Showing 12001 words to 15000 words out of 231169 words

Chapter 5 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9647

nan yana kallonta bazai taba gajiyawa ba.

Direct daga office din Sir Abdool ta wuce Office din Provost...bata samu secretary dinshi a wurin ba dan haka kai tsaye ta tura office din ta shiga da sallama...suna zaune kan sofa shi da Bobby suna mgn and bisa ga dukkan alamu important issue suke discussing... a tare suka juyo suna kallonta...idanu Nur ya dan ware yana kallonta with a broad smile kan face dinshi yace"ohh Lamido it's you?.."dan murmushin itama ta saki tana gyada kai tace"nice sir..sorry i banged in without permission secretary din ce bata nan"...saida ya mike daga inda yake ya koma seat dinshi ya zauna still yana murmushi yace mata"with or without permission you are always welcomed here so you don't have to apologize"...gajeren smile ta kara saki kai a kasa tace"thank you sir"...baice mata komai ba sai ma relaxing da yayi kan seat dinshi yana kallonta...tun daga kan legs dinta dake sanye da black cover shoe daketa shinning as a result of polish da yasha...zuwa pencil trouser da well shaped riganta daya tsaya iya guiwanta...shape dinta sai ya fito yayi daidai a cikin rigan dama gashi sai daukan ido suke sbd iron...a hankali ya gangaro da idanun zuwa chest dinta dake nan rabi a waje rabi kuma rufe da mini hijab sai kuma beautiful face dinta da yafi komai daukan hankalin mutane game da ita...dan bakinta data shafama lip balm sai kuma glasses dinta da yayi daidai da dogon hancinta...sai gashin goshinta zuwa sajenta da suke nan a kwance kasancewar babu hula ko dankwali a kanta...tunda ya fara kallonta dama tayi kasa da kanta bata dago ba tanadai jin yanda idanun ke yawo a jikinta...saida ya gaji da kallon nata dan kanshi yace"Bismillah mana"..ba tayi musu ba ta kara taking two steps zuwa gaban table dinshi ta tsaya...sai kuma ta juya a hankali tana facing inda Bobby daya maidasu invisible yake zaune tace"Good Morning Sir"...ko kallon inda take baiyi ba ballantana tasa rai zai amsa mata...gaba daya hankalinshi na kan wayanshi dake hannunshi...wani irin kullutu taji yazo ya tokare mata a wuya...tunda take baa taba humiliating dinta kmr haka ba...lokaci guda wasu zafafan hawaye suka ciko idanunta amma bata bari sun zubo ba tayi kokari ta maidasu snn ta sake juyawa tana facing provost idonta a kasa tace"Sir it's about miss Ayuba"...shima jikinshi a sanyaye dan baiji dadin abun da Bobby yayi mata ba yace"Ita ke daukanku reproductive health koh?.."kai kawai ta iya daga mishi...ya sauke numfashi yace"have you tried talking to Umar about it?."still kanta kasa tace"i did sir and unfortunately yanada lots of classes da yake taking"...shiru sukayi na wani lokaci kafin Nur yayi breaking silence din da fadin"ohk yanxu abunda zaayi kiyi amfani da course outline ko tutorials ne ki fara musu before i see what to do..inshaAllah zuwa Monday zaa san yanda zaayi"..kai ta sake gyada mishi smn ta juya zata fita daga office din yayi kasa da voice dinshi sosai yana kallon bayanta yace"Lamido kiyi hakuri kinji?.."nan ma kan ta sake gyadawa snn ta fita a office din...tana fita Bobby ya dago big idanunshi yana dubanshi rai a bace yace"laifin me akayi da kake bata hakuri?.."shiru kawai Nur yayi yana kallonshi dan yasan idan sukaja mgnr da nisa ransu ne zaizo yana baci...yasan Bobby da bala'i dan haka bazai kulashi ba amma yasan exactly yanda zaiyi maganinshi...dan haka sai ya mike daga inda yake tareda komawa kusa dashi ya zauna yana dubanshi da wani murmushi yace"babu laifin da akayi mata Sir.. ina bata hakuri ne sbd complain da tazo min dashi..yanxun ya kake ganin zaayi?..for almost three weeks knn babu mai daukansu reproductive health shi Umar aiyuka sun mishi yawa ita kuma miss ayuba ta tafi hutun haihuwa"..saida ya dan tabe baki before yace"sai kasa a nemo wanda kake ganin zai iya muyi employing dinshi"...kamo hannunshi Nur yayi still looking at him yace"but that is a long process..dole muna bukatan someone to take over kafin mu dauki wani"...a fusace ya kwace hannunshi tareda fadin"ai kaine provost so it's your responsibility ka nemi wanda zai taimaka musu bani ba"...gyara zama Nur yayi yace"amma kasan course din is a very sensitive course koh..dole ba ko wane zai iya daukanshi ba"..banza Bobby yayi dashi as shi baiga abun wani tayar da hankali a nan ba amma Nur yana neman yayi complicating things...ganin yanda yayi wani watsi dashi sai ya dan kautar da kanshi ya saki wani murmushi kafin ya sake juyawa yana duban Bobby da wani kalan tausayi a fuskanshi yace"ko kai zaka taimaka ka daukesu please?.."kallon are you alright Bobby ya bishi dashi tareda fadin"are you kidding me?.."girgiza kai Nur ya shiga yi yana cewa"wlh am not kidding Bobby da gaske nake..taimakawa fa nace kayi dan Allah"...tun kafin ya rufe baki Bobby ya saki hadadden tsaki yana binshi da digusting look yace"like are you serious?.. are you even listening to yourself?.."kamo hannunshi Nut yayi yana sake sassauta muryanshi kaman wanda yake gaban surukai yace"Bobby take it easy plss...taimako ne fa kawai zakayi please!"...sake fizge hannunshi yayi looking furious yace"and who told you ina son yin irin wnn taimakon?..na taba fada maka ne?..look if you dare say another word kan wnn issue wallahil azeem you'll see the devil side of me..haka nan sai inje class dinsu ince zan koyar dasu ko na taba fada maka ina shaawan lecturing ne?..of course i don't sbd haka mu bar mgnr haka indai ba so kake duk ranmu ya baci ba"...shiru Nur yayi for some minutse kaman bazaiyi mgn ba sai can yace"nasan you can do it..just think about it please"..bai rufe baki ba Bobby yace"you are also a medical doctor so duk abunda kake ganin zan iya kaima you can do it so just go ahead and do it ka dena damuna please"..ya karasa mgnr yana hade hands dinshi waje daya alaman begging...Nur bai sake cew komai ba kawai ya tsaya yana kallonshi...he's thinking of a way to convince him amma ya rasa...shi kuwa Bobby mikewa yayi a fusace zai fita daga office din Nur yace"yanxun ni ka watsa ma qasa a ido koh?.."ba tareda ya dakata da tafiyarshi ba yace"are you Mummy da bazan watsa maka qasa a ido ba?.."daga haka ya fice abunshi...shi kuwa Nuru wara idanuwa yayi sosai yana kallon hanyar da Bobbyn yabi yana sakin wani dan iskan smile yace"why didn't i think of this before?.."sai kuma ya kwashe da daria hadda tafa hands dinshi yace"Dr.Bobby you shouldn't have mentioned Mummy's name..now i know exactly how to force you"ya karasa yana sake fashewa da daria sai kace mara hankali...shi sam tunanin ya hadashi da Mummy bai zo mishi ba sai daya ambaci sunanta...yanxun kam yasan dole idan yayi mgn da ita zata sashi yayi ko yanaso ko bayaso..jingina kanshi yayi da kujera yana wani shafa gashin kanshi yace"what a brilliant plan!..Dr.Nuru kanka yana ja sosai wlh..Allah ya kaimu anjima".









Ga masu tambayan ko zasu iya turamin kati your answer is no plss...bana amsan kati amma ko wurin masu pos kukaje zasuyi maku transfer..thank you all.❤️

Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank sai a tura evidence of payment through 07063800556.










Rano✨






🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22


05


Kai tsaye office dinshi ya wuce yanata faman tsaki domin har cikin zuciyarshi wani tukuki yakeji..a zahirin gaskia ba iya mgnr da Nur ya fada ne ya bata ranshi kadai ba hadda wnn yarinyar Lamido take ko Gidado...last time daya ganta a clinic sam ba wani tsayawa yayi ya kalleta ba amma dazu despite baya so saida ya kare mata kallo tsaf..kuma a iya kallon da yayi mata ya tabbatar da ta hada jini da fulani...shi sai yanxu ma ya tuna Nur ya taba fada mishi cewar 'yar Gombe ce...lokaci daya yaji gaba daya tsanar yarinyar ya samu matsuguni a zuciyarshi...da yasan bafulatana ce kuma 'yar Gombe da babu dalilinda zaisa ya dauki hannunshi mai daraja yayi mata allura dashi sbd gaba daya Fulani basuyi deserving help ko kuma pity dinshi ba a rayuwa...they are all not worthy of his kindness especially wanda suka fito daga Gombe ya tsanesu..ya tsanesu fiyeda komai..baisan meyasa ganin yarinyar kadai ya dawo mishi da abubuwan da suka faru tsakaninsu da dangin mahaifinsu ba...baisan meyasa tun farkon ganinshi da ita baiyi realising cewa bafulatana bace kuma 'yar Gombe ba har saida yayi mata allura...ya dafe kanshi yasan har abada da ciwon wnn abun zai mutu...yanada riko a rayuwa shiyasa har yanxun ya kasa mance abubuwan da suka faru tsakaninsu da 'yan uwan daddy kimanin shekaru biyar da suka wuce...sam baiji dadin taimakon da yayi mata ba kuma da ace yasan 'yan Gombe zasuzo su cika mashi makaranta da baiyi attempting bude makarantan bama at the first place..haka kuma da yanada damar da zaiyi banning 'yan Gombe and all Fulani from studying at his college da yayi hakan saidai it can never be possible...wnn yarinyan kuwa ji yake kaman yaje ya korata this instant ta bar mashi college dinshi...duk zuciyarshi ta cunkushe ga kuma takaicin da Nuruddeen ya sake dirka mashi duk sun taru suna barazanar fasa mashi zuciya..a fili ya furta"the fool..har wani tunani yake ni inje in zama lecturer dinsu..what nonsense!.."ya karasa mgnr yana dukan table dake gabanshi...haka dai ya karasa yini ranan bai tsinana uwar komi ba a office din...one nayi ya shiga toilet dinshi yayo alwala snn ya fita dan zuwa sallahn jumu'a...driver ya bude mishi kofa ya shiga shima ya zagaya ya shiga saidai kafin ya tayar da motar Nur ya fado cikinta da wani irin sauri kaman wanda aka biyoshi...Bobby bai ce mishi komai sai dan tsaki daya saki tareda kawar da kanshi gefe..shi kuma Nur ya saki hadadden murmushi yana kallonshi yace"i don't mind having a drive with my friend"...da sauri Bobby ya juyo yana kallonshi shima fuska tamke yace"well am not going for a drive as you can see..am going for prayer.. jumu'at prayer sbd haka get out of my car immediately"..kara sakin wani smile Nur yayi yana wani shafa gemunshi yace"i still don't mind going for prayer with my friend and we better get going idan bakaso muyi latti"..tsaki Bobby ya saki yana sakan mishi wani harara murya can kasa yanda driver bazai jiba yace"Fool"..da sauri Nur yace"godia nake my friend..i love you too"..watsa mishi harara kawai Bobby yayi tareda dauke kanshi dan yaga alama idan yaci gabada biyema Nur zai maidashi mahaukaci ne a gaban driver dinshi...shi kuwa Nuru murmushin cin nasara ya kara saki cikin ranshi yace"zakaga rashin mutunchi ai..badai Lamido kayima wulakanci ba dazun?.."tayar da motar driver yayi suka fita daga makarantar...koda suka isa masallacin saida Nur ya sake dirka mashi wani abun haushin..kallon suit dake jikinshi yayi sai ya dan saki tsaki yana girgiza kai yace"yau Friday dinma mutum bazai sa manyan kaya ba..some people need to grow up wlh..basu ajiye komai ba sai shegen zafin rai"...ko kallon inda yake Bobby baiyi ba amma ya shaka iya shaka.😂

Karfe biyu daidai suka baro masallaci...Bobby ba tareda ya dubi Nur dake zaune gefenshi ba yace"a ina zamuyi dropping dinka kasan ba komawa college zanyi ba ni..am going home"..da fara'a Nuru yace"don't worry muje gidan..dama mun kwana biyu bamu gaisa da Mummy ba"..Bobby bai sake yi mishi mgn ba har suka karasa gida...driver na gama parking ko jira ya fito ya bude mishi motan baiyi ba ya bude ya fita abunshi..shi kuma ya dauko briefcase dinshi yabishi a baya...shima Nur fitowa yayi zuwa cikin gidan yana daria kasa kasa gamida girgiza kai dan masifar Bobby daria yake bashi wlh...babu kowa central palor as usual suka wuce parlon Mummy...tana zaune da wasu yammata guda biyu da kallo daya Bobby yayi musu ya wani sake tamke fuska...a hankali ya karasa kusada Mummy ya zauna yanata wani basarwa cikin igbo yace"mummy sannu da gida"...tana murmushi tace"sannu Bobby ya aiki?.."can kasa kasa yace"fine.."Mummy ta maida dubanta ga Nuruddeen daya karaso shima ya zauna kusada Bobby tace"yau an tuna damu knn Nuru"..murmushi yake ya shiga shafa kanshi yace"wlh aiki ne kemin yawa Mummy...duk Bobby ya gama sakar min komai ko taimaka min bayayi"..girgiza kai kawai Mummy tayi tace"to ya aikin?..yasu Mom dinka?.."yace"duk suna lafia Mummy..ina auta?.."tace"auta bai dade da fita ba wai zasuje dubiyan wani abokinsu"..gyada kai Nur yayi alaman gamsuwa...sai yanxu yammatan dake zaune suka samu daman gaishesu...Nur kadai ne ya amsa Bobby kam saima sake tamke fuska da yayi...kallonshi Mummy tayi tace"Bobby bakaga Rayhan bane?.."fuskan nan ba sarari yace"na ganta Mummy"..tace"kuma baka iya amsa gaisuwa ba koh?.."a karkace ya juya yana kallon inda suke murya a dakile yace"lafia lau"..daga haka ya mike ya kama hanyar flat dinshi Mummy ta bishi da kallo kawai tana girgiza kai..cikin ranta take cewa"Ya Allah ka shiryamin Bobby"...shima Nur mikewa yayi yana duban Mummy yace"Mummy bari in shiga ciki"..kai kawai ta iya daga mishi dan Bobby ba karamin sanyayar mata da jiki yayi ba..ya juya kenan zai tafi aunty sumy da Miemie suka shigo parlon suma...dakatawa yayi da tafiyar tareda wara idanu sosai akan Miemie yace"hey pretty!.."murmushi ta saki itama ta karasa kusa dashi tace"Uncle Nur good evening"yace"evening pretty how are you..how was school?.."tace"Alhamdulillah"...juyawa yayi ga aunty sumy da har ta karasa kusa dasu Mummy ya wani daga hannunshi alamar salute yace"Allah ya taimaki babbar yaya..barka da rana"..aunty sumy na daria tace"barka dai Nur kwana biyu..ya aiki"..yace"normal normal aunty ya naki aikin?.."dan tabe baki tayi kafin tace" babu dadi wlh..duk Bobby ya sakar min komai ni kadai"..daria ya saki yace"nima haka nake fama dashi aunty..saidai hakuri kawai"..yana rufe baki Mummy tace"to ka wuce ka tafi Miemie zata kawo maku abinci yanxun nan"..bai sake mgn ba kuwa ya kama hanyar flat din Bobby...itama aunty sumy mikewa tayi bayan sun gaisa da baqin Mummy ta kama hanyar nata flat din itama...Miemie kuma Mummy tace taje ta cire uniform sai ta kai musu abinci...ba musu ta juya itama zuwa flat din mamanta.

Yana shiga ya fada bathroom ko kayan jikinshi ma sai a bathroom din ya ciresu...ruwan sanyi sosai ya sakar ma kanshi wai ko zai samu yaje inda yake son yaje wala'alla ya samu saukin abunda yakeji amma inaa...shi abubuwan ma sun mishi yawa baisan da wanne ya kamata yaji ba..na farko waccan bafulatanar yarinyar da yakejin ya tsaneta sama da komai a dunia...sai kuma Nur da kalan iskancin da yayi koma yake kan yi mishi..yanxu kuma ga wnn jarababbiyar yarinyar itama tazo zata kara mashi akan wanda yake ciki already...shi ya rasa wnn masifa da bazata hakura ta kyaleshi ba tunda tasan ba sonta yakeyi ba..wlh ko yanada niyyar yin soyayya baiga dalilinda zai sashi kula mace marar class irin wnn ba..ace mace kaman chewing gum sai nanikewa kike ana koranki amma bazaki hakura ba..wnn wace irin rayuwa ce?.

Koda Nuru ya shigo yanajin alaman yana bathroom sai ya nemi kan sofa ya zauna yana pressing wayarshi...after like 7 minutes Bobby ya fito daure da towel a waist dinshi...dagowa Nur yayi yana kallon pure white skin dinshi da ruwa ke tsere akai as result of wankan da yayi snn ya saki wani murmushi...murya can kasa ya furta"what a hottie!.."sarai Bobby yaji abunda ya fada amma bai kulashi ba ya karasa gaban mirror ya fara shafa cream dinshi...shima Nur sake juyawa yayi yana facing inda yake hadda su yin tagumi yana cigaba da kallonshi...kawai ayyana baiwar kyau da Allah yayi mishi yake...gani yake kaman Bobby is the most cutest and hottest guy alive...baisan why ba amma shi kam kyawunshi na burgeshi sosai...cikin ranshi yake ayyana idan shi da yake namiji yana admiring kyawun Bobby yammata kuwa ai kilan sai sunyi hauka akanshi cox yanada wani irin kyau da a kallon farko zaka fahimci hakan...ko dan kasancewarshi ruwa biyu ne oho?..dama ai ance duk dunia babu wanda yakai halfcast kyau so maybe shiyasa duk yan gidansu Bobby keda kyau tunda Mom dinsu igbo ce Daddy kuma Fulani...ta cikin mirror Bobby yaga yanda Nur ya sake juyowa yana zuba mishi ido kaman wanda bai sanshi ba dan haka ya dan saki tsaki tareda juyawa yana dubanshi yace"malam what is the look for?..haka nan ka kafa min ido kana starring..are you sick?.."numfashi Nur ya saki tareda sauke hannunshi daga tagumin da yayi before saying"kawai ina kallon hottie ne...the only cute and sexy man around..guy ba dole yammata suyita hauka kanka ba..ga Rayhan can ma tunda na ganta nasan zuwa tayi kuyi zance"...wani kululun baqin ciki yaji ya sake tokareshi just by mentioning Rayhan's name...Goodness he hates that girl with passion...he hates her like hell and not only Rayhan he hates duk matan dake kawo mishi kansu...he hates classless women...sbd tsabar baqin ciki ma kasa cewa komai yayi kawai ya juya zuwa closet dinshi ya shiga ciki ya sako white crazy jean da wata black polo snn ya fito fuskan nan ba fus...gefen bed dinshi ya zauna ya dauki wayanshi knn Miemie ta shigo dakin rikeda tray da aka dora transparent glass jug mai daukeda pineapple juice a ciki...kan dan table dake tsakiyan sofas din ta ajiye snn ta mike...tun kafin ta juya Bobby ya daka mata wani tsawa"Miemie bakida hankali koh?..kina hauka zaki shigomin bedroom without my permission?.. "jikinta har ya dauki rawa tace" Uncle Bobby nayi sallama f.."bai bari ta karasa ba ya shiga nuna mata kofa yace"leave immediately"...ba musu ta juya tana turo baki ta fita daga dakin...Nur ya juya yana dubanshi yace"kaidai bakayi ba wlh...baka ajiye komai ba sai shegen masifa mara amfani"...ya bude baki zaiyi mgn aka sake turo kofan dakin wnn karon Rayhan ce ta shigo daukeda tray din abinci...wani azababben zafi yaji ya faraji all over his body kaman ba yanxun ya fito daga wanka ba...like how dare this girl enter his bedroom like this...how dare she...Nur na ganin yanda yanayinshi ya sauya ya saki murmushi cikin ranshi yace"Allah ya kara"..a fili kuma kallon Rayhan data ajiye trayn hannunta yayi yace"sannu da aiki fa"..tana murmushi ta daga mishi kai...shi kuma ya mike yayi pouring juice da Miemie ta shigo dashi a cup snn ya fita palor yana sipping juice din yace"bari in baku space"...Bobby ya bishi da wani uban harara kaman idanunshi zasu fado kasa...idanuwan Rayhan a kanshi kaman zata cinyeshi itama...bata taba ganin wanda harara yayi mishi kyau kaman shi ba...rai a bace ya juyo da idanunshi gareta voice dinshi har bai fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login