Showing 162001 words to 165000 words out of 231169 words
fiyeda yanda yake son kanshi..labari sosai Aysha ke bata tana yi tana blushing ita kanta mamakin yanda farat daya ya mamaye ilahirin zuciyarta take..ko daxu da safe bataji wnn feeling din game dashi ba amma yanxu gasu nan sai rushing sukeyi zuwa heart dinta kmr zasu fasa ta..so sosai taji tana mashi kusan fiyeda wanda tayi ma Professor Ahmad...saida ta gama labarinta tsaf Billy ta dauki waya tana searching contact din Sa'eed tace"Sa'eed needs to hear this..i cant believe Lamido is in love with Proprietor..what a miracle!.."
Jama'a biki dai ya kusa sbd haka kowa ya fara shiri zamuje har Gombe mu gwangwaje💃🏻💃🏻💃🏻
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
50
Soyayya mai karfi ya shiga tsakaninsu tun daga wnn ranan..Lamido har mamakin yanda take mugun sonshi take..she loves him to the moon and back kmr yanda yake fada mata..kawai gani take babu macen da ta kaita sa'a data sameshi..yana sonta sosai and ya iya kula da mace sosai ba kadan ba..yanda yake treating nata yasa ko kusa bataso taga wata ta ra6eshi don yanxun zasu samu matsala..kulawa takeyi da abunta yanda ya kamata don da gaske bazata so ta rasashi ko tayi sharing dinshi da wata ba..duk wani abu da tasan bayaso ta bar yinshi wanda yakeso kuma tanayi don ta faranta mishi..sbd tsabar nutsuwa yanxu su Lamido kullum hijab ake sawa babba idan an shigo school ta cire..tana sonshi sosai kusan duk wanda ke tareda ita sun san da haka ga kuma kishi da take dashi don akwai ranar da kiri kiri tace bazai duba wata mata ba wai tunda ta shigo sai kallonshi takeyi..haka nan ya hakura bai dubatan ba saida ta bar office yasa aka sake kiranta..farin ciki sosai yake ciki na samun soyayyarta da yayi shiyasa har kullum bazai gaji da yima Allah godia ba...before su gaka Clinical Posting kusan yan asibitin kadan ne basu san Dr Bobby zai auri Lamido ba sbd yanda suke nuna tsantsar caring wa junansu is something else..wani lokaci kota rigashi tashi bata tafia har saiya gama da patients dinshi snn ya maidata hostel..abun nasu is so so interesting sai ma wanda ya gani..a haka har suka kammala posting suka koma makaranta.
A hankali ta turo office dinshi ta shiga fuskan nan ba fus ganin yana tareda secretary dinshi da kuma wata da bata san wacece ba a office din..sake tamke fuska tayi ta karasa ciki rungume da hannayenta ta karasa ciki..tunda ya dago idonshi ya kalleta yasan akwai daru yau..yanda ta hade ran nan yasan drama ne zasuyi shi ba karami ba..File dake hannunshi ya mikawa matar dake gabanshi tareda sallamarta yace suje zai sake namants..ba musu suka bar office din Lamido ta shiga karasowa ciki har yanxun fuskan nan ba sarari..tsayawa tayi gaban desk dinshi tana mishi kallon tuhuma tace"who are they?.."dan wara ido yayi yana kokarin danne daria yace"secretary dina ce baki gane ba kuma?.."yana rufe baki tace"to na meye zasu wani shigo office dinka su zauna?.."kallonta kawai yake yana kunshe daria yace"to yi hakuri"..harara ta watsa mashi mai kyau tana sake dinke fuska tace"Kuma dayar hadda wani zuwa da dingilallen skirt..nidai bana so kana tara irin wayan nan mutanen a office dinka bakasan 'yan iska bane koh?.."yana kallonta yace"baby ba tarasu nakeyi bafa..bakiga aiki ne ya kawosu ba?.."sake rungume hannu tayi ta zauna tana turo baki tace"nidai banaso..dama da aiki suke fakewa suzo suyita kallonka mana"..daria sosai ya saki jin kalamanta..har gobe wani extraordinary farin ciki yakeji idan yaga tana kishinshi haka..abun na qayatar dashi sosai..yanxu matsalanshi daya shine bikinsu da akace dole saita gama makaranta za'ayi..waziri da kanshi yace bazai ma jema da Lamido mgnr ba sbd yasan amincewa zaiyi bayan kuma ba haka sukaso ba..kokarin dakatar da dariyarshi yayi yana kallon yanda saura kiris ta fashe ya kama hannunta yace"to kiyi hakuri baby insha Allah bazasu sake zuwa ba..babu mai sake kallon miki ni kinji"..baki ta murguda tana hararanshi shi kuma yacigaba da kallonta full of affection yace mata"C'mon smile mana..da gaske sun dena zuwa daga yau and ko suna zuwa ma babu ruwana dasu you'll always be my one and only woman..baby I love u so so very much..i love u alot"..murmushi itama ta saki dimples dinta suka fito sai wani blushing take tace"nima da gaske Ina sonka..ban ta6a son wani namiji kaman yanda nake sonka ba Allah..i love u sosai"..gyara zama yayi yana marairaice mata yace"yanxu ya mgnr mu na daxu?.."itama marairaicewa tayi kafin tace"Sir ni bazan iyaba"..tun kafin ta karasa ta katseta da fadin"i told u ki bar kirana da sir din nan bakiji koh..am not ur sir for God's sake am ur partner..ur life partner so please ki bar kirana da wnn sir din is so irritating"..murmushi ta saki tana kallonshi ta wani kashe murya tana karkata kai tace"can i call u partner then?.."murmushi ya saki shima yana kallon eyeballs dinta yace"U can call me anything amma banda sir"..yana rufe baki tace"alright then daga yau ka zama partner kuma kaima dole kace mun partner"..makale mata shoulder dinshi yayi yace"No u are my baby..yanxun enough talking about that..ya mgnr mu na daxu?.."sake langabewa tayi tace"partner bazan iya bafa..kawai sai inje incema Lamido ayimun aure kafin na gama school"..tasowa yayi daga inda yake ya dawo kusada ita ya zauna suna facing din juna yace mata"partner yanxu bazaki tausaymin ba?..for how many months kikeso muyita zama a haka for God's sake..if ke zaki iya jurewa ni bazan iya ba pls..na gaji da zama wothout u i want to get married"..baki ta rufe tana daria tace"partner rashin kunya fa"..yace"ba wani rashin kunya am saying the truth..ke baki ganin kokarina ma?.."..kama hannunshi tayi tana kallonshi in a pleading tone tace"nidai kayi hakuri dan Allah..bazan iya ba"..hannunshi ya zame daga nata tareda mikewa ya koma seat dinshi..kawai bazata gane bane shi kadai yasan halinda yake ciki..idan saita gama makaranta nan da almost four months fa ake mgn..dole ma yasan matakinda zai dauka gaskia..ita Mummy da anyi mgn kullum sai tace bai gama gidanshi ba amma yanxu ai ya gama gidan nashi tunda dama fininshing kadai ya rage to me ake jira kuma idan dai baso suke another sugar daddy yazo ya sake mishi gaba da ita ba..marairaicewa ta sakeyi itama kafin tayi mgn Nur ya shigo office din da files a hannunshi..yana ganinta nan zaune yayi wani saurin juya baya kmr wanda yaga abun kunya yace"A'uzubillahi Subhanallahi na shigo at the wrong time"..wani kallo Bobby ya bishi dashi yanajin kmr yaje ya rufeshi da duka..Lamido dai na zaune tana daria dan da gaske draman dake tsakaninshi da abokin nashi ba karamin daria yake bata ba..sake juyowa Nur yayi yana kallon Bobby da wani shegen smile yace"sorry for the interruption guys..will come back some later"..har ya juya zai fita Aysha tace"Sir ka dawo plss..dama ni tafia zanyi"..tana rufe baki Bobby yace"you won't go anywhere until we finished our discussion"..kallonshi tayi taga ya hade giran sama dana kasa dan haka bata sake mgn ba ta gyara zama tana kallonsu..ta fuskanci shima ba karamin rigimamme bane wlh..at times ma sai taga kmr yafita rigima..juyawa yayi ga Nur da har yanxun yake tsaye rikeda files a hannu shi bai shigo ciki ba kuma bai koma waje ba..saida ya sakar mashi wani harara kafin yace"if u like ka karaso muyi abunda zamuyi as u can see ba zaman banza nakeyi ba"..da sauri Nur yace"ni din banza ince kana zaman banza bayan da idona naga babban aikin da kakeyi..ai ka wuce a kiraka da mai zaman banxa mr romeo"..sake daure fuska Bobby yayi baice mishi komai ba har ya karaso seat dake opposite to her ya zauna ita dai kanta na kasa sai ji tayi gogan nata yace ta koma kan sofa ta jirasu..dan dagowa tayi ta kalleshi tace"sir please..sorry i mean partner please inje anjima sai in dawo"..kallonta yayi yana jajjada mata ki dawo fa da idanunshi..murmushi ta saki tareda gyada kai hadi da lumshe ido meaning she will definitely come back..daga haka tayi sallama da Nur ta bar office din..tana fita Nur ya sauke wani ajiyar zucia yana shafa gemunshi yace"muma dai muzo mu fara love din nan..very soon zakaji nima na hau network wlh..bazanyita zama kuna kasheni da salon love dinku ba kaida Lamido"..harara Bobby ya watsa mashi kafin yace"abunda ya kawoka knn dama?.."girgiza kai Nur yayi tareda daukan files daya shigo dasu ya mika masa ya fara dubawa..shi Kuma Nur banda kallonshi yana murmushi ba abunda yakeyi..mamaki sosai yake na yanda abokinshi ya zama mastern soyayya kmr dai ba shine da yake cewa bazai iya soyayya da diyar kowa ba wai it's a waste of time and resources..yanxun sai gashi tsumu tsumu yana soyayya da Lamido kmr ba Dr Bobby ba shiyasa har kullum bazai dena mamakin yanda ta shigo rayuwarshi farat daya kuma ta canxa mishi ita ba.
Da dare ya shigo parlon Mummy cikin wani baqin yadi daya haska skin dinshi sosai sai baza qamshi yake abunshi...Mummy da aunty sumy na zaune sai faman listing abubuwan da zasu fara siya na lefe suke don shirye shirye sosai sukeyi na biki da baifi saura few months ba..ya karaso ciki ya zauna yana kallon list din da suke yace"Mummy har yanxu list din bai kare bane?.."Mummy tace"ai list bazai kare ba Bobby kasan sha'ani irin wnn wahala ne dashi..idan ba list din akayi ba sai kaga anxo an manta da wasu abun ba'a siyo ba"..dakatawa tayi tareda dagowa tana kallonshi kafin tacigaba"wait..tun yaushe ma nace ka kawota inason mgn da ita kaki?.."shafa kanshi yayi yace"Mummy ba laifina bane bafa..wai kunya takeji bazata iya zuwa ba"..girgiza Kai Mummy tayi tace"to zan kirata da kaina in fada mata"..mikewa yayi ya zuba hannunshi cikin aljihu yace"zan dan fita Mummy"..Mummy tace"to a dawo lafia"..aunty sumy dake ta sauraronsu tun daxun tace"duk wnn wankan nata ne knn?.."dan 6ata rai yayi yana kallonta yace"ke waya fada maki haka?..ni ba wurinta zanje ba"..aunty sumy ta dago tana kallonshi da murmushi tace"ai ba zama zanyi har sai kazo kace aunty na tafi wajen Lamido snn zan gane wajenta zakaje ba"..zuyawa tayi tana duban Mummy tace"dan Allah Mummy baki lura duk yasa manyan kaya wajenta yake zuwa ba?.."dagowa Mummy tayi tana murmushi tace"nima dai na lura Sumayya..ni bansan yaushe ma ya fara sa manyan kaya ba shida kullum cikin suits yake kaman ba bahaushe ba"..Mummy na rufe baki Bobby daketa faman smiling ya dan kwabe face dinshi yace"Mummy ni ba bahaushe bane mana..am Igbo"..hararanshi Mummy tayi tace"for where?..kai bafulatani ne"..aunty sumy tace"rabu dashi Mummy..kaje ka fadawa Aysha haka kaga idan bata fasa aurenka ba"..murmushi yake yana girgiza kai yace"nasan maganinki ai..babansu Miemie kawai zan kira ince ya dawo daga England ya daukeki ku koma gidanku tunda takura mana kikeyi"..daria kawai tasa tacigaba da aikin gabanta jin ya ambaci baban su Miemie..Mummy ma bata sake mgn ba shi Kuma yayi musu sallama ya fita yanata smiling..da mgn daya yayi maganinsu...yana fita ya nufi motarshi da yasha car wash sai kyalle yake ya bude driver seat ya shiga tareda tayar da ita ya fita daga gidan..these driver dinshi ba karamin hutawa yake ba sbd almost everyday shi yake driving kanshi yanxu especially idan yasan wajenta zaije..shifa gani yake ana daura musu aure ma driver office kadai zan dinga kaishi amma duk wani personal al'amuranshi da kanshi zai dinga zuwa yanayi ko don sbd matarshi..shi bazai iya bari driver ya tuka mashi mata ba har ga Allah..kawai gani yake zaiyita kallonta ne ta mirror shi kuma da wani namiji ya kalleta gwara shi a kwana ana kallonshi bai damu ba...driving yake yana murmushi gami da shafa Kai sbd tunowa da ita da yayi..har kullum sonta karuwa yake a cikin ranshi musamman yanxu da yake receiving equal treatment daga wurinta..daxun rigima sukayi sosai sbd tayi mgn a sauko musu da biki tace bazata iya ba shine yayi zucia har ya baro school din bai nemeta ba yasan tana can ta cika fal tana jiran yaje ta sauke mashi...har ya isa college dinsu bai bar tunawa da ita yana murmushi ba..daidai gate dinsu yayi parking snn ya dauki waya yayi dialing numberta don ko sanar da ita zaizo baiyi ba..tana dauka ko jira tayi mgn baiyi ba yace"baby am outside"..ta wani hade rai ita bata yadda ba ya 6ata mata rai tace"ni banida lafia"..murmushi yakeyi yace"eyya meya sameki?.."a shagwabe tace"fever"..yace"alright let me come inside in dubaki"..tun kafin ya rufe baki tace mishi"nidai No..salon ka shigo duk suyita kallonka"..yace"then indai bakiso in shigo ki fito..na baki 3 mins idan ban ganki ba am coming inside"..daga haka ya kashe wayar yana cigaba da murmushin wnn rigiman nata...suna gama wayar ta juya tana kallon Billy dake kunshe daria tace"munafuka"..daria Billy ta fashe dashi harda su tafa hannaye tace"munafurcin me Kuma nayi Lamido?.."harara ta watsa mata tareda mikewa zuwa wardrobe dinsu ta dauko zumbulelen hijab ta dora kan jean da Jessy dake jikinta as always snn ta fita daga dakin bayan ta Maka ma Billy harara..ita dai da kallo ta bita tana cigaba da murmushi tace"wai Ina matsayin matar yayanta takemun wnn iskancin..Lamido Allah ya shiryeki".
Tana fita Kai tsaye inda ta hango motarshi ta nufa..shi Kuma yana zaune ciki yana kare mata kallo don wurin akwai haske dal kmr ba dare ba..hijabinta yakai qasa amma Saida ya fahimci jean da riga ne a jikinta sbd fitowa da wandon yayi ta kasa..lumshe Ido yayi ya bude tareda jingina kanshi da kujera yana cigaba da kallonta har ta iso inda yake..ta bude motar ta shigo snn ta maidashi ta rufe tanata wani ciccin magani ta juya tana kallonshi..murmushi ya Kara saki tareda kama both hands dinta ya rike yana kallon eyeballs dinta yace"menene?."turo baki tayi tace"Pogba"..idanu ya ware da kyau a kanta cikin mamaki yace"Pogba Kuma?.."Kai ta daga mishi akamar eh nan take kuma ranshi yaji ya 6aci..shi duk tunaninshi sbd ya wuce bai nemeta bane daxun take fushi ashe abun nata ne ya motsa bai saniba..sake hannunta dake cikin nashi yayi snn ya sake dubanta cikin kokarin 6oye 6acin ranshi yace"what about him?.."a dan fusace tace"wai mutumin nan mu zai wani tozarta ya bar Manchester United..kasan yanxu wai Juventus..."bata samu sararin karasawa ba sbd wani kallo da ya shiga binta dashi ita sai yanxu ma ta tuna ashe fa tayi kato6ara..innalillahi wainna ilaihi rajiun ta fada cikin ranta.."wane ruwa na kuntowa kaina ni Aisha?.."ta fada a hankali yayinda take kallon yanda yanayinshi ya sauya lokaci daya..dunia idan akwai abunda ya tsana bai wuce wnn Pogban ba..ya tsaneshi to the extent that yakejin duk wani dan Manchester da Yan ball din ma kaf ya tsanesu..dukda cewa shi Pogban musulmi ne amma da gaske tsanarshi yakeji sbd wnn son da yaga tana mashi.. marairaicewa tayi sosai kmr wadda ke dab da fashewa da kuka tace"partner am sor"..bata karasa ba ya dora finger dinshi kan lips dinta yana kallon cikin Idonta yace"u don't have to apologize"..girgiza kai ta shigayi tana kallon 6acin rai Karara kan fuskanshi tace"nidan am sorry plss..wlh mancewa nayi"..baice mata kala ba ya dauke finger dinshi daga bakinta tareda komawa yayi relaxing kan seat din da yake..hankalinta taji ya tashi sosai tasan duk yayi irin wnn fushin da ita to abu ba karamin 6ata ranshi yayi ba..shaf mancewa tayi da wnn kishin nashi wlh da bata ma fara ambaton Pogba a gabanshi ba sbd yanda ya tsaneshi..matsawa tayi jikinshi sosai tareda Kai hannu ta kama left hand dinshi murya can kasa tace"partner"..banza yayi mata baice komai ba..ta sake cewa"partner talk to me manaa..nace am sorry fa"..still baiyi mgn ba sai ma hannunshi daya zare daga cikin nata ya shiga kokarin bude motar zai sauka kawai yaji ta rungumoshi ta baya tana cewa"partner am so very sorry plss..am sorry I hurt u amma ba da gangan nayi haka ba kasan I love u"..lumshe Ido Bobby yayi yanajin heart beat dinshi na sauyawa lokaci guda..kawai sai yaji wasu irin abubuwa sun shiga zagayawa cikin jini da tsokar jikinshi baisan lokacida ya sauke wani gauron numfashi ba..yana jinta a jikinshi yaji duk 6acin ran nashi yayi disappearing sai Kuma wani shauki daya tsinci kanshi a ciki na musamman...tunda yake da ita bata ta6a hugging dinshi haka ba sai yau..this very moment..wani additional sonta yaji yana sake ciko zuciarshi kawai sai ya juya tareda dagota daga jikinshi yayi cupping fuskanta yace"Love why plss..why do u always wants to talk about him..why do u love him this much?.."hannu takai itama tayi cupping nashi face din tana girgiza mashi Kai tace"I do not love him..I love u..only u baby..I love u more than any other person in this whole wide world..u are my soul partner,my future husband,my babies daddy and I love u so much"..sbd tsabar jin dadin kalamanta baisan lokacida ya sake maidata jikinshi yana sauke ajiyar zucia da mugun karfin gaske ba..wani irin sanyin dadi yaji yana ratsa zuciarshi tamkar an sauke mashi mountain daga ciki..these words means the entire world to him..it means a lot to him and he wouldn't mind tacigaba da fada mashi irinsu daga nan har mahdi ya bayyana..kawai baiso ta dena fada ba..sai yaji kaman su dawwama nan wurin tana fada mashi the most sweetest words daya taba saurara all his life..rumgumeta yayi sosai sai sauke numfashi yake kafin ya dagota a hankali yakai lips dinshi ya manna mata peck a forehead dinta yana kallonta wearing a very wide smile kan fuskanshi yace"I love u more baby..I love u like..."kasa karasawa yayi sbd gani yake babu wata kalma da zatayi daidai da son da yakejin yanayi mata a mizani saidai in zuciyarshi zai bude mata ta shiga ta gani kawai idan ba hakaba duk yanda zaiyi bayani bazata ta6a ganewa ba..hade fuskanshi yayi da nata idanunshi rufe yace"I beg u in the..."bata bari ya karasa ba itama ta dora two fingers dinta akan lips dinshi tana kallonshi tace"I promise not to talk about him ever again..am sorry"..sake rungumeta yayi yana sauke ajiyar zucia..bayan few minutes ya rabata da jikinshi yanata doka murmushi ya kalleta kafin yayi mgn tace"I love u"..ya lumshe Ido ya bude shima yace"I love u more baby..and ba na hanaki