Showing 48001 words to 51000 words out of 226732 words

Chapter 17 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12435

sadda ta ji ana ƙoƙarin bude ƙyauren gidan. Ta sa hannu ta share hawayenta gami da goge gumin da ya tsastsafo a goshinta. Maimakon ta ganshi da mashin, sai ta ganshi shi ɗaya, abinda ya daure mata kai bai tsaya rufe kofar ba ya soma kokarin nufo cikin gidan. Tabbas dai Aliyun ne kamar yanda farin wata ya haskamata fuskarsa da kuma t-shirt fa jeans din jikinsa.

A gaggauce ta koma daki ta sanya dogon hijabin sallarta kuma na zuwa makaranta har ƙasa ta fito rike da fitilar wayarta. A barandar kofar falon suka yi kiciɓus.

"Oops! Baby sorry. Ina mangareki ko?"

Ta hau murza idanunta, kirjinta ya shiga bugun tara-tara. Ga abu dai a gabanta amma ta kasa gaskatawa, hakan yasa hannu na rawa ta dago ta haske fuskarsa ido a waje.

"Aliyu?" Ta furta cikin tabbatarwa da kuma alamar tambaya lokaci guda, kafafunta ta ji sun hau wani irin mazari, kwakwalwarta ta kasa daukar abinda ta gani a fuska da yanayin gangar jikin Aliyun.

"Bani hanya Malama." Ya kara fadi cikin muryar ƴan maye. Ba ta da niyyar kaucewa ya kuwa bangajeta ta fadi ƙasa ya shige yana kundumar ashar. Ta kama leɓɓanta biyu da hannunta na hagu kamar mai karɓar punishment a makaranta, kukan take yi amma gani take kamar idan ta bude bakin ihu ne zai fito madadinsa. Tunawa da ta yi kofar gidan a bude yake ya sanya ta miƙewa ta je ta rufe. A hanzarce ta koma ciki, a falon ta sameshi ya zube anan kasan tiles yana maganganu barkatai marasa ma'ana da tsari.

"Aliyu? Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Aliyu me zan gani? Me..me...me?"

Ta kasa ƙarasawa tana sheshshekar kuka, ta zube a gabansa.

"Aliyu ka ce mafarki nake, don Allah ka daina yimin irin wannan wasan. Na yarda na sani taba kawai kake sha, ka bar yimin wasan maye, wallahi ba zan iya dauka ba. Na shiga uku ni Ramlat."

Ta ƙarashe tana mai riko hannunsa. Cikin wani irin dariya na shaƙiyanci ya kamo tufkar da ta yiwa gashinta da iyakar karfinsa har ta saki ƙarar azaba.

"Keee, au baby...don uwarki da kika aureni ba ki...san...ina..hawa...sama...ba? Baby...kin cinyemin kuɗina...na talauce...amma na tsira da hawa gajimare..."

Ta yi nasarar ƙwatar gashinta, da wani karfin zuciya don kuwa yanzun ba ta jin kowane karfi a jikinta ta mike za ta gudu daki, ba zato ta ji ya riƙe kafar sai ga ta yiff! Ta fadi saman tiles, baki da goshinta suka ƙumu a ƙasa. Kan ka ce me sun yi suntum! Kuka sosai ta soma.

"Ka kyaleni Aliyu! Don Allah ka rabu da ni karka kasheni!"

Ta firta jikinta na mugun rawa, za ta iya rantsewa ba ta taɓa yin ido hudu da mutum yana maye ba sai a ranar. Ta fi gani a akwatin talabijin.

Jikinta na rawa bai fasa rabata da hijabi ba kuma ya ketamata t-shirt din dake jikinnata ba, ya shiga sarrafata ya dora dukkan karfinsa a kanta. Fadi yake.

"Shege G-Baba...ya ce na yi son raina dake na huce....Baby farar ƙafa gareki...ubanki bai ban komai ba....Hahaha..uban Muhibbat har gida ya ba..."

Bai karasa ba sakamakon hankaɗashi da ta yi ya bugu jikin kujera, ta mike a guje ta shige ɗaki ta rufe da muƙulli. Anan cikin duhun ta zube ta shiga rera uban kuka, innalillahi wa inna ilaihir raajiun kuwa, ta ambata ya fi dubu. Aliyu mashayi?

Wani irin dunkulewa ta yi a wurin ta shiga risgar kuka. KEWA, yau kewar iyayenta da ƴan uwanta take ji. A yau ta yi dakacen biyewa zaɓin ranta. Tausayin kanta ne ya lulluɓeta. Ta yi kukan mai isarta, tana jin yanda yake surfamata ashariya ta uwa da uba mara kyawun sauraro, ya gaji da bugu ya kife anan, tana jin fita da saukar munsharinsa. Miƙewa ta yi kanta na wani irin bala'in sarawa ta zura doguwar riga, ta tattare takardun ta kwanta saman gado,yanda ta runtse idanu haka ta budesu. Baccin ya tafi, damuwa da bakin ciki sun tararmata sun tsaya a ƙahon zuciyarta. Nan da nan zazzaɓi ya sauka a jikinta, haka ta kwana tana rawar ɗari.

***
Sanyin asuba da kuma iskar dake kaɗawa ce, ta tasheshi daga baccin da ya shimfiɗe yana yi, ya bude ido gami da tallafe kansa da ya yi mishi wani gingirigim. A hankali hasken wayar Ramlat ta taimaka mishi wurin gane inda yake kwancen. Zumbur ya mike tsaye, komai ya dawo mishi tiryan-tiryan. Bai mance yanda ya sha magungunan mura na saka maye a tare da su Sa'ad ba a club. Ya je musu da ɓacin ran yanda a yanzun kasuwancinsa ya ja baya babu wani albarka, har ta kai ya rage facaka yanda ya dace, suka duramasa abin maye, ya yi ta sha babu kakkautawa duk domin ya ji sanyi. Bai kuma mance yanda suka kawoshi gidan ba, yana da tabbacin mashin dinsa ma can ya bari.

Wani wawan tsaki ya ja, ya gaji da wani ɓoye-ɓoyen banza. Shi da gidansa? Ai dole ma wataran ta san halinsa. Maimakon ya kwankwasamata, sai ya wuce dakinsa ya kara shimfidewa saman gado, babu tunanin tashi sallar Asuba.

A gefen Ramlat kuwa, dakyar ta iya lallaɓawa ta yi alwala ta yi sallah, jiri sosai ke kwasarta, ta mike ta koma saman gado, kwanciyarta ba jimawa ta ji amai na yunkurin tasomata. A guje ta faɗa banɗaki ta shiga yunkurin sai dai banda ruwa ba abinda ke fita. Ta gaji da yunkurawar ta wanke baki ta fito. Kifewa saman gadon ta yi ta shiga rera sabon kuka, tunaninta kawai mutuwa za ta yi. Babu wani mai sanyaya zuciyarta a yanzun, Aliyu tana fushi da shi, fushi mai tsanani. Gani take ta tsaneshi, ba kuma za ta iya ci gaba da zama da mutum mashayi ba.

***

Motsin bude ƙyauren gidan ne ya farkar da ita daga azababben baccin da ya kwasheta ba tare da ta shirya ba. Rana tarr a saman kanta, Allah Ya taimaketa ma babu makaranta, Asabar ce. Ba laifi jikin da sauki sai dai ciwon kan bai sauka ba, bakinta babu ɗanɗanon komai. Wanka ta faɗa. Doguwar riga jallabiya kawai ta zura ta daure kanta da ɗankwalinsa.

Cikin faduwar gaba ta bude kofar falon, don bata da tabbacin fita ya yi ko shigowa. Ganin ba kowa sai wayarta da kaya a yashe saman kujera ya bata tabbacin shi ne ya maido su wurin. A hankali ta taka ta dauka ta kai daki, gaban madubi ta kara tsayawa tana kallon yanda goshi da bakinta suka kumbura suntum. Hawaye ta shiga fitarwa, ba ta isa ta je wa Abbanta da wani zancen ba akan Aliyu. Sai dai kuma shi kadai ne ke sauraron ta, banda shi ko waya ta kira su Zulaihat sama-sama suke amsawa.

Kicin ta koma ta dafa ruwan shayi da kayan kamshi kamar yanda Hajiyarta ke yi, ta zauna tana sha. Ba ta jin cin komai don haka ko kulolin tuwon da ta yi ba ta kalla ba balle ta iya ɗumamawa.

Babu abinda ta iya gyarawa a gidan, nan falon ta naɗe tana rawar sanyi, ciwon kai ya fi na baya. Ruwan shayin da ta sha shima haka ta amayar da shi. Bacci wahalalle ya kara daukarta, ba ta ji ƙarar shigowar mashin dinsa ba, sai jin hannunsa ta yi saman goshinta. A firgice ta farka, ganinsa ya sanya ta zabura za ta ruga ɗaki. Ya riketa gam a jikinsa, kawai sai ta fashe da kuka jiki na rawa.

"Don Allah ka yi hakuri ka rabu da ni, na tsaneka Aliyu, meyasa ka ɓoyemin munanan halinka? Wallahi ba zan iya ci gaba da rayuwa da kai ba."

Ya ɗago fuskarta yana mai riko haɓar.

"Baby wannan shi ne so? Don kin ganni a halin da ƙaddara ta jefani shi ne za ki gujeni? Baby maimakon ki ji tausayina ki tayani addu'a? Meyasa kika zo kusa da ni? Kalli yanda na ji miki ciwo? Baby baki da lafiya, jikinki zafi, muje ki sanya hijabi na kaiki asibiti. Kinji?"

Cikin karfin hali ta fincike jikinta ta faɗa saman kujera tana sheshsheka.

"Kar ka kara kirana da Baby. Wannan kuma ba ƙaddara ba ce, son zuciyarka ne! Kana saɓawa Allah kana kiran hakan kuma da suna ƙaddara? Wallahi sam ban yarda ba!"

Kalamanta sun soma yi mishi zafi sai kuma ya danne, lallaɓata kawai yake don ba ta jin dadi, don kuma wani abu da ya ƙudurta a ransa game da itan. Wannan tasa ya gane faɗa da zafi ba nashi bane. Ɗakinta kawai ya shiga ya fito da dogon hijabi ya taho da wayarta.

"Haba, ashe wayarki ba chaji shiyasa na yi ta kira bana samunki. Muje idan mun fita na bada chaji. Ki tayani addu'a, akwai wani ciniki da zan yi yau, idan ya faɗa har kaza zan siyomana, na kunna mana inji. Rashin wutar ya isheni."

Maimakon ta ji sanyin kalamansa, sai ta kasa jin hakan. Asalima baƙaƙen maganganun da ya jefeta da su a daren jiya har da zagin iyayenta sun fi komai tsayuwa a ƙahon zuciyarta. Ta haɗiye komai ta danne, ita kanta yanzun tana bukatar a duba lafiyarta, tana jin jikinta kamar babu jini balle ruwa, kamar ma a yau ɗin za ta mutu.

***
"Congratulations, kina da ciki wata biyu."

Kalaman da ke fitowa daga bakin likitiyar suka sanyata jin hanjin cikinta kamar zasu tarwatse.

"Ciki kuma? Dama haka ake cikin?"

Abinda ta fadi ya sanya daga Aliyun har Likitar dubanta, shi Aliyu ko fuskarsa kadai ka kalla za ka san yana murna da hakan duk da cewa yana auna yanda nauyi zai ƙara hawa kansa.

"Yes ciki, haka report ya nuna. Yaushe rabon da ki ga al'adarki?"

Tsabar rudewa ma ta mance da wani batun al'ada, ita tun zuwanta gidan Aliyu ba ta taɓa ganin jini ba. Shima Aliyun sai a sannan ya ankara da hakan. Maimakon ta yi murna, maimakon a ga tana dariya sai ta rike cikin tana kuka kamar wacce aka fadawa ranar da za ta mutu.

"Bana so, wallahi bana so! Dr ki zubar da shi."

Wani wawan mari Aliyu ya dauketa da shi. Ta rike ƙuncin a zabure ta mike tana dubansa cike da dumbin mamaki.

"Haba Malam, matarka ta sunnah? Ita za ka mara? Wane rashin hankali kenan? Koda ta yi kuskure ba ka ganin yarinya ce, bai kyautu ka lallaɓata ba? A ina aka taɓa marin mace, matar ma ta sunnah?"

Bai ko kalli Likitar ba wacce haushi da takaicinsa ya kamata. Ta zagayo ta kama hannun Ramlat da gaba daya ta gigice kukan ma ya tsaya cak. Ashe dai akwai marin da ya fi karfin kuka.

"Please get out. Ka bamu wuri."

Yana huci ya yi kwafa gami da hadata ita da Ramlat din ya watsamusu wani banzan kallo, har ya kai ƙofar ya juyo ya hau magana.

"Kika kuskura kika yi gangancin zubarmata da ciki, daga ke har ita sai na yi shari'a da ku!" Daga haka ya fice gami da banko ƙofar da ƙarfi har iskar na bugunsu. Dr Sadiya ta zauna kujerar da Aliyu ya mike, sannan ta maida Ramlat din mazauninta suna fuskantar juna.

'Ga ta a haka yarinya mai hankali da nutsuwa, sai dai da alama ba ta yi dacen miji ba.' Cewar Dr Sadiya a ƙasan ranta. Tausayin Ramlat ya kamata,ta danne ta soma yi mata nasiha.

"Ramlat ke fa musulma ce, cikinki koda shege ne ya haramta ki zubar balle kuma cikin sunnah. Ba ki yi kama da mutuniyar banza ba, ba kuma ki yi kama da mata ballagazazzu ba wadanda basu je makaranta ba. Ko mene ya yi zafi a rayuwarki, ki dinga tunawa da Allah. Shi ne Mai yaye dukkan wani azaba. Ki kwantar da hankalinki, idan ma haihuwa kike tsoro ki miƙa lamuranki ga Ubangiji, In sha Allah sai kiga kin haihu lafiya. Mutum nawa ne za ki ga su na neman haihuwar ba su samu ba? Wata ma da kudi za ki ga ta zo nan tana neman maganin da za ta sha ta samu ciki. Wata kuwa har kuka take yi tana faɗin yanda miji da danginsa ke wulaƙanta ta duk akan ba ta haihu ba. Ke kuma da Allah Ya ba wa cikin ma na sunnah ki ce bakya so? Kenan kina nunawa Ubangiji ba ki yi murna da kyautarSa ba?"

Ta girgiza kai tana share hawayen da sai a sannan suka zubo, so ta ke ta ce ba haka bane, so ta ke ta ce yaron ko yarinyar da ke cikinta, ba ta so su dauki ɗabi'un mahaifinsu, sai dai kuma ba za ta iyaba. Ko ba komai wannan sirrinsu ne.

Dr Sadiya ga ci gaba da lallaɓata da ba ta shawarwari har sai da Aliyu ya gaji ya dawo ofishin.

"Wai me ake yi? Ni fa zan iya barinki ki kwana anan idan ba ku kammala ba."

Ya yi maganar a fusace, Ramlat ta mike ta yiwa Dr Sadiya godiya, ita kuwa ta miƙa wa Aliyu file din suka fita. Tun a asibitin tana jinsa yana jan tsaki har dai suka siya magani suka fito yana mitar kudinsa sun kare.

"Wallahi injin ma na fasa kunnawa, kudin sun ƙare. Zan dai siyamaki kazar tunda na sakamaki rai."

Gyada kai ta yi kamar kadangaruwa, fuskarta duk ta kumbura saboda kuka. Bini bini sai ta shafi cikinta. Iskar mashin na neman yi mata yawa don haka sai ta dukunkule ta kwantar da kai kadan a gadon bayansa. Hakan da ta yi dukkansu sai suka ji wani sanyi da kaunar junansu yana kara ɗarsuwa a zuƙatansu.

"Ina sonka Sweet Aliyu, ba zan iya rabuwa da kai ba."

Ta furta a hankali, kalaman sun ratsashi. Ya yi murmushi gami da ɗan rage gudu.

"Baby wa ya ce miki zan iya rabuwa da ke? Ai mai rabamu sai mutuwa Baby. Don ina shaye-shaye addu'a za ki yimin har na daina, kin ji?"

Ya ji sadda ta gyada kai a jikinsa, kusan a tare suka yi murmushi. Murmushin tana yi hawaye na zuba, zuciyarta ta kasa tsanar Aliyun. Soyayyarsa da na abinda ke cikinta suka haɗarmata. Ta kuma daura ɗamarar faɗa wa Allah matsalarta akan Ya shiryamata mijinta.

Sai gashinan Gen din da yake cewa ba zai tayar ba, sai da ya siya mai rabin galan ya kunna suka ga haske. Ranar tattalinta ya dinga yi gami da fadamata karya da gaskiya duk don ta ji tausayinsa ta kuma yarda ba'a son ransa ya soma shaye-shaye ba. Ya kuwa ci galabar hakan.

**


🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

15)

Kallo ɗaya za ka yi mishi ka hango farin ciki tsantsa da walwala marar misaltuwa a saman fuskarsa. Sigari ya sanya a bakinsa yana zuƙa lokaci daya yana fesarwa. Ihu da kurantawa shi kawai ke tashi daga bakin maza da matan wurin.

"Cau cau Aliyu Angon Ramlat!"

Fadin G Baba. Hakan sai ya kara tunzura Aliyu har sai da ya zuƙe kara biyu cikin ƙanƙanin lokaci kafin ya kwantar da kai yana kallonsu ƙasa-ƙasa yana doka murmushi. Ko ba komai yau burinsa ya cika. Ko ba komai ya mallaki abinda ya jima yana dakonsa. Ya na a jingine da kujera cikin club ɗin, yana kallon yanda ake rawa da rausaya mata da maza. Duk ana yi don tayashi farin cikin  samun cikar burinsa. Hannu ya zura a aljihu ya ciro bandir din dubu daya ya bude ya watsamusu. Aka hau kwasa ana ihu da kara korantashi. Abin na mishi dadi. Wayarsa dake saman tebur ya duba, kira ke shigowa ba kuma na kowa ba sai na Granny. Ya mike tsaye ya yi musu bankwana ya fice. Yau bai sha abin maye ba don ya fi son a yi komai cikin hayyacinsa ya gani.

Bai daga kiran ba har sai da ya bude sabuwar karamar motarsa Honda wanda Abulle ta sanya aka siyamishi ya shiga. Ya soma tuki a nutse kafin ya dauki waya ya kira Granny.

"Ina ka shiga wai? Ka zo mu tattauna game da lefen."

Ya yi murmushi gami da kara  lumshe lumsassun idanunsa.

"Ina hanya Kakus, gani nan tafe."

Ya kashe kiran bayan ta mishi addu'ar zuwa lafiya. Ya kai duba ga agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa. Karfe tara da mintoci na dare. Buga sitayari ya yi gami da sakin ƴar ƙara da furta.

"Yes!!" Cike da nishadi ya kara gudun motar gami da ware kiɗa. Har ya isa gidan bai kashe  kidan ba duk kuwa da hango iyayensa maza da ya yi zaune a saman tabarma ƙasan ƴar rumfa a farfajiyar gidan. Duk sadda irin hakan ta kasance, tattaunawa suke game da wani abun mai muhimmanci.

Kallonsa suke har ya kashe motar ya fito zai nufi cikin gida ba tare da tunanin gaishesu ba. Idan da sabo ya ci ma su saba.

Malam Abdussalam cike da takaicin halin ɗannasa ya sunkuyar da kai.

"Kai! Aliyu?!"

Fadin Kawu AbdulRashid wanda ke bi wa Malam Abdussalam a haihuwa. Aliyu ya maido akalar tafiyar garesu.

"Gani. Sannunku."

Yanda ya gaishesu kerere ya fi komai baƙanta ransu. Daƙuwa Justice ya wurga mishi.

"Ungo wannan! Yanzu kai tsabar iskanci da rashin kunya mu kake yiwa gaisuwa irin na ƴan iska?"

Nan ya gane kurensa, sai ya durkusa yana shafar suma. Dama ya riga yasan har gobe dattijon haushin sakin da ya yiwa ɗiyarsa yake. Yana cikin farin ciki yau, don haka bai shirya wani abun ya ɓata ransa ba.

"Ku yi hakuri." Ya ce kai tsaye cikin tausasa murya. Banda warin taba ba abinda ke tashi a jikinsa. Sun gaji da magana daya akansa.
"Allah Ya shiryeka Aliyu, Yasa wataran ka sauya." Cewar Kawu AbdulRashid ransa na zafi.

Nan Justice ya shiga magana.

"Yarinyar nan mun ji labarin abinda ta aikata, kuma ta yi a bakin duniya duk don ta aureka. Ta yi laifi, ta yi kuskure. Mahaifinta ya damƙa amanarta gareka, da kunnenka ka ji kalamansa."

Aliyu ya gyada kai cikin son tuna abinda Abban ya furta gareshi ranar da ya karbi sadakin Ramlat a hannun magabatansa.

*"Ramlatu amana ce Allah Ya ba ni, yanzu kuma amanar za ta koma kanka. Ban ce lallai sai ka kyautata mata ba, ban kuma ce lallai sai ka yi mata adalci a rayuwa ba, duk wannan hakki ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login