Showing 45001 words to 48000 words out of 231169 words

Chapter 16 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9717

tace"wnn baby girl din taka fa sai kai...bazan iya da fitinanta ba"...yayi daria yace"anya kuwa zan yadda dake Billy?.."itama tayi dariyan tace"ai dama bazaka yadda ba na sani...nidai bari na shiga ciki sai anjima"..yace"to shknn Bilkisu ina godia sosai"..bata sake cewa komai ba ta bar wurin..shi kuma ya bude front seat yana kallonta yanajin kaman ya maidasmta cikinshi...ba musu ta shiga ya rufe kofa snn ya zagaya shima ya shiga...kallon juna kawai sukeyi kowa yanajin soyayyan dan uwanshi na karuwa cikin zuciyarshi...a dan zamansu dashi Aysha ta fuskanci zurfin da yayi a karatun boko baisa ya zubar da addininshi ba...yanada addini sosai dan tunda suke bai ta6a yi mata anything dirty ba..ko dirty talk bai ta6ayi mata haka kuma bai ta6a kama koda hannunta ba...wnn dalilin yasa sonshi ke karuwa cikin ranta..tasan matukar ta aureshi tayi dace da salihi kuma muminin namiji...shi kam ganin time na tafiya and baiso ta makara ya dan saki smile yana cewa"i missed you"..ita kuma shagwa6e fuska tayi kaman wata baby tace"i missed you more baby"..yayi murmushi tareda dauke kanshi dab yanda tayi da face dinta yasa yaji kaman yayi hugging dinta...yanason yarinyar nan to the moon...hira suka dan ta6a kadan snn yace mata zai wuce amma su shirya itada Billy da yamma zaizo ya kaisu shopping...ta wani lankwasa murya tace"baby u shouldn't bother munada komai wlh"...hade rai yayi yace"banason musu baby..idan kuma ban isa ku amsa abun hannuna bane fine"...da sauri tace"to kayi hakuri na dena...zan fada mata inshaAllah"...yace"yauwamy little baby girl...yanxun ki shiga ciki kar suga kin dade baki shigo ba"..ba musu ta bude mota ta fita ta sunkuyo ta window suka sake yin sallama snn ya tada motar ya tafi ita kuma ta shige ciki...duk wnn abun da suke kan idanun Bobby daya gama wayan da yake tun daxu amma ya kasa fitowa daga motar...tunda yaga ya bude mata mota ta shiga da kuma yanda yake hango murmushinda take daga nan inda yake yasan confirm wnn boyfriend dinta ne...haka nan yaji wani irin haushinta ya kamashi cikin ranshi yace"she isn't only a spoiled brat she's also a flirt"...har saida yaga ta fito daga motan snn shima ya bude nashi ya fito...driver dinshi da tunda sukazo ya fito waje ya mika mashi briefcase dinshi ya amsa snn yasa kai cikin building din.

Tana zuwa ta samu colleagues dinta office din Chief Nursing Officer inda daga nan akayi posting dinsu various wards...Billy tana Antenal Clinic Aysha kuma tana cikin Labour Room...ranta duk ya 6aci an rabata da qawarta snn kuma an kaita maternity da bata kauna...sam batason aikin labour room sbd azabar wahala...aikine sosai suke yinshi kmr ba gobe shiyasa duk dunia ba ward da take son aiki kaman ANC ko Family Planning Unit...su aikinsu nada sauki and ba'a shifting amma yanxu tasa a labour room da kyar idan ba'a sata shifting ba...tanata 6ace 6acen rai suka fita daga office din..Billy ta wuce ANC tareda sauran da akayi posting dinsu tare itama Aysha suka wuce Maternity.

Karfe goma daidai Dr.Bobby ya shiga Maternity don yin ward round...wata Midwife dake zaune Nurses Station tana cike Register tazo da sauri ta gaisheshi snn ta koma ta fara harhada files din patents...ta dorasu gaba daya kan trolley snn ta turama Aysha data fito daga labour room yanxu tace"Aysha dan je kuyi ward round da Dr in samu in karasa cike Register nan"...ba yanda ta iya haka ta tura trolley din tayi gaba...yana tsaye kusada bed din wata patient da sukayima cs last two days yana mata tambayoyi Aysha ta karaso wurin...ta daure fuskanta sosai tana sunkuyar da kai kasa dan ko Allah yasan batason hada idanu dashi...tunda tazo wurin yaji zuwan nata amma yanda yayi zaka rantse babu wata hallitta a kusa dashi...hankalinshi gaba daya yana kan patient da yakema tambaya ko kallon bayanshi da yasan tana tsaye baiyi ba...tana fada mishi sunanta Aysha ta shiga nemo file dinta cikin tulin files dake kan trolley kawai sai ya kai hannu ya janyo trolleyn zuwa gabanshi ya dauki file din nata snn yacigaba da aikinshi...wani sabon takaici taji ya lullu6eta...meyasa mutumin nan keyi mata haka ne wai?..meyasa bashida kirki ko kadan?..ganin ya tura trolleyn da kanshi zuwa next bed itama ta ta6e baki cikin ranta tace"ka wutar dani nima"..ta juya ta koma ciki...midwife din da taga ta dawo tace"ya kika dawo kuma?.."kai tsaye tace"shi yace in dawo"...mikewa tayi daga inda take zaune ta fita zuwa inda yake..ita kuma Aysha ta zauna inda ta tashi tacigaba da cike nata register...bayan ya gama ward round har zai fita tace mishi akwai wadda ya kamata ya duba cikin labour room dan haka ya juya zuwa labour room din...Aysha na zaune tana aikin gabanta ko kallon inda suke batayi ba...sun shiga ciki suka samu matar dake ciki tanata fama har kan baby ya fara fitowa sukayi kanta da sauri...ganin harta jigata ranshi ya 6aci sosai...ita waccan zaman uban me takeyi da har patient ra kusa haihuwa bata sani ba...midwife da suke tare tana kokarin taimakawa matar ya dakatar da ita...tace"Sir babyn zaisha ruw..."bata karasa ba yace"call that useless da take zaune ta kyaleta ita kadai"...da sauri ta fita ta kira Aysha...yana ganinta ya sake dinke fuska yace"are u mad?..bakida hankali zaki wuce ki bar patient ita kadai cikin wnn situation din?..are u sick or something?.."dan turo baki tayi tace"ai ni bansan ta kusa haihuwa ba...kuma Register nake cikewa"...sbd tsabar takaici kasa ce mata komai yayi...yana nuna patient din yace"go and attend to her and make sure u did not make any mistake cox you'll regret knowing me"...cikin zuciyarta tace"ai ko a yanxu i regret knowing u wlh...me za'ayi da sanin masifaffen mutum irinka"..karasawa tayi inda matar ta shiga taimaka mata...yana tsaye rungume da hannu yana kallonta kaman bai ta6a ganin yanda ake kar6an haihuwa ba...so yake yaga tayi mistake komai kankantarshi yaci mata mutunchi amma baiga tayi mistake din komai ba...wato dai ba brain kadai takeda ba har skills tana dashi...sam baiji ta wani burgeshi ba duk abunda take...ta kar6i haihuwan successfully ta gama ta kuma yi duk wani necessary abu daya kamata tayima matar da babyn sai a lokacin ya juya ya fita..ita kuma ta bishi da harara kaman idonta zasu fado tace"duk wani baqin hali dai a gun inyamurai ya kare...har abada basu son a zauna lafia".

Around 5:30 suka gama shiri suka fito dan zuwa shopping da Prof kaman yanda suka tsara...bakin gate dinsu sukayi ido hudu da Sa'eed dake jingind jikin motanshi yana kokarin kiran one of them a waya...Aysha ta wara idanu tana kallonshi smilingly tace"my bestyyy"...dagowa yayi yana kallonta sai kuma ya daure fuska yana hararanta...ta karasa kusa dashi da sauri tana cewa"haba my besty...hope ba fushi kakeyi dani ba"...hararan nata ya sakeyi kafin yace"ba wani your besty...ni da aka manta dani"...da sauri tace"oh C'mon besty kaima dai kasan ba wanda ya isa ya mantaka..jiya fa na kira wayanka ban samu ba Allah"..kafada ya daga yace"baki damu ki ganni ba ai..ni da na damu ai gashi nazo har inda kuke"...kaman zatasa kuka tace"besty wai meye haka plss?..kanaso Billy tayi mana daria koh?.."juyawa yayi ya kalli Billy dake tsaye tana kallonsu ya wani kwa6e fuska irin yanda bestyn tashi keyi idan abubuwan suka motsa yace"Billy hadda ke ma koh?..kikaje kika biyewa besty kuka manta dani..is that fair?.."murmushin da bata shiryaba ta saki ganin yanda yayi da face dinshi...ta buda hannaye tace"ni babu ruwana da tsakaninku...kawai inzo in shiga anjima ku bani kunya"...murmushi shima ya saki yana kallonsu with smile yace"nayi missing dinku da gaske...sai nakeji kaman nayi tsuntsu naje Bauchi da Gombe"...murmushin suma suka kara saki Aysha tace"da gaske munyi missing dinka muma...yasu Mom da Lubna"..yace"they are all fine..amma ina zakuje ne haka?.."Aysha ta saki wani qayataccen murmushi kafin tace"wlh Baby ne yazo wai zai kaimu shopping.. muje kayi dropping namu bakin gate nasan yana can yana jiranmu"...kallonta Sa'eed yayi cikeda mamaki kafin ya juya yana kallon Billy yana neman karin bayani..ta daga kafada tana dan smiling dan ta gane me yake nufi tace"ai soyayya ya dade dayin nisa...bakaji har baby ma ake cemishi ba?.."Yace"shine nima nake mamaki ai..but when did this happened banida labari?.."tace"gaka ga bestynka ai"...juyawa yayi ya kalleta kafin yayi mgn tace"besty mu shiga mota idan mun tafi zanyi maka bayani"...baiyi mata musu ba ya bude motar suka shiga..yana gama warming dinta yayi reverse suka dauki hanyan fita hostel din...basuyi nisa ba yace mata"umhum ina sauraronki"...a nuste ta bashi labarin duk yanda sukayi dashi...saida ta gama yace"amma kina ganin ba matsala besty?..i mean kin tabbata mutumin kirki ne shi?.."da sauri tace"sosai mutumim kirki ne wlh besty...ask Billy ta fada maka tunda muke dashi bai ta6a min wani abu da bai kamata ba..he really is a gentle man"..gyada kai Sa'eed yayi yace"to Allah yasa..but still ya kamata muyi bincike a kanshi..i don't want you dating a wrong guy kar azo a samu matsala"..murmushin jin dadi ta saki kafin tace"i trust you completely my besty...kayi duk binciken da kaga ya kamata"...dan juyawa yayi ya kalleta sai ya saki murmushi yace"za'ayi min dadin baki a cuceni"...tana daria tace"ba wani dadin fa..it's the truth"..sake gyada kai yayi baice komai ba...Billy dama tana back seat tana chatting dinta so ko sauraronsu batayi...suna fitowa main gate suka hango motarshi parke daga gefe..saida ya karasa har kusada motan nashi snn yayi parking...suka bude mota suka fita shima ya fito daga cikin nashi motan...Sa'eed ya karasa ya bashi hannu suka gaisa kafin yace"Hope dai za'a bani aronsu for just an hour?.."yana murmushi yace"of course..Allah ya kiyaye hanya"..Prof ya amsa da"Ameen"snn sukayi sallama Sa'eed ya shiga motanshi ya wuce suma suka shiga na Prof suka wuce.











Rano✨





Wnn littafin na kudi ne...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
16
Shopping sosai Prof ya shiga yi musu Aysha tun tana cewa ya kyaleshi haka har ta hakura kawai ta zuba mishi ido...ta lura ba karamin money spender bane shi..baijin kashe kudi sam..yanda yake musu siyayya ko shekara guda zasuyi a school sai haka...Billy dama batayi mgn ba kallonshi kawai take...saida ya dauki duk wani abu da students kamar su suke bukata snn ya wuce counter...bayan yayi payment akai musu packaging wani messenger ya dauki kayan yabisu dashi mota...ya zubasu nan cikin booth suma suka shiga suka wuce...a hankali Aysha ta juya tana kallonshi tace"Babyy.."ya dora hannu kan lips dinshi yace"shushsh ba sai kince komai ba pls"...shirun tayi bata sake mgn ba kaman yanda ya bukata...saida ya tsaya Pizza Hut yayi musu takeaway snn suka wuce Hostel...a bakin gate dinsu yayi parking Billy ta bude mota ta fita bayan ta mishi godia...Aysha kuma sake juyawa tayi tana kallonshi da cutest eyes dinta cikin shagwa6an da yake mutuwar so tace"Baby u shouldn't have done this...i told u munada komai da komai fa"...kallonta yayi for like 5 mins kafin ya dauke kanshi yana sakin murmushi...this girl is damn cute..bai ta6a ganin wanda shagwa6a yakema kyau kaman ita ba..she is just different..sake turo baki tayi hadda bubbuga legs dinta a kasa tace"Baby manaa"...daria ya saki sosai har jikinshi na dan jijjigawa yana daga hannu yace"ohk am sorry...amma ke din ce bakiji baby girl...idan har am important to u zakiyi accepting kayan nan and azaki sake kokarin hanani siyan maki wani abu ba"...turo baki tayi tana kallonshi kaman zatasa kuka...kallonta kawai yake yanajin kamar yakai hannu yaja dan bakin da take turo mishi...tace"shikenan nima daga yanxu duk abunda na gani na siyan maka sai kayi accepting ka yadda?.."gyada kanshi yayi yace"na yadda"..nan da nan ta saki murmushi har dimples dinta suka lotsa...sun dan ta6a hira kadan kafin yayi mata sallama ya wuce ita kuma ta kwashi kayan da suka siyo ta shiga ciki...bata samu Billy a dakinsu ba dan haka tana ajiye kayan ta fita zuwa room 2b da ta jiyo hayaniyarsu a can...tana shiga wata daga cikinsu mai suna Rahma tace"yauwa ga Lamidon nan ma tazo"...karasawa tayi ciki ta zauna tana kallonsu tace"meya faru ake neman Lamido?.."Rahma ta sakw cewa"mgnr bikin Aneesa ne wlh...kinsan munyi mata alqawarin zamuyi selecting music mai dankaren dadi muyi training sbd muyi performing ranar dinner dinta?.."gyada kai Aysha ta shigayi tace"inaga shine dalilin da yasa take nemana...ko daxu naga missed calls dinta ina tareda Baby"...Rahma tace"yauwa to shine mukeso ki za6o mana latest music mai dadi snn ki koya mana rawan da zamuyi tunda dai kaf Hostel din nan ba wanda ta iya wani rawan kirki idan bake ba"...dan murmushi Aysha ta saki kafin tace"to ku da kuketa wnn lissafin Aneesan tace muku 'yan class dinsu baza suyi bane?..kunsan fa 'yan Nursing din nan da shegen iyayi"...wnn karon Billy ce tace"yo Lamido kamar bakisan 'yan class din nasu bane?..babu abinda zasu iya wlh shiyasa itama Aneesan ta nememu kuma bai kamata mu watsa mata qasa a ido ba...dukda ba department dinmu daya ba year dinmu daya and tanada kyakyawan relationship damu sbd haka ba wanda ya kamata ya fitar da ita kunya idan ba mu din ba..koya kukace Midwives?.."da sauri suka hada baki suna fadin"Zancenki dutse hajia Bilisu"..sauke ajiyar zuciya Aysha tayi tace"shikenan sai mu fara this weekend...amma wane time kuke ganin zamuyi selecting evening ko night"...Rahma tace"kam night ai sai yafi sugar Lamido..yanda zamusha sha'aninmu babu wani takura"...gaba daya sukayi na'am da wnn shawara dan haka suka tsaida mgn kan zasu ringa dance training dinsu every Saturday and sunday around karfe 8 na dare.

Tun daga wnn rana suka fara training dinsu kaman yanda suka tsara...every weekend suke taruwa suyi abunsu ba wanda ya sani...a haka suka cinye satin farko na clinical posting dinsu suka cinye na biyu...a cikin sati na uku ne za'ayi bikin and sun gama training dinsu tsaf daidai da anko duk cikinsu ba wadda batayi ba...duk tsawon wnn lokacin Aysha bata sake haduwa da Dr.Bobby ba a Hospital kuma yana shiga ward dinsu Allah ne kawai baisa sun sake haduwa ba shiyasa take cewa Allah ya amsa addu'anta dan koshi yasan yanda ta tsani ganinshi shiyasa suke samun sa6ani dashi.

Yau Saturday za'ayi dinner Aneesa gashi evening duty take kuma ta rasa wadda zata kar6an mata aikin zuwa gobe...jiyama Allah ne ya taimaketa wata daga cikin staff din dakin ta kar6i evening din tayi mata ita kuma tayi mata morning sbd event din jiya kamu ne so tana tashi daga Hospital din ta koma Hostel suka shirya suka tafi...event din yau kuma na dare ne gashi bata san wanda zai rike mata aikin ba...tun daxun take zaune gefen gadonta tana daure da towel sai tufka da warwara takeyi...tsoro takeji kar ta tafi biki wani matsala ya faru ayi blaming dinta...sai wata zuciyar tace mata tayi tafiyarta kawai ai bai zama lallai ita kadai take evening ba so dayar zata rike dakin...da wnn shawara na zuciyarta ta yanke hukuncin zuwa bikinta kawai dan Allah ya gani bazata iya hakura da zuwa dinner nan ba...yanda sukayi training idan bataje ta baje kolin rawan nan ba matsala za'a samu ta sani...Billy data fito daga wanka ta kalleta ganin tayi nisa cikin tunani tace"to ya muke ciki ne Lamido?..kin samu mai rike miki aikin?.."sauke ajiyar zuciya tayi a hankali tace"ashe bani kadai zanyi evening din bama..da akwai wata staff kuma nasan bazaki zuwa ba"...Billy da har ta fara shiryawa tace"har naji dadi wlh dan Allah ya sani idan bakije bikin nan ba bazamu ji dadinshi ba muma...yanxu ki karasa shiryawa kisa kayanki nasan wnn dan rainin wayon bestyn naki ya kusa zuwa...kuma dai kinsan make up da zuwa da wuri mukayi ba bazamu samu mai kyau ba"...wani murmushi Aysha ta saki tareda mikewa zuwa wardrobe dinta tace"tsakanin keda bestyn za'aga waye dan rainin wayo a cikinku...ke kice mishi dan rainin wayo shima ya kiraki da haka..duk zaku gaji da munafurcinku ne ma ku dawo kan hanya"...cak Billy ta tsaya da kokarin saka skirt da takeyi tace"what are u insinuating?.."Aysha ta fashe da daria itama ta fara zura kayanta tace"nothing ooo...am just talking to myself "...tsaki kawai Billy ta saki taci gaba da shiryawanta...ko ten minutes basu kara ba suka gama shiryawa kowa ta dauki abinda take bukata suka fita inda Sa'eed ke jiransu...yana daukansu direct sukayi Zoo road inda za'ayi musu make up.

Mummy ce ta Aunty sumy suka fito compound din gidansu kowacce sanye cikin lace dinta na alfarma sunyi kyau sosai da gani kasan gidan biki zasuje...sai Ilham da Miemie dake sanye cikin nasu lace din suma iri daya da yayi matukar amsarsu Sab kuma ya dade da komawa makaranta...aunty sumy har ta bude motarta da zasuje bikin da ita Mummy tace" sake kira min Bobby Sumayya...wlh idan baije bikin nan ba sai naci mutunchinshi"...aunty sumy murmushi tayi kafin ta sake dialing number Bobby ta mika mata wayan...saida ya kusan katsewa yayi picking Mummy ko jira yayi mgn batayi ba cikin igbo tace"wato ka rantse dai bazaje bikin nan ba ko Bobby?..haka daxu kiri kiri kaki zuwa daurin aure shine yanxu dinner ma kace bakazo ba?.."saida ta bari ta kai aya snn yayi kasa da murya yace"Mummy ina Hospital fa..wlh aiyuka ne a gaba na idan baki yadda ba ga Nur ki tambayeshi"...a takaice tace"bawa Nur din waya"...ba musu ya mika mishi wayan...shima yana amsa before yayi mgn Mummy tace"kana jina Nuru?.."yace"inaji Mummy"...tace"tell him duk ya sake muka bar wurin dinner nan baije sai yaga 6acin raina wlh...kan wane dalili zaiki zuwa bayan yasan yanda nake da uwar yaron nan...snn shima abokinshi ne amma sbd iskanci ya mishi yawa ya wani cemin yana aiki a gabanshi"...Nur yayi kasa da murya sosai yace"kiyi hakuri Mummy zamuzo tare inshaAllah...Allah ya huci zuciyarki"...bata sake cewa komai ba ta kashe wayar...suka shiga motar aunty sumy gaba dayansu suka fita daga gidan...shi kuwa Bobby dafe goshinshi yayi yana dan murzawa a hankali...duk yaji maganganun da Mummy ta fada and baiji dadin musun da yayi mata ba sam...ya mance when last Mummy tayi mishi mgn cikin fushi haka...kuma shi kanshi yasan bai kyauta ba...angon abokinshi ne sosai dan lokacin suna lagos shine babban abokinshi...Mom dinshi kuma aminiyar Mummy ce itama tun a Lagos suke zumunchi har zuwa yanxu basu dena ba shiyasa ma take kokarin hadashi aure da qanwar angon Rayhan shi kuma baya sonta sam...kafin Nur yayi mgn ya dauki car keys dinshi tareda mikewa yace"muje ka rakani wajen bikin nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login