Showing 153001 words to 156000 words out of 226732 words
ya gani yana murmushi ya ɗaga.
"Kira da safiyar Allah, bashin me na ci?"
"Haba Malam, ina ka shiga ne wai? Jiya na kira duka wayoyinka amma a kashe, lafiya dai ko?"
Hussein ya lumshe ido ya ja guntun tsaki tuno da shirmen Zeenatu.
"Share kawai, lafiya lau ne. Ya aka yi?"
"Ba ka da labarin an kai wa Ramlatu hari?"
Wani irin miƙewa Hussein ya yi gaba ɗayansa har santsin bargon na ƙoƙarin kifar da shi ƙas.
"What?"
Labarin komai Hisham ya ba shi.
"Tana wane asibitin?"
Ya sanarmasa.
"Yanzu zan zo."
Daga nan ya katse kiran bai jira komai ba.
***
MISALIN ƘARFE TAKWAS NA SAFE...
Hawaye ta ke fitarwa yayinda ta ke tariyo komai a kwanyarta. A yanzun da Hajja ke salati da tambayar wa zai aikatamata hakan? Itama a sannan kwakwalwarta ta shiga aikin tunani. Kasancewar ta juyamusu baya ya sa ba wanda ya lura da tashinta. Cikin dare dai ta farka sannan ta ƙara komawa bacci.
"Abin dai da ɗaure kai." Hajiya ta furta tana ƙara riƙe carbin hannunta da ta ke ja.
"Nifa ina zargin matar Hussein wallahi. Tunda..."
"Yi shiru kawai Rafee'ah, zato dai zunubi. Irin haka ne sai ki ga ana zaton wuta a maƙera sai aka same ta a masaƙa."
Rafee'ah ta yi shiru amma dai kam zuciyarta cike take da zarginta. Kwankwasa ƙofar da aka yi ne suka bada iznin shigowa. Hisham ne da AlHassan, suka karasa aka gaisa.
"Kada dai ace har yanzu ba ta farfaɗo ba?" Cewar Hisham.
"Aa, ta farfaɗo cikin dare, har na taimaka ta ɗan zagaya. Sannan ta yi salla da Asuba ma. Baccin ne dai ya ƙara kwasarta."
Ramlat da ke jin bayanin Hajiya sai ta runtse idanu, wani radadi kafaɗarta ke mata, sai dai idan har za ta iya jure wannan adalilin Hussein, idan har zaa iya yaudararta a kafamata tarko a kansa, toh ba karamin so ta ke yi mishi ba. Ta ƙara aminta da hakan.
"Au dama idanunki biyu?" Cewar Rafee'ah wacce ta zagayo domin gyaramata ɗankwalin kanta da ya zame.
Ta dube ta, ganin tana hawaye ta sa hannu ta shiga sharemata.
"Haba Ramlat, meye kuma na kukan tunda Allah Ya riga da ya tsare? Yi shiru don Allah. Ko za ki tashi zaune?"
Ta gyada kai. Da taimakon Rafee'ah ta miƙe zaune ta jingina da filo. Ta gaida Hajja da su Alhassan.
Wayar Hisham ta yi ƙara ya duba, shi kansa AlHassan tunda ya ji batun zuwan ɗan uwansa ya rasa sukuni. Burinsa kawai ya gan shi don ya tabbatar da komai. Aikuwa shi ɗin ne.
"Kana waje? Ok gani nan zuwa."
Yanda Hisham ya miƙe hakanan shima AlHassan ya mara mishi baya. Rike hannunsa ya yi.
"Ka yi hakuri, nan zai shigo, ka jira ya karaso ciki ka ganshi."
Ramlat da kirjinta ya tsananta bugu ta dubi Hisham a hargitse. Nan da nan wasu hawayen suka kwaranyo. Baki na rawa ta ce.
"Hussein..Hussein ne?"
Hisham ya dubeta.
"Shi ne, ku kwantar da hankalinku yanzu zan kawo shi."
AlHassan a dole ya dakata sai dai ya kasa tsayuwa wuri guda, safa da marwa ya shiga yi yana kallon ƙofa. Koda aka tura ƙofar aka shigo. Hisham din ne a gaba, a bayansa kuma Hussein. Kamar wani gunki haka AlHassan ya ja burki yana kallonsa ƙurr.
"Hussein...?" Ya furta, furucin da ya ja hankalin Hussein dake sanye da Maroon shadda da hula, ya dubeshi.
[3/16, 1:55 PM] +234 703 629 0938: I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/97Mzs8D3Qcb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
49)
Gaisawa suka yi da Munir yana ƙara taya su murnar daidaituwa.
"Allah Ya kara kiyayewa, Ya yi sakayya" Cewar Munir. Da murmushi ƴan biyun suka amsa da amin. A hankali ya kai duba ga Ramlat, ganin haka ta yi saurin sunkuyar da kanta. Ya maida idanunsa ga ƴan ɗakin, kafin waninsu ya kai ga cewa wani abu, an ƙwanƙwasa ƙofar. Hisham wanda ya fi kusa da ƙofar ya buɗe. Chairman Aliyu Dikko ne tsaye daga bayan masu kula da lafiyarsa biyu, yana aikin gyara zaman malun-malun dinsa.
"Assalamu alaikum. Don Allah nan ne ɗakin da aka kwantar da Ramlatu Khalid?" Faɗin ɗaya cikin security din da suke tare. Hisham ya dubesu, yanzun ya gane ko wane. Kofar gaba daya ya buɗe. Suka dubeshi, Ramlat nan da nan ta haɗe fuska gami da gyara zaman mayafin da ya ɗan rufe jikinta. Hussein ya harɗe hannu a kirji yana kallonsa kamar yanda shima Chairman ya yi musu ƙuri da idanu. Ya kalli AlHassan kuma ya kalli Hussein ɗin wanda bambancin sutura da kuma gilashi kadai ya sa ba zai iya rantsuwar mutum guda ba ne. Ya daure ya dake yana mai miƙa hannu a yi musabaha, Munir da AlHassan duk suka miƙa banda Hussein wanda ya kauda kai, fuska a ɗaure ya dubi ɗan uwansa.
"Muje ko?"
Yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin, ganin haka da yawa cikinsu ma suka fita, ya yi saura daga Ramlat sai Chairman. Ya zauna saman kujera gami da ba ƴan rakiyarsa umarnin tsayawa daga waje.
"Sannu Baby, ashe kuma harbinki aka yi? Su waye wadannan?"
Tun Baby da ya kira ta da shi, ta ji gabanta ya yanke ya yi wani irin faɗuwa, ba wanda ya faɗomata a rai sai Aliyunta. Ta yi mishi addu'a a ƙasan ranta kafin ta ƙara yin ƙasa da kanta, har dai ya kammala ɓaɓatunsa ya mike ba ta ce mishi uffan ba sai da ta ga ajiye bandir na ƴa dubu har biyu a gefenta.
"Bana so, ka ɗauke abinka."
Ta furta a kausashe. Ya yi murmushi.
"Haba Baby..."
"Kar ka ƙara kirana da wannan sunan!"
Ya jinjina kai.
"Na ji, lokacinki ne yanzu, ki yimin duk abinda ki ka yi niyya. Nan ba da jimawa ba za ki koma ƙarƙashin ikona."
Ta ja guntun tsaki, ya gyara zamam rigarsa ya fice. Ba jimawa da fitarsa su Amrah suka dawo ɗakin.
"Yau naga ikon Allah, wannan shi ne ƙarfin hali wai ɓarawo da sallama. Mutumin nan ba zai gaji ya kyaleki ba?"
Faɗin Rafee'ah tana ɗaga kuɗaɗen da Chairman ya ajiye. Kafin Amrahbta ce wani abu aka ƙara ƙwankwasa, da sauri Rafee'ah ta ajiye kuɗin. Ɗaya daga cikin abokan tafiyar Chairman ne, manyan ledoji ne har uku ya shigo da su. Ya ajiye.
"Ranki ya daɗe, Alhaji ya ce a miƙo. Allah Ya ƙara lafiya." Har zai juya Ramlat ta dakatar da shi.
"Maida."
Ya yi murmushi.
"Ki yi hakuri Ranki Ya Daɗe, ban isa na ketare umarninsa ba. A dai yi hakuri a karɓa."
Daga haka ya kama ƙofa. Za ta ƙara magana Amrah ta girgizamata kai, dole ta haɗiye gami da yin ƙwafa.
"Ki rabu da shi, ba laifinsa ba ne tunda dai shi ɗan aike ne. Allah Ya kyauta. Amma dai babu alamar mutuminnan zai saduda."
Amrah ta fadi bayan ya fice.
"Wai nikam Aunties, anya Hussein ba ya son Antinmu? Kun ga yanda fuskarsa ta sauya da ganin Chairman?"
Hunainah ta furta tana duban dariya ƙasa-ƙasa na zolaya.
"Ke Hunainah! Kin riga ni a fili amma nikam na rigaki a zuci. Ni wani kallo ma na gani kamar a duniyar romeo da juliet wallahi."
Abinda Rafee'ah ta ce ta basu dariya sosai idan ka cire Ramlat wacce ta san ba haka tsakaninta da Hussein, asalima ita ke kiɗa da rawarta. A fakaice ta share kwallar da ta cika idanunta. Shigowar Munir ya sa suka bar maganar, hakan ya fi komai yi mata dadi. Anan ya ke sanarmusu Hussein sun wuce tare da AlHassan da Hisham daga can za su biya wurin police station.
"Af, nikam Yaya su waye suka yi wannan aika-aikar? Sun yi magana?"
Ya taɓe baki jin tambayar Rafee'ah.
"Eh toh, su na ta dai walagigi da hankulan jama'a, amma ko mene idan an shiga kotu gaskiya za ta yi halinta. Mace ce, sunanta Halima. Ta dai yi ikrarin kishin Ramlatun ne yasa ta aikata hakan. Ganin za ta auri Chairman. Wannan shi ne rashin sani wanda ya fi dare duhu. Idan ma da gaske take, toh ta yi a banza."
"Ya sunanta?" Ramlat ta tambaya a hanzarce. Ya ɗan yi shiru don shi kam ya mance ma da sunan.
"Nan fa ɗaya, na mance."
"Halima?"
Ta tambaya gabanta na faɗuwa.
"Yes! Sunan kenan. Amma ya aka yi ki ka sani?"
Girgiza kai ta yi, ta ba su labarin takun saƙar da suke yi tun zuwanta ma'aikatar Revenue kafin ta bar shi.
"Amma ba na tunanin ta san akwai wata alaƙa tsakanina da Hussein."
"Ki kwantar da hankalinki ke dai, ko ma mene yanzu kam ai zai fito fili tunda an cafke ta."
Ramlat ta girgiza kai karo na biyu tana duban Yaya Munir.
"Hakane, amma ban taɓa zaton tsanar da Halima ta yimin ya yi ƙarfin da ko bindiga aka ba ta za ta kasheni ba, na yi mamaki matuƙa."
"ƊAN ADAM aka ce maki, mai wuyar gane hali. Allah Ya kyauta." Cewar Amrah. Suka amsa da Amin. Ita dai Ramlat har sannan mamaki bai sake ta ba, ta ƙara jin tsanar auren Chairman.
***
Chairman Aliyu Dikko, wanda ganin mijin Hajiya Zeenat da wani photocopy dinsa ya ɗaurewa kwanya, ya kasa haƙuri sai da ya fiddo waya ya dannamata kira. Har ya katse ba ta ɗaga ba sai a karo na biyu sannan ta ɗaga.
***
Lokacin tana gida ta hargitse tana jiran shigowar Hussein don su bar garin zuwa wata Jahar kafin lamura su kwaɓe. Ga dai tana ta kiransa ya ƙi ɗagawa. Lokacin ne kuma kiran Chairman ya shigo, kamar ba za ta ɗaga ba a farko, sai dai ta ɗaga.
"Nikam Zeenat, mijinki Hassan da Husseini ne?"
Ta saki rigar Hussein da ta ke shirin sanya wa a akwati. Gaskiyar Gora kenan da yace su na tare?
"Lafiya? Kin yi shiru?"
"A ina ka gan su?"
Daga amsar ya fahimci ruɗewarta. Kai tsaye ya ce.
"A asibiti na je duba Amaryata Ramlatu, kinsan harbinta aka yi. Shi ne na tadda su a ɗakin. Sai wani hararata yake yi kamar na kashemasa wani. Na yarda da zarginki, son yarinyarnan yake kuma kwalalensa."
Tusa Hajiya Zeenatu ta saki wanda ya tahomata da guntun kashi. Ta sharce gumi ta hau safa da marwa.
"Yanzu a can ka baro su? Wane asibitin?"
"Zan miki ƙarya ne? Nawa za ki ban idan na miki ƙaryar? Idan kina son ganewa idanunki ki taka ki je."
Ya sanarmata asibitin, ba ta jira komai ba ta katse wayar. Banɗaki ta shiga ta sauke nauyin cikinta, ta kimtsa jiki sannan ta fito. Sun rabu da Hajiya Batool akan zasu haɗu su je wani ƙauye domin a yi musu aiki maikyau. Sai dai ba ta jin za ta jure wanzuwar Ramlat a doron ƙasa, za ta sa a karo na biyu a kashemata ita. Duk abinda zai faru sai dai ya faru.
Ta fice daga gidan gaba ɗaya.
***
Chairman da tun bayan kammala wayarsu da Zeenatu ya yi shiru yana tunani.
"Ina maka rantsuwa da Allah zan sa a kashe Ramlatu idan ni ban kashe ta da hannuna ba muddin ta yi kuskuren shiga rayuwata da mijina."
"Dakata!" Ya ba direba umarni, ganin haka direban ya ja ya yi parking a gefe.
Chairman ya fidda waya ya ƙara kiran Hajiya Zeenatu, yana ta ringing ba ta ɗaga ba. Haka ya yi ta dialing shiru, don haka ya yi saurin cewa direban ya mishi magana da daya daga cikin abokan tafiyarsa. Da sauri direban ya fita zuwa ɗayar motarya kira.
"Sir."
Chairman ya dube shi.
"Ku juya ku koma asibitinnan, ku tabbatar kun kula da marar lafiyarnan. Ina zuwa."
Ya hau lalube cikin hotunansa har ya fiddo hoton Hajiya Zeenatu a wajen wani taron biki da suka hadu. Koda wasa ban yarda ku bar wannan matar ta shiga dakin ba."
Ya jinjina kai cike da girmamawa ya karbi odar ya koma motarsa. Motar Chairman ya wuce su kuma suka juya zuwa asibitin.
***
Hussein ya yi shiru kawai yana kallon Halima wacce har sannan ta ƙi faɗar gaskiya. Sai ka rantse hankalin a kanta yake, amma ina! Zuciyarsa na wani ɓangaren, sai hura hanci ya ke yana ƙara cin magani. Garin Kanon ta fita ransa, so yake su juya tare da ɗan uwansa kawai. Sai dai kafin nan yana son nunawa Hajiya Zeenatu kurenta. Yana son maka ta a kotu yanda za ta fuskanci fushin hukuma, duniya kuma ta san da abinda ta aikata.
Wayar AlHassan ta yi ringing, gani Dada sai ya yi murmushi ya fita daga station din. Hisham ya ɗan daki kafaɗar Hussein kaɗan, dubansa ya yi kawai ya watsamasa harara ya kauda kai.
Dariya sosai Hisham ya yi.
"Ikon Allah, to ni kuma me na yi? Nasan fa me ke cin ranka"
Hussein ya gyara tsayuwa gami da ɗan lumshe idanu bai ce uffan ba.
"Kar ka yiwa kanka saki na dafe, tun kafin lokaci ya ƙuremaka gwara ka faɗamata abinda ke ranka."
Ya dubi Hisham.
"Me kake nufi? Kuma wa kake nufi?"
Hisham ya bude baki zai magana ya ɗaga mishi hannu.
"Malam bana son shirme, yimin shiru. Kai a komai sai ka sanya wasa da zolaya. To ka fita idona."
Dariya sosai ya ba Hisham. Daidai sadda AlHassan ya dawo ya dubesu yana dariya.
"Lafiya dai? Tom and Jerry?"
Murmushi kawai Hussein ya yi.
"Dada ce?" Ya tambaya. Gyada kai AlHassan ya yi yana murmushin shima.
"Yes, ita ce. Sai dai ban fadamata komai ba, na dai ce ina tafe da wani babban albishir."
Jinjina kai Hussein ya yi.
"When? Nima na ƙagu na gan ta."
"Very soon in sha Allah."
"Maiduguri fa?"
Cewar Hussein kamar zai yi kuka.
Dariya AlHassan ya yi.
"Duk za mu je da yardar Allah. Saboda rashinka na ɗauke ƙafa, ganina yana sa Hajjo kukan tunawa da kai. Wannan ta sa tsakaninmu sai waya."
"Ina son hukunta ta." Hussein ya fadi zuciyarsa na zafi, fuskar Hajiya Zeenatu ya ke haskowa da kuma cuɗanya iri-iri da ya yi tare da ita.
"Muje daga waje please. Nan ba wurin tattauna wannan zancen ba ne."
Suka dubi Hisham mai magana, su ka maida hankali ga Halima da ta yi musu ƙuri da kumburarrun idanunta. Duk hirar da ake yi tana ji, kalaman Hussein na ƙarshe ya sa tsoro ya ƙara kamata. Kada dai ita yake nufin a hukunta? Ita kam ta shiga uku. Ba ta mance shawarar da kaninta ya ba ta ba da ya zo.
"Idan kinsan ba da gaske kike ba Yaya Halima, ki fito ki fadi gaskiya kafin lokaci ya ƙuremaki. Nidai gaskiya ban yarda da abinda kika faɗamin ba."
Ta share hawaye tana ci gaba da kokwanto a ƙasan ranta. Ta faɗa ko kuma ta yi shiru? Ita kanta ta rasa wanne za ta zaɓa. Har suka fice tana kallonsu. Ta bi wurin kwananta da kallo, ta ja majina. Anya Hajiya Zeenatu dagaske ta ke za ta cire ta a wannan taskun? Shiru ta yi, karshe ta yanke shawara ta aika ƙaninta wurin Hajiya Zeenatu ya yi mata bayanin halin da take ciki.
***
Ramlat ta yi shiru, ita kadai a dakin, su Rafee'ah sun wuce, sai Hajiya dake bandaki ɗauro alwalar sallar Azahar.
Nos Khadija ta kwankwasa ta shigo tana jan kayan dressing din ciwo a ɗan keke. Suka yiwa juna murmushi. Ɗan zaman da ta yi a asibitin sun saba, mace ce mai kirki.
"Su kuma waɗannan ƴan sandan da aka zubamana a bakin ƙofa fa? Da alama dai Angonnaki na baki kulawar da ta dace."
Wannan ne karon farko da ta ji haushin Nos Khadija, sam ba ta son abinda za'a haɗa ta da Chairman. Tun kafin su Munir su tafi, suka zoda zummar tsareta bisa umarnin ubangidansu. Har ta soma faɗa Munir ya ce ta rabu da shi kawai. Shi ya sani. Taɓe baki ta yi ba ta ce komai ba. Daidai sadda Hajiya ta fito, suka gaisa da Nos Khadija gami da yin ƴar raha don mace ce mai tsokana da kuma ja da wasa. Tana cire Bandage din kafadar suna ta hira abinsu, bayan ta goge ta ƙara rufewa sannan ya dubi Ramlat jin Hajiya na faɗan ba ta son cin abinci.
"Ki dinga cin abinci don Allah Ramlat, haba yar uwa, ina yabonki? Ki ci yanda idan na ba ki magani ba zai sanyaki jiri ba. Yanzu zan dawo."
Ta gyada kai ba don ta so ba, ita kawai komai ma ba dadi ya ke mata.
***
Hajiya Zeenatu tunda ta doshi barandar ɗakin da Ramlatu ta ke ta hangi wasu masu kayan ma'aikata tsaye a bakin ƙofar ta yi turus. Wuƙar da ke cikin jakarta yasa ta kasa ƙarasawa, juyawa ta yi tana tunanin ina mafita? Ta ya za ta cimma burinta? Yanzun ta tabbatar Hussein ba zai kara yi mata kallon mace mai daraja da ƙima ba a idanunsa, amma tabbas idan ta bar Ramlat na yawo a doron ƙasa tofa shakka babu, wataran za ta ji batun aurensu. Abinda ba za ta taɓa ɗauka ba har abada. A kan idanunta, Nos Khadija ta shiga, hakanan a kan idanunta ta fito. Wata dabara ta faɗomata don haka koda Nos Khadija ta zo wucewa ta wurinta ta saki fuska sosai suka gaisa.
"Nace don Allah idan babu damuwa, ina son ganinki."
Nos Khadija ta bita da kallo, a shekaru ta girme mata sosai hakanan kuma ba ta yi mata kama da wacce ta fito daga ƙaramin gida ba.
"Shikenan, ba ni minti biyu."
Hajiya Zeenatu na murmushi ta gyada kai. Ba jimawa Khadija ta dawo suka ɗan fita waje.
Shiru Khadija ta yi tana jin bayanan Hajiya Zeenatu. Kirjinta ya shiga dukan uku-uku.
"Ki sani, wallahi-wallahi duk wani jin dadi na rayuwa kin sameshi kin gama matukar kika yimin aikin da na sanyaki. Zan ba ki duniya iyakar ƙarfina. Za ki taka duk ƙasar da kike so, za kuma ki shiga duk inda kike so a faɗin garinnan ba wanda ya isa ya ce maki don me?"
Jikin Khadija ya ɗauki wani irin rawa. Tunda take a duniya, tunda ta ke, ba ta taɓa jin lamari irin haka ba. Wani irin tsoron da ba za ta iya misaltawa ba ya shige ta. Daga yanayinta Hajiya Zeenatu ta gane babu nasara don haka ta bude jaka ta fiddo bandiran kudi ƴan dari biyar guda biyu ta miƙamata, Allah Ya taimaka babu jama'a a wurin, ta ɗago mata lafiyayyar wuƙa sabuwa fil ta nunamata.
"Ki zaɓi ɗaya Hajiya Khadija, idan ba haka ba ni da kike gani don na kasheki ba komai ba ne a wurina. Sai na ɓatar da ke