Showing 183001 words to 186000 words out of 226732 words
9:18 AM] +234 703 629 0938: I just published "BABI NA HAMSIN DA SHIDA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1017117739?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=NPwmUPq5q%2BNDXCvudnu9VtPx9xZ93DXS%2BXNO4Gp8IGMT8cs%2FH9GyIFlv%2Fhb%2BKgVVkXrnM1fZVi41cUdjwyw1cEK3IG5H1c7vZKRmCwE0POba10BIvSct65MXWSFYf6%2Fz
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
56)
'Me yake nufi da ni?' Ta jefawa zuciyarta tambayar da nan da nan ta samo amsar da ta ji wani mugun ɗacinsa. Hussein na nufin ra'ayinta ba komai ba ne, yana nufin koda ba ta sonsa ta rayu da shi. Ko kuma dai daga saƙon da ya turomata yana son ta fahimci ya gane tana sonsa amma ya dinga basarwa. Nan da nan ta ji wani haushinsa ya mamaye zuciyarta. Ta ci alwashin sai ta rama abinda ya aikata gareta, ba za ta taɓa yin musu a aurensa ba, amma ta rantse sai ya gane shayi ruwa ne.
"Allah Yasa hakan ya zamemin alheri." Ta ba Kawu amsa a hankali, gaba daya suka amsa da amin cike da jin dadi. Suka sanya mata albarka a karshe suka sallameta. Mikewa ta yi bayan ta share hawayen yanda ba za su gani ba, ba tare da ta ɗau kuɗin ba ta bar wajen. Kawu Sunusi zai magana Kawu Jamilu ya katseshi da zummar za su damƙawa Hajiya.
Ba ta wani jima cikin gidan ba ta yi musu sallama sai dai ba su fahimci komai ba don ta ɗan saki fuska kamar ba ita ba.
Koda ta koma gidan, ba abinda ta nunawa Hajiyarta. Wannan ya kwantar da hankalin Hajiyar don dama tun fitar Ramlatun ta ke cikin zullumin ta yanda za ta karɓi lamarin.
"Idan kin sauya kayan sai ki fito mu shiga kicin, na fadamaki yau Hassan zai shigo a gaisa."
Maganar Hajiya ta katse yunkurinta na shigewa ɗaki da ta yi niyya, ta juyo ta amsa da toh bayan ta haɗiyi miyau mai ɗaci.
***
Hajiya Zeenatu ta shigo falonta gaba daya jiki a sanyaye, likita ya duba ta amma ya ce bai gane komai ba, karshe aka haɗata da tests kala-kala akan ta yi ta kawo sakamako a gani. Ranta gaba daya a jagule ga wani jiri-jiri da ke ɗibanta. Turus ta yi ganin mutum zaune a falon. Ta daure ta shigo da fara'ar da bai kai zuci ba. Suka dubeta gami da amsa sallamarta.
Hussein ne fuskarsa cike da wani farin ciki sai AlHassan dake zaune yana amsa waya Madam dinsa Kausar, ganinta yasa shi yin sallama da ita.
"Ah, ɗan uwanmu zuwa babu sanarwa?"
Ya yi murmushi, sai yanzun dai ya zo gidan dan uwannasa don haka ba su hadu da Hajiya Zeenatun ba sai a yau, amma a Hotel ya sauka tare da Kawunsu Adamu wanda shi a yau da safe ya juya ya kama hanyar Adamawa.
"Hajjaju, Allah Ya huci zuciyarki. Nima zuwan ne ya tasomin babu shiri. Aiki na zo yi daga kamfaninmu na can. Ko shi Ogannaki haka ya gan ni babu zato ba tsammani."
Ta yi dariyar yaƙe gami da satar kallon Hussein da ya ɗora ƙafa ɗaya saman kujera hankalinsa ya koma kan waya yana zabga murmushi.
"Hakan ma ai daidai ne. Dama kuwa ina da saƙon da zan bayar a kaiwa Ɗiyata. Gwara da Allah Ya kawoka."
Ya yi dariya yana gyara zaman gilashinsa.
"Ba ki da matsala. Tana godiya."
Daga haka ta maida duba ga mijinta.
"Yallaɓai barka da hutawa."
Ta fadi da wani irin shagwaɓa wanda ya ba AlHassan dariya, sai dai ya haɗiye kawai ya miƙe.
"Bari na ɗan amsa waya." Yana kaiwa nan ya fice zuwa farfajiyar gidan, wannan ya ba Hajiya Zeenatu damar ƙarasowa ta zauna gefen Hussein. Ya ɗan dubeta da kulawa.
"Ya jikin naki?"
Cike da damuwa ta karya wuya.
"Likita ya duba ni, ya ce ba zai gane taƙamaiman matsalar ba sai an yimin gwaje-gwaje. Yanzu dai haka ya ban gwaji zuwa gobe zan koma mu gani. Amma na fi kaunar na hakura idan mun je London sai a yimin magani sosai."
Ya gyaɗa kai yana murmushin da ke ƙara tafiyar da imanin Hajiya Zeenatu a kansa.
"Saurin me ki ke? Ita lafiya ta fi komai ai. Ki kwantar da hankalinki. Tunda har kika ga na dakatar da aiki toh hakan na nufin na shirya koyaushe ne ma mu bar ƙasar. Abinda ya fi yanzu ki je goben ki yi gwaje-gwajen har a gano matsalar a shawo kanta. Gwara ki ɗan samu sauki sai mu wuce. Amma fa sai mun fara biyawa Adamawa kinga su Dada kun gaisa."
Ko ɗarr ba ta ji ba, a wautarta gani ta ke har a sannan babu wanda ya gane da hannunta a ɓatan Hussein.
"Yanda ka tsara hakan za'a yi Ranka ya daɗe."
Kauda kai kawai ya yi bai ce uffan ba, ta mike ta haye sama. Ya bi bayanta da kallo, sai kuma ya yi murmushin mugunta. Shi kadai ya san me ya bar wa zuciyarsa. Tabbas sai Hajiya Zeenatu ta kusa haukacewa idan ta gano taƙamaiman shirin da ya ke yi.
Wayarsa dake ringing ya duba. Hisham ne. Murmushi ya yi don ya san labari ya isa kunnensa.
"Kai dan iska ne fa! Wai me nake ji daga bakin My Princess? Dagaske kai ne ka kai kuɗin auren Ramlatu?"
Lumshe idanu ya yi, sunanta kaɗai idan ya ji sai tsigar jikinsa ya tashi. A hankali ya shafi sumar kansa.
"Mamaki ka ke yi? Ba haka ka ke so ba?"
Dariya Hisham ya yi.
"Haka nake so, sai dai ka rainamin hankali fa. Zan rama amma. Kar ka yi tunanin zan tayaka campaign."
Taɓe baki Hussein ya yi kamar yana kallonsa.
"Campaign after marriage? Ni zan yi abina dama."
Hisham ya ɗan dara don shi abin kam dadi ya yi mishi ba kadan ba. Addu'a ya yi da fatan alheri. Hussein ya amsa da amin kafin su yi sallama. Agogo ya kara dubawa, da sauran mintuna a kira sallar Magriba. Ya ƙagu ya ganshi a gidan su Ramlat. So ya ke ya sanyata a idanunsa. Bai zaci za ta ga saƙonsa ta shareshi ba, abin ya ba shi mamaki. Hakan yasa ya ke son zuwa ganinta da kansa.
***
Kawu Modibbo rai a ɓace ya ke amsa wayar ƙaninsa Adamu.
"Me ya kawoka Kano? Wato Adamu har wuyanka ya yi kaurin da za ka shigo inda nake ka kasa nemana? Idan kuma aka yi magana sai ka nuna ka fi uban kowa riƙon zumunci ko?"
Kawu Adamu da mamakin yanda Modibbo ya san da zuwansa garin Kano ya ba da amsa ta wayar.
"Wa ya fadamaka na je Kano?"
"Ɗanka Yahaya muka yi waya ya cemin ka shigo Kano tare da Hassan. Ko karya ya ke yi?"
Ganin yanaamsawa a zafafe ne yasa dole Kawu Adamu ya sauko ya shiga bada hakuri da fadin.
"Wani ɗan uzuri ne ya shigo da ni, kuma shigowar ta gaggawa ce shiyasa ban samu na karaso ba. Amma ayi hakuri don Allah."
Kawu Modibbo ya yi shiru, can kuma ya ce.
"Wane uzuri ne haka?"
Har Kawu Adamu zai ba shi bayani sai ya tuna roƙon alfarmar da Hussein ya yi mishi akan cewar ba ya son Kawun ya san da batun aurensa. Bai faɗamasa dalili ba ko ba komai dai ya sani Kawun bai kaunarsu, amma shi kuma ya ce ba komai zai mishi wannan alfarmar.
"Daurin auren wani ɗan abokina ne ya kawo ni."
Kawu Modibbo ya ji sai dai bai yarda ba, maimakon ma ya ci gaba da sauraronsa kawai sai ya yanke wayar. Shiru ya yi yana tunani, ɓacin ransa na ƙara ninkuwa. Yanzun ya lura yan uwansa da wadanda ma suka tsani Amina da Aminu a baya da kuma wadanda dama ke sonsu, duk sun hada kai, shi aka ware. Wani bakin ciki ya ji a ransa, karshen satinnan zai tattara ya je Adamawar tunda akwai bikin yar gidan ƴar uwarsu, Gwaggo Karime. Tunda gaba daya za'a hadu, zai kara zaman meeting da yan dakinsu ya ji dalilin wannan sabon sauyin.
***
Bakwai da mintuna, Ramlat ta hada lafiyayyen friedrice da gashin kifi wanda a gefensa ta soya dankali ta saka sai sauce. Ta yi zoɓon da ya ji kayan kamshi ta sanya a firij. Sosai ta saki jikinta musamman wayar da suka yi da Amrah ta kara ba ta shawarar yanda za ta tafiyar da Hussein har ya fahimci shayi ruwa ne.
"Sannunki, sai a je a kimtsa jiki. Allah Ya yi albarka."
Ta juya bayan ta dora komai saman tebur, ta dubi Hajiya da ke fitowa daga ɗaki. Murmushi ta yi kawai ta kauda kanta. Ita kadai ta san me ta ke kissimawa a zuciyarta. Kwafa ta yi don gani ta ke komai ma za ta iya kawai don Hussein ya fahimci ya ƙuntata mata.
Maimakon kimtsawar, sai ta zube saman gado, wayarta ta jawo. Missedcalls har uku duk daga Baban Hanif. Kafin ta gama shanye mamakinta sai wani kiran ya kara shigowa. Ta ɗaga da sallama, ya amsa.
"Allah Ya huci zuciyarki Maman Affan, ina ta kira an ƙi a saurare ni ballantana kuma a yimin uzuri."
Ta mike zaune.
"Ka yi hakuri, ba haka bane. Ba na kusa. Ina wuni ya gida?"
"Lafiya kalau. Babu damuwa, na yi."
Shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ɗora maganar.
"Na so maganar da zan maki ya kasance gani ga ki, amma ba na tunanin yanzu ina da wannan ikon na zuwa kofar gidanku. Da farko ina mai ba ki hakuri bisa dukkan wani abu da ya faru a dalilin aurenmu. Na yarda haka Ubangiji Ya tsaramana. A gaskiya Ramlatu, tun fara zancen aurena da ke, iyayena suka dakatar da ni bayan bincikensu yasa sun binciko tarihinki. Sun kuma gane cewar aurenki biyu ba kamar yanda ki ka fadamin cewa aure daya ki ka taɓa yi ba. Duk da labarin aurenki na farko da aka ban, hakan bai sa na gwuiwata ta sare ba. Na ci gaba da zuwa wurinki, idan ba ki manta ba, kin sha tambayata meke damuna, na ce maki ba komai. Wallahi wannan shi ne dalili."
Ya ɗan tsahirta, itama ba ta ce komai ba don dama ta san hakan kan iya faruwa, sai dai ba ta zaci za ta ji zafin abin har haka ba.
"Kina ji na?"
Ya tambaya, ta amsa da Uhm. Sannan ya ɗora.
"A takaice dai, wancan dalilin shi ne yasa iyayena suka ce sam ba da yawunsu ba muddin na aureki. Ina kokarin shawo kansu ne sai ga kira daga Kawunki (Baba Dakta), ya yimin maganar turo magabata, na ba shi bayanin halin da ake ciki. A karshe ya nuna ya kamata na hakura tunda har iyaye ba su so. Koda an yi ba dadinsa za'a ji ba. Amma wallahi Ramlat ina sonki. Ba yanda..."
"Karka damu, komai ai nufin Allah ne. Allah Bai kaddara zan zama iyalinka ba. Mu bar shi a haka. Allah Yasa ya zamemana alheri."
Ajiyar zuciya ya saki har tana jin hucinsa kafin ya amsa da amin. Daga nan suka yi sallama tare da yiwa juna fatan alheri.
Ta kurawa wayar idanu cike da tunani, kenan wai wannan abu da ta kusan aikatawa har ake fasa aurenta dominsa, da ace ta aikata yaya kenan? Nan da nan ta ji kwalla ta cicciko a idanunta. Da yanzun tana cikin yanayi irin wanda Halima ta tsinci kanta, da yanzu ita an ma kashe ta. Tausayin Hilal da ya fadomata a rai ta ji, rabonsa da Kano yanzun wata kusan biyu kenan. Tun sadda ya zo ya yi musu sallama akan ya samu sauyin wurin aiki zuwa Benue ba su ƙara jinsa ba sai jefi-jefi idan ya samu hawa online a whatsapp sukan gaisa.
"Uncle oyoyo!" Muryar Ansar da Affan ta ji daga falon, wannan ya nunamata cewa Hussein sun shigo din kenan. Ta mike ta shinshina jikinta, gaba daya kamshin girki ta ke yi, dolenta dama ta yi wankan ko ba don shi ba don haka sai ta rage kaya ta ja zanin wankanta ta fada bandakin.
Bayan ta fito ta shirya tsaf cikin doguwar rigarta na material, ba ta shafa komai a fuskarta ba, shimfida darduma ta yi ta zura hijabi ta hau sallar isha'i. Hajiya ta shigo har sau biyu tana magana. Na farko ta shigo tana wanka, na biyun kuwa yanzun tana sallah. Koda ta idar a gaggauce ta ninke dardumar ta fita. Ba ta son Hajiyar ta ƙara dawowa a karo na uku ta san rai ne zai ɓaci. Ba tare da ta cire hijabin ba ta fita.
Su biyu ne da shiga iri ɗaya, shadda ce ruwan blue, hatta da karamin aikin da aka yi musu iri guda ne. Hular kansu ma hakan ta ke, sun yi kyau har sun gaji. Su biyun ne kadai a falon, Hussein na zaune a ƙasa yayinda AlHassan ke saman kujera yana danna waya su Ummi zagaye da shi. Sallamarta ya sanya shi ɗago kai ya dubeta. Ta wani ɗaure fuska babu wani zumudi balle har ta kalleshi. Sai kawai shi din ya ci gaba da kallonta ƙasa-ƙasa yana kokari ya ga sun hada idanu. So ya ke ya karanci idanun ko zai gane manufar sauyawar fuskarta. Ta karaso gami da zama a hannun kujera ta gaishesu.
"Ranki ya dade Mrs Hussein, girman kujerarki ne ai. Idan laifi muka yi a yafemana, irin wannan shan ƙamshi, fitowar sai an ga dama?"
Kalaman AlHassan suka sa ta murmusawa, tana jin nauyinsa hakanan kawai.
"Ba haka bane, sallah na tsaya yi ne."
"To dafatan an samu a addu'a? Allah Ya amsa."
"Amin. Ina zuwa."
Daga haka ta mike ta nufi kicin, sarai ta na kallon Hussein ta gefen idanu, kallonta yake sosai, ta yi mamaki kwarai ganin ba ya daga cikin ɗabi'unsa.
Kayan abincin ta hada komai a tebur har ruwa da lemu ta ajiye kafin ta dawo falon ta yi musu iso zuwa saman teburin.
"Nikam da dai za ki sa a ƙasa ya fi min dadi. Kai fa?"
AlHassan ya fadi gami da duban Hussein. Ya gyada kai alamar hakan ma ya yi. Ta amsa da toh sannan ta koma kicin ta dauko katuwar ledar abinci wacce da wuya su yi amfani da ita idan ba azumi ne ya taho ba. Yanzun kam gashinan a kusa-kusa. Falon ta dawo ta matsar da centertable sannan ta shimfida. Bisa kuskure idanunta ya kai kansa, ta kauda kai lokaci guda tana kara hade fuska. Juyawa ta yi bayan ta ba Ummi umarnin bin bayanta. Marasa nauyin ta dinga ba ta ta kawo falon, ita kuma ta ji da masu nauyin. Komai ta jera, tuni AlHassan ya sauko, tana ji yana jan Hussein da hira amma yana amsawa tamkar ba ya so, a karshe sai shima ya kama girmansa ya watsar da shi ya maida hirar ga Ramlatu don tuni ta kora yaran ɗaki da kallo kawai. Sun san halinta, muddin aka yi baƙi zasu ci abinci to fa basu isa su zauna ba musamman ma tunda sun ci.
"Wai nikam Ramlat a ina kika koyi girki haka? Kamshin kadai ya mamaye hancina har yawuna ya tsinke tun kafin na kai baki."
Ba ta san sadda ta yi dariya har fararen haƙoranta na fitowa ba.
"Wurin Hajiyata mana. Amma dai ka bari ka ci kafin ka yanke hukunci."
Ta karashe gami da turamasa plate din da ta shaƙe da shinkafa ta kuma ɗoramasa kifin a gefe, ga zoɓo har turiri yake a kofi.
AlHassan ya jinjina.
"Gaskiya ne. Amma ko a ido ai an san mai dadi."
Ba ta ce komai ba banda murmushin, ta ja plate ta shiga zuba wa Gogannata wanda ya hau danna waya amma kacokan hankalin a kan hirarsu yake, shi kansa ƙamshin abincin dukan kofofin hancinsa yake yi, ya haɗiyi miyau ya fi a ƙirga. Ƙamshin zoɓon da ya ji citta da abarba da su flavour, yana kara kwaɗaitamasa son sha.
"Bismillah."
Ta fadi da wani salon kashe murya kamar ba ita ba. Ya ɗago kai ya dube ta. Hankalinta na ga zoɓon da take tsiyayawa a kofi ammafa kirjinta wani bugu yake don ta san idanunsa a kanta su ke kamar yanda jikinta ya ba ta.
"Na gode."
Ya fadi a ciki-ciki, ta ajiyemishi zoɓon, ta mike ta bar falon. Koda ta kai ƙofa, ta dan saci kallonsa, har sannan ita ya ke bi da ido duk kuwa da cewar ya kafa kofin zoɓon a baka. Mamaki ya sa ta saurin kauda ki ta shige daki.
Wani dadi ranta ya yi tana jin kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Wato dai haka Hussein ke ji idan ya na mata wannan shan ƙamshin. Ta yi dariya ita ɗaya a ɗaki kafin ta kife saman gadon cikin annashuwa. Sai da aka kwashe mintuna talatin sannan Ummi ta shigo kiranta. Ta maida hijabin ta fito, sun kammala har ma Hajiya ta fito, kayan kuwa ta tabbatar Ladidi ce ta kwashe tunda ba ta kai ga tafiya ba.
Hussein ya miƙe ya fita tare da Ansar, zuwa can sai ga Ansar din ya dawo.
"Mami, ki zo inji Uncle."
Ta dan saci kallon Hajiya da AlHassan, hira suke abinsu kamar uwa da ɗa, ganin ba su damu da kallonta ba yasa ta miƙewa ta shiga daki. Sai da ta ɓata mintuna fiye da biyar ba don kuma wani abun ta ke shafawa ko gyarawa ba, can kuma ta fito ta fice.
Yana tsaye a jikin motarsa ya harde kafafu hakanan hannunsa a harɗe a kirji. Tun tahowarta ya ke kallonta. So da kaunarta na ratsa dukkan wani ɓangare na zuciy da gangar jikinsa sai dai shafe mintocin da ta yi ba ta fito ba ya yi masifar sosa ransa. Don haka koda ta tsaya sai shima ya ja baki ya yi shiru. Ramlat ta soma gajiya da tsayuwar don haka ta dubeshi babu fara'ar a zo a gani.
"Shikenan ina iya tafiya?"
Kallon da ya watsamata yasa ta kallon gefe guda.
"Idan har ba ki daukeni a bakin komai ba, kina iya tafiyar."
Shiru ya biyo baya, jin ba ta ce komai ba sai ya sauke ajiyar zuciya.
"Akwai abinda na yi maki? Ko kuwa duk baƙin cikin na rabaki da masoyinki karo na biyu ne?"
"Komai nufin Allah ne. Haka ya tsaramin a rayuwa. Na kuma karɓa da hannu bibbiyu."
"Hakane, sai dai kina nufin ba da son ranki ba?"
Yanda ya yi maganar da wani irin sanyi, yasa ta yin murmushi kadan.
"Kamar yanda kaima ba da son ranka ba, haka nima yake a wurina. Ina ganin dai mun yi anko."
"Yaushe kika fara duba? Me kike nufi da mun yi anko?"
Daga muryarsa ta gane ɓacin ransa, ta kara gyara