Showing 15001 words to 18000 words out of 226732 words
dariya kusan a tare, ya ƙara yi mata godiya ta bada saƙon gaisuwa ga mutan gidan daga bisani suka yi sallama.
"Mene?" Ta furta tana mai duban Maman twins da Rafee'ah.
"Kin fimu sani ai, har kin samu wani majnun ɗin ba labari ko?"
Ta saki baki kawai ta kasa magana.
"Bar ta. Ni kai da naga ana shirin kasamin in law."
Hajiya ta dubi Maman twins.
"Wa kenan?"
"Baba Bashir yayan Baban twins mana, wanda matarsa ta rasu. To ai shi ne ya ga Ramlar kwanaki can ya nunan ana so. Maganar kenan da nake son nayi da ita amma ƴar albarkar ba ta kirani ba, ba ta zo gidannawa ba."
Ramla ta ja guntun tsaki.
"Don Allah ku bar wannan maganar, shi fa da kuke ganin mun yi waya, takalmi ne na tayashi zaɓar ƴarsa shi ne dalilin da ya kira suka yimin godiya don takalmin ya burge ƴar. Maman twins shi kuma Bashir ai kin ba shi lambata, sau ɗaya ya taɓa kirana kuma na ɗaga mun gaisa na ba shi hakuri. Mai kuma zan daga kiransa ya kara cemin?"
Daga haka ta kwashi tarkacenta ranta na zafi ta kama hanyar barin falon.
"Ai fa, wannan zafin rai da taurin kan ba zasu taɓa bari ki yi gaba ba Ramla. Ki dai bi sannu tunda yanzu ke mai ba wa wasu labari ce. Kinga dai makomarki."
Ba ta san sadda ta juyo gaba dayanta ba tana duban Rafee'ah wacce ta fusata. Ba dai ta ce komai ba ganin Hajiya na tsawatarwa ta juya ta wuce ciki, sai dai kafin ma ta kai ga shiga dakin tuni ta soma fidda hawaye. Tana ƙarasawa ta rufe gam da muƙulli ta faɗa saman gado. Ta yiwa kanta illa, tun ran gini tun ran zane, tana kyautata zaton dalilin ne yasa abu kadan ta aikata sai cibi ya zamo mata ƙari. Miƙewa ta yi ta rage kayan jikinta ta faɗa wanka. Koda ta fito shiryawa ta yi cikin doguwar jallabiya mai ɗankwali. Idanunta ya kai ga ɗan akwatin mai kalar golden da ke ajiye saman mirror dinta. Ƙarasawa ta yi ta buɗe, wani envelope ta fiddo ta zauna gefen gado ta buɗe. Hotunan ta ciro tana ƙaremishi kallo. Wani lokaci ta tuno wanda har abada ba zai gushe daga kwakwalwarta ba.
***
*MATAR MUTUM*
Tun tafiyar Hilal ta ƙara jin kewa ta cika zuciyarta. A bangare guda ga tunanin Aliyu da ya zamemata abin yi safe da rana. Wannan ta sanya suna kammala zana jarrabawarsu ta zango na biyu a makaranta, (2nd term), ta tattara Abba ya kaita Yakasai ta yi hutun a can ko ta sami nutsuwa.
Ta ci sa'a kuwa jikokin gidan wadanda suka kasance sa'anninta duk suna nan suma. Aikuwa suna ganinta suka ruƙunƙumeta da murna.
"Oh yarannan shikenan kuma za ku hana bakinmu ya huta da bari-bari kamar wasu ƴan shekara hudu. Ai ko su A'isha sun fi ku hankali." Cewar Talatu ƴar kawun Abba wacce ta dawo nan da zama daga Daura.
"Bar su su yi son ransu Talatu idan ba so kike yanzu Hajja ta maidaki Daura ba." Fadin Abba yana dariya. Hajja dake taunar goro tana tayashi.
"A'a to, rabu da su. Wataran sai labari duk suna gidajen aurensu."
Maganar Hajja ta ba su Ramla kunya, duk suka mike su ka yi ɗaki har suna bangazar juna.
"Magulmata." Fadin Hajja cikin dariya. Abba ya shantake har da cin kwaɗon zogale kafin daga bisani ya yi musu sallama.
Washegari da misalin karfe uku na yammaci ƴanmatan su biyar, Usaina, Maryam, Jidda, Nafisa sai Ramla. Suka shirya suka fita zuwa gidan babban ɗan Hajja Zulai, Kawu Kabiru don ziyara.
Tun kafin su fita titi Ramla ke mitar ita kam ba wacce za ta dauka saman cinyarta sai dai su yi abin hawa biyu.
"Kai Mrs Hilal, don ɓarnar kuɗin mota?" Fadin Jidda tana auna abinda zasu kashe daga Yakasai zuwa Zoo road.
"Aa fa, da gaskiyar ƙawalli, ba zan yarda nima na ɗora kowaccenku a cinya ba, ke kuma Jidda idan har za ki iya hawa bayan kujera shikenan."Faɗin Usaina.
Ta ƙasashe suna dariya don ita kanta ta faɗa ne, a ƙiba kam duk Jidda ta fi su.
"Allah Ya kiyaye." Cewar Jidda.
Aikuwa dai sai rabawa suka yi, kusan a tare suka samu abin hawa, Ramla da Usaina su biyu kacal a adaidaita sai Jidda, Maryam da Nafisa wuri guda.
Sai da suka kusa Zoo road ya samu fasinja. Sallama ya yi ya shigo, kusan da sauri ta dubeshi. Shi ne, shima yana zama ya kai duba gareta. Duk da yanda ta yi saurin kauda kwayar idanunta gefen Usaina wannan bai hanashi ganeta ba. Ta ƙara matsawa jikin Usainar ganin yanda jikinsu ke ɗan gogar juna. Murmushi ya yi ya matsa ta yanda ya san za ta fi sakewa.
Bai ce uffan ba banda murmushin da yake faman dokawa, abin mamakin shima Zoo road ya nufa. A hankali ta kai duba gareshi ta cikin karamin gilashin ɗan sahu. Kwayar idanunsu ya sarƙe da juna ta yi azamar janyewa. Ba ta ƙara gangancin kallonsa ba, mutumin da take kwana da tashi da tunaninsa. Kirjinta bai bar bugu ba, ba ta fahimtar zantukan da Usaina ke yi.
"Sauka mana." Ta ji muryar Usaina karo na biyu, sai sannan ta dawo nutsuwarta ta dubi gefenta, tsaye ta hangoshi a waje yana sallamar mai adaidaita. Ta kauda ido ta fito, Usaina na bayanta.
"Ɗauka har da nasu." Ya furta ga ɗan sahun.
Nan suka ce a'a, ya rantse shi zai biya, Ramla na shirin jan musu ta ji Usaina ta ɗan bugi kafaɗarta alamar ta yi shiru. Godiya suka yi mishi, hango su Jidda sun tsaya ya sanya Usaina nufarsu.
"Ramlat."
Ta tsaya cak gami da juyowa ta dubeshi, ba ta yi mamakin jin ya ambaci sunanta ba don Usaina ta kira sunan ya fi a ƙirga cikin adaidaita. Ya ɗan matso kaɗan.
"Karo na biyu Allah Ya yi haɗuwarmu. Tun sadda na sanyaki a idanuna har yau bani da sauran sukuni. Wallahi ina sonki!"
Ya furta fuskarsa na nuna alamar gajiyawa da kuma gaskiyar abinda ke ransa.
Ta matse yatsun hannunta jin yanda kirjinta ke bugu, ta ɗan kuramasa idanunta da suka cicciko da kwalla. Shima kallonnata yake da nashi mayun idanun wadanda tuni sun dulmiya cikin tafkin kauna da shauki.
"Ayya ka yi hakuri Malam, wallahi an sakamata rana. Nan da shekaru uku ba kaɗan bikinta."
Kalaman Usaina ya maidota hayyacinta, ta tsinci bakinta da maimaita abinda aka ankarar da ita.
"Eh, an sanyamin rana. Ka yi hakuri."
Ya yi murmushin yaƙe. Ya dubi Usaina.
"Kaicon wanda zai yi wasa da damarsa. Akwai kuskure a jan lokaci har haka. Watakila kuma rabon Aliyu ce. Ina muku fatan alheri."
Ya dubi Ramla da fuskarsa wacce ta yi narai-narai.
"Matar mutum Ramla, matar mutum.."
Daga haka ya juya ya bar wurin. Ramla ta tsaya kamar wata mutum-mutumi. Kafaɗarta aka jijjiga.
"Ke dillah can! Mene hakan? Waye shi? Ko kin manta da sanya ranar da ke kanki? Ke Usaina waye shi?"
Duk Nafisa ke wannan kalamin daidai sadda suka ƙaraso, zantukan ƙarshe sun sauka saman kunnuwansu.
Tuni ta soma tafiya kanta a ƙasa, tana ji Usaina na basu labarin abinda ya faru suna jan tsaki da kiran kwalelansa. Can kuma ta ji suna koɗa iya ɗaukar wanka da kuma kyan da Allah Ya mishi daidai gwargwado. Ta shiga tariyowa.
Milk shadda ya sanya da aka yiwa aiki daidai da zamanin, ya dora hula brown da ratsin milk din. Dogo ne don har ya fi ta da kaɗan, yana da hasken fata. Tafiyarsa ma kadai za ta burge mutum. Yana da ɗan duhun lebba, gashin kansa a cike luf-luf wanda ya taho har gefen fuskarsa ya haɗe da ɗan ƙaramin gemunsa. Lafuzzan Aliyu ma kadai abin burgewa ne.
Murmushi ta yi wanda ya taho tare da hawaye, ta yi azamar sharewa lokacin da Maryam ta dafa kafaɗarta. Ta kai duba gareta.
"Ina za ki?" Sai sannan ta waiga ta gansu tsaye a ƙofar gidan yayinda ita kuwa ta ɗan yi gaba. Tabbas tunanin Aliyu ba zai kasheta ba. Ta yarda matar mutum kabarinsa don haka ta haramtawa rai da gangar jikinta tunaninsa tunda har shima ya fahimci Hilal ne zaɓin Allah a rayuwarta, kamar yanda shima ya samu daidai shi.
'Allah Yasa hakan kake nufi.'
Ta furta a ƙasan ranta.
Sun wuni cur a gidan Kawu Kabiru tare da iyalinsa, tun Ramla na ƙin magana da faɗawa tunani har dai ta yi watsi da komai sai dai ta kasa yakice kalmar Ina sonki da Aliyu ya furta. Da zarar ta tuno a karon kanta sai ta saki murmushi.
Sai yamma suka bar gidan.
Haka ta ci gaba da rayuwa gidan kakanninta tare da su Jidda, duk kuwa hakan bai tafiyar da tunanin Aliyu ba. Abinda ke tsorata ta bai wuce yanda so da kaunarsa ke neman rinjayar zuciyarta ba. Har yakan maida tunanin Hilal gefe guda ya ajiye.
Sai da ya rage sauran kwanaki uku su koma makaranta sannan duk aka watse kowannensu ya koma gidansu, nan ma ji suke kamar kar a rabu.
***
"Wai ke ba za ki buɗe kofar ba? Me kenan hakan? Ba'a isa a faɗamaki ki ji ba?"
Muryar Maman twins ta bugi kunnuwanta, ta share hawayenta ta tattara hotunan ta maida mazauninsu sannan ta bude kofar fuska a haɗe.
Shigowa ciki Maman Twins ta yi tana fadin
"Allah Ya shiryamana ke Ramla, bansan sadda za ki rabu da wannan bakin ran naki ba. Haba jama'a! To sai ki fito Hajiya na nemanki."
Ta miƙe ta bi bayanta zuwa falon. Hajiya sosai ta buɗe mata wuta kan ba ta son irin haka, dole ta ba Hajiyar hakuri itama Rafee'ah ta bata.
Kafin su bar gidan sai da ya kasance komai ya wuce kamar ba su yi ba.
***
Kwanci tashi asarar mai rai, cikin ikon Mai Duka bikin A'isha ya taho gadan gadan, ana saura sati ƴan Daura suka dinga cika gidan. Wasu a can Yakasai wasu kuwa anan wurin Hajiya.
Ana saura sati a sanya A'isha a lalle Ramla ta ɗauki katukan daurin aure da na wuni ta kai ofishinsu. Ranar da ta kama Asabar kuwa, takanas ta shirya yara sai gidan Muhibbat wanda daga nan zasu wuce gidan Ramla rabon kati. Mutane biyu masu muhimmanci a rayuwarta kenan.
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
08)
_*Dawowa Labari*_
A kofar gidan Amrah ɗan sahu ya ajiye Ramlat. Ta biyashi tana mai kama hannun Affan wanda duk ya ɓata kayansa da cakulet suka fara knocking. Aka bude, harararta Amrah ta yi.
"Sai yanzu ko? Yinin kenan?"
Ramlat na dariya ta juya.
"Shikenan, bari mu juya daga nan." Da sauri ta kama hannunta ta maidota baya suna dariya.
"Ni ban ce ba, yi hakuri."
Suka shiga ciki suka zauna, nan take sanarmata sai da ta biya gidan Muhibbat.
"Allah Sarki Muhibbat, matarnan akwai kirki wallahi. Ba ruwanta, kinsan babu ranar da ba za ta turomin gaisuwar juma'a ba."
Murmushi Ramlat ta yi.
"Ai wannan daban take cikin mutane ma. Allah dai Ya bamu ikon yin zumuncin mu ma."
Amrah ta amsa da Amin. Ramlat ta shiga waige-waige.
"Ke ina ƴata wai? Tun da kika ce min kun dawo ita nake son ganin yanda ta girma."
"Tana wurin Mama na kai mata yaye. Abinda ya ban mamaki ko ciwon nono ban yi ba."
Ramlat ta dara.
"Kika sani ko wani cikin ya shiga? Tsarabar Lagos?"
"Allah Yasa. Ai nikam ina so wallahi."
Ba ta yi mamakin kalaman Aminiyarta ba don tun bayan aurenta sai da ta shekara biyar ba ta samu ciki ba sai yanzun. Mijinta Ɗahiru ya ce ba ita babu planning sai ta yi biyu.
"Allah Ya kawo mai albarka toh. Nidai yanzu yunwa nake ji."
Miƙewa suka yi a tare zuwa kicin Amrah na fadin.
"Mutuminki ɗan wake nayi niyyar yi kuwa, na haɗa komai ki dora ruwa idan ya tafasa ki yi sakin bari na yanka mahaɗin."
"To da ban zo ba fa?"
Amrah ta yi dariya.
"Ai kuma tunda kin zo din magana ta kare. Yi hakuri ki taimaka ban jin dadin jikin."
Haka ta soma sakin ɗan waken tana yi suna hira.
"Ni kuwa ina Hilal?"
Tambayar Amrah ta tunasar da ita yanda suka yi a kwanakin baya, text ya yi mata akan ta sanyamishi rana da lokaci ya zo su tattauna abu mai muhimmanci sai dai ba ta yi karambanin ba shi amsa ba, daga ranar kuma bai ƙara nemanta ba.
"Kamar ban kyauta masa ba, amma a wurina hakan ne daidai."
"Me kika yi mishi?" Jin abinda Amrah ta ce yasa ta fahimci zancen zucin ya fito fili, nan ta bata labarin yanda suka yi. Ajiye wuƙar hannunta ta yi ta juyo da mamaki ƙarara saman fuskarta tana dubanta.
"Meyasa kike yiwa kanki irin wannan gangancin?"
Cikin rashin fahimta ta ɗan dubeta.
"Wane gangancin kuma?"
Haushi da takaici ya kusan kashe Amrah anan tsaye.
"Tambaya kike Ramsy? Ko kin manta na tunamaki waye Hilal? For all abinda ya faru bai sa ya juyamaki baya ba, bai kuma sa ya bar sonki ba, don me yanzu kin samu damar gyara laifukanki kike kokarin juyamasa baya? Allah Kike son yiwa butulci?"
Murmushi mai ciwo Ramlat ta yi, ba ta ce komai ba ta juya ta ci gaba da sakin ɗan wake, sanin hali na idan ta ga dama ba za ta ce uffan ba yasa Amrah itama ta ci gaba da aiki sai dai ta kumbura kiris ya rage ta fashe. Dama sun saba irin haka tun yarinta.
Ita kuwa sai da ta kammala ta wanke hannu ta jira ya dahu ta kwashe ba ta ko tsaya tambayar inda filas yake ba ta dauko. Sai da za ta zuba ne Amrah ta dakatar da ita.
"Wannan na Daddy ne." Tana nufin mijinta, murmushi Ramlat ta yi don tasan ƙawarta ta shaƙa, ta fice daga kicin rike da plastic din da Amrah ta yanka kayan cin dan waken. Sai da ta soyamusu manja sannan ta fito itama. A falon suna zaune sannan ne Ramlat ta dubeta a nutse.
"Tsaya don Allah ki saurareni."
Amrah ta dakatar da zuba ɗan waken da take kokarin zubamusu bayan ta ɗibarwa Affan nashi ya ja gefe. Harararta ta yi.
"Me kuma za ki cemin bayan kin maidani wata banza don kawai ina nunamaki abinda ya dace."
Hannunta ta riko tana dubanta.
"Kiyi hakuri, wallahi duk ba haka bane. Amrah yanzu ke a tunaninki da wane ido zan kalli Hilal na ba shi dama a karo na biyu bayan ni ce ummul aba'isin duk wani abu da ya faru a baya? Ko kin manta ba da Hilal kadai zan zauna ba? Akwai matarsa kuma akwai danginsa da babu ranar da zan goge bakin fentin da na yiwa kaina a idanunsu? So kike na bar wa ƴaƴan da zan haifa da shi abin gori? Yanzun ma wadannan din da ya na ƙare? Kin fi kowa sanin abinda ya faru, kuma kin fi kowa sanina Amrah. Da ace zan iya auren Hilal, da tuni yanzun wani labarin ake banda wannan. Amma bakin alƙalami ya bushe, zan iya yin aure ga kowane mutum a doron ƙasa banda Hilal. To balle ma auren babu shi a gabana yanzu, na gwammace na zauna na kula da yarana. Hakan zai fiyemin komai dadi."
Tausayinta sosai ya kama Amrah, har ba ta san sadda hawaye ya zubomata ba, ita kanta uwar gayyar sai jin ɗuminsa ta yi saman kuncinta. Ta kuwa shiga yi ba kakkautawa.
"Na cuci rayuwata Amrah, na cutar da mutane da dama wanda har gobe ban bar dana saninsa ba. Amrah har gobe ina tunanin bakin cikina ne sanadin mutuwar Abbana duk kuwa da irin rabuwa ta salama da amincin da muka yi. Ƴan uwana ba sa fahimtana, har gobe suna min kallon mai laifi a idanunsu. Ya zan yi ne wai?"
Nan fa suka shiga kukan har Affan wanda ganin Mominsa na kuka shima ya shiga yi. Dakyar suka rarrashi kansu sakamakon ƙarar da Affan yake da kuka yana rirriƙe Ramlat. Komai da komai ya shiga dawowa kwanyarta, daga lokacin da ta saki jiki suka soma gudanar da soyayya mai karfi tsakaninta da Aliyu, daga lokacin ne komai ya faro asali wanda har gobe ta kasa goge *BAƘIN FENTIn* a zuƙatan masoyanta.
***
*BAƘIN FENTI*
_*Komai yana da sila, komai da mafarinsa. Duk abinda bawa bai ɗora kan turba mai kyau da tsari ba, mafi yawan lokuta ƙarshensa nadama ne! Koda ace a haka kaddarar ta zo masa.*_
"Wai Ramsy me kike ne? Ki fito kina ɓata lokaci."
Muryar Amrah kenan sa'ilin da ta ke kokarin shigowa dakin. Zuwa yanzu ta kai matakin da ba ta jin za ta ɓoyewa kowa a duniya sonta ga Aliyu. Wannan tasa ko bayan shigowar Amrah ba ta fasa amsa wayar a nutse ba ba ta ko damu da kallo da murmushin Amrah ba.
"Kai wannan Hilal, shi ba ya jin kudinsa ko? Daga Malaysia mutum ya kira a yi ta wayar fin sa'i biyu? To nidai don Allah ya kyalemin ke ai daya, idan ba haka ba wallahi zamu yi lattin."
Ba ta da niyyar ba ta amsa, ta fahimci ba ta gane wanda suke wayar ba, ko ma ta ce ba ta sanshi ba.
Daga dayan gefen Aliyu wanda ke zaune a falon Muhibbat yayinda ita kuwa ke kicin tana shiryamusu abincin rana ya ɗan hade fuska kamar tana kallonsa.
"Baby waye Hilal? Baby ashe ban Kai darajar da har yanzu za ki iya sanar da mutane ni din kike so ba ba wani banza ba? Watanni goma da soyayyarmu wanda ya fi karfin na wadanda suka kwashe shekaru goma suna yi shine har yanzu ban samu karɓuwa ba? Sai anjima."
Ya katse wayar gaba daya yana fitar da huci. Fitowarta kenan daga kicin, ta ji dukkan abinda yake fadi, sai dai ta yi kamar ba ta ji ba. Ranta na ƙuna kamar koyaushe, ta haɗiye kwallar dake barazanar tona abinda ke ranta. Ganin ya ɗan kalleta ya kauda kai ya ja tsaki ya sanya ta kakalo murmushi ta nufi inda yake zaune a darare.
"Yaya na kammala girkin."
Ya yi mata kallon sakara. Ta sauke kwayar idanunta, a duniya