Showing 180001 words to 183000 words out of 226732 words
ka ke mata."
Nan ma dai shirun ya kara samu maimakon amsa, Hisham dole ya ja baki ya yi shiru don ya soma jin haushi.
"Zamu je Yakasan?"
Ya tambaya bayan ya yi tuƙi mai ɗan tazara daga gidan su Ramlat. Ajiyar zuciya ya saki ya dubeshi da jajayen idanun da ɓacin rai ya rinar.
"Ba zan iyaba. Mu yi hakuri ko zuwa gobe ne, ba ta ɓaci ba."
"Ok!" Yanda Hisham din ya amsa sai ya tabbatar da fushi ne don haka ya yi ɗan murmushi.
"Ka yi hakuri."
Shima Hisham don ya rama sai ya shareshi, a karshe ma ɗaya daga cikin waƙoƙin Breaker ya kunna mai suna So.
A hankali Hussein ya lumshe idanu yana sauraron waƙar, wani abu ke ratsa zuciya da gangar jikinsa sai dai kuma yana ji a jikinsa ba mai yiwuwa bane. Daga yau zai mishi iyaka da zuciyar da gangar jikinsa har sai ya ga abinda hali ya yi.
***
Hajiya Zeenatu ta ƙara buɗe zanin jikinta, fitowarta daga banɗaki kenan. Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi, maimakon da ta soma shafa cream na ƙuraje da likita ya ba ta, kurajen su mutu sai abin ya kara yin gaba. Don a farko iyakar cinyarta ne kadai, yanzun kuwa har su na kokarin dabaibaye dukkan wata gaɓa daga ƙugunta zuwa ƙasa. Ta kuma lura da wani abu guda, ko yaya ruwan ya taɓa jikin fatarta sai wani kurjin ya fito.
"Na shiga uku ni Zeena! Me zan gani?!"
Ta dora hannu a kai nan da nan idanunta suka fito ƙululu kamar za ta yi kuka. Wato dai don bakin ciki cuta bai tashi yi mata kamun kazar kurkuku ba sai da ta ke dab da more rayuwarta da miji? Sai da komai ha daidaita babu tsafi balle asiri?
Wani irin miƙewa da ta yi sai da zanin ya faɗi, ba ta bi ta kai ba ta karasa sif na kayanta, doguwar riga ta sauya hannunta har wani irin rawa ya ke yi, ta gwammace yau ta je babban asibitin Malam ta ga likitan fata. Tana ji a jikinta abin daga fatarta ne. Ba ta yi tunanin ciro waya ta kira Hussein da zummar neman izni ba, sai da ta shiga mota, koda ta fadamasa a dawo lafiya kawai ya ce daga nan bai ƙara uffan ba, itama ba ta son ya kara don yanzu ta lafiyarta ake. Babban tunaninta yanzu komai na tafiyarsu London ya zama ready, ga samu ga rashi. Haka ta ke ji a ranta.
***
Yau kwanaki biyu kenan da Yusufa ke zaryar gidan su Ramlat sai dai ba ya samunta. A karshe dai ya nemi lambar wayarta ya kira. Bayan sun gaisa ya yi kata kwatancen ko waye shi. Jin ya ce shi ɗin ƙanin Halima ne yasa ta maida hankali ga sauraronsa.
"Aunty maganar ba ta waya ba ce, saƙo ne daga Yaya Halima, tun ba yau ba ta ban ta ce na isar gareki. Na so ajiyewa wurin Maigadin gidanku amma kuma bana so ya kasance bai isa hannunki ba."
Da mamaki Ramlat ta gyara zama saman kujerar Office din.
"Kana ji? Ko zan maka kwatancen ofishin da nake aiki sai ka kawomin."
Cikin zumudin hakan ya amsa da toh ya kuma yi mata godiya.
Wuraren karfe biyar da mintoci na yamma sai ga Yusufa. Da kanta ta fita suka gaisa, sau ɗaya ta taɓa ganinsa, rashin lafiyar Kakar Halimar da ya tashi suka je dubiya asibiti daga tsohuwar ma'aikatarta. Suka gaisa kafin ya ciro takarda a ninke ya miƙa mata.
"Ki yi hakuri wallahi saƙonnan ya fi sati a hannuna, rasuwar Kakarmu ce ta sanya ban kawomaki ba sai yanzun. "
Cike da jimami ta ce.
"Kaka ta rasu? Allahu Akbar, Allah Ya yi mata rahma. Yasa aljanna makoma. "
Yusufa ya amsa da amin. Daga haka suka yi sallama bayan ta mishi ihsani.
Kasancewar an kusan tashinsu daga aiki yasa kawai ta jefa a jakarta.
Ba ita ta samu damar warware takardar ta karanta ba sai bayan Magriba. Lokacin ta samu nutsuwar wanka har ma da na cin abinci. Ga abinda ta kuntsa.
_*Assalamu alaikum Ramlat.*_
_*Da farko zan soma da ba ki hakuri, haƙiƙa na sani ni Halima ban cancanci komai daga gareki ba ballantana har ki yafemin. Sai dai duk da haka ina mai nadama da dana sanin abinda na aikata gareki. Ni mai laifi ce, ina neman gafararki Ramlat. Hassada da son abin duniya irin nawa ya kai ni ya baro. Yau ganinan a gidan da ko a mafarki ban taɓa zaton zuwansa ba.*_
_*Na aikata bisa tursasawar Hajiya Zeenatu da kawarta Hajiya Batulu. Duk irin tsanar da na yi maki ba zai sa na yi yunkurin kashe ki ba. Duniya aka kwaɗaitamin, ni kuma na karɓa da gaggawa ba tare da tunanin abinda zai je ya dawo ba. Ina neman gafararki. Ki yafemin domin Allah Ramlat. Wallahi a yanzu haka na tsani kaina. Ba ni da kwanciyar hankali daidai da kwayar zarra. Ki yafemin ko zan samu ganin haske a rayuwata da kuma mafarkaina. Na gode.*_
_*Halima Shehu.*_
Ajiyar zuciya ta saki sannan ta ninke takardar, a hankali ta sanya bayan hannu ta share hawayen saman fuskarta. Ba ta taɓa kawowa Hajiya Zeenatu ce ta sa Halima kasheta ba. Sai dai tayar da zancen ta san ba shi da amfani, ta bar wa Allah komai.
Ta ƙurawa takardar idanu sai kuma ta yi murmushin yaƙe ganin cewar Halima ba ta da masaniyar ita ta jima da yafemata ma. Gefen dirowar gadon ta buɗe ta cilla.
"Mami! Mami!"
Ansar ne ya shigo hannunsa riƙe da wayar Hajiya yana game.
"Wai Hajiya ta ce ki zo, ga Baba Dakta ya zo."
Ta ji kirjinta ya buga. Ta amsa da toh sannan ta mike ta yafa mayafin doguwar rigar da ke jikinta. Hajiya na zaune ta sha lulluɓi su na ɗan taɓa hira. Ta karasa ta durkusa ta gaidashi. Ya kalleta da fara'arsa. Ta mike ta koma kicin ta kawomishi ruwa da lemu. Sannan bisa umarnin Hajiya, ta ja yaran zuwa ciki don su yi magana.
Hankalinta ya kasa kwanciya a dakin, zirga-zirga kawai ta shiga yi, ganin an kwashi mintuna yasa ta kasa hakuri sai da ta ɗan kasa kunne. Ta ji Hajiya da na fadin.
"Ai wannan ba a bukatar jin ta bakina ko ita Ramlatun. Ramlatu da Amrah duk daya ne. Dukkan hukuncin da ku ka yanke a kanta nasan ba za ta taɓa yin da na sanin zaɓinku ba in sha Allahu. Balle kuma dama akwai fahimtar juna tsakanin yaran. Ni dama hankalina ya fi kwanciya da shi tunda ko ba komai ba wannan ne aurensa na farko ba. Allah Ya sanya alheri. Ya sa ayi muna raye."
Ramlat tuni ta ji wani gumi na tsastsafo mata, kirjinta ya tsananta bugu, ta ji Baba Dakta na kara godiya da yiwa Hajiyar addu'a. A karshe ma yake batun zai je takanas can Yakasai ya ga su Kawu su yi magana. Gwuiwa a sake ta juya ta koma saman gadon, Affan ya damu da kai ƙarar Ummi ta ɗauki wayar Mamin, ba ta san sadda ta dakamasa tsawar da dukkan yaran sai da suka tsorata ba. Ta ja guntun tsaki ta riƙe kai, salati kawai ta ke yi da addu'ar Allah Yasa hakan ya zamemata alheri. Ta dafe saitin kirjinta, ba ta taɓa zaton lamarin aurenta da Baban Hanif zai zo mata da yanayin ɓacin rai kwatankwacin na Hilal ba sai yanzu. Sai dai wannan karon alƙawari ta yiwa kanta, ko me zai je ya zo, za ta rungumi zaɓin iyayenta da hannu bibbiyu.
"Ki godewa Allah da zaɓinSa. In sha Allah jikina yana bani wannan aurennaki shi zai zama na dindindin duk kuwa da cewar sai an yi hakuri kuma an kai zuciya nesa saboda kananun maganganun da kan iya tasowa."
Wannan shi ne kadai abinda ta ji a bakin Hajiya, nan ta tuna wayarta a safiyar yau da Baban Hanif, inda cike da damuwa yake sanarmata irin tashin hankalin da yake fuskanta daga iyayensa game da aurenta da ya yi niyyar yi. Labari ya zo musu cewar ta taɓa yunkurin kisa a aurenta na farko. Wannan ne dalilin da yasa gaba ɗaya a kwanakin ta kasa gane inda ya nufa.
Ramlat ta dubi Hajiya karo na ba adadi tun zamanta a falon, waya Hajiya ta shiga yi da Munir, ta kasa kunne amma a karshe ma sai Hajiyar ta miƙe ta nufi ɗaki. Ranta sai ya soma ɗan baci. Ko ba komai ba wannan ne aurenta na farko ba, ya kamata ta san wa za ta aura ai. Hakan kuma bai nufin jayayya za ta yi da su. Ko kadan, ta rantse koma waye ta yarda kuma ta amince da aurenta da shi, kawai dai tana son sanin waye. A gefe guda kuma jikinta yana ba ta cewar ta yi BANKWANA DA HUSSEIN. Bankwana na har abada.
"Mami! Wayarki."
Ta sa hannu ta karɓa a hannun Ummi. Baban Hanif din ne kuwa ya kira don haka ba ta jira ya kara ba ta bi bayansa. Sai da ta shiga daki ta rufe kafin ta amsa sallamarsa. Bayan sun gaisa a gaggauce ta ce.
"Kun yi magana da Baba Dakta ne?"
"Eh ya kirani dazunnan da yamma, mun yi magana sosai da shi. Labari ya zo maki kenan?"
Ta kasa magana kawai sai ta kashe wayar gaba daya, kai ta dora saman gwuiwar ƙafafunta ta shiga rera kuka. Kukan jin zafin Hussein da ya kasa kallonta matsayin masoyiyarsa. Ta gasƙata cewa yanzun babu wani abu da zai ƙara shiga tsakaninta yanzun. Ta ji kuma ta hakura da zaɓin Allah. Dakyar ta iya miƙewa ta faɗa ɗakin yaranta, kowannensu ta gyarawa gado don yanzun ta sauyamusu da gado kanana na yara kowanne da na shi. Ta kakkaɓe, ta ba su umarnin kwanciya. Kasancewar sun saba da baccin wurin hakan yasa su na kwanciyar bayan ta sa sun yi addua, bacci ya ɗauke su.
Ta yi shiru tana kallonsu bayan ta gama kwashe shirgin kayan da suka zubar a ƙasa ta ninke kayan sif din da ya lalace. Aliyunta ne ya faɗomata, zuciyarta ta ƙara karyewa, nan ta shiga rera wani sabon kukan. A karshe don kanta ta rarrashi zuciyarta ta share sannan ta fita ta ja musu ƙofar.
"Ashe AlHassan ya zo garinnan?"
Ta dubi Hajiyar da le tambayarta, robb ta ke faman shafawa a ƙofofin hancinta.
"Ban sani ba wallahi. Yaushe?"
Murmushi Hajiya ta yi.
"Ai da Husseini muke waya, sai ya ba shi muka gaisa. Wai jiya-jiyan nan. Amma ya cemin zuwa gobe zai shigo in sha Allahu."
"Allah Ya nunamana."
Ta fadi a ɗan gaggauce don ji ta ke yi kamar ta fashe da wani kukan.
Hajiya na lura da ita kuma abin na ba ta mamaki amma ba ta ce uffan ba. Ta san dai idan ma da wani abu na daban a zuciyar Ramlatun, dole yanzu ta yi kokarin kawar da shi tunda dai bakin alƙalami ya riga da ya bushe.
***
Tun sadda Hajiya ta shaidamata cewar ana nemanta a Yakasai, Kawunnanta, kirjinta ke bugu da sauri. Affan wannan karon maƙalewa ya yi zai bi ta, dole ta shirya shi suka fita tare. Adaidata Sahu suka hau kasancewar motarta ta samu matsala.
A hanyar ma babu cikakkiyar nutsuwa tattare da ita sakamakon tunanin abinda zai biyo baya da ta sa a rai. Kiran ko kusa bai ba ta mamaki ba, ta san dama tunda har aka ce an mata miji to komai ma za ta gani. Har dai suka iso ba ta jin ta ba Affan kwakkwarar amsar tambayoyinsa na shirme da ya ke mata. Karshe ma da ya dameta cewa ta yi za ta bar shi a cikin Napep din dole ya ja baki ya yi shiru.
Ɓangaren Baba Dije ta soma shiga. Bayan sun gaisa ta ce.
"Ina tayaki murna ƴarnan, kin yi goshi wannan karon ba shakka. Allah Ya sanya alheri ya nunamana lokacin."
Ta rasa yanayin da ta shiga. Ta kasa amsawa hakanan ta kasa cewa komai don haka kawai sai ta mike ta fita tana murmushin yaƙe.
"Ayiririri!"
Guɗar da ta ji yasa ta waiga, Baba Hajara ce yayar Hajiyarsu. Su uku ne kadai mata a wurin Hajjar, Baba Hindu, Baba Hajara sai Hajiya. Mazan kuwa su uku, Kawu Jamilu, Kawu Bello da Kawu Sunusi, su ne manyan maza a ɗakin.
Jiki a sanyaye ta gaida ta kafin ta karasa ɗakin Hajja itama Baba Hajara na daga bayanta.
Hajja ce zaune tana shan fura, tana ganin Ramlatun itama ta saki fuska.
"Kishiyar ce a tafe kenan? Sannu da zuwa."
Ita dai ba ta ce uffan ba, Affan ya karasa a guje ga Hajja. Zama ta yi gwuiwa a sake kafin ta maida hankali ga Baba Hajara.
"Wai Baba lafiya?"
Baba Hajara ta zauna tana dariya, ba ta kai ga magana ba Hajja ta katse ta.
"Na rabaki, idan ba so kike tarihi ya maimaita kansa ba. Ki bari ta ji komai daga bakin Ubanninnata. Ai ba abinda zamu ce ga Dakta (Baba Dakta) sai godiya da fatan alheri. Allah Ya biyashi da aljanna. Yanda yake nunamaku kulawa kamar ƴaƴan da ya haifa a cikinsa, Allah Yasa aljanna makoma. Na ji ma ance ya kawomaku kayayyakin abincin azumi, to nan ma haka ya aikomin. Wannan bawan Allah sai fatan alheri da fatan Allah Ya jiƙan iyaye."
Baba Hajara ta amsa da amin, itama Ramlat ta amsa ta hanyar motsa lebbanta amma dukkan wata gaɓɓa ta jikinta ta yi sanyi. Can kuma sau ga shigowar saƙo. Hussein ne. Ta bude hannunta har rawa ya ke don yanzu ta kasa fahimtar komai.
_*"Ban yarda da dukkan wani so da za'a yi shi kafin aure ba. Ban kuma yarda akwai kulawar da namiji zai yiwa mace ba da za ta kere kulawar miji ga matarsa. So da kauna na gaskiya ya fi ma'ana idan aka zama mallakin juna. Ina taya junanmu murna."*_
"To wai me yake nufi?" Ta tambaya a fili bayan ta karanta ya fi sau biyar amma ba ta gane komai ba.
"Wa kenan?" Hajja da Baba Hajara har suna haɗa baki wajen tambaya. Ta ma kasa cewa uffan sai kai da ta girgiza tana sharar gumi ga kwalla cike a idanunta.
"Idan ma za ki saka ranki a inuwa tun wuri gwara ki sanya don wannan karon na tabbatar wanda za ki aura ba fetur ba, Allah Yasa tankin mai gaba daya za ki zazzaga maku, zai yarda ku mutu ƙurmus! Sawun giwa ya take na raƙumi!"
Hajja ke wannan sababin ta karashe da kurɓar furarta ta bar Baba Hajara da dariya. Ita dai Ramlat ba ta ce komai ba sai hawayen da ta shiga sharewa, gaba daya gaɓoɓin jikinta sun yi sanyi, yanzun kuma abin haushi ya ke bata.
"Yaya Ramlatu ki zo inji Kawun Zaure."
Wato Kawu Jamilu kenan wanda shi hanyar shiga sashinsa na daga wurin zauren gidan, ai ba ta ma jira Hauwa diyar Kawu Sunusi ta karasa faɗin saƙon ba ta yin zumbur ta miƙe tsaye har wayarta na faɗuwa amma ba ta ko damu da ɗauka ba. Tana ji Hajja na fadin.
"Kuma yarinya ta dawomin daki da baki kamar gonar auduga sai na yi ƙasa-ƙasa da ita. Maza Affan bani wayarnan idan mijinnamu ya zo sai ya siyamata wani."
Tana jin dariyarsu amma babu wanda ta tanka asalima baki ta turo ta ɗan ja guntun tsaki tsabar ɓacin rai. Haka ta dinga tafiya har sashin Kawu Jamilu, duk a zatonta shi kadai ne, sai ganin sauran Kawunnan da ta yi zaune ƙasan bishiya suna taɓa hira. Ta karasa gami da durkusawa ta kwashi gaisa. Suka amsa fuska a sake duk da cewar kanta a ƙasa yake amma sautinsu ya nuna hakan. Sai da aka gama gaisuwar da ɗan barkwanci kafin Kawu Jamilu ya yi gyaran murya ya soma magana.
"Toh Ramlatu, abu na farko shi ne mu miƙa godiyarmu ga Ubangiji domin Shi ya yi mana dukkan ni'ima. Ya kuma so ki da dukkan rahma da mu ɗin gaba ɗaya. Alhamdulillah."
Ya ɗan ja numfashi gami da gyaran murya sannan ya ci gaba.
"Kamar yanda ki ka ji daga bakin mutanen gida, abin alheri ne ya sameki. Babanki Dakta ya yi maki zaɓi bisa damar hakan da kika damƙa maki. Kar kuma hakan yasa ki yi zaton cewa shi da kansa ya haɗa auren, aa, shi yaron ma asali tun ana zancen aurenki da Dikko ya tunkari Baba Daktan da batun aurenki sai dai Baba Daktan ya ba shi hakuri ya kuma sanarmasa da batun Dikko, a karshe ya yi mishi kwatancen gidannan ya ba shi lambar wayar Kawunki Bello cewar yana iya zuwa nan wurinsa ya faɗamasa ko Allah Zai sa a dace. Da yake shima yaron nada hankali ya ce aa babu komai, ya yarda Allah bai kaddara ke din rabonsa ba ce. Ba ya son ya yi nema cikin nema. Wannan ne dalilinsa na janyewa bayan ya nemi alfarmar su bar maganar tsakaninsu. Yanzun ma da kika ji, magana ce ta kawo magana shiyasa ya faɗamana shi Babannaki. Sai kuma cikin ikon Allah lamarin aurenki da shi Dikko ya lalace, anan ne kuma bayan kin bar wuƙa da nama a hannun Daktan, ya ba wancan yaron iznin turo nashi magabatan bayan shawarar da ya yi da mu kuma muka amince. Alhamdulillah, Ramlatu ke ba yarinya ba ce, mun kuma sani, yanzun kin fi baya hankali. Kin kuma ƙara hankaltar rayuwa. Mun sani, wannan karon ba za ki ba mu kunya ba in sha Allahu."
Zufa sosai ta ke fitarwa, ta hadiyi miyau mai ɗaci, ba ta bar ambaton Innalillahi a ƙasan ranta ba har zuwa sadda Kawu Jamilu ya miƙomata damin kudi ƴan ɗari biya-biyar a baƙar leda bayan ya warware ledar ya turo kudin gabanta.
"Wannan ne kudin aurenki, dubu ɗari gashinan. Juma'a mai zuwa cikin yardar Allah za'a ɗaura aurenki da HUSSEINI MODIBBO. Ina ce haka sunan yake ko?"
Ya karashe yana duban yan uwansa da dariya, suka dara lokaci guda.
"Hakayake Yaya." Kawu Sunusi ya bada amsa.
Ta rasa me za ta ce, ta kuma rasa me za ta yi, a zaune ta ke amma jiri ta ke ji. Kanta ya yi wani irin sarawa, lokaci guda ya shiga ciwo. Hawayen da ta tsayar a ɗazun, suka ci gabada kwaranya su na ɗiga saman k
rafar ɗari biyar biyar din da Kawu ya ajiyemata. Wa ya faɗamusu sonta yake?[3/17,