Showing 174001 words to 177000 words out of 231169 words

Chapter 59 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9713

murmushi tayi dialing number dinshi tana fadin"bama za'a Kai ga hakaba zaizo yayi maganin kayarshi"..yana daukan waya bayan ta gaisheshi tace mishi aunty Fiddausi tace idan zai iya zuwa Bauchi yazo ya duba musu ita batada lafia as usual Kuma taki yadda ayi mata allura snn taki tasha magani..Bobby da yaji abun kmr gaba ta kaishi nan take yace zai taho yanxun nn don shima son ganinta yakeyi musamman yanxu da akace batada lafia yasan ko yace sai gobe ma ba iya baccin kirki zaiyi ba so gwara ya taho yanxun..suna gama waya ta sanar da aunty Fiddausi yanda sukayi dashi dan haka tasa aka fara shirya mishi abinci kala kala yayinda hajia Ai ke kwance daki tana bacci bata ma San abunda ke faruwa ba.
Bobby na gama waya da Billy ya shirya kanshi sharp sharp ya dauki duk wani abu da yasan zai bukata tareda key din mota ya fita ka tsaye ya shiga flat din Mummy ya mata sallama kan zaije Bauchi wai Aysha batada lafia..Mummy batayi yunkurin hanashi ba ta bishi da addu'an dawowa lafia don tasan yanda duk ya rikice din nn idan ma ba'a barshi ya tafi ba hankalinshi ba kwanciya zaiyi ba...yana fita ya fada mota direct ya wuce gidan su Nur haka ya azalzaleshi ya shirya sharp sharp snn suka shiga motanshi suka kama hanyan Bauchi..Nur sai mita yake mishi wai daga dawowa gida ko hutawa bai barshi yayi ba yazo ya wani jajibeshi zuwa Bauchi sbd rashin hakuri ba yanda baiyi dashi akan ya bari sai gobe ba amma ya dage sai yau sai kace dai a kanshi aka fara soyayya.

Karfe hudu da wani abu suka shigo cikin Bauchi..driver aunty Fiddausi ta tura ya taho dasu daga inda suke har zuwa gidanta..shi ya fara shiga ciki kafin suma su shiga da nasu motan..parking Bobby ya karasa ciki yayi yayinda driver daya rakosu ta shiga cikin gidan ya sanar da aunty Fiddausi karasowarsu..Jim kadan ya dawo yace musu tace su shiga ciki..basuyi musu ba suka fita daga mota dukabi bayanshi har zuwa cikin gidan..a main parlor suka zauna shi Kuma driver ya fita..bayan few minutes Billy ta shigo parlon rikeda tray din su juice a hannunta..ta karaso ciki ta ajiye tray akan table snn ta zauna kan one seater tana dan sunkuyar da kanta tace"barkanku da zuwa"..Nur ya fara cewa"barka Bilkisu..ya jikin Lamidon?.."tace"da sauki sosai"..juyawa tayi tana kallon Bobby ya sakar mata murmushi..murmushin itama ta saki snn ta shiga gaishesu..bayan sun gaisa ta mike ta bar parlon can sai gata ta sake dawowa da wasu dirka dirkan warmers ta ajiye snn ta sake komawa ta kawo wasu ta kuma ajiyewa snn ta wuce don kiran aunty Fiddausi..tare suka dawo da ita parlon ta karaso ciki ta zauna opposite to them tana dubansu da murmushi sosai fuskanta tace"sannunku da hanya"..durkusawa sukayi har kasa suka gaisheta dukda ko zata girmesu ba irin sosai din nan ba..aunty Fiddausi ta amsa gaisuwarsu tana murmushi bayan sun zauna tace"ku fara cin abinci sai raka ku inda take..bacci ma takeyi don batasan da zuwanku ba"..tana rufe baki Bobby da ya matsu ya sanyata Idonshi yace"am..ni bana tareda yunwa aunty"..dan murmushi aunty Fiddausi ta saki kafin tace ma Billy"ki rakashi dakinda take"..ba musu Billy ta amsa da toh ta juya ta kama hanyar dakin Bobby yabi bayanta yayinda oga Nuruddeen ya baje ya shiga bama cikinshi haqqinshi don a cewarshi soyayyar Bobby bazai hanashi cin abinci ba shikam...Billy na nuna mashi dakin ta juya ta bar wurin yayinda shi Kuma ya tura kofar dakin a hankali ya shiga da sallama...wani irin sanyi dakin ya dauka sosai sbd ac dake kure ita Kuma tana kwance can karshen gado ta kudundune kanta cikin blanket tana bacci peacefully kmr ba mara lafia ba..a hankali ta shiga takawa har zuwa bakin gadon ya tsaya yana kallon yanda tayi coiling kanta a kan gadon kmr ba mutum ba..stool ya janyo ya zauna dab da gadon yana facing dinta kafin yakai hannunshi a hankali ya janye blanket din..da uban gashin kanta dake tsefe ya fara cin karo sai kuma cute and beautiful face dinta da yaga har wani glowing yakeyi a Idonshi..baisan ko sbd ya jima bai ganta bane amma yaga ta Kara kyau sosai ba kadan ba...janye blanket din yayi daidai stomach dinta sai yaga tayi motsi tareda jan blanket din zata sake rufewa dashi yayi saurin janyeshi tareda daukan remote ya kashe air condition din dakin gaba daya...kallonta yacigaba dayi yanajin wani abu mai matukar karfi yana kokarin fizgarshi zuwa gareta baisan lokacinda ya lumshe ido tareda sunkuyawa yayi pecking forehead dinta ba..hannunta ya kama ya rike yana cigaba da kallonta kmr Wanda keson gano wani abun..left hand dinshi da yake free ya mika yayi feeling temperature dinta yaji jikinta normal babu wani zafi kawai sai ya saki wani hadadden murmushi yana shafa gemu zuwa sajen fuskanshi Kuma still hannunshi na cikin nata..a hankali ta fara motsawa sbd zafi data faraji as a result of kashe ac da yayi..lokaci daya Kuma ta bude Idonta tar tana kallonshi shima sai ya tsayar da nashi idon a kanta yana kallonta...mikewa tayi zaune da sauri tana Mirza idonta to make sure ba dreaming take ba Kuma sai taga its real ba mafarki bane..wara idon tayi da kyau tana kallonshi kallo irin na mamaki kafin tace wani abu ya rigata da fadin"ya jikinki?.."hadiye yawu tayi da sauri tana gyada kanta tace"naji..sauqi..amma ya akayi kazo nan?.."murmushi ya saki yana kallonta yace"kirana sukayi wai bakida lafia kuma kinqi yadda ayi allura and kinqi shan magani"..turo baki tayi tana hade rai lokaci guda tace"to nidai bazaka mun allura ba wlh"..murmushi yakeyi har yanxu yace"baby bakida lafia fa?.."rau rau tayi da Ido kmr zata fara kuka tace"Allah kamun allura fasawa zanyi"..daria ta bashi sosai jin abunda ta fada..ya fuskanci these days rigima takeji dashi dan abu kadan zata ce mishi fasawa zatayi..Saida ya gaji da dariarshi kafin yaja dogon hancinta yana cigaba smiling yace"da yake fasawan a hannunki yake Koh?.."turo baki tayi tace"nidai kada kamin allura dan Allah"..gyada mata kai yayi alamar bazaiyi ba..dan kura mata ido yayi for like 3 mins sai Kuma ya saki murmushi yana kallon eyeballs dinta yace"meke damunki?.."a hankali tace"fever"..tun kafin ta rufe baki ya shiga girgiza kai yana cigaba da kallonta yace"ba fever ba dai..ki fadi gaskia"..daure fuska tayi tana harare harare tace"nidai fever ne ke damuna"..shiru yayi yana kallonta kawai sai ya girgiza kai..Aysha da gaba daya ta gama tsarguwa da wnn abun nashi tace"and what does that mean?.."shoulder ya daga mata alamar nothing..da sauri tace"ban yadda ba wlh..da akwai wani abu cikin ranka"..girgiza mata kai yayi alamar ba komai ita kuma ta wani hade rai zata kwanta baisan lokacinda ya janyota jikinshi yana danne dariarshi ba..murya can kasa yace"kawai ki fadamun period kike ba sai kina wani 6oye 6oye ba mana..am ur soon to be husband"..tun kafin ya rufe baki ta daddage ta tureshi daga jikinta ta sake juyawa zata kwanta yayi saurin dawo da ita jikinshi yana cigaba da dariarshi yace"nifa bada wani abu na fada ba..am sorry"..banza tayi dashi ta shiga kokarin kwace kanta..ya dagota tareda cupping fuskanta still yana murmushi yace"bafa laifi kukayi ba ni kyautamun ma kukayi keda period din naki da kukeyin abunku tun yanxu ba sai..."bata bari ya karasa ba ta toshe mishi bakin da hannu daya tana dukan chest dinshi da dayan hannun tace"banaso..banasoo"..sake rungumeta yayi yana sakin daria sosai yace"to kuyi hakuri na dena"..sake dukan chest din nashi tayi yace"to kiyi hakuri love..am sorry ba period kike ba"..daga haka ya dagota daga jikin nahi yana kallonta da kyau yace"yanxu kici abinci sai muyi allura"..girgiza kai ta shigayi tana cewa"No pls"..da sauri yace"ohk to ki samu kici wani abu sai kisha magani"..gyada mishi Kai tayi alamar toh..shi Kuma ya mike daga inda yake zaune ya mika mata hannunshi yace"tashi muje parlor kici abinci"..girgiza kai ta sakeyi tace"rigana baida tsayi kaje zan fito"..yace"U sure?.."Kai ta gyada mishi meaning she's sure..bai sake cewa komai ba ya fita daga dakin ita Kuma ta mike da kyar ta janyo hijab ta zura snn ta shiga takawa a hankali ta fita zuwa parlon..itadai tsoronta Allah tsoronta kada yace zaiyi mata allura dan bataso wlh..haka kawai salon azo bikinta allura nayi mata ciwo.

















Rano✨





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
54
Biki ya rage sati daya Aunty Fiddausi ta tattara su gaba daya suka wuce Gombe sbd preparation na biki da zata taya yayarta...zuwa lokacin sosai amarya Aysha ta canxa tayi wani 6ul 6ul da ita kaman ba amarya ba don ba wani stress na biki data daurama kanta..duk wani abu daya kamata ayi Billy ce takeyi tareda sauran cousins dinta sai kuma Aunty Fiddausi...sbd cika fa gidansu ya farayi da mutane na nesa da suka fara zuwa Ammi tace ita da Billy suje can gidan wani small uncle dinta da bai dade da aure ba su zauna tareda sauran friends dinsu da zasuzo idan an fara biki...haka kuwa akayi suka tattara duk wani abu da sukasan zasuyi amfani dashi har a kammala biki suka wuce can gidan uncle din nata dake few houses away from nasu gidan...sun rage yawan events da suka tsara zasuyi sbd Lamido ne yace lallai lallai duk yawan events dinsu kada ya wuce kwana uku dan haka sun bar Henna Party ranar Wednesday.. Thursday Cocktail party..Friday kuma Kamu da Mother's Eve wanda Ammi ta shirya..Saturday ayi daurin Aure by 11 daga nan kuma a wuce da amarya Kano inda zasu gabatar da nasu events din a can.

Yau Tuesday tun safe sukayi shirin tafia saloon Billy na zaune parlor tana waya da Hamma bai Kai ga dawowa Gombe ba ita kuma amarya Aysha tana daki tana karasa shiryawa don su wuce saloon din da wuri..tana zaune gaban mirror tana kokarin parking gashinta kiran ango ya shigo wayarta..ajiye comb dake hannunta tayi tareda daukan wayan tana marairaicewa tayi picking tana cewa"partner dan Allah kayi hakuri mu tafi plss..wlh daga ni sai Billy zamu tafi ba wani ne zai kaimu ba"..girgiza kai Bobby yayi kmr tana gabanshi yace"baby i told u Sab is coming to take u guys ku Kara hakuri mana..ban yadda ki shiga motar wani ya fita dake ba wlh"..da mamaki sosai tace"u mean tun daga kano ka tasoshi sbd yazo ya kaimu saloon?.."girgiza kai ya sakeyi yana shafa kanshi yace"no yana Gomben dama tun jiya Mummy ta aikoshi bai dawo ba..yanxun yacemin ya fito daga gida so u guys should wait for him"..a hankali tace"partner kishinka yayi yawa mana..an kusa bikin ma bazaka dena wnn abun ba"..tun kafin ta rufe baki yace"duk abunda zaki fada ki fada amma da gaske bazan saki matata sakaka kowane Kato yana kallon min ita ba..ubangiji da kanshi yace ya tsine ma wanda bai kishin matarshi so bazan zama among wayanda tsinuwan Allah zai tabbata a kansu ba"..murmushi tayi tana girgiza kai tace"dukda haka naka yayi yawa partner..ya kamata ka rage plss"..shiru taji yayi kmr bazaiyi mgn ba sai can taji yace"kinsan wani abu?.."girgiza mishi before saying"aah"..wani munafukin murmushi ya saki yana shafa gemunshi murya can kasa yace"i can't wait to be with you..Allah kadai yasan yanda nakeji kaman in janyo Saturday ya dawo yau"..ya karasa mgn yana lumshe ido kai kace a gabanta yake..Lamido dai diff tayi tana sauraronshi jin ya fara sauka daga layi..ita ta rasa dalilinda yasa ya dawo bashida kunya yanxu..gaya mata duk maganan da yazo bakinshi yake ita ya barta da jin kunya..turo baki tayi tareda mikewa daga inda take zaune tace"nidai tafia zanyi Ammi na kirana"..da sauri yace mata"hang on plss"..shiru tayi tana sauraronshi..shi kuma ya wani kwantar da murya yace"bakice kina Sona bafa"..murmushi mai kyau ta saki tana kallon kanta ta mirror kafin a hankali tace"Partner"..murya can kasa shima yace"yes partner"..sake kashe murya tayi tana wani kashe ido cikin wani irin siga tace"Ina sonka sosai..i love u"..lumshe ido Bobby yayi yana safe chest dinshi still smiling yace"i love u more wlh..son da nake maki Allah kadai yasan amount dinshi"..har yanxu bata bar smiling ba itama tana lumshe ido..batasan why har yanxu bata gajia da sauraron words din nn nashi ba..she loves him to the extent that duk wani word da zai furta mata means the entire world to her..she loves him to the core...kafin wani cikinsu ya sake mgn kiran Ammi ya shigo wayanta..tana dubawa taga itace sai tayi saurin maidawa kunnenta tana cewa"partner excuse me plss..Ammi naga ke kira tun daxu bansan ko nemana take ba"..gyada kai yayi tareda kashe kiran ita Kuma tayi saurin daukan call din Ammi tana cewa"hello Ammi"..a fusace Ammi tace"wai zaman uban me kukeyi a gida baku fito ba tun daxu?.."da sauri tace"yi hakuri Ammi cewa yayi ya turo Sab yazo ya kaimu shiyasa bamu fito ba"..tsaki Ammi taja kafin tace"to yana zuwa ku tafi and ki tabbata kin biyo ta nan don akwai baqin da zaku gaisa dasu"..a hankali tace"to Ammi"..daga haka Ammi ta kashe wayarta ita kuma tayi saurin karasa parking gashinta ta dauki bag dinta da veil dinta a hannu ta fita daga dakin..har yanxu Billy na nan parlor suna waya da Hamma..Aysha ta karasa ciki tana yafa veil dinta akai tace"su Laila da Majnoon har yanxu ba'a gama wayan bane?.."harara Billy ta watsa mata before tace"inace kema wayan kika gamayi da Romeo dinki yanxu?.."girgiza kai Aysha tayi tana karasa veiling dinta..daidai nan Kuma kiran Sag ya shigo wayarta and ko bata dauka ba tasan karasowa yayi dan haka a hanakli ta isa inda Billy ke zaune ta fizge wayar hannunta tareda kaishi kunnenta tana cewa"Hamma a dan daga mana kafa plss..zamuje saloon"..murmushi Hamman nata ya saki tareda kashe wayarshi..Billy da already ta gama shirinta kafin ta fito ta mike tana rataya bag dinta a shoulder dinta tace"to muje amaryar proprietor"..murmushi kawai Aysha ta saki tareda juyawa suka fita daga gidan..suna fita ta hango motar Sab Parke a gefe dan haka suka nufi can direct..yana hangosu ya fito daga motar ya bude musu kofa yana kallonsu da murmushi har suka karaso..Aysha na kallonshi with a smile tace"haka nan ya tasoka daga aikinka Koh?.."girgiza kai Sabeer yayi yana murmushi shima yace"duk aikin da nake ai muhimmancinshi baikai wnn ba aunty"..murmushi ta kara saki ta shiga cikin motar Billy ma ta shiga snn shima ya zaga ya shiga ya tayar da ita suka bar wurin..Saida suka hau titi Lamido tace"dukda haka nidai banji dadin tasoka da yayi kana zaman zamanka ba..Saida fa nace mishi daga ni sai Billy zamu tafi amma bai yadda ba"..Sab dake jinjina zafin kishi irin na dan uwanshi yace"haka nan fa yake aunty..tareda wani cousin dina da zamu zo yace bai yadda in tahoda kowa ya kalleki ba shine na saukeshi a gidan Waziri nace mishi yanxu zanje in dawo"..murmushi Aysha keyi tana girgiza kai tasan halin kayanta tsaf zai aikata hakan shiyasa batayi mamaki ba..har yanxu tana murmushi tace"ni kaina kishin Partner har tsoro yake bani fa..inaga shi baiqi ace babu wanda zai sake kallona ba har karshen rayuwa"..daria Sab ya saki yana cigaba da driving dinshi yace"zai iya aikata hakan wlh"..Billy dai na zaune baya tana jin conversation dinsu..tun bata sa baki ba har daga baya itama ta shiga suka farayi da ita..bayan ya saukesu yace idan sun gama sai su kirashi ya maida su gida shi Kuma ya juya kan motarshi ya koma gidan Waziri.

Lokacin da Sab ya maidosu gida was around 3..kofar gidansu tace yayi parking sbd amsan da kiran da Ammi keyi mata tun safe dan haka daga nan sukayi sallama dashi ya wuce su kuma suka shiga cikin gidan da yake nan taf da mutane...saida suka tsaya suka gama gaishe gaishe a parlor na baqin dake ciki kafin suka wuce bedroom din Ammi..daga ita sai aunty Fiddausi a dakin sai wata cousin dinsu suna lissafa cards din mother's eve da dole Ammi tasa aka karo sbd wanda akayi da farko har ya kare..karasowa ciki sukayi suka zauna suna gaisawa dasu..cousin din Ammi mai suna Rahina tace"aah su amare an samu shigowa knn"..Lamido tayi kasa da kai tana sake gaisheta..Aunty Fiddausi ta debo cards kusan guda 40 ta mikama Billy tace"ungo wnn koda na hannunku zaku kare sai kuyi amfani dasu"..Billy tasa hannu ta amsa tana counting dinsu tace"wlh kuwa kmr kinsan wanda kika bani har sun kare"..Aunty Fiddausi tace"nasan za'ayi hakan ai shiyasa na kwasan maku wnn"..daga haka ta kwashi wasu da suka ware na 'yan uwan daddy ta fita daga dakin don kai musu nasu..Ammi ta gyara zama tana duban Aysha tace"zauna muyi mgn"..ba musu ta zauna kusa da Billy tana kallonta..daure fuska Ammi tayi tana cewa"mgn dama zanyi Miki akan African time..wlh Aysha kika sake na tara jama'a a wuri kikaje kikayi zamanki bakizo da wuri ba da sunan make up zakiga yanda zanyi dake a gidan nan..dama da wuri ku fara make up dinku don bazan dauki a 6ata mana lokaci ba kin sani"..gyada kai tayi tana dan marairaicewa tace"wlh da wuri zamu fara Ammi"..Ammi tace"good..saura kuma kiqi nutsuwa kizo kina wnn raye rayen naki da kika saba"..sake marairaicewa tayi tana duban Ammin nata bata dai ce komai ba..Ammi tace"kika wani tsareni da ido ko bakiji abunda na fada bane?.."kasa tayi da kanta kafin a hankali tace"naji..amma to Ammi nidai dan Allah kice kar asa waqoqin gwanja kinga bansan sanda zanyi rawar bafa"..rai a 6ace Ammi ke kallonta tace"qanin ubanki ne Ado Gwanjan?.."da sauri ta girgiza kai tana turo baki..Ammi tace"to kije kiyi rawar kiga idan banci mutuncinki ba..ki bar ganin aurenki za'ayi wlh idan kikayi ba daidai ba Ina iya zuwa har gidan mijin naki inyi maganinki"..har yanxun kanta na kasa tace"to kiyi hakuri"..Ammi bata sake tankata ba ta dauki wasu cards cikin wanda ke xube gabanta ta mikama Billy tace"idan Kun fita ki nemi Husna ki bata..kuma kice mata idan batayi sauri ta kawomun abunda na aiketa ba itama zataci ubanta"..murmushi Billy ta saki tareda mikewa ta amsa cards din Aysha ta mike suka fita..suna fita cousin din Ammi dake sauraron draman nasu tana daria tace"yanxu Maimuna har yanxu baki dena wnn fadan naki ba..yarinya tana amarya kin wani sanyata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login