Showing 117001 words to 120000 words out of 226732 words

Chapter 40 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12473

kece da ita, hatta ita Ramlat sai ta ji maganar nata banbarakwai, ta kara hade fuska.

"Haba Hajiya Ramlatu, yanzu fa na gama fadamaki ke ba yarinya ba ce. Wane sokon ne zai yi gangancin tsallake sati biyu ba'a ɗauka muku aure ba? A'a ban yarda ba gaskiya. Nidai ki karɓi ƙoƙon barata ki ba address da kanki a ganina zai fi mana mutunci."

Ta yi shiru, ya ci gaba da magiya kamar ba Chairman mai cin magani a gaban staffs ba, haka ba don ranta ya so ba ta mishi kwatance. Ranar kowa ya kalleshi yasan yana cikin farin ciki marar misaltuwa.

Koda aka tashi, kai tsaye tsohon department din da take ta ziyarta. Ta kuwa ci sa'a duk suna ciki, aka gaisa ba ta ko bi ta kan Halima mai amsa gaisuwar ciki-ciki ba.

"Yanzun nake shirin shiga wurinki. Ƴar halak kin ƙi ambato."

Ta kai duba ga Naja'atu Azare mai wannan batu, suka yi dariya. Takardar gayyatar biki ta fiddo daga jakarta ta miƙa mata. Murmushi sosai Ramlat ke yi har fararen haƙoranta na bayyana.

"Kai na ji dadi sosai wallahi, ki ce abun ya zo. Allah Ya nunamana, Yasa muna raye." Aka amsa da Amin.

Hira ta tsaya yi a karshe suka dunguma gaba daya matan suka fita, Halima har lokacin fuskarnan ba fara'a.

"Wai ke me akai miki kike ta cin magani?"

Saudat ke tambayar tana dubanta.

"Ba komai, sai Allah Ya kaimu."

Daga nan ta yi gaba ta bar su.

"Wai nikam Ramlat kamar dai akwai wata a ƙasa tsakaninku da Halima, na lura duk sadda kike wuri ba ta fiye kaunar hakan ba." Samira ke wannan maganar tana duban Ramlat. Ita kam murmushi kawai ta yi, tana ji suna faɗin rashin kyautatawar Halima a lokuta da dama ita dai ta musu sallama ta nufi inda ta yi parking. Idan da sabo ya ci ace dama ta saba da halinta. Murmushi ta yi da wani bahagon tunanin da saƙe-saƙen zuciya ke jefawa ɗan adam ya ziyarceta, wato ace ta yarda da auren Chairman, Allah Kadai Yasan irin kiyayyar da za ta fuskanta daga Halima. Ba ma daga gareta kawai ba, har da yawa cikin matan wajen.

***
  Zaune gaban Boka Gora, Hajiya Zeenatu ce da Hajiya Batool kowannensu rai a ɓace.

"Shekaru sama da goma muna tare da kai, kar ka yi mana haka. Ka taimakemu ka kula da damuwarmu. Bamu da wanda muke da shi da zai share hawayenmu face kai." (Wa'i'yazubillah)

Gora ya yi wata dariya ta shaiɗanun da suka riƙa kafin ya ɗaure fuska tamau. Ya kwalalo musu manyan idanuwansa da suka sha kwalli.

"Kar ku rainamin hankali! Wa ya fadamaku zan kasa sanin kun yi doguwar tafiya har wata ƙasa don a yi muku asiri? Cin amanar da zai biyo bayan dukkan taimakon da na yi muku a baya kenan! Yanzun da ku ka zo me kuke so nayi bayan komai ya warware! Komai ya lalace! Ke Zeenatu! Ki fara tattara kayanki ki bar ƙasarnan don asirinki ba zai je ko'ina ba sai tonu! Ita dai yarinyar da na gargaɗeki a kanta, ita ce silar rushewar dukkan ayyukanki! Ke kuma Batulu! Nan ba da jimawa ba, ɗanki zai zo da batun ƙarin aure! Auren da zai rushe duk wani asiri da kika yi tsakaninsa da matarsa! Anan ne duk abinda kika binne zai fito fili muraran!"

"Ƙarya kake! Wallahi ƙarya kake! Dama na faɗamaki kar mu zo wurinsa!"

Hajiya Batool ke maganar jikinta har yana ɓari, fuskarnan wacce man bleaching ya maida jawur, sai ƙara kyalli take. Ita kuwa Hajiya Zeenatu idanun kamar an watsa barkono. Ba ta san hawaye ke fita daga idanunta ba sai da ta ji suna kokarin shigewa bakinta. Shi kuwa Gora banda wata shegiyar dariya ba abinda yake yi don ko kaɗan kalaman bai ɓatamasa ba, ya saba ganin irin wannan hauka da jahilcin na mata.

  Tsawa Hajiya Zeenatu ta dakawa aminiyarta ganin gaba ɗaya ma ta ƙi maida hankali ta nutsu su nemi mafita. Ita da take da tashin hankalin rasa miji irin Hussein ba ta yi gigitar da Hajiya Batool ta yi ba. Ta sa mayafi ta sharce gumi idanunta a kansa.

"Mun tuba, wallahi mun tuba ba zamu ƙara saɓawa umarninka ba. Ka taimakemu Gora, a wannan gaɓar idan ka ce za ka bar mu, ba wanda zai tsira."

Ya ci gaba da kallon ƙasar da ke shimfiɗe gabansa yana ƴar dariya gami da gyara hannun babbar rigarsa.

"Akwai tsada..."

Bai ma kai ga ƙarasawa ba duk suka tari numfashinsa.

"Zamu biya ko nawa ne, wallahi ko duka abinda muka mallaka ne."

Ya jinjina kai, kaf ba wacce bai san halinta ba a cikinsu. Yana da karatun kowaccensu don tun ana damawa da su a siyasa da bariki yake tare da su. Maida hankali kan ƙasa ya yi can kuma ya ɗago ya dubi Hajiya Zeenatu. Yanzu da ace zai faɗi ainahin abinda ya gani, toh ya tabbatar kuɗaɗen da suka Kaɗaita masa ba zai samu ba, gwara ma Hajiya Zeenatu akwai sakin hannu, anan ne suka sha bamban da aminiyarta da ta kasance marowaciya.

"Aikinku zai yiwu, sai dai dama ai na riga da na faɗamaku akwai kashe kuɗi. Batun kuma shi mijinnaki ina tabbatar maki ba zai haɗu da ɗaya cikin ƴan uwansa ba. Sai dai kuma ki kara kiyayewa ga barin kowace mace shiga rayuwarsa. Idan na ce kowacce, ina nufin hakan!"

Ya fadi kai tsaye, kusan bayanai biyun ƙarshe da ya yi sun kasance abinda ya hanga ɗin.

Jinjina kai Hajiya Zeenatu ta yi, nan kuma Gora ya shiga lissafomata abinda za'a siya. Da ta gaji ta bude jaka ta fiddo bandirin ɗari biyar sabbi har biyu ta ajiye a gaban buzunsa.

"Gashinan, na bar maka wuƙa da nama, duk abinda ya kamata nidai a yimin don Allah. Sannan idan da hali a yiwa ita yarinyar turen aljanu su zama silar ajalinta. Nidai ko haukatamin ita ne don Allah a yi Gora."

Wani murmushi Gora ya yi ya sa hannu ya dauki kudin gami da faɗin.

"An gama! Kedai kawai ki sha kuruminki."

Daga haka ya juya ga Hajiya Batool wacce ganin irin yanda ya  kwantar da hankalin Hajiya Zeenatu da bayanan gamsuwa da kuma karfafa gwuiwa, itama sai ta ji nata ya kwanta. Nan ya shiga kora mata karya da gaskiya itama ta hau ta zauna ta cikashi da kudin. Kafin dai a bar gidan Gora an shirya, dariya ake yi har yana neman su ba shi haɗin kai yanda suka saba.

"Alƙawari ne mun yi maka, zamu cika mu ziyarceka da zarar aiki ya kammalu." Cewar Hajiya Zeenatu da take ji kamar an mata albishir da mutuwar ɗan uwan Hussein.

Wata dariya suka yi tare kafin su fice. Sai a sannan hankulansu ya kwanta.

***
   BAYAN KWANA UKU.

  Tun wuraren biyu na rana ta samu kira daga Alhassan (wanda tuni ta sauya mishi suna daga mutumin mall zuwa Alhassan kamar yanda ta ga username ɗinsa a WhatsApp). Sanarmata da batun zuwansu da iyalinsa ya yi, wannan tasa bata zauna ba, ita da Hajiya da Ladidi suka shiga kicin don yin kayan maƙulashen tarbar baƙi. Suna tsaka da aikin sai ga Zulaihat da Rafee'ah, mamakin irin wannan garar da ake shiryawa ta kamasu.

"Baƙi za ku yi ne Hajiya?" Cewar Zulaihat tana duban kajin da Ramlat ke soyawa.

"Au, ashe mu ba zamu ci daɗi ba kenan sai zamu yi baƙi?"

Dariya ta basu.

"A'a, amma dagaske naga kayan ne da yawa har da su zoɓo da ginger. Duk na waye?"

Murmushi Hajiya ta yi.

"Ku tambayi ƙanwarku."

Ramlat ta sanarmusu batun zuwan Alhassan wanda suka taɓa jin ta yi waya da su. Rafee'ah ta kama baki tana dariya.

"Ah lallai, ki ce surukinmu ne zai iso. Kai abu ya yi kyau."

Yamutse fuska kawai ta yi kafin ta murmusa, ita dariya ma suke ba ta idan suna haɗa ta da AlHassan. Ko za ta kwana ta na faɗamusu zumunci ne kawai tsakaninsu ba yarda zasu yi ba don haka ta ja bakinta kawai. Hajiya da su Zulaihat suka koma falo, itama tana kammala suyar ta haɗa chicken pepper dinta ta zuba yanda ya kamata, da taimakon Ladidi suka kwashi kayan zuwa saman tebur. Lemukan suka sanya a firij. Tana zama a falon ba jimawa, wani tunani ya faɗomata a rai, cikin sauri ta mike zuwa ɗaki. Wayarta dake hannun Ansar wanda ke kwance yana buga game ta karɓa haɗi da faɗin.

"Kaima Monday ta zo ba zama za ka yi ba sai ka je makaranta tunda ka warke."

Ya hau tura baki.

"Tashi ka je ga su Maman Twins da Anti Rafee.."

Ba ta kai aya ba, da murnarsa ya dira ƙasa ya fice. Murmushi ta yi kawai. Abinda ya shigo da ita ta tuna hakan yasa ta saurin kiran Hisham.

Bayan sun gaisa ya gama jan ta da tsokana yanda ya saba sannan ta samu damar magana.

"Idan ba damuwa don Allah ka shigo gidanmu kamar wuraren biyar haka."

"Toh Antinmu, ina fatan dai ba ƙarata Princess ta kawo ba? Dagaske sharri take min."

Murmushi Ramlat ta yi, Hisham ba ya rabo da zolaya.

"Ni ba haka nace ba, abu ne mai muhimmanci akan abokinka, sai dai duk abinda za ka gani kar ka yi magana. Please."

"Shikenan, kar ki damu, In sha Allah zan shigo."

Daga nan suka yi sallama ta faɗa wanka. Koda ta fito, ba kwalliya ta yi ba sai dai ta gyara fuskarta ta shafa hoda da man leɓe. Ko ba komai baƙinta ne. Ta shirya ta fito falon daidai sadda su Ummi suka dawo daga makaranta. Dakyar Ramlat ta korasu islamiyya har Ansar don a farko ganin iyayennasu sun so su ƙi zuwa.
Sai a sannan su Rafee'ah masu kwasar  garar abinci suka yi wa Ramlat kallon tsaf ganin yanda ta sh sutura mai kyau. Ramlat ta yamutse fuska kadan.

"Ku faɗa kawai, abinda ku ke nufi ba shi bane."

Dariya suka yi.

"Kin ji yarinya da tsarguwa."

Fadin Zulaihat tana duban Rafee'ah. Taɓe baki Rafee'ah ta yi, ita me za ta ce? Ta dai lura Ramlat ba ta kaunar maganar aure don haka a yanzu nata mujiya. Aka bar zancen aka faɗa labarin gidan Yaya Munir wanda a yanzu don kansa ya zo ya samu Hajiya ya rantse rabawa matansa gida zai yi. Wannan kalami ya sa su dariya musamman Zulaihat abokiyar takun saƙarsa.

"Maganinsa! Tun farko nan ba na nunamasa hakan zai fiyemishi ba amma ya nunan shi din gwani ne. Kuma adali."

"Toh dai yanzu ko mene ai shikenan tunda ya riga da ya faru." Faɗin Hajiya kenan.

Haka suka yi ta hira kafin a kira la'asar duk su mike don ɗauro alwala. Wurare karfe hudu da rabi sai ga wayar Alhassan, nan ta ƙara yi mishi kwatance, a ƙarshe ma ta fita don tarbarsu.

Har suka ƙaraso idanunta na wani gefen, ya fito daga motar sanye da dark blue din shaddarsa sai gilashin da ke ƙaramasa kyau. Ya karya hula kamar Bakano.

Yarinya karama ta fito ta sha ƙananun kitso shuku a kanta, an sanyamata ribbons masu kyau da ya ƙaramata kyau. Ganin har da dattijuwar da nan take jikinta ya bata cewar ita ce Dada, yasa ta ƙarasawa tana ƙara yi musu barka da zuwa. Kausar da Hafsat sosai Ramlat ta burgesu, ta jagorancesu har cikin falon Hajiya wanda aka ƙara kimtsawa, Alhassan ne dai ya toge a farfajiyar gidan ya ƙi shiga. Bayan sun zauna aka gaggaisa, can kuma ta shiga daki ta kira Hajiya. Su Zulaihat ma suka biyo bayanta.

Dada ba ta jin hausa sosai, a haka dai aka gaggaisa, wani abin Hafsat ce ke cin gyaranta.

"Kinga abin Allah mai haɗa zumunta."

Fadin Hajiya tana murmushi ganin yanda Fatima ta maƙalewa Ramlat kamar dama can sun taɓa haɗuwa.

"A bar ki a nan za ki zauna?" Fadin Hafsat tana duban Fatima wacce ke ƙara shigewa jikin Ramlat. Da sauri ta wangale baki gami da gyaɗa kai, duk sai ta sanyasu dariya.

Anan ne Ramlat ke ji dagasken dai su na da ƴan uwa a garin, kwatancen da ta yi yasa nan take suka gane gidan musamman Hajiya da Yakasai ya zama unguwar da ta ci ƙuruciyarta a ciki. Sai dai basu taɓa shiga gidan ba don ba wani fita suke yi ba sosai a unguwa, hakanan su ma mutan gidan ba kowa suke shiga sabgarsa ba sai wanda ya isa.

***
Hisham gwanin cika alƙawari sai gashinan ya zo tun ma biyar saura. Babban abinda ya ƙara kwadaita masa zuwan bai wuce na cewa da ta yi lamarin ya shafi Hussein ba. Ya faka motarsa a waje, Maigadi na shirin bude gate ya dakatar da shi gami da nuna yanzun shima zai fito. Bayan sun kammala gaisuwar ya ƙaraso ciki, ji ya yi kansa ya sara yayinda kirjinsa ya shiga dukan tara-tara. Ba don a yau ɗin ya ziyarci Hussein a ofishinsa ba, ya kuma san kalar kayan da ya sanya da ma kalolin motocin gidan Hussein din, zai iya rantsewa ya ƙara wannan na tsayen Hussein ne.

'Kenan Hussein ƴan biyu ne?' Ya jefawa kansa tambayar da nan take ta amsamishi da eh. Tambayoyi kala-kala ke ɗawainiya da shi. Ya ƙaraso ganin da ya yi Alhassan ya zubamasa idanu fuska a sake, wayar da yake dannawa ya mayar cikin aljihu gami da miƙamishi hannu. Musabaha suka yi, hatta da muryarsu sai ya ji tana mishi kamanceceniya. Ja ya yi ya tsaya cikin danne mamakinsa, damuwa sosai ya mamayeshi. Ya tuna gargadin Ramlat akan kar ya yi wata katoɓarar don haka ya daure yana jan Alhassan da hira da zolaya kamar ya sanshi. Anan ya kara tabbatarwa ba Hussein bane, wannan wani ne daga Adamawa kuma sunansa Alhassan. Yana so ya tambaya ko yana da wani dan uwan haihuwar amma ya danne.

Kafin dai Ramlat ta fito ta yiwa Alhassan iso don ya shiga gidan, Hisham da AlHassan hira suke yi sosai, ya fahimci kusan halayyarsu ta daya don har Alhassan ma ya fi Hussein sakin fuska.

Ramlat na ganinsu tare ta karasa, suka hada ido da Hisham wanda ke kallonta bakinsa cike da tarin tambayoyi, ta gaidashi. Ta yi musu jagora zuwa falon Hajiya.

Nan aka ƙara gaggaisawa sannan AlHassan suka koma sitting room. Abinci da komai ta kai musu. Bayan kammala ci, suka yi shirin tafiya.

Ya yi daidai da dawowar su Ummi daga makaranta.

"Yaranki ne?" Dada ta fadi tana kallon Fatima, murmushi ta yi kawai ta sunkuyar da kai.

"Ai Dada daga gani ma ba tambaya, wannan yarinyar tana kama da ita sosai." Kausar ta fadi tana mai jawo hannun Ummi da nutsuwarta ya burgeta.

"A'a, wallahi ta fi ta kyau."

Fadin Hafsat, tana nufin Ummi ta fi Ramlatun kyau.

Nan Kausar da Hafsat aka shiga musu, su Zulaihat me zasu yi ba dariya ba. A karshe suka yi musu sallama suka kama hanyar tafiya zuciyoyin kowannensu cike da farin ciki. Babu ma kamar Hafsat wacce kafin fitowarsu daga gidan Modibbo ranta ya ɓaci da yanda Modibbo ya amsa gaisuwarsu a wulaƙance. A hanya har rantsuwa ta dinga yi ba za ta ƙara zuwa wata sabgarsu ba. Ba wanda ya kulata don kowa ransa ba dadi.
A yanzun tana jin za ta iya zuwa ta yi fiye da sati ma a Kano saboda karamci irin na Ramlat da ƴan gidansu. Ko ba komai ta samu wasu ƴan uwa a garin.
A ɓangaren Dada ji take inama haka Modibbo da sauran ƴan uwanta ke sonsu, da ta tabbatar ba ta da sauran damuwa.

***
Bayan tafiyarsu Ramlat ta takowa Hisham har wurin motarsa. Cike da damuwa ta tari numfashinsa, kaf yanda ta haɗu da AlHassan ba ta ɓoyemishi ba. Ya jinjina kai ya ƙara sakin ajiyar zuciya karo na ba adadi.

"Wallahi kaina ya ƙulle Ramlat, wannan lamari da ban mamaki yake. Zargina ya tabbata na cewa Hussein rabashi aka yi da ƴan uwansa. Koda ba rabasun aka yi ba, toh lallai akwai wani laifi da aka aikata gareshi har ya yi sanadin da ya fidda kowa a babin rayuwarsa. Mutane masu mutunci da kamala, sun bani tausayi sosai na rashin sanin inda yake."

Ranta ya sosu, sosai ta ji tausayin Hussein ya ƙara mamayeta. Ta karyar da wuya.

"Bari kawai, ni kaina abin yana dauremin kai. Amma fa bana son sanar da su komai, ba kuma na son su haɗu da juna har sai mun gano bakin zaren."

Jinjina kai Hisham ya yi.

"Gaskiya ne Ramlat, don Allah ki dage, ki ƙara shawo kan Hussein yanda za ku shaƙu. Watakila ta hanyarki mu samu wani information din tunda na lura wallahi ya soma damuwa da ke."

Gabanta ya fadi. Ta dubi Hisham sosai.

"Bangane ba."

Murmushi ya yi don ba ya jin dariyar dalilin damuwa da tausayin abokinsa da ya mishi ƙatutu. Tayar da motarsa ya yi.

"Ke dai ki yi aikinki. In Sha Allah nasarar ma da kike tunani zamu samu fiye da ita."

Ta amsa da toh kawai ba tare da ta tanka ba, dakyar ta iya ba shi sallahun gaida A'isha. Har ya ja motar tana juya maganarsa ta ƙarshe, to wace irin damuwa da ita kuma? Ta kasa fassara wannan kalamin.



***
'Addu'a, shi ne abinda ban fiye maida hankali wurin yi ba."

Ya furta a fili cikin ba kansa amsa, shi kadai ne a mota yana ja bayan dakyar ya samu fitowa daga takunkumin Hajiya Zeenatu na yi mishi rakiya duk inda zai je.

Ya yi wannan maganar a sanadin wa'azin Mufti Menk da ya gama saurara a motar, malamin na tunadar da Bawa akan ya dinga zama yana yiwa kansa hisabi, mene ne abinda ya san yana aikatawa kafin lokaci ya ƙuremasa.

Damuwa da ƙunci suka cika zuciyarsa, ko sallah ya yi a gaggauce yake yinta, bai damu da zuwa Masallaci ba ya bi jam'i ko lokutan azumi balle kuma sallar Asuba wacce wani zubin sai rana ta fito take gabatar da ita. Idanunsa suka kaɗa, shakka babu shi laifukansa nada yawa a wurin Allah.

Ruwa ake yi tamkar da bakin kwarya bai fasa tuƙi ba sai dai yana tafiyar ne kamar wanda kwai ya fashewa a ciki. Wannan ma kadai ya isa ya jawowa bawa munanan abubuwa, yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login