Showing 219001 words to 222000 words out of 231169 words

Chapter 74 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9714

yayi kusada ita sosai tareda kama hannunta yace"then me kikeso?.."ta juya ta kalli su Billy taga duk hankalinsu naga abincin da sukeci snn ta dawo da idanunta gareshi tana wani hade rai tace"Custard zansha"..ya dan marairaice mata yace"amma baby custard kadai bazai rikeki ba tunda duk yau bakici abinci sosai ba"..kallonshi ta danyi yanda taga duk ya tashi hankalinshi sai ya bata tausayi dan haka ta sake janyo plate din abincin tana jujjuyawa tace"to zan faracin wnn idan mun koma sai insha custard din".. kanshi ya shiga gyada mata yana murmushi sosai yace mata"yauwa partner"..ta saki dan smile snn ta shiga cin abincin a hankali shi kuma yana aikin kallonta..ganin shi baida niyyar cin abincin ta juya tana dubanshi tace"kai bazaka ci ba?.."hannunta ya kama ya rike idanunshi a kanta yace"ni ke nakeso kici..banso kina zama da yunwa"..murmushi ta Kara saki snn ta maida plate din nan tsakiyarsu tasa mashi spoon tana cewa"to muci wnn din tare"..murmushin shima ya saki bayan yayi pecking hannunta snn ya dauki spoon ya shiga cin abincin shima..daurewa kawai take tana turawa amma ko kadan batajin dadinshi a bakinta..bayan sun kammala suka dawo parlor inda Mummy ke zaune tana jiransu suka dan taba hira bayan sunyi sallahn isha yace su mike su koma gida..Husna dai tace"Uncle Bobby nidai zan kwana a nan tareda Miemie"..Bobby na murmushi yace"to Mummy kinada baqi knn"..Mummy tace"aikam kin kyauta Asma'u dan da baki Fadi haka ba nasan ita kanta Miemien cewa zatayi a can zata kwana"..Aysha dai kunyarta takeji yasa ta kasa cewa komai..bayan sun mata sallama suka koma gidan tareda Billy da Yusra..duk yanda taso ya bari taje inda su Billy hanata yayi sbd fever dake sake sauko mata..dole tayi sallama dasu ta dawo dakinshi inda yake nan zaune yana jiranta...custard din da tace tanaso yaje ya dama ya kawo mata tasha sosai snn ya rage mata kayan jikinta suka kwanta..can dare ta tashi tana ta kwarara amai don kaf abincin da taci saida ta amayar dashi..duk hankalinshi ya tashi haka ya gyara wurin tsaf snn yayi mata wanka ya dawo da ita ya kwantar a kan gadon tanata faman kuka kmr karamar yarinya..hankalinshi yakai kololuwar tashi gaba daya ya rasa inda zaisa kanshi yaji dadi..da dadewa dama yasan zaisha fama da ita musamman daya fuskanci dan banzan raki ne da ita..dan ciwo karami da bai taka Kara ya karya bama langwai take mashi balle laulayi da kowa yasan yanda yake da cin rai musamman daya kasance shi ba wani specific magani yake dashi ba dole saidai mutum yayi hakuri har lokacin tafiarshi yayi..duk yanda yaso ko black tea ne tasha kasa Sha tayi wai idan tasha zatayi amai haka nan ya hakura ya kyaleta bayan ta gama kukan bacci yayi gaba da ita.

Wahsegari ta tashi normal babu fever as usual dama kullum kalau take tashi da safe sai dare yake sake dawowa..da kanshi ya mata wanka ya bata one of three quarters dinshi ta saka da wata shirt dinta dake dakin nashi snn ta fito zuwa wurin su Billy..da mamakinta sai taga suma sun tashi itada Yusra har ma sunyi wanka sun shirya..zama tayi suka fara labari kafin Kuma daga baya tace su shiga kitchen su fara girki don yau dai ba bazata bar Mummy da sawa ayi musu girki ba tunda ta samu sauki.. tare suka shiga kitchen din da Billy Yusra kuma suka barta a nan parlor tana kallon cartoon..Billy ce ta shiga peeling Irish yayinda ita kuma Aysha ta dauko chicken a freezer ta shiga gyarawa zatayi musu pepper soup..karnin Kazan na bugun hancinta taji wani irin amai ya taso mata aikuwa ta matsa jikin sink da sauri ta shiga kwarara aman..Billy ta bar peeling Irish da takeyi ta karasa nan kusada ita tana mata sannu..bayan ta gama ta bata ruwa da kuskure bakinta snn taja stool ta zauna tana maida numfashi..Billy dake murmushi tun daxun ta karasa ta dauki Kazan ta shiga wankewa tunda ta gama gyaran tace"ohh Allah da iko yake"..a kule Lamido ta juya tana kallonta tana daure fuska tace"ban gane ba"..Billy ta gama wanke kazar tasa ruwa snn ta dora a kan gas ta zuba duk abunda ake buqata snn ta rufe tukunyar ta koma kan Irish tacigaba da ferewa ta kuma kasa dena murmushi..ganin yanda taki kulata tace"Billy wai meye haka?.."Billy tace"kici gaba da 6oyemun kinada ciki nima ramawa zanyi wlh"..shiru tayi kmr bazata ce komai ba sai kuma can tace"shi ya fada maki koh?.."Billy tace"wlh ba wanda ya fadamun..bayan duk wnn fever da amai da kikeyi still sai inyi zaune sai wani ya fadamun kinada ciki kmr dai ba health personell ba..have u forgotten am a registered midwife?.."Aysha ta dan saki murmushi tana cewa"to registered midwife munafuka"..Billy ta shiga wanke Irish data gama peeling tace"ba wani munafurci fa.. addu'a na ya karbu knn"..tana rufe baki Aysha tace"wlh ke kimamun baki muguwa.. inshaAllah kema yanda bakinki ya kamani sai nawa ya kamaki..ke preterm ma zaki haifa inshallah 7 months da biki kawai saidai Muji ance kin haihu"..Billy ta kwashe daria tana cewa"aikam bakinki saidai ya tsaya kanki inshaAllah"..Lamido tace"idan na fara labour zan roka maki tunda kinsan ance adduar mace mai labour karbabbiya ce"..Billy tasa daria..haka dau suka cigaba da aikinsu suna hira kmr wanda sukayi jiya bai ishesu ba..Bobby dai ko da ya fito yana jiyo sautin dariarta a kitchen tayi Hamdala dan yasan tunda yaji haka sauki ya samu knn.

Karfe 11 suka gama shiryawa bayan sunyi sallama da Mummy suka shiga mota zuwa gidan aunty sumy kmr yanda Aysha ta dage ma Bobby kan sai ya kaisu sun gaisheta..ita da Billy da Yusra suna motarshi yayinda Husna da Miemie suke motar Nur da sai wani giggiwa yake yau gashi ga pretty a mota daya..sai kuma abun ya hadu da Husna mai shegen rawar kai itama aikam baka sukaita zuba masa iyayi yana kallonsu da murmushi yana kuma mamakin wnn iyayin da suke dashi a shekarun nan nasu...aunty sumy ta karbesu hannu bibbiyu ta dinga nan nan dasu kmr ta maidasu ciki don so..sosai suma suka ware suka saki jiki da ita suka kwashi labari don itama ba daga baya ba wajen surutu..Nur ne kadai ya kasa sakewa duk yajishi a takure sbd nauyinta da yakeji yayinda ita kuma ko a jikinta don batasan ma yanayi ba..Bobby banda tsokanarshi ba abunda yake yana masa daria amma bai kulashi ba sbd baida lokaci tanka mashi tunda a gidan surkai yake..sun jima sosai a gidan don a nan sukayi lunch daga nan kuma suka mata sallama suka wuce bayan ta cika su Billy da gifts iri iri..basu zame ko inaba daga gidan nata sai wani park mai kyau..sunyi enjoying wajen sosai don sai after four suka bar wajen..daga nan kuma ya kaisu shopping yace kowa ta dauki abunda takeso..su Husna an samu abunda akeso nan aka shigo kwasan kaya kmr wanda zatayi changing wardrobe..Billy dai kasa daukan komai tayi sai Lamido ce ta daukan mata snn ta dauka ma Yusra..har su Ammi saida yace ayi musu tsaraba dan haka sukayi spending lokaci mai tsayi a nan cikin mall din basu gama ba..bayan sun bar wurin yanaso ya biya eatery suyi takeaway na abinci Mummy ta kira tace he shouldn't buy food that already an gama preparing musu dinner..haka suka koma gida sukayi dinner din a nan zuwa lokacin Aysha dauriya kawai take don abokin daren nata ya fara dawowa wato fever amma bata bari sun gane ba har suka gama hiransu snn suka wuce tareda Yusra da Billy kmr dai jiya Husna da Miemie Kuma suna gidan Mummy.














Rano✨





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank State...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
68
Washegari around 2 Hamma Najeeb yazo ya daukesu suka wuce bayan sunyi sallama da Mummy da kuma Aysha da taci kuka ta koshi kmr idan sun tafi bazata sake haduwa dasu ba..sosai takejin zatayi kewarsu..Mummy da Bobby sun cikasu da tsaraba sosai na abun arziki haka suka tafi suma sunajij kewarta kaman yanda itama takejin nasu..Yusra har kuka saida tayi wai zata zauna tareda Adda amma haka nan ba yanda suka iya suka rabu suna kewar juna.

Laulayi sosai Aysha ke fama dashi dan tun zazzabin yana tashi da dare har saida abun ya dawo kusan ko yaushe akwai fever jikinta ga kuma ba dama taci abinci sai ya dawo kmr zata fitar da kayan cikinta..sosai take shan wahala cikin lokaci karami ta rame tayi wani irin haske fau wanda kana gani dama zakasan ciki ne daita..Bobby kullum yana tareda ita dan zuwa yanxu ko hospital bai fiye zuwa ya dade ba sbd yanda hankalinshi bai kwanciya idan baya tareda da ita..ko abinci bata iyaci saidai taita kame Kamen kwadayi amma abincin kirki dai bazata tsaya taci ba sai idan jan ido yayi mata..sosai shima take bashi wahala dan gani yake ko ita da cikin ke jikinta bazata kaishi shan wahala ba..kullum fatanshi shida Allah ya rabata da cikin lafia don sosai ya matsu yaga ya rike da ko 'yarshi..wani lokaci sai ya zauna yayita surutu shi kadai wai babynshi yake mgn..ko Kuma yakai kunnenshi cikin nata wai yanaso ya jiyo heartbeat din babyn..sosai yake kulawa da ita da kuma cikin dake jikinta don duk wani abu da mai ciki ke buqata yana mata likewise wanda ba'a buqata ya nesanta ta dashi..lokacin da cikin ya isa antenatal da kanshi yake zuwa hospital da ita yayi mata duk wani necessary abu snn suje ayi mata duk tests daya kamata..scanning ma da kanshi yake mata don haka nan ma wani lokaci zaice suje yayi mata scanning yanason yaga ya kwanciyar babynshi yake..haushi yake bata sosai idan taga yana wnn abubuwan don gani take duk ranan da ta haihu kilan dena ma kulata zaiyi ya koma kan babynshi..tana ganin abubuwa iri iri dai akan wnn cikin ba daga Bobby ba ba kuma daga Mummy dasu Hajia Aunty Sumy ba..har kunya suke bata idan sukayi wani abu akan cikin amma su ta fuskanci ko a jikinsu..koda yake zuwa yanxu ta riga ta gama gane cewa jinin igbo dake running a jikinsu shike haifar musu da wnn rashin kunyan dan abubuwa da yawa idan sukayi saidai ta tsaya tana kallonsu tunda hausawa dai da Fulani tasan bazasu iya rabin rabin abunda sukeyi ba..tun cikin nada 3 months suka fara siyan kayan baby suna ajiyewa daga shi Bobbyn har zuwa kan su Mummy ta kasa gane Wanda zafi zakuwa da haihuwarta..yanda suke tulan kayan suna ajiyewa kai kace a kanta za'a fara haihuwa duk dunia..kulum cikin browsing unisex kayan yara suke designers masu kyau wai they don't want the baby to lack wani abu a dunia..kulawa sosai take samu ta kowane bangare amma hakan bai hanata wani lokaci ta sanyashi gaba tana kuka wai itadai ya cuceta musamman yanxu da cikin ya fara girma sai yasa mata wani irin qiba kusan duk kayanta sunyi mata kadan saidai taita fama da dagayen riguna...gashi mugun kunyar cikin takeji shiyasa ko Ammi ta kasa fadawa saida wasu sisters din daddy sukazo suka ganta da cikin shine da suka koma suka cema Ammi sai ta fara shirin tarban jika..sosai Ammi tayi mamakin wai Aysha nada ciki amma ta kasa fada mata dan dai ta Santa da rashin kunya kilan dai hankali ta farayi shiyasa ta kasa fada ma kowa kuma wai har uwar tata Fiddausi bata fadama ba lallai Aysha ta fara hankali kam..cikinta nada wata shidda aka sanya bikin Hamma da Billy four months masu zuwa aikam tasha takaici sosai wai ba'a tashi sa ranar ba saida aka daidaici lokacin haihuwarta sbd baaso taje biki..Billy taita mata daria tana tsokanarta wai Kilan lokacinda za'a fara bikin ita tana cikin labour room tana fama da kanta hakan kuma ba karamin bata ranta yakeyi ba dan har kuka saida tayi da akace four months aka saka.
Wnn knn...

Zaune take cikin parlonshi ta tasa katon warmer dake cike taf da awara a gabanta tanaci tana hadawa da uban yaji data ajiye kusada warmer din..daga ita sai wani qaton rigarshi blue daya tsaya mata iya guiwa..cikinta yana nan yayi zaune kmr yanda itama take zaune..a gefe guda kuma tv na aiki tana kallon wani series..yanda ta dukufa tanacin awaran dama kana gani zakasan ba lafia take ba dan mai lafia dai bazaiyi wnn abun ba saidai irinsu masu juna biyu..after like 7 mins Bobby ya shigo parlon hannunshi rikeda katon jug da aka zuba tamarind juice a ciki..yana zuwa ya ajiye matashi gabanta yana kallon uban yajin data ajiye gabanta yace"yanxu sake dauko yajin nan kikayi baby?.."dan marairaicewa tayi tana kallonshi tace"nifa bazan iyaci a haka ba partner"..tun kafin ta rufe baki ya dauke yajin daga gabanta yana hararanta yace"to bazaki karaci ba wlh"..kallonshi tayi da sauri tana kwabe fuska tace"dan Allah partner ka bani dan kadan zan zuba wlh"..girgiza mata kai yayi yace"No kici haka..ga tamarind din nan Mummy tayi maki"..turo baki tayi ta wani daddage ta ture warmern daga gabanta snn ta mike da tulelen cikinta a gaba ta wuce bedroom dinshi..da kallo kawai ya bita yana jinjina kokarin da maza suke da matansu masu ciki..gaba daya yanxu ta zama masifaffiya dan dan abu karami zaiyi ta haushi da fada Kai kace itace Hajia Nadia data durkusa ta haifeshi..hakan kuma bai taba damunshi ba dan yasan ba yin kanta bane condition din da take ciki ne ya haifar mata da haka..mikewa yayi shima ya dauki tamarind da sauran awaran nata ya bita dakin dashi..saida ya ajiyesu bisa table snn ya karasa kan gadon tareda dagosu gaba daya itada cikin nata ya dorasu kan laps dinshi..hawaye sosai ya gani a fuskanta nan take kuma hankalinshi ya tashi dan dunia idan akwai abunda ya tsana yanxu bai wuce wnn kukan nata ba..sam bayason gani sai yaga kmr yana affecting da ko yarshi dake cikinta..rungumeta yayi batareda damuwa da cikinta dake zungurinshi ba yace"yanxu baby sbd yajin kikemun kuka haka?..bakiso hankalina ya kwanta koh?.."hannu takai tana share hawayen tace"to ai bazan iyaci a haka ba kuma ni ban koshi ba"..nashi hannun ya mika ya karasa goge mata tears din yana cewa"banason yajin yayi affecting babyna ne ke kuma naga baki iyacin kadan ba"..kallonshi tayi hawaye na sake ciko idonta tace"ai dama baka damu daniba ni..wlh tunda na samu ciki ka dena sona"..cupping fuskanta yayi tareda manna mata peck a forehead dinta yana kallonta da murmushi yace"i love u both baby..ku biyun are my family so i love u equally"..tun bai rufe baki ba ta kwace fuskanta daga hannunshi tana sake rushewa da kuka tace"wato u love us equal..tun babyn baizo dunia ba kana cewa u love us equal then idan yazo kilan watarana cewa ma zakayi baka san wace ni ba".. Bobby couldn't help it but laugh da jin wnn mgnr nata..rungumeta yayi yana daria sosai yace"don't tell me kishi kikeyi da abunda ko dunia baizo ba"..sake daure fuska tayi tana turo baki tace"kaima ba gashi kana nuna bambanci ba"..dagota yayi ya sake cupping fuskanta yace"u don't have to be jealous baby..i love u more..my every little happiness depends on u love so i love u more..i promise i love u more"..sake turo baki tayi tareda raba jikinta da nashi tace"indai da gaske u love me more ka bani yajina in karasa cin awarata"..ba musu ya dauko yajin ya zuba mata dan kadan snn ya daukota ya ajiye kan sofa ya fara massaging legs dinta yace"to gashi nan yi sauri ki karasa ci sai ayi wanka"..bata sake cewa komai ba tacigaba da cin awaranta shi kuma yana massaging legs dinta da suke dan kumbura time to time..dan kadan ta rage cikin tulin awaran dake gabanta snn ta kora da tamarind da Mummy keyi mata kullum sbd shi kadai take iya sha..shi kuma ya dauketa suka shige bathroom.

Washegari kafin ta tashi ya fita sbd kiran da Nur keta Maka mashi wai there's emergency a college clinic kuma shi bai cikin makarantan..kafin ya fita saida ya tabbata ya ajiye mata duk wani abu da take buqata tareda dan short note snn yayi pecking forehead dinta da katon cikinta ya fita..lokacinda ta tashi was around 11 ta shiga bathroom dinshi tayi wanka snn ta fito ta shafa cream da turare ta zura jallabiyarshi ta fita..these days gaba daya kayanshi take sawa dan nata kusan duk sunyi mata kadan..riguna ya ware mata manya da jallabiyas marasu tsayi sosai ya bata yace ta dinga sawa tunda duk maternity gowns da yasa aka dinka mata bata sawa wai nauyi suke mata..tana fita parlonshi taga ya ajiye mata goruba da tsamiyar biri da shansu zame mata kullum kmr ka'ida..ta saki murmushi tareda karasawa zata dauka sai taga ya ajiye mata note a kusa dasu dan haka ta zauna snn ta dauki note din ta fara karantawa kmr haka"hey love..sorry zaki tashi baki ganni ba naje clinic ne wai there's emergency but bazan dade ba zan dawo..take care of urself and my baby for me..love u"..da murmushi sosai ta karasa karantawa snn ta dauki gorubarta ta fita main parlor tanaci..bangaren mai aikinta ta nufa tayo mata mgn snn ta dawo cikin parlon ta zauna..mai aiki na zuwa bayan ta gaisheta tace"dan Allah saude kin iya wainar flour?.."da sauri mai aikin tace"na iya Hajia"..tace"yauwa to shi nakeso kimin yanxu..akwai flour a store kar kisa kwai amma kisa attaruhu sosai yanda yajin zai fito and kisa maggi ma da yawa"..yarinyar ta amsa mata da"toh"snn ta juya zuwa kitchen ita kuma ta shiga cin goruba tana kokarin kunna tv..Kiran daddy ne ya shigo wayarta ta dauka da sauri tana cewa"daddy ina kwana"..yace"lafia lau Aysha ya jikinki?.."tace"Alhamdulillah"..yace"to Allah kara lafia ga mamanki zakuyi mgn"..daga haka daddy ya bawa Ammi wayar itama Aysha ta gaisheta ta amsa da tambayarta ya jiki..duk kunya suke bata idan suna tambayar ta ya jikin nn wlh..kawai saita dinga imagining shknn sun san yanda akayi ta samu cikin..Ammi tace"maganin nan da aka kawo kinasha yanda akace maki dai koh?.."tace"Ina sha"..Ammi tace"to kicigaba da Sha dan Allah yanda aka fada maki..amfani ne dashi sosai karkiyi wasa dashi"..kanta a kasa tace"toh Ammi..yanxu Ammi dan Allah bazaki sa baki ya barni inzo in ganku ba?.."Ammi tace"keda kike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login