Showing 84001 words to 87000 words out of 226732 words

Chapter 29 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12460

gidan kenan bari na har abada. Tun tana ganinsu daidai har ta soma ganin bibbiyu kafin ta zube a wurin.
   Koda ta farka bayan an yayyafamata ruwa, sai ta farka da wani irin azababben naƙuda. Tuni aka rarumeta zuwa asibiti.

  A wannan yanayin Ramlatu ta haifi ɗanta namiji.

***
  Rashin Aliyu babban rashi ne da ba za ta taɓa mancewa ba. Ta yi rashin Abba, ta zo ta rasa Aliyunta. Mutane biyu mafi girma da daraja a gareta. Cikinsu ba wanda bai taka rawa a rayuwarta ba. Sai a sannan ta yi kuka iyakar yinta, ta rungume jaririnta a jiki tana jin kamar ta hadiyeshi don so da kauna. Kamanninsa da Aliyu kamar an tsaga kara an karya, hatta da hasken fatar Aliyu ba abinda ya bari. Hirarrakin da ya dinga yi mata a kwanakin ne ya shiga dawomata, ta kuma fahimci ba na komai bane face bankwana. Irin ba kwanan da idan an tafi ba za'a ƙara waiwaye ba. Ba za'a kara dawowa ba sai dai a je a tarar.

"Sunansa Affan."

Abinda ta ce kenan tana duban Umman Amrah. Umman ta yi mamaki don ta dauka sunan mahaifinsa zai ci, sai dai ta gyada kai ta karɓi yaron ta kaiwa Malam don ayi mishi huduba. Ita kuwa sunan da Aliyun ya zaɓarwa ɗan kenan tun kafin ya zo duniya, ba ta ga dalilin da zai sa ta sauya ba.

  Tun daga lokacin rayuwarta ta dawo sabuwa, tun daga nan komai ya sauya. Ta koma mai yawan daure fuska a maimakon sakinsa, ta zama wata shiru-shiru irin shirun da sai ta so take sakin jikinta ta yi magana da dariya. Har ta kammala takaba ta koma makaranta ba ta sauya zani ba. Hajiya ta rungumi jikokinta kamar ita ta haifesu, nasiha da ban baki shi ne abinda take yiwa Ramlat koyaushe.

Dakyar ta soma sakin jiki har ta kammala karatunta ta hadu takardunta, a sannan ne kuma aka yi bikin Amrah suka bar ƙasar da mijinta. Baba Dakta da kansa ya yi cuku-cuku ya samarmata aiki a ma'aikatar kula da haraji ta ƙasa na branch dinsu dake Kano. (KIRS)

  A duniyar Ramlat, babu aure, babu kula kowane namiji da sunan soyayya. Ta hakura da kowane jin dadin rayuwa, ta gwammace ta kula da yaranta har su girma su zama wani abu a rayuwa. Wannan tasa ba ta taɓa bada fuska ga kowane namiji ba. Ta kame kanta, ta kuma rike mutuncinta. Duk nacin mai naci sai dai ya hakura.

Haduwarsu ta farko da Hilal bayan shekarun da suka biyo baya, abinda ta soma roƙonsa shi ne gafara. Ta nemi gafararsa akan laifinta kafin ta nemawa mijinta gafararsa. Ranta ya yi haske ta kuma yi godiya da jin cewar ya yafe tuntuni. Daga lokacin ne kuma ya dawo da zumunci a tsakaninsu. Tun tana kaucewa tana dauke kai, har dai ta hakura ta ɗaukeshi matsayin Yaya Munir a wurinta kamar yanda ta ke yiwa Muhibbat kallon yar uwa kuma ƙawa a wajenta.

***
   CI GABAN LABARI....
  


 

 I just published "BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/z1qmOMpjFab



🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

28)

Ana saura kwanaki uku kacal bikin A'isha, Ramlat ta yi kitsonta yiri-yiri da ƙunshi. Da kanta ta ɗaurawa Ummi ƙunshi na gam bisa tilastawar Hajiya don ta rantse Ummi sai an mata ƙunshi.

"Kema dai Hajiya, wannan yarinyar za ki dinga biyewa. Ai gashinan ta ɓatan lokaci." Fadin Ramlat sadda ta ke goge ƙafar Ummi da ƙaramin tawul, lallen duk ya caɓa ya haura ba ta zauna ba.

"Ko ma mene dai ai ta yi din, ke wane irin caɓar da lalle ne ba ki yimin ba kina ƙarama?"

Dariya Ramlat ta yi ganin abin ya juyo kanta.

  Ana gobe za'a sanya A'isha a lalle suka shiga kasuwa tare da Rafee'ah, siyayya sosai suka yi na abinda ya rage na kayan daki, maimakon su yi gida, sai suka wuce kai tsaye gidan A'isha dake unguwar Badawa layout suka kai. Anan suka iske masu aikin wuta na ta fama. Sai da suka tabbatar komai sun saka yanda ya dace sannan suka baro gidan. A kan titin Rafee'ah ta saki baki ganin yanda Ramlat ke tuƙi kamar mace.

"Ke Ramlat, ki yi hankali da ni wallahi kar ki kashe Baban Daddy ni."

Dariya Ramlat ta yi sadda ta sha gaban wata Crv-Honda ta yi gaba.

"Kin cika tsoro wallahi, ina nake gudu?"

"Kinga ko? Kin gani ki daina wannan over-taking din, ki rufan asiri nidai. Shiyasa na tsani zama gaban mota ko a tafiya ne, haka kawai ki ƙashe ni lokacina bai yi ba."

Dariya sosai Ramlat ta yi daidai sadda mai Honda dinnan ya taho da mugun gudu ya sha gabansu.

"Wancan dai ya dauka tsere muke da alama, toh ba.."

Ai Rafee'ah ba ta iya ta ƙarasa ba ganin yanda itama Ramlat ta fisgi motarta ta kara shan gabansa tana mai duban motar ta gilashinta tana dariya. Ina wuta Rafee'ah ta jefata, nan ta shiga fada kamar ta ari baki. Wai tana mace tana wasa da rayuwarta.

"Shikenan naji na daina." Abinda ta ce kenan har sannan dariyar mugunta take. Junction din state road ne ya tsayar da su, anan ne suka tsaya dab da motar. Kamar ance su waiwaya, gaba daya suka dubeshi baki sake, an ci sa'a kuwa ya sauke gilashin.  Mamaki suke da murmushi gaba dayansu, shi kuwa dariya yake musu.

"Hilal?" Fadin Rafee'ah wanda ta fi kusa da inda yake. Suka yi dariya a tare. Ita kanta Ramlat ta sha mamakin ganin shi ne. Ba su san shi da wannan motar ba.

"Kai Maman Affan, wannan gudun naki gaskiya zai sa mu rabaki da motarnan." Ya fadi yana duban Ramlat bayan sun gaisa da Rafee'ah.

"Bar ta, ai ba ka ji yanda ƴan hanjina suka kaɗa ba wallahi. Sai da na gwammace bamu fita a motar ba, dama sai da ta ce mu hau ɗan sahu ni kuma na gwammace na zuba mai mu tafi a motarta."

Ita dai Ramlat kauda idanunta ta yi tana murmushi da kuma gujewa kallon da Hilal ke watsamata.

"Yanzu ina ku ka yi?"

Ya fadi sadda aka soma yi musu horn ta baya, shaidar an bada hannu. A gaggauce Rafee'ah ta ce.

"Gida muka nufa."

Kai kawai ya gyada ya fisgi motarsa, itama ganin haka ta ɗan bada wuta kadan.

"Allah Sarki, wannan bawan Allahn har yanzu fa sonki yake."

Ta yi kamar ba ta ji me Rafee'ah ke fadi ba, karshe ma ta ɓige da kunna muryar Umar M Shareef cikin waƙarsa na Zan rayu da ke.

Ji ta yi Rafee'ah ta kashe hakan yasa ta dubanta sannan ta kauda kai ta maida titi.

"Wato ba kya son maganar ko? Ke abu baya wucewa ne Ramlat? Idan shi ya manta abinda kika yi mishi ya dawo yana bibiyarki, ke kuma a wa da ba za ki mance Aliyu ba ki..."

"Don girman Allah mu bar maganar. Ina haɗaki da Allah ki yi shiru."

Ta yi ta roƙon Rafee'ah har abin ya dauremata kai, karshe Rafee'ah ta sauke ajiyar zuciya.

"Ai shikenan, rayuwarki ce."

Ba ta tanka ba illa dai har suka isa gidan ba wanda ya kara magana. Ta lura kowa ya tashi burinsa ta koma gidan Hilal alhalin ita tasan ba mai yiwuwa bane. Ba ma Hilal ba, auren gaba daya ta hakura da yinsa. Ai idan mace za ta iya rike kanta da mutuncinta shikenan. Wannan shi ne tunanin Ramlat.

***
Suna shiga kai tsaye wanka kawai ta yi ta sauya kaya sannan ta fita tsakar gidan inda mata ke aiki, wasu aikin sinasir wasu kuwa suna yayyanka albasa. Kowa dai da aikin da ya ke yi, ta wuce kai tsaye cikin sa'anninta su Naja'atu su Maryam. Ana yi ana hira da shewa. Wannan ya fi komai yi mata dadi, ta ji wata irin nutsuwa. Yaran duk suna falon Hajiya su na wasa. Hira suke na abinda ya danganci magungunan mata. Kowacce da kalar wanda take koɗawa a cewar ta ta ga aikinsa sosai.

"Ke Maryam, bari na fadamaki wani abu, wallahi kinji rantsuwa ta Allah, wanda na samu wajen Ƴar Maraɗi ba karuwai ba, daidai da masu kishiya, miji bai isa ya haɗa matsayinsu ba. Abin nufi komai naki zai zama daban, za ki bambanta da kowace mace a wurin miji."

"Kuma shiga hakki fa?"

Ramlat ta tsinci kanta da jefawa Sa'adah ƴar Daura wacce yanzun aure ya maido Kano, tambaya.

Sa'adah ta taɓe baki.

"Amma dai ai banda kishiya ko?"

"Ke Sa'adah, duk da haka fa ba daidai bane. Wasu magungunan ma duk haram ne amma mata son zuciya ya rufemana idanu."

Fadin Naja'atu kenan. Nan dai suka ci gaba da tattaunawa game da magungunan da mata ke amfani da shi duk don su samu gurbi a zuƙatan mazansu.

"Maman Affan, tun dazu wayarki ke ta ringing."

Ramlat dake hawaye saboda  albasan da ta ke yankawa, ta bude idanun dakyar tana kallon wata ƴar uwarsu Dije da ta damƙa amanar wayarta a hannunta. Karɓa ta yi tana sharce fuska gami da dubawa. Lambar baƙonta ne na Mall, ta yi mamakin dalilin kiran kuma a karo na biyu. Me kuma zai ce da ita? Take tambayar kanta, ta share kawai ta koma bakin aikinta, ba jimawa wayar ta ƙara daukar ƙara. Ganin shi ne dai yasa ta miƙewa ta bar wurin tana ji suna mata tsiyar wai ta gaji da nuƙu-nuƙun ta faɗa tarkon wani.

"Assalamu alaikum."

Shi ne abinda ta ce, maimakon ta ji muryarsa sai ta ji muryar yarinyar ya doki kunnuwanta.

"Waalaikumussalam wa rahmatullah wa barakatuhu. Mami."

Dan murmushi ta yi, madadin takaicin da ta ji a farko na shiga rayuwarta da mutumin zai soma, sai ta ji sanyi jin muryar yarinyar da ba ta wuce tsarar ɗanta ba.

  "Fatima, kina lafiya?"

"Lafiya kalau Mami. Ga Dada."

Kafin Ramlat ta ce wani abu, tuni ta damƙawa Dada wayar. Sai murya ta ji. A ladabce suka gaisa ta kara da fadin.

"Ki yi hakuri fa kin hadu da rigimar Fatima, tun dazu ta matsawa ubannata sai ya kiramata ke kun gaisa wai ita dai tana sonki wataran ya kaita ta ganki."

Dariya Ramlat ta yi.

"Ba komai Dada." Ta fadi kamar yanda ta ji suna kiranta. Suka ƙara gaisawa sannan suka yi sallama ta katse wayar.

Kallon screen din ta tsaya jiki a sanyaye. Tunaninta ya tafi ga mahaifin Fatima wanda kamanninsa tamkar an tsaga kara an karya da Mijin Hajiyar da suka zo ma'aikatarsu. Kodayake, ba nan ne haduwarsu ta farko ba sai dai ya tsayamata a rai. Tsayuwar da kawai so take ta san alaƙarsu da Baban Fatima. Ta kuma sani, ba ta da wani dalilin da za ta fake da shi ta yi tambayar. To wa ma za ta tunkara cikinsu.

Ajiyar zuciya ta saki ta koma cikin ƴan uwanta ba ta ko kula jan da suke yi mata ba. Murmushi kawai ta yi don tasan ba wannan ne a gabanta ba.

***
  Ranar juma'a aka sanya Amarya a lalle, sai da ta je wurin aiki ta dawo ta iske farfajiyar gidannasu da aka ƙawata da kayan kyale-kyale, ya yi kyau sosai. Babu batun anko, kowa kayansa ya sanya.

Ta hade abinta tsaf cikin atamfa Batik kalar orange mai surkin ja. Ba ta yi wani kwalliyar a zo a gani ba, yanda dinkin ya zauna ɗas a jikinta ba karamin kyau ta yi ba. Kai ba ka ce ta haifi yara uku ba.

Anyi lalle lafiya, an ci an sha. Amrah da Muhibbat sun zo dukkansu, anyi hira da dariya abinsu tsaf. Sai da Magriba ta doso kafin a soma tafiya yin Sallah, tuni Muhibbat ta wuce.  Ramlat kuwa kasancewar ba ta da Sallah yasa ta miƙewa ta zauna, dole ta tashi ba don ta so ba don Amrah ta rantse sai sun je ta taimaka mata da cirewa Zaituna famfas don tunda ta zo bikin, yarinyar sai ta ƙi zama wurin Ummanta, ta naniƙe mata.

"Kedai wallahi kin shiga uku da kwuiyar masifa, ace famfas dinma ba za ki iya fiddawa yarinya ba?"

"Naji ko me za ki ce, ki yi ta faɗa. Nidai ki cire din."

Fadin Amrah, murmushi kawai Ramlat din ta yi. Suna shiga dakin, ta ji kamar ta juya. Bilkisu ce zaune sai kanwarta Salma, sai wata budurwa da ba ta sani ba. Suna daga gefe zaune yayinda Zulaihat ke dakin tana sallah. Sanin da ta yi ta gaisheta ne yasa ta yi gaba zuwa banɗaki ta bar Amrah suna gaisawa.

Ta cirewa Zaituna famfas ta fito daidai sadda Bilkisu ke tambayar Amrah.

"Ni kuwa don Allah ba Muhibbat ce tsohuwar matar Aliyu na ganku tare ba?"

Amrah ta saci kallon Ramlat da ta dauke kai tana maidawa Zaituna wando kamar ba ta san me suke ba, ta kara duban Bilkisu da murmushin yaƙe.

"Eh ita ce."

Taɓe baki Bilkisu ta yi.

"Shi ne har da zuwa gayyar soɗi? Kai wasu ma akwai karfin hali, wato har gayyatar ta aka yi?"

"Gwara da kika gyara Anti, kin yi kiɗanki kuma kin yi rawarki. Ba gayyar soɗi ta zo ba, Ramlat da kanta ta kai mata katin gayyatar."

Amrah ke maganar tana murmushin tura haushi. Maimakon haka sai Bilkisu da Salma suka tuntsira dariya.

"Wai, Sis? Dan adam ma bai da kunya wallahi."
Salma ke fadi tana duban Bilkisu. Ramlat ta dubi Amrah.

"Malama kin fasa alwalar ne? Zan koma can kya iskeni."

Daga haka ta sa kai za ta fita, maganar Bilkisun ta dakatar da ita.

"Yanzu ke Ramlat tsabar rashin ta ido, matar da kika yiwa kwace ita ce yanzun kika dawo kina wani zumuncin neman suna da ita? Ta dai bi a hankali kar a maimaita ƴar gidan jiya."

Cak ta kasa koda motsi, juyowa ta yi ta dawo da baya. Ta san take-taken Bilkisun. Tun safe take jefa habaici, ta zagi dangin miji ta zagi kishiya, duk don Yaya Munir zai ƙara aure ne. Zuwanta gidan bikin kusan da biyu ta yi.

"Ramlat, fita daga dakin nan."

Ta dubi Zulaihat wacce idar da sallarta kenan, ta kara da roƙarta.

"Don sonki da Allah da ManzonSa s.a.w nace ki fita."

"Ki kyaleta mana, au karya aka fada? Da ta tsayamin kerere tana da bakin magana ne?"

Bilkisu ta fadi har tana fidda huci da girgiza ƙafa, dama kiris take jira ta yi musu tas don yanzun cikinsu ta tsani kowa, kallonsu kawai take yi. Mijinta zai ƙara aure tasan har da amincewarsu da na uwarsu.

Maimakon Ramlat ta yi magana sai ta  fasa gami da kara rike Zaituna a jikinta su bar dakin.

Koda ta koma farfajiyar gidan, kurawa ƴanmatan dake rawa kawai ta yi amma ta kasa cewa uffan. Tunani ta fada, ba Bilkisu ce farkon fadin hakan ba game da alaƙarta da Muhibbat, akwai sadda mahaifiyar Muhibbat din ta isketa a gidan ƴarta, tana jin sadda ta ke yiwa ƴar faɗa akan don me za ta dinga jawota gidanta. Wannan abu ya yi mata ciwo, yana daga dalilan da yasa ta janye jiki daga Muhibbat din, sai dai matar na mata kauna ta don Allah, wannan tasa ba ta rabo da taɓota ta whatsapp ko ta aikomata saƙon gaisuwar juma'a ta text. Dalilin kenan da yasa itama ke ganin kirkinta. Ji da ta yi an taɓa kafaɗarta ne yasa ta kallon mai shi, Amrah ce. Zama ta yi.

"Kar fa maganar waccan banzar ya dameki, ai bayan fitarki kamar su doki juna ita da Maman Twins. Wallahi tas ta yi mata har da cewa aure kamar Munir ya yi ya gama. Matarnan ta yi jijjiga da zuba ruwan bala'i, ke da tana da iskokai a ta tayar. Ashe itama Maman Twins ciki take da ita, da safe wai ta mata magana ta dauke kai kamar ba ta ji ba. Sau kusan uku suna hakan, kuma ta ji ƙananun maganganun da take game da auren Yaya Munir tana zagin dangin miji."

Murmushi Ramlat ta yi.

"Ya ci ace na daina damuwa da lamarinta, na lura ba na ƙare bane."

"Atoh, ashe dai kin gane. Ya kamata ki yiwa kanki fada. Damuwa ba ta maganin komai."

Gyada kai kawai ta yi, zuwan su Naja'atu ne yasa su sakin zancen a ci gaba da raha.

***
  Washegari tun safe suka tashi aka shiga aikace-aikace, sauƙinta ɗaya, wasu ayyukan na abinci, Hajiya bayarwa ta yi order. Kamu da yini ne wanda za'a fita a yi a wani katafaren event centre na masu faɗa a ji. Ango da kansa ya kama wurin.

  Karfe uku aka sanya, sai dai halin mutanenmu, ba'a soma tafiya ba sai bayan la'asar.

Ƴan matan Amarya ankonsu daban, wata Atamfa ce kalar fari da blue. Fadin irin kyan da suka yi ma ɓata baki ne. Hakanan a ɓangaren ankon sisters, maimakon su uku, (Ramlat, Zulaihat da Rafee'ah), sai ya kasance su duka suka yi har su Naja'atu su Amrah da ma wasu cikin ƴan uwansu na cikin gari. Atamfa ce su ma blue zallah mai adon fari kaɗan kaɗan ba kamar na ƴanmatan ba. Wannan karon sosai Ramlat ta yi kwalliya domin mai kwalliyar aka dauko ta musamman har gida ta yiwa jama'a da dama. Amarya da ƙawayenta kuwa fita suka yi.

Wurin ya cika taf, Amarya da Angonta Hisham sun yi kyau har sun gaji. Maza da mata ne a wurin kowanne da nashi ɓangaren. Shiga take tana fita ita da Rafee'ah da su Naja. Amrah karamin cikinta mai ɗan karen laulayi yasa ta samun gefe ta yi zamanta tare da Affan da Zaituna ba tare da ta biyemusu ba. Takan kalli Ramlat akai-akai ta yi murmushi. Ita kanta aminiyarta ta yi mata kyau.
Ta jima rabon da ta ganta cikin walwala da farin ciki irin haka, sai ta dawomata Ramlat dinta sak da suna ƴanmata kafin komai ya sauya.

Ita kuwa Ramlat, waje ta nufa ta tarbo matan ofis dinsu da suka zo mata takanas bikin A'isha. Halima, Naja'atu Azare, Fa'iza da Zuhra.

Halima sai cin magani take don tun a motar Zuhra da ta nemi ayi gulmar Ramlat din, suka ƙi bada fuska ta cika ta yi fam. Yanzun kuwa ganin irin masu hannu da shuni da aka tara a wurin sai jikinta ya yi sanyi, ko ba komai wutsiya raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Ramlat suna da kudi daidai gwargwado, kamar yanda ta lura, dangin Angon su ma ba baya ba. Har suka karasa suka nemi wurin zama ba ta bar mamakin yanda wurin ya haɗu ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login