Showing 147001 words to 150000 words out of 226732 words
ya tsami banza. Kamar yanda kin sani, na sani, komai nisan jifa ƙasa zai faɗo. Toh idan ba mu yi dagaske ba, asirinmu na dab da tonuwa."
Nan da nan ta haɗe rai.
"Me kake nufi?"
Kawu Modibbo ya gyara zama yana mata kallon ƙyar.
"Wata yarinya ta zo min da zancen da ya rushe dukkan walwalata. Tana ƙoƙarin shaidamin cewar ta san inda Husseini yake, duk da ba ta fito fili ta yi bayanin komai ba, amma daga yanda ta ambaci shi Hassan ta alaƙantashi da Husseini shakka babu akwai babban al'amarin da ta sani."
"Ya sunanta?" Hajiya Zeenatu ta nemi sani a hanzarce yayinda kirjinta ke bugu, tana tsoron kar hasashenta ya zama gaskiya. Sai dai abinda ta guda shi ya faru, sunan da ta ke fatan kar ta ji, shi dai ta ƙara tsinkaya daga bakin Kawu Modibbo.
"Ramlatu ta ce sunanta."
Wani miƙewa da Hajiya Zeenatu ta yi sai da shi kansa Kawu ya ƙara tsorata. Jikinta ya shiga rawa nan da nan idanunta suka kaɗa.
"Baƙa ce, ba ta da jiki sosai kuma.."
"Abinda ya tunkaro mu, ya fi ƙarfin mu tsaya ɓata lokaci a kan suffantawa ba. Ki faɗi kai tsaye idan kin santa."
Ya faɗi cike da ƙagara. Ta haɗiyi miyau tana goge gumin goshi.
"Tsinanniyar yarinyar da aka sha yimin gargaɗi a kanta kenan! An tabbatarmin muddin ban nisanta Hussein daga duniyarta ba, to shakka babu komai zai lalace. Kenan yanzu ta gano dangin Hussein? Wannan mayyar ina ce?!"
"Mafita za mu nema. Kin sani, baragurbin kwai idan ya fashe, yakan shafi kowa ba mutum guda ba. Za ki fi ni shiga matsala. Kin san komai don haka a bar kaza cikin gashinta. Tun lokaci bai ƙure ba ya kamata a ɗau mataki."
"Kasheta zan sa a yi."
Kai tsaye ta furta tana fidda hucin ɓacin rai. Kawu ya dubeta sosai, duk da cewar yana shuka abubuwa a doron ƙasa, bai taɓa tunanin ya kashe rai ba.
"Kina ganin hakan zai haifar da ɗa mai ido? Kisa na nufin abubuwa da dama ciki kuwa har da rabuwarki da shi Hussein don za ki ƙare a kur..."
"Dakata, ai ba ni zan kashe ba. Zan saka a kashe ne. Mace ƴar uwarta zan saka, ita kanta ba za ta fahimci komai ba. Na santa a bakin Dikko, mayyar kuɗi ce da za ta iya aikata komai saboda shi. Don haka ka bar min wuƙa da nama yanda ka ce, za ka sha mamaki nan da awannin da suka rage kafin safiya."
Kawu ya jinjina kai, suka ƙara shawarwarinsu sannan ya fice.
A gaggauce Hajiya Zeenat ta kira Hajiya Batool ta ba ta labarin komai har shawarar da suka yanke.
"Wannan ya yi kuma ina goyon baya dari bisa dari. Gwara tun wuri a yi ta kuma ta ƙare."
Da wannan suka yi sallama ta kira Chairman a waya. Cikin gaggawa ta ce
"Ka turomin lambar yarinyarnan."
"Wa?" Ya nemi sani.
"HALIMA."
Dariya ya ɗan yi mai sauti, sanadin Halima ya san duk wani tarihi na Ramlatu, duk da cewa ya san da biyu ta faɗamasa, amma ya zamar masa tamkar ƙarin makaman yaƙi a wurin iyayen Ramlatun har ya same ta. Sanadin wannan ne ya sanya har holewa ya yi da ita na sati kafin ya biya ta da maƙudan kuɗaɗen da suka kusa zautar da ita.
"Wani abu ne ya taso?"
Ya nemi sani.
A ɓangaren Hajiya Zeenat ta ja tsaki.
"Wankim hula ke neman kai ni dare, turomin yanzu-yanzu."
Daga haka ta katse kiran ta kwashi tarkacenta ta fita. Ba zai yiwu su tattauna da Halima a wurin ba. Hussein zai iya shigowa kowane lokaci.
Tun kan ta kai motarta lambar Halima ya shigo. Kai tsaye ta ɗauka ta kira bayan ta daidaita zama cikin mota ta rufe.
"Hello."
Halima ta furta.
"Kina magana da Hajiya Zeenatu mamallakiyar A&Z."
Hajiya Zeenatu ta yi shiru don ba ta san ta ya za ta soma bayani ba. Ga mamakinta sai ji ta yi Halima ta ce.
"Lah, na san wurin ai ina zuwa lokaci -lokaci. Ai kin taɓa zuwa inda nake aiki kwanaki can kika biya kudin haraji. Na sanki sosai. Ranki ya dade, Allah Ya ƙara girma."
Murmushi Hajiya Zeenatu ta yi, dagaske ba za ta samu matsala da wannan ba. Don haka ta muskuta.
"Halima ina son ganinki, idan ba damuwa a yau kuma a yanzu."
"Aa babu wata damuwa Hajiya, ki fadi inda zan zo na sameki kawai."
Nan Hajiya ta yi mata kwatancen gidan Hajiya Batool. Ta dinga amsawa daga bisani suka yi sallama bayan Halima ta tabbatar mata yanzun za ta taho.
***
Hajiya ta isa unguwar Yakasai ranta a tsananin ɓace, ko sashin Hajja ba ta shiga don tasan tsaf za ta hanata tada kowace magana. Kai tsaye ta wuce rumfar Malam Bello inda anan ne yawanci Kawunnan ke zama a sha hira kuma a tattauna matsaloli. Da yake rana ce, aikuwa ta ci sa'a ganinsu a rumfar. Su biyar zaune, Kawu Bello, Kawu Sunusi, Kawu Jamilu, Haruna sai Usman.
Kawu Bello na ganinta ya haɗe gira, ta ƙarasa ta zauna aka gaisa.
"Sai kuma kika ji an turo kuɗin Ramlatu ko?"
Kawu Usman ya furta yana washe haƙora da duk goro ya ɓata. Ta haɗe gira.
"Na ji Yaya, sai dai sam ba'a kyauta ba. Ba ku yiwa yarinya daidai ba. Kada ku manta Ramlatu ba yarinya ba ce yanzu, addininta ya ba ta damar zaɓen miji a karon kanta. Idan ma ku ka dauke batun ta, na tabbatar ku kanku ba ku tsaya wani dogon bincike a kan mutuminnan ba saboda.."
"Saboda yana da kudi ko? Haka kike so ki ce! Wato mu gamunan mayun kudi? Rabi yaushe kika sauya haka? Kina son ki nunamana ke da Khalid ku ka haifi Ramlatu?"
Kawu Bello wanda tun zuwanta ya ke a fusace shi ne ya hau wannan kumfar bakin. Hajiya ta ɗago ta dubeshi don tuni ta soma hawayen idanun sun ƙanƙance.
"Ba iko nake nunamaku da Ramlatu ba, amma fisabilillah duk irin munin ɗabi'u mutuminnan da na lissafamaku a baya bai hana kun murzawa idanunku toka ba kun ba shi damar ya turo kuɗi. Wannan auren ba zai taɓa yiwuwa ba idan har ina raye, ku gafarce ni amma Ramlatu ba za ta auri Chairman ba."
"Yanzu na fahimci inda Ramlatu ta ɗauko kafiya da taurin kai. Ashe ba a ƙasa ta kwasa ba, a nono ta tsotsa. Wato yanzu da babu ran Malam shi ne ki ka samu kwarin gwuiwar cin karenki babu babbaka Rabi. A baya ke yarinya ce mai takatsantsan da ɓacin ran ƴan uwanki, amma saboda kin haifa, kina kuma taƙama da dukiyar marayun yaranki da ubansu ya bari, shi ne za ki wulaƙantamu. To gwara da aka yi tusa ai halin kowa ya fito."
Sosai kalaman Kawu Haruna sun soki zuciyar Hajiya kamar mashi, ta kalleshi ta kasa magana. Sai Kawu Usman ya sa baki
"Ni abinda ban gane ba Yaya Bello, kai da bakinka ka tabbatarmin da yardar Ramlatu a auren wannan mutumin, yanzu kuma sai na ke jin sabon labarin da ya sha bamban da wanda na sani. Wato dai dole ne za ku yiwa yarinya? Wannan ai ba girmanmu ba ne."
Ya fadi a sanyaye amma ransa a ɓace, haka yake mutum mai hakuri da gudun duniya. Sai a lokacin Kawu Sunusi ya tanka ta hanyar zubawa Usman daƙuwa.
"Ka ci ƙaniyarka Usmanu, mu sa'anninka ne da za ka yi fito na fito da mu? Ai ko Murja ba za ta yi mana haka ba."
Kawu Usman jin Kawu Haruna yana sanya Yayarsa ciki ya sa shi jan baki ya yi shiru sai dai ya rantse ba zai ƙara sa hannu a cuci yarinya ba.
"Aa Haruna, zancen Usmanu gaskiya ne, ni kaina ai shi Bello cemin ya yi da amincewar yarinya aka yi komai. To ba za ta saɓu ba, ke Rabi ki je. Ni da kaina zan yi kiran shi Dikkon na ba shi hakuri. Ita Ramlatu ta je ta ciro kudin ta turomin da hannuna zan ba shi."
Kawu Jamilu ke maganar a daure, kasancewar shi ne babbansu a wurin don daga Kawu Yakubu sai shi, kuma bai fiye magana ba sai ta ɓaci wannan yasa suke ɗan shakka-shakkarsa. Kawu Bello ya soma share gumi, babu abinda ke ba shi tsoro sai yanda zai yi ya biya kuɗaɗen da ya ci na Chairman. Ƙananun filaye har biyu ya siya ba tare da sanin ƴan uwannasa ba. Wannan tashin hankalin ya sa ya kara magantuwa.
"Haba Yaya, ka mance da auren Ramlatu na baya? Ka mance irin tijarar da ta yi mana? Yanzu Rabi ke har kin mance kina ɗauremata gindi?"
Hajiya wacce ta ke jin ya zamemata dole ta koma wajen Malam Mu'azzam ƙanin babansu na Daura ta yi shiru ba ta ce masa uffan ba. Suka ci gaba da ja in ja, daga ita har Kawu Usman ba wanda ya ƙara tankawa. Kawu Jamilu ya kafe lallai a mayar da kudi yayinda Bello da Haruna suka ce sam ba zai yiwu ba. Wannan ne karon farko da suka yi mishi musu a rayuwa. Ko ba komai shima Haruna ya ci rabonsa. A karshe dai Hajiya ta mike ta wuce sashin Hajja ina ta tarar da Zulaihat zaune su na tattauna maganar.
"Aa, kenan dagaske dai Uwani ta ke za ki zo?"
Hajiya ta harari Zulaihat wacce ita kuma yanda idanun Hajiyar ya yi ja ya ɗaga hankalinta. Ta koramusu duk yanda aka yi. Hajja ta yi salati.
"Ke Rabi! Ban ce ki bari zan je na same su da kaina ba?"
Hajiya ta girgiza kai.
"Ki bar ni kawai Hajja, ni yanzu gobe ma Daura na nufa zan je na sami Baba Mu'azzam da kaina mu tattauna."
"Hakan ya kamata ki yi tun farko ba yanzu da muka dawo ba. Meyasa tun acan shi ba ki mishi bayani ba sai yanzu da ki ka je kike kokarin rushe zumuntarku da ƴan uwanki."
Hajiya ta kalli Mahaifiyarta da mamakin furucinta, ga dai Hajja girma ya ja amma kyawun jikinta yasa ta ke nan ƙyam da ita tubarakAllah.
"Ƙarya na yi kike kallona Rabi? Meyasa za ki tunkare su, ni ban isa ki zo ki fara shawarta ta ba shi ne za ki yi gaban kanki. Yanzu idan wannan ya haɗaku rikici fa? Mun cika alƙawarin da muka ɗaukarwa Babanku kafin rasuwarsa na ganin zumuncinku ya kara ɗanko?"
Hajja ta karashe gami da fashewa da kuka. Hankalin Hajiya da Zulaihatnya tashi, suka shiga ba ta hakuri da neman gafara, dakyar ta sauko ta kuma yi mata fada sosai.
"Idan irin haka ta faru ba'a yanke hukunci cikin fushi. Hakuri ake yi da kuma kai zuciya nesa."
Ta amsa da toh tana sharar kwalla.
***
Zufa sosai ya shiga ketowa Halima, kirjinta na dukan tara-tara. Da gaskiyar ƴar uwarta da ta taɓa gargaɗinta akan son abin duniya.
_*"Watarana idan ba ki yi hankali ba Halima, son kudinki zai kai ki ya baro. Kuɗi sheggun abu ne da idan har ka sa a ranka za ka aikata komai don ka same su, toh ina mai tabbatar maki cewa wataran za su yi sanadin rushe rayuwarka."*_
"Kin yi shiru Halima."
Hajiya Batool ta faɗi tana murmushi yayinda Hajiya Zeenatu ke kallonta cike da nazari tana shakkun ko za ta yi musu abinda suke so.
"Ba fa a kyauta za ki yi wannan aika-aikar ba. Hajiya Zeenatu za ta dauki nauyinki ki je duk ƙasar da kike so ki rayu cikin aminci da walwala. Za kuma ta ba ki gida da mota mallakinki. Ke ba wannan ba, duk abinda kike so za ta yi maki. Kawai ke dai ki aikata abinda muke sonki da shi."
Halima da jikinta ke kakkarwa ta sharce gumin da sanyin Ac bai sa sun fasa zuba ba. Duban Hajiya Zeenatu da Batool take kamar wasu zakuna wanda kwakkwarar numfashi idan ta fitar bai musu ba za su tashe ta daga aiki yanzun. Ta yi shiru tana nazarin kudaden da kuma sauyin rayuwar da za ta samu.
_*"Abu ne da kika jima kina nema, kullum kina cikin kallon hotunan ƴan film da yaran masu hannu da shuni kina kwaɗayin ki samu fiye da haka. Lokaci ne ya yi Halima, mene don ki kashe rai ɗaya tilo kin gudu? Nawa aka yi?"*_
Nan da nan ta samu wani irin sukuni a ranta. Da murmushi ta ɗago ta dube su wannan karon. Wannan ya sa suka dubi juna su ma suka murmusa.
"Hakan na nufin kin amince?" Cewar Zeenatu.
Ta gyada kai tana dariya.
"Ɗari bisa ɗari na amince Hajiya, na tsani Ramlatu sai dai ban zaci zan iya kasheta ba, amma yanzu yanda nake ji zan mata duk abinda ya kama idan har hakan na nufin samun ɗaukaka ta a duniya. Na dai so ace tana raye za ta ga yanda Halima za ta zama, amma ba komai, yaranta za su gane mata."
Ta ba su dariya sosai har da cafkewa. Sai kuma aka shiga tattauna yanda za'a yi komai kuma a darennan. Ta yi shiru tama sauraronsu tana gyada kai. A karshe ta ce.
"Na amince. Duk yanda ku ka ce zan bi na yi."
Murmushi Hajiya Zeenatu ta yi.
"Yauwa ƴar gari, yanzu bani lambar ita Ramlat din. Ki tabbata kin isa wurin kafin ta je."
"An gama ranki ya daɗe." Tana kai wa aya ta ciro waya ta ba ta duka lambobin Ramlatu guda biyu sannan suka Hajiya Zeenatu ta ba ta kudi har dubu ɗari wai ta ɗan taɓa. Wannan ma ya ƙara zuzuta Halima. Ta fice da murnarta da kuma ɗaukar ALWASHI.
***
Hajiya da Zulaihat suka zauna saman kujera, Ramlat ta fito daga ɗaki da sauri. A farko ta yi zatom shiriritar Ansar ne da ya ke batun dawowarsu. Lokacin ƙarfe shida na yamma, don haka ba su yi wani dogon zance ba sai da aka idar da Magriba.
Zama suka yi Hajiya ta ba Ramlat labarin duk yanda aka yi.
"Ai yau ba gobe ba, ki je ki fiddo kuɗaɗen nan ki kawo su kwana a hannuna. Da kaina zan koma na kai wa Yaya Jamilu."
Ramlat kamar ta rungume Hajiyarta don dadi, ta dinga godiya da addu'a. Murmushi kawai Hajiya ta yi.
"Shikenan ma kinga sai ki ragemin hanya."
"Kai Maman Twins, nan da nan ba mota zan ɗauka ba."
"Haba ƴar Hajiya ƴar gatanta, daure don Allah muje da mota kinga ko yaya kika ɗan ragemin zai min sauƙi."
Ramlat ta yi murmushi.
"Baƙonmu ya zo?" Hajiya ta tambaya.
"Eh tun ɗazu, yanzu ma nake shirin zuwa na kirashi mu yi magana. Wallahi duk ya matsu."
"Wa kenan?" Zulaihat ta nemi ba'asi.
Nan Hajiya ta labarta mata, sosai ta ji ya ba ta tausayi.
Ramlat ta mike ta yiwa AlHassan iso, suka gaisa da Hajiya da kuma Zulaihat, a karshe suka yi mishi addu'ar Allah Yasa a dace da abinda ake nema ya yi ta jin dadi da godiya. Bayan fitarsa Ramlat ta bi bayansa gami da ba Zulaihat hakuri kan yanzun za ta dawo. A harabar gidan suka zauna saman kujera. Ya gyara zaman gilashinsa yana dubanta.
"Nema ne da muka jima mu na yiwa Hussein, yanzu sai abin kusan muke tunanin ya zo ƙarshe idan har yana raye kuma yana hannun matarnan."
Ya ba ta labarin duk yanda suka yi da Rasheed abokin Hussein, ya ƙara da fadin.
"Don Allah my sis idan har da wani abu sa kika sani game da matarnan kar ki ɓoyemin. Jikina yana bani ɗan uwana yana raye."
Tausayi sosai ya bata don har idanunta suka cicciko da kwalla. Ta sharesu.
"Ka kwantar da hankalinka, labari ne mai tsawo kamar yanda na faɗamaka. Shakka babu nasan inda Hajiya Zeenatu ta ke kamar yanda na sani cewa Hussein yana tare da ita tsawon shekarun da ku ke nemansa."
Ai wata irin zabura da Alhassan ya yi ya mike tsaye sai da ya razanata.
"Dagaske kike?! Hussein na hannunta?! Ya akai kika san Hussein din?! Tashi muje ki kai ni wurinsa don Allah."
Jikinsa har rawa yake yi, ga mamakinta ma hawaye ya soma. Dakyar ta kwantar da hankalinsa.
"Don Allah ka zauna mu yi magana. Idan har daga jin wannan ka shiga ruɗani, ta ya za ka iya amsar dukkan labarin da zan ba ka?"
Hakan da ta faɗi sai ya koma mazauninsa yana jero hamdala ga UbangijinSa. Lallai kukansu ya zo ƙarshe. Hawayen Dada zai daina zuba.
"Mami! Mami!!"
Suka dubi yaran, AlHassan na ji kamar ya zanesu don sun katsemishi hanzari. Wayarta ce su ke kokarin miƙo mata. Ta karɓa tana fadin mene.
"Kira aka yi kuma an miki saƙo."
Fadin Ummi, ta karba ta basu umarnin su koma ciki. Har za ta ajiye wayar saman cinyarta, ta hangi suna kamar ma Hussein a karshen saƙon da aka turo wacce lamba ce.
"Yi hakuri don Allah." Ta faɗi a gaggauce, hannu na rawa ta buɗe.
_*"Za su kashe ni. Ramlat ke kaɗai za ki iya taimakamin. Ki zo ki cece ni. Hussein."*_
Ta karanta ya fi sau uku, hannunta na rawa, wani saƙon ya ƙara faɗowa. Adireshin wurin da yake ne kawai.
"Wai meye haka? Innalillahi." Ta furta tana mai mikewa da fashewa da kuka. Da sauri AlHassan ya karɓi wayar don dama ba a nutse ya ke ba. Yana karantawa ya dubeta.
"Hussein ɗina zaa kashe?! Su waye? Taho mu je!!"
Duk a hargitse ya yi wannan kalamin, ya nufi motarsa amma mukullin na ɗaki, don haka a guje ya koma ciki har yana mance ɓangarensa a gidan yana faɗawa falon Hajiya, ganinsa a rude yasa Hajiya miƙewa tare da Zulaihat.
"Lafiya?" Suka nemi sani. Maimakon ya amsa sai ya kasa don haka ya fice, Allah Ya taimaka ya gane dakin, ya shige ya dauki mukullinsa a aljihun kayan da ya fidda. Su Hajiya tuni sun fito harabar gidan inda Ramlat ke safa da marwa cike da tashin hankali tana kuka kamar ranta zai fice.
"Meke faruwa?" Tuni AlHassan ya tayar da mota yana mata horn. Ta dubi su Hajiya.
"Za su kashe Hussein."
"Ki taho mu je ko?!"
Tsawarsa ta sa duk suka dubeshi, su Hajiya na ta salati gami da fadin.
"Kai Hassan kar ka yi tuƙi a wannan yanayi! Ka tsaya!"
Amma ina! Ramlat ba ta ƙarasa rude ƙofar ba ya ja, Baba Maigadi tunda ya ga an tayar da mota ya tsaya bakin gate, ganin ya taho kawai sai ya buɗe masa.
Ita ce ta dinga yi mishi kwatance, sai dai kafin su kai wurin saƙo ya ƙara faɗowa.
"Dakata!" Ta faɗi da