ramlat daga kallo ɗaya ba ta ƙara duban inda take ba har suka karasa.
Chairman ya na juyi saman kujerarsa yake duban wacce aka kira da Ramlat duba irin na ƙurillah. Ya haɗiyi miyau maƙwat. Koda ya taɓa ganinta ya manta saboda dubunnan matan da ke zirga-zirga a Revenue.
"Yallaɓai gatanan."
Oga Ɗalhatu ya ƙara magana a karo na biyu ganin kamar Chairman ba ya tare da shi, Chairman ya yi gyaran murya kafin ya maido nutsuwarsa ya saita kansa.
"Yauwa Ɗalhatu, kana iya tafiya." Cike da girmamawa Oga Ɗalhatu ya amsa gami da barin wurin.
"Wannan ita ce?"
Chairman ya fadi gami da ɗauke kallonsa kamar ba ya so daga kan Ramlat zuwa na Hajiya.
"Ita ce! Karuwa la'ananninyar Allah! Ita ce ke bibiyar mijina.!"
Zuciya ya zo wa Ramlat wuya, wannan suna da Hajiya ke laƙabamata ya isheta.
"Ni ba karuwa ba ce, kuma da kike fadin wai ina bibiyar mijinki, ki tambayeshi ki ji sau nawa shi ya tako zuwa gidanmu da sunan zance."
Ba zato Hajiya ta shammaceta ta kifamata mafi, itama ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta ɗaga hannu da zummar ramawa, tsawar Chairman ta dakatar da ita ta sauke hannun tana kara zura dara-daran idanunta cikin na Hajiya. Itama Hajiya Zeenatun kallonta take kafin cike da zafin rai ta dubi Chairman.
"Me na faɗamaka?! Me nace game da yarinyar nan?! Wallahi Dikko idan ba ka sallami wannan yarinyar a ma'aikatarka ba ka sani abinda ka binne a hannuna yake, da kaina zan tona asirinka a ..."
"Haba Hajiya Zeenatu, ya isa mana! Haba!"
"Ke wuce ki bar nan!" Ramlat ta haɗasu duka ta watsamusu banzan kallo kafin a fusace ta bar ofis din, ba ta jin ko ɗarr, ta shirya abinda ya fi kora daga aiki ma a yi mata idan har akan Hajiya ne. Matar da ba ta san darajar dan adam ba, ba ta kaicon a koreta daga aiki.
"Me kake nufi da hakan Dikko?!"
Hajiya Zeenatu ta furta rai a ɓace. Shima daure fuska ya yi yana saita tunaninsa.
"Na ce ki bar komai a hannuna zan dauki mataki a kanta ko?"
"Dikko na sanka kamar yunwar cikina, kar ka yi wasa da hankalina."
Wani murmushi ya yi.
"Haba Hajjaju, na fadamaki da kaina zan dauki mataki don wallahi nikam na ga abinda ba zan kyale ba."
Ta yamutse fuska.
"Me kake nufi?"
Ya gyara zama ya kora ruwa a cikin ƙaton tumbinsa sannan ya yi mata bayani daki-daki, wani murmushi ta yi kafin kuma ta kwashe da dariya yana tayata. Da yatsa ta nuna saitin kwanyarta.
"Kai dinnan na yarda akwai ƙwaƙwalwa!"
Ya shafi sanƙonsa.
"Haba Hajjaju! Ai mun ci dubu sai ceto. Ke dai ki kwantar da hankalinki."
Da wannan ta mike ta fice.
***
Da wani irin fushi take tuƙi, yanda Hisham ya matsu ta je su yi magana haka itama ta matsu ta je ta ba shi saƙo ya faɗawa Hussein akan matarsa. Har ta isa ƙofar gidan A'isha ba ta ji wani sassauci a zuciyarta ba. Maigadin zai budemata ƙyaure ta dakatar da shi, ko'ina ta rufe ta faɗa gidan.
Falon babu kowa shiru, sallama ta yi ba amsa don haka ta yi zamanta tana jijjiga ƙafa, tunawa da ta yi ba ta yi sallar La'asar ba ne yasa ta miƙewa ta faɗa ƙaramin ɗakin saukar baƙi na A'isha.
***
A'isha ta fito daga daki ta yi turus ganin jaka da mayafi, can kuma ta fahimci ko na wace, da wani ɗoki ta faɗa ɗakin da ta san za ta iya ganinta ciki, ai kuwa ta ji motsin ruwa a banɗaki, ba jimawa Ramlat ta fito. A'isha ta tsaya wani sakaka tana kallonta.
"Ke kuma ina kika shiga na zo ina ta sallama shiru?"
Maimakon ta ba ta amsa, sai ta jefamata tambayar da ke cinta.
"Lafiya kuwa? Kinga yanda idanunki suka kumbure suka yi ja?"
Guntun tsaki ta ja, tana jan skirt din atamfarta don ya sauka sosai.
"Bani hijabi."
Abinda ta ce kenan ba ta ko damu da ba ta amsa ba, A'isha ta juya ta fita can kuma ta dawo dauke da Hijab. Warware hijabin ta yi ta shiga kokarin zurawa.
"Ki kira mijinki idan ba ya gida ki ce na zo, sauri nake ba zama zan yi ba A'isha."
Daga haka ta shiga kokarin tayar da sallah hawaye na ciccikowa daga idanunta.
A'isha dai ta lura akwai matsala don haka ta fita ta ja mata ƙofar. Wayarta ta fitar ta kira Hisham kamar yanda ta nema ta sanar da shi zuwan Ramlat din. Ya yi mamaki don a zatonsa sai zuwa yamma.
"Ki ce ta ɗan ƙara hakuri, nan da awa In Sha Allah zan iso."
Daga haka A'isha ta katse wayar. Kicin ta faɗa ta haɗomata abinci a faranti da lemu da ruwa. Komai ta haɗa ta kai mata ɗakin, a sannan ta idar da sallah ta zauna kawai ta yi shiru. Ƙarasawa ta yi ta ajiyemata a gefenta kafin ta ce.
"Mun yi waya ya ce nan da awa zai iso in Sha Allah."
Gyada kai kawai Ramlat ta yi.
"Wai don Allah meke faruwa haka ne? Duk kin tayarmin da hankali na rasa nutsuwa."
Sai a sannan ta ɗan yi murmushin yaƙe.
"Ba komai."
Haushi ya sa A'isha miƙewa ta fice. Sai duk kuma ta ji ba ta kyauta ba, ai laifin wani ba ya shafar wani. Don haka ta janyo plate din ta tsakuri abincin gami da korawa da lemu. A falon ta tarar da A'isha ta ƙura wa talabijin idanu tashar Zee World. Babu tabbacin ma hankalinta na wurin. Zama ta yi.
"Ke Auta sarkin fushi, ba wani abu bane ba fa. A wurin aiki ne aka ɓatan rai."
Ganin haka itama A'isha ta sauko.
"Kai amma kin faɗarmin da gaba, dama nayi tunanin hakan. Allah Yasa dai ba wannan Halimar ba ce."
Murmushi Ramlat ta yi. Ta tuna irin walwalar da Halima ke yi na ganinta cikin wannan yanayi, wanda dai ba ya sonka zai wuya ya so ka.
Share batun suka yi suka koma hirar abinda ya shafi bikin Munir. A hankali kuma zuciyarta ta ɗan yi sanyi.
Karfe biyar da wasu mintocin, Hisham ya shigo gidan. Gaisawa kawai suka yi yana jan ta da zolaya sannan ya faɗa ciki don kimtsawa, A'isha ta mara mishi baya.
Ba jimawa ya fito da alama wanka ya yi, ya sauya daga manyan kaya zuwa jallabiya.
"Antinmu ina wuni."
Ta ɗan harareshi.
"Na gaji da wannan doguwar gaisuwar, na ƙagu ka faɗamin dalilin wannan neman don nima inada magana."
Ya yi dariya.
"Allah Ya ba ki hakuri toh."
Daga nan ya bata labarin komai har zuwa kan kauracewa Hajiya Zeenatu da Hussein ke buƙatar ta yi. Wani huci take yi har hancinta na buɗuwa da rufewa.
"Ka gama?"
Cikin haɗiye dariyarsa ya gyaɗa kai.
"Zan so ace shi wanda ya turo ka da wannan saƙon yana zaune tare da mu..."
"Sai na kirashi."
Ya katse ta da hanzari, ta ja guntun tsaki.
"Banda wannan lokacin, sai dai ka fadamasa ta cikin gida ake fara komai kan a duba waje. Ya isa da matarsa ne za ta dinga bibiyata har wurin aiki tana ɓatan suna? Waye mijinnata da har ya ishi mutum kallo? Wallahi nikam na fi karfin zama inuwa daya da wannan banzar matar tasa ko nace uwar mata don a haife ma ta haifeshi."
Ta shiga basu labarin abinda Hajiya Zeenatu ta yi yau a ofishinsu. Hisham kansa shima ransa ya ɓaci.
"Amma wannan dai ba ta da hankali ko?"
A'isha ta furta cike da ɓacin rai.
Ba tare da Ramlat ta kula ba ta ci gaba da magana tana duban Hisham
"Don haka ka yi mishi magana, matarsa ta fita hanyata! Wallahi darajar zumuntarku da shi nake dubawa, amma idan har bai dau mataki a kanta ba, ni kuma ba zan fasa gasamata magana a ko'ina muka hadu ba idan ta taɓoni. Abin nata ya wuce hankali har wurin aikina? Me ma tsaremata wai? Ni ba son Mijinta nake ba, shima ba sona yake ba! Ya kamata ta san wannan!"
Gyada kai Hisham ya yi.
"Hakane, gaskiya kuma abin na neman wuce gona da iri. Kiyi hakuri don Allah, ni da kaina daren yau ba gobe ba da yardar Allah zan sameshi mu yi maganar. Sai dai fa Ramlat, akwai abinda ya ban mamaki da kuma ɗaurewar kai game da Hussein."
Za ta so su yi maganar sai dai a yanda yau ranta ke a ɓace sunansa ma ba dadin faɗi yake mata ba, don haka ta mike tsaye tana yamutsa fuska.
"Nikam mun gama magana ai inaga, gida zan wuce kafin Hajiya ta neme ni."
A'isha da Hisham suka dubi juna, murmushi Hisham ya yi, ya mata uzurin halin da take ciki na ɓacin rai. Har mota suka yi mata rakiya sannan suka koma ciki. Kai tsaye ya dau waya ya kira Hussein ya sanarmasa yana son su yi magana, suka ajiye wajen da zasu haɗu.
***
Hajiya Zeenatu ta dubi mijinta da ya ajiye waya.
"Fita za ka yi kenan?" Ta fadi zuciyarta na wani irin sanyi na farin ciki, ko ba komai za ta samu ta fita nata aikin. Fuskarsa cike da mamakin yanda yau ba ta mishi ƙorafin fitar dare ba ya dubeta. Dariya ta ɗan yi ta kama hannunsa ta ɗan murza.
"Naga kamar da Hisham ka yi waya. Ai ba zan hanaka zumunci da shi ba. Ko ba komai ya so ka da alheri bai bar min kai cikin mawuyacin hali ba rannan. Amma naga kamar da ɗan hadari a garin."
Murmushi ya ɗan yi.
"Kar ki damu Hajjaju, ba nisa zamu yi ba ai, dayake shima nan Lamiɗo Crescent ya ke."
Ba haka ta so ba don haka da azama ta tari numfashinsa.
"Toh amma fa gaskiya ina son ka tahomin da Balangunnan na rijiyar zaki mai dadi. Na kasa cin abincin John."
"Yanda kike so hakan za'a yi."
Suka yiwa juna murmushi kafin ya mike ya dauki wayoyinsa da mukullin mota.
"Sai na dawo ko?"
Ta gyada kai tana wani lumshe masa idanu a son ta burgeshi karshe. Tana jin fitarsa ta mike da azama ta hau sama tana nishi da gyara ɗaurin zaninta da ke neman faɗuwa. Sai da ta soma fiddo ruwan maganinnan ta faɗa banɗaki ta yi tsarki da shi tas ta maida cikin jarkar sannan ta maidashi maɓoyarsa. Daga nan ta sanya layar a jaka ta dauki mukullin motarta ta fita.
Maigadin dai ba abinda ya shallesa, tashi ya yi ya bude ta fice ya maida ƙyauren gida.
Tuƙinta take tana mai jin wani ƙarfin gwuiwa na zuwarmata wanda ke ƙara sanyata jin ba za ta fasa abinda ta yi niyya ba. A farko ta dauka lamarin Ramlat mai sauƙi ne da za ta iya maganceshi da hannunta, gari ne ba za ta bari ba, asalima ba za ta taɓa aikata yin wanka a tsakar dare ba kuma ba don ba za ta iya bane, sai don a ganinta asarar lokaci ne don babu abinda zai sa ta bar garin saboda Ramlat. A cewar ta Ramlatu ta yi kaɗan, gwara dai ta yi wanda za ta mallake Hussein yanda fita ma sai da izninta zai yi. Kallon sararin samaniya ta yi yanda ake zuba walƙiya. Ta ƙara maida hankali ga tuƙinta tana sharara gudu kamar wata namiji.
Ba ta tsaya ko'ina ba sai a wani filin Allah da ba gida gaba babu a baya. Gari sai walƙiya ake yi da iska mai daɗi. Wani rami ne ƙato wanda a ƴan unguwar basu komai da shi sai aiken almajirai su zubarmusu da shara sai kuwa ƴan shaye-shaye da kan zo su maida wurin matattara. Babu tsoron jinnu balle shaiɗanu ta nufi bolar gadan-gadan.
Tsammaninta babu kowa a wurin saboda yanayin iskar da ake da kuma walkiya, a zatonta za ta yi aikinta ta kammala kamar yanda Isuhu ya ce kar wanda ya ganta, sai dai tana hawa saman bolar gami da kokarin zura layar, wata fitila ta hasketa ga kuma hasken walƙiya.
"Kaii...wa..ye anan?"
Daga yanayin maganar za ka san ɗan maye ne.
Cikin Hajiya ya ɗuri ruwa, ba ta yi aune ba wani ruwan hawaye ya tahomata, ba wai tsoron ɗan mayen ne ya shigeta ba illa ɓatamata aikin dubunnan da aka yi.
"Allah Ya isa Batool!"
Abinda ta ce kenan a fili don da shawararta ta zo wannan bolar, sam ba nan ta so zuwa ba.
Hankali a tashe ta sauko duk da hakan sai da ta soke layar. Daidai nan ɗan mayen hannunsa riƙe da wuƙa ya zagayo yana ƙara kallonta sosai. Zobunan gwal ne a hannunta duk da ta saka mayafi bai hana a gani ba. Da sauri ta ce.
"Kana so? Gwal ne?"
Wata dariya ya yi yana rangaji. Ta saba karawa da irinsu. Kafin ya kai ga magana ta ciro ta damƙa masa.
"Kai Hajjaju! Kin san homular! (Formular)"
Ita dai haushinsa take ji kamar ta shaƙeshi, ta fice a wajen yana ta mata kirarin da ba ta ma fahimta don a hargitse ta ke.
***
Ga Ramlat kuwa, kasa sanarwa Hajiyarta ta yi akan abinda ya faru a wurin aikinsu ta yi, ta dai sanarmata dalilin kiran da Hisham ke mata.
"Toh kinga wannan ma kadai ya isa ki yiwa kanki faɗa ba ruwanki da shiga harkarta ballantana har ta kaiku da samun matsala. Àllah Ya rufa asiri dai."
Daga haka suka rufe zancen.
***
Hussein ya yi shiru ya kuma baza kunne yana sauraron Hisham har ya kai aya, fuskarsa kadai ka kalla za ka ga damuwa da ɓacin rai kwance.
"Kenan duk abinda nace ba ta ji ba?" Fadin Hussein a kausashe.
"Ramlat ko wa?"
Hisham ya nemi sani. Girgiza kai kawai Hussein ya yi kafin yace.
"Ka bata hakuri, ka kuma..."
"A'a Malam, wallahi na gaji. Nima fa ina da aikina ba masinja ba ne. Haka kawai sai a takuran da kaiwa da kawowa wurin faɗar saƙo. Toh na gaji fa, ana cin lokacinmu nisa Princess. Haba, aure ko wata ba'a yi ba an ban sabon aiki?"
Harɗe hannu Hussein ya yi a kirji yana dubansa fuska dauke da murmushi, ya maida idanunsa sararin samaniya yana ganin yanda ake zuba walkiya da kuma iska. Ba ta
"Give me her digits."
Ba Hisham ba da mamaki ya kusan kaiwa ƙasan gwuiwa, hatta shi ɗin da ya nemi lambar sai da ya ji faɗuwar gaba, ya nemi tsoro da fargabar abinda hakan zai haifar ya rasa, ji yake kamar akwai abinda ke danneshi.
"What did you say?" Hisham ya faɗi kusan a birkice. Maimakon ya amsa sai ya fiddo wayar ya ajiye saman mota ya bude murfin zaman direba ya shiga ya soma kokarin tayarwa. Ganin haka Hisham ya dauki wayar bayan ya fiddo tasa wayar, hannunsa har rawa yake yana mai jin wani farin ciki, fatansa yake so ya tabbata. Lambar Ramlat na Mtn da Airtel duka sai da ya ɗuramasa, kowanne ya ɗan danna kira amma sai ya kashe bai bari ya shiga ba, so yake dai lambobin su fada cikin Log.
Ta cikin gilas ya miƙa masa wayar.
"Shegen sama, gashinan ba ruwana kuma idan Hajiya ta gani, wallahi kar ma ka ambaci sunana. Ban yi saving ba, idan ka ga dama ka sanya Rabe a kan sunan ko Talle Mai Wanki."
Dariya sosai Hisham ya ba shi, suka hau yi can kuma ya ɗan lumshe ido ya bude.
"Zan rama ɗaya bayan ɗaya wallahi, ka yimin duk abinda ka ga dama yanzu. Sannan ni ba da wata manufa ma nemi lambar ba kar ka yi zaton akwai wata bayan Zeenat, wai don na ragemaka zirga-zirgar ce. That's it."
Hisham dai dariya ya yi bai ce uffan ba. Suka yi sallama ya ja motar ya nufi Rijiyar Zaki.
***
Washegari direba ta sanya ya kai yara makaranta, ko bakomai tana son yin baccin safe kadan sannan ta yi shirin Ofis. Ga garin ya yi luf sakamakon ruwan da aka samu a daren jiya. Wannan ne ya bata damar komawa bacci mai dadi bayan tafiyarsu. Ba ita ta farka ba sai da wayarta ta Soma ringing.
Duk yanda ta kai ta share hakan ya gagara don mai kiran bai yi ɗaya ya haƙura ba. Da wani irin takaici ta mike ta ja tsaki kafin ta duba sunan dake yawo sama screen. Hilal. Ɗagawa ta yi da sallama.
"Ayya na tasheki a bacci kenan. Shikenan ma yi magana anjima. A yi bacci lafiya."
Bai jira cewarta ba ya katse kiran, murmushi ta ɗan yi ta kara maida kanta cike da kasala. Wayar dai ta ƙara ringing, a dolenta ta miƙe zaune. Lambar Salisu na ofishinsu ke yawo saman screen. Ta ɗaga da sauri.
"Ramlat, kina ina ne?"
"Haba Yallaɓai, ba sallama ba komai?"
Ƴar dariya ya yi sannan ya yi sallamar suka gaisa, ya ɗora.
"Kiyi hakuri, abin ne naga gwara na sanar da ke shiyasa shaf na mance da wannan batun."
Cikin rashin nutsuwa ta zuro kafafunta ƙasa.
"Lafiya Salisu?"
"Ji nayi Oga Ɗalhatu na maganar an miki sauyin wurin aiki, za ki koma ɓangaren Chairman, a matsayin secretary ɗinsa."
Kirjinta ya bada dam! Koda ace ranta a ɓace yake jiya, ba ta mance irin shu'umin kallon da Chairman Aliyu Dikko ke watsamata ba. Ba ta son ta munana zato game da abinda ba ta da tabbacinsa kamar yanda take ganin baƙin jama'ar ma'aikatar da ke gulmar Chairman din da cewa ɗan iska ne. Don haka sai ta kyautata zato.
"Ko kina da masaniya ne Ramlat? Naji ba ki ce komai ba?"
Dan murmushi mai sauti ta yi.
"Banda ka faɗi bani da labari Salisu. Yanzu ai zan shigo ofishin