Showing 207001 words to 210000 words out of 226732 words
ba ki san ki danne zuciyarki da abinda ke cikinta ba. Jefa iyaye cikin damuwa masifa ce a garemu. Kuma ina mai ba ki shawara ki dage da nemawa kanki zaɓin Allah, ki rabu da biyewa son zuciya wurin dagewa akan zaɓinki."
Hafsat wacce tuni ranta ya yi fari sumul ta gyada kai.
"In sha Allah Addata. Ina godiya sosai. Sai dai Adda ba ki ban labarin da ki ka ce."
Ramlat ta murmusa.
"Kar ki damu, ai ana tare."
"Da'iman kuwa da yardar Allah." Fadin Hafsat, suka dara kafin Ramlat ta fice ita kuwa bandaki ta shiga ta wanke fuskarta. Ramlat na sallama da Dada sai ga Hafsat din, sosai ta yi mamakin walwalarta, ta karasa ta fda jikin Dadar tana neman gafararta cike da shagwaɓa. Murmushi Dada kawai ta yi gami da jinjinawa Ramlatun. Ta tabbatar aikinta ne.
***
A ɓangarenta kuwa, ganin fitilu a kashe ya ba ta mamaki matuƙa, ita dai ta san ba ta kashe ba. Haka ta ci gaba da tafiya a hankali har ta kai ga makunnin, kafin ta kunna ya riga ta. Ta juyo ta dubeshi, kafin ta kai duba ga cikin falon. Baki da hanci kawai ta saki tana dubansa ta kuma maida duba ga abinda idanunta ke gani.
[3/17, 9:18 AM] +234 703 629 0938: I just published "BABI NA SITTIN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1024183736?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=kerlmbTD11RJIZ1OU3cjRAuaKiLriOJD0fY0ly4CVNRLiEciXy1qh%2BgcHslN3fAHkmM%2BuxbSZlMyLFyekdT2BAKcap35wfLbDInDLU%2Bf6jBwfeAcG9qlXUARTAIfqHS%2B
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
62)
*Assalamu alaikum masoya Karfen Kafa. Ina mai ba ku hakurin jinkirin da ake samu kafin posting. Ku yi hakuri pls. In sha Allah aski ya zo dab gaban goshi.* 🥰
Hajiya Batool ta zabga uban tagumi tana kallon Aminiyarta, ba ta san ta inda za ta fara magance mata matsalarta ba alhalin ita kanta yanzu cikinsa ta ke. Gaba daya ɗanta ya kwashi matarsa sun bar garin sun koma Abuja da zama. Waya ta kira sai ya ga dama yake ɗagawa balle a kai ga aike. Komai na rayuwa ya sauyamata, kasuwancin ya ja baya babu albarka ciki.
Hajiya Zeenatu wacce ta gama kai wa bango da shirun Batool, ta kundumar ashar da faɗin.
"Wannan wane irin wulakanci ne Batool, na kawomaki kukana ina neman mafita shi ne tsabar wulaƙanci ki ka shareni ki ka maida ni wata banza?! Hussein ne fa, kin fi kowa sanin yanda nake son Hussein amma har na gama ba ki labarin cin kashin da ya yimin gaban yan uwansa ki kasa jajantamin?!"
Tana maganar tana faɗa rai a ɓace. Hajiya Batool ta sauke ajiyar zuciya.
"Me zan maki? Wane irin nusarwa ce ban maki ba don Allah? Amma ke makahon son yaron nan ya sanya ba kya ji ba kya gani, ai gashinan ya nunamaki shi na zamani ne!"
Hajiya Zeenatu ta yi kwafa, ba abinda ya faɗomata a rai sai cin mutuncin da ya yi mata a farkon haɗuwarsu, da gaskiyar Batool da ta ce makahon so ya rufe idanunta. Ta sauke ajiyar zuciya.
"Naji, koma me ya faru, ina da hannu a ciki. Amma kuma kin san ba zan zauna haka ba ko? Kin san sai na rama? Ki tashi mu shirya mu leka wurin Gora. Mene a ciki? Zan durkusa na ba shi hakurin laifin da na yi mishi idan ya so ya samarmana mafita."
Hajiya Batool ta yi shiru, itama fa yanzun tana da bukatar hanyar da za ta bi a karkato da hankalin ɗanta gareta, ta kuma amince idan ya dawo ko wacece ya aura idan har hakan zai yiwa Fa'iza ciwo. Abinda ma ta lura da shi, itama kanta Fa'iza tama tsubbace-tsubbacenta shi ne dalilin da yasa ta fi karfinta. Sauke ajiyar zuciya ta yi, ta tuna kowacece Fa'iza, dama tun can ƴan gidansu ba wata cikakkiyar tarbiyya ce da su ba, ganin irin arzikin da ubanta ke da shi matsayinsa na tsohon minista ya sanya tun ɗanta bai wani ba soyayyar da Fa'izar ke mishi muhimmanci ba, har sai da ta yi yanda ta yi ta tursasashi. Yanzun gashinan tana girbar abinda ta shuka.
"Na yarda muje. Idan ma bai sauraremu ba, za yiwa Mariama waya mu wuce Nijar kawai. Na fi yarda da aikin buzayennan ma."
Da wannan suka shirya suka fice wurin Gora.
***
ADAMAWA..
Dada ta dubi Ramlat cikin nutsuwa ta ce.
"Kinga abin Allah ko? Ba ya kyale azzalumi, shiyasa duk abinda aka dage da kai kuka gareShi, watarana zai shuɗe ya zama tarihi. Ba wanda ya fi ban mamaki a lamarin sai ɗan uwana Modibbo, ban yi tsammanin ƙiyayyar ta kai har haka ba, amma ina nan inda nake, shiru ma magana ce. Allah ne zai maganinsa don nikam ban isa nayi ba. Ba na jin wannan karon zan iya yafemishi wannan zaluncin da ya yimin ni da yarana. Duk yanda zan so na ji alaƙarsa da matarnan, zan jira har zuwa lokacin da zai kawo kansa garemu."
Hafsat da ke zaune itama sai ta ji jikinta ya kara sanyi, wayarta ta kara kalla, wani saƙon ne na Taheer ya kara faɗowa, duka dai ban hakuri ne da nuni da yake mata cewar laifin wani ba ya shafar wani. Kalaman soyayya zafafa ya ke jifanta da su, ta yarda so ba karya ba ne, tana son Taheer sosai, duk da son ta ke mishi bai kai wanda shi ya ke mata ba, amma dole za ta sanyawa zuciyarta dangana. Ta san babu ta yanda aurensu zai yiwu. A hankali ta mike ta zame daga falon ta shige ɗaki, hawaye ne ya tahomata sai dai dole ta haɗiyeshi. A yanda ta ke da zafi, ba ta yi zaton soyayyar Taheer zai russunar da ita har haka ba har ma ta ji inama ɗan wani gidan ne daban ba gidan Kawun ba.
Ɓangaren Ramlat itama haka ta koma sashinta cike da tunane-tunane, ta kara ganin girma da ƙimar uwar mijinnata. Tabbas mahakurci mawadaci. Kai tsaye ta shiga gyaran duk inda bai ba ta ba, sai da ta tabbatar gidan ya kimtsu babu sauran dauɗa da kayan datti a kicin sannan ta kara gyara jikinta ta shirya cikin doguwar riga ƴar kanti milk mai adon duwatsu. Sam ba shi da nauyi. Ta feshe ko'ina na jikinta da turare. Saman doguwar kujera ta shimfide ta zurawa ƙaton enlargement na hoton mijinta idanu. Murmushi sosai ta shiga yi tana tuna kalamansa da ma saƙonni da dama waɗanda ya isarmata a daren jiya. A hankali ta lumshe idanunta wani farin ciki na mamayeta, wani lokacin ta kan ji kamar mafarki, wai yau ita ce a garin masoyinta kuma matsayin matarsa. Ta jima cikin tunani kafin wani bacci mai dadi ya kwasheta.
Ya jima da shigowa gidan, sai dai yana sashen Dada su na tattauna. Koda ya karaso gidan, ya isketa tana bacci murmushi kawai ya yi, ciki ya karasa ya rage suturar jikinsa ya ɗan watsa ruwa don ba laifi garin ana ɗan zafi. Gajeran wando three-quarter ya sanya da yar shirt marar hannu, gaba daya ƙirarsa ta bayyana muraran. Koda ya fito ya ci karo da Hafsat da ke faman sallama amma gwanartasa ba ta ji ba. Kofar ya bude ya sanya yatsa a bakinsa yana mata alamar ta yi shiru, murmushi kawai Hafsat ta yi hango dalilin, Adda Amal ke bacci. Hanya ya ba ta ta karasa kan tebur ta ajiye kwandon abincin ta juya ta fice ya rufe ƙofar a hankali. Cikin falon ya dawo ya zauna saman kujerar da ke fuskantarta, waya ya ke amsawa da Hisham sai dai rabin hankalinnasa yana ga Ramlatun yayinda ya ke kallon sauka da hawan numfashinta. Harma da yanda rigar ta fiddo surarta fa yi mata kyau. Wani lokacin kuma ya maida kai ga ƙawatacciyar fuskarta da kallon ke sanya shi nishaɗi.
A jikinta ta ji ana kallonta, a hankali ta soma kikkifta idanu kafin ta budesu kaɗan, ganinsa zaune yana kallonta ya sa ta ware duka dara-daran idanun kafin ta mike zaune ba shiri. Kunya ta sa ta mikewa sum-sum don ta shiga ɗaki ta ƙara wanko bakinta, sai dai tana zuwa gefensa ya yi azamar riƙota ta faɗo cinyarsa ta zaune ɗabas. Ta sunkuyar da kai yayinda shi kuwa wayar yake amsawa amma hannunsa guda ya kasa tsayuwa wuri guda, karshe ma zancen kasa fita ya yi yanda ya dace sakamakon fuskarsa da ya tura a ƙasan wuyanta yana shaƙar ƙamshin jikinta. Hisham ko fahimta ya yi ko mene? Kawai sai ji ya yi wayar ta ɗauke don haka ya kalli wayar sai kuma ya ajiye a gefe yana murmushi, ita kuwa Ramlat da gaba ɗaya ta rufe idanunta numfashinta na hawa da sauka da sauri, ta kara yunkurin miƙewa. Ya riketa sosai.
"Wai ina za ki je? Ba ki yi missing ɗina ba."
Kai ta girgiza ta kasa magana. Ya bi bakin da kallo kafin ya dubi idanu da ta bude a yanzun.
"Kin daina magana ko me? Wani abu ki ke ci?"
Ya maida dubansa ga bakin da take ƙara damtsewa.
Girgiza kai ta yi alamar aa, tana kokarin tashi sai ya ƙara riketa ya yi murmushi.
"Oh na fahimta, wato daga bacci kika tashi ba kya son ki yi magana naji wari ko?"
Kunya da takaicinsa ta ji har ba ta san sadda ta watsamasa harara ba. Ya kara murmusawa.
"Na nawa kuma?"
Ta waro ido.
"Me kake nufi?"
Ba ta san sadda ta yi furucin ba sai kuma ta yi saurin rufe bakin ta mike a guje ta yi daki ta bar Hussein da yi mata dariya. Koda ta wanke baki da fuskar sai kunya ta hanata fitowa falon, ta samu gefen gado ta zauna ta na mai jin haushin kanta. Yanzu dariyar ma da ya yi watakila don ya shaƙi warin bakinta ne. Tana nan zaune ya shigo, fuska ta ɗan haɗe ita a dole kar ya yi mata dariya. Hannu ya miƙamata yana murmushi. Ta kasa miƙamasa nata, sai shi ne ya gaji ya ja kamo hannunta ya miƙar da ita ta faɗo jikinsa har tana take masa kafafu da lausassun tafukan kafafunta. Goshinsu haɗe wuri guda, ta kankame rigarsa don ji ta ke kamar za su zube.
"Ko ba ki wanke ba ni ban ji komai ba."
"Uhmm."Abinda ta ce kenan, amma ita dai ta san ko yaya mutum ya yi bacci to fa sai a hankali.
"Wai idan na riƙe ki me kike ji? Sai naga kina kanne idanu."
Wayyo kunya, ta buɗe idanun tarr ta dubeshi da harara, murmushi ya yi don dama kwayoyin idanun yake son gani.
"Kai ka ga haka."
Daga nan ta zame jikinta ta yi falon ya bi ta a baya. Haushin kanta ma ta ji.
Tana zama ya zauna a gefenta, ta matsa, ya matso. Ta dubeshi, ya sakarmata murmushi. Kafin ta yi yunkurin mikewa ya kamata sosai, ya shiga aikamata da sakonni daban-daban wanda dolenta ta russuna. Sai da ya gaji don kansa ya matseta a jikinsa yana maida numfashi. Lalubo kunnenta ya yi bayan ya zagayeshi da harshensa ya shiga yi mata magana a tausashe.
"Na fi ki mance kaina idan muna tare. Na fi ki rawar jiki da mazari. Kar ki damu da duk abinda Hussein ya fadi ko kuma zai fada, haka nake, ina son tsokana ko don na yi dariya. Ina sonki sosai, ina kaunarki."
Murmushi tayi kafin ta kara shigewa jikinsa, ya kuwa ba ta kyakkyawan mazauni. Sun ɗan jima a haka kafin su mike zaune.
"Yunwa fa nake ji." Ya fadi, ta mike, ita kanta yunwar ta ke ji don tuni abincin safe ya narke.
Sai da ta soma zuba mishi, tana kokarin zuba wani ya hanata.
"Ba fa na son muna raba plate. Ki fahimta please."
Ta gyada kai.
"Zan kiyaye."
Daga nan ta dauki cokali ta matsa suka soma ci. Bayan sun kammala ta tattare komai ta kai inda ya dace. Koda ta dawo shi tuni ya yi daki, alwalar sallar la'asar ya yi. Ya dube ta.
"Bari na wuce masallaci."
Ta amsa da toh da yi mishi kyakkyawan addu'a sannan ya fice ita kuma ta kara miƙe ƙafa don har sannan ba ta samu tsarki ba. Ta sani sai a gobe za ta samu don ita mutum ce mai ƙidaya kwanakin al'adarta. Hakan na taimakawa kwarai wajen sanin lokacin farawa da kammalawa na kowane wata. Wannan yasa a wayarta ta ke da App mai suna FLO, tana lissafe da kwanakin farawa da kammalawar period dinta.
Tana nan zaune ya shigo amma fuskarsa ba kamar yanda ya fita ba, gaba daya a ɗaure. Ya karaso ya zauna bai ko kalleta ba. Ta ji gabanta ya fadi.
"Sannu da dawowa."
Kai kawai ya gyadamata, hakan ya ba ta tabbacin ba lafiya ba. Shi kuwa a hanyar dawowarsa ce ya biya wurin Dada, Hafsat ya tarar kadai a falon tana amsa wayar Taheer har tana ba shi shawarar ya gwada zuwa neman aurenta hannun yayyunnata. Wannan ne ya fusatashi, ya kuma kirata da marar zuciya da ba ta tausayin Dadarsu. Ya kammala fatattakarta ya kwace wayar sannan ya shigo.
Ramlat gaba daya ta ji damuwa da sauyawarsa don haka ta yi shahadar miƙewa ta karasa kusa da shi ta zauna. Ta daure ta kamo hannunsa ba tare da ta yarda ta kalleshi ba ta ce.
"Ka yi hakuri, ko me aka yi maka, ka zama mai hakuri don Allah."
Shi kuwa kallonta ya ke kawai. A hankali yanayinsa ya soma sauyawa, ɓacin ransa ya ragu sosai, ba abinda ya ke ji sai matukar kaunar kasancewa da matarsa kuma halaliyarsa. Ita kuwa dagaske bacin ransa ne ya taɓa ta, ba ta kaunar ganinsa a yanayi irin hakan.
"Toh ya isa, ko su kike ki jefani yanayin da ba za ki iya magancemin ba?"
Sai ta ji gaba daya ya ba ta kunya, ta dan harareshi da wasa tana mai zame hannunta cikinnasa, ya yi murmushi ya zauna sosai yana fuskantarta.
"Yarinyar ce naga alamun ba ta ji, ta yi zurfi a soyayya da wancan yaron."
Ramlat duka ba ta fahimci me ya ke son cewa ba, ta tsuramasa idanu cike da neman ƙarin bayani.
"Hafsat."
Ya fadi kai tsaye, nan ta fahimci komai, ta san da soyayyar Taheer ɗan Modibbo da ita Hafsat din, tausayinsu ya kamata, ta tabbatar laifin Babansa ya shafi soyayyartasu.
"Ka yi hakuri."
Haka kawai ta iya cewa don ta tabbata idan ta fadi wata kalmar bayan hakan, zai iya hucewa a kanta.
Da wannan ta samu suka share zancen inda ya shiga yi mata bayanin ya soma neman aiki. Ta bishi da addua da fatan alheri.
***
KANO
Taheer a fusace ya shiga sashin Hajja Fatouma mahaifiyarsa. Tana kallon yanayin fuskarsa ta ji zuciyarta ta taɓu, tun sadda ta fahimci irin son da ya ke yiwa ɗiyar Dada ta san akwai matsala. Kaf cikin yaranta ta fi sonsa, ko don kasancewarsa namiji na farko a ɗakinta? Ba ta da masaniya, to haka ma daga bangaren Modibbo, duk wani tsaurinsa yakan sassauta akan lamarin Taheer. A yanzun da shi kansa Modibbo kunyar kansa da kansa ya ke ji, ya kuma kasa samun sukuni ko ƙanƙani game da lamuran su Hussein, ta tabbatar ba zai iya komai ba don su ba mahaukata ba me da za su ɗauki ƴarsu su ba Taheer duk da irin abinda ubansa ya shukamusu.
Maimakon Taheer ya zauna, sai ya durkusa ya kama ƙafarta, ga mamakinta hawaye ya ke.
"Hajjata zan iya mutuwa wallahi, kirjina zafi kawai ya ke yi. Ina son Hafsat, bana jin zan iya rayuwa idan babu ita. A yau Hamma Hussein ya kira wayata ya yimin gargadi kan na rabu da ita. Ba zan iya ba Hajjata, ba zan iya ba mutuwa zan yi. Na kasa sukuni tun da muka yi waya da shi, ji nake kamar na shirya gobe na wuce Adamawa."
Ta girgiza kai tana sharemasa hawaye da hannunta, ita kanta nata idanun ne suka cicciko da kwalla.
"Karatun naka fa wanda saura kiris ka kammala? Kar ka kara cewa za ka wuce Adamawa a yanayin nan a muke ciki, ba za su taɓa kallonka ba. Ba za ka yi wata ƙima ko daraja a wajensu ba saboda tun ran gini tun ran zane. Mahaifinka ne silar komai, a yanzun da girmanmu ya gama faɗuwa a gabansu gaba ɗaya, ba na jin ko karen gidansu zai ragamaka idan ku ka ci karo."
Ya numfasa yana jin ciwon gaskiyar da Hajjarsa ke fadi, don ɗacinsa har a maƙwagoro ya ke ji. Ya haɗiyi zazzafan miyau ya dubeta da jajayen idanunsa.
"Idan har dagaske Abban ya yi nadama, meyasa ba zai taka da kansa ya je ya samu Dada da su Hamma ya ba su hakuri ba? Idan mutuwa ta daukeshi a wannan yanayin fa? Shi ne silar lalacewar komai, don haka ya je ya gyara. Na fadamaku, idan na rasa Hafsat ba zan rayu ba. Ita ce numfashina."
Daga haka ya mike ya fice yana tangaɗi sakamakon jirin da ke kwasarsa, bai kai ga ficewa daga ɗakin ba ya zube warwas a bakin ƙofa. Wani ihu da salati Hajja Fatouma ta yi a lokaci guda wanda ya jawo hankalin mutan gidan har shi kansa Modibbo da ya samu zazzaɓi ya lafamasa ya ɗan fara gyangyadi. Ba karamin gigicewa ya yi da ganin shalelan nasa a yanayinnan ba, tuni ya nemi zazzabin ya rasa balle ciwon kai, nan da nan aka kwashi Taheer sai asibiti.
***
Tun zamansu a gabansa, ya haɗe fuska kamar bai taɓa dariya ba. Ba abinda ke mishi yawo a idanu sai irin cakumar da Hajiya Zeenatun ta yi mishi a haɗuwarsu ta ƙarshe kafin wannan. Yanzun tsabar makirci ita ce gabansa har tana kuka da neman gafararsa. Ya yi wani shu'umin murmushi mai nuni da cewa sai ya rama. Kwanaki can ya yi mata aikin da bai yi tsammanin za ta warke da wuri har haka ba, don haka zai mata wanda kaf dukiyar da ta ke taƙama da shi sai ya tarwatse.
"Shikenan, na ji ya wuce. Sai dai ina mai gargadinki akan kar ki kara yin gangancin da ki ka yi gareni a baya."
Hajiya Zeenatu ta kalli Hajiya Batool suka sauke ajiyar zuciya kusan a tare kafin su dubeshi da fara'a.
"Ranka ya dade Gora, ba zan kara ba ko giyar wake na sha saboda na ga abinda na gani bayan na kaurace maka."
'Kaɗan kika gani, yanzun za ki ga fiye da hakan. Gora ba ya yafiya, ba ya mance sharri.' Abinda ya fadi kenan a ƙasan ransa daga nan ya ɗan bubbuga ƙasa kamar gaske, can ya dago ya dubi yanda