Showing 114001 words to 117000 words out of 226732 words

Chapter 39 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12472

an faɗamin. Ina fatan dai za ki saki jikinki ki ajiye kauyanci gefe ki ci arziki inda kika ganshi."

Ɗan haɗe gira Ramlat ta yi tana mata duban ido cikin ido.

"Bangane hausarki ba, me kike nufi?"

Dariyar ƴan duniya ta yi.

"Dama ba lallai ki gane ba, amma nidai ina mai ba ki shawarar kar ki yi wasa da damarki."

Daga nan ta ficewarta ta bar Ramlat tsaye. Wani murmushi ta yi gami da girgiza kai itama ta soma tafiya nutse.
Ta rasa ranar da Halima za ta nutsu ta yi hankali, kullum tunaninta iri guda ne.

'Allah Ya shirya.' Ta furta a ƙasan ranta.

***

 
"Wannan asarar kuɗi har ina wai?!! Duk aikin da na ɗauko sai ya lalace! Abu ne da bai taɓa faruwa da ni ba duk tsawon wannan shekarun! Ina tsoro kuma."

Hajiya Zeenat ke wannan ƙorafin kamar ta zubda hawaye a tsakar falon Hajiya Batool da misalin ƙarfe uku da mintoci na rana.

"Ni na rasa ma me zan ce. Kusan duk  yanda aka kurantamana wannan mutumin ba haka muka riska ba. Kinga yanzu wai yaronnan Dubai zasu wuce da shegiyar yarinyarnan siyayyar kayan haihuwa? Ban isa na faɗi aibunta ba zai hau ni da  faɗa kamar shi ya haifen."

Tsaki Hajiya Zeenatu ta ja.

"Ke naki ai da sauƙi tunda ba mijin bane, ni ina miki maganar duk aikin da nayi sai ya lalace. Duk abinda na ɗauki niyyar na yi sai kiga an yi rashin sa'a a kai. Jikina ne ke yin sanyi, amma ba zan karaya ba. Har abada kuwa."

Ta ƙarashe tana mai goge zufa sa'ilin da kwakwalwarta ta tafi ga tunanin wani abu da ya kasance a can baya wanda nan da nan ya jefamata tsoron da ta ke gujewa a zuciya.

"Toh wai me zai hana mu koma wajen Gora? Kamar dai aikinsa ya fi na wannan buzun. Duk buge ce."

Jinjina kai Hajiya Zeenatu ta yi.

"Kuma hakane, kin fadi gaskiya."

Cewar Hajiya Zeenatu cikin karaya, yanzun dai ta saduda, banda ma asarar kuɗi, aikin ma da ta yi nema ya ke ya rushe, nema yake ya zama tamkar ba ta taɓa yi ba. Ita da kanta ta soma ganin sauyi acikin rayuwar Hussein. Ya rage shakkarta.

Suka yi ta tattauna yanda zasu ɓullo wa matsalolinsu kafin su yi sallama su rabu zuƙatan duk babu dadi.

***
BAYAN SATI ƊAYA.

Tun shigowarsu garin na Dabo tumbin giwa Fatima ke ji kamar tayi fiffike ta yi ta zagaye gari tsabar farin ciki da jin dadin yau ga ta a Kano. Da wayonta haka dai ba ta taɓa zuwa ba. Don haka bakinnan nata a wangale ga hannunta riƙe da cakulet tana sha.

Uban ya dubeta yanda ta hakimce gaban mota, duk son uwar da haka, hakura ta yi don ba ta iyawa rigimar Fatima wani sa'in, zamanta ta yi kusa da Hafsat da Dada.

"Wai nikam Fatima kodai a Kanon zamu bar ki ne?"

Fadin Kausar tana dariyar yanda yarinyar ta kifa goshi a kan gilashi tana ƙarewa waje kallo.

Da wani ɗoki ta dubi Mamarta ta gyaɗa kai, yanda ta yi duk sai ta ba su dariya.

"Allah Ya rayaki dai Fatin Biyu"

Dada ta furta da dariya. AlHassan wanda walwalarsa ta ɗan ja baya tun shigowarsu garin sai a sannan ya ɗan saki fuska. Autar Dada ta ɗan dunguro kanta.

"Ke da ace za'a bar ta kinga alamar ba za ta zauna ba?"

Aka dara. Haka suka yi ta hirarrakinsu har suka kai gidan Kawunsu Modibbo.

Yana parking ya budemusu ƙofa kafin ya zagaya ya sa yara su fiddo akwatunan. Ya ɗaure fuska ya sauya kamar ba AlHassan ba mutum mai yawan fara'a.

"Zan je na dawo."

Abinda ya ce kenan, Dada ba ta yi mishi dole ba ganin sauyinsa, ta kauda kai don tasan ba da son ransa suka zaɓi kwana a gidan Modibbo ba madadin ɗaki a Hotel da ya yi niyyar kama musu. Suna shigewa ciki shima ya ja motarsa ya fice.

***
  Kausar ce tsaye bayan ta dawo daga ɗakin Amarya tana duban yanda Dada ta zage tana faman aiki tuƙuru a sashin Hajja Fatuma. Tana kallon yanda jikokin Hajja Fatuma suke yin yanda suka so babu mai kwaɓa balle magana, yaranta mata na hakimce saman kujera suna hira da sha'aninsu ita kuwa ta shiga cikin ƴan aiki ana gyaran kaji. Juyawa ta yi ta koma sashin Amarya dakin da suka sauka. Nan ta tarar da Hafsat tana sauyawa Fatima sutura zuwa na bacci, a gefenta Rasheeda ce, ɗiyar Amarya da zasu yi sa'anni da Hafsat. Su dai kam dama jininsu ya hadu don har chatting suna yi. Ganin yanda Kausar ta shigo fuska a ɓace yasa Hafsat gane inda zancen ya dosa.

  "Anti kin ce ta zo ta ci abinci?"

Sai a sannan ne ma ta tuna abinda ya kai ta wurin Dadar, ta ja guntun tsaki.

"Kinga halin mantuwa ko?"

Miƙewa Hafsat ta yi a fusace, ita kam yau sai ta taho da uwarta don ba bauta ta zo ba.

Za ta fice Kausar ta riko hannunta. Ta dubi Rasheeda.

"Don Allah kirawo Dada."

Rasheeda ta mike ta fita. Ta riga ta san komai dangane da irin tsangwamar da Dada ke sha a wurin Hajja da Modibbo mahaifinsu har ma da wasu cikin ƴan uwansa.  Ta kuma rasa dalilin wannan ƙiyayya, a ganinta abinda ya wuce ya riga da ya wuce.

"Kai Adda, nidai wallahi da kin bar ni na je, na gaji da wannan abu. Tun zuwanmu awa nawa yanzu ace Dada ko abincin kirki ba ta ci ba? Daga zuwa gaishesu ta dawo sun haɗata da aiki don rashin tausayi, kuma shi ne ita ta karɓar? Nidai sai na gayawa Hamma.."

"Kul! Kar ki soma. Kinsan dama ba da son ransa aka yi wannan tafiyar ba, abin ya zo mishi ne a ba yanda ya iya. Yanzu kika kirashi tayar da hankalinsa kawai za ki yi kuma ranmu ya ɓaci. Ke dai ki bi gargadin da Dada ta yi maki a rabu lafiya. Gasunan dai kinga su Hanifah duk suna zaune, nima ban ishesu kallo ba tunda a cewarsu ina auren AlHassan."

Yamutse fuska Hafsat ta yi.

"Wallahi Adda, Adda Hanifah ƙarya take. Son Hamma take yi kamar yanda ɗan adam ke son rayuwarsa. Ai inada labarin komai, kuma ma.."

Sai ta yi ɗif, sai yanzun ta ke tuna katoɓarar da ta yi, ta ɗan datse harshe da haƙori ta yi shiru. Dada da ke tsaye bakin ƙofa ta ƙaraso ta bata rankwashi a kai, ita kuwa Kausar dariya ma ta yi. A saninta ko giyar wake AlHassan ya sha ba zai auri Hanifah ba. Har abada ya tsani zuri'ar  Modibbo. A wani ɓangaren kuma itama ta san da wannan soyayyar ta Hanifah ga mijinta, takan ga kiranta sau tari a wayarsa, bai yi saving lambar ba, amma ita tana da lambar a wayarta. Allah Ya hana bincike, shiyasa ba ta zurfafa ba. Sai kuma sanin da ta yiwa Modibbo na bala'in son kansa da kuma ƴaƴansa, wannan ne waekness dinsa. Duk abinda yaransa ke so koda ba ya son abin, zai yi yanda zai yi ya nemamusu farin ciki. Wannan ya yi sanadin lalacewar wasu a yarannasa.

"Ke za ki biyewa wannan shashasha har ki wani tsaya zurfafa tunani? Kin yarda da abinda ta ce kenan?"

Dariya Kausar ta yi tana girgiza kai.

"Ko kadan." Suka ɗan dara, Hafsat ta turo baki. 

"Toh nidai gaskiya Dada ba zamu yarda da wannan aikin da kike fita ba, idan kika ci gaba zan kira Hamma."

Dada ta yi murmushi cikin harshen fulatanci ta amsa.

"Dayake shi ya haifeni ko? Banda abinki Hafsatu, ni da gida ɗan uwana? Wa ya fadamaki abinda na yi faɗuwa ce? Babu, zumunci na sadar kuma Allah zai duba."

  Ita dai Hafsat ta ja hannun Fatima suka fice zuwa falon Amarya. Banda Dada ta tilastamata kuma tana son zuwa gurin Rasheeda, ba abinda zai sa ta tako ƙafarta Kanon, a yanzun ma ji take da ace akwai wasu ƴan uwannasu can za ta yi tafiyarta.
  
  Da yammacin ranar AlHassan ya iso ƙofar gidan Modibbo, waya kawai ya yi ya ba Hafsat umarni fitowa tare da Fatima su yawata. Da wani irin ɗoki Hafsat ta mike ta shirya Fati suka fice ba su ko tsaya sallama da kowa ba banda Adda Kausar da suka faɗawa ta sanar Dada.

   Fuska ta daure ganin yanda Taheer ɗa ga Hajja Fatuma ya tsuramata idanu yana kallo. Bafulatanin usuli wanda daga ka ganshi ka ga jinin Mamman Gidado.
Dagasken gaske tana lura da yanda yake wani safa da marwa a sashin Amarya wanda hatta da Rasheeda sai da ta nuna mamakinta a fili, acewarta abu ne mai wahala ka ganshi a sashin nasu.

Har ta isa ta buɗewa Fatima gaban mota ta shiga itama ta bude gidan baya ta faɗa babu walwala. Alhassan ya dubeta yana murmushi sadda ya ja motar.

"Ke kuma ke da wa?"

Turo baki ta yi.

"Bakomai."

Ya taɓe baki. Ko me ya faru ai su suka sani, shi dai kam dama bai nunamusu yana son zuwan ba.

"Daddy ina zamu je?"

Cewar Fatima a ɗokance. Ya ja kumatunta da murmushi.

"Surprise ne."

Ya yi ta biyemata su na surutu har suka iso tafkeken shagon na A&Z.

   Hafsat sai a lokacin ta saki ranta, suka fito suka jera ciki. Da ka gansu ka san jini ɗaya ne.

Kai tsaye suka hau sama, ma'aikatan sai kallon AlHassan suke yi kusan a mamakance. Duk a zatonsu Mijin Madam ne, ganinsa da budurwa ya ba kowa mamaki, har da samari da ƴanmatan da suka mayar da wurin wajen zuwansu. Shi kuwa Alhassan wayar da aka kirashi ce ta sanya shi ba Hafsat kudade tare da ba ta umarnin ta suyamusu duk abinda ya dace, yana jiranta a waje.
Sauri yake sosai yana son barin hayaniyar cool music da ke tashi a wurin ganin Director ɗinsa na wurin aiki ke kiran. Magana ce za su yi mai muhimmanci. Karo ya ci da ita sadda ta sanyo kai nan take wayarsa ta faɗi, ya ɗago ita kuwa ta matsa baya gami da fadin.

"Yi hakuri fa."

Ɗagowar da zai yi sai da ta ji hantar cikinta ya kaɗa. Ba don ace tare suke tafe da mijinta Hussein ba, kuma yana cikin  mota sanye da kananan kaya, madadin wannan da ke sanye da shadda blue, za ta rantse shi ne tsaye. Murmushi ya yi mata da nunamata ba komai kafin ya yi gaba. Har tana tuntuɓe haka ta juya ga mararta da ta cika taf da fitsari, haka ta karasa ga Hussein wanda ya juyamusu baya yana kokarin rufe motar. Ganinta a gigice yasa shi dubanta da mamaki.

"Lafiya?"

Dafashi ta yi gami da riƙe kai.

"Lafiya, a'a ba lafiya, muje don Allah. Jiri nake ji shiga mu tafi."

Hussein dai abin ya dauremishi kai, zai yi musu abin mamaki Hajiya ke roƙonsa ya bar kowace magana a gefe su wuce su koma gida. Ba ta da lafiya. Dole ya shiga motar bisa umarninta itama ta shige. Ba ta samu nutsuwa ba sai da ya doshi gate, sai dai kafin ya kai ga fita jikinsa kawai ya yi wani irin la'asar yayinda ya ji kirjinsa na dukan uku-uku, ya kalli bayansa ta mirror. Bai ga kowa ba face wani matashin da ba zai fi shi a shekaru ba, tsaye jikin mota ya juyamusu baya yana amsa waya.

"Ya kake tafiya kamar ba ka so? Ka yi sauri don Allah."

Maganar Hajiya ta dawo da shi nutsuwarsa, ya ɗan ƙara ƙarfin gudun.

"Wai meke faruwa? Naga lafiya muka shigo wajennan."

Girgiza kai ta yi tana share gumi.

"Nima dai ban sani ba. Watakila plantain da kwai da na ci ne ya ɗan juyamin ciki."

"Kuma kika ce jiri?"

Ta ja guntun tsaki ganin zai ƙureta, ita dai yanzu ta fi kaunar a kyaleta tayi tunani mai kyau. Wannan ya nuna twin brother din Hussein ya zo Kano kenan? Lallai dole ne ta hana Hussein zirga-zirga. A farin farko dai za ta bincika ta ji dalilin zuwansa, idan har zama ne na dindindin, barin Kano na har abada ya gansu ita da mijinta koda ba ya so. Haka ta yi ta tufka da warwara, Allah-Allah take su isa yanda za ta samu damar yin tunani mai kyau.

  Shi kuwa AlHassan koda ya gaji da gaisuwar da wasu daidaikun ma'aikatan masu wucewa suke mishi sai kawai ya shige cikin motarsa ya zauna ya ci gaba da wayar. Har su Hafsat suka fito ɗauke da ledoji yana waya. Hayaniya kwakkwara hanasu ya yi, kusan har ya soma tuƙi suka yi tafiyar mintoci yana waya. Can dai ya katse ya ajiye, da murmushi ya dubesu.

"Sorry, ban kyauta muku ba ko?"

Fatima ta turo baki ta gyaɗa kai. Dariya ta basu.

***
  "Hajiya Ramlatu, ina son ganinki."

Shi ne abinda ya ce kenan bayan ta saka wayar a kunne. Ramlat ta ajiye kan wayar ranta na zafi, tsabar raunin hankalin Chairman ya soma isarta, tana kallon abin kamar da biyu yake yi.
   Ta mike ta gyara zaman naɗin laffayarta ta tabbatar ko'ina na jikinta ya ƙara rufuwa ruf sannan ta ƙarasa ciki.

Kallon haramun dai bai fasa ba don haka ta daure fuska.

"Gani Yallaɓai."

Ta faɗi a ladabce cikin basarwa don yanzu ta bar ganin ƙima da mutuncinsa.

"Amm..yanzu a kan aiki muke don haka ba zan ce komai ba. Sai dai idan ba damuwa ko za'a yimin iznin zuwa gida?"

'Anzo wurin.' Ta fadi a ƙasan ranta. Girgiza kai ta yi.

"Ka yi hakuri Yallaɓai..."

"A'a kinga Ramlat, ba batun nayi hakuri bane. Tsakani da Allah ba zan iya ba. Na fadamaki yanzun muna bakin aiki ne, magana ce kuma zan zo muyi ta fahimta."

Shiru kawai ta yi, ganin ta ƙi ce mishi uffan ne ya sa shi magana.

"Zan ba ki daga nan zuwa Monday, please ki yi tunani mai kyau. Ki sani, koda ace a baya sharri ne a zuciyata, yanzun babu ɗigon wannan Ramlatu. Wallahi babu."

Yanda yake magana kamar wani yaro sai ma ya so ba to dariya, ita dai ba ta ce komai ba.

"Shikenan kina iya tafiya."

Ta juya ta fice ba ta ce mishi uffan ba, Chairman ya bita da kallo kafin ya lumshe idanunsa ya sauke ajiyar zuciya. Sanin gidansu Ramlat abu ne mai sauƙi a wurinsa, sai dai ya fi kaunar bi ta hanyarta ko don ya goge wannan kallon girma ya faɗin da ta ke yawan jifansa da shi. Ko ba komai dai da gaskiyarta. Da niyyar cuta ya zo sai soyayyarta na gasken ya sauya komai.

***


 I just published "BABI NA TALATIN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/4aFXFyDdjbb

🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

37)


LAMIƊO CRESCENT

"Ki soma faɗamin wannan ƙullen da kike yimin na mene wai? Ina da aikin yi, kin hana ni fita."

Hussein ke maganar a tausashe da ɓacin rai saman fuskarsa. Zeenatu dubansa take yi don ta rasa ma hanyar ɓullo mishi. Ba ta son fitarsa, jinta take kamar wata zararriya, gaba daya babu aikinta ɗaya da ya tafi daidai. A baya ta rantse ba za ta bar garin Kano ba amma kam a yanzun a shirya ta ke da yin nesa da duk abinda zai sa Hussein ya suɓucemata.

"Tafiya zamu yi, Kano nake son mu bari."

Kallonta kawai yake yi cike da tunanin meke damunta har haka. Dariya ta so kwacemasa don shi kansa yana mamakin irin ƙwarin gwuiwar da ya ke samu na yi mata jayayya akan duk abinda ya zartar a yanzun.

"Kinsan me kika ce kuwa?" Ya fadi kansa tsaye yana kallonta har sai da ta ji ƙirjinta ya bada dam! Dakyar ta haɗiyi yawu.

"Me kake son ka ce? Jayayya za ka yi da ni? Ba za ki bi ra'ayina ba?"

Ya yi shiru kawai yana kallonta da wani mamaki, wani tsana yake ji kamar yana son tasomishi sai wata soyayya da bai san mafarinta ba ta zo ta danne wannan tsanar. Kauda kai ya yi gami da miƙewa daga saman gadon.

"Kiyi hakuri, abu ne da ba zan iyaba."

Daga haka ya faɗa banɗaki. A gigice Hajiya Zeenat ta miƙe ta fice zuwa ɗakinta. Wanka ta yi a gurguje ta shirya. Kamar yanda ta zata hakan ce, ya shirya da zummar zuwa ofis. Bai yi mamakin shirin da ta yi ba illa murmushi da ya yi, abin kam ya ba shi dariya. Wannan bibiyar bai san kuma ta mece ce ba duk da a bayan ma tana yi mishi don wani sa'in kamar daga sama haka yake ganinta a  ma'aikatarsu.

  Ya shirya suka fita tare, ita ke tuƙi don a cewarta za ta fita daga nan duba Hajiya Batool ba lafiya, bai damu da gasken take ko a'a ba. Ya dai amsa zuciyarsa a ɓace.

***
Tuƙinta cikin nutsuwa take yi, yau gaba daya ta makara a dalilin zazzaɓin da ya kama Ansar sai da ta kai shi asibiti tukunna ta maida shi gida. Ta so ta ƙi zuwa sai dai hakanan ta daure tunawa da aikin duba wasu files na Tax.
   A harabar wurin parking ta ajiye motar ta ƙarasa ciki. Ko zama ba ta kai ga yi ba wayar dake saman tebur ta ɗau ƙara, tsuke fuska ta yi gami da jan tsaki ciki-ciki. Tun sadda suka yi haka da Chairman ta ƙi jinin abinda zai sa ta haɗu da shi sai dai ba yana ta iya. Wayar ta ɗaga da sallama, ya amsa gami da ba ta umarnin ta je. Dire wayar ta yi ta ajiye jakarta ta fita bayan ta gyara zaman hijabinta.

Yana zaune da manyan kaya har da babbar riga, idanunsa sanye da gilashi yana danna laptop. Shigowarta yasa shi kallonta.

'Ban yafe ba.' Ta furta a ƙasan ranta. A fili kuwa gaidashi ta yi a ladabce, ya amsa yana wani washe haƙora. Bayan gama jin dalilin da yasa ba ta shigo da wuri ba ya gangara kan abinda ke cin ransa. Chairman ke kiran yana sonta, dama tuni ta riga ta gane.

"Ke ba yarinya ce karama ba, nasan kinsan me nake nufi kike kaucemin. Wallahi na gaji, bani da burin da ya wuce na aurenki a yanzu Ramlat. Don Allah kar ki ce za ki ƙi. Na miki alƙawarin gidanki daban, ba zan haɗaki da matana ba."

Ya kammala surutansa tana sauraro, ƙarshe ta soma da ba shi hakuri.

"Inada wanda zan aura don har anyi magana."

Wata dariya ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login