Showing 198001 words to 201000 words out of 226732 words
makwafci kuma amini ga mahaifinku, kun daukeshi tamkar mahaifin. Kuna girmamashi sosai kamar yanda ya ke kula da ku. Sau ɗaya na taɓa yiwa Hisham rakiya gidansa, a wata ziyarar gaisuwar Juma'a da ya yi. Yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa nake ganin girman Hisham, mutum ne mai son sada zumunci musamman ranakun juma'a, wataran yakan ɗauke ni muje tare, wataran kuwa shi da matarsa suke zuwa. Wasu lokutan kuma uzuri kan hana ni zuwa. Ko Hisham bai san na je gidan Baba Dakta ba, ya sa aka kai ni falon saukar baƙi, daga bisani ya fito muka gaisa. Na yi mamaki sosai da ya shaida ni alhalin sau ɗaya muka ga juna. Bayan mun gaisa sai na rasa ta inda zan fara, karshe ya dube ni da kyau ya ce na saki jiki da shi, na daukeshi kamar Uba, kar nayi shakkar komai na fadamasa meke tafe da ni. Wannan yasa nan take na ji kaunar mutumin nan. Zuciyata ta samu nutsuwa na fayyacemasa cewa na zo neman iznin aurenki ne. Ya gama saurarona, a karshe har ya yimin tambayar ko dama muna soyayya da sauransu. Duka na ba shi labarin gaskiyar yanayin alaƙata da ke. A karshe ya yimin yar nasiha game da hakuri da kuma fawwalawa Ubangiji komai, ya sanarmin cewa an riga da an yi maki miji don magana yanzu ma ta je ga Kawunnanki kuma sun karɓi mijinnaki da hannu bibbiyu. Ya bani hakuri ya kuma ce na ci gaba da addu'a duk abinda Allah Ya yi na sa a raina shi ne mafi alheri. Ba haka na so ba, amma na ji sauƙi daga radadin da naji akan batun an miki miji da farko saboda Baba Dakta mutum ne wanda ya iya kalamai masu nutsar da zuciya da kwakwalwa. Anan ne na nemi alfarma a wajensa kan yanda muka yi maganar ya zama tsakanin ni da shi. Murmushi ya yi ya nunamin kar na sami damuwa."
Ramlat kallon Hussein kawai ta ke yi, so da kaunarsa na ƙara samun matsuguni a kwakwalwarta da ma dukkan wasu sassa na jikinta. Shima idanun ya ƙuramata na sakanni kafin a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ɗan murza hannunta ya ɗora.
"Ramlat, na ci wuya a ƴan tsakaninnan, daga lokacin da na gane ina matuƙar sonki har zuwa sadda ake rikice-rikicen aurenki da Chairman. Ban ƙara samun walwalwa ba. Komai kika ga ina yi maki wala da farin ciki ko akasinsa, kawai yi nake. Idan na yi tunanin zan rasa ki sai na ji hatta da ke din ma haushinki nake ji. Babban dalilin da ya hana na kasa faɗamaki a lokacin, ban gama haƙiƙancewa kina sona din ba ne ko kuwa kawai tausayina kike. Sannan ni mutum ne mai burin duk matar da nake so, na nunamata son a aikace. Ya fi armashi akan mu tsaya muna ta maida martanin kalamai ta waya da zahiri. Ke yanzu abin ma bai fi burgeki ba?"
Ta sunkuyar da kai tana murmushi. Ya ɗora zancen.
"Kinsan wani abu? Nayi mamaki iyaka da na ji labarin ke ce silar haɗuwata da ɗan uwana, mamaki bai ƙara kashe ni ba sai da na ji labarin a sanadiyyata aka harbe ki. Sosai abin fa ya taɓa ni ya dakarmin zuciya. Wannan ne yasa na ƙara ƙullatar Zeenat. A lokacin kuma na kara ji a jikina babu wani abu da zan iya sakamaki duk wata sadaukarwa da ki ka yi gareni face na maidaki karshen ikona kuma mallakina. A bakin Hisham na soma jin labarin duk wani faɗi tashi da ki ka yi kafin aurenki da Hilal, har ma bayan aurenki da Aliyu. Kinsan me? Sai na tsinci kaina da wani mugun farin ciki, tausayi da ma soyayyarki a zuciyata, amma ban nunawa Hisham ba asalima haushi na dinga ba shi har ya yi fushi ni kuwa na haye mota na wuce na yi maki siyayya na dawo. Bana duba Ramlat, amma a lokacin haka kawai na dinga ji a raina da yardar Allah za ki zama mallakina. Musamman da Hisham ya ba ni tabbacin ba kya son Chairman kuma su Hajiya ma ba sonsa su ke yi ba. Abin dai daga Kawunnanki ne. Wannan ne ya sanya ni cikin annashuwa. Kinga wancan aurennaki, ke ki ka yi kiɗa da rawarki, wannan karon kuwa tunda har yan uwanki ma ba sa ta Chairman, to fa abun zai zo da sauki. Na ci gaba da addu'a da miƙawa Ubangiji kukana har zuwa lokacin da na ji labarin fasa aurenki da Chairman. Sai kuma ga wanj Baban Hanif na neman yimin shigar sauri. Sai dai ban sha wahala da shi ba saboda takanas Baba Dakta ya neme ni ta waya lokacin muna Adamawa ya ce idan har dagaske nake to shi kam hankalinsa ya fi nutsuwa da ni, bai kuma tunkareni ba sai da ya ji ta bakin Hajiyarmu. Bai fadamin dalilin da yasa aka bar maganar Baban Hanif ba, ya dai bani damar na turo magabatana tunda har kin bar masa wuƙa da nama, to shi kuma ya zaɓamaki ni a matsayin mijin aure. Na ji dadin lamarin sosai. Anan ne muka yi shawara da iyayena, ba ɓata lokaci muka taho Kano tare da ɗan uwana da Kawu Adamu. Aka shige gaba aka yi duk abinda ya dace. Kin ji dukkan abinda ya faru."
Ta gyada kai tana murmushi, ya saki hannunta ya miƙe, kayan kallo ya shiga kashewa kafin ta ga ya soma rage fitilun falon bayan ya tabbatar kofar falon a rufe ta ke gam! Ganin haka sai ta mike ta tayashi da rufe kofar fita na kicin da kuma kashe fitilun da rufe kofar kicin din gaba ɗaya. Koda ta juyo sai suka ci karo, ya yi saurin riƙota. Goshinsu haɗe wuri guda kowannensu na maida numfashi, za ta zame ya yi saurin riƙeta da kyau. A hankali kuma ya ja baya.
"Ban gama ba ki labari ba, ki yi shirin kwanciya ki zo, ina jiranki."
Daga haka ya yi gaba tana kallo ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya shiga. Ta sauke ajiyar zuciya, ba ta daina murmushi ba kamar yanda ba ta gaji da jin wannan daddaɗan labarin da ya ke ba ta ba. Ta tuna Kawu Bello da ya ce dama Hussein din ya taɓa neman aurenta wurin Baba Dakta bai samu ba sai a wannan karon. Da wannan tunanin cike da wata iriyar kasala ta ƙarasa ɗakinta. Sai da ta ƙara wanka don ƙamshin da ta ji Hussein yana yi sai ta ke ji kamar ita banda wari ba abinda ke fita daga jikinta. Loko da saƙo duka sai da ta bi ta wanke kafin kuma ta fito ta goge jiki ta shiga mulka turaruka masu kamshi kala-kala. A ƙarshe ta fiddo wata doguwar riga mai hawa farare ƙal ta sanya, ta ɗora hula da ya rufemata gashinta. Duban kanta ta ke yi a madubi, rigar ta ciki da kaɗan ta wuce gwuiwarta sai top din da ta ketare zuwa ƙaurinta. Girgiza kai ta yi, a haka ma kwarjini Hussein ke mata ina ga kuma ta isa gabansa a haka? Da saurinta ta karasa wardrobe ta fiddo zani. Ido ta fiddo waje kirjinta ya harba jin hannuwansa zagaye a ƙugunta.
"Kin yi kyau, shi ne ki ke kokarin rufemin abinda Allah Ya halarta min gani?"
Ta lumshe idanu, kunya sosai ta ke ji, ta kasa kataɓus. Juyo da ita ya yi suka fuskanci juna. Har lokacin ta kasa buɗe idanun. Kallon fuskarta kawai ya ke yi yana jin sanyi a zuciyarsa. A ƙasan ransa banda hamdala babu abinda ya ke yiwa Ubangijinsa. Jin shirun ya yi yawa ne ta bude idanunta ta dubeshi. Ganin idanunsa har sannan a kanta suke sai ta yi azamar ja baya ta cire jikinta daga nashi.
"Ki yi alwala." Ya juya ya koma ɗakinsa, ta sauke ajiyar zuciya. Hussein zai kasheta da kala-kalan soyayyarsa. Jikinta ya yi sanyi da ta tuna ba ta da sallah, daga yanayin Hussein ba sauki. Sai kawai ta ji ya ba ta tausayi. Ta kashe fitilu ta rufe kofar, tana tafe tana tuna aurenta da Aliyu, ranar da aka kawota sam ba ta da walwala ko misƙala zarra, wannan karon kam Allah kadai Yasan yanda ta ke jin zuciyarta musamman idan ta tuna yan uwanta da ma abokan arziki duk suna son aurenta da Hussein. Wannan ma abin ta ƙara godewa Allah ne. Fatanta Allah Ya basu zaman lafiya da iyali nagari.
Yana saman darduma, ga dukkan alamu sallah ya idar, ba ta shiga dakin ba tun da aka kawo ta sai lokacin. Sosai ya burgeta. Dardumar da ta ga ya shimfida sai ma ya ba ta dariya ta danne. Ganin ta koma gefen gado ta zauna ya sanya bayan kammala addu'arsa ya dubeta.
"Sallah fa?"
Ta kalleshi ta sunkuyar da kai, daga yanayinta ya gane cewa ba maganarsa. Don haka ya mike kawai ya yi nafilarsa ya yi addua, tare suka shafa ya miƙe.
"Taho mu kwanta na ƙarasa ba ki labari."
Yana fadin hakan ne yana nufar makunnin fitilun dakin, kashesu ya yi gami da kai hannu ya kunna na gefen gadon. Hasken ba yawa, kwanciya ya wuce zai yi kai tsaye.
"Ɗan tsaya." Ta dakatar da shi, ya ja ya tsaya kawai yana kallonta. Abin rufar ta ja ta kakkaɓe gadon ta gyara zaman filon kafin ta dube shi da murmushi.
"Bismillah."
Ya kwanta itama ta kwanta, fitilar ya kashe. Ɗakin ya yi shiru na wani lokaci, numfashinsu na gauraya wuri guda kowanne na shaƙar daddaɗan ƙamshin jikin ɗan uwansa. Ya kai hannu ya zame hular kanta, yana shafa kitsonta, ta lumshe idanu. Ya soma magana.
"Heart, kin yi zaton ba sonki nake ba, kamar ma dai kawai zan aureki ne. Ba ki san cewa Hussein ya soma sonki tun kan ki soma sonsa ba."
Duk da cewa babu haske sai da ta zaro ido. Kunya ta sanya ta runtse idanunta. Dama ya san tana sonsa?
Shi kuwa jin ta yi shiru sai ya kai hannu saman fuskarta, murmushi ya yi mai sauti.
"Kar fa ki yi mamaki, na sani. Sai dai ba karamin nishaɗantuwa na dinga yi idan naga kin yi narai-narai kina son yin kuka duk a tunaninki na bana sonki. Sai Hisham wanda yake sanya ni nishaɗi idan ya sauya fuska yana tayaki yaƙi. Kuma yasan sarai ina sonki amma na nunamasa nifa a'a."
Hannunta ya kai saman kirjinsa. Ta nutsu tana jin yanda ya ke bugu da ƙarfi.
"Kamar yanda kike jin zuciyata na bugawa a kowane daƙiƙa, wallahi Ramlat haka nake jin sonki a kowane dakika. Kwakwalwata ba ta taɓa samun hutu daga tunaninki ba, kar ki ƙara ji a ranki cewa zaman doya da manja zamu yi. Kar ki ƙara sanya wa a ranki wannan bawan Allahn ba ya sonki. Kinji?"
"Uhm." Ta faɗi a hankali, hakan yasa shi janyota ba shiri ya shiga aikamata saƙonnin da suka birkita tunaninta har ta shagala itama wurin maida martani. Nan fa ta ruɗa Hussein, ita kuwa shawarwarin yayyunta da su Amrah ke yawo a kwakwalwarta.
_*"Kar ki wasa da kowacce dama, kar fa ki manta Hussein bai san soyayya ba sai a kanki. Don haka ki saki jikinki ki rike mijinki da hannu bibbiyu."*_
Ta tuno kalaman Maman Twins.
***
WASHEGARI....
Tana jin sadda ya maida kanta saman filo madadin a farko da yake a saman kirjinsa, ya gyaramata ya ƙara rufe ta da tattausan bargon sannan ya miƙe. Murmushi ta yi ta buɗe idanu, banɗaki ya buɗe ya shiga, nan ya fahimci Asuba ce. Ta kai hannu a hankali ta shafi makwancinsa, so da kaunarsa marar adadi na kara ninkuwa a zuciya da gangar jikinta. Idan ta tuna manyan kalamai da kuma yanayin ruɗewar da ya yi duk a kanta, Hussein kuka na hawaye ne kawai bai mata ba, ya yi wani furucin da dole ya ba ta tausayi a sannan wato inama a kanta ya soma aure. Jin motsin fitowarsa bai sa ta rufe idanunta ba saboda fitilun ɗakin a kashe suke. Ganin yana laluben makunni yasa ta saurin rufe idon. Kimtsawa ya yi ya fice masallaci a gaggauce don ya so ya makara.
Tana jin fitarsa ta kunne bedside lamp ta mike zaune rungume da bargo, murmushi take kamar wata sabuwar kamu, ta gaji da murmusawar ta koma ta kwanta bayan ta kashe fitilar. Har Hussein ya dawo ya hau gadon ya jawota jiki, idanunta ƙirr. A hankali kuma wani sabon daddaɗan bacci ya soma fisgarta.
Ita ta riga shi farkawa wuraren karfe bakwai da rabi na safe, miƙewa ta yi ta nufi dakinta. Kai tsaye brush ta soma sannan ta faɗa wanka tana ji kamar an mata albishir da gidan Aljanna. Ba ta da wani sauran buri mai yawa a yanzu face na ta kyautatawa mijinta hakanan da addu'ar Allah Ya rayamata yaranta, Ya ja kwanan Hajiyarta mai sonta.
Koda ta fito shiryawa ta yi cikin doguwar rigar atamfar da ta matse daga sama, ƙasan kuwa ya buɗe amma ba sosai ba. Ta yi kyau musamman ma kwalliyar da ta yiwa fuskarta. Sai da ta shafa turare a gaggauce kafin ta fito da zummar shiga kicin. Sai dai ƙarar wayarta ya katse hanzarinta, ganin sunan Hafsat ta ɗaga. Suka gaisa.
"Dama kira nayi na ji ko kun tashi. Ganinan zan kawomaku abin kari."
"Toh Hafsat, sai kin karaso."
Daga haka ta ajiye wayar, ba jimawa aka kwankwasa ƙofar. Buɗewa kawai ta yi don ta san Hafsat ce. Suka yiwa juna murmushi. Ta karaso ta ajiye kayan hannunta saman tebur. Duk yanda ta so akan ta tsaya su yi ƴar hira amma ina ta ƙi.
"Rufamin asiri Adda Amal, zan dawo anjima dai in sha Allahu. Ban shiryawa faɗan Hamma Hussein ba."
Dariya ma ta ba Ramlat, suka yi sallama ta tafi. Ciki ta koma don ta ga ko ya farka. Tsaye ta iske shi daga shi sai gajeran wando sai kuwa tawul yana faman goge sumar kansa. Sunkuyar da kai ta yi gami da kokarin fita. Caraf ya damƙo hannunta.
"Dodo na zama?"
Ta girgiza kai tana murmushi ba tare data juyo ba. Dawo da ita baya ya yi, ta kasa kallonsa. Karshe ta wayance da gaidashi. Maimakon ya amsa sai ya sumbaci kuncinta.
"Kin yi kyau sosai."
"Na gode." Ta furta a hankali.
"Tunda ba za'a taya ni ba, a zauna a jira na kammala."
Ba musu ta karasa gefen gadon ta zauna, ganin ya juyamata baya yana kallon madubi yasa ta ɗago kai tana ƙarewa mijinta kallo da irin baiwa da ni'imar da Allah Ya mishi na kyawun sura. A fakaice yana kallonta, dariya ma ta dinga ba shi, satar kallon na mene alhalin shi ɗin nata ne halak malak? Har ya kammala da gaban madubin ya juyo bai bar murmushi ba, ganin ya juyo kuwa ta yi saurin kauda kai. Ƙananun kaya ya fiddo ya sanya. Ya koma gaban madubin ya fesa turare, a ranta ayyanawa take son ƙamshi irin na Hussein ko mace sai haka.
Kafin ma ya tunkarota ta mike, suka dubi juna kowanne da abinda ya ke saƙawa a ransa. Ta sunkuyar da kai.
"Barka da Asuba, fatan ka tashi lafiya?"
Ya kama hannunta ya jawota ya sa a jikinsa sosai.
"Lafiya na tashi, ina fatan kema haka?"
Suka kwashi ƴan sakanni kafin ya hau yi mata raɗa a kunne, kunya ta sa ta tureshi tana murmushi.
"Mene hakan wai?" Ta faɗi kamar za ta yi kuka. Ya taɓe baki.
"Gulma ce bana so."
Hararar wasa ta mishi ta juya da sauri ya kuwa bi bayanta yana fadin.
"Ni kike wa wannan kallon?"
Ganin dai kokarin cafketa ya ke yasa ta juyo tana dariya.
"Don Allah ka yi hakuri, na tuba."
Ya shafi sumar kansa kawai ya yi gaba zuwa tsakiyar falon.
"Nan za ki kawomin mu ci, bana son can."
Ta amsa da toh kafin ta yi gaba yana binta da kallo kamar za ta gudu ta bar shi. Sai da suka kammala karyawa tsaf sannan ya bata umarnin saka mayafi su je gaida Dada. Ɗakinta ta koma, dama ba nisa mayafin ya yi ba, ta gyara zamansa sosai ta zura flatshoe. Koda suka kama hanya, hannunta ya lalubo ya kama ya murza har sai da ta lumshe ido ba ta yarda ta kalleshi ba. Ɗan matsowa ya yi har kafaɗunsu na gogan juna.
"Wai ni bakin tsiwar naki mutuwa ya yi? Ko na lalubo amsar a daren jiya?"
Ta tsaya cak ta shiga kokarin zame hannunta a nashi, ya kara damƙewa yana dariya.
"Wallahi sai na ɗaga ki cak mu shiga har wajen Dada. Kin san zan iya ko?"
Dole ta hakura ganin akwai ma'aikata a farfajiyar gidan ta kuma tsorata don ta san halinsa dagasken yake.
Dada ta yi farin ciki matuƙa da ganinsu, ita kuwa Ramlat wacce ta samu dakyar ya saki hannunta, kunya sosai ta ke ji don ma Allah Ya taimaka baƙi duk sun watse, wasu yau da Asuba suka wuce.
Anan wurin Dadar ya bar ta ya fice wurin AlHassan.
***
KANO...
*DA SAURAN RINA A KABA..!*
[3/17, 9:18 AM] +234 703 629 0938: I just published "BABI NA SITTIN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1021339453?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=4X2TU9EgqK9sZlhD1RiJLYSmRa3JHzKonALRYeMQgs42rcaB4hSZEFfZEuyDyjNLmgxQTxRGGIYovRiJIB7fWJjhHoMqPgV6u1FPxMnKYkUE%2FDXuKH3NHflk4iDkMg3R
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
60)
Caraf aka damƙe hannunta, ta dubeshi tsakar ido ya yi mata wani kallon banza, kallo na tsana da ya jima yana dannewa. Idanun Hajiya Zeenatu ya yi wani mugun kaɗawa. Ganin komai ta ke kamar a mafarki. Wani irin uban zufa ya haɗemata duk da iskar da fankokin ke bayarwa. Yarfar da hannunta ya yi. Bai kuma yi wata-wata ba ya dauketa da mari hagu da dama. Kallo daya idan ka yiwa fuskar Hussein za ka fahimci tsantsar ɓacin ransa. Abu ne da ya jima yana dannewa. Hannunsa har rawa yake sadda ya ke nunata da yatsa yana magana.
"Ko a mafarki! Kar ki ƙara tunanin cutar da matata!"
"Hussssseiin.." Ta furta da rawar murya ga hanjin cikinta da ta ke jin sun dunkule wuri guda. Idan ba ta yi ƙarya ba ma, ta ji fitar tagwayen tusa daga jikinta.
"Yes, Hussein ne. Wanda kika kashewa rayuwar shekaru biyar! Kika raba shi da asalinsa! Ki ka tauye kuruciyarsa don kafirin zuciya da zalunci irin naki! Idan ke mahaukaciya ce da ba ki gano kuskurenki ba, kika daukemu shashashai ki ka ci gaba da yin yanda ki ka so da tunanin kin ci galaba ko kuma tunanin ni