Showing 117001 words to 120000 words out of 231169 words
banaso"...kallon Nur Bobby yayi cikin sigar ka taimaka mun...Nur ya saki murmushi tareda karasawa inda take yace"Lamido ba allura za'a maki bafa..duba kafan kawai za'ayi ko da akwai matsala ta ciki"..yana rufe baki tace"nidai dan Allah banason zuwa sir..bazan iya takawa ba"..kallonta kawai yakeyi rungume da hannu ita kuma sai tayi kasa da ido tana goge tears dinta tace"to zanje..amma dan Allah banda allura wlh ciwo yakemun"..Nur yace"baza'ayi maki allura ba inshaAllah..yanzu matron da Billy zasu taimaka maki ki mike tunda bazai iya tafiya ba"..batace komai ba sai hawaye data cigaba dayi..tsoro takeji kar suje suyi mata allura ita dai..a muguntan Dr Bobby tasan wlh da kyar idan baiyi mata allura ba tunda baida imani...Billy ce ta dauko hijab ta saka mata snn suka kama hannunta itada matron din don fita da ita waje...taku daya ta iyayi ta saki wani kara da saida Bobby yaji shi har cikin zuciyarshi...nan da nan saiga hawaye a fuskanta ta shiga kokarin durkushewa nan kasa sbd azabar zafi da taji har cikin bones dinta...girgiza kai kawai take murya can kasa tace"bazan iyaba"..kallonta duk suka tsaya yi harda Bobby da yakejin kukan nata har can cikin ranshi..ji yake kamar yaje ya sungumeta yayi waje da ita amma ba halin yin haka...sai da kyar da taimakon Billy suka samu ta yadda ta mike suka riketa har zuwa inda sukaƙi parking...kafin su karasa Nur ya bude musu kofa dan haka suna zuwa suka Sanya ta ciki Billy ma ta shiga suma suka shiga snn Nur ya tada motar suka tafi...Bobby dake zaune front seat jingina kanshi jikin kujeran yayi tareda lumshe idanu..jin kukan nan nata yakeyi har cikin zuciyarshi yayinda wani irin zafi da kunchi suke sake rufe shi..Allah kadai yasan yanda yakeji nunawa ne kawai baiyi amma yana cikin matsala gagaruma ma kuwa...kasa cigaba da hakuri yayi ya juya yana kallon yanda take rikeda kafan tana kuka..murya can kasa yace"kukan ya isa haka dan girman Allah"..ko kulashi ba tayi ba ta cigaba da kukan ta...a takai ce har suka isa Freedom bata bar kuka ba...Bobby duk ya rikice ya tasa inda zai tsoma kanshi yaji dadi..Nur na gama parking duk suka bude mota suka fito banda ita da ko motsawa ba tayi ba...Billy ta zagayo ta bude mata kofa tareda kamo hannunta tace"ki daure mu karasa ciki"..rike hannun nata tayi snn ta sakko da kafan a hankali sai kuma ta gagara mikewa..Nur dai na tsaye yana kallonsu shi kuma Bobby ganin sake bata musu lokacin take kawai ya karasa wurin baiyi wata wata ba ya daga ta cak ya nufi cikin asibitin da ita..sai ihu taka tana ita ya sauketa amma ko tanka mata baiyi ba har ya karasa office dinshi su Billy na binsu a baya..Nur ya karasa ya bude office din suka shiga..kai tsaye ya direta kan gadon dake nan cikin office din fuskan nan a daure kamar bai taba dariya ba...yana ajiye ta ya bude wani drawer ya dakko wani muscle pain killer ya ajiye kan trolley snn ya shiga bathroom ya zuba ruwa cikin wani bowl mai zurfi ya hada da towel dan karami snn ya dawo dakin..daga Nur har Billy kallonshi kawai suke ba wanda yace kala..kujera ya janyo ya zauna nan kusada ita snn ya zaka towel din cikin lukewarm watare daya debo ya matseshi snn ya kama kafan nata ya rikeshi da kyau yanda bazata iya kwacewa ba ya shiga danna mata towel din a wurin..banda ihu da musu mutsu ba abunda take amma ta kasa kwace kafar daga hannunshi sbd rikon da yayi mata bana wasa bane..danna mata kawai yakeyi ba tareda ko kallonta yayi ba sbd gudun abunda hakan zai haifar mashi..yasan idan ba haka yayi mata ba ba bari zata yi ayi mata abunda ya dace ba and Allah ya sani bazai taba samun sukuni ba idan ba gani yayi kafan nata ya warke gaba daya ba..idan zai biye ta zuciyarshi nan ma bazai iya mata abunda ya dace ba kuma shidai akan ya bari wani ya tabata gwara shi yayi mata duk abun daya kama ta idan yaso daga baya sai yayi aikin rarrashi dan dai yasan rigima ne zai sashi kamar ba gobe..tunda ya fara bai saurara mata ba sai da ya tabbatar kafar ya gasu snn ya kyaleta..ya dauki towel da bowl din ya maida su bathroom ya dawo sai kuma ya dauki maganin da zai shafa mata a kafar yana kallonta..kuka take yi sosai har numfashinta na seizing kamar zai dauke..ga wani uban zufa data hada sharkaf kaman wanda aka gasata a oven..tausayinta yaji ya kama shi ganin yanda take kuka yasan dole zataji zafi amma ya zaiyi?..shima ba a son ranshi yayi mata haka ba babu yanda zaiyi ne kawai..janyo kujeran yayi a hankali ya zauna still yana kallonta duk sai yaji ya kasa aikata komai..juyawa yayi ya kalli Nur wai ko zai taimaka mashi amma sai yaga shi dariya ma yakeyi abun shi sai kuma ya juya ya fita daga office din...Billy ma ba tayi wata wata ba tabi bayanshi don Allah ya gani bazata iya zama nan ciki ba...juyawa yayi yana kallonta suna hada ido ya dauke nashi da sauri ya shiga matsa maganin a hannunshi..sam baison wnn raunin dake kokarin dakatar dashi ne...runtse ido yayi ya bude snn yayi watsi da raunin dake dake kunno mishi kai ya kamo kafan nata a hankali zai shafa maganin kawai sai yaji ta kanakameshi tana sakin wani marayan kuka..lumshe ido yayi yanajin wani irin yanayi a cikin jikinshi...wani irin weird feeling da bai taba tsintan kanshi ciki ba..cikin muryanta da bai fita sosai tace"sir dan Allah..dan Annabi kayi hakuri"...lumshe ido ya sakeyi yanajin zuciyarshi na wani irin tattarewa ya cunkushe can wuri daya yana bugawa da mugun karfi...a hankali yakai hannunshi ya zagaye bayanta dasu bakinshi saitin kunnenta yace"am..sorry..plss"gyada kai kawai takeyi tana cigaba da kuka tace"toh bazaka shafamin ba koh?.."dagota yayi daga jikinshi yayi cupping fuskanta yana kallon cikin idonta yace"hakan bazai yiwu ba Aysher..kiyi hakuri a shafa maki ko yayane zakiji sauki"..girgiza kai ta shiga yi tana cigaba da hawaye tace"dan girman Allah No..mutuwa za.."bata karasa ba ya rufe mata bakin yana girgiza kai duk ya gama goge maganin hannun nashi a jikinta...kamata yayi ya kwantar da ita kan gadon snn ya sake matsa maganin a hannu yayi saurin kama kafar ya shiga murzawa a hankali..banda kuka da ihu ba abunda Lamido take har wani shidewa take sbd azaba shi kuma bai saurara mata ba saida ya tabata maganin ya shiga ciki snn ya ajiye kafar..har yanzu kuka takeyi tana sauke ajiyar zuciya shi kuma ya kama hannunta a hankali ya sake cewa"am..so..sorry love"..ko sauraranshi ba tayi ba ta kwace hannunta tana cigaba da kuka shi kuma yayi tagumi kawai yana kallonta..Allah kadai yasan yanda kukan nan nata ke daga hankalinshi..ita kanta da tasan yanda yakeji idan tanayi da batayi ba ko dan sbd shi...haka yayita kallonta tana kuka da yayi yunkurin taimaka mata zatace bataso..duk tabi ta sake daga mishi hankali da kukan nata..saida bacci ya dauketa snn ya sauke ajiyar zuciya..mikewa yayi daga inda yake zaune ya leka ya tabbatar baccin tayi da gaske snn ya gyara mata kwanciya a hankali yanda bazata tashi ba..lumshe ido yayi yakai lips dinshi forehead dinta ya manna mata peck a hankali murya can kasa yace"get well soon love..i love you"..daga haka ya gyara mata kafar snn ya janyo kujeran dab da ita ya zauna tareda rike hannunta cikin nashi ya dora kanshi gefen gadon shima daga haka bacci ya sadado yayi awon gaba dashi.
Nur na barin office din dama kai tsaye inda ya ajiye motarshi ya nufa ya bude ya shiga ciki sai ga Billy itama ta karaso ta dan langabe kai tace"sir nima ka ajiyeni hostel plss"..kallonta yayi kafin yace"why?..bazaki bari ku koma tareba?.."da sauri tace"nasan proprietor zai dawo da ita sir dan Allah ka mai dani"..bai sake cewa komai ba ya bude mata motar yace"to shigo"..ba musu ta shiga ciki Nur ya tayar da motar suka fita daga asibitin.
Karfe sha daya da kusan rabi Lamido ta shiga bude idonta a hankali har ta waresu fes akan Bobby da har yanzun kanshi ke kife nan kusada ita yana nashi baccin..zare idanun tayi da kyau tana kallonshi da mamaki ganin ya wani kwakwume mata hannu ya rike cikin nashi..daddagewa tayi ta kwace hannun nata tana zabga masa harara kamar idonta zasu fadi kasa..daidai lokacin shima ya farka tareda dago kanshi a hankali sai yaci karo da nata idon tana hararanshi...baice komai ba ya mike da sauri ya fada bathroom..wanko face dinshi yayi ya fito sai yaga ta hade kai da gwuiwa kamar zatayi kuka...da sauri ya karasa inda take ya zauna nan gefen gadon yana dubanta a hankali yace"what again?.."dagowa tayi tana kallonshi fuska daure tace"ni ka mai dani hostel"..kallonta ya tsaya yi for some secs kafin ya hada hannayenshi waje daya in a pleading tone yace"nace fa am sorry..da gaske bazan kara ba kiyi hakuri plss"..batace komai ba sai juya mishi baya da tayi zata fara hawaye yace"idan Allah noo..please am sorry..ki yafemin"..goge hawayen tayi kafin ta juyo ba tareda ta kalleshi ba tace"to ka mai dani hostel nidai"..yace"zakiyi hakuri ki dena fushi?.."gyada mashi kai tayi..da sauri yace"thank u so much"..tana turo baki tace"kuma kada ka sake tabani nidai"..yace"ban karawa inshaAllah..ki tayani da addu'a"..da mamaki ta kalleshi tace"addu'an me?.."shiru kawai yayi yana kallonta dan baisan yaushe mgnr ya fito ba..a hankali yace"kafan yayi sauki?.."still kai ta daga mishi tana cigaba da turo baki shi kuma sai yayi kasake yana kallonta kaman wani soko..kallonta yakeyi full of love and affection..yarinyar na burgeshi fiyeda tunanin mai karatu..komai tayi burgeshi yake sai yaga tana kyau da duk wani abu da tayi shiyasa yake kishinta sosai...a yanda yake kishinta shi ko cewa za'ayi babu wanda zai na kallonta duk dunia sai shi kadai so zaiyi amma yasan hakan ba mai yiwuwa bane...agogon hannunshi ya duba yaga its almost 12 and Allah ya sani yana tunanin yanda zai maidata hostel cikin daren nan dan yasan Nur da kyar idan ba tafiya yayi ba..dagowa tayi ta kalleshi zata sake mgn wayanshi dake cikin aljihu ya fara ringing..ya zaroshi da sauri ganin Mummy ke kira yayi picking tareda kaiwa kunne..a daya bangaren Mummy tace"kana kina Bobby?..ya jikin nata?.."yace"da sauki Mummy"..tace"ka tabbata da sauki ba wani problem din?.."yace"yes Mummy"..sai kuma ya juya yare zuwa igbo yace mata"Mummy babu mota hannuna and inaso in maidata hostel yanzu..Nur ya wuce tun daxu"..Mummy tace"saidai in turo Sab ya kawo maka..amma why not ka bari ta kwana asibitin sbd a sake tabbatar da samun saukin nata..kuma ga dare yayi"..ajiyar zucia ya sauke yana kallon Aysha da tayi masa kuri da ido tana kallonshi jin ya wani canxa yare cikin ranta tace"dan kyar idan ba gulamana yakeba wlh..inyamurin banza"..ba tareda ya dauke idonshi daga kanta ba yace"bazata yadda ba Mummy..nima kaina ba son zuwa hostel din nasu nake da daren nan ba amma idan ban maidata ba daga min hankali zata yi nasani"..shiru yaji Mummy tayi kafin can tace"ko zaka kawota nan gida ta kwana zuwa safe ka maidata hostel din?.."shirun shima yayi kamar me nazari yace"anya kuwa zata yadda Mummy?..rigima zatai tayi wlh"..dan murmushi Mummy ta saki jin abunda ya fada kafin tace"ba rigiman da zatai inshaAllah..if tana kusa ka bata wayan muyi mgn"..bai sake cewa komai ba ya mika mata wayan yana dubanta a hankali yace"My Mom..wants to..talk to u"..batayi musu ba ta karba tana turo baki tasa wayan a kunne..Mummy tace"daughter ya jikin naji?.."da sauri tayi kasa da kai kmr Mummy na ganinta tace"Mama ina yini"..Mummy daketa faman smiling tace"lafia lau daughter..ya jiki?.."tace"Alhamdulillah"..Mummy tace"MashaaAllah..dama ce mishi nayi ya kawoki gida sbd dare yayi bai kamata yaje hostel dinku yanzu ba..snn ya sake duba kafan naki to make sure ba wani problem kuma..hope bazaki ce aah ba?.."Lamido tayi shiru tana tunanin amsar da zata bata..gani tayi gwara ta kwana gidan nasu akan dai ta kwana asibiti..afterall ba daki daya zasu kwana ba dan haka bazata damu kanta ba...saida Mummy ta sake mgn snn a hankali tace"toh Mama"..Mummy tace"nagode sosai daughter Allah miki albarka..yanxun zan turo Sab da mota yazo ya dauko ku"..Aysha tace"toh"..daga haka kuma Mummy ta kashe kiran..ajiye wayar tayi tana kallonshi kama zatasa kuka tace"shine zaka hadani da mamanka koh?.."murmushi ya saki kafin a hankali yace"am sorry"..turo baki kawai tayi ba tace komai ba..shi kuma sai ya cigaba da kallonta before saying"kinci abinci?.."banza tayi mashi kamar bataji ba..ya sake cewa"Aysher am talking"..nan ma shiru ba mgn dan haka ya dan daga murya yace"Lamidooo"..juyowa tayi a fusace tana kallonshi tace"ni banaso"..kmr wani abun tausayi yace mata"am sorry tou..zakici abinci?.."ta girgiza kai alamar no snn ta sake komawa ta kwanta..shima baice mata komai ba sai kallonta kawai da yakeyi kamar yau ya fara ganinta...after like 20 minutes Sab ya iso asibitin bai shigo ciki ba ya kirashi a waya ya fada mashi ya karaso dan haka ya mike ya isa inda take bayan ya tattaro mata takalmanta dake kasa yace"get dawn mu tafi..ya iso"..ba tace komai ba ta sauka daga gadon ta zura takalmanta snn ta shiga takawa a hankali sbd zafi da taji kafan na mata..daxun da yake kwance take sai bataji ciwon komai ba amma yanxu zafi takeji sosai saidai bai kai na daxun ba tunda tana dan iya takawa...ita ta wuce gaba Bobby na binta a baya har suka fita waje..ko yaya ta danyi kwakwaran mosti sai yaga kaman faduwa zatayi bai dai yi kokarin riketa ba har suka iso parking lot..Sab na hangosu ya fito ya bude musu motar..tana karasowa ya nuna mata front seat yana fadin"sannu"..wani harara Bobby ya sakar masa kafin ya bude back seat ya zurata ciki shi kuma ya shiga front seat din Sab dake murmushi ya shiga driver seat snn ya tayar da motar suka tafi...baya cikakken minti biyu bai juya ya kalleta ba..gaba daya hankali da zuciyarshi suna gareta..gani yake kmr wani abu zai faru da ita idan baya gani shiyasa yake juyawa akayi akayi..Sab dai driving dinshi yakeyi amma a karon farko yau yaga wani irin canji tattare da yayan nashi kuma dukda Mummy bata sanar dashi wacece Lamido a wurinshi ba shi ya gama tabbatarwa kanshi matsayinta sbd wnn special attension da Bobby yake bata bana wasa bane..ba ko wane ordinary mutum ake bama wnn attension din ba sai mutumin da ake mutuwa so da kauna shi kuma ya tabbata Uncle Bobby son yarinyar nan yake...haka har suka karasa gida ba wanda yace tak a cikinsu sai Bobby daketa faman juyawa yana ganin halinda take ciki sai kace wadda take labour...Sab na gama parking ya bude mota ya fita shima Bobby ya fita snn ya zagaye ya bude mata kofa yana dubanta a hankali yace"to sauko"..ba musu ta fito daga motar tana wani dangale kafa kmr mai karaya a jiki..taku daya biyu tayi sai ta koma da sauri ta zauna cikin motar da bai riga rufe kofar ba tana girgiza kai idonta har sun ciko da hawaye tace"bazan iyaba"..kallonta kawai Bobby keyi yana mamakin taki irin nata..durkusawa yayi nan inda kafan nata yake yana kallo shidai baiga wani alamun har yanzu yana ciwo ba tsabar langwai ne kawai irin nata..shi baisan yanda za'ayi duk ranar da akace ga Lamido a labour room ba..kilan saita daga hankalin kowa kafin ta haihu..tunanin haka ya sashi sakin murmushin da bai shirya masa ba kafin ya kama kafan a hankali ya shiga tofa mata addu'a akai ita kuma ta wani lumshe ido tana jin abunda yakeyi...saida ya dauki almost 5 mins yana mata addu'a a kafar kafin ya gama..ya ajiye kafar tareda mikewa yana dubanta yace"to yanxun ki gwada mu gani nasan zaki iya"..ba tace komai ba ta sake sauka daga motar ta shiga takawa a hankali kmr mara laka a jiki..shi kuwa murmushi kawai yakeyi yana bin bayanta cikin ranshi yana jinjina tsananin raki irin nata..yasan da baiyi mata yanda yayi daxun ba da wlh haka zatayi ta zama kafar yana sake rurucewa shi kuma tana daga mashi hankali amma da bai bari raunin da yake dashi yayi tasiri a kanshi ba yayi mata abunda ya kama ta ai gashi yanzu har ta mike tana taka kafar...har suka shiga parlor bai dena kallon yanda take tafia yana sakin murmushi ba..Mummy da Anty Sumy dake zaman jiransu a parlor suna ganinsu duk suka mike aunty Sumy tayi saurin kamota ta karaso cikin parlorn da ita tana cewa"sannu Aysha"..Mummy ma bayan sun zauna tace"sannu daughter"..murmushi kawai Aysha tayi tareda dan dukawa tace"Mama ina yini"..Mummy tayi saurin mikar da ita tana fadin"lafia lau..ya jikin maki?.."kai a kasa tace"naji sauki"..Mummy tace"toh Allah ya kara sauki"..tace"Ameen"..sai kuma ta juya tana gaishe da aunty Sumy..itama ta ansa da ta bayanta ya jiki tace da sauki..Bobby dai na zaune yana kallonsu feeling relieved sbd ganin da gaske jikin nata yayi sauki..shi kanshi yafi son ta kwana a nan din yanda ko wani matsalan zai tashi cikin dare bazai rasa abunda zaiyi ba unlike in tana hostel da bai zama lallai ma yasan halin da take ciki ba..Mummy ce ta dubeshi ganin yanda yake smiling tace"ya jikin naka kaina?.."murmushi kawai ya kara saki maimakon ya amsa mata sai cewa yayi"Mummy ba taci abinci ba"..yana rufe baki Lamido tace"banajin yunwa fa"..Mummy tace"ya kamata kici wani abu kafin ki kwanta..Sumayya shiga kitchen ki hada mata ko tea ne tasha bari na shiga da ita ciki tayi wanka"..Anty Sumy ta mike zuwa kitchen ita kuma Mummy ta kama hannun Aysha suka nufi flat dinta...other bedroom dinta da ba amfani takeyi dashi ba ta shiga da ita ta ajiyeta kan gado ita kuma ta shiga bathroom ta hada mata ruwa mai dan zafi ta fito mata dasu towel da komai da zatai amfani dashi snn ta fito tana dubana tace"toh shiga kiyi wanka zakiji dadin jikin ki"..ba tace komai ba ta mike zuwa bathroom din Mummy tabita da kallo tana murmushi..zuwa yanxu ta tabbatar ita din farin cikin Bobby ce shiyasa a kullum addu'anta bai wuce Allah ya karkato da hankalinta gareshi ba...tana kokarin fita daga sakin aunty Sumy ta shigo da tea da omalet ta ajiye sai kuma ga Bobbyn nan shima ya shigo hankalinshi kan Mummy yace"Mummy batada kayan sawa