Showing 126001 words to 129000 words out of 226732 words
yanda ta kaya tsakaninta da Chairman yanzun a Ofis.
"Kai jama'a! Wai shi wannan mutumin da me yake taƙama ne? Ai sai ki yiwa kanki kiyamullaili, ba zama za ki yi ki zuba ido ba. Wallahi ki yi kokarin fito da miji ki yi aure abinki ya fiyemaki alheri, ke kanki kinsan tunda ya furta ba kyaleki zai yi ba."
Ramlat idanunta suka cicciko, batun fito da miji sai ya yi mata famin rashin Aliyu. Banda kaddarar mutuwa da ke kan kowa, yanzun da ba tana cikin inuwar aure ba? Waye zai ganta har ya ce yana sonta ko kuma ita ta ji son mutumin da ya yi mata nisa?
"Ni wallahi da ace wannan Hussein din ba shi da mata, wallahi zan so ki aureshi. Mutum ne iya mutum. Ke ko shi ko dan uwansa Hassan."
Kalaman Amrah suka sa ta fiddo idanu tana dubanta, Amrah ta yi dariya.
"Meye toh? Allah kuwa ni na fi so ma ki yi auren nesa. Kinsan mutane magulmata ne. Abinda ya riga ya wuce ma sai su ɗagoshi. Kuma fa ni sai naga kamar Hussein dinnan sonki yake."
Guntun tsaki Ramlat ta ja. Gabanta na faduwa, yanzun ko sunansa aka ambata sai ta ji sauyi a zuciya da kwanjinta😜
"Malama mu bar maganarnan, ba ta da fa'ida."
Dariya sosai Amrah ta yi, ta fuskanci inda Ramlatun ta sa gaba kawai dai ta yi shiru ta ga gudun ruwanta. Matar da ko labarin Hussein ta ke bada wa sai yanayinta ya sauya.
"Uhum, a juri zuwa rafi." Fadin Amrah kafin ta kai mangwaron da ta kammala yankamusu bakinta. Harara ta kuma samu daga Ramlat.
***
ADAMAWA...
[3/16, 1:55 PM] +234 703 629 0938: I just published "BABI NA ARBA'IN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/dlZmI7H2Cbb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
40)
*Assalamu alaikum. Masu karanta Karfen Kafa ku yi hakuri. Na fadamaku exams zan soma gobe In Sha Allah. Daga wannan post din kuma sai sadda ku ka ji ni. Nagode sosai sosai.*
ADAMAWA..
Ɗaure fuska ya yi kamar bai taɓa dariya ba yana duban Dada, cikin harshen fulatanci ya yi magana.
"Akan me zai sauka a gidannan? Me hakan ke nufi?"
Dada ta harareshi.
"Taheer ɗan uwanku ne, don ya zaɓi gidannan matsayin wurin kwanansa ba laifi bane. Kar ka manta ɗan ɗan uwana ne."
AlHassan ya ɗan dafe goshi, sam bai ji dadin wannan hukunci ba. Sallamar direba rike da ƙaton akwati yasa AlHassan miƙewa.
"Ni zan wuce Dada, akwai inda zan je."
Ta bishi da a dawo lafiya, a kofar suka yi kiciɓus da Taheer. Dauke kai ya yi kamar bai ganshi ba zai wuce, da sauri Taheer ya karasa ya mika masa hannu da sallama. Akan dole ya bude nashi hannun suka gaisa daga nan bai ƙara cewa uffan ba ya yi gaba.
Taheer ya bishi da harara, dama ca ya tsaneshi saboda girman kai. Shi kuwa ya zo kuma sai ya cimma manufarsa, idan ana so dole sai Hafsat ta so shi ta kaunceshi. Sai ya aureta.
Dada ta tarbeshi a mutunce, aka mika kayansa dakin su AlHassan na baya.
Hafsat dake makaranta tana dawowa ta yi kiciɓus da shi a falo yana cin abinci suna hira da Dada kamar dama can sun wani saba. Turus ta yi tana kallonsa ranta na wani irin zafi, Dada ce ta lura da ita.
"Mene na tsayawa haka kamar kin ga Dodo?" Dada ta furta cikin harshen Fulatanci sanin da ta yi Taheer din kusan ba abinda aka koyamusu, manyan yara Modibbon ne kaɗai masu jin fulatanci. Su kam saura sai Hausa da turanci.
Maganar Dada ya kai hankalin Taheer ɗin ga Hafsat, ƙuramata idanu ya yi, ta watsamasa harara ta kauda kai gami da karasowa ciki. Maimakon ta ba shi haushi sai ta ba shi dariya. Ya yi murmushi.
"Welcome my dearest."
Ya faɗi sanin da ya yi shi ɗin ma Dada ba ji ta ke ba. Ciki-ciki ta gaidashi saboda hararar da Dada ke watsamata. Ya amsa a sake. Ta mike ta faɗa ɗakinta har wani kwalla ta ji sun cikamata idanu tsabar ɓacin ran ganinsa. Ta rantse ba za ta ƙara kwana a gidannan ba, gidan AlHassan za ta wuce.
Tana soma haɗa kaya kenan sai ga Dada. Nan ta yi mata kaca-kaca ta kuma rantse muddin ta ce za ta bar gidan sai ta saɓamata.
"Ku kenan haka ku ke son na mutu da bakin cikin ban shirya da ƴan uwana ba? Yayana ya mutu ya bar ni zuciyarsa cike da burin ganin watarana su Hamma Modibbo sun riƙemu matsayin jininsu kuma ƴan uwa, bai samu ya ga hakan ba, sai yanzun da Allah Ya soma amsa addu'a ta har gashinan wani a gidan Modibbo ya yi sha'awar zuwa gidannan ku ke neman ku sanyamin ciwon kai? Toh sa ƙafa ki fita daga gidannan mu zuba ni da ku!"
Dada na kaiwa nan ta fice ranta na suya. Hafsat ta yi cilli da atamfar da ke hannunta ta fashe da kuka. Dada ba ta san manufar Taheer na shigowa gidannan ba. Ita kuwa ta rantse nan duniya ba wanda zai sa ta aurensa. Sai dai ko me zai faru ya faru.
***.
_*So ne baƙin duhu zallah, a faƙaice zai yi ma illah, ciwon so ba ya biɗar sassaƙe...*_
*Hamisu Breaker.*
KANO.
Karfe biyar da mintuna na yammacin Asabar, tsaye yake jan abin motsa jikin na (Treadmill), daga shi sai riga da gajeran wando. Ya sanya tawul a saman wuyansa, a hankali yake tafiya ba kamar Hisham dake gefe yana zabga uban gudu ba.
Kacokan kusan hankalinsa ba'a jikinsa yake ba, Hisham ya kalleshi ya fi a ƙirga, karshe ya tsayar ya sauka yana maida numfashi, kai tsaye water bottle ya dauka dake gefen jakunkunansu ya shiga kurɓa can ya ƙaraso ya tsaya gami da dafe ƙarfen da Hussain ke kai, ya ƙuramasa ido.
"Lafiya?"
Ya fadi yana maida numfashin gajiya.
Hussein ya dubeshi. Sai a sannan ya yi amfani da ƙaramin tawul din ya goge gumin da ke zirarowa daga goshinsa har yana ɗiga daga karan hancinsa zuwa baki.
"Me ka gani?"
Gira Hisham ya ɗaga yana murmushi.
"Sai wani tunani kake kamar wanda ya faɗa tarkon so."
Kallonsa Hussein ya yi a karo na biyu kafin ya sauka ya zauna saman kujera.
Hisham bai hakura ba ya ƙaraso ya zauna gefensa.
"Kai mutumin, na fa gama gane bakin zaren. Ka dai yi gamo."
Guntun tsaki Hussein ya ja.
"Kai maganar ma da ba ta kamata ba yinta ka ke yi. So kuma? Ban da lokacin shirmennan."
Murmushi kawai Hisham ya yi. Kamar ya ce wani abu sai dai bai ce ba.
Wayar Hisham din ce ta dauki ƙara, ganin sunan da ke jiki ya sanya shi satar kallon Hussein yana murmushi. Shi kam bai ma san yana yi ba, wai harara a duhu.
"Ranki ya daɗe Antinmu."
Fadin hakan yasa Hussein satar kallonsa, ya basar kamar bai gani ba, can ya ce.
"Af, wayarta ba chaji ne toh inaga don ba ta saba kashewar ba."
Can ya ƙara faɗin.
"Toh Allah Ya kaimu goben, amma dai a tahomin da yaranmu."
Hussein ya gaji da satar kallon ya juyo gaba dayansa yana mai tsuramasa idanu.
Dariya Hisham ya yi, ba don bayanin Ramlat din ya ba shi dariya ba sai dai yanayin amininnasa.
"Ayya toh Allah Ya maidomana su lafiya. Allah Ya kaimu goben. In Sha Allah idan na koma zan sanarmata."
Daga haka ya kashe wayar. Yana dariya ciki-ciki ya ce.
"Kai kuma wannan mayun idanun da ka tsuramin fa? Toh wallahi kurwata kurrr!"
Duka Hussein ya kai mishi a kafaɗa, ya yi dariya. Shi kuwa ya mike ya dauki jakarsa ya yi gaba zuwa hanyar banɗaki. Yana jin Hisham na fadin.
"Oho dai, na gane komai!"
Har ya kammala shiri yana maimaita kalmar na gane komai din da Hisham ya furta.
Sai da ya kimtsa sosai ya fito, wannan karon dogon wando ja ne ya sa da t-shirt bodyhug fara ƙal.
"Sai ka taho."
Hisham ya bude baki.
"Au haka za ka yimin? Toh ai shikenan. Nidai gobe kam ba zan zo ba, inada baƙuwa ta musamman a gidana."
Taɓe baki Hussein ya yi.
"Matsalarka." Daga haka ya yi gaba bayan ya yi sallama da ƙalilan da suke a dakin motsa jikin. Hisham ya bishi da kallo yana dariya.
***
WASHEGARI...
Cikin shirinta tsaf na riga doguwa ta shadda kalar sea green ya sha adon stones. Mayafi ƙarami ta ɗora samansa. Tuƙi take hankalinta kwance, kaso na damuwarta
Sati daya kenan da ta nemi sauyin wurin aiki, ta samu takardar sauyi daga ma'aikatarta zuwa ma'aikatar ilimi. Wani farin ciki na musamman take ji, ko ba komai za ta rabu da alaƙaƙai. A gefe guda kuma ta gama fahimtar yanda ta yi nisa a son HUSSEIN. Soyayyar da idan ta tuna shi ma dadi take ji, murmushi take yi
Ta bude hirarsu ya fi a ƙirga, ta tuna zantukansu ya fi sau dari a satinnan. Ji take inama yanda take jinsa shima haka take a wajensa. Har ta ƙaraso gidan A'isha ba ta bar tunaninsa ba.
"Assalamu alaikum."
Ta furta sadda ta isa ƙofar falon, ƴar aikin A'isha mai suna Bingel, ta amsamata sallamar. Laulayi da ta soma ne yasa dole Hajiya nemarmata ƴar aiki wata dattijuwa. Suka gaisa ta karasa cikin falon daidai da fitowar A'ishar daga ɗaki. Baki Ramlat ta saki tana kallon yanda duk ta zabge ta rame. Ta ƙaraso ta zauna.
"Kai Auta, duk laulayin ne?"
Yamutse fuska A'isha ta yi kamar ta yi kuka. Cike da shagwaɓa ta amsa.
"Wallahi Maman Affan ni duk cikin ma ya isheni. Allah kuwa ji nake kamar a .."
"Astagfirullah! Kar ki karasa Princess. Ina rabaki."
Suka dubeshi, Hisham ne wanda ya fito daga dakin sanye da jallabiya. Dariya ma suka ba Ramlat. Ta dara kadan, ya ƙaraso yana hararar A'isha. Daga bisani suka gaisa da Ramlat.
"Kin ganta nan, girki ma yanzu ba ta fiye yi ba yayi dadi. Wataran gishiri ya yi yawa, ko maggi ya yi yawa. Wai dama haka ake laulayin da shegen tsawo da kuma wuya?"
Murmushi sosai Ramlat ta yi.
"Irin naku kenan sai hakuri."
Nan dai ya yi ta caccakar A'isha ita kuwa sai cika take da batsewa. Dariya kawai Ramlat ke yi, ganin dagasken fita yake son yi siyo abinci ta mike tsaye.
"Haba dai, wallahi ka barshi bari na girka tunda na zo."
Ya kuwa shiga godiya, ya ja hannun A'isha wai ta zo ta kwanta ta huta ya mata tausa. Kunya ya kama Ramlat, ta yi saurin faɗa wa kicin tana murmushi. A can ƙasan ranta ƙara godewa Allah ta yi da baiwar da ya yiwa ƴan uwanta na mazaje nagartattu masu sonsu. Tunanin Aliyu ya faɗomata da yanda aka sha fama akan aurenta da shi da kuma Hilal. Idanunta suka ciko da kwalla. Ta haɗiyesu sakamakon Bingel da take tare da ita a kicin din.
Shinkafa da miya kawai ta girka, ganin suna da kayan ganye sai ta yanka kabeji da su karas ta haɗa coleslow.
Ta shirya komai saman tebur kafin ta dawo falon ta zauna tana danna waya. Muhibbat ta kira suka gaisa ganin kwana biyu ba su yi magana ba. A karshe ta nemi Amrah a waya suka hau hira. Har zuwa sadda A'isha ta fito.
Zama ta yi tana hamma, dagasken dai bacci ta yi don idanunta da fuska sun nuna.
"Ya kike ji yanzun?"
Gyada kai ta yi.
"Da sauki sosai. Sai dai yunwa."
Murmushi Ramlat ta yi.
"Daukomin hijab sai ki je ga abincin can saman tebur."
Miƙewa Aishah ta yi ta koma daki, ca ta fito rike da Hijab da darduma. Ramlat ta shimfida ta tayar da sallah, tana cikin sallar Hisham ya fito yana amsa waya.
"Dagaske kake ko wasa?"
Can kuma ya ce.
"Ok ganinan zuwa."
A'isha ta dubeshi tana kokarin zuba abinci a plate. Kafin ma ta tambaya ya amsa da dariya yana satar kallon Ramlat.
"Wai kinsan kuwa Hussein ne ya zo yana waje? Bari na shigo da shi."
Daga haka ya fita, har suka shigo tare ba ta idar ba. Jin sallamarsa sai da gabanta ya fadi kafin ta yi istigfari a zuciya ta maida hankali ga sallarta. Sai da ta idar ta shiga addu'a hannun har yana rawa. Ya na zaune kujerar da ke fuskantarta. Gaisawa suke da A'isha amma kusan hankalin yana kanta. A'isha ta saci kallon Hisham ya kashemata ido daya. Ta girgiza kai, ta san dama shi ya haɗa hakan.
Ramlat ta kasa cire hijabin, ta mike ta ninke dardumar.
"Ina wuni." Ta gaidashi, ya amsa a hankali. Rabonsu da juna tun wayar a suka yi kwanaki, ko a WhatsApp bai ƙara kulata ba.
"Ku muje mu ci abinci, don wallahi Princess yunwa take ji."
Fadin Hisham yana mai miƙewa.
"Na ƙoshi." Daga Hussein har Ramlat kusan a tare suka furta, abin sai ya ba Hisham da A'isha dariya. Suka saci kallon juna, kunya ta kama Ramlat ta kauda kai. Shi kuwa Hussein murmushi ya yi.
"Toh duk sai kun ci wallahi."
Fadin Hisham.
A dole suka bi bayansa, Ramlat ta dage a falon za ta ci.
"Kai Sis." Fadin A'isha kamar ta yi kuka. Hussein ya ja kujera ya zauna bai ce musu uffan ba. Wayarsa ta yi ƙara ya mike cak ya fita gami da fadin.
"Ina zuwa."
Hajiya Zeenat ce, tambayar inda yake ta hau yi, ya dafe goshi.
"Ina gidan Hisham, wani abu?"
"Shi ne ba za ka fadamin ba? Na dawo gida ban ganka ba."
Ransa ya ɗan sosu.
"Da za ki fita yawon biki kin fadamin?"
"Ni kake faɗawa haka?" Fadin Hajiya Zeenatu cike da wani irin firgici.
Ya lumshe idanu ya bude.
"Sai na dawo."
Daga haka ya katse kiran. Ya koma ciki.
Madadin ya ganta a tsakar falon, sai ya ganta zaune kujerar gefen da ya tashi, ya karasa ya zauna.
"Hala Madam din ce ko sabuwar kamun da muka yi?"
Fadin Hisham yana ƴar dariya da satar kallon Ramlat.
Kirjin Ramlat ya buga, wani irin kishi ya turniƙeta. Ba ta san Hisham na da zancen da hankali ba zai dauka ba, zance marar kan gado ba, sai yanzun. Wani haushi ya bata, abincin ma ya daina yi mata dadi, dama tun zaman Hussein ƙamshin turarensa ya mamaye ilahirin jikinta ya haifarmata da kasala. Yanzun jikinta ya idasa mutuwa.
"An fadamaka kowa irinka ne kenan."
Abinda Hussein ya ce kenan bai ƙara uffan ba ya bar Hisham da dariya.
Tunda ya soma cin abincin wani dadi ke ratsa kunnuwansa. Ya kasa ɗagowa har sai da ya yi nisa da soma ci, can dai ya dubi Hisham.
"Nikam Princess dinka hala ta yi makarantar koyon girki ne."
Haba! Ai daga Hisham din har A'isha da uwar gayyar Ramlat, dariya suka ya basu. Ya dubesu yana dan yarfa hannu, ya tsaida kallon kan Ramlat.
"Mene abin dariyar?" Ta sunkuyar da kai tana murmushi.
"Antinmu kinga karo na biyu wannan bawan Allahn na buga santi akan girkinki. Gaskiya yau goron da zai ba da kamata ya yi ya fi na rannan."
Ita dai ba ta ce komai ba, ta kasa ci gaba da kai lomar, karshe ma miƙewa ta yi.
"Na ƙoshi."
Daga nan ta yi gaba da sauri ta koma cikin falon ta zauna ta basu baya tana sauke ajiyar zuciya. Shima gogan bai ƙara magana ba har ya kammala ci ya mike ya bar Hisham da A'isha ma ƙusƙus.
Wuri ya samu ya zauna yana danne waya, sai dai rabin hankalinsa a kanta yake. Tun yana satar kallo har ya koma kallon sosai. Karshe ya maida hankali saman wayar, whatsapp ya shiga. Ganinta online ya taɓota.
"Thank you."
Ta bude saƙon kafin ta saci kallonsa, murmushi yake amma idanunsa na saman waya.
"Kallon fa? Kar ki mata kwace."
Jin bing na shigowar saƙo ta maida hankali ga wayar. Abinda ta gani kenan, ta turo baki kadan ta kashe data gami da jefa wayar cikin jaka.
Miƙewa ta yi ta dauki mayafinta ta nufi dakin baƙi. Hijab din jikinta ta cire ga gyara zaman mayafin ta fito. Lokacin su Hisham sun dawo falon.
"Ba dai tafiya ba?"
Fadin A'isha.
"Tafiya zan yi, Hajiya ta ce kar nayi dare."
"Kai kamar wata karamar yarinya. Ko hira fa bamu yi ba. Prince ka yi mata magana."
Fadin A'isha a shagwaɓance. Sakin baki Ramlat ta yi don ita abin ma na A'isha da Hisham mamaki yake bata. Soyayyar dai kamar ana ƙaramata zuma.
"Ji, toh banda uzurin gabana da zan ƙare a gidanku?"
"A'a amma don Allah ki zauna, kinga fa yanzu shida, ga hadari a gari..."
"Shiyasa ai zan tafi, kinsan ban fiye tuƙi idan ana ruwa ba."
A'isha kuma ta rasa abin faɗi. Hisham dama bai ce ba, so yake abokinsa ya ce!
Jakarta ta dauka cikin lallashi ta ce.
"Haba Autar Hajiya, In sha Allah za ki ganni kwanannan, ai yanzun sai ana leƙowa ana dubaki. Yauwa Maman Twins ma sun ce na fadamaki suna nan zuwa."
Jin haka yasa A'isha sakin ranta kaɗan.
"Toh ai shikenan. Allah Ya kaimu."
Ramlat ta amsa da amin tana murmushi.
Hussein ya mike yana duba agogo.
"Nima zan gudu."
"Kamar hadin baki?" Fadin Hisham.
Girgiza kai Hussein ya yi.
"Yamma ta yi ga hadari."
Gyada kai Hisham ya yi.
"Ai shikenan, don ma dai kai din baki da hanci ne. Ba nisa sosai."
Hussein bai amsa ba ya bi bayan Ramlat da tuni ta fice.
Hisham na dariyar mugunta ya yiwa A'isha raɗa a kunne ya bi bayansu.
"Innalillahi, garin yaya?" Fadin Ramlat a hankali tana jin kamar ta yi kuka. Hussein ya juyo yana dubanta, iska na faman ɗaga mayafin nata da ja mata rigar. Tayarta ya gani a sace.
"Ya Salam, Antinmu garin yaya hakan ta faru?"
Fadin Hisham sadda ya karasa yana kyafkyafta idanu ganin iska na neman yi mishi lahani. Kamar ta yi kuka ta dubi Hisham.
"Wallahi nima bansani ba."
Ta furta cike da takaici.
A'isha ta danne dariyarta, game din dadi yake mata sosai. Tuni Hussein ya bude motarsa ya shige ya ba ta wuta.
"Shigo na kaiki." Abinda ya ce kenan. Ta dubeshi ta maida duba ga su Hisham.
"Je ki don wallahi hadarinnan yanda ya haɗe ba zan iya fita ba. Sai dai ko ki kwana zuwa safe."
Ta haɗa daga shi har A'ishar ta watsawa harara.
"Gobe na ƙara zuwa gidanku."
Nan kuma suka hau aikin ban hakuri, ta karasa ta bude gidan gaba ta zauna. Hussein ya dubi abokinsa.
"Sai