Showing 153001 words to 156000 words out of 231169 words
daga Bauchi don daddy baya gari ya koma wurin aiki...a bakin gate sukayi parking Bobby sai kallon gidan yake cikin ranshi yace"so this is their house?.."ya karasa da wani murmushi kan face dinshi...yaron da ya rakosu ne ya shiga ciki yace ma Ammi sun iso ita kuma ta tura Husna tace ta shiga dasu parlon daddy..babu wasting of time kuwa Husna ta fito tana hangosu ta karasa kusa dasu ta washe musu baki tace"sannunku da zuwa"..Nur ne ya fara cewa"yauwa sannu yanmata..ke qanwar Lamido ce koh?.."gyada mishi kai tayi still smiling tace"nike binta ai..sunana Husna Lamido"..Nur dake gyada kai yace"MashaAllah Husna Lamido"..juyawa tayi tana kallon Bobby daya rungume hands dinshi yana kallonsu..suna hada ido ya sakar mata smile tareda cewa"Sannu Husna Lamido"..murmushinta ta kara fadadawa kafin tace"Ammi tace ku shigo ciki"..daga haka tayi gaba sukabi bayanta har cikin gidan..parlon daddy ta shiga dasu as instructed by Ammi snn ta gaidasu ta fita...Nur ya shiga kallon parlon yana yaba kyau da yayi mashi...shiko Bobby idonshi bai sauka ko inaba sai kan wani picture dinsu gaba daya lokacin suna kanana..ita da Ammi ne a pic din daddy ya dauki Husna Ammi kuma ta dauki Yusra aysha kuma tana tsakiyarsu...tayi murmushi a picture din har dimples dinta sun fito..murmushi da bai shiryaba ya saki yanajin wani weird feeling tattare dashi..sake maida dubanshi yayi ga dayan picture din shima gaba dayansu ne amma wnn sun girma gaba daya snn akwai Hamma Najeeb a jiki..dan hade rai yayi ganin yanda take zaune kusa dashi gaba daya suna daria kawai sai yaji baiji dadin zama kusa dashi da tayi ba..da sauri ya dauke idonshi daga hoton don gudun kada ya karasa spoiling mood dinshi da dama ba daidai yake ba...wani fitinannen kamshi ne ya bugi hancinshi kafin ta shigo parlon a hankali tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki...kallonta kawai Bobby yake yanajin zafin a yanayin da ta fito..is she mad zata sanya turare haka ta fito kuma ba tareda hijab ba?..juyawa ga Nur yaga sai wani kallonta yake yana murmushi nan take yaji 6acin ranshi ya karu akan wanda yake ciki..shi baima san kaddarar data kaishi daukan Nur ya taho dashi ba gashi nan sai kalle mashi ita yake a banza kmr yaga matarshi...karasowa ciki tayi ta zauna hankalinta gaba daya kan Nur fuskanta ba yabo ba fallasa tace"sir good afternoon"..Nur da har yanxu ke murmushi yace"good afternoon amarya Lamido ya hutu?.."dan murmushi kawai tayi tareda cewa"Alhamdulillah"...Bobby daya cika yayi fam ya shiga dubanta da angry eyes dinshi yace"bakida hijabi ne?.."daure fuska tayi ba tareda ta kalleshi ba tace"bani dashi"..yace"then tashi muje a siyo"..banza tayi dashi tana sake dinke fuska..shi wnn irin masifaffe ne wai?..a nan dinma sai ya mata bala'i bazai bari su rabu lafia ba?..mikewa yayi hands dinshi a aljihun wandonshi yace"ki tashi muje a siyo nace"..ko motsawa batayi ba Nur dai da yaga abun na Bobby azimun ne sai ya mike ba tareda ya kalli inda yake ba yace"i will wait for u in the car"..daga haka ya fita daga parlon shi kuma ya shiga takawa a nuste zuwa inda take yayi kata wani tsaye yana kallonta kmr soldier...dan dagowa tayi a hankali ta kalleshi taga kallonta shima yake kmr an aikoshi nan da nan ta sauke nata idon tana kunkuni...zama yayi nan kusa da ita still yana dubanta yace"and wa ya fada maki ana sa turare haka a shiga cikin mutane?.."kallonshi ta juyo tanayi kmr zata sanya kuka..ya lumshe ido tareda jingina da jikin kujerar yana maimaita innalillahi a cikin zuciyarshi..kada kuma ta fara tunanin yana overacting amma Allah ya san ba karamin kishi yake dashi a kanta ba..ganinta a haka shi kanshi saida yaji wani abu balle kuma Nur da bai hada komai da ita ba..shi bayason ana ganin beauty dinta ne and fesa turare ko Allah ya haramtawa mata su fesa su fita sbd kamshi ba karamin fitina yake haddasawa ba..a hankali ya bude idon nashi tareda gyara zama yana dubanta yace"why are you ignoring my calls?.."tace"ba komai"..girgiza kai ya shigayi yana dubanta cikin ido yace"karya kikeyi"..ta wani zaro ido tana kallonshi saura kiris daria ya subuce mata tace"sir karya kuma?.."kai ya sake gyadawa alamar haka yake nufi...ta dan turo baki tace"nidai ba karya nake ba"..kallonta ya tsaya yi kawai kmr baiji abunda ta fada ba...riga da skirt ne a jikinta na lace da yayi matukar amsarta..ta daura dankwalinta as usual saidai wnn karon bata fito da gashi ba don tasan sai yayi mgn sai kuma veil dinta data yafa a kafada...gani yake duk dunia babu macen da zata kaita kyau a idanunshi..ita komai ta sa kyau yake mata shiyasa a kullum kishinshi karuwa yakeyi a kanta...lumshe ido yayi tareda sauke ajiyar zucia cikin voice dinshi da yaji ya dashe all of a sudden yace mata"i love u so much Aysher..plss i beg of u ki bar kin answering calls dina..am about going crazy.i..i am..."kasa karasawa yayi kawai yayi shiru yana sauraran heart beat dinshi...kallonta yacigaba dayi voice dinshi na rawa sosai yace"have mercy on me plss..i promise to love u till my very last breathe..I promise to be a good husband..i will never rufuse u anything in the world just wanted u to love me nor matter how little i wont complain..kawai ki soni ki zauna dani for i dont think i can live without u..i love you dearly"..lumshe idanu Aysha tayi tana sauraran words din nan nashi..bata san why ba amma words din really galddens her heart..sunyi mata dadi sosai ba kadan ba..kawai mamaki take yanda the whole Dr Bobby ke pouring mata love words haka..bata san ita ko tana sonshi ba amma this very moment taji ya burgeta matuka..da dadewa dama tasan son da yake mata ba gama garin so da ake iya samu a ko ina bane sai wanda Allah ya zaba yake bama masoyi mai matukar sonka kamarshi..kawai gani take Allah knows best shiyasa ya hada aurenta da nashi..idan kuwa haka ne ita bazata ja da ikon Allah ba saidai tayi fatan hakan ya zama alkhairi a garesu baki daya...ganin yana mata wnn kallon nashi mai sawa taji wani iri ta mike da sauri har veil dinta yana faduwa ta dauka da sauri ta fita daga parlon ta bar Bobby da lumshe ido yana saqan kamshin da ta tafi ta bar mashi...yana nan zaune after few minutes ta dawo dauke da tray a hannunta ya mike da sauri ya amsa tray din ya ajiye kan table ita kuma ta sake fita ta dawo da wani..a takaice saida ta cika musu gaba da kayan ci dana sha snn ta kama haya zata fita yayi saurin cewa"where are u going to?.."tace"zan kira provost ne yazo kuci abinci"..girgiza mata kai ya shiga yi yana zaro wayanshi yace"don't worry i will call him..amma haka kike fita Aysher duk mazan dake gidan nan suna kallonki?.."juyawa tayi ta koma ciki ba tareda tace komai ha don bata ma san abunda ya kamata ta fada ba..shi kuma yayi dialing number din Nur yana dagawa yace ya shigo suci abinci..ba musu Nur ta dawo parlon ita kuma ta mike tana fadin"bari inyi excusing naku idan kun gama sai in dawo"..kai kawai Bobby ya iya daga mata yabi bayanta da kallo har ta fita snn ya sauke ajiyar zuciya ya fara cin abincin...sai yanxu ya samu kwanciyar hankalin cin abinci amma daxu ji yake gaba daya tension din dunia kanshi ya kare.
Bayan sun gama cin abincin ta dawo tareda Yusra data dage sai taje ta gaishesu...kanta a kasa har ta karaso ciki ta zauna..Bobby daketa kallon Yusra ganin kamar Ilham dinshi yace mata"hey cutie"..washe baki tayi tana gaisheshi yace"ya sunanki?.."tace"Yusra Lamido..kaine wanda zaka auri Addah?.."dan wara ido yayi yana kallonta da murmushi yace"yeah nine..waya fada maki ni zata aura?.."da sauri Yusra tace"Adda Husna ce tace wai kai proprietor dinsu ne kuma wai kai inya..."Aysha bata bari ta karasa ba ta toshe mata baki...Bobby sai yayi relaxing yana kallonsu..dukda bata bari ta karasa ba yasan inyamuri zata ce..girgiza kai kawai yayi yana murmushi..Aysha ta mike rikeda hannun Yusra suka fita daga parlon tace"ni zaki tonawa asiri Yusra?.."a hankali tace"kiyi hakuri Adda mantawa fa nayi"..Aysha tace"oya wuce ki koma wajen Ammi kar na sake ganin kafarki a nan"..ba musu ta wuce ta bar wurin ita kuma ta sauke ajiyar zucia tareda komawa ciki...bata samu Nur a parlon ba sai shi kadai...tana karasawa ta zauna yace mata"daddy baya gari ne?.."tace"eh yana Abuja"...gyada kai yayi kafin ya sake cewa"inyamuri kike cemin koh?.."wani irin zare idanu tayi hadda su dafa kirji tace"Nii😳"..murmushi ya kara saki yana gyada kanshi yace"yes ba gashi zata fada kin hanata ba"..turo baki tayi tana kawar da idonta daga wnn kallon nashi tace"nidai ba haka nake cewa ba ba ruwana"...daria mgnr nata ya bashi aiko ya shiga yinta kmr me..saida ya gama don kanshi snn yace"ko haka kika fada ma ba wani abu ke bakaya laifi ai..and niba igbo bane..ni bafulatani ne just like you"..shiru tayi tana wasa da fingers dinta..shi kuma kallonta yakeyi yanajin tamkar ya janyota jikinshi yace"ko har yanxu baki yadda nima dan Gombe bane?.."sake turo baki tayi cikin gajiya da tambayoyin nan nashi tace"na yadda"..shiru ya sakeyi for some minutes kafin kuma yace"so yanxu dai ni zan aureki?.."sake sunne kai tayi tanajin wani irin faduwar gaba..shi kuma har yanxun ya kasa dena murmushi yacigaba da fadin"i just can't wait for ranar da za'a daura mana aure..am eager in ganki cikin gidana as my wife"..wnn karon rufe fuskanta tayi da hands dinta don wani irin kunya taji ya rufeta..shiko murmushi kawai yake saki non stop murya can kasa ya kira sunanta"Aysher"..dagowa tayi a hankali tana kallonshi..shima kallon nata yakeyi kafin yace"i love you..to the moon and back..kuma nagode sosai for agreeing to marry me insha Allah bazakiyi regretting decision din nan ba"..kasa ta sakeyi da idonta tanajin wani baqon al'amari na zaga jikinta...banda yake ba abunda take yau duk uban surutunta nemanshi tayi ta rasa kuma ta rasa dalili..duk wnn rashin kunya data gama planning zata mishi saita kasa sbd kwarjini na musamman da taga ya mata uwa uba kuma wnn words da yake sake kashe mata jiki dasu...duk sai taga ya sauya kaman ba proprietor data sani mai dan karen masifa ba...shiko murmushi yaki yankewa a face dinshi sam sai wani jin dadi yake kmr anyi mashi bushara da aljannah...sake kasa da murya yayi kafin yayi mgn wayanshi dake ajiye kusa dashi ya fara ringing..dubawa yayi yaga wanda ke neman katse mashi wnn jin dadin sai yaga Mummy dan haka yayi picking da sauri yana cigaba da murmushi da igbo yace"Hello Mummy"..da igbo din itama ta amsa mashi da"tun daxu nake kiran wayoyinku bai shiga..ka bani ita mu gaisa idan kuna tare"..mika mata wayan yayi yana binta da wani kallo mai wuyar fassarawa yace"Mummy"..ba musu ta amsa wayan tareda kaiwa kunne..a daya banagaren Mummy tace"daughter"Aysha ta sake sinne kai tana murmushi tace"Mama ina yini"..Mummy tace"lafia lau ya hutu"..tace"Alhamdulillah"..Mummy tace"maasha Allah dama so nake in maki godia for accepting him..Allah maku albarka yasa haka ne alkhairi a tareda ku"..kasa tayi da kanta ta kasa amsawa..ita duk bata san yaushe kunya ya shigeta har haka ba wlh..bata taba zaton zataji wani abu wai shi kunya ba a rayuwarta amma yau gashi tanaji kuma batasan dalili ba...godia sosai Mummy ta sake kwararo mata snn tace ta gaida Mamanta..ta amsa mata da zataji snn ta mika mashi wayar...yana karba ya sake maidawa kunne yana sauraran abunda take fada yanata murmushi...baice komai ba har saida ta gama snn ya ajiye wayar...agogon hannunshi ya duba yaga time na wucewa gashi yau zasu koma Kano dan haka ya wani langabar da kai yana kallonta in a pleading tone yace"tafia zamuyi Aysher..amma dan Allah i beg of u ki bar fesa turare haka da yawa idan zaki fita kuma ki taimakamun ki dinga sa hijabi please"...dagowa tayi ta kalleshi ya sake narke mata idonshi aikuwa ta dauke nata da sauri jin wani abu ya fito daga cikin idon nashi ya shiga nata..itadai ta shiga uku da idanun nan nashi da ba dama ta kallesu ko ya kalleta dasu sai ya sata jin wani iri..ganin har yanxu batace komai ba ya sake kasa da murya yace"kinji?.."kai kawai ta iya daga mashi ba tareda ta kalleshi ba..shiko bai dauke idanunshi a kanta ba ya sake cewa"And dan Allah ki taimaka ki dinga daukan wayana..hankalina tashi yake idan ina kira baki dauka ba kinji?.."nan ma kai ta sake gyada mashi without saying a word..gaba daya yawun bakinta ma taji ya kafe mata all of a sudden..kallonta yake yana so ya samu eye contact da ita amma taki dagowa..yace"to kiyi mgn da Ammi zamu gaisheta kafin mu wuce"...ba musu ta mike ta fita daga parlon shi kuma ya bita da kallo yanajin sonta na sake zagaya duk wani system na jikinshi...after like 5 mins ta dawo tace Ammi tace su shiga dan haka ya kira Nur a waya ya dawo snn suka shiga main parlor gaba dayansu...Ammi na zaune kan one of kujerun parlon sanyeda hijab sai Yusra a gefenta...suka karasa ciki duk suka zauna a kasa Ammi nata cewa su koma kan kujera amma basuyi hakan ba suka fara gaisheta a haka...ta amsa da fara'a tareda tambayan iyayensu duk sukace suna lafia..nasiha sosai tayi musu kafin su mata sallama su fita Bobby na sakejin matar ta kwanta mashi a rai sbd kamalarta..wato ba daddy kadai ne dattijo a gidan ba ita kanta Ammi dattijuwa ce..sunada halin girma sosai ba kadan ba..ya kuma san yayi dace da Allah yasa zai auri diyarsu don mutanen kirki ne..shi sai yau ya samu ganin tsananin kamar da Aysha takeyi da Amminta..irin kama sosai wanda ko mgnrsu ma kusan iri daya ne likewise dimples dinsu...halayyan su ne kawai ya bambamta don yasan da kyar idan wnn fitinan na Aysha a wurin Ammi ta dauko..ita batayi kala da fitinannu ba sam amma ita indo a kallon farko da mutum yayi mata yana iya gane tsantsar rashin jin dake tattare daita dukda ma dai yanxu ta girma ta rage kiriniya...ita kadai ta rakosu har compound don Husna ta wuce islamiyya...suna gama sallama da Nur ya bude mota ya shiga yayinda shi kuma Bobby ya karasa inda take tsaye ya zaro kudi a aljihunshi ya mika mata yana cewa"sorry ban kawo maki komai ba..hankalina ne duk ba daidai ba lokacinda zamu taho amma ga wnn kisai duk abunda kikeso"..girgiza mishi kai tayi alaman bazata karba ba..ya wani langabar da kai yana kallonta yace"dan Allah accept it..bazanji dadi ba in kikamun haka"..shiru kawai tana kallonshi..ya kamo hannunta yasa kudin a ciki snn ya sake kasa da murya still bai bar kallonta ba yace"shknn zamu wuce..ai ranan sunday zakuyi resuming school koh?.."kai a kasa ta amsa da"eh..zamu tafi clinical posting"..gyada kanshi yayi yana murmushi don tuna zai samu damar ganinta son ranshi a asibiti yace"i can't wait for sunday..i love u sosai"..kasa ta sakeyi da kanta batace komai ba..yace"Aysher look at me mana"..dan dagowa tayi ta kalleshi suna hada ido ta juya zuwa cikin gida da sauri har tana tuntu6e shi kuma ya shiga shafa kanshi yana sakin murmushi ba kakkautawa...shi kanshi baisan ya iya murmushi ba har haka..gaba daya 6acin ran daya kwaso tun daga kano yana zuwa gareta sai ya nemesu ya rasa sai farin ciki daya baibayeshi kuma.."oh Allah nagode maka..Allah Alhamdulillah bazan gaji da godia kan wnn kyauta da kayimun ba..i will be forever grateful"..abunda yake fada knn yayinda ya karasa inda motarshi yake ya bude ya shiga snn driver ya tada ita suka fara tafia...ko a cikin motar relaxing yayi kan kujera yana shafa kai yana murmushi kamar sabon kamu..Nur dai na zaune gefe yana kallon ikon Allah..a fili yace"muma dai mun kusa isowa wurin nan...lokaci karami muke jira muma mu shigo sahun manya"...Bobby dai kala baice dashi ba yacigaba da murmushinshi..idan yace zai biyewa Nur yasan tsaf zai iya harxukashi suzo suna rigima gaban driver shiyasa bazai kulashi ba ko don ma farin cikin da yake ciki a yanxu haka.
Wnn dai page din gobe ne na dawo muku dashi yau so koda kun jini shiru gobe ga abunku nan na baku.😄
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
48
Ranar sunday around 11 suka baro Gombe zuwa Kano sbd posting da zasu fara..saida suka fara tsayawa Bauchi sukayi picking Billy da duk ta kasa sakin jikinta da Hamma sbd mgnr so daya 6ullo tsakaninsu..yana ankare da ita shiyasa tun farko baiso tasan yana sonta ba sai sun kammala school amma mgnr da Lamido yayi shi ya hargitsa komai..tana zaune back seat sai sunkuyar da kanta take kmr munafuka..ita kuma Aysha banda daria ba abunda take mata..shidai yana jinsu baice komai ba sai kallonta da yakeyi ta mirror time to time...karfe biyu da wani abu suka shigo Kanon Dabo kai tsaye kuma suka wuce FCNM kmr ko yaushe dai...sai yanxu hankalin Aysha ya dawo jikinta ta shiga tunanin rayuwar da zatayi da proprietor yanxu kuma..a dan wnn lokacin ta fahimci ba karamin mara kunya bane shi..yanda yake nuna yana sonta gaban uban kowa abun har tsoro yake bata kada yaje yayita nunawa har kowa ya fahimci abunda ke tsakaninta dashi...a 6angarenta dai har yanxu tasan ba sonshi take ba kawai dai taji zata iya aurenshi ne sbd son da yake mata da kuma kasancewarshi za6in iyayenta...ga mamakinta suna shiga premises na makarantan sukaci karo da motarshi parke wajen parking space alaman yana cikin makarantan knn..tuj daxu yazo yana so ya ganta shiyasa ko office dinshi bai shiga ba yayi zaune nan cikin mota tunda yanafa tint so ba wanda zai ganshi...kmr ance ya dago suna shigowa kuwa ya juya yana kallonsu..ranshi yaji ya 6aci da ganin wanda ya dawo dasu..to meye hadinta da wnn kuma yanxu?..har abada bazai manta shine wanda akaso bashi aurenta ba kawai Allah ya rubuta bashine mijinta ba amma da yanxu wani mgn akeyi ba wnn ba...yana kallon lokacin da ya fito ya rakasu zuwa inda zasu duba posting..da kanshi ya duba masu gaba daya ya kuma ce Freedom aka sake posting nasu again wnn karon Aysha ko