Showing 138001 words to 141000 words out of 226732 words
ba ta kaunar zama da su Rafee'ah, zancen dai daya ne, na Chairman. Ta fiddo miji ta gujewa aurensa.
Karshe ta watsar da duk wani tunani ta rage sutura ta shiga wanka. Bayan ta fito ta tarar su Nusaiba gaba daya na zaune ana kari da doya da kwai da shayi wanda ya ji citta da kanumfari.
"Ke kuwa Ramlatu yaushe za mu sha naki bikin?"
Ta yi kamar ba ta ji maganar Gwaggo Hansai ba, ta ci gaba da goge ruwan jikinta. Ba ta ce uffan ba. Duka Dije kanwar Gwaggo Hansai din ta kai mata bakinta cunkushe da burodi.
"Ja'ira, ai tana jinki. Ta fi kaunar muje ana daurin aure ta dawomana. Maimaita tarihi ko? Toh dagaske banni ƙara zuwa bikinta."
Aka yi dariya don an san zolaya ce ta Dije, ita dai Ramlat ta kara tamkewa ta mike ta kwashi kayanta, ta fasa shirin a falo, ta koma uwar ɗaka.
***
Kamar wanda aka daskarar da jinin jikinsa haka ya yi ɗif, a hankali ya sauke ƙarfen da ke hannunsa yana maida numfashi, gumi kam kamar ruwa haka yake ɗiga daga cikin gashinsa, saman fuska har zuwa jikinsa. Kallon Hisham ya ke yi da wani irin faɗuwar gaba. Hisham ya toshe kunnuwansa da earpiece yana gyada kai alamun waƙar da yake ji na tsumashi sai dai kacokam hankalin yana ga Hussein. Yana sane ya fesamasa batun auren Chairman da Ramlat duk kuwa da cewar yasan maganar rawa take yi ba ta tabbata ba. Amma ɗan hakin da ka raina ai shi ke tsonemaka ido. Gwara tun wuri ya yiwa abin tufka, ko ba komai zai ƙara karantar inda Amininnasa ya dosa.
Tasowar ta Hussein, da kuma fisge Earpiece din daga kunnensa duka-duka abin ya zamewa Hisham kamar kiftawar idanu. Ya haɗiye dariyarsa ya kara daure fuska.
"Lafiya Malam? Me ya yi zafi? Daga cewa Chairman Aliyu Dikko zai au.."
"Kar ka ƙarasa." Ya fadi a kausashe yana nunashi da yatsa idanun sun kaɗa cike da wani irin matsanancin kishin da bai san mafarinsa ba. Hisham ya cika da mamaki don bai zaci abin zai kai haka ba. A hankali Hussein ya zauna a gefensa ya yi shiru, can kuma ya dubeshi a sanyaye.
"Wasa ka ke yi, sai dai irin wannan ba maganar wasa ba ce. Please kar ka ƙara."
Hisham ya karkace yana dubansa.
"Don me? Toh kai mene naka ciki? Me zai dameka? Menene haɗin biri da gada?"
Ran Hussein ya yi tsananin ɓaci.
"Ni ka ke kira biri? Hisham har wuyanka ya kai tsaikon da za ka haɗani da biri?"
Dariyar Hisham ta kasa ɓoyuwa, lallai ya ƙara yarda Hussein bai iya Hausar ba. Dariyar ta kara fusata Hussein wanda dagaske ya ji zafin birin da Hisham ya ambata. Abin ya haɗemishi biyu don haka ya mike ya dauki jakarsa don suturta jiki. Hisham ya bishi da kallo yana mai ba shi tausayi. A yanzu ba shi da abar kauna sai Ramlat, sai dai ya rasa dalilin abokinnasa na ƙin ba wa zuciyarsa abincinta. Ko a ɗazun, kasancewar Hussein ya rigashi zuwa wurin motsa jikin, kama shi ya yi dumu-dumu da hoton Ramlat din yana kallo yana murmushi. Ganinsa ya wartsake ya sanya wa wayar muƙulli.
Yana nan zaune ya fito, madadin gajeran wando, ya sanya dogo mai santsi fari ƙal mai haɗe da riga. Ya sanya baƙin gilashi yanda idanun suka ɓuya.
"Sai Allah Ya kaimu."
Ya furta can ƙasan maƙogwaro yana duban Hisham din a fisge. Hisham ya rike hannunsa.
"Haba abokina, ka yi hakuri idan ɓacin ran da na jefaka ya kai girman haka. Karin magana na yi maka, haka Bahaushe ke karin maganarsa. Ba wai da gayya na haɗaka da dabba mafi muni ba."
Hussein ya sa hannu ya dan ja karan hancinsa kaɗan yana duban gefe.
"Wani abu na ƙara faɗi?"
Hisham ya dubeshi dakyau.
"Ba ka faɗa ba, amma ba haka muka saba sallama ba. Mafi yawan lokuta tare muke fita. Yau kuma ba alamar za ka jirani."
Guntun tsaki Hussein ya ja.
"Sauri nake."
Ya furta kai tsaye har da duban agogonsa kalar silver.
"Karin maganar ce ko damuwar Ramlatu ce?"
Ya ji tambayar Hisham kamar daga sama, shiru ma mintuna kafin ya dubi Hisham ta cikin gilashin.
"Abinda ka fadi gaskiya ne?"
Yanda ya yi maganar a sanyaye, sai hakan ya sanyaya jikin Hisham. Shirun da ya yi, Hussein ya samu amsarsa.
"Sai da safe."
Daga fadin haka ya yi gaba. Murmushi Hisham ya dan yi. Shakka babu da Ramlatu za ta samu Hussein ba karamin farin ciki zai mata ba. Yana matukar son ganinsu tare sai dai kuma sanin tarihin Ramlatun kan sanyaya masa jiki. Anya Hussein zai gan ta da gashi?
***
_*Nan kusa za'a yi bikin Ramlat da Chairman Aliyu Dikko don na ji labarin zai kai kuɗi.*_
Wannan kalaman ke yawo a kwanyarsa har ya hanashi maida hankali ga tuƙin da ya ke yi. Dole ya gangara gefen titi ya kashe wayar ya kwantar da kai bayan kujera. Runtse idanu ya yi na ƴan mintoci kafin daga bisani ya ƙara fiddo waya ya buɗe hotunan Ramlat yana ƙaremusu kallo. Saura ƙiris ta zama mallakin Chairman yana nufin abubuwa da dama. Shugabanta wurin aiki, wanda ya fi shi kudi da muƙami, wannan na nuna kwaɗayi ƙarara. Hira da ita da ma kallon hotunan har da ganinta a zahiri zai zama haram a gareshi, wannan ma wata damuwar ce mai zaman kanta.
Ransa idan ya yi dubu to ya ɓaci, kirjinsa zafi yake. Mafarkinsa na ƙara yawo a kwanyarsa, gaba daya ya hargitse lokaci guda. Ya tuna abu daya kwakkwara da ya danganci rayuwarsa ya kasa. Neman haske cikin duhu yake amma abin ya gagara. Koda ya tsananta tunani, kansa ya ci gaba da sarawa da ƙarfi, cikin dauriya ya kai hannu ya kunna CD na karatun Al-kur'ani da ke kan rediyon. A hankali ya soma samun nutsuwar zuci da na gangar jiki, ɗif, sai ya nemi yanayin ya rasa. Wannan kadai ya tabbatar da zargin da ya sha yiwa kansa a baya, wato ba shi da lafiya, kuma ya zamar mishi dole ya ga likita.
Ya kwashe mintuna biyar a wajen yana kallon motocin da ke safa da marwa kafin daga bisani ya ci gaba da tuƙinsa.
***
BAYAN KWANAKI UKU..
ADAMAWA
Tun fitowarta daga ɗakin ta ke ƙunƙuni tana zuba abincin zuciyarta na tuƙuƙi ga wani ƙololon abu dabya tokaremata ƙahon zuciya. Tahir kallonta yake kamar ya haɗiye, nan duniya ba ya jin akwai wacce zai so sama da Hafsat. Aure ne yana ji a jikinsa tamkar an yi an gama.
"Kin yi kyau."
Ya faɗi kamar mai raɗa bayan ya ƙaremata kallo cikin riga da siket din jikinta na Atamfa. Harara ta watsamasa, ba don ta so ba ta dawo gidan don a farko tattarawa ta yi ta koma gidam AlHassan da zama. Ya yi murmushi madadin hararar ta ƙona ransa, wannan ya ƙara ba Hafsat haushi, ta ja tsaki. Ita kuwa Dada ta ci gaba da hirarta da Tahir ranta na mata wani irin dadi. Kusan yanzun ta saba da shi sosai don kamar ba yaron da a baya ya ke wucesu kerere babu ko gaisuwa ba. Ta kuma ƙara fahimtar ɗabi'un yaron, jikinta na ba ta cewar duk wani mugayen halayensa akan waɗanda ba ya so ya ƙare. Kuma zuga ce kawai.
"Dada anya ba nan zan dawo da zama na dindindin ba?"
Ya fadi yana mai kallon Hafsat, ta dubeshi da sauri, ya kashemata ido ɗaya, ta mike sadda Dada ke ba shi goyon bayan maganarsa fuskarta a sake.
Ya yi daidai da sallamar AlHassan. Suka amsa, Tahir ya gaisheshi, ya amsa a ɗan sake don yaron ya soma ɗan sakin jiki da shi, ya fahimci koda yana da matsalar, a yanzun ta kau.
"Ke kuma zo dama ina nemanki."
Muryar AlHassan ya katse Hafsat daga tafiyar da ta soma. Ta ji kamar ta sa ihu, Tahir kam ransa ya ƙara fari ƙal sadda ya soma kai lomar abincin da ta girka da hannunta. Ta dawo ta zauna ta gaidashi kamar ta yi kuka. AlHassan ya murmusa don yasan kanun zancen.
"Jiya ina kika je? Na zo ance kin fita."
Ta ɗan tura baki.
"Gidan su Iklima na je."
Ya ɗan ɗaure fuska.
"Kuma ai na hanaki zumuncin da yarinyar ko kin manta?"
"Ka yi hakuri."
Ta faɗi a ƙagauce don Allah-Allah ta ke yi ta shiga ciki don tserewa kallon da Tahir ke mata.
"Shikenan, je ki."
Ya ba ta umarni lura da ya yi har sannan babu wata shaƙuwa tsakaninta da yaron. Shima ya fi kaunar hakan ko don gudun abinda zai je ya zo. Wayarsa ta yi ƙara, ya duba, Rasheed ne daga Saudia.
Ya ɗaga suka gaisa a mutunce.
"Ina ta so na kiraka sai dai Allah bai ban iko ba sai yanzu. Ya su Dada?"
Alhassan ya murmusa.
"Alhamdulillah, gamunan duka lafiya. Nima rashin lambarka ne ya sa na hakura. Fatan ka iske mutan gidan lafiya?"
"Duka kowa lafiya. Akan Hussein ne nayi kiranka. Na tuna wani abu."
Jin haka AlHassan ya miƙe da sauri har Dada da Tahir na binsa da kallo.
"Lafiya?" Dada ta tambaya. Ya ɗan dubesu.
"Babu komai Dada, bari na amsa waya ina zuwa."
Daga nan ya fita waje da sauri-saurinsa. Hannunsa har rawa ya ke yi.
"Ina jinka Rasheed, me ka tuna?"
Rasheed ya ba shi labarin kaf abinda ya faru a ranar da suka yi bikin kammala makarantarsu a DUBAI shi da Hussein. Bai ɓoyemishi wani labari da Hussein ya ba shi ba a ranar har suke dariya.
Safa da marwa AlHassan ya fara gami da dafe goshi.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!Meyasa ban tuna da hakan ba? Meyasa muka kasa tunawa da cewar itama za ta aikata?!"
Rasheed ya amsa.
"Nima ban tuna da lamarinta ba sai yanzun da Mamina ta ankarar da ni!"
Cikim gigicewa AlHassan ya ƙara jefamasa tambaya.
"Maminka? Ta santa?"
"Eh ta san ta, farin sani ma! Zan tambayi dukkan wani bayani game da ita zuwa safiyarku zan kiraka, ina ji a jikina ɓatan Hussein nada alaƙa da ita. Mu binciki inda take don mu tabbatar."
Gumi sosai AlHassan ke yi, kirjinsa na bugu da ƙarfi. Ya dafe goshi karo na biyu.
"Please kar ka ɓata lokaci Rasheed."
Ya fadi kamar zai yi kuka.
"Na damu da Hussein, na daukeshi dan uwa ba aboki ba. In sha Allahu komai zai zo karshe. "
Jinjina kai AlHassan ya yi cikin son gasƙata hakan. Daga bisani suka yi sallama.
"Meyasa ban tuna da ita ba?!" Ya fadi a fili zuciyarsa na wani zafi. Kamar faifan bidiyo haka komai ya shiga dawomasa filla-filla. Ya runtse idanu yana addu'ar neman dacewa.
***
DAURA..
Idan Ramlat ta ce bikin ya yi mata dadi toh fa ƙarya ce kawai saboda kusan faɗa iyayen aka yi game da aurenta da Chairman wanda ba su da labarin zuwansa har Daura gaida tsoffin sai a sannan. Hankalinta da na yayyun ya tashi.
"Wato dai Chairman makircinnasa ya kai inda ya kai!" Cewar Sauda bayan sun gama sauraron labarin Chairman daga bakin Ramlat.
"Mtsw, iyayenmu ne abin duniya yanzu sai ya rufemusu ido wallahi, daga ƙin gaskiya sai ɓata fa. Yanzu idan aka bari kika aureshi mene makomarki? Nikam gaskiya ke na fi jin haushi ma wallahi Ramlat, kiyi hakuri kinsan ban iya ɓoye abinda ke raina ba. Amma kefa bazawara ce, ta ya ya kuma ta ina za ki zauna a tauye hakkinki? Kamar ba ke ce kika jajirce a baya har kika auri wanda ranki ke so ba?"
Naja ta fadi ranta na ƙuna, Ramlat dai dubansu take kowa da irin kalar ƙorafinsa. Zagi kam Chairman ya sha. Tsam! Ta miƙe ta fita dama hijab ne a jikinta, tana ji suna kiranta da tambayar ko haushinsu ta ji amma ba ta ko iya waigowa ba. Kai tsaye ɗakin Malam Yahaya tsoho mai ran ƙarfe, cikin maza shi ɗaya tilo ya yi saura a ɓangare iyayen su Abba, wato Malam Abdullahi, Mu'azzam da ma sauransu. da suka rasu.
Yana zaune yana shan fura ga rediyonsa a kusa, sallamarta ya dauki hankalinsa, ya amsa ta karasa ta zauna.
"Wace ce ne? Ko Uwani ce?"
Ya tambaya yana kakkanne idanu don ba kasafai ya ke gane mutane ba. Bakin har rawa yake ta amsa
"Malam ni ce, Ramlatu."
Ya yi ƴar dariya.
"Ki ce Amaryar Dikko ce. Ince dai lafiya?"
Kiranta Amaryar Dikko ya ɓata ranta ainun, ta haɗiyi miyau mai ɗaci. Idanunta sula cicciko da kwalla.
"Malam don Allah ka taimakamin, kai kadai za ka yiwa su Kawu Bello magana su ji. Wallahi bana son Dikko, don Allah ku ban lokaci na muku alƙawarin kawomaku wanda zan aura nan kusa da yardar Allah."
"Wane magana kike yi haka Ramlatu? Abinda ki ka aikata a baya ne kike kokarin maimaita shi a yanzun? Ki fita idona wallahi! Ni ba ubanki ba ne da kika raina."
Zuciyarta ta yi wani irin nauyi, ta kasa daurewa sai da hawayen suka zubo. Wannan baƙin fentin da ta gogawa kanta ba ta san sadda zai gogu har yan uwa su yi mata kallon mutum mai ƙima ba. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta zayyanemishi duk wasu munanan ɗabi'un Chairman da ta sani. Ya yi shiru yana saurare har ta kai aya. Shiru ya biyo baya kafin ya jinjina kai.
"Shikenan, zan wakilta Iro (babban ɗansa) ya bincikamin a can Kanon. Idan har babu ɓurɓushin gaskiya game da abinda kika faɗa lallai ki sani, ni da kaina zan ɗaura aurenki da mutuminnan."
Ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin dama-dama. Kusan tun zuwanta banda Gwaggo Hansai da ta fahimceta da ɗaiɗaiku cikin gwaggonnin nata, sai yanzu ta samu nutsuwar da ba ta ji ba. Ga zafin Hussein ba ta ƙara magana da Hussein ba yau kwana huɗu kenan da zuwanta garin.
A sanyaye ta mike ta fita, kiciɓus suka yi da Harira ɗiyar Amaryar Kawu Bello ta biyu, dagaske laɓe ta yi a zauren. Sai dai ta wayance.
"Af, ke ce a ciki? Dama abincin Malam ne Gwaggo ta ce na miƙa."
Ta gyadamata kai kawai ta yi gaba. Ta rantse dai ba ta auren Chairman. Don haka za ta bi ta salama ta san yanda akai ta rabu da shi. A baya ta yi tunanin za ta iya hakurin zama da shi ko ba so, sai dai yanzun da so da kaunar Hussein ke ƙara ruruwa a zuciyarta, ba ta jin ko kusa za ta iya. Allah-Allah ta ke yi su koma Kano don tuni ta samu cikakken sunan Kawun su Hussein dake Kano a wurin Hafsat. Dabara ta yi mata da cewar ta shiga Yakasan ta ga wata mai kama da ita. A haka har ta gangaro inda Hafsat ta yi mata bayanin cikakken sunan Kawunnasu. Babban burinta ta koma Kano ta je ta sameshi. Ta fi kaunar bin komai daki-daki.
Maimakon ta koma ɗakin, sai ta wuce sashin surukar Malam, matar Iro, Hajara, anan ta yi zamanta tana danna waya. Muhibbat ta kira suka gaisa sannan ta haɗata da su Ansar da Ummi aka gaisa. Ba karamin kewar yarannata ta yi ba, ta yi musu albishir na dawowarsu a gobe.
Saƙo ta ga ya shigo, saƙon daga AlHassan, ta mike zaune da azama ta shiga whatsapp.
*"Ƙanwata, kinsan wata Hajiya Zeenatu Bashir a Kano? Ta taɓa zaman Saudiyya, kuma tana taɓa siyasa a baya. Yanzu dai ban da masaniyar komai a kanta."*
Dafe kirji ta yi. Shikenan duk yanda aka yi NESA CE TA MATSO KUSA!
[3/16, 1:55 PM] +234 703 629 0938: I just published "BABI NA ARBA'IN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/LUjPZHlQycb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
44)
_*"Eh na san ta."*_
Har ta rubuta hakan, sai ta goge da sauri. Toh idan ta ce ta san ta kai tsaye me ta yi kenan? Girgiza kai ta yi.
Shiru ta yi na ƴan sakanni ba zato wayarta ta shiga ringing. Ta duba, AlHassan ne. Ta danna gami da karawa a kunne. Dakyar ya samu nutsuwar amsa sallamarta.
"Kin buɗe saƙona ba ki ce komai ba. Kin san ta?"
Ramlat ta sauke numfashi.
"Ka yu hakuri sai dai magana ce mai tsawo da ba za ta yiwu ta waya ba, yaushe za ka samu shigowa Kano?"
"Ko gobe ne zan iya tahowa Ramlat. Ki amsamin da kin san ta ko aa."
Ganin irin ruɗanin da muryarsa ta nuna, yasa ta saurin amsa mishi.
"Na san ta. Har abinda ba ka zato duk na sani, idan da dama gobe.."
"Kar ki damu, gobe in sha Allah zan zo Kano."
Ya katse hanzarinta da gaggawa. Ta amsa da toh, godiya ya yi mata ya katse kiran.
Abu na farko da ya daurewa Ramlat kai, ta yaya Hussein ya gane zai iya samun wani bayani ta hanyarta? Sannan a ina ya san sunan Hajiya Zeenatu? Wannan tambayar babu mai amsamata sai shi da kansa don haka ya haɗiye abinta. Ta shiga zullumi ba kaɗan ba, ganin ta kasa danne abin, kawai sai ta kira Hisham.
"Ran Amarya ya daɗe."
Ta ja guntun tsaki, Hisham tun sadda ya ji labarin Chairman ya ke zolayarta.
"Ba wannan ba please, magana ce da ta shafi Hussein."
Jin haka sai ya maida hankali. Ta ba shi labarin yanda suka yi da AlHassan har da ƙudurinta na zuwa ganin Kawun Hussein dake zaune a Kano
"Da mamaki ace mutumin dake zaune cikin ƙwaryar Kano ya kasa sanin akwai wani jininsa a Kanon. Sai dai ban san irin raunin alaƙar dake tsakaninsu ba. Ina goyon bayan ki gwada zuwa ki sameshi. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ta ya ya Hussein zai soma fuskantar lamarin? Anya ba kuskure ba ne kai tsaye AlHassan ya tunkareshi ba?"
Ramlat ta jinjina kai.
"Shiyasa nake son zuwa na faɗawa Kawunnasu. Idan ma ya sani ka ga za mu sani, amma ba na jin zai sani. Haba, ɗan uwansu fa."
"Hum, shikenan Ramlat. Allah Ya maidoku lafiya. Ya ɗora mu a kansu."
Ta amsa da amin kafin ya ba Aisha wayar suka gaisa da taɓa hirar Daura daga bisani suka yi sallama.
***
WASHEGARI...
*LAMIƊO CRESCENT*
"Na yarda, wace ƙasar ki ka zaɓa mana?"
Mamakin amsar Hussein ya daskarar da Hajiya Zeenatu lokaci guda, ta ƙara matse layar hannunta domin ta yi imanin shi ne dalilin da yasa ya yi amanna da zancenta.
'Allah Ya yi maki albarka Hajiya Batool aminiyar kwarai.'
Ta fadi a ƙasan ranta bayan ta tuno shawararta ta bi ta je wurin Bokansu ta karɓo layar.
Farr ta yi da ido baki yaƙi rufuwa tana duban Hussein da rabin hankalinsa ke kan Laptop ɗinsa