Showing 105001 words to 108000 words out of 231169 words

Chapter 36 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9703

tsala sosai snn ya samu bacci.

Washegari Thursday ranan shiga college dinshi ne amma yana sane yace bazaije ba sbd bama yaso ya ganta ballantana ya karya alkawarin daya daukan ma kanshi...ko a gida bai zauna ba ya shirya ya tafi hospital sbd yasan idan Mummy ta ganshi a gida zata tashi hankalinta ne and shima kanshi yana bukatar ya fita ko dan wani wurin ne yaje at least zai shaki fresh air.
Lamido na shigowa makaranta ta nufi office dinshi kaman yanda yace kullum taje ta gaidashi da safe and ita kanta tanada bukatar yin mgn dashi akn abunda ya faru jiya..ga mamakinta bata sameshi office dinba haka ta koma class tana sake trying numbershi yana shiga amma bai dauka ba...suna fitowa break ta sake komawa office din nashi still baya nan kuma tanata kiran wayanshi har ta gaji bai dauka ba...hankalinta ya tashi sosai tasan yanxu kilan yace zai hadata da daddy...tasan dan abu karami ke 6ata mishi rai amma ita ai bada niyua tayi ba...ranar har suka bar school bata ganshi ba kuma bai dauki wayanta ba...hankalinta ya tashi fiyeda yanda take zato duk sai taji wani iri dan tunda suke bai ta6ayi mata haka ba...a 'yan kwanakin nan da yake mata mutunchi ta fara fahimtan waye shi...sure tasan yanada fada amma kuma yanada kirki and yasan darajan mace...gaba daua jinta take wani iri addu'anta bai wuce Allah yasa kada ya hada da daddy ba.
Washegari friday same thing happens shima har suka tashi Lamido na nemanshi bata ganshi ba wayanshi kuma tun yana kin dauka har ya fara rejecting call din...hankalinta yayi mugun tashi har hakan yaso bata mamaki dan bata taba tunanin zata damu haka ba...da dadewa tasan ta saba dashi amma batasan sabon yakai hakaba sai yanxu...koda yake bataso ya hadata da daddy ne shiyasa hankalinta yaki kwanciya...a takaice saida ta kwashi three days tana nemanshi bata samu ganinshi ba...ranan Sunday tana zaune dakinsu itca kadai saida ta bari Billy ta fita snn ta kira Nur a waya sbd tasan idan sukayi mgn a gabanta zatacigaba da cewa soyayya ne tsakaninta dashi ita kuma bata son haka..yana dauka tace"sir dama ina neman proprietor ne"..Nur yace"baki sameshi a waya ba?.."a hankali tace"baya dauka"..da mamaki Nur yace"ban gane baya dauka ba?.."tace"sir inata kira bai dauka..rejecting call dinma yakeyi"..Nur ya danyi shiru for some minutes before yayi adding"kinyi mishi laifi knn?.."a hankali tace"sir kawaifa kirana yayi bansan shi bane na zata baby ne shknn fa yaketa fushi dani har yanxu..kuma sir ni ina tsoron kar ya hadani da daddyna"..shiru Nur yayi yana saurarnta yana murmushi...addu'a yake Allah yasa itama ta damu dashi koda baikai rabin damuwar da yayi da itaba..saida ya gama smiling dinshi before yace"bani two minustes inyi mgn dashi"..a hankali tace"toh"snn ta kashe wayar...suna gama mgn Nur ya dannawa Bobby kira..ringing biyu ana uku ya daga da sallama...Nur yace"maza ina ka shigane kwana biyu?.."Bobby yace"wlh banjin dadi ne shiyasa kajini shiru..ya aiki".."Alhamdulillah kana gida ne?.."Nur ya tambayeshi kai tsaye shi kuma ya amsa da fadin"no ina hospital"...da sauri yace"ohk gani nan zuwa asibitin yanxu..bakada lafia ne naji muryanka somehow?.."ajiyar zuciya Bobby ya saki before saying"sai kazo din dai kawai"..Nur ya amsa da"ohk"..daga haka kowa ya ajiye waya..sake kiran Lamido Nur yayi tana dauka yace"munyi mgn dashi yace yana hospital yanxu haka..ko zaki shirya in kaiki?.."shiru tayi tana nazari for a while sai kuma a hankali tace"toh.."yace"ki shirya yanxu gani nan zuwa"..ta sake amsawa da"toh.."snn ta kashe wayar..mikewa tayi ta dora dogon hijab akan jessy da straight skirt dake jikinta..tazo fita daga dakin saiga Billy ta shigo ciki..kallonta takeyi from sama zuwa kasa tana ta6e baki tace"ina kuma aka nufa hakia indo?..fushin ya kare knn?.."wani irin harara Aysha ta watsa mata snn ta bangajeta ta fice daga dakin Billy ta bita da kallo baki bude tana cewa"anya kuwa Lamido batada aljanu?.."

A hankali take tafiya har ta iso first gate na hostel din dan haka Nur na karasowa bai karasa ciki ba yayi picking dinta a nan suka wuce...suna hanya da yaga yanda tayi shiru ta zubama spot daya ido yace"duk Dr Bobby ya sanyaki a damuwa koh?.."da sauri ta daga kai tana cewa"eh mana..kumafa ni banga abun jin haushi a mgnr dana fada ba"..murmushi Nur yayi yana girgiza kai cikin ranshi yace"ai bazaki ganiba dama"..daga haka ba wanda ya sake mgn cikinsu har suka iso Freedom...yana gama parking duk suka bude mota suka fita zuwa cikin asibitin...saida sukazo daidai office dinshi taji wani irin faduwar gaba ya risketa..ko wane kalan masifa zai sauke mata oho?...Nur ne ya fara tura kofar ya shiga kafin itama tabi bayanshi...Bobby dake kwance kan sofa ya bude idanu a hankali ya saukesu kan Nur then back to Lamido dake tsaye bayanshi sai faman sunkuyar dakai take...da sauri ya mike zaune yana kallonta da kyau duk idanun nan a waje kaman yaga abun tsoro..yakai hannu yana murza idanuwan nashi wai ya tabbatar ba mafarki yake ba ba kuma gizo take mishi kmr yanda ta saba ba..ganin da gaske itam ce nan tsaye a gabanshi baisan sanda ya wani daure fuska yana kallonta ba...a hankali tayi kasa da idonta tanajin yanda tsatstareta da wnn idanun...kafin tayi mgn ya nuna mata kofa yace"out of my office"..da sauri ta dago tana kallonshi wnn karon shi ya kawar da nashi idon kafin ya sake fadin"i said ki fitarmin daga office"...kafin tayi mgn Nur yace"Haba Bobby"..k kallonshi baiyi ba ya sake nuna mata kofa ita kuma tayi tsaye taki tafia kawai sai ya dafe head dinshi da hannu bibbiyu yana sauke numfashi...ganin haka Nur ya dan matsa kusada ita murya can kasa yace"karki yadda kibar office din nan ba tareda kun daidaita dashi ba..idan yacigaba dayi maki masifa kawai kuka zakisa shknn kinyi maganinshi"..yana gama fadan haka ya juya ya bar office din..jin karar kofa ya sashi bude ido sbd yana tunanin itace ta fita amma sai yaga Nur ne...sake dawo da kallonshi yayi gareta murya can kasa yace"ba cewa nayi kibar min office ba?.."da sauri tace"sir dan Allah kayi hakuri"..girgiza mata kanshi yayi yace"kimin laifi ne kike bani hakuri?.."kwabe fuska tayi zatasa kuka tace"nifa bansan kaine ba Allah"..kallonta kawai yake ganin zata fara mishi kuka bayan ba abunda yayi mata..shi baisan dalilinda yasa ma Nur ya daukota ya kawo mashi ita har nan ba..ajiyar zuciya ya sauke gamida dauke kanshi daga gareta ya sake komawa ya kwanta kan sofa...ita kuma ganin yanda yaba banza ajiyarta sai ta daddage ta rushe da kuka kmr yanda Nur yace tayi..da dadewa tasan bayason kuka tasan kuma shine kadai abunda zatayi ya saurareta...sake runtse ido yayi jin yanda take mishi kuka ya dauki throw pillow ya danne face dinshi dashi wai ko zai denajin kukan nata amma a banza..da dane ya tabbata ko zata shekara tana kuka a gabanshi bazai dameshi ba amma yanxu wani irin rauni kukan nata ke haifar mashi..sai yaga kaman yayi mata wani abun alhalin kuma ba uwar da yayi mata..har cikin zuciyarshi yakejin kukan..kasa daurewa yayi ya mike zaune yana kallonta da idonshi da sukayi red yace mata"wani abun nayi maki da zaki sani a gaba kina kuka?.."cikin kuka tace"sir kaine fa kaki hakura"..yace"cewa nayi ban hakura ba?..ni bakiyimin laifin komai ba kawai kije I don't want to see u"..haushi sosai mgnrshi ya bata dan haka ta juya a fusace zata bar office din garin sauri ta take hijab dinta dake jan kasa aikuwa ta tafi luu saura kiris ta fadi Bobby yayi hanzarin mikewa ya tareta a jikinshi...ta runste ido tana sauke numfashi dan yanda ta gama tsorata ta gama sadakarwa zata jita a kasa sai kuma taji ba haka ba...shi kam kallonta kawai yakeyi kaman an aikoshi...the more ya kalleta the more yake sake ganin asalin beauty dinta wanda da bai cika gani ba sam...zuciyarshi yaji tayi wani tattarewa ta dunkule waje daya sai wani irin harbawa take da mugun karfi...ya lumshe ido ya bude still yana kallon yanda har yanxu ta kasa bude idanunta baisan ya akayi ba kawai shidai yaji ya hadata da jikinshi..rungumeta yayi da kyau yana sauke numfashi a jere kaman wanda yayi race tareda lumshe ido yanajin wani irin mixed feeling tattare dashi...Lamido kuwa mutuwar tsaye tayi jin yanda ya cacimeta sbd tsabar tsorata kasa ko motsi tayi balle tayi kokarin kwatan kanta..Bobby kuwa is far gone sam bai ankara da abunda ya aikata ba saida yaji ta fara mutsu mutsu a jikinshi..sakinta yayi da sauri yakai hannu ya dafe head dinshi tareda fadawa kan sofa...sai sauke ajiyar zuciya yake kmr wanda yayi tsere..he just can't believe what happened..he can't believe he hugged her after all alqawuran daya daukan ma kanshi...runtse ido yayi yana salati dama abunda yske gudu knn shiyasa tun farko yace ta tafi amma taki tafiya...yasan idan yacigaba da ganinta abubuwanda yake 6oyewa suna iya kokarin tona mashi asiri and now see what happened..ya kasa controlling kanshi har yayi hugging nata wanda yakeda tabbacin mutuncinshi ja iya zubewa a idonta...Aysha kuwa shiru tayi ta kurawa spot daya ido kawai tana mamakin abunda yayi mata...gani take kodai aljanu sun shafeshi ko kuma yana fama da serious rashin lafia tunda ga alama nan ta gani yanda yake dafe da kanshi..kuma tasan yana cikin hankalinshi bazai aikata abunda ya aikata ba for she trust him..tasan yanda suke rigima dashi ko wani ya gani tareda ita so ta tabbata bazaiyi hugging dinta for his selfish interest ba..kilan yayi haka ne don ya taimaketa ko kuma sbd wani abu dake dawainiya sam bata kawo wai da gaske sonta yake ba...ganin har yanxu bai motsa ba ta karasa a hankali ta zauna kan one of kujerun office din tana dubanshi murya a hankali tace"sir ai ka hakura koh?.."a hankali ya bude ido yana kallonta..ta wani sake langabewa tace"nace fa bansan kaine ba"..gyada kai kawai yayi kafin ya safe maida eyes dinshi ya rufe..tace"kuma bazaka fadama daddy ba?.."nan ma kan ya daga mata without saying anything..shiru sukayi a office din shi yanajin kaman ya fallasa mata asirin zuciyarshi ita kuma tana tunanin wane irin ciwo ke damunshi da duk yabi ya canxashi haka?..mikewa tayi tana murmushi tace"sir zan tafi"...kai kawai ya sake daga mata ta juya ta fita shi kuma ya sake dafe kanshi yana cije lips dinshi...baisan garin ya yayi loosing control dinshi ba wlh..Allah dai yasa yarinyar nan batayi masa muguwar fahimta ba.






Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
33
Tana fita taga ba motan Nur a parking space dan haka ta kirashi a waya..yana dauka yace mata"Lamido kiyi hakuri wani abu ne ya tosomin yanxu nan aka kirani shiyasa na tafi..kiyi mgn da Dr Bobby nasan zai maidaki"..bata iya cewa komai ba har ya gama bayaninshi ya kashe wayar...kuyawa tayi a hankali ta koma office din nashi...ta tura kofar ta shiga kai a kasa..yana zaune yanda ta barshi ya dago idonshi da kyar yana dubanta yace"what?.."tace"provost ne yace mu tafi tare waishi ya tafi wani wuri"..bai iya cewa komai ba ya mike zuwa wani drawer ya dauki drugs dinshi ya 6alla snn yayi dispensing ruwa yasha maganin dashi...duk wnn abun da yake bai sake kallon inda take ba sbd baison ya sake aikata wani abun..yana gama sha ya dauki waya da keys dinshi yace mata"muje.."ba musu ta juya suka fita daga office din...yasa key ya rufe snn suka wuce parking lot...dirver na hangoshi yazo ya bude mishi kofa as usual yana karasowa ya shiga ita kuma Aysha ta bude front seat zata shiga da sauri yace mata"are u mad?..C'mon come back here"..batace kala ba ta maida kofan ta rufe snn ta bude nan kusa dashi ta shiga..shima driver ya shiga tareda tayar da motar suka fita asibitin...ko a hanya Bobby bai kallon inda take..haka nan yajishi duk a takure sbd kusancinda sukayi da juna..gaba daya bai yadda da kanshi bane a yanda yakeji din nan yasan tsaf zai iya sake aikata wani abun kwatankwacin na dazu shiyasa duk yaki ya saki jikinshi ya wani takure can karshe kaman ba motarshi ba...Aysha kuwa bata ma lura da abunda yakeba don duk a zatonta bashida lafia...shiru motar babu mai cewa komai banda sanyin ac ba abunda ke tashi sai Lamido dake dan motsawa time to time...har suka isa FCNM Hostel ba wanda yace qala..driver na gama parking ya bude motar ya fita ya rage su biyu kadai a ciki...a hankali ta kama handle zata bude kofar sai kuma ta juya tana kallonshi nan kuma taci karo da idonshi a kanta kusan a tare kowa ya janye nashi idon...dan murmushi ta saki tana dubanshi tace"sir nagode..sai anjima"..kafin ta bude motar taji shima a hankali yace"am sorry"..sake juyowa tayi tana kallonshi still da murmushi sai kuma ta girgiza kai tana cewa"bakayi laifin komai ba sir..nasan u are a good person and bakayi kama da irin wnn mutanen ba..so u don't have to apologize"..wani ajiyar zuciya da bai shirya ba ya sauke har dan wani smile yayi sbd samun relieve najin abunda tace...at least dai yasan batayi mashi kallon mutumin banza ba..shi sai yaga yau tayi wani irin nustuwa na musamman kaman dai ba Lamido da kullum suke rigima da ita kan rashinji ba...baisan ko sbd ya fara sonta ne kuma ya fara ganin nutsuwarta ba amma dai yau ta burgeshi fiyeda tunaninshi...bude motar tayi ta fita kafin ta rufe ta sake sunkuyowa tana dubanshi har yanxu da wnn murmushin kan fuskanta tace"thank u so much sir..sai anjima"..kai kawai ya iya dagawa yana kallon yanda murmushin keyi mata kyau kaman wani soko..rufe mishi kofar tayi snn ta juya ta tafi shi kuma hadda su sauke glass yana sake binta a kallo yanajin wani abu kaman maganadisu nason janshi gareta dan haka ya sauke glass din tareda maida kanshi yayi relaxing akan kujera yana cigaba da tunaninta...gaba daya ta mamaye jini da tsokarshi ta yanda bai iya cikakken mintuna 10 ba tareda yayi tunaninta ba...ta 6ata mishi rai jiya amma yau ta faranta mishi matuka..kawai sai yaji dadin yanda yaga ta nutsu da kuka yanda batayi misunderstanding dinshi ba..sai kuma yanda ta damu har saida ta nemo inda yake ta bashi hakuri..she really is amazing and ya tabbata if abubuwa zasu cigaba da kasamcewa haka watarana yana iya samun soyayyarta..tunanin hakan kadai ya sake saukar mashi da wani farin ciki...duk wnn kunci da 6acin ran da yake ciki sai yaji sunyi disappearing..a haka driver ya shigo ya sake tayar da motar suka dauki hanyan gida.

Da fara'a ya shigo cikin gidan saidai mutanen daya gani parlon zaune tareda su Mummy yasa yaji new 6acin rai na neman taso mishi...suna jin shigowarshi suma gaba daya suka maida hankali kanshi kaman dai jiran zuwanshi suke...dauke kanshi yayi ba tareda yace qala ba ya kama hanyan flat dinshi Mummy da aunty sumy suka hada ido kafin Mummy ta mike ta dubi mahaifiyar Isma'il grandma din su Miemie knn tace mata"ina zuwa bari inyi mgn dashi yanxun nan"..daga mata kai matar tayi duk jikinta yayi sanyi..ita gani take kaman shi zai hana su samu yafiyar da sukazo nema wurinsu..dukda already sun riga sun gama mgn har Mummy tace itakam bata rikesu ba dama ta yafe musu itama aunty sumy jin Mummy tace haka itama sai bataja zancen da nisa ba tace ta yafe..su Miemie kuwa ya rage nasu su yafe ko karsu yafe amma sunsan komai dadewa watarana zasu yafe musu tunda duk tsiya dai ahalinsu ne...Mummy na shiga dakin ta sameshi zaune gefen gado ya hada uban tagumi kai kace uwa da ubanshi ne suka mutu..yana ganinta kaman jiran shigowan nata yake yace"Mummy why dan Allah?..why?.."kallonshi kawai Mummy keyi dama tasan za'ayi haka..tun kafin suzo dama tasan rana irin wnn zaizo and gashi yayi reacting exactly yanda take tunanin zaiyi...tasan yanxu ko auren sumayya za'a maida daga wurinshi za'a fara samun matsala sbd wnn dan banzan rikon nashi da bai iya mance abu komai tsahon lokacin daya dauka...karasawa tayi kusa dashi ta zauna tana dan murmushi tace"yau an hadu da Lamido knn?.."tana rufe baki yace"Mummy ba mgnr Lamido ake ba meya kawo mutanen can cikin gidan nan dan Allah?..me sukazoyi mana?.."ajiyar zuciya Mummy ta sauke tareda kamo hannunshi still murya kasa kasa tace"yafiya sukazo nema Bobby..sunaso mu yafe musu dukkan laifukansu na baya kuma nidai na yafe musu..itama Sumayyan ta yafe sbd haka dan Allah kar kace zakayi kokarin causing scene a wurin nan dan Allah"..kallonta kawai yake yanaji yanda 6acin ranshi ke ninkuwa ninkin ba ninkin...kamar zaisa kuka yace"yanxu sbd Allah Mummy duk abubuwanda suka aikata har kun manta knn?..kin manta wulakancin da sukayi mata kawai sbd ba ita sukaso ya aura ba shine yanxu sbd sunaso ya maida ita zasu wani kwaso legs dinsu suzo mana gida..Mummy yanxu ko don sbd su Miemie bazaku duba wnn al'amarin ba..sukayi abandoning dinsu for almost seven years shine yanxu zasu wanizi suce ku yafe musu ku kuma ku yadda dasu?.."yana rufe baki Mummy tace"kaine ya kamata ka hakura kodon sbd su Miemie din..duk yanda muka kai da rashin sonsu fa bamu isa mu rabasu da yaran nan tunda jininsu..snn kuma kowa ya kallesu yasan sunyi regretting abunda sukayi so don me bazamu yafe musu ba?..meyasa bazamu yafe musu ba tunda sukazo har gida neman a yafe musun..kada ka manta ubangiji da kanshi yana son masu yafiya..idan ka kasance mai yafiya sai Allah kaima ya yafe maka..baka tunanin ko don wnn ya kamata a yafe musu?.."shiru kawai Bobby yayi yana sauraronta amma shidai harga Allah baiga dalilinda zaisa kawai daga zuwansu su wani ce sun yafe musu ba..juyawa gareta sai yaga ta daure fuskanta tsaf dan haka yayi kokari ya sassauta nashi tareda yin kasa da nashi muryan kafin yace"Allah ya baki hakuri Mummy..ba haka nake nufi ba"..sassauta nata muryan itama tayi before tace"kuma anjima inason mgn dakai"..a hankali ya amsa mata da"toh"..snn Mummy ta mike ta bar masa dakin shi kuma ya rage kayan jikinshi ya fada bathroom yana sake tunawa da Lamido da duk abubuwanda suka shiga tsakaninsu yau..ya lumshe ido yana sakin wani murmushi daya tuna yanda yayi hugging dinta..he felt kaman ya rike 'yar jaririya sbd taushin jikinta..ga wani qamshi da shidai bai ta6ajin irinshi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login