Showing 135001 words to 138000 words out of 226732 words

Chapter 46 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12487

ba. Ta jinjina kai.

"Ai shikenan, zan yi magana da shi Bellon, ya dace su yi bincike mai kyau a kansa, idan da hali ma gwara a tattara a ajiye zancensa gefe. Sai dai kuma da sharaɗin ki fiddo miji nan kusa. Da ƙananun shekarunki ba zamu zubamaki ido ki yi ta zama haka ba aure ba kuma kina yawon wurin aiki, babu ƙima da mutunci a hakan Ramlatu."

Ramlat ta gyaɗa kai cikin tausayawa kanta.

"Ki tayani addu'a Dada, Allah Ya zaɓamin nagari."

Dada ta amsa da amin. Ta ɗora da faɗin.

"Yaushe angwayen nawa zasu dawo ne?"

Murmushi Ramlat ta yi, tana gyara zaman mayafinta, takanas ta biyo daga wurin aiki don ta roƙi alfarma wurin Dadar.

"Ni kaina ina kewarsu, amma mun yi waya da Muhibbat ta cemin za ta je ta ɗaukosu zuwa gidanta su yi kwana biyu tukunna ta maidosu. "

"Allah Ya nunamana. Za ku je Daurar?"

Dada ta ƙarashe tana ɓallar goronta daidai sadda Ramlat ta dauki jakarta.

"In sha Allah zamu je. Inace su Nusaiba ma duka za su je?"

"In sha Allahu. Ai bikin na gida ne."

Fadin Dada, a karshe suka yi sallama ta fice ba ta ko yi sallama da sauran jama'ar ba don tana jin haushinsu ganin mafi yawa na goyon bayan Chairman. Ita mamakin ma irin karɓuwar da Chairman ya yi a gidan ta yi don ko a gidansu bai samu hakan ba.

***
  Tsakaninta da Hussein sai gaisuwa, ta rasa dalilin sauyawar alaƙarsu. Wani jzolaya da wasa duk ya daina. Kamar wani kalma na sabo bai taɓa ratsawa tsakaninsu ba. Wannan ya jefata damuwa, ga matsin lamba daga Chairman wanda ba dare ba rana sai ya kira. sai dai har ya kammala ringing ba ta ɗauka, idan ya dameta kuwa ta latse wayar gaba ɗayanta.

Tafiyarsu Daura ta gabato har Hajiya zaa je wannan karon sai Amarya Hunainah wacce ta saki jiki da su sosai ake zumunci ba kamar Bilkisu ba wacce tun hayan auren Munir ta haɗe danginsa kaf ta jerasu layin munafukai. Wannan ne ya siyawa Hunainah daraja da ƙima ba kaɗan ba a idanun su Ramlat. Gidanta ne dai har sannan  Ramlat ɗin ba ta taka ba, ba kuma don wani abin ba.

Ana gobe zasu wuce gaba daya su Rafee'ah har Hunainah mai karamin ciki sun zo cikin gidan kwana, Aisha ma ta na nan ta zo ayi sallama. Hira suke yi cike da nishaɗi ana dariya, sallamar Munir ce ta katsesu. Suka amsa ya dubi Ramlat.

"Ke wancan na wajen ne Chairman din naki?"

Nan da nan annashuwar Ramlat ta dauke.

"Zuwa ya yi?"

Ta fadi ranta a ɓace, tasan ya kira ta ƙi ɗagawa ya yi mata text akan zai zo su gaisa ta maida masa martanin ba ta buƙatar hakan.

"Nikam dai bari na leƙa naga waye wannan Chairman din."

Rafee'ah ke faɗi tana ƙoƙarin miƙewa.

"Shi auren a igiya kika ratayeshi? Ba ki da kai fa Rafee'ah naga alama."

Munir ya fadi gami da harararta.

"Goɗai-goɗai da ke kina abinda ko Auta ba za ta yi ba. To ki je ki ce masa me? Ki leƙa wuta ma ko?"

Dariya suka sa mata idan ka cire Ramlat da ta yi daki ranta na ƙuna. Kamar ba za ta fita ba, sai kuma ta yanke ta je kawai ta tunkare shi komai zai faru ya faru. Mayafin rigar jikinta ta yafa. Koda ta fito lokacin Hajiya na zaune.

"Ke dama haka kike zuwa hirar fuska kamar baƙin tukunya?"

Munir ya faɗi yana duban Ramlat da ta nufi Hajiya don sanarmata. 

"Yaya Munir nidai da ka roƙarmin alfarmar mutuminnan ya bar zuwa gidannan. Na faɗamasa ya kyaleni bana sonsa wallahi."

Taɓe baki Munir ya yi.

"Au, wato dai gidan jiya kike neman a maimaita? Ai yanzu babu mai miki dole Ramlat, a baya ma ba'a iya anyi maki ba sai yanzu? Ta inda aka hau ai ta nan ake sauka, ki samu wadanda suka karɓi kuɗinsa."

Yanda gaban Ramlat ya buga da ƙarfi, haka fuskokin Hajiya da su Zulaihat ya nuna razani da mamaki.

"Me kake nufi? Kuɗin auren Ramlatun su Yaya Bello suka karɓa?"

Munir ya dubi Hajiya yana mai murmushin tambayarta.

"Haba Hajjaju, a karɓi kuɗin auren Ramlatu ba ki sani ba? Kawai dai yana sakarmusu bakin aljihu ana bushasha."

Wani wahalallan ajiyar zuciya Ramlat ta sauke, cike da bakin ciki ta kama hanyar ficewq daga falon. Maganar su dinma sai suka bar ta anan adalilin Hunainah dake wurin, ko ba komai suna buƙatar sirri.

***
  "Girman kujerarki ce tasa na jure dukkan wata shanya da kika yimin, sai dai koda na bushe ganinki ya maidani ruwa tsundum."

  Murmushi yake yana ci gaba da dubanta, jinsa yake kamar wani saurayi mai shekaru talatin idan yana gabanta. Ramlat ta dubeshi a ɗaure.

"Ina haɗaka da girman Allah da ManzonSa s.a.w ka fita hanyata. Kaga mu ba yara bane da za mu tsaya muna magana da maimaici. Ina za ka ji daɗin zaman aure da wacce ba ta jinka a ranta? Wane kyautatawa ka ke tunanin za ta yi gareka?"

Chairman ya yi wata ƴar dariya.

"Kina tunanin barazanar kisa a daren amarcinmu zai sa na sake ki? Aa Hajjaju, wannan namiji ne ba muna maza ba. Ba ki da abinda za ki faɗarmin da gaba har ya yi sanadin rushewar alaƙarmu."

'Innalillahi..' Ta kai har ƙarshensa yayinda jiri ke neman kwasarta. Dakyar ta samu ta daidaita tsayuwarta bayan ta dafe Black Camry din Chairman. Wani yawu ta haɗiya.

"Me kake nufi?" Ta fadi cikin sarƙewar harshe. Chairman ya yi dariya karo na biyu.

"Abun dariya, kunkuru ya yiwa busjiya ƙafa, banda abinki Ramlatu ai maganar duniya ba ta ɓuya, kin ɗauka haka kike zaune ana ganin ina neman aurenki ba'a kawomin sukarki ba? Ai ba zai yiwu ba. Kedai ayi sha'ani kawai."

Shiru ya biyo baya ga idanunta sun cicciko da kwalla.

"Idan ka gama zancen zan koma ciki."

Chairman ya marairaice.

"Haba Ramlatu, me kike gujewa a auren mutum irina mai muƙami da kuma rufin asiri? Kinsan adadin matan da ke neman irina kuwa? Da za ki ga matan da ke bina za ki cika da mamaki. Ramlatu sonki nake dagaske amma kin ƙi fahimta. Da ace na biyewa Kawunnanki da tuni an daura auren, yanzu ma abinda ya kawoni batun turowa ne suka bn iznin nayi, shi ne na zo mu kara daidaitawa kafin lokacin."

Kamar wacce aka harbawa mashi, haka ta ji wani radadi a kirjinta. Daidai sadda ta ke share hawayen da ya zuba saman kuncinta ta kalleshi.

"Me ka ce? Iznin ka turo fa suka yi maka?"

" Kwarai kuwa, kuma kinsan dama ce da ba zan taɓa bari ta suɓucemin ba. Na zo ne don kawai na kwantar da hankalinki, ki ƙara samun nutsuwa da ni don idan har ina numfashi kina yi, babu wanda ya isa ya rabani da ke."

Ranta ya ɓaci ainun.

"Sai mu gani inda ake dole! Aure ne bana yi, ba zan aureka ba. Ina mai tabbatarmaka ko ka turo babu inda zancen zai ɗara."

Daga nan ba ta juya ba ta ko waigo ta ji dalilin kiran da ya shiga kwalamata ba.

***
"Lafiya?"

Kusan lokaci guda suka jehomata tambayar ganin yanda ya faɗomusu ɗakin. Ta kasa magana sai kallo, karshe ta wuce ɗaki.
Ganin haka Munir ya mike ya fita waje, Chairman ya shige abin hawa har ya fice. Ya dawo ciki ya sanar da su ya tafi.
Gaba daya suka bita dakin idan ka ɗauke Hajiya da Munir da suka faɗa tattaunawa game da lamarin Ramlatun.

"Ai mafita fa a wajen su Kawu shi ne kawai ta nemo wani ta kai musu. Yanzun bata da abinda zai kwace ta a hannunsu. Su gani suke sun kama dami a akala. Rannan ma na shiga gidan na tarar Malam (Kawu Rabe) yana ta rubutu, wai mai neman auren Ramlatun yake rubutawa na tsarin jiki. Kinga kuwa ba karamin kamu suka yi mishi ba, fahimtar da su barin aurennan sai da taimakon Allah."

Hajiya ta yi salati. Tana mamakin ƴan uwannata, idan kuma ta tuna wasu abubuwan da suka wanzu a baya na irin rashin jituwarsu a wasu lokutan matsayinsu na ƴan uba, sai ta ga fiye da hakan ma zai iya afkuwa. Haɗin kan ma da yanzun ake yi da iyalinta tasan bai je koina ba. Yaransu dai gashinan sun fi su hankali.

"Biri ya yi kama da mutum, Allah Ya kyauta."

Ta furta a fili ranta na zafi. Munir ya amsa da amin.

***
  A bangaren Ramlat kuwa, daga Zulaihat har Rafee'ah zagin Chairman suke su na ƙarawa. Hunainah dai tausayin Ramlat ta ke ji sosai.

"Kema kin so hakan ta faru, ai kinsan babu yanda za'ayi a zubamaki ido. Ruwan ido ne ko me? Don ba za ki ce ba ki da manema ba. Korarsu kike kin ƙi ba kowa fuskar fitowa, daga samarin har masu auren da dattijai. Ai gashinan ana neman yi miki bita da ƙulli."

Fadin Rafee'ah dake jin kamar ta shaƙe Ramlat tsabar takaici. Ta furzar da bacin ran ta hanyar dakawa ɗiyarta Daddy  tsawa ganin kokawar da suke da kanwarsa Afrah.

"Uhum, kema dai Rafee'ah kya faɗa. Ai tunda haka ta zaɓa sai ta zauna a cuceta. Koda dai watakila za ta iya tunda ba yau farau ba."

"Ba yau farau ba? Meyasa abinda ya wuce ba za ku bar tayarwa ba? Meyasa ku ka riƙi abinda na aikata ku ka kasa yimin uzurin kasancewata cikin ajizai kamar ku?"

Ramlat ta furta da duban Zulaihat. Su kansu ba wai da wata niyyar abin ke tasomusu ba, sai dai a lokuta irin haka idan ta ƙona ransu, takan motsa musu da abinda ya wuce ɗin.

"Anti Hunainah ki zo inji Uncle."

Daddy wanda ya fita ya shigo yana faɗi iyakar ƙarfinsa. Hunainah ta miƙe ta fita don yin sallama da mijinta.

"Har maganar ta kai ku kasa dannewa a gaban Hunainah?"

Cikin karyewar zuciya Ramlat ta furta.

"Hum ai shikenan. Allah Ya kyauta."

Rafee'ah ta faɗi tana mai miƙewa ta fice daga ɗakin. Sosai Zulaihat ta fuskanci ƙanwarta.

"Ya kamata ki nutsu ki yiwa kanki faɗa Ramlat. Ke ba yarinya ba ce, kin taɓa aure kin kuma hayayyafa, ba girmanki bane a soma ƙirgamaki aure wannan ne yasa gwara ki watsar da komai ki fuskanci rayuwa tun lokaci ya ƙuremaki. Da ki yi auren jeka na yi ka, gwara ki dau dogon lokaci ki auri wanda za ki zauna da shi har mutuwa ku rayu. Idan har ba ki tsaida wani kin kawo matsayin miji ba, kina ji kina gani za'a ɗaura aurenki da wanda ki ke gujewa. Na fadamaki ki nutsu ki san me kike. Ki kuma haɗa da addu'a, za mu tayaki."

Ramlat ta gyada kai tana jin wani sassauci na ratsa zuciyarta. Zulaihat ta fita ta bar ta anan zaune. Shiru ta yi tana mai ƙurawa hannunta da ya sha lalle idanu, mutuwa mai tonon silili. Hakan ta ayyana yayinda hawaye nta suka soma ɗiga.

***
Tafe yake cikin shiga ta alfarma, a gefensa Hajiya Zeenatu ce tana zabga uban murmushi. Hannuwansu sarƙe cikin juna.

"Husseini!" Ya ji wata murya ta kwalamasa kira, kusan lokaci guda suka juya shi da Hajiya Zeenat. A fuskar Hajiya Zeenatu, tashin hankali ne tsagwaronsa, idan ka ɗauke Hussein wanda idanunsa suka kaɗa suka yi jazur. Damƙe hannunsa da Hajiya Zeenatu ta ƙara ya sanyashi dubanta a hargitse.

"Husseini kai ne?!" Ya juya ga matar da ke tsaye tana dubansa dakyau.

  

 

 
[3/16, 1:55 PM] +234 703 629 0938: I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/i7Akdw4Ovcb



🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

43)

_*Tafe yake cikin shiga ta alfarma, a gefensa Hajiya Zeenatu ce tana zabga uban murmushi. Hannuwansu sarƙe cikin juna.*_

_*"Husseini!" Ya ji wata murya ta kwalamasa kira, kusan lokaci guda suka juya shi da Hajiya Zeenat. A fuskar Hajiya Zeenatu, tashin hankali ne tsagwaronsa, idan ka ɗauke  Hussein wanda idanunsa suka kaɗa suka yi jazur. Damƙe hannunsa da Hajiya Zeenatu ta ƙara ya sanyashi dubanta a hargitse.*_

_*"Husseini kai ne?!" Ya juya ga matar da ke tsaye tana dubansa dakyau.*_

_*"Kar ka je gareta! Zo mu tafi!"*_

_*Hajiya Zeenatu ta furta iyakar karfinta. Matar na jin haka ta taho gadan-gadan da zummar nufar Hussein kai tsaye tana fadin.*_

_*"Ni ce Husseini! Dadarka ce! Ka manta ni?"*_

_*Ba ta kai ga ƙarasawa ba ta ci uban tuntuɓe za ta faɗi. Sai dai caraf aka riƙeta. Hussein ya dubi mai shi, mace ce cikin fararen kaya. Daidai sadda Hajiya Zeenatu ta soma jan hannunsa, hawaye yake fitarwa yana dubansu da wacce bai san ko wacece ba. Caraf aka riƙe hannunsa, dole suka tsaya cak.  Fuskar Ramlat ya gani na wani haske da kyalli, murmushi ta ke yi madadin kukan da Dada da kuma shi suke yi, ta ɗago hannunsa ta sanya a cikin na Dada ta matse su.*_

_*"Har abada babu wani ko wata da zai ƙara shiga tsakaninku."*_

_*"Ƙarya kike!" Hajiya Zeenatu ta furta tana ihu.*_

 

***
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"
Ya furta a fili yana maida numfashi kamar wanda ya yi tsere, jikinsa gumi yake fitarwa duk kuwa da sanyin da ke a ɗakin. Kirjinsa bugu yake da sauri-sauri. Ya kai duba ga makwancin Hajiya Zeenatu. Bacci take ta lulluɓe har kai da bargo. A hankali ya dauki wayarsa a gefen gado ya kalli agogo, biyar saura mintuna, tabbacin Asuba ce. Don haka ya mike yana juyayin mafarkinsa.
'Dada?' Ya maimaita a zuciyarsa yana juya sunan, yana da wata mai suna Dada? Kuma a ina? Tunani ya yi mishi yawa har ya ɗaura alwala ya fito, kansa wani irin sarawa ya ke. Me mafarkinsa ke nufi? Ramlat ya gani, ihun kuma da Zeenatu ta yi na menene?

Babu mai amsa masa, wannan tasa ya  fice daga dakin zuwa falo gami da shimfida darduma ya yi nafila. Bayan idarwa ya yi addu'a. Masallaci zai fita, don haka sai ya koma dakin ya tashi Hajiya Zeenat sannan ya fita. Ta bishi da kallo har ya fice sannan ta ja tsaki tana miƙa, ta lura da wani ustazanci da ya soma. Sallah a masallaci ya daina wuce shi, ita dai tana jin tsoron ibadar da ya soma maida hankali a kai. Ko ba komai ai ta sani wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Ƙarfin ikon Allah da addu'a ya shallake dukkan ƙarfin mai ƙarfi.

  Jiki a sanyaye ta miƙe tana tunanin mafita.

'Ku bar ƙasar zuwa wata ƙasar kawai!'

Wani ɓangare na zuciyarta ya shawarceta. Sai dai tana tunanin ta yanda za ta sa Hussein ya amince da wannan shawarar da tun ba yau ba ta ke ƙoƙari a kai.

***
  Misalin shida na safe, iyalan gidan Alhaji Khalid Mu'azzam sun fito fess sun sha wanka har da yaransu idan ka dauke Ramlat da nata yaran ke gidan Muhibbat. Dalilin yaran ne Ramlat ta yi ƴan soye-soye na snacks da zasu ci a hanya.
Ta sha adon doguwar rigar atamfa kalar ruwan toka da sirkin ja da yellow an mata dinkin Bubu. Ta ɗora ƙaramin mayafi kalar ja a samansa. Murmushi ta ke sai dai iyakarsa leɓɓanta bai kai ga shiga zuciyar ba. Tunani goma da ashirin take duk ita daya, rayuwar yaranta, auren Chairman, soyayyar Hussein da ta ke ji kamar Son Maso Wani ta ke yi kawai. Wannan ne yasa da safe ta tashi idanun ƙozai-ƙozai shaidar bacci bai wadaceta ba.

Bayan sun ɗuru a motar da Munir yasa aka hayo musu ta kasuwa, tana daga can baya tare da yara sai Hunainah a ɗayan gefen. Ta bude whatsapp, ta gwada yiwa Hussein sallama sannan ta sanarmasa da tafiyar da za ta yi zuwa Daura. Daga nan ta sauka online ta kira Amrah suka ƙara sallama. Ba ta son yi mishi text gudun kada ya faɗa hannun Hajiya Zeenat.

'Koda shi ne abu na ƙarshe da zan maka, in sha Allah zan yi Hussein. Zan sulhuntaka da ƴan uwanka.'

Abu na farko da ya faɗo ranta bayan wannan tunani, shi ne Kawunsa da aka ce yana zama a Kano. Da dabara za ta nemi cikakken sunansa a wurin Hafsat, sauƙinta ma unguwarsu ɗaya da kakanninta (Hajja).

Ta toshe kunnuwanta da earpiece tana sauraron Suratul Maryam tana bi a hankali idanunta a lumshe. Wakokin soyayya ba ta da muradinsu a lokacin kasancewar ba karamin ingiza zuciyarta suke yi ba akan Hussein.

Tafiya ta yi nisa, shiru na ƴan sakanni, karatun ya tsaya, ta duba. Kira ne daga Hussein. Kirjinta ya bada dam! Ta ɗaga ta yi sallama a hankali tana mai satar kallon su Hajiya, hirarsu suke yi na dangi yayinda Hunainah ta rufe kanta da mayafi alamun bacci ya ɗauketa ko zai ɗauka, ba ta da tabbaci.

"Tafiya ba sallama? Ba ki faɗamin ba sai yau?"

Daga yanda ya yi furucin za ka fahimci ɓacin ransa.

Daƙyar ta iya motsa leɓɓan.

"Ka yi hakuri."

Shiru ya biyo bayan can kuma ya sauke ajiyar zuciya.

"Naso yau na ganki."

Ta yi luum da idanu, ta kasa yarda da abinda kunnuwanta suka jiyemata.

"Uhm?" Ta nemi ba'asi.

"Hoton zan karɓa ta ƙarfi tunda an hana ni."

Ya faɗi a shagwaɓance, ya sanyata murmushi tana mai sunkuyar da kai kamar yana gabanta.

"Zan turomaka."

"Promise?"

"Yes."

"Kinsan hoto ɗaya rowa ce ko?"

Ta ƙara faɗaɗa murmushinta.

"Uku fa?"

Tana jin sautin murmushinsa. Can ya amsa.

"Thanks. Allah Ya kaiku lafiya."

Bai jira amsarta ba ya katse kiran, karatun ya ci gaba. Kaso saba'in na damuwarta ya ragu, ta ji wani kwarin gwuiwa. Nan da nan ta shiga Gallery dinta ta hau kallon hotuna. Duk wanda ta ga shi ya dace ta aika sai ta ga kamar bai kai ba. Ruwan ido, abinda ta tsana ta ke jin haushi a wurin Amrah, ita ce yau ta ke yinsa. Dakyar ta haƙura ta zaɓi wasu guda uku ta aika kasancewar da network a wurin da suke nan da nan ya je, ba ta jira godiyar ba ta sanya wayar a Airplanemode tana murmushi.
  Koda suka isa yan uwan sun sha mamakin sauyawarta. Ƙofar Baaru kusa da gidan Sarkin Daura, nan ne ainahin gidan iyaye da kakannin su Abba da Hajiya yake. Gida ne babba na gandu, zaman iyaye da ƴaƴa. Sun tarar da su Nusaiba mutan Kano duk an hallara. Hajja da abokiyar zamanta ma suna nan. Gida ya cika da ƴan uwa gwanin dadi. Sashen Ƙanin Malam Abdullahi kakanta nan ta yada zango wurin su Nusaiba sa'anninta, don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login