Showing 222001 words to 225000 words out of 226732 words

Chapter 75 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12442

ta ƙaraso. Hannu kawai ta ɗagamata shaidar inda take ya ishe ta.   Sai da aka kira dangin Ango Tahir  don su yi liƙi sannan ta mike suka ɗunguma har su Teema, a hanya suka haɗe da su Rafee'ah aka shige fili, Maman twins na rantsuwar a farko ba ta ganeta ba. Sai dai su na liƙin tuni mazan suma suka taso don zazzage nasu aljihun, ta ɗaga hannu da nufin somawa ya kai hannunsa saman nata. Juyowa ta yi har fuskarsu na haɗuwa numfashinsu na gauraya wuri ɗaya.  A hankali ya zare kudin a hannunta ya shiga liƙawa kaf a kan Amarya da Angon, ta juya za ta wuce ya riƙe hannun gam suka fita tare. Maimakon su koma mazauni sai kawa ya yi waje da ita har wurin motarsa. Ta fincike hannunta, tuni idanunnata sun cicciko da kwalla.

"Ka kyale ni."

Hussein ya tsaya kawai hannunsa a kirji yana karemata kallo, ta yi mishi irn kyan da baki ba zai iya faɗi ba. Tsananin kewarta da son kasancewa da ita ne ke cin zuciyarsa.

"Da iznin wa ki ka zo nan?"

Ta tsuke baki, ya kuwa bishi da kallo yana cije lebba.

"Ka riga ka san da fitar ai."

Ta fadi cike da dakiya. Bai ce uffan ba ya juya ya yi amfani da mukullin motarsa ya bude, hannunta ya kama ya zagaya da ita ya bude gaban motar da nufin sanyata ciki. Ta dubeshi da zummar magana, sai dai yanayin ɗaurewarsa ya kaɗa hanjinta ba shiri ta hadiye abinda take shirin fadi ta shiga a fusace tana huci. Sai da ya zagaya ya zauna sannan ta dubeshi.

"Motata fa?"

Bai ce mata uffan ba ya yi ribas suka fice. Ranta ya ƙara zafi gashinan ko hoto ba su yi ba da Amaren balle kuma ƴan ankon.

"Amma kasan ba kai ka kawoni ba ko?"

Idan motar ta bata amsa, toh Hussein ya bata. Wayarta ce ta shiga ringing, ta ciro, kafin ta duba ko ta ɗaga ya karɓe. Ba ta san me aka ce ba  kamsr yanda ba ta san wace ce ba.

"Muna tare."

Daga haka ya katse kiran ya jefa wayar aljihun gaban riga. Ramlat dai har da hawayen takaici, ba ta bar haskoshi da waccan budurwar ba kamar yanda ta ke jin zafin raba ta da wurin bikin da ya yi.

Su na isa gidan ya sa hannu ya zare purse dinta yana kallonta tsakar ido Ta kauda kai tana tura baki. Dariya ma ta ba shi ya murmusa. Mukullin motarta ya zare ya miƙa mata. Yana unlocking kofofin ta bude ta fice zuwa sashinta ranta a jagule. Shi kuwa sai da ya ba direba mukullin da kudin mota akan ya koma idan an tashi ya taho da waɗanda suka je a cikinta.

***
Tana shiga ɗakinta ta faɗa saman gado ta shiga rera kuka kamar wata yarinya ƙarama. Ganinta kwnace saman gado tana kuka ya hau doka murmushi, kawai ji yake ya rama shariyar da ta dinga yi mishi a kwanaki biyunnan. A nutse kuma ya soma takawa har ya karasa gadon. Jin ƙamshin turarensa sai ta ɗago ta share fuska, kokarin mikewa  ta ke yi ya riƙo hannunta gami da jawo ta ta faɗa jikinsa. Kanta bisa kirjinsa gaba daya fuskarta ta nutse yayinda hancinta ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa. Lumshe idanu ta yi sadda ya sa hannuwansa gaba daya ya rungumeta tsam. Sai a sannan ta kara tabbatar da cewar ta yi kewar mijinta. A hankali ya zame ɗankwalin kanta ya shiga shafa gashinta.

"Duk kawaici da kauda kan da nayi maki don naga gudun ruwanki, ba ki gane ba ko? Kin maida ni kamar wani hoto, kin nunan sabgar gabanki ya fi ni ƙima da muhimmanci. Tun soma bikinnan ba ki da lokacina, ba ki damu da ni ba. Shikenan ni kuma sai na kasa nuna ɓacin raina?"

Yanda ya ke magana a tausashe sai jikinta ya yi sanyi, shakka babu kam, ba ta kyauta ba. Ta ɗago a hankali ta dubeshi tana narkar da fuska.

"Ka yi hakuri. Na sani ban kyauta ba, amma don Allah ka yimin uzuri tunda dai ka sani biki ne ake yi, ga baƙi ina da su."

Ya kama haɓanta suka tsurawa juna ido.

"Sai kuma ki ke jin nauyin kwana da mijinki don kina da baƙi? Ki ka kyalewa wasu ƴan matan shi su samu matsugunni a nan?"  Ya nuna kirjinsa yana ɗaga mata gira da murmushi.

Nan da nan kishin ya dawo sabo fil ta tureshi za ta mike, ya kara fisgota ya rike gam yana dariya.

"Na dauka kishiyar kike ra'ayi."

Ba ta san sadda ta harareshi ba, don mamaki sai ya yi dariya.

"Shiyasa na ganka da wata busashshiya kana yawo da ita a cikin bainar jama'a don ka zubarmin da ƙima a gane ni Ramlat ban da wata daraja da.."

Bai bari ta karasa ba ya tallafi haɓanta ya haɗe bakinsu wuri guda da zafi-zafi.

Tun tana yunkurin ƙwatar kanta har dai ta saddaƙar. Can kuma da kansa ya sake ta, ya mike yana dubanta da shanyayyun idanunsa. Da wata irin kasala ya miƙa mata hannu, ba musu ta miƙamasa, suka ɗunguma zuwa nashi ɓangaren. A nan kam alƙalami ba zai iya wassafa yanda masoyan suka kasance ba cike da matsanancin kewar junansu. Ranar dai dinner anan suka ci suka sha abinsu.

Koda jama'a aka dawo, ta sha tsokana sai toshe kunnuwanta ta yi kawai.

***
  Sati biyu da kammala biki, jama'a kowa ya watse, an miƙa Amarya Hafsat zuwa Kano, tafiyar da ba'a yi tare da Ramlat ba don sam Hussein ya ce ita da Kano ba yanzu ba. Haka ta hakura, Rasheeda kuwa Abuja aka miƙa ta wurin aikin mijinta.

Tun bayan bikin ya kasance Ramlat ba ta da kuzari, koyaushe tana kwance, wani lokacin bacci wani lokacin kuwa yanayin jikin ne kawai ba ya mata dadi. Dada kanta ta soma fahimtar sauye-sauyen Ramlatun, abinka da babba, sai ta ce mata lallai ta yi zamanta a ɓangarenta  ta dinga hutawa tunda a sannan Dada ba ita kadai ba ce, wata dattijuwa kuma yar uwarta dake Mubi, Mariya ta dawo nan domin taya Dada zama. Mace ce da ba ta taɓa haihuwa ba ga kuma girma da ya ɗan kama ta babu mijin aure. Ita kanta tana jin dadin zama da Dada.

Kamar koyaushe, yau dinma tana kwana a falo, daga ita sai vest fara mara hannu da wando pencil da bai karasa ƙaurinta ba. Tun fitar Hussein take jin tashin zuciya, ta rasa meke mata dadi. Kamshin komai a gidan ma ji ta ke yana hawa kanta, karshe ma miƙewa ta yi kawai ta zura dogon hijabinta ta zagaya ɗan barandarsu da ake hango garden ta shimfida ƙatuwar dardumarta ta zauna. Ba laifi ta ɗan ji sauyi, ahankali kuma bacci ya yi awon gaba da ita.

Sallama ya yi har sau uku shiru, da mamaki ya karasa shigowa falon a karshe ya shiga leƙa kicin da dakuna. Bandaki ma wayam, yana shirin leƙawa sashinsa ya hango ƙofar fita ta hanyar kicin a bude don haka ya karasa. Sosai abin ya ba shi mamaki, ba ta taɓa yin haka ba, ga dai iskar fanka da komai a falon amma ta dawo nan ta kwanta, yanzu kam ya yarda ba ta da lafiya. Karasawa ya yi ya sa hannu saman goshinta. Zafin da ya ɗan ji ne ya sa shi shafa gefen fuskar.

"Ya Salam."

Jin hannunsa ta yi firgigit ta farka da salati. Ya kama hannunta.

"Sannu Heart, dama ba ki da lafiya? Tashi muje asibiti."

Ta mike zaune tana shafe fuskarta, sosai kam ta yi bacci don har yamma ta kawo kai, ta tuno ko sallah ba ta yi ba.

"Ban yi sallah ba."

Ya taimaka mata ta mike, yana rike da ƙugunta suka ƙarasa ciki, sai dai su na sanya kai a falon ƙamshin airfreshner da ta fesa ya hautsina mata ƴan hanji. Tana kokarin zama jikinsa daga natata hanyar amfani da hannun damanta ta dora saman kirjinsa za ta tureshi, shi kuwa ƙara riƙo ta yake a rude yana tambayar lafiya. Sai dai ina! Tuni ta soma sheƙa amai har yana ɓata jikin Hussein. Nan da nan ta zaro ido a rikice, ba ta mance sadda ta yiwa Aliyu amai a jiki ba ya ɗauketa da lafiyayyan mari yana ɗura ashariya.

"Ka yi haku.."

"Shii! Muje ki wanke jikinki." Ya ja ta suka nufi bangarenta, sai da ya cire rigarsa da ta ɓaci har da singilet, kafin itama ya ciremata nata dogon hijabin. Bandaki ya shiga ya hada ruwa. Wankan suka yi tare, duk wani abin ƙamshi da ya ɗauko za ta girgiza kai ta ce ita ba ta so, Hussein dai murmushi ya ke da fatan Allah Yasa abinda yake tunani ya tabbata. Sai da ya daukomata kaya sannan ya wuce sashinsa ɗaure da tawul a ƙugu. Ƙananun kaya ya sa kawai ya fesa turare. Aikuwa tana jin ƙamshin turarensa ta fada bandaki a guje ta shiga sheƙa wani aman, koda zai shigo ya dakatar da shi kamar ta yi kuka.

"Ni bana son kamshin turarenka."

"Toh fa." Ya tsinci kanshi da faɗi, turaren da a baya take masifar so kenan, Sorry kawai ya furta sannan ya fita daga dakin. Kaya ya je ya sauya sai dai wannan karon bai yi gangancin fesa turaren ba. Suka ɗunguma suka wuce asibiti, ta waya ya shaidawa Dada ya kai Ramlat asbiti. Dada murmushi kawai ta yi da addu'ar Allah Ya bata lafiya.

Kyakkyawan albishir din da ya yi fata kuwa shi ya samu, wato dai ciki ne da ita. Yanda ya dinga tarairayarta tun daga asibitin har gida, ita abin ma kunya ya dinga ba ta.

Tun daga ranar kuwa kulawar da Hussein ke ba ta na musamman ne, tausayi sosai ta ke ba shi ganin yanda ta ke laulayi mai wahalarwa. Ita kanta abin tsoro ya dinga ba ta, gani take kamar wannan haihuwar farko ne za ta yi don komai sabo ta ke ganinsa.

Kafin watannin haihuwar su cika gaba daya ta sauya, ta rame, sai ƙaton ciki wanda scanning ya nuna ɗa ɗaya ne kawai. Kowa kallon mai haihuwar biyu yake mata, duk yanda ta so ya bari ta je Kano ta haihu ya ƙi, itama don kanta ta hakura da batun zuwa don ko nawa za'a ba ta a yanda take ji,  ba za ta iya bin hanyar Kano ba.

***
Bacci ya ke sosai, yayinda ita kuwa baiwar Allah ta zubawa silin din ɗakin idanu wanda hasken farin wata ya haska, mararta da bayanta babu inda ba ya ciwo, a hankali ta miƙe zaune tana cije baki, ta rasa ma ina za ta sa ranta, wani irin murɗawa da ya yi ba ta san sadda ta ɗakawa Hussein duka ba. Ya mike kuwa firgigit don a farko bai dauka mutum ne ya dakeshi ba, hannu yasa  ya kunna fitilsr bedside yana kallonta gami da ruƙo ta.

Ta matse hannunsa ƙam!

"Mutuwa zan yi wallahi!"

"No! Naƙudar ce? Bari muje asibiti."

Haka ya mike tsaye yana gyara zaman pyjamas dinsa. Dakyar ya samu nutsuwar ganin mukullin motar, ficewa ya soma yi da ita, Buzu Maigadi da  fitowarsa daga bandaki kenan, ya ajiye butar ya karaso da sauri ya taimaka ya karbi mukullin motar ya budemishi yana kwaranyo addu'ar Allah Ya bata lafiya. Lokacin wuraren ukun dare ne. Sai da Hussein ya zaunar da ita kafin ya koma a guje ya dauko akwatin da tun shigar cikin wata tara ta haɗa abinta.

Su Dada basu sani ba sai ƙarar buɗe kyaure da rufewa suka ji. Ba shiri ta fito ita da Baba Mariya a ruɗe, nan Buzu ke fadamusu Madam ce ba lafiya. Nan da nan a rude suka kira wayar Hussein, amma ina tana ta ringing bai ɗaga. A dole suka koma ciki don ba direban da zai kai su. Nafiloli suka shiga yi da addu'ar Allah Ya sauketa lafiya don sun sani loda sun je, ba abinda za su iya yi mata sai addu'ar.

***
Ramlat suna zuwa ko awa ɗaya cikakka ba ta yi ba ta haifo ɗanta namiji, sai dai kafin Nos ta yi wani yunƙurin, wata naƙudar ta kara zuwar ma Ramlatu, da mamaki Metron da Nos suka ƙara yin kan Ramlat, wannan karon sai da aka haɗamata da ruwan naƙuda, ba karamin galabaita ta yi ba, Hussein kamar kansa zai tarwatse yana daga waje, ga kukan jariri yana ji kuma ana fadin ai ba ta kammala ba. Ga murna ga kuma tashin hankali da tausayin matarsa. Kalmar mutuwar da ta ambata har yanzu ba ta sakeshi ba, fargaba sosai ya ke ciki duk kuwa da ya sani mutuwar ba a baki ta ke ba.
 
Kukan jaririn da ya kara ji, sai ya rude, ya rasa na farkon ne ko na biyun, kawai sai ya cusa kai ba tare da neman izni ba. Aikuwa wata jaririyar ce aka kara cirowa Ramlat. Ita kuwa ta lumshe ido sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi.

Dole ya fita yana murna, kafin a kammala gyarasu ya shiga laluben waya don ya sanarwa Dada da ɗan uwansa sai dai wayam. Hakanan ya hakura ya dinga murna da farin cikinsa shi ɗaya. Gaba daya jariran aka kawomasa, Metron na fadin sai fa ya ba ta goron albishir, dariya ya yi yana ɗaukarsu.

"Ki biyoni bashi."

Itama dariyar ta yi ta miƙa masa tana fatan Allah Ya rayamasa.

Kammanin Dada sak ko kuma yace kamanninsa yake hangowa a fuskar yaran wadanda suma ke cike a kansu a saman fuskarsu.

Sumbatar kowannensu ya yi yana mai jin taruwar kwalla a idanunsa, ashe dai wataran mafarkinsa zai tabbata, zai ga gudan jininsa? Ya soma yiwa namijin huɗuba a kunne kafin ya juya ga macen.

Daga nan kuma ya yi zamansa yana ƙaremusu kallo, haka har aka soma kiraye-kirayen Assalatu. Aka ba shi umarnin ganin Ramlat, ya shiga ciki. Ta zubamusu do tana kallonsu cike da kauna, yana karasowa ta yi murmushi.

"Alhamdulillah." Ta furta, ya ajiye yaran a gefe kusa da ita ya sumbaci goshinta shima ya na hamdalar. Dakyar ya samu ya wuce masallaci. Ana idar da sallah ba jimawa sai ga AlHassan tare da su Dada.

Kowa ya ga ƴan biyunnan sai ya hau murna. Dada har da hawayenta tunawa da ta yi da Yayanta kuma ɗan uwanta Aminu.

Ranar dai Ramlatu ta sha baƙi dakyar aka fice aka bar ta ita kadai ta samu bacci mai nauyi ya fisgeta. Jariran kuwa su na hannu, wannan ya dauka wannan ya dauka har sai da Hussein ya yi ta maza ya ce ya isa hakanan su ma a bar su su huta. Duk shaƙiyancin da ake mishi ko a jikinsa. Ya shimfidesu a kusa da uwar ya tsaya ya kuramusu idanu yana kallo. Ya kalli Ramlatun ya kallesu. Tausayinta ya kamashi, ba karamar wuya ta ci ba. A karshe dai ya fice ya bar su. Sai da Dada ta lallaɓashi kafin ya koma gida ya yi wanka ya sanya suturar arziki ya kuma biya shago ya siyo kayan jarirai na mace don kusan rabin siyayyar duk na namiji suka yi jin abinda scanning ya bayar.

Kwanan Ramlatu biyu aka sallameta, sashin Dada ta koma inda Baba Mariya ke wanketa tas ita kuwa Dada ke wanke jarirai.

Hussein ko yana ofis ba ya rabo da waya. Ranar suna aka sanyawa yara suna Amina da Aminu, farin cikin Dada ba ya misaltuwa. Daidai da iyalan Kawu sai da suka zo suna wannan karon har da Umma matar Baba Dakta, Hajiya ma ta so zuwa sai dai makarantar yara ta sanya dole ta hakura amma itama kam zuwa lokacin kewar diyarta take ji. Abinda ya yiwa Ramlatu dadi bai wuce na zuwan Muhibbat ba. Sosai ta yaba da wannan karar da ta yi mata, abin mamaki kuma har saƙo ta samu na kayan jarirai daga iyayen Hilal, matar Hilal ta kira ta mata barka ta kuma yi mata fatan alheri. Koda ta ke ba su Rafee'ah da suka zo suna labarin wayar, dariya suka yi.

"Ai ke yanzu wacce da kika sani a baya yanzu ba ita ba ce, ko ma dai mene ai yanzu dole ta sauko tunda aure zai ƙara kuma yanzu ko ba komai ta ga  kin auri wanda ya shanye mijinta a komai da komai na rayuwa.
Jinjina kai kawai ta yi tana murmushi a ƙasan ranta tana mai hamdala da Ubangiji.

***

Rayuwa sosai ta ke yiwa Ramlat da mijinta dadi, zuwa lokacin gininsa da yake ya kammala sai fenti da ake yi da kuma zuba furnitures da ya yi saura. A wannan lokacin ne kuma ba zato ya yi mata albishir da kai ziyara Kano. Dama tun sadda ta yi kwanaki arba'in ta ke saka rai da hakan, ya nuna ba yanzun ba. Har faɗa suka yi ta gama fushin ta haƙura ta sauko. Haka ta dinga shirya tsaraba, Dada ma ta haɗamata da nata.

Hajiya ba karamin farin ciki ta yi ba, abincin da Ramlatun ta fi kauna shi ta girka mata, hakanan Umma itama ta aikomata girki. Su Ummi kamar su haɗiye ƴan biyu wadanda suka dauko hasken mahaifinsu kamar ka latsa jini ya fito. Duk ganin da Ramlat ke yiwa Ummi tana da gashi sadda tana ƙarama ashe ba komai bane idan aka haɗa da na Meena. Kamar yanda suke kiran Amina don Dada sam ta hana a ɓoye suna.
Hisham kuwa koda ya ga amininsa sai ya hau dariya da zolayarsa ganin yanda ya ajiye naman wuya ya ƙara zama wani fresh. Har gidan su Hisham din ya je ya gaida mahaifiyarsa kafin ya koma masauki.
  Washegari ya juya Adamawa ya bar Ramlat, sati biyu kawai ya ba ta hakanan ta hakura don a son ranta ne ta yi wata guda cif. Ai kuwa a sati biyun ta zage yan uwa da abokan arziki, koda ta je gidan Yaya Munir ta kara shan mamakin zamantakewar matansa wadanda tuni ya haɗe su gida daya. Salma kanwar Bilkisu ita kanta ta sauya ta yi sanyi. Anan suka hadu ta dinga ba ta hakurin abinda ya faru a baya, banda murmushi ba ahinda Ramlatun ta yi don har ga Allah ita kam yanzu dukkan kunci ko bakin cikin da ta shaƙa a baya ta bar sanya damuwarsa a rai sai dai ta tuno ta auna da yanzu ta godewa Allah.
  Ana jibi zasu tafi ne ta fita tare da Amrah, daga gidan Muhibbat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login