Showing 27001 words to 30000 words out of 226732 words

Chapter 10 - KARFEN KAFA complete hausa novel

Unknown   

11 Oct 2024

12421

ba. To tunda ta faru ta ƙare kuma shikenan. A ranar aka sallameta bayan an tabbatar babu wata matsala, Mama ta tattara diyarta suka koma gida. Ita kanta ta ji dadi da ta ji Muhibbat na batun a raba aurensu da Aliyun. Ranar da take jira kenan.

***
   Da sallama ta shiga gidan, ta yiwa Hajiya sannu da zuwa, ko arzikin kallo ba ta samu ba. Cikin sauri ta fice dakinsu, sai dai tana shiga ta ji an rufe kofar, da hanzari ta waiga. Hajiya ce tsaye da wayarta a hannu, ta ƙaraso tana dubanta.

"Zauna magana zamu yi." Ba musu ta zauna a ƙasa ta sadda kai.

  "Banda Hilal, akwai wani da kike kulawa ne?"

Ta kalli uwar sai kuma ta sadda kai. Jin ba za ta yi magana ba yasa Hajiyar kara magana.

"Na tambayeki ba don ban riga da na sani ba, a'a, ina so ne da bakinki inji kin fada. Idan akwai ya sunansa? Kuma tun yaushe ku ke tare?"

Ta runtse ido tana mai jin ko'ina a jikinta na amsar kuwwar Aliyu, gwara kam a yi ta ta ƙare.

"Sunansa Aliyu."



🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

09)

    Tun shigarta ajin ta hango Amrah ta sauya wurin zama daga kujera mafi kusa da ita zuwa can ɓarin hagunta, ba ta yi mamaki ba don dama duk sadda saɓani ya haɗasu sai an gane a ajin ko don sauya wurin zama. Ba ta yi gigin zuwa inda take ba ganin malaminsu ya taho. Sai dai kusan rabin hankalinta yana gareta, a yanzun ta gane kurenta sosai, Amrah yar uwa kuma Aminiya tun suna yara bai kamata ace ta yi mata hakan ba. Yanzun ta fi koyaushe bukarta kasancewarta abokiyar shawarar da suke haƙowa su binne ba tare da kowa ya ji ba. Sai dai a ranta tana da yaƙinin muddin ba za ta bata goyon baya game da sheƙar da ta sauya ba, komai ma ya biyo baya ba matsalarata bace. At her age, Babu wani ko wata da za ta bari ya tauyemata ƴancinta.
Test har biyu suka yi, da na Economics da Commerce, bai bata wuya sosai ba, ko ba komai tana da basira daidai gwargwado sannan ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin karatu bisa shawara sanyin idaniyarta.

Ana tashi break ajin duk an fita sai ita sai kuma Amrah da ta maida hankali ga kwafar note. Wurinta ta nufa kai tsaye, ko ba ta ɗago ba ta san ita ce, takaici ya kamata. Nan da nan kalaman da ta jefata da su suka dawomata, wasu hawaye ta ji sun soma wanke mata fuska.

"Ko ba amintaka tsakaninmu Ramlat, zan ci darajar kaunar da nake miki kamar ƴar uwata ta ciki ɗaya. Akan namiji kika zageni kika wulakantani tamkar ba ki sanni ba. To ni kuwa me za ki cemin? Tsayuwarki ba ta da amfani don yanzun babu komai tsakanina da ke face gaisuwar musulunci, shima gaisuwar idan naga za ki wulakantani ba lallai ba tilas."

Tana maganar tana jijjiga biro tana fidda hawaye, itama kanta uwar gayyar hawayen take. Damuwa biyu suka tarar mata, ga na bakin cikin dawowar Hilal da kuma gaggawar bari a sanyamusu ranar aure da ta yi, ga kuma na zafin abinda ta aikata ga Aminiyarta wanda har sai da Aliyu ya ankarar da ita kuskurenta. Hannunta ta kama wanda dole Amrah ta tsayar da rubutun don dama tuni ta daina fahimtar abinda take kwafa sakamakon hawayen da ke maida idanunta gani dusu-dusu. Littafin kuwa duk ya soma jiƙewa.

"Ki yafemin don Allah don Manzon Allah s.a.w, nayi kuskure ba zan ƙara ba. Na fahimci laifina. Idan na kara ki dauki dukkan matakan da kika yi niyya."

Jin chanjawar muryarta da kuma kukan ya karya zuciyar Amrah, basu soma ƙawance don wani can ya rabasu ba. Sun saba su yi fadansu kuma su shirya ba tare da sun bari wani third party ya shigo tsakaninsu ba.

Dakyar ta yarda suka shirya karshe kuma suka hau hira har da dariya tamkar ba su ba.

"Waye Aliyu?"
Tambayar da Amrah ta jefomata kenan. Sai da gabanta ya fadi tsabar so da kaunar mai sunan. Ta lumshe idanu ta bude tana murmushi gami da duban agogon tsintsiyar hannunta.

"Saura 3mins a dawo class, ki bari idan an tashi i promise to tell you everything about him."

Murmushi ta yi.

"Shikenan."

Ana tashi kuwa suka ci sa'a ba'a zo ɗaukar kowannensu ba, don haka suka samu wuri can ƙasan bishiya saman kujera suka zauna. Babu abinda ta ɓoyemata dangane da Aliyu da karfin dangantakarsu a yanzu. Cikin hawaye ta kara da fadin.

"Wallahi wallahi kin ji rantsuwa ta ƴar musulmi, ban taɓa son wani yanda nake son Aliyu ba, ciki kuwa har Hilal! Ba zan iya auren Hilal ba, ba kuma zan yarda a auramin wanin Aliyu ba ko waye shi."

Baki sake Amrah ke dubanta. Ko a jiyan da suka yi wannan rikicin, ta san cewa ko wane Aliyu, Ramlat ta yi nisa a begensa.

'Ko asiri ya mata?'

Girgiza kai Ramlat ta yi gami da dariya mai ciwo.

"Kinsan Allah ba wani asiri, wannan son tsaftatacce ne."

Amsar yasa ta fahimtar zancen zucinta ne ya fito muraran.

"Wallahi gani nake kamar wata Ramlatun ce zaune anan ba Ramsy Ramlat da na sani ba. Kwanakin nan dama na lura da yanda walwalarki ta sauya, na lura sauyi a yawancin abubuwanki ta yanda hatta da wayarki kina kaffa-kaffa kar a taɓamaki. Ashe wata tsiyar kike shirin tafkawa!"

Nan da nan Ramlat ta ɗan sauya fuska.

"Ki bar kiran tsiya akan abinda bawa ba shi da iko a kansa, ko daga labarin da na ba ki na haɗuwarmu da Aliyu, ke kanki kin san haɗin Allah ne ba yin kanmu ba. Wallahi na guji Aliyu kamar gudun rai da ajali amma kuma ya zan yi tunda Allah Ya ƙaddara akwai ɓoyayyen lamari tsakaninmu?"

Miƙewa Amrah ta yi a fusace.

"Na gaji da jin wannan tatsuniyar! Na gaji da jin wanin Hilal a bakinki Ramsy! Me ya shiga kwakwalwarki wai? Ramsy Hilal fa? Mutumin da kika so a ganin farko, ban taɓa zaton irin wannan son mai shiga a yaɗuwar farko yana shafewa ba. Shawarar da zan ba ki shi ne ki nemi zaɓin Allah, kar ki biyewa zuciya ki yi saki na dafe, kar kuma ki biyewa sharrinta ki ƙare a zaɓen tumun dare! Ki sani babu hannun Amrah a cikin shafin Aliyu, har gobe ina sonki da Hilal kuma ina hango maki kyakkyawar rayuwa da mutum kamili irinsa da yardar Allah. Ban san Aliyu ba ban kuma taɓa ganinsa ba, sai dai ina miki rantsuwa bai kwantamin ba. Allah Ya ganar da ke Ramsy. Kin ban mamaki."

Daga haka ta juya tana shirin barin wurin ta ji amon muryar ƙawarta wanda ko cikin bacci ta tashi ba zai ɓacemata ba.

"Hilal dai! Ke ki aureshi mana muga ƙarshen so!"

Ta yi maganar cike da tsawa da nuna jin zafi ta ƙarara, anan Amrah ta gane irin nisan da Ramsy ta yi a lamarin Aliyu. Ta juyo a sanyaye, kuka ta yi zaman yi mai nuni da ranta na suya, tana tare da damuwa. Tausayi ta ba ta sai dai ba ta jin za ta taɓa ba ta goyon baya ta bar nagartaccen mutum mai alƙawari irin Hilal akan wani wanda ba su san halayyarsa ba. Ta koma ta zauna gefenta, sai da ta bari ta yi mai isarta sannan ta soma magana a tausashe.

"Kiyi hakuri Ramsy, ki yi hakuri da dukkan kalamaina."

"Me za ki cemin tunda kin kasa fahimtana, idan kika kasance ta farkon juyawa lamarina baya, ya kike son na yi?"

Ɗan murmushi Amrah ta yi, tausayin Ramlat da kuma Hilal na cin ranta. Shakka babu an mishi kwacenta lamarin zai ba da wuya.

"Kiyi hakuri, na yi kuskure. Shawara kika buƙata ko?"

Ta gyaɗa kai kamar wata ƴar goye.

"Addu'a, ki yi addu'a sosai na neman zaɓin Allah. Ki hakura ki tausasa zuciyarki kar ki biyewa son ranki. Ramlat ga duk namijin da zai kiraki a lokutan da yake tare da matarsa ta sunnah har a ranki ki ji maƙurar so yake maki ina tabbatar maki kin yi babban kuskure. Juma'ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganeta. Wannan cin fuska ne, ina roƙonki ki bar shiga hakkin wata saboda zai iya zuwa kanki ki ji haushi. Ba karfin sonki bane ya sanya, ki lura."

Ta ci gaba da ba ta shawarar mika lamura ga Allah da kuma ci gaba da ɓoye batun Aliyu a gida, Ramlat ta dauki shawararta tunda ko ba komai akwai sauran lokaci na kammala karatun da kuma auren. A ranta ta kudurta ganar da Hilal a sannu-sannu yanda zai fahimci ta sauya sheƙa ta kuma bar ra'ayin aurensa. Batun rabuwa da Aliyu bai taso ba!

"Amrah Abdullahi! Bala yana magana!'

Suka juya ga mai maganar, Zuhra Ishaq ce ƴar ajinsu wacce suka fi kira da Big Mama saboda ƙibarta, tun tana jin haushi har ya zamemata jiki. Tsaki Amrah ta ja tana mai miƙewa da daukar jaka lokaci guda tana aikamata daƙuwa jin ta raina direban gidansu wanda a haife ma zai haife su. Tare suka tako da Ramlat tana ƙara ba ta shawara.

"Nagode, zan yi aiki da shi. Ki tayani da addu'a dai." Murmushi Amrah ta yi ta bita da toh, sai dai kuma ta san kafiyar Ramlat, fatanta kar ta jawo abinda zai hargitsa lamura.

Tun da yammacin ranar da suka yi waya ya sanarmata zai shigo bayan Isha'i su gaisa take cika take batsewa, duk wanda ya kalleta ya san ba ta cikin walwala.

"Ke kuma meke damunki wai?"

Fadin Zulaihat da ta wuni a gidan.

"Bar ta Uwani, ta yi kuncin ta gama, yanda kika ganta tun sadda ta ji labarin dawowar yaronnan take cika da batsewa. Ban san kuma me hakan ke nufi ba. Ina fatan kar ta ba ku kunya."

Hajiya ke maganar ranta a ɓace don dama tun ɗazun ƙuncin da Ramlat ke yi da tsakin da take bugawa akai-akai ke cin ranta, magana ce kawai ba ta yi ba. Maganar Hajiyar yasa Zulaihat kallonta dakyau, ga mamaki ma hawaye ta shiga sharewa.

"Meke faruwa ne Ramlat? Kun yi faɗa ne?"

Ta girgiza kai, takaicinta yasa Hajiya sungumar Khalifa yaron Zulaihat na farko suka bar falon. Zulaihat ta dawo gefenta ta zauna.

"Fadamin damuwarki. Ko Hilal din ne ba ki yi murna da zuwansa ba?"

Duk kwarin gwuiwar da take tunanin tana da shi sai ta ji ta kasa kataɓus, ta kasa fadawa Zulaihat abinda ke ranta game da Hilal.

"Ko kin daina sonsa?"

Ta dubeta da sauri ganin ta harbo jirginta. Girgiza kai Zulaihat ta soma tana murmushi gami da yi mata kallon yarinya karama don duka a sannan ba ta fi sha biyar ba.

"Kar ki soma don Allah Ramlat, ina mai tabbatar maki ba wanda zai goyamaki baya. Kar ki sake ki ɓullowa da wanin Hilal matsayin saurayinki. Take-takenki kenan wanda ba zan so ya janyomaki wani tambari kuma abin yayatawa ba a dangi. Ture ma batun dangin da kuma mu, ba ki kyauta ba, za kuma ki amsa sunan mayaudariya. Ina so ki binne kuma ki ci gaba da haɗiye abinda ke ranki, ki tattara wajen miƙa wa Ubangijinki. Shi zai zaɓamaki abinda ya fi alheri. Kar ki yarda kuma kar ki yi gangancin bada kofar da za'a ƙara fahimtar inda kika dosa. Allah Ya kyauta don kuwa akwai matsala."

Daga haka ta mike ta bi bayan Hajiyar zuwa ɗaki, itama ganin ba amfanin zamanta sai ta koma ɗakinta, kuka ta yi son ranta sannan ta fito. Ta ga alamar babu wanda zai fahimceta, zuwa yanzu za ta kwantar da hankalinta har ta kammala Sakandire, a wannan lokacin ne za ta san abin yi.

Da wannan shawarar ta ɗan saki ranta ta sauya, koda Hilal ya zo hakanan ta danne komai ta hau gyara jikinta babu ko kwalliya. Tana jin muryarsa yana gaisawa da su Hajiya, can kuma ta ji an murda kofar ɗakin an shigo. A'isha ta gani.

"Yaya, Hajiyata ta ce ki je waje ga Yaya Hilal."

Ta gyada kai tana hararar A'ishar cike da bakin ciki. Mayafin abayar da ta sanya kawai ta ja ta rufe kanta, a falon ta tarar da Hajiya don tuni Zulaihat ta tafi.

"Hajiya zan je."

Ga mamakinta fuskarta a sake ta amsa.

"Toh wuce mana. Kar ki kai dare dai."

Ta amsa da toh tana satar kallon ledojin da ke kusa da kafar Hajiyar wanda ba tantama shi ya kawo.

Yana tsaye jikin motar ƙirar Honda wacce ta yi daidai da zamanin. Bayansa take hangowa, cikar kamala da ingarman jiki irin na maza ƴan kwalisa kuma abin muradin kowace mace, Hilal ya kai. Tana tafe kamar wacce kwai ya fashewa a ciki tana karantarsa, zuwa lokacin ya juyo shima ya zubamata idanunsa. Kallon da take mishi da ace a sannan akwai sauran cikakken nutsuwa tattare da shi, zai fahimci ba kallo ne mai nuni da kewa ba, kallo ne na ƙurillah, na ƙeƙe da ƙeƙe. Kallo ne na son gano abinda ya fi Aliyunta da shi wanda har ake zubamata gargadin ɓoye sittin zuciyarta. Shakka babu ya sauya, fatarsa ta kara murjewa, farinsa kuma ya kara fitowa. A gefe guda ya kara kyan da zai burge ƴanmata banda ita.

"Assalamu Alaikum." Ta furamta muryarta can ƙasan maƙoshi. Ya amsa yana mai jin kamar ya sanyata a aljihu su tafi tare.

"Ina wuni. An dawo lafiya?"

Nan ma bai ƙasa a gwuiwa ba ya amsa kafin ya bata umarnin su koma wurin kujeru zai fi. Suna tafe yana kallonta yana murmushi, ita kuwa banda guntun tsakin da take a ƙasa ranta ba komai. Hankalinta ma kacokan ya koma ga wayar da ta baro jone tana chaji, tsoronta kada Aliyu ya kira ba ta kusa ya yi fushi.

  "Faɗin yanda nayi kewarki ma ɓata baki ne. Ban ma san da kalmar da zan yi amfani wurin nunamaki kewarki da nayi ba. Ina sonki My Future, ba don akwai sauran rina a kaba ba, ai da aurenmu ko wata ba zai kai ba."

Ya ƙarashe zancen a marairaice, ba ta san sadda ta watsamishi wani kallo ba wanda ya ba shi dariya don a zatonsa na wasa ne.

"Ok I'm Sorry, I don't meant it. Sai dai har ga Allah ina jinki sosai a raina. Kamar fa karamaki kyau ake."

Duk wasu kalamai da yake fadi ba burgeta yake ba, murmushin yaƙe kawai take a wasu lokutan don ba yanzu take son fito da abinda ta binne ba. Duk kokarinta sai da Hilal ya gane kamar da matsala. Ganin haka ya nunamata zai wuce sai an kwana biyu tunda ya dawo kenan.

"Kamar ba ki yi murna da ganina ba. Haka kawai jikina ke ba ni kamar akwai matsala. Please ki fadamin kuskurena ni kuma na miki alƙawarin gyarawa."

Tsaki ta ja a kasan ranta, a fili kuwa ta yi murmushi.

"Na yi murna sosai fa, kawai dai yau na wuni da ciwon kai. Kuma hakanan nake jin jikina ba dadi. Kar ka damu."

Ta shiga istigfari a ƙasan ranta, shi kuwa tuni ya rude don dagaske ya yarda.

"Shi ne ba ki fadamin ba, ban ji dadi ba. Please yi hanzari ki je ki sha magani ki kwanta kinji? Zan kiraki anjima."

Ta gyada kai.

"Nagode. A gaida su Umma." Ta juya da sauri don dama jinta take kamar a kan ƙaya.

"Hey!" Dole ta dakata gami da juyowa. Yana rike da murfin mota yana bin ta da kallo kamar ya haɗiyeta.

"I so much love you!"

Maimakon ta amsa, sai ta bishi da murmushi da azama ta juya ta ci gaba da tafiya, a bangarensa ya fassara hakan da kunya. Wanda shi ke karamasa ƙaimi wurin sonta, duk kuwa da wani sashi na zuciyarsa bai gamsu da tarbar da ya samu ba.

'Na yi tunanin fiye da haka, zumuɗi, walwala, ɗoki.'

'Ka manta ba ta da lafiya? Ka yi mata uzuri. Ba ta da abin so idan ba kai ba.'

Da wannan tunanin ya ji karfin gwuiwa, hakan ya dawo da walwalarsa, burinsa yanzu ya haɗa dukkan takardun karatunsa ya bautawa ƙasarsa sannan ya kama aiki. Hankali da nutsuwarsa kacokan su dawo kan abar sonsa.

***
   Tafiya na ta tafiya, rayuwa na zuwa na sauyi masu tarin yawa. Kama daga siffofin halittu har ya zuwa zuciyoyi da kuma nasarori ko akasinsa.
Hakan ce ta faru da Ramlat sadda take cuku-cukun zana jarrabawar WAEC/NECO don hada kwalin Sakandire.  Dukkan wata cika ta ƴa mace ta sameshi idan ka cire rama da ƙashin wuyar da ta yi sakamakon zullumin da ta jefa kanta ciki ganin na taso da shiri gadan-gadan na aurenta da Hilal da zai biyo baya nan da watanni hudu.

"Ke za ki soma shiga gidan aure a class din mu. Ina ji daga ke sai G smally."

Faɗin Amrah sadda take kokarin gutsirar eggroll da ta ke korawa da lemun Pepsi. Da gayya ta ƙi duban fuskar ƙawarta don tasan cikin dayan biyu ne, ko ta samu harara ko kuma..

"Mtsw, aikin banza!"

Murmushi Amrah ta yi ganin ta ƙarasamata tunanin da ba ta san tana yi ba.

"Mene abin tsaki? Ai gwara ki yi wani sabon abin, ba abinda zan fahimta. Tunda ke ba kya jin shawara har ta kai matakin da za ki karyar zuwa gidanmu don kawai Aliyu ya zo ku gaisa."

Kwarewa Ramlat ta kusan yi da lemun Mirinda da ta ke sha. Murmushi Amrah ta yi ta ci gaba da cin Eggroll dinta hankali kwance.

"Allah Ya isa, kina neman kasheni da rai. Toh wa kike faɗawa? Ke bari na fadamaki, yanzu ko kofar gidanmu Aliyu zai taka ba na fargaban komai. Ke dai ban sanki da tone-tone ba. Gwara ki ci gaba da ɓoyen wannan sirrin. Ni wannan yanzu bai fiye damuna ba. Damuwata wai Muhibbat tana da ciki. Kuma cikin Aliyu."

Ta ƙarashe tana mai jin kwalla na cika idanunta, baki sake Amrah ke dubanta. Karshe sai ta sanya salati kafin ta ɗora.

"Kin hadu da aiki, kin kuma hadu da wahala wallahi Ramlat. Shiga hurumin kuma da ba naki ba za ki fara? Amma dai ina fatan ba ki nuna bakin cikinki a gabansa ba? Tunda ke ba kya aiki da hankalinki yanzu."

Guntun tsaki ta ja gami da harararta wanda ya yi daidai da zubowar hawayen.

"Mene naki a ciki idan na nuna toh? Waye ba ya kishin abinda ba ya so? Ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login