Showing 96001 words to 99000 words out of 226732 words
bola ta binne ba matsalarta ba ce, ta shiga makabarta ma ta kwaƙule ido akan abin duniya wannan ba ta ɗaukeshi wani abu mai wuya ba. Tsakar dare ne ta tabbatar ba wanda zai iya ganinta kan bola, za ta iya wannan. Abu mafi ciwo mai sanyamata ta ji ta tsani kowace ɗiya mace, bai wuce na zuciyar Hussein da wata za ta mallaka ba. Wannan ya fi komai yi mata zafi. Gani take kamar ta hakura da sauya garin ta zauna ta bibiyeshi har ta yi tozali da yarinyar ta cakamata wuƙa a maƙoshi.
Murmushi ta yi, sai lokacin ta samu sukuni, sai a sannan ta samu mafitar da a ganinta ya fi na wannan Malamin. Koda ba ita ba, za ta sanya a kashemata ita yanda wata ma ba za ta ƙara sha'awar shiga rayuwar Hussein ba.
Har Hajiya Batool ta gama shigar da nata koken aka ba ta magunguna, Hajiya Zeenatu ba ta san anyi ba don ta tafi tunanin yanda za ta kashe baƙar dagar da ke shirin ruguza gininta.
Isuhu kallon Hajiya Zeenatu kawai yake yana nazari, a ido ma karantar mutum yake balle kuma ga ya buga ƙasa. A jikinsa yake jin ba za ta aikata yanda ya ce ba sai abinda zuciyarta ta saƙa mata. Murmushi kawai ya yi don ya ga irinsu da yawa. Ya kuma tabbatar za ta yi kukan nadama, da ƙafarta za ta dawo wajensa ta nemi wani taimakon, a lokacin ne zai nunamata iyakarta.
Suka kammala suka biya maƙudan kuɗi kafin su mike su fito, saurayin shi ya kai musu har mota sannan ya wuce da su gidan ƙawar Hajiya Batool, Hajja Mari (Maryam). Kasuwanci ne ya soma ƙulla ƙawancensu, saurayin yaronta ne yardajje mai mata ire-iren aikinnan. Ita ta haɗasu da shi don su je ayi musu komai.
Hajja Mari ta shiryamusu lafiyayyen abinci iri-iri, a karshe ta kara jaddadamusu kada su yi wasa da aikin Isuhu Bakka Tsoron Allah (Ba ka tsoron Allah) don shi ɗin aikinsa kamar yankan wuƙa ne. Duk wannan bai sa Hajiya Zeenatu ta sauya ƙudurinta ba.
Sun sha hira sosai a gidan Hajja Mari kafin su yi mata sallama saurayin ya maida su masaukinsu da zummar washegari zai zo ya kai su tasha su hau mota zuwa Maraɗi, anan ne kuma direban Hajiya Batool zai zo ya iskesu su wuce Kano.
***
ADAMAWA
Kusan a hargitse ya shigo gidan, Dada ya soma cin karo da ita zaune saman kujera tana faman haɗa zufa. Ya karasa da sauri ya zauna daga shi sai doguwar jallabiya.
"Dada lafiya? Meyafaru?" Ya yi tambayar yana dubanta da kulawa. Girgiza kai ta soma tana sharar hawaye.
"Mafarki nayi marar dadi akan ɗan uwanka. Jikin yana ƙara bani yana raye kuma a duk inda yake yana bukatar addu'armu."
Al-Hassan ya sauke ajiyar zuciya gami da ɗan runtse idanu ya bude cike da damuwa, ba ya son ya sanar da ita nashi kalar mafarkin kar hankalinta ya tashi, kusan shima kwanakinnan yana yawan mafarkinsa cikin wani irin yanayi.
"Kiyi hakuri Dada, addu'armu ya fi buƙata a duk inda yake. Idan ma yana rayen Allah zai amsamana roƙonmu, Zai sadamu da shi in sha Allah."
Dada ta share hawayenta ya fi a ƙirga amma kara tsiyaya suke.
"Kana ganin ina raye zan sake ganinsa?"
Da murmushi ya amsa.
"In Sha Allah Dada. Za ki ganshi."
Ta hau gyada kai. Can kuma ta ce.
"Kawunka Modibbo ya kira, ya gasamin maganganu masu zafi duk akan iyayenku, na dauka tunda basu duniyar komai ya wuce, ashe ba haka ba?"
Ya kara kallon Dada, twin sister din mahaifinsu, Aminu Gidado. Ubansu daya da Modibbo sai dai ba uwa daya ba. A dakinsu su biyu kacal uwarsu ta haifa kafin ta rasu.
A rashin Aminu da matarsa, ta riƙe Alhassan da Hussein tamkar yaranta na cikinta ko ma fiye da hakan. Don irin son da ta nunamusu ko iyayensu sai hakan. Yanda ta damu da rashin Hussein kai ka rantse ita ta durkusa ta haifeshi ba Aminu ba.
"Tunanin me ka ke yi?" Ta faɗi tana mai hankaltarsa. Ya yi murmushin yaƙe.
"Babu komai Dada."
Kafin Dada ta kara magana, wata kyakkyawar budurwa wacce kallo ɗaya za ka yi mata ka san bafulatanar ce ta gaske, siririya kuma fara tas. Hafsat kenan, Autar Dada. Hannunta dauke da Flask na ruwan zafi, ta saki baki tana kallon AlHassan, ya harareta, hararar da ta bata dariya.
"A'a me ya yi zafi? Ka zo ka rarrashi tsohuwar tamu ko? Yau tun safe ta rikicemin da koke-koke kamar wacce aka yiwa mutuwa. Ashe sai da ta kiraka ta samu sukuni." Fadin Hafsat sadda take shigowa falon sosai.
"Dada wataran sai na ɓalla ƙashin yarinyarnan kuma na dauketa na miƙa asibiti an gyara tas! Ta rainamin ke da yawa da sunan Auta, to kuwa maganinta zan yi, aure zamu yi mata."
Tuni Hafsat ta nemi dariyar da take ta rasa, nan da nan ta marairaice.
"Allah Ya huci zuciyarka Abu Fatima, don Allah ka yi hakuri."
Murmushi ya yi ganin ta yi mishi wayo, wato amfani da sunan da Kausar kadai ke kiransa da shi. Dada dai ba ta sanya baki ba sai murmushi. A karshe dakyar Hafsat ta shawo kansa ya janye ƙudurinsa. Ita a duniya ba ta da buri sai na zurfafa karatu. Wannan ne dalilin da yasa ba ta kula kowa, samarin zuri'arsu masu kawomata hari su ne suka tilastamata zaman gida ta daina shiga sabgar yan uwa gudun kar a ƙaƙabamata auren zumuncin da bai taɓa bata sha'awa ba.
Duk yanda Dada ta so AlHassan ya karya a gidan hakan ya faskara, ya lallaɓa bayan ya ga ta maido walwalarta ya yi gaba zuwa gidansa cike da damuwar rashin ɗan uwansa wanda a yanzu sosai yake ji a ransa cewa yana raye. Ba kamar a baya da yake tunanin ya mutu ba. Idan kuwa hakane, zai kara zage damtse wurin cigiyarsa.
***
KANO.
Ramlat da ƴan uwanta sun haɗu suna kallon lefen Hunainah Amaryar Muniru. Zulaihat tun soma kallo take murmushi can dai ta ɗago ta dubeshi.
"Wato dai wannan auren ko aurenka na fari ba ka saki bakin aljihu irinsa ba. Nidai ina ƙara faɗa, ka rabamusu gida wallahi don Bilkisu ba kanwar lasa ba ce."
Ya harareta.
"An fadamaki akwai macen da za ta firgitani har na kasa daukar mataki a kanta? Gida dole na haɗa su, ai idan ita Bilkisun ta ga kyautatawar da Hunainah za ta yimin shi ne da ta hankalta ta gyara."
Rafee'ah ta cafe zancen.
"Um um dai Yaya, wallahi naga irinku da yawa kuma daga karshe sai ku zo ku lashe aman da ku ka yi. Duk yanda kake tunanin mata ya wuce nan. Zama gida daya ba kwanciyar hankali."
Ya taɓe baki, ko ba komai yana cikin farin ciki ba ya neman rigima da kannennasa.
"Aikin banza kai, haka itama Hunainah ta dagemin akan lallai ba ta son zamanta da Bilkisu don kawai ta mata irin abinnan na mata, ta kirata a waya ta firgita ta da yi mata gargadin aurena. Ni kuwa a ranar hannu ne kaɗai ban ɗaga akan Bilki ba. Albarkacin su Yasmeen ta ke ci, ai na faɗamata. Ni akwai macen da za ta kawomin wargi ban yi kasa-ƙasa da ita ba?"
Ramlat ta ɗago kai ta dubeshi wani dan murmushi ya suɓucemata kafin ta maida kai ta ci gaba da jera kayan shafar da ta ciro. Yaya Munir kenan, ga dukkan alamu zai iya dukan mace idan ya so. Tana jiyemishi tsoron wani abu, sai dai ba ta furta ba don ba fata take mishi ba, ta bar wa cikinta. Amma kuma buɗar bakin Zulaihat ta ce.
"Af, wannan dai alamu sun nuna za ka iya dukan matarka. Kar dai ka zama Ali.."
Sai ta yi saurin yin shiru, har a ranta ba ta ji dadin sunan Aliyu da ya tahomata ba, ta dubi Ramlat da ko kallonta ba ta yi ba kanta a ƙasa. Rafee'ah ta yi mata ido akan ta yi shiru. Koda ma Rafee'ah ba ta fadi ba, ita mai kama bakinta ce, a kasan ranta ta roƙamasa gafarar UbangijinSa.
"Ki fita idona wallahi Zulaihat! Kar kiga kin haifi wadannan yaran masu kama da kulɓa har yanzu ba ki fi karfin na mareki ba."
Maganar Yaya Munir duk sai ya basu dariya har Ramlat din da ta haɗiye zancen Zulaihat, ko ba komai ta ga nadama a fuskar Yayarta. Zulaihat ba kanwar lasa ba, haka suka yi ta cacar baki da Munir a karshe dai fitowar Hajiya daga ɗaki suka yi shiru bayan ta tsawatar. Bai bar gidan ba sai da ya rantse Zulaihat ba za ta je kai lefe ba don cewa ya yi da ace banda Hajiyarsu, Abban yana da wata mata zai ce Zulaihat ba ɗiyar Hajiyarsu ba ce.
Haka ya gama bambamin faɗan ta rainashi ya zura takalmansa ya bar gidan.
***
Washegari aka kai lefen Hunainah, Umman Amrah ce ta jagoranci tafiyar, aka tsaida nan da sati biyu biki. Ramlat ba ta samu zuwa ba saboda aiki. Sai da ta taso kafin ta tsaya a wani katafaren wurin siyar da kayan maƙulashe na A&Z. Ba ta taɓa zuwa ba sai dai talalr wurin har a gidajen rediyo tana ji.
A duniya tana son ta ga ta faranta ran Hajiyarta da yaranta idan har tana da kuɗi a jikinta. Albarka sosai Hajiya ke sanyamata duk radda ta samu kuɗin da ta yo musu siyayyar kayan dadi suka ci. Kamar yanda ta saba, waya ta yi ta ce kar su ɗora tukunya, wannan abu ya fi komai yiwa mutan gidan daɗi. Ranta fari sol ta rufe motarta ta nufi ciki.
Da ace Ramlat na da masaniyar wurin ko mallakin wanene ko wacece, har abada ba za ta tako ƙafarta ciki ba.
Ko sakanni uku ba ta yi da shiga ba, wani al'amarin da ya kusan tarwatsamata kwanya ya afku.
I just published "BABI NA TALATIN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/gSzBjkXxTab
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
32)
Katafaren wurin hawa biyu ne, na farkon kayan snacks ne kala-kala, saman kuwa wurin siyar da ice-cream ne kowane irin ɗanɗano. A farfajiyar wurin kuwa kaji ne manya gashin inji ake siyarwa. Kai tsaye saman ta haye ta nufi wurin masu kula da wurin, ƴanmata da samari ne ƴan ƙarya a wajen, basu ko tsonemata ido ba, burinta ta yi abinda ya kawo ta ta bar wurin, sai dai tsayuwarta ba jimawa kamar ance ta waiga, ido huɗu suka yi da juna, daidai sadda ta fito daga wata ƙofa. Kallon mamaki da tsana ta ke yiwa Ramlat har ta ƙaraso inda take a matuƙar fusace.
"Ke! Wai ke wace irin mayya ce?! Duk yanda na kai ga nesantaki da mijina hakan bai isheki ba? Wannan wane irin bibiya kike mishi?!"
Ba Ramlat ba, gaba daya mutanen wurin suka maida hankali ga Hajiya Zeenat dake tsaye tana cika da batsewa. Ramlat ta kai maƙura da irin wannan cin mutuncin da Hajiya ke mata. A yau ta ji shirun ya gagareta don haka ta watsamata banzan kallo sama da ƙasa.
"Daga ke har mijinnaki ba ku isheni kallo ba. Kuma ma banda abinki Mama, ai matar da ta yarda da kanta a zuciyar mijinta, ta kuma yarda da mijinnata, babu wata ɗiya mace da za ta razanata balle har ta damu kanta. Sa'arki ɗaya, ba zan iya haɗa miji da sa'ar uwata ba, da babu abinda zai hana ni auren mijinki ko don na nunamaki bambancin aya da tsakuwa!"
Hannu Hajiya ta ɗaga da zummar marinta, caraf ta riƙe hannun tana murmushi kafin ta yarfar.
"Kin yi kaɗan Mama. Mari wata dai ba Ramlat ba."
Tana kaiwa nan ta juya a fusace ta kama hanyar barin wurin, tana jin Hajiya na kwalawa Maigadin wurin kira, har suka kusan cin karo da Ramlat, tana sauka yana hawa, ta kuma ji sadda ta ke bada umarnin koda wasa ya ƙara bari ta shigo wurin ya tabbata ranar barin aikinsa kenan.
Ranta a tsananin ɓace ba ta ko kallon gabanta sosai, ba ta yi aune ba ta yi karo da mutum, tsantsin tiles da ya kusan kifar da ita yasa ta saurin riƙe kafaɗarsa da dukkan hannuwanta. Ƙamshin tsadadden turarensa ne ya kashe dukkan wata lakar da ke jikinsa. Ko sakan ba ta yi ba ta saita kanta gami da kauda hannunta a jikinsa, kallon kallo suka yi. So yake ya tambayeta dalilin ɓacin ranta, amma ganin wacce ke saukowa tana haɗa matattakala bibbiyu zuwa uku yasa shi yin shiru.
"Dama na faɗa! Yarinyarnan karuwa ce! Karuwa ce! Kun gani ko? Kun ga kalar iskancin da ta ke yi a jikin mijina ko?!"
Samari da ƴanmatan da aka bari a sama tuni suka garzayo ta jikin gilasai suna kallon ƙasan. Wadanda basu taɓa ganin mijin Hajiyar ba sai a sannan suka ganshi, ƴanmata ido ya soma wani kakkarwa, basu taɓa zaton haka mijin Hajiyar yake ba. Wasu kuwa suna ganinsa a wurin don mafi akasari don shi suke takowa su zo, amma basu taɓa kawowa a ransu mijin wannan uwar matar ba ce.
Ramlat ta dubeshi da idanunta wadanda ɓacin rai ya sauya, gani take ya kamata ta rama abinda Hajiya ke mata. Babu ruwanta da abinda zai biyo baya, idan har hakan zai baƙantawa Hajiyar to a wurinta daidai kenan.
Murmushinta da ba kowa ke ganin irinsa ba ta jefamasa gami da yi mishi kallon da sai ka rantse wani masoyinta ne take tare da shi. Shi kuma har sannan ɓacin ran abinda Hajiya Zeenatu ta yi bai sakeshi ba, fuskarsa a ɗaure. Sai dai ganin irin murmushin da Ramlat ke mishi, bai san ya akai ba sai ya tsinci kansa da maidawa kura aniyarta.
"Ka yi hakuri Heart, ko ma mene zan jure a kanka. Kar fa ka yi tunanin zan bar ka a kowane yanayi, wallahi ta yi kaɗan ta firgitani. Soyayya kuma yanzu muka fara. Ina jiran kiranka."
Tana kaiwa nan ta ɗaga yatsunta biyu tana murmushi ta bar wurin, Hajiya Zeenatu ta kunduma ashar gami da ɗaga ƙafa da zummar bin bayanta, caraf ya riƙe damtsen hannunta.
"Ba girmanki bane!"
Abinda ya fadi kenan cikin sanyin muryarsa kuma ƙasa-ƙasa yanda ita ɗaya ce za ta ji, samari da ƴanmata wurin da abinda Ramlat ta yi ya burgesu suka hau tafi da ihu har da masu fiito. Baƙin ciki da takaici ya sa Hajiya watsawa mijinta kallon banza da jajayen idanunta, ta yi rantsuwa akan sai ta kashe Ramlat da hannunta. Hussein sai ya raina kansa a hannunta. Ga mamakinta kamar karamar yarinya ya shiga jan hannunta suka fita daga wurin ya cusata a motarsa, fitowa ta yi ya dubeta.
"Ina za ki?"
Wani banzan harara ta watsamasa da ya sanya shi rudewa. Ya kasa magana sai faduwar gaba.
"Ki yi hakuri."
Bakin ciki bai bar ta ta yi magana ba, ta rasa wannan wane irin aiki ne, wani sa'in ya yi tasiri a kansa, ya dinga shakkarta, wani sa'in kuwa sai ka rantse babu ko ɗigon asiri a kansa.
"Ai ba kai ka kawoni ba! Ka motarka ka bar wurinnan tun kan na yi maka abinda za ka yi nadamarsa!"
Kamar wanda mahaifiyarsa ke ba shi umarni, ya bude gidan gaba ya shiga. Gilasan duk a sauke.
Kallonsa Hajiya Zeenatu ke yi har ya tashi motar, fuskarnan ba'a sake ba kuma ba'a ɗaure ba, duk iyakar nacinta ta kasa gano kalar rikiɗewar da maganganun Ramlat ya jefashi ciki. Idan ta tuna ranta baƙi yake, komai dangane da Ramlat take da buƙatar sani. Wannan kuma ba zai mata wuya ba, ta ci alwashin rusa dukkan farin cikinta koda za ta rasa dukkan abinda ta mallaka. Jikinta ke ƙara ba ta ita ce yarinyar da Isuhu da Gora suka yi mata gargaɗi a kai.
Har ya bar wurin ba ta fasa kallonsa ba kafin a rikice ta shige nata motar ta bar wurin. Kai tsaye gidan Hajiya Batool ta nufa.
***
"Me na faɗamaki?! Ke kin tsaya kan lallai ba za ki bar garinnan ba da hannunki za ki ɗauki mataki a kan yarinyar! Ai wallahi Zeenatu ji nake kamar na ɗaukeki na jefa a wuta tsabar haushin da kika bani!" Hajiya Batool ke zuba wannan ruwan masifar kamar ta ari baki. Dama cike take da ɓacin ran yanda tana wankan magani a tsakar gida Maigadinta ya ganta, takaicin ya ɓatamata aiki ne yasa ta sallameshi ta kuma yi mishi gargadi mai girma akan yunƙurin tona asirinta.
Hajiya Zeenatu ta share hawaye.
"Wannan bala'i da me ya yi kama, yarinya ta zamemin ƘARFEN ƘAFA? Yarinyar da a haife a haifi wanda ma ya girmeta balle ita? Wallahi ina kara fadamaki kowane gari zan je tunda har aka tabbatarmana sai ya aureta toh za ta biyoshi tunda mayya ce. Abu ɗayan dai shi ne mafita, na kasheta da hannuna ko kuma na gallabi rayuwarta ta yanda na lahira ma sai ya fi ta jin dadi. Batool ina son Hussein fiye da yanda nake son rayuwata, ba irin mazan da ake dandanawa bane a kyale, kuma wallahi wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na ga bayan Ramlatu."
"Au kin ma san sunanta ashe?"
Ta gyada kai.
"Har inda take aiki na sani, zan kuma ci ubanta."
Hajiya Batool ta jinjina kai cike goyon bayan aminiyarta.
"Duk abinda ya dace ki aikata ki yi idan har zai nesanta ta daga Hussein. Amma kafin komai, ki soma yi mata kyakkyawan gargadi, idan ta ji shikenan, idan kuwa bai samu shiga ba sai ki aikata yanda kika so."
Da haka suka ci gaba da saƙe-saƙensu akan Ramlat.
***
Ramlat kuwa, wani wurin ta nufa ta yi musu siyayya, ko kusa ba ta ji ko ɗarr da abinda ta aikata ba asalima wani irin murmushi da dariya take ita kadai a mota cike da nishadi. Ko ba komai yau ta rama abinda Hajiya Zeenat ke mata akan zargi da baƙin kishi irinnata. Da wannan nishaɗin ta isa gida, Hajiya sai da ta kasa hakuri ta tambayeta. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta sanarmata duk yanda lamuran suka faru. Baki sake Hajiya ke dubanta.
"A'a Ramlatu, kar fa ki jajiɓomana abinda ya fi ƙarfinmu. Ke ko tsoro ba kya ji."
Taɓe baki ta yi haɗe da murmushi tana kokarin kai tsokar nama bakinta.
"Hajiya kar wannan ya dameki, daidai nake da ita