Showing 171001 words to 174000 words out of 231169 words

Chapter 58 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9687

kai lefe wa Lamido inda shima ya kar6a tareda saura uncles dinta..farin ciki sosai sukayi da ganin uban kayan kowa yana Allah sambarka..daga nan Kuma suka tsaida biki bayan sati hudu da gama council exam dinsu..sosai su waziri sukayi na'am da da ranar sbd ita kanta amaryar tabada buqatar hutawa kafin lokacin bikin nata...dukda Lamido yaso hada bikin dana Hamma Najeeb amma hakan bai yiwu ba sbd wani special assignment da aka turashi yi a Cameroon and bazai gama ba sai bayan shekara daya..wnn dalilin yasa dole suka bar nashi bikin har zuwa lokacinda zai dawo shi kuma Bobby tunda ya matsa lallai so yake ayi nashi sai a fara yinshi kafin zuwan na Najeeb din..lokacin da labarin sa ranar ya iske Bobby Saida yaji ba dadi..yanxu bayan duk wnn jiran da yayi so suke ya kara cinye wani month bayan exams dinsu snn ayi biki?..Sam baiji dadin wnn four weeks din ba..shi da zasu gane ma da dawo da bikin sukayi ya dawo one month din amma ba su sake Kara mishi another month akai ba...yana zaune office dinshi tun daxu sai jujjuya mgnr yake yanajin haushi kmr tasan halinda yake ciki saiga kiranta ya shigo wayarshi..daukan wayan yayi tareda relaxing kan kujera yayi answering call din ba tareda yace komai ba..a daya 6angaren Lamido najin yayi picking ta wani kashe murya tace"partner nah"..dan turo baki yayi exactly yanda take tura mishi nata bakin yace"stop calling me that"..wara ido tayi da mamaki tace"why?..what happened?.."sake marairaicewa yayi kmr zaisa mata kuka yace"wai bakiji ma abunda ke faruwa ba?.."dan rausayar da Kai tayi itama kmr yana ganinta tace"meya faru?.."tun bata rufe baki ba yace"two months..sbd Allah wane hutawa akeso kiyi har na tsahon one month bayan kammala exams..ya kamata aji tausayina mana"..Saida ta bari ya gama haqilonshi snn ta saki wani murmushi tana cewa"Partner its just four weeks fa..before u know it zakaga har lokacin yazo"..girgiza kai kawai yake yana dafa head dinshi alaman she won't understand..ita Kuma jin baice komai ba ta sake lankwasa murya tace"sati hudu ai kaman yau n..."bata karasa ba katseta da fadin"idan kika sake kiramin four weeks din nan zakiga other side of me wlh..a tunaninki four weeks din kmr four days yake?.."dan daure fuskanta tayi tana turo baki tace"nidai kayi hakuri..ai bani nasa maka biki ba zaka wuce a kaina"..shiru yayi kmr bazai sake mgn ba yace"haka kikace?.."with full confidence dinta tace"yes"..yace"ohk then"..sai kuma ya dakata ya shiga sakin murmushi yana shafa gemu zuwa sajen fuskanshi murya can kasa yace"don't worry my turn will soon come..and yes ya kamata ki samu enough hutu sosai for what u are about to face"..dan daure fuska tayi tana muzurai tace"what are u insinuating?.."yana cigaba da shafa uban gashin kanshi yace"nothing oo..it's nothing"..shiru tayi tana ture turen baki sai kace ganinta yake..shi kuma har yanxu bai dena smiling ba ya sake cewa"kullum Ina cewa zakiga other side of me baki ta6a gani ba koh?..to a wnn ranan zakiga the real definition of my other side"..tun kafin ya rufe baki tace"banaso"..yace"badai ni kike cema its just four weeks ba?..zakiga it's just four weeks duk ranan da kika shigo hannuna..a ranan zaki gane Attahir nake ba proprietor ko Dr Bobby ba"..ya karasa mgnr da wani killer smile a fuskanshi..yanda yake mgn kadai says it all domin duk wanda yaga how he's talking yana lumshe ido zai gane da mace ne yake waya..kawai baqin cikin da yake na Kara mishi one month duk yayi disappearing sbd tunawa da wani abu da yayi..hakan kuma yasa yaketa sakin murmushi yana shafa kai kmr wani sabon kamu...Alhajia indo kuwa jikinta ba karamin sanyi yayi da wnn kalaman nashi ba..ta lura fa dama these days wani sabon iskanci yakeji dashi haka zaiyita 6aro mata mgn yana sata jin kunya shi kuma ko a jikinshi..ita bata ta6a sanin there is this side of him ba sai yanxu..duk ya wani dawo mai dabi'un 'yan iska shiyasa yake bata tsoro ma...jin yanda tayi dif kmr bata jinshi ya sake relaxing yana lumshe ido kafin yace"baby"..banza tayi mishi tana turo baki kmr yana gabanta..ya sake cewa"partner"..still taki tankashi kawai sai ya saki murmushi yana girgiza kai yace mata"duk wnn abun fa love wasa nake maki..ke bakisan wasa bane?.."murguda baki tayi tana sake dinke fuska tace"ba wani wasa..Allah idan kacigaba da tsokana na fasawa zanyi"..Bobby ya dan wara ido yana sake murmusawa yace"baby idan kika fasa kuma ai mutuwa zanyi"..tace"to ka dena tsokana na nidai"..tun kafin ta rufe baki yace"na bari..ban karawa believe me"..ajiyar zucia ta sauke kafin tace"shknn"..ajiyar zuciyar shima ya sauke tareda lumshe ido yana sake relaxing kan seat dinshi yace"I..love..you..and i can't wait to..marry you".

Bayan sati hudu...














Rano✨






Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
53
Bayan sati hudu...
Yau Friday sukayi final laper dinsu and tun da suka fito daga exam hall around 11 kowa yaje ya sake shiri cikin sign out shirts da sukayi iri daya kowa nashi dauke da sunanshi a jiki..hall da suka saba gabatar da celebrations aka bude musu suka shiga nan sukaita celebrating kammala exams dinsu saura fitowa results kuma..har dj suka kira yaketa playing musu waqoqi iri iri masu rawa nayi masu daukan pictures ma sunayi...a extreme end of the hall Lamido zaune tana kallon su Billy daketa dirkan rawa kan stage da sunga wani da bai musu signing jikin shirts dinsu ba zasu bar rawan suje ayi musu signing din suma suyima wanda basuma ba snn su sake komawa dance floor..haka suketa yi tun daxun ita tana nan zaune tana kallonsu..kawai tunanin yanda zasu kwashe da Bobby takeyi idan yaga shirt dinta da signing musamman ma signing na namiji sai kuma rawa Kiri kiri da takeso tayi amma sbd tsoron kishi irin nashi ta kasayi..har sha'awan Billy da sauran colleagues dinta dake wurin takeyi sai taji inama ba'a college din nan yake ba itama da ba abunda zai hana mata enjoying wnn ranan amma yanxu bata isa ba...Billy ce ta nufo inda take zaune da sauri tana zuwa ta Mika mata wayanta dake hannunta tana cewa"Ur Hamma wants to speak to u"..ba musu Aysha ta karbi waya suka fara mgn dashi ita Kuma Billy ta dauki bottled water dake ajiye nan kusa da ita ta zauna tana sipping ruwan tana sauke numfashi...after like 4 mins suka gama mgn da Hamma Aysha ta shiga mikawa Billy wayanta kafin tace"Billy dan Allah zan danyi rawa ko kadan ne kinga fa ba zuwa zaiyi ba nasan yana hospital wlh"..girgiza kai Billy ta shigayi tace"aah fa ba ruwana Lamido bazaki hadani da wnn rigimammen mijin naki ba..haka nan kisa yazo yana tsareni da idon nan nashi da dadine dasu ba"..langa6ewa tayi tana kallonta kmr zata sa kuka tace"yanxu knn kinfi sonshi akaina Billy?..dan girman Allah in dan shiga inyi Allah ba dadewa zanyi ba"..girgiza Kai Billy ta sakeyi saidai kafin tace wani abu Aysha da ta riga tazo wuya sbd haushi tace"ko baki yadda ba sai nayi wlh saidai kije kiyita fada masa din i don't care"..daga haka ta mike zata bar wurin Billy ta dawo da ita da sauri tareda mikewa itama tana kallonta tace"amma banda signing kou?..kinsan fa halin mutumin nan Lamido banson kuxo kuna samun matsala akan haka"..kwace hannunta Aysha tayi ta bude bag dinta ta fito da wani shirt din sabuwa sak irin na jikinta tana nunawa Billy rigan tace"indai ba kece munafukar da zaki fada masa ba ba yanda za'ayi ya sani..ana gama min signing kafin mu fita hall din nan ma zan cire in saka wnn"..kallonta kawai Billy keyi ita wnn abun bai gamsheta ba..a yanda taga yake mgn jiya tasan wlh da kyar idan basu samu matsala kan haka ba tunda he made it clear cewar bayason wnn abun...ganin har ta kama hanyan dance floor ta daga shoulder alaman ba ruwanta snn itama ta bita a baya...tana hawa kan stage din sai kuma ta juya zata sauka da sauri colleagues dinta suka kamata suka maidata wurin..daya daga cikinsu taje ta samu dj tace mishi class rep dinsu ta shigo don haka ya samu Waqar favorite dinta mai azabar dadi yayi playing musu zasu cashe yanxun nan..dj kuwa ba musu ya sakar musu waqa mai dadi nan suka shiga rawa suna janta wai itama dole sai tayi..tun tana nokewa tanajin tsoro har dai daga baya ta saki jiki ta dilliqi rawar ta son ranta..at that moment gaba daya mantawa ma tayi da wani warning dinshi na jiya kan baiso tayi rawa and bai yadda wani ya taba rigarta da sunan signing ba..enjoying dinta takeyi kawai tana cashiya kmr ba Lamido ba...saida tayi me isarta snn ta fara zuwa ana mata signing jikin shirt dinta duk wanda ta gani da sauri take zuwa wurinshi yanayi mata zatayi sauri ta rufe wurin da kimono din jikinta wai duk sbd kada ya samu labari idan yazo...a takaice har after five suna cikin hall din nan suna abu daya..ganin yamma ya farayi hankalinta ya dawo jikinta tasan yanxu duk inda yake ya kusa shigowa college din don haka baki alekum ta fita daga cikin hall din zuwa wani dan small room dake kusada wurin ta shiga ciki da sauri ta zare kimono dinta tana kokarin cire sign out shirt din kawai taga mutum a gabanta..batasan sanda gabanta yayi wani irin yankewa ya fadi ba..lokaci daya ta saki rigar tana yarfa hannayenta hawaye har ya ciko eyes dinta tace"wayyo Allah na"..kala bai ce mata ba sai kimono daya dauka ya mika mata..da sauri ta kar6a ta maidata jikinta tana kallonshi..tana gamawa ya kama hannunta a fusace suka fita daga room din..direct office dinshi ya nufa da ita mutane nata kallon yanda ya riko hannunta amma kobi ta kansu baiyi ba don abunda ya dameshi kadai ma ya isheshi..yana bude office din ya turata ciki snn shima ya shiga ya maida kofar ya rufe ya shiga kallonta da eyes dinshi da sukayi jaa sbd bacin rai...kuka sosai ta fara tana yarfe hannayenta shi Kuma baice mata komai ba sai tsareta da yayi da eyes dinshi da taji sun dawo mata eyes dinshi data sani a baya masu sanya mata firgici da nutsuwa ba tareda ta shirya ba..da sauri ta matsa zuwa kusa dashi ta dan daga Kai tana kallonshi sbd yafita tsayi sosai kawai sai ya lumshe eyes dinshi don bazai iya juran kallonta a haka ba karyar mishi da zucia zatayi...ba zato ba tsammani kawai yajita fada jikinshi ta kankameshi tana sakin wani kukan da koshi yasan na shagwa6a ne kawai muryanta na rawa tace"am so..rry"..lumshe idanu ya sakeyi yana sauke ajiyar zucia..baisan ya zaiyi da rashin jin Aysha ba amma ko Allah yasan ba karamin wahalar dashi take ba..bude idanunshi yayi tareda dagota daga jikinshi ba tareda ya kalleta ba yakai hannu ya bude kimono dake jikinta nan take uban signings din dake jikin riganta suka bayyana..kallonsu kawai Bobby keyi ranshi na sake 6aci..duk Wanda yayi signing din nn yasan ya ta6a masa jikinta Kuma shidai Allah ya isanshi wlh..da iya class mates dinta ne ma da sauki tunda mata ne amma yasan baza'a rasa 'yan nursing a cikin Wanda sukayi mata signing din ba...runtse Ido yayi da karfi da yaga har wurin chest dinta saida akayi signing..ya juya bayanta nan ma yaga har waist dinta signing ne kaca kace kawai sai ya juya tareda zaunawa kan sofa yana date head dinshi da yaji kaman zai 6alle sbd ciwo..karasawa tayi ta zauna kusa dashi tareda dora kanta a shoulder dinshi tana hawaye sosai tace mishi"dan Allah kayi hakuri partner..zaka iya punishing dina da any kind of punishment amma don't be mad at me plss..am sorry"..hannunshi yakai a hankali yana shafa kanta sbd yanda kukan ke ta6a zuciarshi kwarai...sake langabewa tayi tana sauke numfashi..shi Kuma murya can kasa yace mata"you danced right?.."shiru tayi tana rarraba ido kmr munafuka shi Kuma ya saki murmushi mai ciwo dama ya tambaya ne wai ko hasashenshi zai zama ba gaskia ba amma shirun da tayi ya tabbatar mishi da cewa tayi rawa..zafi sosai yakeji cikin ranshi Wanda inda zai fito dashi ya nuna mata yanda yakeji kilan tsorata zatayi ta gudu shiyasa yake kokarin dannewa kawai..zuwa yanxu ya fuskanci zafi da takura babu abunda zai kara mata sai kangarewa so it's better ya fara binta da lallami da nasiha kilan Allah yasa ya dace..sake Kai hannayenta tayi ta zagaya bayanshi zuwa stomach dinshi dasu dukda ba gama zagayawa sukayi ba tace"partner am sorry please"..Kai kawai ya iya gyadawa yana shafa kanta a hankali yana karanta duk addu'an da yazo bakinshi..inshort sun duki lokaci mai tsaho a haka tana bashi hakuri kafin ya samu saukin abunda yakeji..Saida ya dan nustu snn ya shiga nata nasiha sosai Wanda har kusan kuka yasata sbd yanda yake mgnr shows ba karamin zafin abun da tayi yakeji ba..bata bar office din ba saida ta tabbata he is no longer upset with her snn yayi dropping nasu a hostel da kanshi bayan sun sha love dinsu.
Washegari da safe bayan sun gama 'yan koke kokensu na rabuwa da juna Hamma Najeeb yazo ya kwashesu dasu da komai nasu sai jihar Gombawa diban fari..ba'a kwana daku ba wai sai a tashi daku.
Wnn knn..

Kwananta biyu da komawa small mom dinta tazo ta dauketa suka wuce Bauchi wai za'a fara mata gyaran jiki and stuffs dai da akeyi na gyaran amarya..dukda Ammi bataso haka ba sbd zaman Fiddausi da Aysha a cewarta ba abunda yake karawa sai lalata Ayshan sbd ba wani fada take iya mata ba..amma da daddy yasa baki haka nan ta hakura suka tafi Bauchin bada son ranta ba..ita fa so tayi a dan zaman nn da zatayi ta gyara mata zama sosai ta yanda bazata je gidan miji tana basu kunya ba don tasan halin kayarta tsaf har yanxu ba cikakken hankali ne da ita ba.
Tunda ranan da suka isa Bauchi ko kofar gida bata sake fitowa ba wai idan ana gyara ba'a son shiga rana...mai gyaran jiki sosai auntyn nata ta dauko takanas take gyara mata ita ciki da waje don komai daya danganci gyaran amarya ana mata and ita da kanta ta fara ji da kuma ganin canji a jikinta..biki ya rage saura 3 weeks Billy ta dawo gidan aunty Fiddausi da zama sbd shirye shiryen biki da suka fara ka'in da na'in...events sosai Billy suke shiryawa ita da Provost don sune Organizers na komai da zasuyi a bikin..dama Kuma halinsu ya kusa zuwa daya dan haka suketa planning events kala kala hadda na shirme dan kusan week guda za'a kwashe ana bikin..ko Lamido da take mayyar biki Saida tace ma Billy events din sunyi yawa da taga uban abubuwan da suka rubuta za'ayi amma sai Billy tace mata babu ruwanta nata kawai zuwa ne amma ko event guda baza suyi cancelling ba.

Shirye shirye sosai akeyi ta kowane 6angare..baga ahalin Lamido da Waziri ba..ba Kuma ga ahalin hajia Mummy da aunty Sumayya ba...bride and groom dai nasu Ido ne kawai almost komai na bikin shirya musu akeyi so nasu kawai suyi attending ne..lokacinda aunty sumy ta fada mishi events da zasuyi cewa yayi a rage that shi bayason big wedding wai gajia zaiyi ma da attending events din..amma aunty sumy tace ko event daya bazasuyi cancelling ba idan yaga dama kar yazo su zasuyi abunsu tareda amarya...murmushi kawai ya iya sakar mata ya wuce flat dinshi yana dialing number amaryarshi da rabonshi da sanyata a ido tun ranar da tabar Kano..kiri kiri yanason zuwa ya ganta yarinyar nan ta hanashi wani wai aunty Fiddausi bazata bari ba which he knows she's lying of course..kawai shima sai ya rabu da ita cikin ranshi yace zaiyi maganinta ne idan ta shigo hannunshi..ganin har Kiran ta katse bata dauka ba ya ajiye wayar ya shiga wanka don dawowarshi knn daga clinic.

Aunty Fiddausi ta shigo dakin da take kwance hannunta rikeda bottled water mai sanyi sai sachet na inflanil a hannunta ta karaso ciki ta zauna gefen Aysha dake kudundune cikin bargo tace"oya mike ki samu Kisha maganin nn yanxu zaki samu sauki inshaAllah"..dan bude Ido Aysha tayi tana ganin magani a hannunta ta wani yatsine fuska tana marairaicewa tace"aunty dan Allah kiyi hakuri da kanshi zai dena wlh"..a fusace aunty Fiddausi tace"kinsan Allah zan kira Adda in fada mata wnn iskancin da kikeyi..Shan magani kawai ya gagareki kuma don walakanci har likita na kira tazo ta dubaki kememe kina hana ta maki allura yanxu maganin ma Kuma bazaki Sha ba sbd kin maidani yar iska"..sake marairaicewa tayi tana duban small mom din tata tace"aunty na rantse da Allah idan nasha bakina sai yayi sati yanamin daci..shi Kuma allura fa kinsan dai yanda yakemun ba saina fada maki ba"..a fusace aunty Fiddausi ta ajiye drug da ruwa dake hannunta tace"sai kiyita zama da ciwonki har bikin naki yazo ni ba ruwana"..daga haka ta mike tayi ficewarta daga dakin..a waje suka kusa karo da Billy zata Kai mata tea tasha..ganin yanda ta fito rai a 6ace Billy tace"bata Sha maganinba Koh?.."aunty Fiddausi tace"inafa tasha..yarinya dai shege taurin kai kmr mutanen farko"..girgiza kai Billy tayi tace"bari in kai mata tea din nan inzo aunty nasan wanda ko bataso zai iya mata allura"..daga haka ta wuce dakin ta dire mata tea din gabanta ko kallonta batayi ba ta juya ta fita Aysha ta bita da harara kmr Idonta zasu Fadi kasa..kawai batada lafia ma bazasu daga mata kafa ba kowa sai yayita nata masifa kmr an gaji da ita...Billy na fita ta iske aunty Fiddausi zaune a parlor samun wuri tayi itama ta zauna snn ta dauko wayanta tana searching contact dinshi tace"aunty proprietor ne kadai zai iya mata allura komai isakancin da zatayi"..kallonta aunty Fiddausi tayi kafin tace"sai Kuma mu tasoshi tun daga Kano sbd yazo ya mata allura Bilkisu"..Billy tace"zaizo wlh aunty shima nasan da kyar idan ba son ganinta yake ba yanxu..rabonshi da ita fa tun da mukayi graduation"..ajiyar zucia aunty Fiddausi ta sauke tana cewa"to kirashi ki fada mishi yazo yasan yanda zaiyi da ita nidai..dan wlh idan ta kaini bango ubanta zanci babu ruwana da ita amarya ce tunda batada mutunci"..Billy na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login