Showing 27001 words to 30000 words out of 231169 words
dinshi dake a hannunshi ba ya karasa cikin dakin da sauri...gefen Mummy ya zauna ya kamo hannayenta hankali tashe sosai yace"Mummy what is happening here?..why are you two crying?.."damke hannunshi Mummy tayi ta juya tana kallonshi tace"your grandfather Bobby..Waziri..idan bawan Allahn nan ya mutu baisan inda kuke ba bazan ta6a yafema kaina ba Bobby..you need to see his condition..he is seriously.."bai bari ta karasa ba ya rungumeta a jikinshi...itama saitayi lakwas a jikin nashi tana cigaba da hawaye...suka hada ido da Anty Sumy dake kallonsu tana hawaye itama..da ido ya tambayeta me yake faruwa ta buda mishi hannu alaman he has no idea...saida yaji kukan nata ya dan tsagaita snn ya sake dagota still yana rikeda hannayenta yace"Mummy kukan ya isa haka please kar bp dinki yayi rising..besides waya fada maki condition da wazirin ke ciki?..how did you know?.."tace"a news na gani wai ciwon nashi yayi worst har sun daukeshi daga Egypt zasu maidashi india..Bobby he is seriously sick inaso kuje ku dubashi idan ya dawo"..cikin 6acin rai tuno abubuwan da suka faru a baya yace"but Mummy why?..why zamuje dubashi bayan bai damu damu ba..bai damu ko muna raye ko mun mutu ba?.."yana rufe baki tace"because he is your grandfather Bobby..komai girman laifin da yayi he is still the father to your Dad and nobody can change that"..ta kamo hannunshi snn tacigaba"do you think if your Dad was alive zaiji dadin yanda kake treating mahaifinshi?..do you think he would be happy if we choose to hide ourselves from them komai girman abunda suka aikata?.."a hankali ya zame hannunshi daga nata lokaci daya idonshi sukayi jajir sbd 6acin rai yace"but Mummy we didn't hide ourselves from them sune basuga daman su nemi inda muke ba..for five long years Mummy idan suna sonmu meyasa basu nememu ba?.."yana rufe baki tace"because he is sick Bobby..sanin kanka ne tun ranan da mahaifinku ya fadi ya mutu bai sake samun lafia ba"...cikin anger daya fara kasa controlling yace"dukda bashida lafia if he really love us..if he really want to see us he could've at least ask one of his selfish and wicked sons to look for us but he didn't and do you known why?..because he hates us..he despise..."bai kai ga karasawa ba yaji saukan kyakyawan mari a cheeks dinshi...ya dafe cheek din da sauri yana duban Mummy dake kallonshi rai a 6ace itama...Anty Sumy ta taso da sauri ta kama hannun Mummy hawaye na wanke fuskanta tace"Mummy take it easy please..kinsan condition dinki Mummy kar wnn abun yasa bpnki yayi rising please"..ta karasa mgnr tana kuka sosai...Bobby da yayi suman wucin gadi sai yanxu ya dawo hayyacinshi...tun da yake zai iya counting sau nawa Mummy ta dakeshi but now she slapped him sbd azzaluman mutanen can..wasu hawaye yaji suna cikowa idanunshi amma ya dake bai bari sun zubo ba ya dora kanshi a shoulder dinta murya can kasa yace"am sorry for hurting you Mummy amma kinsan gaskia nake fada fa..mutanen nan basu ta6a kaunarmu ba Mummy..kema basa sonki amma meyasa kikeso mu sake kai kanmu inda suke bayan duk laifukan da sukayi?.."dago kanshi tayi tareda cupping fuskanshi tace"because they are your relatives Bobby..they are your Family and Family will always be considerd as Family nor matter what..so try to understand me please"...shiru kawai yayi yana yanajin yanda maganganunta suke neman kashe mishi jiki...Anty Sumayya dai na zaune tana kallonsu..itama Mummy ganin tasirin da maganganunta sukayi ta sake yin kasa da murya tace"try and understand Bobby please..ko bamu nemesu yanxu ba dole watarana dalili zai sa mu nemesu shiyasa nakeso mu daidaita dasu tun kafin zuwan wnn lokacin.."shiru ya sakeyi idanunshi lumshe yana sauraronta...ita kuma Mummy ta dan saki murmushin cin nasara snn tacigaba"kaga watarana Aurenku ne zai taso kuma nasan kasan duk dunia babu inda mutum zaije neman aure a bashi ba tareda dangin mahaifi ba..and gaba daya ku ukun babu wanda keda aure gara Sumayya ta ta6ayi hadda yara amma kai da Sabeer baku ta6ayi ba Bobby..dole kuma watarana lokaci zaizo da zamu bukaci suzo su nema muku aure"...sake daure fuska yayi jin ta fara zancen aure yace"indai wnn mutanen ne zasu nemamin aure Mummy wlh na gwammace har in mutu banyi aure..Anty Sumy da Sab kuma duk wanda bazai kar6i aurensu a wurina ba saidai ya hakura"..ta bude baki zatayi mgn ya dora finger dinshi kan bakinta yace"enough talking about them please..yanxu ki samu ki kwanta kina bukatan hutu sbd bp dinki..maganan zuwa dubiyan Waziri kuma Allah ya dawo dashi lafia sai muje"...lokaci daya murmushi ya mamaye fuskanta tace"da gaske zakuje Bobby?..tasan indai ta samu ta shawo kanshi ragowar basuda matsala dama Bobbyn shine mai taurin kain...yace"anything for you Mummy..yanxu dai ki samu ki huta sosai"..da sauri ta shiga gyada mishi kai tace"Allah ya muku albarka"..yace"Ameen Mummy"..Anty Sumy ce ta taimaka mara ta kwanta shi kuma ya juya a hankali ya fice daga dakin zuwa nashi...a gurguje yayi wanka tareda alwala ya fito ya tayar da sallah tubda an idar a masallaci...ya dade zaune yana addu'a kan Allah ya mantar da Mummy mgnr zuwa dubiyan nan dan fa shi har yanxu baiji zai iya daukan kanshi ya kai Gombe ba..har abada gani yake bazai ta6a iya mace kalan rashin imani da suka gwada musu ba har shi wazirin daya kasance kakansu...da kyar ya samu ya mike daga wurin da yayyi sallahn ya fada kan gado ya kwanta...ya runtse idonshi da karfi yana jin duk wani abu daya faru na daow mishi kaman yanxu yake faruwa...bayason yana wnn tunanin amma ya kasa dakatar da kanshi.
ASALIN LABARI...
Our free pages sun kusa karewa fa..keep on subscribing before kuji diff kaman an dauke wuta😹
Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment ta 07063800556.
Rano✨
🤍Dr.BOBBY🤍
By Aysha Rano✨
Wattpad@aysharano22
10
ASALIN LABARI...
Lokacinda Attahir wato mahaifin Bobby yakai ma mahaifinshi Wazirin Gombe mgnr yanason Auren Nadia daya hadu da ita a kano kai tsaye yace bai amince ba sbd kasancewarta ba bahaushiya ba...hankalinshi ya tashi sosai ganin da gaske waziri naso ya rabashi da matar da yafi kauna a dunia..ya jema mahaifiyarshi da mgnr itama ta nuna batada taimakon da zata iyayi masa har tunda mahaifinshi yace ya hakura da ita kawai ya hakura...bai hakuran ba yacigaba da lalla6a waziri yana nusar dashi illar nunama wanda ba yarenku daya ba banbanci...ya kuma nusar dashi cewa har tunda ta kasance musulma kuma yar Nigeria yana ganin ko addini bai haramta mishi aurenta ba...ran waiziri ya 6aci sosai ya kuma ce matukar shi ya haifeshi bazai ta6a amince mishi ya auri inyamura ba...wnn mgn ba karamin daga hankalin Attahir yayi ba...step brothers dinshi da suke ganin waziri ya fifitashi a kansu nan suka samu damar shiga suna cigaba da ingizashi kan kar ya yadda ya amince ya hada jini da inyamurai wnn zuga kuma yayi tasiri a wurinshi sosai...Attahir da yaga bashida wani mafita kuma bazai iya hakura da Nadia ba kai tsaye yaje ya samu kakarshi mahaifiyar waziri knn yayi mata bayanin duk abunda ke faruwa nan kuma ta goyi bayan lallai sai an aura mishi matar da yakeso...hakan ba karamin 6ata ran waziri yayi ba amma ya hakura ba don yanaso ba ya tura aka nemo masa auren yarinyar har Enugu state bisa umarnin da mahaifiyarshi ta bashi kan lallai lallai ya aurama Attahir matar da yakeso idan baiyi haka ba kuma itama zata tsine masa kmr yanda yayi ikirarin zai tsinewa nashi dan.
Cikin lokaci kankani akayi bikinsu aka gama...sbd sanin da yayi cewa yan uwanshi da mahaifinshi ba son auren suke ba sai ya nema mata gida a kano ta zauna itama tacigaba da karatunta...tsakaninshi da Gombe saidai yaje ya gaisa dasu ya dawo kanon ma kuma bai cika zama ba sbd a lokacin yana aiki a Delta state...tun bayan aurensu kuma ko mutum daya baizo daga cikin 'yan uwanshi da sunan yazo ganin matarshi ba...a haka suka dauki tsawon shekara daya bata ta6a ganin wani nashi a inda take ba..a lokacin ta damu sosai da rashin zuwan nasu shi kuma saidai ya bata hakuri yace mata komai zai wuce...ana haka ya samu kira daga waziri kan lallai ya tattaro ya dawo Gombe da zama a cewarshi wai matarshi ke hanashi zuwa ziyararsu yanda ya kamata...baiyi nasa musu ba ko kadan as baison ya sakeyin laifi a wurinshi haka ya tattarata kaman yanda wazirin yace suka koma gidanshi dake cikin Gombe...da farko Nadia taji dadin komawan nasu sbd tana ganin idan tana kusa da yan uwanshi zasufi saurin kar6anta a matsayin suruka sai kuma daga baya ta gane mutanen nan bazasu ta6a kaunarta ba...kyara da tsangwama ba kalan wanda bata gani ba a wurinsu abun har ya kai ko taro sukeyi bata isa ta shiga cikin matan brothers dinshi ba dan zasu yita jifanta da munanan kalamai suna cewa ita inyamura ce..hatta yaransu sunan da suke kiranta dashi knn inyamura...a lokacin data samu cikin Sumayya tayi farin ciki sosai sbd tana ganin kilan idan ta haihu zata iya samun soyayyar waziri dana sauran 'ya'yanshi ko dan sbd abunda zata haifa...mahaifiyar mijinta dama bata ta6a samun matsala da ita ba hakama Munubiya..kawai dai basa iya sakewa su nuna damuwa da ita sosai sbd gudun 6acin ran waziri...duk wnn abun da ake Attahir bai ta6a daga baki yace zaiyi mgn ba sbd yasan ko yayi ba amfani zaiyi ba tunda goyon baya suka samu wajen waziri...'yan uwanshi da dama tuni yasan basa kaunarshi sbd soyayyan dake tsakaninshi da waziri shiyasa suke amfani da wnn damar suna rura wutar tsanarshi cikin zuciyar babanshi...yana sane sarai suke tunzurashi yake aikata duk abubuwan da yakeyi shiyasa bazai taba bude baki yayi complain ba fatanshi daya Allah ya rabashi da mahaifin nashi lafia.
Lokacin da aka haifi Sumayya Attahir yayi farin ciki sosai hakama qanwarshi mahaifiyarshi sun tayashi murna matuka saidai babu daman nunawa sbd waziri...lokacin da ya dauketa ya kai masa ita ko kallonta baiyi ba yace ya fitar mishi da ita a wurin...wnn abu ba karamin 6ata ranshi yayi ba...yana ganin ko arniya ya aura bai kamata ace his own father yayi treating yarinyarshi irin haka ba..abun ya 6ata ranshi matuka...wnn dalilin yasa baiyi shawara dashi kan sunan da zaa sama yarinyar ba kamar yanda sauran 'yan uwanshi sukeyi duk wanda matarshi ta haihu shi ke za6an sunan da za'a sa...baiyi shawara da kowa ba yasa mata Sumayya sunan qanwar Nadia da bata dade da rasuwa ba a lokacin...aikam taji dadi sosai dan bata ta6a zaton zaisa sunan yar uwarta ba.
Haka rayuwa yacigaba da tafiyan musu yau dadi gobe babu har Sumayya ta fara wayo..a lokacin itama sai aka fara tsokanarta da inyamura ko kuma su kirata da 'yar inyamura..wnn abu ba karamin daga hankalin mamanta yake ba amma ba yanda ta iya haka a koda yaushe take bata hakuri tareda fada mata cewa watarana komai zai wuce wnn dalilin yasa ko ina bata zuwa kullum tana gida nane da mamanta idan mahaifinta na gari kuma tana nane dashi...duk wnn abun dake faruwa Nadia bata nuna mishi damuwarta sbd yanda yake iya bakin kokarinshi yaga basuyi lacking komai ba itada 'yarshi.
Bayan Sumayya saida ta dauki tsowon shekaru hudu kafin ta samu wani cikin...farin cikin da Attahir yayi da jin labarin cikin har mamaki ya bata...da dadewa tasan yanada son yara tunda tana ganin yanda yakeji da Sumayya amma yanda yake farin ciki da cikin ko wanda bai ta6a haihuwa ba sai haka...wnn dalilin yasa yake kulawa da ita yanda ya kamata...duk yake gari da kanshi yake kaita antenatal idan baya nan kuma tayi driving kanta...a kullum cikin godema Allah take sbd yanda mijinta har yanxu kiyayyan mahaifinshi dana brothers dinshi baisa ya canxa mata ba..ga kuma budi da Allah ke kara mishi a kullum.
Lokacinda haihuwa yazo mata sai akayi rashin sa'a baya gari...daga ita sai Sumy a gidan gashi tanata kiran wayanshi bai shiga as dama ya fada mata zasu shiga jeji she might not reach him sbd network issue...ba yanda ta iya haka ta kira number wani brother dinshi tayi mishi bayanin halinda take ciki yace mata baya gari saidai ta kira wani...bata hakura ba ta sake kiran wani shi kuma yace zai turo matarshi amma shiru har kusan bayan awanni bai turo kowa ba..gaba daya ta fita hayyacinta as ciwon kara gaba yakeyi sosai gashi kuma batada number wani cikin brothers din nashi sai su biyu ga kuma sumayya daketa faman kuka tun daxu ganin halinda mamanta ke ciki...tayi kokarin kiran munubiya a waya itama bata sameta ba..a karshe dai dole sai sumayya ta aika tayi mgn da wata neigbour dinta ba bata lokaci matar tazo ta taimaka mata suka tafi asibiti...lokacin wajen karfe 9 na dare...suna zuwa aka kar6eta akayi labour room da ita..midwives kusan uku ne kanta suna kokarin taimaka mata amma har gabannin asuba bata haihu ba ga dan karen wahala da takesha...sun kira doctor da yake on call sun mishi bayani yace zaizo kawai ayi masa Cs kafin doctor din yazo kuma sai ta fara fitting(jijjiga)..hankali tashe one of midwives dake kulada ita ta sake kiran doctor ta fada mishi tana fitting yace gashi nan kan hanya ya kusa zuwa...dama tunda suka fada mishi yanda blood pressure dinta yayi rising yasan da kyar idan baiyi leading to preeclampsia ba.
Doctor na karasowa basuyi wasting time ba suka shiga da ita theatre...neighbor dinta data kawota asibitin na tareda Sumayya da aka samu tayi bacci da kyar sbd jiya bata samu tayi sosai ba...before a shiga da ita theatre din kiran mijinta ya shigo wayanta dake hannun matar data kawota...nan tayi picking ta kumayi masa bayanin halinda ake ciki...hankalinshi ya tashi sosai ya kuma ce gashi nan tahowa Gombe yanxun nan...suna gama mgn ya wuce airport ya taki sa'a kuma ya samu flight din Kano nan ya sayi ticket ya zauna jiran lokacin tashi yayi.
Bai samu isowa Gombe ba sai around 10...daidai lokacin kuma ake fitowa da ita daga theatre..baisan time din da hawaye ya cika idonshi ba ganin yanda aka turota kan trolley bed an rufeta da wani green kyalle kaman babu numfashi a jikinta...shiyasa tun jiya yakejin hankalinshi ba kwance ba ashe halinda suke ciki knn.
Kai tsaye akayi moving nata Amenity dake female surgical ward...wanda suka kawota suka dagata daga kan trolley bed snn suka dorata kan bed din dakin suka fita...Nurse din da tayi resuscitating baby ta mika mishi babayn ya amsa da sauri itama ta juya ta fita..ya rage dagashi sai Sumayya a dakin dan matar data kawota kin shogowa tayi tace mishi zata koma gida...yayi mata godia tareda kyauta mai tsoka snn ta tafi...a hankali ya karasa kan wani kujera ya zauna har yanxun yana rikeda babyn a hannunshi...ya sauke idanunshi kan babyn da a kallon farko yaga tsantsan kamannin da yakeyi dashi...lokaci guda wani murmushi da bai shirya mishi ba yayi escaping lips dinshi...soyayya babyn yaji yanaji sosai har cikin jininshi..haka suka hada kai shi da little sumayya sunata kallon babyn daketa mustu mutsu abunshi.
Lokacinda Anaesthesia ya saketa ta tashi daga bacci sai yaga hawaye a idonta...hankalinshi yakai kololuwar tashi ya kuma ce dole ta sanr dashi damuwarta...itama din ba yanda ta iya duk yanda take kokarin 6oye mishi abubuwan da suka faru kasawa tayi saida ta fada mishi...6acin ran da ta gani a fuskanshi bata ta6a ganin irinshi a tattare dashi ba..yanxu kiyayyan da suke masa har yakai ga suyi abandoning matarshi tana labour wanda ba dob taimakon neighbor dinsu ba da kilan yanxu ya rasa matarshi da kuma babyn data haifa..zai iya yafe komai amma banda wnn cin kashin da sukayi masa..wnn dalilin yasa ya yanke shawaran da zaran ta warke zai daukesu su bar Gombe gaba daya tunda baiga amfanin zaman nasu ba.
Haka yake jinyar matarshi shi kadai sai neighbors dinta dake yawan xuwa kullum wasu har suyi girku su kawo...mahaifiyarshi ma bata taba zuwa ba sbd waziri daya hana amma munubiya zuwanta biyu shima duk wazirin bai sani ba take zuwa...saida ta samu sauki sosai yace ta fadi sunan da takeso a sa ma babyn nan take kuma tace sunanshi takeso yasa sbd tana ganin duk dunia yanxu batada wanda ya kaishi sai 'ya'yanta...baiyi mata musu ba yayi mishi hudu ba da sunan Attahir tace zasu ringa kiranshi Bobby.
Daga asibiti ko gidansu basu koma ba suka wuce kano...bayan kwana biyu suka bi flight zuwa delta state inda a nan suka cigaba da rayuwa tareda yaransu.
Bayan shekara biyu suka koma Lagos sakamakon transfer da akayi mishi ya koma Lagos din da aiki...lokacin Sumy nada 6 years Bobby kuma nada 2...tsahon wadan nan shekarun kuma basu sake zuwa Gombe ba saidai yaje shi kadai ya dawo...ana haka Allah yayiwa mahaifiyarshi rasuwa...wnn karon kam gaba daya suka tafi kuma basu dawo ba sai bayan kwana bakwai...har zuwa lokacin kuma daga waziri har sauran siblings dinshi babu wanda ke kaunar matarshi da yaranshi...haka akwa kwashi tsahon shekaru babu jituwa tsakaninsu wanda hatta yaran dukda ba wasu shekaru sukeda ba sunsan akwai matsala tsakanin iyayensu da familyn babansu especially Bobby da yafi 'yar uwarshi riko da kuma zafin zuciya.
Sbd wnn matsalan yasa ko auren qanwarshi da zaayi bai samu labari ba sai gab da bikin...yaji ciwon hakan sosai sbd ganin cewa yarinyar nan batada kowa yanxun daga wazirin sai shi da suke ciki daya da ita tunda mahaifiyarsu ta rasu...haka sukaje Gombe suka dawo bayan kammala bikin.
Bayan shekara goma Nadia da yaranta ke kira Mummy ta sake haifan namiji wnn karon yaron yaci sunan waziri Adam suke mishi laqabi da Sabeer.
Zaman Lagos na musu dadi sosai don basuda damuwan komai kuma babu wanda ke kyamansu unlike Gombe da ko zuwa basu sonyi sbd yanda 'yan uwan Dad dinsu suke treating dinsu.
Bobby nada 17 years ya gama secndary school Sumayya kuma already ta fara karatu a University of Lagos shi kuma Sab yana primary school...zuwa wnn lokacin mahaifinsu yayi kudi sosai dan yana matakin deputy controller General na Nigerian Custom...kai tsaye ya tura Bobby America dan yacigaba da karatunshi a can.
Sumayya na kammala karatu aka aura mata isma'il da suka fara soyayya tun a university aka mikata gidanta dake Kanon dabo...unluckily itama mother inlow dinta bata sonta...dama Isma'il kadai ne danta namiji sauran duk mata ne suma kuma ba son nata suke ba...bayan shekara daya da biki ta haifi