Showing 87001 words to 90000 words out of 231169 words
zabga mai harara ta baya..wnn dalilin yasa da yawa daga 'yan class dinsu ke zargin akwai wani abu tsakaninsu wasu kuma sunyi zaton dan uwanta ne kamar yanda idan aka tambayeta sai tace"dan uwan daddyna ne fa".
Yau Thursday tun 3 Sa'eed ya daukesu zuwa gidan lalle sbd gobe zasu wuce kaduna bikin Lubna...amarya sai damunsu take da kira wai suyi sauri suje itafa ba wasu qawaye gareta ba...basu samu gamawa da gidan lallen ba sai after six dan haka Sa'eed na daukosu direct ya kama hanyan college dinsu..a hanya yaketa kallon lallen da Aysha ke nuna mashi tana fadin"besty lalle na yayi kyau koh?.."Sa'eed dake driving dinshi yace"sosai ma kuwa besty..aike din dama mai kyau ce so duk wani abu da zakiyi dole ma yayi suiting dinki"...Lamido ta saki murmushi tanata blushing tace"godia nake besty nah..shiyasa nake sonka wlh..besty bansan wane irin missing dinka zamuyi idan ka tafi ba"..ta karasa kmr zatasa kuka...shi kuma dan murmushi ya saki ba tareda yace komai ba don kuwa shi kanshi yasan dole yaji a jikinshi duk ranan da akace ya bar FCNM..yasan duk lokacinda yaso ganinsu bazaiyi mishi wahala ba ya dauko mota ya taho kano amma yasan bazai ta6a samun enough time dasu kaman yanda suke samu a yanxu ba...bayason zancen yayi tsayi sbd karyar mishi da zuciya suke dan haka ya kallo Billy ta mirror yana sakin smile yace"Billy banji kince komai ba"...harara mai kyau ya samu daga wurinta hakan kuma ya bashi daria sosai dama yasan abunda zatayi knn..shi tunda yake bai ta6a ganin wanda abun harara bai mata kadan kaman Hajia Bilkisu ba..ya tabbata zaiyi missing dinta fiyeda tunaninshi sbd wnn draman dake tsakaninsu...har suka karasa hostel ba wanda ya sake cewa komai a cikinsu..suna zuwa ya saukesu sukayi ciki shi kuma ya juya kan motarshi ya koma gida.
Washegari suna room dinsu sunata faman hada kaya a akwati yau ko makarantan bazasu shiga ba sbd da wuri zasu wuce...Aysha nata kiciniyar kulle akwatin da suka cikashi 6am da kaya kaman wanda zasuyi shekara a kaduna yayinda Bilkisu ke zaune gefen bed dinta ta zuba uban tagumi tana tunani..kamar daga sama taji tace"Lamido nifa har yanxu tsoro nakeji wlh..ina tsoron wani abu ya samemu a hanya bayan ko gida basu san zamuje kaduna ba"..tsaki Lamido ta saki tana cigaba da sabgar gabanta tace"matsalana da Billy dawo da mgn wlh...tun jiyafa muka gama mgnr nan na fada maki wlh kika sake gida sukaji zancen tafiyar nan bazasu bari muje ba kuma dai kinga idan mukayi haka bamuma Lubna adalci ba tunda da kunnenki dai kikaji tace batada qawaye sai mu..and koba wnn ba ko don besty bai kamata muki zuwa bikin nan ba nasan in Allah ya yadda lafia zamuje mu dawo lafia kawai dan kinsama ranki abun ne amma inshaAllah lafia zamu dawo kuma ba tareda kowa ya sani ba"...gyada kai Billy tayi cikeda gamsuwa dan har wani ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake cewa"to Proprietor kuma fa?..did u tell him?.."da sauri Aysha ta shiga girgiza kai tace"waye ya aikeni in fada mishi salon yace babu inda zamuje knn..kema dai kinsanshi Billy wlh indai ya samu labari bazai bari ba"..Billy tace"amma kina ganin baza'a samu matsala ba?..ina nufin zai iya yuwa har muje mu dawo baiyi noticing ba?.."Aysha na gyada kai tace"of course mana..ai kinsan ba kullum yake zuwa makaranta ba gobe ne kawai mu kuma monday inshaAllah zamu dawo so he won't know in Allah ya yadda"..gyada kai kawai Billy tayi saidai har yanxun cikin zuciyarta tanajin tsoro..har mamakin yanda ita Aysha bata damu ba take sai wani shiri takeyi tanajin dadi zataje garinda bata ta6a zuwa ba..tsakaninta da kaduna saidai ta wuceshi idan zasuje Abuja amma bata ta6a shigan garin ba.
Karfe 10 da wani abu suka kama hanyan kd...ita da Billy ne sai wani cousin din Sa'eed suka tafi gaba daya a motar Sa'eed din...ko a hanya Billy hankalinta ba kwance yake ba dan koya taji sun shiga gargada zata hau sallallami tana zare idanu wai a tunaninta ko hatsari ne zai ritsa dasu.😂
Basu samu isa kaduna da wuri ba sbd holdups da sukayita cin karo dasu a hanya sai kuma shi kanshi hanyan da ba wani kyawu kwarai ne dashi ba...lokacin da suka shigo kd was after one sosai dan har wasu masallatai sun fara sallahn jumu'a...kai tsaye unguwansu ya wuce dasu bayan ya kira Lubna ta shaida mishi cewa tana gidan wani uncle dinsu dake nan kusada gidan nasu...saida ya isa har kofar gidan snn ya sake kiranta nan da nan kuwa sai gata ta fito tana ganinsu ta daka tsalle ta wani cacimesu sai kace ba amarya...bayan sun gama cacime cacimensu suka karasa cikin gidan Sa'eed yabisu da kayansu ciki snn ya fito zuwa gidansu don yaje ya shirya sharp sharp ya wuce masallaci don ana idar da sallahn jumu'a za'a daura aure.
Suna shiga ciki Lubna ta kaisu suka gaisa da matar gidan snn ta jasu zuwa dakinda take ita kadai din da gaske ba wasu qawayen kirki gareta ba...mai make up na zaune tana jiranta tun daxu akaso farawa tace sai sunzo tukun za'a fara...zaunawa tayi aka fara mai aikin gidan kuma ta kawo masu abinci da drinks bayan sun gabatar da sallah suka zauna suka faraci...ko kafin a gama mata make up sun gama dan haka kowacce ta mike ta fara shiryawa don 'yan daurin aure suna gab da dawowa.
Tare suka shiga gidan gaba daya su ukun bayan an gama cancada ma amarya kwalliyarta...Sa'eed da kanshi ya kaisu suka gaisa da Mom dinshi dukda taron jama'a dake gidan...daga nan kuma angwaye sukazo aka shiga daukan hotuna...su Lamido sai iyayi akeyi to abun nema ya samu...sai bayan sallahn asr suka koma can gidan uncle din amarya tareda few daga cikin friends dinta...karfe takwas na dare aka fara tafiya dinner...sudai suna tareda amarya tace qafarta qafarsu shi kuma Sa'eed yace lallai saidai ya tafi dasu..haka sukaita fafatawa daga karshe dai dole Lubna tayi hakuri ya wuce dasu bayan sun gama shiryawa...suna sanye cikin lace dinsu sea green iri daya duk cikinsu ba wadda tayi make up amma fadan kyawun da sukayi is a waste of time...tun daga mota Aysha ta dauko wayanta ta fara musu snap kala kala wani suyi gaba daya su ukun wani itada Billy wani kuma itada besty...koda suka isa hall din dinner ma cigaba da gashi sukayi...basu bar nan wurinda suke ba saida amarya da ango suka karaso...bayan an gama tsara masu shiga dasu Billy taja baya zatayi musu video Lamido kuma as usual tana sahun farko na wanda zasuyi rawa...ana sakar musu kida suka fara takawa zuwa ciki..Billy dai na gaba tana tafiya da baya baya tanata daukan video a wayanta...har suka raka bride and groom mazauninsu bata dena dauka ba...Aysha kuma bayan amarya da ango sun zauna ta nufi table din da ta hangesu zaune..videos din Billy ta hau nuna mata suna daria..Sa'eed ya kalli yanda take rawa yace"besty knn..na rasa wane irin soyayya ke tsakaninki da rawa wlh"...murguda mishi baki tayi batace komai ba...a takaice kafin a bar wajen dinner Aysha tayi rawa har jikinta saida ya gaya mata...pictures da videos kuwa tasha su a wajen Billy har ma da wanda bai kamata ba...saida suka koma gida suka nutsu kowa yayi shirin kwanciya snn Aysha tayi selecting wasu daga pics da videos da sukayi tayi posting a status dinta bayan tayi blocking duk wani wanda tasan idan ya gani labarin zai iya isa ga parents dinta...tana gamawa da whatsapp ta shiga instagram nan ma tayi posting snn ta kira babynta a waya sukasha hira abunsu..suna gamawa kuma bacci yayi awon gaba da ita.
Kano...
Tun safe Bobby ya shigo College dukda cewa saturday ne koda ya shigo bai samu zama ba don meeting suka shiga da staff bayan sun fito shi da Nur suka sake zama da wasu masu fili da yakeso ya siya a kusada college din daga nan kuma suka shiga hostel so gaba daya bai samu zama ba saida suka dawo daga sallahn jumu'a...yana shiga office driver ya kawo lunch daga gida snn ya fita...baa jima ba kuma sai ga Nur ya shigo..tare sukaci abincin a nan bayan sun gama ya kira driver ya tafi da ragowan shi kuma ya zaro phone dinshi ya shiga whatsapp sbd tun safe bai duba messages dinshi ba...reply ya farayi duk wani message mai muhimmanci yayi replying har zai ajiye wayan sai kuma ya fasa ya fara duba status..he is not a fan of viewing or uploading status amma yau haka nan yaji he should just check yaga what people are posting...na aunty sumy ya fara dubawa yaga picture dinshi ne a farko sai na ilham sai kuma na Sab da Miemie a hade...daga nata ya duba na Nur yaga pictures da Public Relation Officer na college din yayi musu daxu during meeting da sukayi ne duk yayi posting..dan ta6e baki yayi snn ya sake yin gaba har zai bude na wani colleague dinshi Dr Michael sai kuma ya fasa sbd ganin sunanta da yayi cikin jerin wanda sukayi posting...ba tareda tunanin komai ba ya danna sunanta nan take kuma picture din farko ya bayyana..ita kadaice a pic din tayi daria both dimples dinta sun fito..wani irin abu mai nauyi yaji yazo ya tokareshi a throat..dannewa yayi ya wuce gaba sai yaga itada Billy suna kallon juna still suna daria har dimples dinta sun fito...wnn karon zafi ya faraji all over his body ganin again ko mayafi babu a jikinta and ta fito da gashinta waje as usual..the next one kuma su uku ne a jiki ta turo bak tana kokarin sanya glasses dinta Billy kuma nayi mata mgn Sa'eed yayi musu selfie..na gaba kuma video ne ita kadai tanata dirkan rawa Billy tayi mata...sbd tsabar 6acin rai baisan lokacin da ya buga table dake ganashi ya furta"what the hell"da mugun karfi ba...daga shi kuma sai another video data daukesu su uku sunata murmushi sun sanya Sa'eed a tsakiya sai wanda aka daukesu tareda amarya da ango...haka dai yayita binsu daya bayan daya yana gani har saida ya gama gani tsaf snn ya ajiye wayar kan table ya dafe kanshi da both hands dinshi...Nur da tunda yaji abunda ya fada dazu ya dago yana kallonshi amma sai yaga all attension dinshi yanaga wayanshi yace"lafia dai?.."banza Bobby yayi dashi yana dafe da kanshi...wani irin zafi yakeji tun daga cikin zuciya zuwa gangar jikinshi..shidai ya rasa wace irin fitinanniyar yarinyace ita?..baisan wane irin rashin ji gareta ba?..yanxu kuma fisabilillahi ina taje sukayi wann pictures haka?..sbd tsabar batada hankali har rawa taje tayi a bainar jama'a..yasan kusan duk wanda ke wurin ya gama ganinta kilan ma baza'a rasa wanda yace yana sonta ba...tunanin hakan yasa yaji wani irin abu mai nauyi yazo ya tsaya mishi a kahon zuci...numfashi ma da kyar yake yinsa sbd azaba..shidai yasan Lamido idan ba nutsuwa tayi ba tana iya haifar mashi da ciwon zuciya watarana sbd abubuwan nan da yakeji a kanta sun fara wuce tunaninshi...duk wani jarumta da karfin halinshi na yaga ya 6oye abunda yakeji sbd Nur dake zaune wurin kasawa yayi...wani irin tari ya farayi sosai yana dafe da chest dinshi..Nur ya mike daga inda yake da sauri ya dauko ruwa daga fridge ya mika mishi yana cewa"sannu..have this zakaji sauki"...baiyi masa musu ba ya amsa ruwan dan shi kanshi yasan yanada buqatan duk wani abu mai sanyi a halin yanxu sbd turirin dake fita daga cikin zuciyarshi...tunda ya kafa goran ruwan a baki bai sauke ba saida ya shanyeshi..Nur dai na tsaye yana kallonshi har yaga ya dan samu nutsuwa snn ya zauna nan kusa dashi yace"mene wai..meka gani ya tayar maka da hankali haka?.."girgiza kai kawai Bobby yayi don baijin zai iya bude baki yayi mgn a halin da yake ciki...hannu Nur yakai ya dauki wayan nashi sai yaga sunan Lamido a jerin status da yayi viewing...bai tsaya wata wata ba shima ya shiga ya fara gani..saida ya gama tsaf snn ya dago yana kallon Bobby da har yanxu idanunshi ke lumshe yana dafe da head dinshi yace"so kishi ne ya motsa knn?.."wani irin kallo ya watsa masa kafin ya sake maida idonshi ya rufe...Nur ya fashe da daria yana cewa"idan ba kishi ba me kakeyi Dr Bobby?..you better wake up wlh"..ya karasa yana sake kwashewa da daria...Bobby dai diff yayi yana sake jin 6acin ranshi na karuwa...a fusace ya nunashi da yatsa yace"how dare you zakazo ka sani a gaba kanamin daria?..are u madd?.."ya karasa mgn da wani irin ihuu da saida Nur ya dora hannu a kunnenshi...bayan ya gama dariyarshi yace"continue deceiving urself kaji?..just keep on denying the fact that u love her..idan bakayi wasa ba kana zaune zata auri wani and ba yanda ka iya"...tun bai karasa ba Bobby ya sake buga table dake gabashi cikin karajii yace"how dare u?..how dare u talk to me like this?..nina fada maka ina sonta?.."gigiza kai Nur ya sakeyi yana shafa gemu cikin shakiyanci yace"har yanxu baka wahala ba shiyasa kake wnn kumfan bakin..idan kaji wuya da kanka zakazo ka sameni kayi kasa da voice dinka kace Nur i don't know what to do plss help me..bansan yaushe na fara son yarinyar nan Lamido take ko Gidado?..".Ya karasa mgnr yana wani ta6e baki exactly irin yanda Bobbyn keyi kafin ya sake fashewa da daria...qala Bobby bai iya cewa ba ya mike ya kwashi wayoyinshi ya fice daga office din..idan ya tsaya ya tabbata za'a iya taruwa azo kallonsu don yanda zuciyarshi ke a kusa yana iya kwada mashi mari wlh..kawai takaici yakeji na wnn pictures da tayi posting ?..is she mad or something?..kwata kwata bata san kishin kanta ba..wai ma ina sukaje har sukayi pictures din at the first place?..yana buqatan ya kirata amma a wnn lokacin idan ya kirata kilan zaginta kawai zaiyi sbd yanda yakeji...kai tsaye motanshi ya nufa driver ya bude mishi ya shiga snn shima ya shiga suka fice daga makarantan..dama duk abubuwan da suka kawoshi college din ya gama..rabon zaiga wnn bakin cikin nema kila ya zaunar dashi.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
28
Kai tsaye gida driver ya nufa dashi..suna isa ya bude mota ya fita zuwa ciki..yayi sa'a ba kowa central parlor dan haka ya wuce flat dinshi..yana shiga ya ajiye wayoyinshi gefen gado ya shiga rage kayan jikinshi sbd azabar zafi da yakeji cox ba zuciyanshi kadai ke mashi zafi harda ilahirin jikinshi...saida ya tabbata ya cire komai shorts kawai ya bari da singlet snn ya shiga bathroom ya sakar ma kanshi ruwan sanyi duk a kokarinshi na ganin ya dena feeling zafin da yakeji amma a banza...saida ya kwashe almost 30 mins bayi yana abu daya kafin ya fito daure da towel yana goge gashin kanshi...turare kadai ya isa fesawa ya shiga closet ya sako amrless da three quarter snn yazo ya dauki one of wayoyinshi dake zube nan kan bed din nashi ya ya zauna yana kokarin kiranta..if u see how he's frowning his face zakayi tunanin bai ta6a yin daria ba..he looks more angry than ever...kiran na shiga amma har ya gama ringing bata dauka ba saida ya sake kira ta daga tana wani tattaro duk nutsuwarta tace"Sir good evening?.."bai amsa mata ba sai cewa yayi"where are u?.."shiru ta danyi tana tunanin dalilin tambayar sai kuma tace"Sir banji me kace ba"...yace"i said where are u now?.."Aysha ta hadiye wani yawu praying Allah yasa ba asirinta ne ya tonu ba tace"sir..ina..hostel..mana..bacci nake daka kira shiyasa ban dauka ba"...dukda halinda yake ciki saida ya saki murmushi ganin raina mashi hankali zatayi yace"oh really?..kina hostel right?.."cikin dakiya tace"ehh.."yace"then come outside gani nan zuwa hostel din naku yanxun nan"..zaro ido Aysha tayi tana dafe chest dinta tace"na shiga uku"..Bobby da yaji sarai abunda ta fada yace"ki fito waje yanxun nan am coming right away"..da sauri tace mishi"sir dan muhammadu rasulillahi kayi hakuri..tsakanina da Allah bana cikin hostel yanxu haka?.."kai tsaye ya sake fadin"then ina kikaje?.."wani yawu ta sake hadiya kafin tace"gidan biki"..Bobby yayi shiru yana sauraronta baisan mema zaice mata ba...so yake ya sauke mata kwando kwando na rashin hankalin da tayi amma yafiso ya ganta a gabanshi tukun...ita kuma jin yanda yayi shiru sai ta sakeyin kasa da murya tace"sir please!.."ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"kina dawowa ki sameni office tunda ke bakida hankali?..kuma kika bari na sake kiranki zakiga abunda zai faru?.."hawaye sosai suka ciko idanun Aysha tace"sir nifa gaba daya bana gari"..wnn karon shine ya zaro eyes dinshi tamkar tana gabanshi yace"ban gane bakya gari ba..explain urself"..murya can kasa yaji tace"muna kaduna"..ya bude baki zai kwaso masifa kawai yaji diff ta kashe wayarta...Bobby yabi wayarshi da kallo yana mamaki..sake dialing yayi yaji ta kashe wayan gaba daya nan take ya runtse ido yanajin zafin da yakeji yana sake karuwa...nan take zazza6i yace salamu alaikum..can saiga ciwon kai da jiri duk sun dirar masa at once..har wani irin sanyi yana kadashi ga temperature dinshi da yayi rising...da kyar ya iya daga legs dinshi ya dora kan gadon snn ya kwanta a hankali ya lullu6e da duvet..lokaci daya yaji kaman an kanainayeshi ya kasa koda daga finger dinshi..sake runtse ido yayi yana mamakin yanda duk ciwon suka saukan mishi at once..few minutes ago baijin komai ba in banda slight headache da 6acin rai amma yanxun ji yake ko mikewa tsaye bazai iya yi ba sbd ciwo...koda yake ba abun mamaki bane dan yanxu zakaga mutum lafia qalau anjima kadan ace maka ya mutu so wnn ba komai bane daga cikin qudurar ubangiji...jikinshi har shivering ya fara gashi ko kwakwaran motsi bai iya yi balle ya tashi ya kashe acn da yake zaton ita ke kara mashi sanyin da yakeji...su Mummy kam ba wanda yasan ya dawo a cikinsu don time din da ya shigo bai hadu da kowa ba dan haka yamma nayi suka shirya Sab ya fita kaisu unguwa a motan Mummyn...basu suka dawo gidan ba sai after magrib sai a nan ne Mummy ta fara mamakin rashin dawowarshi har yanxu sbd yace mata yau ko Hospital bazai shiga ba yanaso ya huta...ganin har anyi sallahn isha tara na