Showing 186001 words to 189000 words out of 231169 words

Chapter 63 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9712

akan nata for like 3 secs snn ya janye yana sake rungumeta sosai a jikinshi...Aysha dai tsuru tayi tana rarraba ido don Allah ya gani ba karamin tsorta tayi da yanayinshi ba..yanxu ya zatayi ta fitar da kanta daga wnn cakwakiyar ne?..wani tunani ne yazo mata kuma tayi na'am dashi dan haka bata sake yunkurin kwace kanta daga jikinshi saima Kara lafewa da tayi tana lumshe Ido..lokaci mai tsaho suka dauka a haka shima idanunshi na lumshe banda Hamdala da godia wa ubangiji ba abunda yakeyi a cikin zuciyarshi..a hankali yayi breaking hug din bayan yayi pecking forehead dinta ya sake daukanta cak zuwa flat dinshi..ita da idanunta na kulle ne har suka shigo parlonshi...dan bude idon tayi a sace ta shiga karema parlon nashi kallo shima yayi mata kyau sosai daga nan Kuma ya wuce bedroom dinshi..yana shiga ya direta a kasa tareda kama lafayan dake jikinta ya warwareshi ya ajiye akan gado sai kuma ya shiga karema jikinta kallo riga da skirt din jikinta sunyi mata kyau ne sosai kuma sun amshi jikin nata..sake karasawa yayi yayi hugging dinta yana dan rocking dinsu a hankali ya sake ce mata"Mrs Bobby"..nan ma dai shiru ta sakeyi ba bakin mgn shi kuma ya sake matseta jikinshi yakai bakinshi daidai kunnenta kafin yace"matar Bobby talk to me mana..what happened to ur mouth?.."makale shoulder dinta tayi alaman she won't say a thing shima bai sake takura mata ba ya ajiyeta nan gefen bed dinshi snn ya shiga bathroom..alwala yayi ya fito snn itama yace ta shiga tayi alwala zasuyi sallah..ba musu ta shiga bathroom din itama tayi alwala ta fito..ya dauko lafayanta daya ajiye kan bed ya yafa matashi kmr hijab snn ya shimfida musu praying carpet suka tada sallah...raka'ah biyu sukayi tareda addu'o'i sosai na samun zaman lafia da kwanciyar hankali mai dorewa da kuma zuri'a mai albarka..sun dauki almost ten minutes Bobby nata kwararo addu'a kafin ya idar..yana mikewa itama ta mike tana dan kallonshi kasa kasa tace"zan..je..dakina"..murmushi ya sakar mata bayan ya mayar da praying carpets din inda suke ya kama hannunta suka fita daga dakin..main parlor suka dawo ya dauki ledan da suka shigo dashi suka karasa zuwa dinning..da kanshi yaja mata seat ta zauna shima ya zauna kusada ita snn ya bude ledan..kaza ne a ciki da yaji kayan lambu sai qamshi yake sai Kuma fresh milk mai sanyi..mikewa yayi zuwa kitchen ya dauko plate da cup snn ya sake dawowa ya zauna yayi serving dinsu..itadai tana zaune tana kallonshi batada bakin mgn...bayan ya gama da kanshi ya shiga feeding dinta tana tun nokewa ita bazata ci ba har dai ta hakura ta danci Wanda zataci don tasan ba saurara mata zaiyi ba idan ba cin tayi ba..ya dauki fresh milk din shima ya bata a baki tasha dan kadan tace ya isheta snn ya daidaita saitin inda tasa bakinta shima yasa nashi bakin a wurin ya karasa shanye Wanda ta rage..suna hada ido ta wani dauke kai tana turo baki shi kuma ya kashe mata ido daya yana murmushi...Kazan yaci dan kadan shima snn yasa sauran a fridge ya maida plate da cup din kitchen snn ya sake kama hannunta suka bar dinning din..ganin hanyar bedrooms dinta suka nufa har wani ajiyar zucia ta sauke shidai baice mata komai ba har suka shiga dakinda aka ajiyeta daxu..direct closet dinta ya bude ya shiga yana duba kayan da zai dauka mata na bacci bai gani ba dan haka ya fito zuwa inda aka jere boxes din lefenta ya shiga budesu har yaci karo da wanda ke cike da undies da sleeping dress ya dauki box din gaba daya snn ya sake kama hannunta suka koma flat dinshi..ajiye box din yayi a kasa snn ya zauna zai fara bude box din yaga yanda tayi wani tsaye a gabanshi tana turo baki sai ya mike yana sakin smile ya karasa inda take..hannu yakai ya zame dankwalin dake kanta nan take black long hair dinta ya bayyana..lumshe ido yayi tareda kai hannu yana shafa gashin nata yana sauke numfashi..he just every single thing about this girl..he loves everything she have..saida ya gama shafa gashin nata to his satisfaction snn ya jata ya zaunar da ita gefen gado yana ce mata"sit right here"..murguda baki tayi kmr zatasa kuka tace mishi"kaina a bude fa"..dungure mata kai yayi yana dan hararanta yace"see you..sai kace ba kece mai son fitoda gashin naki waje ba"..daure fuska tayi tana sake turo baki shi kuma ya saki murmushi gamida girgiza yace"continue pouting those lips na kusa nayi maganinsu ai"..da sauri ta maida bakin nata tana sake daure fuska..shi Kuma bai sake bi ta kanta ba ya bude box din ya shiga neman mata kayan da zatasa..duk wanda ya dauko tana gani har wani dagashi yake yana kare musu kallo snn ya ajiye..saida ya daga almost ten duk baiga Wanda yayi mashi ba ita kuma tana zaune tana kallon ikon Allah..wani taga ya dauko red din riga mai hannun vest da bombshort mai net a jiki..wani murmushi ya saki yana sake jujjuya kayan ya kare musu kallo snn ya mika mata tun ma kafin yace wani abu cikin daure fuska tace"na rantse da girman Allah bazan sa wnn ba"..kallonta kawai ya tsaya yi kmr ta kwashe da daria amma ya dake..irin wnn shiga masallaci haka..wnn rantsuwa da wuri tunma kafin yace tasa din..baiyi mata musu ba ya maidasu ciki snn ya dauko wata purple din riga batada tsayi sosai itama kuma hannun vest ne da ita amma jikinta is very cotton unlike wancan da yake net..sake Mika mata rigan yayi shima bai jira tayi mgn ba yace"na rantse da girman Allah sai kin sa wnn rigan"..kallonshi kawai takeyi fuskan nan a kwabe da gani kiris take jira ta sakar masa kuka amma batayi ba..karban rigan tayi ta ajiye tana wani kawar da kai gefe shidai baice mata komai ba ya tattara sauran kayan ya maidasu cikin box din snn rufe ya daukeshi ya ajiye a gefe..tana ganin ya fara rage kayan jikinshi ta wani runtse ido wai bazata gani ba..murmushi kawai yake mata har ya gama cire kayanshi ya fada bathroom..brush kadai yayi ya fito don already yayi wanka kafin ya taho..yana fitowa itama yace taje tayi brush ta sako rigan nata ta fito..batayi musu ba ta mike ta fada bathroom shi kuma ya dauko wani three quarter fari yasa tareda singlet shima white snn ya hau gado ya kwanta yana jiran fitowarta yau ko pyjamas bazai sanya ba shi Kam..a hakanshi zai kwana yanda zaifi jin dadin baccin sosai...Aysha kuwa tunda ta gama brush din ta sanya rigar taga gaba daya tsayinta ko guiwarta bai kai ba sai ta nemi wuri ta zauna tana tunanin yanda za'ayi ta bari ya ganta da wnn rigan..idan ba iskanci ba dama taya zai wani bata wnn dan iskan rigan yace tasaka kuma a gabanshi..sai yanxu take sake tabbatar da mgnr da ake cewa gaba daya maza basuda kunya..Saida ta kwashi kusan minti goma a na ciki kmr daga sama kawai taga mutumi a gabanta ya dauketa cak ya fita bathroom din da ita..runtse Ido tayi tana karanta innalillahi a cikin ranta har taji ya kwantar da ita akan gado shima ya kwanta tareda switching off bedside lamp dakin yayi duhu don already ya kashe sauran bulbs din..hannunshi yakai tareda janyota ya hada da jikinshi tanajin yanda yake sauke ajiyar zucia a jere a jere itadai tayi mukus kmr mara lafia..cikin wata irin murya da bata sanshi dashi ba taji yana cewa"ki tayani addu'a rabbi ya bani ikon kulawa dake gwargwadon iyawata..Allah ya bani hakuri da juriar zama tare dake ba tareda cutarwa ba..Allah yasa na iya rike amanarki da iyayenki suka bani snn kada Allah ya kawo ranar da ni Attahiru zan juya maki baya ko in dena sonki ko inyi maki wani abu dazai sosa zuciarki..kada Allah ya nunamin wnn ranar har karshen rayuwata"..gaba daya shiru sukayi na dan lokaci kafin yacigaba da cewa"Ina sonki sosai Aysher kuma har dunia ya tashi nasan bazan ta6a son wata kmr yanda nake sonki ba..I love u so much and Ina godia wa Allah daya bani ke a matsayin mata..inshaAllah bazakiyi regretting aurena ba har abada"..hawaye taji sun wanke mata fuska har batasan lokacinda ta rungumeshi ba itama kawai sai sheshshekar kuka take tama kasa bude baki tayi mgn..son da yake mata da dadewa tasan mai girma ne and wnn maganganun da yayi sai taji tausayinshi ya kamata sosai..taji bazata iya aikata abunda ta shirya zata aikata don hanashi kasancewa da ita ba instead zata hakura ta kuma jure duk wani abu da zaizo mata dashi..she's going to be strong for him ko don sbd yanda yake azabtuwa da soyayyarta...lokaci mai tsaho ta dauka tana kuka a jikinshi Wanda har hakan ya fara ta6a zuciarshi..a hankali ya dago fuskanta yana kallo kafin daga bisani ya lumshe ido tareda hade bakinshi da nata..aikuwa diff ta hadiye kukan ta shiga rarraba idanu kmr shege a rabon gado...lokaci mai tsayi suka dauka a haka kafin ya zame bakinshi a hankali tareda sake hadeta da jikinshi yana shafa gashin kanta muryanshi can kasa yace mata"sleep"..da sauri da kulle idanuwanta tana sake lafewa a jikin nashi gabanta yana cigaba da faduwa har wani zazza6i taji yana neman kamata..addu'a kawai take Allah ya bata karfin halin da zata iya juran duk abunda zaizo mata dashi don sosai take a tsorace musamman da Billy ta sake tsoratar da ita daxu...shi kuma gani yayi bai kamata ya aikata wani abu a yau din ba sbd yasan gobe gidan zai cika taf da mutane sai kuma body temperature dinta da yaji yayi rising kmr fever zai rufeta..a hankali yaja duvet ya lullu6esu dashi snn yayi addu'a ya shafa mata shima ya shafa a jikinshi daga haka ya gyara mata kwanciya ya dora kanta a chest dinshi snn ya lumshe ido yanason bacci yazo yayi awon gaba dashi har baizo ba..har ita ta samu baccin shi nashi idanun a kekashe suke tamkar ba dare ne ba..kawai farin ciki kasancewa tareda ita ma kadai ta isa yasa bacci yayi kaura daga idanunshi..ganin da gaske ba baccin zaiyi ba sai ya kwantar da ita kan pillow a hankali ya sauka daga gadon ya shiga bathroom ya dauro alwala snn yazo ya tada sallah don ya sake nuna godia wa Allah daya cika mashi burinshi na samunta a matsayin mata.

Koda ya tashi da asuba bai tada ta ba saida yayo alwala kafin ya wuce masjid ya zauna gefen gado yana kallon cute face dinta da ko kadan baya gajia da kallonshi..hannu yakai yana shafa gashin kanta snn ya lumshe ido yayi pecking forehead dinta followed by cheeks dinta sai tip of her nose..bude Ido tayi a hankali tana kallonshi yana murmushi yace mata"it's time for subhi"..mikewa tayi zaune tana murza idonta yayinda shi kuma ya kamata suka mike tsaye snn ya jata zuwa bathroom..tap ya kunna snn ya nuna mata shi da hannunshi yana cewa"ablution"..dan bata rai tayi kafin tace"ni fitsari zanyi"..yace"kiyi mana..i didn't stop u"..yanda ta zare idanu sai kayi zaton wani mummunan sa6on yayi..shi kuma kallonta kawai yakeyi yana kunshe daria..ganin da gaske ba fitsarin zatayi ba ya fita daga bathroom din yana girgiza kai..cikin ranshi fadi yake"duk ki gama guje gujenki ne ki dawo hanya yarinya"..yana fita ta tsuguna da sauri tayi fitsarin tayi tsarki duk cikin hanzari take yi wai kar ya dawo bata gama ba..tana gamawa tayi alwala snn ta fita..a cikin dakin ta sameshi ya shimfida mata carpet yana rikeda zundumemen hijab dinta da yaje bedroom dinta ya dauko..karasawa tayi ta tsaya kan carpet din tana mika hannu nufin ya bata hijab din amma sai yaki bata instead sai matsa kusada ita tareda zura mata hijabin..kallonta yayi a hankali yace"zanje masallaci"..ta gyada mishi kai alamar toh daga haka ya fice daga dakin ita kuma ta tada sallah zatayi raka'atainul fajr kafin lokacin sallah ya karasa.

Lokacinda ya dawo already itama ta idar da nata tana addu'a dan haka ya zauna gefen gado har ta gama addu'an ta shafa snn ta mike tana ninke carpet din..mikewa yayi shima ya amsa carpet din ya karasa ninkewa ya ajiye inda yake snn ya zare mata hijabin jikinta shima ya ajiye daga haka kuma jata suka koma kan gado..idanunta a lumshe yaji tace mishi"Ina kwana"..ya saki murmushi yana kara sanyata a jikinshi yana shafa gashin kanta yace"lafia lau wife..how was ur night"..dan murmushi tayi ba tareda cewa komai ba shima kuma bai sake cewa ba ya lumshe Ido kafin bacci yazo yayi gaba dasu at once.

11:33 su Aunty Fiddausi suka shigo gidan don yi mata sallama sbd wucewa zasuyi Gombe yanxun nan..sunata kwada sallama a parlor amma tsit kmr dai ba mutane a gidan..Billy ce ta dauki waya zata kirata Aunty Amina tace ba saita kirata ba su wuce kawai idan yaso sai suyi sallama ta waya..hakan kuwa sukayi don komawa can gida sukayi nan ma sukayi sallama da Mummy da sauran yan uwanta snn suka tafi bayan an cikasu da abubuwan biki kala kala.
12 da wani abu kiran Nur ya tashesu daga baccin da suke..rai a 6ace Bobby yakai hannu ya dauko wayanshi ba tareda ko duba wanda yayi Kiran ba yayi picking tareda sakawa a kunne..on the other side Nur ya saki wani daria yana cewa"oh ni Nura..Bob i hope dai ba zuwa ka nakasta yarinyar mutane har zuwa wnn lokacin kuka kasa tashi a bacci ba"..wani tsaki da Bobby yaja ita kanta Aysha dake kwance abun saida ya bata mamaki..shi kuwa Nur bai damu da tsakin nashi ba yace"dama Mummy tace a kiraka kazo kayi sallama da masu wucewa Enugu amma idan baka gama..."Bobby bai bari ya karasa ba ya kashe wayarshi yana kara jan tsaki..wlh Nur ba karamin dan rainin hankali bane..he is freaking annoying..wall clock dake dakin ya kalla aikuwa ya wara ido ganin da gaske har 12 ya wuce yana bacci..lallai bacci kusada masoyi akwai dadi tunda gashi har hakan yasa yakai time dinda bai ta6a kaiwa yana bacci ba..ikon Allah knn...sauka yayi daga gadon da sauri ya fada bathroom shi duk a tunaninshi bacci takeyi baisan tun lokacinda ya tashi itama ta tashi ba likimo kawai tayi don batason yasan idonta biyu...wanka yayi sharp sharp ya fito zuwa closet dinshi ya saka qananun kaya ya dan shafa turarukanshi masu dadin qamshi snn ya dau key da phone dinshi ya fita zuwa gidan nasu...tana jin fitarshi ta diro daga kan gadon da sauri har zata fita sai kuma ta dawo ta gyara mishi gadon tsaf ta gyara ko ina snn ta dauko sweeper ta share dakin dukda ba wani datti yayi sosai ba...bayan ta gama ta zuba turaren wuta a burner tareda sauke duk curtains din dakin snn ta fita zuwa nata dakin..nan ma dan gyare gyaren tayi snn ta cire rigar jikinta ta fada bathroom..brush ta farayi snn tayi wanka tareda alwala ta fito daure towel data gani a bayin...saida ta karasa tayi locking kofarta da key snn ta iya zama nan gaban mirror ta shiga shafe shafenta..tana gamawa ta dauko fitted gown na wani lace silver da black ta saka snn ta kafa daurin dankwalinta ya zauna daram ko make up artist sai haka..gashin nan an fito dashi ta kasa sai daukan ido yake sbd kyallin da yake..powder ta shafa a fuska da eye pencil a ido sai farin wet lips lips dinta..nan take ta fito a amarya sak son kowa kin wanda ya rasa..ta dauki turare duk tabi jikinta dashi snn ta dauki waya ta zauna tana kiran Billy..tana dauka ne take sanar da ita cewa sunzo yi mata sallama bata tashi a bacci ba don haka sun wuce Gombe..ranta duk ya 6aci ta kira Aunty Fiddausi kmr zatasa kuka tace"yanxu Aunty shine kuka tafi ko sallama bamuyi ba?.."Aunty Fiddausi tace"to munzo baku tashi daga bacci ba Aysha ya kikeso ayi?..kiyi hakuri kiyi ai bada jimawa ba zan dawo..Allah ya baku zaman lafia da yara na gari"..turo baki tayi kmr tana ganinta tace"nidai Aunty da Kun kirani a waya ai zan tashi"..tsaki Aunty Fiddausi ta saki tana cewa"sbd mahaukata ne mu irinki kawai saimu hau kiranki ki baro wajen mijinki ki taho..kar ki nutsu kicigaba da wnn shashancin wlh dawowan da nace zanyi ma sai in fasa"..da sauri tace"aah Aunty dan Allah kiyi hakuri plss..na dena"..daga haka bata sake cewa komai ba ta kashe wayarta tana gunguni..kawai suka wani kama hanya suka wuce ba tareda ko ganin karshe sun bari tayi musu ba...tana kokarin dialing number Ammi kiran Husna ya shigo wayar..murmushi ta saki mai kyau tareda gyara zama kafin tayi picking call din..wani ihu da Husna ta sakar mata a kunne saida ta janye wayar daga kunnenta na wucin gadi..can sai taji voice din Yusra itama tazo suna ihun tare..saida suka gama duk tana sauraronsu snn suka shiga gaisheta Husna hadda cewa"Adda ya gidan naki dan Allah..ya Proprietor..how was the first night"..banza Aysha tayi mata bata amsa ba sukaci gaba da mgn da Yusra..Husna ta kwace wayarta wai sai suje suyi mgn da wayar Ammi amma ba nata ba tunda walakanci ma take mata...ba musu kuwa ta kira wayar Ammi nan ma suka gaisa Ammi nata sake jaddada mata tayi biyayya wa mijinta snn banda sakarci itadai tana amsa mata da toh..bayan sun gama Yusra ta sake kar6an wayan sukacigaba da hiransu..inshort dai ranar ba wanda batayi mgn dashi ba a gida don hatta Hamma da daddy duk saida ta kira ta gaishesu..bayan sun gama wayan kuma ta mike ta fita parlor don yunwan da taji tanaji.















Rano✨




Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07064800556.
58
Tana fita parlor taci karo da Nusaiba yarinyar aunty Munubiya da Miemie sun shigo dauke da basket din abinci...tana ganinsu ta saki murmushi tareda karasowa tana kallonsu tace"sannunku"..Miemie ce tace"yauwa aunty amarya..ga abinci Mummy tace mu kawo"..karasawa dinning sukayi suka ajiye abincin snn suka dawo parlon suna gaisheta ta amsa da fara'a sosai don da gaske taji dadin ganinsu at least dai bazata yini ita kadai ba...dinning din suka wuce gaba daya don cewa tayi su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login