Showing 33001 words to 36000 words out of 231169 words

Chapter 12 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9650

ya sallami yarinyan da suke tare snn ya shiga kallonsu with a smile yace"so how was the exams?..Aysha tace"exam Alhamdulillah besty ya naka?.."yace"it was fine"...kallon Billy dake duba littafin hannunta yayi yace"so Bilkisu ya exams?.."tace"lafia lau"...ya kalli Aysha suka hada ido snn ya sske cewa"sai wani hade rai kikeyi sbd kin ganni...ki kwantar da hankalinki munayin counsil bazaki sake ganina ba"...ya karasa mgnr kaman wani abun tausayi...lokaci daya sai Billy ta dago tana kallonshi...idan akwai abunda ta tsana bai wuce yayi mentioning counsil exam ba duk sai taji jikinta yayi wani sanyi...ganin yanda ta kura mashi ido suka sake hada ido da bestyn shi sukasa daria...bayan sun gama yace" my Mom will be coming tomorrow.. hope zakuje ku gaisheta?.."da sauri Aysha tace"of course zamuje mana bestie..Allah ya kawota lafia...and yauwa bestie zaka kaimu lalle ranan Thursday idan mun fito daga exams...kasan cikin week din nan zaa fara bikin Adda Ruky"...yace"na sani besty amma baki ganin zaku samu matsala idan aka ganku da lalle?..nasan kinsan cikin ethics dinmu hadda kin applying wadan nan abubuwan"...tace"i know besty amma bansan ya zanyi bane...tun Thursday fa zaa fara bikin kuma ni bazan samu zuwa ba sai friday kaga banida time din yin lalle da sai na bari idan mun koma muyi...besides nafi son lallen kanawa yanxu..yafi namu kyau"...bai sake cewa komai ba kawai ya girgiza kai dan yasan tunda tasama ranta sai tayi lallen nan duk abunda zai fada ma ba changing mind dinta zatayi ba.

The following day kaman yanda suka tsara bayan sun fito daga exams suka koma hostel sukayi changing kaya snn ya kwashesu zuwa Tarauni gidan kakarshi...suka samu Mom dinshi zaune a parlor da Hajia sai dan autansu Mahmud...suka karasa ciki suka zauna snn suka gaisheta...ta amsa musu da fara'a tana tambayan su ya karatu...suka amsa da fine...tace"ga bestie ga Bilkisu koh?.."Sa'eed dake sauraronsu yace"Mom ashe baki manta ba"..tace"ya za'ayi na manta tunda kullum cikin zancensu kake"...Hajia tace"nima nan haka yake damuna da zancensu..magana daya biyu zaice besty tayi kaza ko kuma Billy tace kaza"...daria sukayi gaba daya jin yanda Hajia ke immitating mgnrshi...yana dan hararanta ta gefen ido yace"yanxu Hajia haka nake mgn?.."tace"oho kai ka sani"...sister dinshi ce ta fito daga daki waya kare a kunneta...tana ganinsu tayi hanging call din ta wani karasa cikin parlon da gudu ta fada jikinsu...Sa'eed yac"Lubna meye haka?..karya min su kikeso kiyi ne?.."ta daga jikin nasu tace"sorry yaya..nayi farin cikin ganin kawayena ne...kawayena da basu damu dani ba"..ta karasa mgn kaman zatai kuka...Mom tace"to sai ku shiga daki ku karasa mgn dan naga kaman they are not comfortable here"..Lubna ta mike tsaye rikeda hannayensu tace"yanxu kuwa Mommy"..daga haka
ta jasu zuwa dakinda ta fito Sa'eed ya bisu da kallo har suka shige...Hajia dake ankare dashi tun dazu tace"mutum dai yayita yaudaran kanshi da sunan kawance..watarana kana zaune wani zaizo ya dauke ya barka da cizon yatsa"...juyawa yayi yana kallonta yace" me kike nufi?.."tace"me kuwa nake nufi daya wuce kana son mace kana yaudaran kanka wani wai kuna kawance..idan bakayi da gaske ba kana zaune zata auri wani ta barka wlh"...yace"to ke waya fada miki inason wata a cikinsu?..we are just friends "..tace" shine nace kacigaba da yaudaran kanka Sa'eedu"...bai sake mgn ba ya juya yana kallon Mom dinshi sai yaga daria take musu..zaiyi mgn tace"babu ruwana tsakaninku ne wnn"..

Suna shiga daki suka zauna suna sake gaisawa...Lubna tace"da gaske mutanen nan baku damu dani ba..ko nemana fa ba wanda yakeyi a cikinku"...Billy tace"wlh abubuwan ne sai a hankali Lubna amma inshaAllah daga yanxu zumunchi sai kince ya isheki koba hakaba Lamido?.."da sauri tace"sosai ma kuwa..daga yanxu mun kulla knn har sai mun isheki"..tace"nikam ba wani dadin baki da zakuyi min dan bazan taba yadda ba sai naga kunzo har kd bikina snn zan yadda daku"..Billy tace"u mean an kusa bikinki?.."tace"in the next three months inshaAllah"..Aysha tace"Allah ya kaimu ya sanya alkhairi...amma besty bai ta6a fada mana ba wlh"..Billy tace"shine nima nake mamaki ai..koda yake kadan knn daga aikin Sa'eed"...nan kuma hiran nasu gaba daya ya koma kan bikin Lubna da irin shirye shiryen da zasuyi...if u see yanda suka sake da juna suna labari zakayi zaton tasowa sukai tare tun kuruciya nan kuwa basu dade da sani juna ba shima ta dalilin Sa'eed wani lokaci da tazo ta dade a kano ya kaita hostel dinsu shknn suka kulla kawance...basu fito daga dakin ba saida yazo da kanshi yace su fito ya maidasu snn suka fito...sukayi sallama da Mom da Hajia da har yanxu suke parlor...Mom ta basu dambun nama da tayoma Sa'eed da Hajiyarta cikeda wani flask aikam sukaita godia snn suka tafi har Lubna data dage zatayi musu rakiya...kaman yanda ya saba duk ya fita dasu sai ya siya musu kayan kwalama yake maidasu yauma haka ya tsaya a grand square ya sai musu su chocolates da sweets snn yayi dropping nasu a hostel su kuma suka koma tareda Lubna.

Washegari Thursday suna zaune a premesis kafin time din shiga exam dinsu yayi motan Proprietor ya shigo makarantan...Ayshata wani hade rai dan tana gani ta gane motanshi ne...ko gama parking motan baiyi ba securities da some of staff da sukaga shigowanshi sukayi inda motan yake kaman yanda suka saba...tana daga zaune tana ganin yanda suka bude mishi kofa ya fito sunata wani washe mashi baki hadda masu risinawa suna gaisheshi kaman wani ubansu...Billy ce ta fara lurada ita sai tace"are you okay?.."ta saki wani tsaki tana fadin"mutanen can ne suke bani haushi wlh...dubi yanda sukema inyamurin mutumin can kaman zasuyi mishi sujada...kawai dan mutum nada kudi sai kuyita kaskantar da kanku a wurinshi da yawa daga cikinsu mafa sun girmeshi"..girgiza kai Billy tayi tace"to ke ina ruwanki...kuma an fada maki ba inyamuri bane har yanxu kin ki yadda koh?.."ta maka mata wani harara tace"wai wnn mutumin zaki kalla kice ba inyamuri bane haba Billy.."Sa'eed daketa sauraronsu yace"da gaske ba igbo bane shi besty..ance dai Mom dinshi igbo ce amma babanshi bafulatani ne fa"...da sauri Billy tace"tell her...bafulatanin ma kuma dan garinku"...da sauri ta daga kai tana kallonta tace"what do u mean?."Billy tace"ina nufin dan Gombe ne shi mana"...tun kafin ta rufe vaki tayi spitting tana binta da wani disgusting look tace"God forbid...how could such a heartless person come from Gombe?..gaskia i doubt that kilan dai bakuji daidai ba...and wether u accept it or not mutumin can inyamuri ne kuma na tabbata yana daga cikin masu assasa yakin Biafra sbd tsabar mugun halinshi"...daria suka sa mata gaba dayansu aikuwa ta cika tayi fam har ta mike zata bar wurin Billy ta janyota da sauri tace"to shikenan Sa'ees tell her mun yadda inyamuri ne shi"..da sauri yace"eh mana kuma a cikin inyamuran ma yana daya daga cikin masu assasa yakin Biafra so are we good now?.."murguda musu baki tayi tana hararansu...ganin time din exam ya gabato duk suka mike zuwa classes dinsu.

Karfe biyu da wani abu ya daukesu suka tafi lalle kaman yanda suka tsara...Lubna ce tace tasan wani gidan lalle a Na'ibawa sun iya lalle sosai dan haka kai tsaye can ya nufa dasu.

Basu suka baro gidan lallen ba sai after six kowacce da rangadeden lallenta mai kyau har Lubna da tace bazatayi zuwan banza ba dan haka dole akayi mata itama...tun da suka fito yake yabon lallen nasu amma wai na bestynshi yafi kyau...Lubna tace"Yaya wnn dai son zuciyarka ka fada gaskia"..Billy tace"ai kadan ma kika gani daga aikin Sa'eed"...Lamido dai dariya take sai kuma ta dan rausaya kai tana dubanshi tace"yanxu besty hostel zamu koma knn?.."yace"eh mana you guys have exams tomorrow "..tace" mun riga mun gama karatu wlh besty dan Allah ka kaimu yawo kaji"...ya dan harareta yace"wani wai kun gama karatu sai kace yin karatun kike"...tace"nidai dan Allah muje yawo pllss ko Billy "..dagowa tayi ta watsa mata harara yace" then we are definitely going back to hostel tunda hajia Bilkisu bata yadda ba"...da sauri Lubna tace"Billy kice kin yadda plss"...kmr bazata ce komai ba sai can tace"shikenan amma we won't stay long"..Aysha tace"hakanma mune da godia hajia bilkisu"...daria kawai Sa'eed yayi yace"to ina zamuje yanxu?.."da sauri Aysha tace"mu fara zuwa mudassir da akwai veils da nakeson siya"..yace"besty da shopping"...tace"ba haka bane besty kaga ko ban siya a nan dole ina sauka Gombe inje in siya kasan fa gobe ne kamun adda ruky"..jinjina kai kawai yayi sarai yasan halin kayarshi da shegen son biki...suna isa mudassir din gaba daya suka fita zuwa ciki...ta kwashi veils wajen guda four snn ta dauki shoe da bag...Billy ma ta dauki nata sai Lubna da suka tilasta mata ta dauki mayafi itama...sunzo wajen biyan kudi Aysha ta mika card dinta..Sa'eed ya watsa mata wani kallo yace"and what's that?.."tace"besty kullum fa kai kake biya yau daya dai ka bari na biya plss"..bai sake ce mata komai ba ya amsa card dinta daga hannun mutumin snn ya bashi nashi...ana gama cire kudin suka fita daga wurin rikeda ledojin kayan da suka siya...daga nan Chicken Republic suka wuce suka samu table suka zauna snn aka kawo musu menu kowa yayi ordern abinda yakeso...suna nan zaune kafin a kawo abincin sukaji sallama kusa dasu gaba daya suka juya inda sukaji sallaman...wani mutumi ne da akalla zaikai iri 50 to above yana nuna empty seat dake wurin yace"may i?.."Sa'eed ne yace mishi"Bismillah"...a hankali yaja kujeran ya zauna snn ya mikama Sa'eed hannu suka gaisa yace"sorry i interrupt you guys...wlh tun daga kabuga na biyoku har nan wajen"...mamaki sosai ya bayyana a fuskokinsu jin tun daga kabuga yake binsu...ganin kallon da suke mishi sai ya saki murmushi ya nuna Aysha da finger dinshi yace"because of her"...wani mamakim ya sake kamasu jin abunda ya fada...shi kuma ya saki murmushi yana duban Sa'eed da yayi tunanin ko yayansu ne yace"can i please talk to her in private?.."shiru Sa'eed yayi ya juya yana kallonta sai yaga tana wani blushing kanta a kasa cikin ranshi yace"dama nasan za'ayi haka wlh..besty da shegen son sugar daddies"...jin har yanxu baiyi mgn ba mutumin ya sake fadin"only 5 minutes plsss"..yaja plss din da har saida ta dago ta kalleshi...a hankali Sa'eed yace"Sure u can"..mutumin yace"thank u so much..you are a life saver"...daga haka ya mike tsaye yana mata wani kallon kasa kasa yace"Ma'am"...batayi mgn ba ta mike tabi bayanshi zuwa wani table a can gefe...da kanshi yaja mata kujera ta zauna snn shima yaja ya zauna yana facing dinta yace"Allah yasa dai banyi laifi ba"...ta danyi murmushi hadi da girgiza mishi kai...shi kuma yayi mata kuri da ido kamab ya samu tv...saida suka hada ido ya sauke wani numfashi tareda cewa"u are very beautiful...shiyasa ina kallonki naji komai nawa ya tsaya..naji bazan iya hakuri ba har saida na biyoki...Allah yasa ban kawo kaina inda za'a wahalar dani ba"...still murmushi ta kara saki tana girgiza kai...yace"my name is professor Ahmad Abdu Kurawa and i think i have fallen for you"...shiru kawai tayi tana kallonshi sai taji ya burgeta sosai...this is exactly why she loves sugar daddies cox they are straight forward ba wani kwana kwana a tsarinsu...snn ga iya handling mace da nuna mata so da kauna...shiyasa duj ta shirya yin aure batada burin da ya wuce ta samu sugar daddynta ta aura yanda zata yita zabga shagwa6a son ranta ana lallashinta...jin batace komai ba ya wani rausaya voice dinshi yace"dan Allah say something plss..wlh i love you..i love you so so so much"...murmushi ta kara saki tana rufe fuska da hannayenta sai ya saki murmushin shima kafin yace"ohk i guess i have to give u some time to think right?.."da sauri ta gyada mishi kai..yace"alright then you take your time...amma plss kiyi min mgn inji sai in tabbatar da banyi zuwan banza ba"...still smiling tace"sunana Aysha Ahmad Lamido"...yana gyada kai yace"your name suits you...dama ina ganinki naji a jikina wnn beautiful soul din must be Aysha..thank you so much Aysha for giving me your time...yanxun zan wuce sbd na bar yaro a mota kema kuma naga 'yan uwanki suna jiranki"..batace komai ba sai murmushi shi kuma ya zaro card dinshi ya ajiye mata yana cewa"ga card dina nan saiki kirani or better still bani number dinki cox i can't the risk of loosing you"...batayi musu ba ta amsa wayanshi tasa number dinta...saida yayi dialing yaga ya shigo snn ya katse tareda mikewa tsaye yana kallonta yace"to ni zan wuce beautiful Aysha..zan kiraki inshaAllah and Allah yasan baza'a bani negative news ba"...tace"inshaAllah"...yace"alright bye"...itama tace mishi"bye"snn ya juya ya fita itama ta mike ta dauki card dinshi daya ajiye ta koma inda suke..Lubna tace"so har kun daidai knn?.."itadai tayi murmushi tareda fara cin abincinta...Billy tace"ai bama saikin tambaya ba Lubna wlh nasan da kyar idan batayi accepting dinshi ba..Lamido da shegen son sugar daddies"...shidai besty yana jinsu baice musu komai ba...suna gamawa suka bar wurin time din dare ya farayi sosai yayi dropping nasu a hostel su kuma suka wuce Tarauni.







Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment ta 07063800556.












Rano✨






🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

I dedicated this whole page to my darling small mom🥰❤️Hajia Fiddausi Musa Kibia aka Mrs MD aka Maman Mufeed da Mufeedah🥰❤️Ina roqon Allah ya biya maki dukkanin buqatunki na alkhairi Aisha Indo loves u so much🥰❤️


12


Washegari Friday zasuyi final paper na first semester level two knn..zasuyi hutun two weeks snn su tafi clinical posting...tun wajen 7 suka baro hostel zuwa cikin makaranta..daga ita har Billy murna suke zasuje gida dan ko weekend sun kwana biyu basu je ba...kafin time din exam yayi provost ya kira wayanta yace tazo yanason ganinta...babu wasting of time kuwa taje office dinshi yace list din yan class dinsu yakeso ta bashi yanxun nan...ta juya zata fita ya dawo da ita ya mika mata pen da paper yace ta zauna nan ta rubutasu yasan zata iya tunda ba wani yawa garesu ba...ba musu ta amsa ta zauna ta fara rubutawa shi kuma Nur yacigaba da aiki a Laptop dinshi...a hankali Bobby ya turo office din ya shigo...idanuwanshi basu sauka ko inaba sai hannun Lamido da lallenta yayi wani moroon yanata shinning abunka da farar fata...ranshi yaji ya 6aci sosai like how dare this girl apply henna a hannunta bayan tasan baya cikin ethics... har ya karaso cikin parlon basu sani ba sai kawai sukaji yace"keh.."a gigice ta dago tana kallonshi..fuskan na sarari yace"bakuyi professional ethics bane?.."voice dinta na dan cracking tace"mun...yi"yace"then why did you apply this rubbish a hannunki?.."tayi shiru kanta kasa tana 6oye hannunta...Nur dake kallon abokin nashi da mamaki yace"C'mon Bobby ni banga wani abu anan ba..maybe kafin su tafi clinical posting ya baje so relax "...a fusace ya juya yana kallonshi yace" amma kai kanka kasan duk wayan nan abubuwan is prohibited a profession dinta koba a clinical area bane"...shiru kawai Nur yayi yana kallonshi..baisan why he easily gets angry when it comes to her ba..he remember yanda yayi acting ranan da sukaje hostel...ita kuwa Aysha daure fuskanta tayi tana dan turo baki har yanxun kanta kasa dan ko a mafarki batason sake hada idanu dashi...(note:nasan wayansunku will be like ya zaayi a hanata yin lalle sai kace a secondary school..well duk wanda yayi health institution yasan banbancinsu da secondary school dan kadan ne coz sunada strict dokoki snn kuma akwai ethics so ba yanda zaayi mutum yazo yana yin anyhow a irin wnn makarantun sbd suna dealing da lives of many people..da akwai rules da dole mutum sai yabi while in school ko kuma clinical area..na farko dai applying lalle is prohibited especially during clinical posting..snn ba'a sanya kayan ado musamman duk wabi abu da zai dauki hankalin patient ta hanyar sound dinshi ko wani abu shiyasa ake sanya uniform and ko takalmi bada kowanne ake zuwa ba dole sai preferred wanda aka za6a..irinsu zobe su agogo da sauransu suma duk are prohibited sbd suna iya daukan hankalin mara lafia shiyasa ake fara training mutum ya saba tun a school kafin ya tafi clinic..so i hope u understand dan nasan wasu zasuce wnn ta cika tsanani da yawa ko kuma ace tana rubuta abunda ba haka bane bayan haka tsarin kudan duk wani health institution yake saidai wasu sufi wasu tsanantawa)...karasawa yayi cikin office din ya tsaye nan inda take zaune snn yace"a ka'idar wnn abun da kikayi suspension za'a baki kuma bazaki dawoba har sai ya baje amma yanxu tunda you are going for holiday punishment dinki shine bazaki rubuta exams dinki na yau ba"...a rikice ta dago tana kallonshi idonta har ya ciko da hawaye...kallon nata yakeyi shima aikam nan da nan tayi kasa da nata don bazata iya daukan wnn kallon nashi ba...Nur ya taso daga seat dinshi ya zagayo inda yake yace"Bob me kakeyi ne haka pls?..meyasa bakajin mgn?.."a fusace yace mishi"ita why bazaka tambayeta meyasa batajin mgn ba?..meyasa ta cika fitina duk wani abu da tasan zai ja mata matsala bazata hakura dashi ba"...shiru gaba daya sukayi suna kallonshi...shidai Nur har yanxu bai dena mamakin wnn behaviour din nashi ba...shi kuwa ganin kallon da yake mishi ya karasa ciki ya dauki wani file akan table dinshi snn ya juya ya fita daga office tunda dama abunda ya kawoshi knn...kaman jira takeyi ya fita ta saki wani kuka mai ciwo...Nur ya dawo kusada ita da sauri yana kallonta a hankali yace"Lamido stop crying plss...dont cry"..girgiza kai kawai take as tasan idan daddy yaji an hanata rubuta exam sbd lallen da tayi applying fada ne zata sashi kilan ma saiya hada da duka..sam ba mai daukan iskanci bane shiyasa take mugun tsoronshi...ganin yanda take kuka Nur ya sake kwantar da murya yace"dan Allah stop crying kinji...duk wnn abun da kikaga yanayi baikai zuciyanshi ba...yanxun kije can office din nashi ki bashi hakuri"...yana rufe baki ta dago a razane tana kallonshi...sai kuma ta hau girgiza kanta tace"Sir bazan iya zuwa ba...inajin tsoro"...yace"don't be..ba abunda zaiyi miki inshaAllah believe me...kawai idan kinje ki kwantar da muryanki kice yayi hakuri dan darajar Mummy da Daddy na tabbata idan kika fadi haka zai hakura"...shiru kawai tayi tana kallonshi kaman bataji me yace ba...saida ya sake mata mgn snn ta fita daga office kaman mara lafia...secretary dinshi na ganinta tace ta jira ta fara mishi mgn...landline dinshi ta kira ta fada mishi yanada bakuwa kai tsaye yace a barta ta shigo...saida ta gama goge

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login