Showing 30001 words to 33000 words out of 231169 words
Miemie da aka sama sunan grandma dinta ta wajen uba wato Maryam ake kiranta Miemie...har zuwa wnn lokacin basa jituwa da sisters din mijinta dama mamansu gaba daya..kullum cikin nuna mata kiyayya suke kawai sbd ba ita sukeso ya auraba snn kuma da kasancewar Mum dinta igbo...wai Isma'il ya gur6ata musu family tunda ya hada musu jininsu dana inyamurai...haka aka cigaba da tafiya har ta sake haifan Ilham...ita kuma sunan Mummy aka sa mata Nadia ake ce mata ilham...wnn maida suna ba karamin tada rigima yayi tsakinshi da familynshi ba..wai don me zai sama yarinya sunan inyamurai...Sumayya da bata ta6a tanka duk abunda suke mata ba wnn karon kasa hakura tayi saida ta wanke su tatas ta kuma ce duk wanda ya sake izgili ga sunan mahaifiyarta sai sun kwashi 'yan kallo dashi...labari na zuwa ga Isma'il mahaifiyarshi ta sanyashi gaba da kuka wai matukar yana sonta sai ya saki Sumayya tunda batasan darajanta ba tayi mara rashin kunya...da sukaga bazai saketa ba sai sukasa ya sake auran 'yar sister din mamanshi sbd a kuntatawa Sumayyan...sunyi nasara kuma domin duk son da mijinta ke mata saida ta fara ganin canji tattare dashi...ya fara mata abubuwa wanda da ba haka yakeyi mata ba...gaba daya ma sai rayuwarshi ta koma 6angaren amaryarshi ita kuma ko oho don ko inda take bai cika zuwa ba...wnn abu yayi matukar daga hankalinta sosai tana ganin ko don yaranshi ai bai cancanci yayi abandoning dinta haka ba...daga karshe datayi kokarin nuna masa rashin dacewar abunda yakeyi sai yace taje ya saketa saki daya...bata sake wasting time ba kuwa ta hada kayanta ta wuce Abuja sbd a lokacin Daddynsu na matakin Controller General na Nigerian Custom so sun koma Abuja da zama...lokacin Ilham tana da shekara uku...haka suka cigaba da zama tareda iyayenta da kuma yaranta basu da matsalan komai...after a year Bobby ya kammala karatunshi a America lokacin shekaranshi kusan 9 a can...gaba dayansu suka shirya suka tafi America sukayi witnessing convocation dinsu snn suka dawo tareda shi Bobbyn da yakeda 27 years a lokacin...Sab kuma yanada 17 years kuma shima ya kammala secondary school.
Bayan kaman sati biyu da dawowanshi suka tafi kano wani taro da akayi inviting Daddy sai yace suje gaba daya...suka sauka nan gidanshi dake garin shi kuma ya wuce inda zasuyi taronsu...duk tsahon wnn shekarun daga Bobby har siblings dinshi babu wanda ke marmarin zuwa Gombe sbd cikinsu ba wanda baisan kalan hatred da sukeyi ma Mummynsu da su kansu ba...Bobby kuwa a lokacin ko mgnrsu ma baisonji...wani lokaci sai Daddy ya kira waziri ya waya ya hadasu su gaisa amma kowa zai kar6a shi kuma sai ya kirkiri wani abun ya tashi ya bar inda suke...Mummy duk tana lura dashi ta kuma san baya kaunarsu ne sam amma ko kusa batajin dadin hakan...tanaso ace ya samu kyakykyawan mu'ala da dangin mahaifinshi ko don sbd nan gaba ba wanda yasan me zai faru sai Allah.
A ranan bayan sun tashi daga taron shima ya wuce gida tareda zugan securities dinshi...misalin karfe 4:16 na yamma kiran wani brother dinshi ya shigo wayanshi...bayan ya dauka yake sanar dashi cewa waziri ne ba lafia kuma tun jiya yake cewa a kirashi yazo yanason mgn dashi...hankalinshi tashe sosai yace gashi nan zuwa Gomben yanxun...ba yanda Mummy batayi dashi kan ya bari da safe ba tunda yamma yayi amma yace sam bazai iya kwana while mahaifinshi nacan babu lafia kuma yana son ganinshi ba...babu yanda ta iya haka tabishi da addu'a...before ya fita ya shigo cikin gidan ya samu Miemie da Sab sai Sumayya a parlor nan yace musu zaije Gombe ya dawo suma suka mishi addu'an sauka lafia...yana shirin fita Bobby ya shigo parlorn rungume da Ilham da tayi bacci a hannunshi...shi kanshi yana ganinshi all dressed up yasan da akwai inda zaije...bayan ya fada mishi Gombe zaije ga mamakin dukkaninsu da shi kanshi Bobbyn yace zai rakashi...Daddy yayi mamaki sosai don sarai yasan duk yaran ma babu wanda yafi tsanan Gombe kamanshi amma yau shi da bakinshi yake cewa zai rakashi...bai yadda ya bishi ba yace zai tafi da driver shi kuma yanada bukatan ya zauna ko don ya kula da Mummy da sauran yaran...haka nan ya hakura amma har cikin ranshi baiso haka ba...shi kanshi baisan dalilinda yasa yau yaji yanason bin mahaifin nashi zuwa Gombe ba...duk abunda ke faruwa Mummy na zaune tana kallonsu itama bason tafiyan nashi takeba especially da yace dagashi sai driver zasu tafi bazai tafi da securities dinshi ba...a takaice bai samu ya bar gidan ba sai around 5...kaman yanda ya fada dagashi sai driver din nashi sukashiga mota suka kama hanyan Gombe...suna dab da shiga garin dan sun wuce Azare kawai sai ganin babban mota suka from no where tayo kansu gadan gadan...a kokarin driver na ya kaucewa motan sai kan motan ya kwace daya hannunshi gaba daya...daga nan kuma basu sake sanin inda suke ba sai ganinsu sukayi a Hospital...yana bude idanunshi yaci karo da waziri dake rikeda hannunshi idonshi yayi jajawur sbd tsabar rudun da yake ciki...ga kuma wasu daga brothers dinshi suma zaune a wurin...cikin tsananin ciwon kan dake addabarshi yayi kokari ya rike hannun mahaifinshi dake rikeda nashi...idonshi na zubda hawaye yake neman mahaifin nashi da ya yafe mishi...shima kanshi wazirin kaman zaisa kukan yace ya yafe mishi dunia da lahira..shima kuma yana rokon yafiyanshi kan duk abubuwan da ya aikata wa iyalinshi...shi kanshi yasan bai kyautawa abunda yake amma sam ya kasa denawa...yanxun kuma daya ganshi kwancs cikin jini sai duk wnn tsanar da aka sa yake mishi ya 6ace 6att sai tarin kaunar da yake mishi tun can baya suka shiga dawo mishi...lokacinda su Mummy suka karaso gaba daya ba wanda ke cikin hayyacinshi...kuka kawai suke har suka karaso inda yake...idanunshi ya shiga zagayawa akansu yanajin kaman kallon karshe yake musu...ya kalli Mummy da idanunta sukayi suntum sbd kuka sai Sumayya da har yanxu bata dena kukan ba...can gefe kuma Sab ne da Miemie suma rungume da juna suna nasu kukan sai kuma Bobby dake rikeda hannun ilham idanunshi a kasa sbd bayason suga yanda idanunshi suka sauya sbd kuka...hannu kawai ya mika mashi alaman yazo gareshi...cikin karfin hali ya saki hannun ilham tareda karasawa kusa dashi ya zauna ya kama dayan hannunshi da yake free...murmushi sosai yaga yanayi dan haka shima sai shiga kakalo murmushin yana kallonshi...cikin muryanshi da ko fita baiyi sosai ya nuna su Mummy dake jere suna faman kuka yace"na bar maka su amana...inaso ka kulamin dasu fiyeda yanda nakeyi...inaso ka zama gatansu...ko kusa kar ka bari suyi kukan rashina Bobby...they are now your responsibility"...kukane sosai ya kwace ma Bobby ya kasa cewa komai sai kai kawai da yake girgiza mishi...shi kuma ya sake kallon Mummy cikeda wani irin rauni yace"Your Mom...batada kowa Bobby...banaso tayi kukan rashina make sure ka kulada ita yanda ya kamata"...wnn karon ba Bobby kadai ke kuka ba gaba daya sauran ma kukan suke wiwi...suka hada ido da Sabeer shima ya mika mashi hannu yazo nan suka hada kai da Bobby sunata kuka abunsu...waziri dake zaune yana kallonsu bai ta6a jin ya tsani kanshi ba kaman yanda yaji a yanxu...kallonsu kawai yakeyi tunda suka shigo yanda ba wanda yabi ta kanshi a cikinsu...ya fuskanci akwai soyayya sosai tsakin yaran snn kuma yayi mamakin ganin yanda sukayi girma gaba dayansu...sai yakejin wani ciwo na rashin sakewa jikokin nashi da har Sumayya tayi 'ya'ya biyu bai taba ganinsu ba...ya kasa dauke idonshi daga kan Bobby sbd tsantsan kaman da yakeyi da Attahir dinshi...gaba dayansu ma sai yaji wani soyayyansu na daban na shiganshi...yaji gaba daya suna wani burgeshi gasu gaba dayansu tubarkallah dasu akwai kyau...hakika ya aikata kuskurenda shi kanshi baya tunanin zai iya yafema kanshi...bayan like an hour doctor yazo yace su barshi ya samu hutu...haka suka fita daga dakin sukayi cirko cirko a waje...Waziri dake waiting room yana hangosu sai ya fita daga dakin yace ace musu su shiga daka ciki su zauna...basuyi mishi musu ba suka shiga cikin dakin shi kuma ya kowa wani tareda yaranshi guda biyu da sukayi mishi rakiya...suna nan zaune akazo aka sanar dasu rasuwar drivern da suke tare dashi...hankalin kowa ya sake tashi masu kuka suka cigaba da gashi.
In summary dai shima Daddyn cikin dare Allah yayi mishi cikawa...fadan tashin hankalin da suka shiga 6ata baki ne...Mummy kuwa dama ana fada mata ta fadi wurin a sume...har wahegari bata farfadoba ga kuma bp dinta da yayi rising sosai dole aka bata alluran bacci.
Daga nan direct Gombe suka wuce dashi...lokaci daya mutuwan nashi ya watsu a gari kusan ko ina...karfe goma na safe akayi jana'izarshi aka kaishi gidanshi na gaskia(ubangiji kasa muyi kyakkyawan karshe)...shina waziri tun a wnn lokacin ya fadi dan ko jana'iza ba'ayi dashi ba...mutuwan ya dakesu ne sosai ba kadan ba...su Mummy kuwa gidanshi dake nan Gombe aka bude suka shiga itada yan uwanta da abokan arziki.
Ranan da akayi kwana bakwai rigima ya 6arke tsakaninsu brothers din Daddy suka dage kan lallai bazasu fita daga Gombe ba tareda anyi rabon gado an fiddama mahaifinsu kasonshi ba...a cewarsu tunda mahaifinsu nada gado suma suna dashi wai idan suka yadda suka bari Gombe ba'a raba ba suna iya yin sama da fadi da wasu abubuwan...kasancewar Waziri na kwance tunda akayi rasuwar sai baisan abunda yake faruwa ba...tareda Bobby sukaita yawo duk inda kadarorinshi suke ya kaisu suka gani snn aka shiga kotu akayi rabo aka fitarma waziri da rabonshi kaman yanda yake a addinance...a ranan da aka gama a ranan ya tattara su gaba daya suka bar garin ba tareda ko waziri sunje sun duba ba...duk yanda Mummy tayi dashi kan suje suga jikinshi snn suyi mish sallama kin yadda yayi dan shi gani yakeyi ma kaman da wazirin aka hada baki aka kashe musu mahaifi tunda kira akai aka ce shine bashida lafia amma da sukazo sai sukaga akasin haka.
Abuja suka koma direct sukayi parking abunda zasuyi parking...ya sai musu sabon gida a kano kuma bai yadda wani cikin 'yan uwan Daddy sun saniba snn ya sake daukosu suka dawo...gaba daya saida yabi ya canxa musu sim card dukda dama ba wani communicating sukeyi da yan uwan daddyn ba amma still saida ya canxa musu dan kwata kwata baison sake ganin kowa a cikinsu...su barsu suji da ciwon kashe musu mahaifi ma da sukayi...ko Sab da ba wani contact dinsu yakeda ba saida Bobby ya amsa layinshi ya bashi new one...Mummy dai bada son ranta yake abubuwan nan ba amma ko yaya tayi mgn sai taga ranshi ya 6aci fiyeda tunani...da farko ma cewa yayi sai yayi bincike if ya samu da akwai sa hannun one of them a accident din Daddy then bazai ta6a hakura ba saiya mgnr court...da kyar da sidin goshi Mummy ta samu ta taushe shi ya hakura da zancen...itadai har zuciyarta bata zargin akwai sa hannun wani a cikinsu...kawai tanaga ai duk kiyayyan da suke mishi bazasu iya aikata wnn danyen aiki especially akan dan uwansu...a lokacin abokan mahaifinshi da yawa suna kokarin taimaka mishi ya samu aiki amma yace shi sam bazaiyi aikin force ba infact bazai ma iya aiki under government ba...da taimakon wani uncle din Mummy wanda ya kasance likita ya bude katon Hospital dinshi mai suna Freedom Specialist Hospital...ya dauki ma'aikata sosai kuma most of them yare ne as gaba daya yanxu ya tsani hausa fulani because yana ganin kaman duk halinsu daya da 'yan uwan daddy...snn kuma ya tsani Gombe ya tsani duk wani abu daya fito daga garin...bayan shekara daya Allah yasa mishi albarka sosai dan ya kusan ninka abunda ya kashe a iya wnn shekaran...daga nan sai yayi tunanin ya bude Nursing and Midwifery College snn ya bude primary da secondary school duk a nan cikin kano...da yake kudi ne suke aikin in no time ya samu fili ya siya aka fara mishi aiki...a shekara na biyu ya bude Freedom College of Nursing and Midwifery Kano da kuma Freedom Science Academy Kano...nan ma yayi employing staff sosai suma kuma daga igbo sai yoruba sai kuma sauran tribes amma bai dauki bahaushe ko daya ba...a lokacin ya damqa Freedom Science Academy a hannun Aunty Sumy cox 6angaren data karanta knn shi kuma College din ya damqashi hannun abokinshi Dr.Nur...da shawarwarin Mummy dana sauran mutane abubuwa suke tafiya yanda ya kamata...cikin shekaru kalilan ya samu kudi fiyeda tunanin mai karatu...ya cire Miemie da ilham daga school da suke zuwa ya maidasu freedom shi kuma Sab ya nema mishi admission a Nigerian Police Academy Wudil as yana matukar son ya zama Police sbd it was his Dad's ambition.
In summary cikin shekara biyar Bobby ya zama hamshakin mai kudi a kano state...tuni ya gina musu very big mansion a can airport road inda babu mutane sosai...gaba daya rayuwarshi yanxub bai cika son mu'amala da mutane ba especially hausawa cox yana ga kaman suma zasuyi treating nasu some how sbd kasancewar Mummy inyamura...gidane mai kyau da girman gaske inda babu wanda zai takurama wani a cikinsu...a takaice dai yana kulawa dasu sosai sosai kaman yanda yayima Daddy alkawari...cikin shekarun nan kuma ya sake bude another College of Nursing and midwifery a Lagos sai kuma Freedom College of Health Sciences and Technology shima a Lagos...da yake a can ya girma har yayi primary da secondary school so yanada mutane a can sosai da suke handling mishi Colleges din as bai cika samun time yana zuwa sosai ba saidai yana providing musu duk wani abu da suke bukata...bayan nan kuma ya bude Freedom Medical College Gwagwalada Abuja...itama ba karamin kawo mishi kudi takeyi ba and a wata baifi yaje sau daya ba wani lokaci ma sai yayi two months baije ba sbd aiyuka da suke mishi yawa...haka rayuwansu yacigaba da tafiya har zuwa yanxub da Mummy ke son dawo mishi da duk pain da agony da suka fuskanta a baya.
Inaga gobe zaku jini shiru sbd zan danyi tafia...sai zuwa jibi in Allah ya kaimu💞🌸
Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidencs of payment ta 07063800556.
Rano✨
🤍Dr.BOBBY🤍
By Aysha Rano✨
Wattpad@aysharano22
11
Bayan sati hudu...
Yau tuesday Aysha na zaune cikin dakinsu kan study table ta dora macbook dinta akan table din tana kallon wasan Manchester United da Liverpool live...sai ihu takeyi tana nishadi duk ta cika dakin nasu da ihu sbd best player dinta Pogba gana performing well...yana ta6a ball zata hau ihu yanxu ma daddagewa tayi ta kwalla wani uban kara tana fadin"Goaal..yes yes..go on senior Man..go ahead"...Billy data fita karatu tun daxun sbd exams da suka fara jiya ta shigo dakin rungumeda katon text book dinta a kirji...ta karasa ta ajiye text book din kan shelve snn ta shiga rage kayan jikinta tana hararan Aysha tace"duk kinbi kin cikama mutane daki da ihu sai kace a kanki aka fara kallon ball"...Aysha da gaba daya hankalinta ke ga abinda take kallo ta saki wani smile tace"bazaki gane bane Billy wani hadadden ci Ronaldo yayi yanxun nan...and kinsan waye yayi assist?.."sake ta6e baki Billy tayi tana daura towel a jikinta tace"ya wuce Martial ko Rashford...ko kuma wnn gantalallen Lingard din"...tace"to duk basu bane Pogba ne..kuma gaskia kika sake cewa Lingard dinmu gantalalle za'aji kanmu dake a hostel din nan"...sake ta6e baki Billy tayi tareda shiga bathroom...har ta fito daga wanka hajia indo na nan inda take tana kallon ball dinta...ihu kuma ba fasa yinshi tayi ba saidai Pogba bai ta6a ball amma sai tayishi...Billy tayi banza da ita ta gama shiryawa abunta snn ta shiga kitchen ta hado corn flakes ta fito...tana zaune tana sha wayanta yayi kara...ta dauka ganin one of colleagues dinsu dake cikin hostel ne...tambayanta yarinyan keyi yaushe zasu fita karatu dan duk aka fara exams suna haduwa suyi karatu gaba saya su 'yan class dinsu dake cikin hostel din su 15...Billy ta amsa da bata sani ba su tambayo Lamido...tana tsaka da kallonta mutum biyu suka shigo dakin...daya daga cikinsu tace"Lamido ya mgnr karatun mu na yau ne?..kowa yana Common Room fa ku biyu kawai ake jira"...san juyowa tayi tayi musu kallo daya duk hankalinta naga kallon da take sam bataso a wuceta tace"safiyya dan Allah kuje ku fara da Billy ana gama wasan nan zan zo"..tana rufe baki Billy tace"babu wani farawan da zamuyi kawai idan bazaki koyawa mutane ba ki fada musu ba sai kima hanya hanya ba"...ta fada tana wani basarwa tasan tunda ta fadi bazata iya cigaba da kallon ba dan a dunia ta tsani mutum yace tayi mishi wulakanchi taki koya mishi wani abu...harara sosai ta sakarwa Billy kafin ta juya tana dubansu tace"ku bani 5 minutes plss ana tafiya half time zanzo"...Billy ta juyar da kai tana kunshe daria dama tasan maganinta knn...kaman yanda ta fada ana tafiya half time din ta mike ta fita hajia Bilkisu tabi bayanta...gaba daya sauran sun taru a Common Room din su biyu kadai ake jira...dakin yanada girma sosai snn da akwai expensive set of kujeru masu kyau a ciki hadda su tv da fridge da standard ac inshort dai babu abunda babu ciki har su curtains da center table like normal parlor dai sosai...each apartment sunada Common Room dinsu da bama wani zama ciki sukeyi ba sai idan abu ya kama irin haka...bayan sun zauna Billy tace"to yanxu da wanne ya kamata mu fara"...da sauri wata tace"mu fara complicated midwifery dan Allah...daxun dana daukoshi zan fara karatu har wani hazo hazo naga ina gani sbd tsabar bana fahimta"...gaba daya sunyi na'am da haka dan haka suka fara da shi din...course outline dinsu suke dauka sunabi one by one suna explaining snn duk wanda yakeda tambaya ya fada a amsa mashi...suna gamawa dashi sukayi other course din da shima zasuyi exam dinshi gobe snn suka watse.
Washegari bayan sun fito daga exam Aysha ta shiga kiran Sa'eed da tun safe bata ganshi ba...yana dauka tace"bestie where are you?.."yace"ina downstairs...kun fito daga exams?.."tace"eh..bari muzo downstairs din"...tana kashe wayan ta dubi Billy tace"muje yana kasa"...Billy ta wani hade rai tace"wai me zaiyi miki ne da kiketa nemanshi tun daxu?.."Aysha bata ce mata komai ba taja hannunta suka sauka kasa...can wajen wasu flowers masu kyau suka hangoshi yana zaune da wata class mate dinshi da alama yana koya mata abu ne...karasawa wurin sukayi suka zauna shi kuma