Showing 144001 words to 147000 words out of 231169 words

Chapter 49 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9698

first ka fara kwantar da hankalinka ka samu sauki tukunna"..tun kafin ta rufe baki ya shiga girgiza kai still idonshi a kulle yace"bazaki ganeba Mummy..aure za'a mata..aure zatayi ta barni..kakanta yace ya za6ar mata miji Mummy bazan iya cigaba da zama garin nan ba mu koma kano please!."kuka ne sosai yaci karfin Mumny dake rikeda hannunshi ta kasa cewa uffan...Aunty Munubiya kanta saida kwalla ya cika mata ido..karasawa tayi kusa dashi bayan tayi dropping basket dake hannunta tace"dama sbd ita kazo Gombe ba sbd grnadfather dinka ba?..kana tunanin idan kuka tafi yanxu waziri zaiji dadi ne?.."mikewa ya shiga kokarin yi zaune da sauri Mummy ta taimaka mashi ya jingina da pillow..har yanxun ya kasa bude idanunshi don yana budewa zafin da yakeji cikinsu ke sake karuwa..yakai duk hands dinshi ya dafe forehead dinshi dasu cikin muryanda ke nuni da tsagwaron damuwar da yake ciki yace"Aunty bazan iya zama ba..bazan iya zama bayan nasan zata auri wani ba"..yana rufe baki Aunty Munubiya tace"to idan ka koma kanon kana tunanin ka dena ganinta ne?..karewa ma naga a college dinka take karatu kuma hutu na karewa zata koma tunda ba gamawa tayi ba shima sai kace zaka bar college din sbd ita?..get a grip of yourself mana Bobby..be a man inshaAllah Allah bazai barka haka ba"...sauraronta kawai Bobby keyi without saying anything..bazasu gane bane..bazasu ta6a gane halinda yake ciki ba shiyasa duk zasuyi wnn maganganun...a yanda yakejin zuciyarshi yasan dab take da samun matsala shi kuma baison yacigaba da zama yana dorawa Waziri damuwa kada hakan yayi sanadin da hawan jininshi zai sake tashi...gaba daya Gomben ta fita a ranshi and matukar ba komawa Kano yayi ba yana iya samun matsala...da za'a taimakeshi a cireta daga college din ma shi da yafi mashi yanda idan ya tafi ya dena ganinta kenan for good...sake komawa yayi ya kwanta zuciyarshi na cigaba da bugawa da gudu...Mummy takai hannu tana shafa uban gashin kanshi da bai cika askewa ba tace"ko tea bazaka sha ba Bobby?.."gyada mata kanshi yayi alamar bazai sha ba..da sauri Aunty Munubiya tace"aa ya kamata kaci wani abun gaskia..doctor yace kafin medication ya zama lallai kaci abinci"..banza kawai yayi da ita idonshi rufe don gani yake bazata gane halinda yake ciki ba...da kyar da sidin goshi suka samu yasha tea din snn ya sake komawa ya kwanta before time din medication.
Washegari ma haka ya tashi ba walwala dukda cewa fevern da yakeji ya sauka amma har yanxun bai dena ciwon kai da jiri ba...tunda ya tashi baiyi mgn ba duk yanda aunty sumy taso yace wani abu kin kulasu yayi sai binsu da yake faman yi da ido kmr bai sansu ba..fuskan nan nashi kuwa a tamke kamar na shanu shi kadai yasan abubuwan da yakeji a cikin ranshi...da yamma sai ga Lamido yazo dubash tareda daddy da baima san yana garin ba saida Lamido yace yazo ya rakashi duboshi...mamaki sosai ya kama daddy ganin yanda ya koma cikin lokaci kankani dukda cewa a haka kokari yake yaga bai nuna musu asalin damuwar da yake ciki ba..da yake sun samu waziri a asibtin basu suka tafi ba sai dab da magrib...daddy na zuwa gida yace Ammi ta shirya ita dasu Aysha yanaso Najeeb ya kaisu asibiti su dubo jikinshi a daren...haka kuwa duk suka shirya suka fita inda Hamma ke jiransu...tana ganin shine a motar ta wani hade rai tana muzurai..baice mata uffan ba ya bude motar Ammi da su Husna suka shiga baya aka barta a tsaye alamun ita suke nufi ta dhiga front seat knn...budewa tayi ta shiga tana wani kumbura kamar kububuwa..shikam Najeeb daria ma abubuwan nan nata suke bashi wlh...wai shi Maama takema wnn iskancin kawai sbd ance za'a hadashi aure da ita...ya tada motar suka tafi kuma har sukaje asibiti ba wanda yayi mgn cikinsu sai Yusra daketa damun Ammi da tambaya kaman 'yar jarida...bayan ya gama parking Ammi ta bude mota ta fita yaranta sukabi bayanta...itama hannu takai zata bude yayi saurin danna lock yana kallonta...juyawa tayi tana dubanshi fuskan nan a kwa6e tace"Hamma meye haka?..ni ka budemun mota in fita"..tana gama fadin haka sai kuma ga hawaye ya shiga silalowa kan fuskanta shidai yayi shiru yana kallonta baice komai ba...kamar wanda aka tsikara ta dago tana kallonshi tace"Hamma wai dama kana sona ne?..meyasa Lamido ke cewa zai hadani aure dakai?..dan Allah Hamma kayi wani abu bazan iya auranka ba wlh"..matsawa kusada ita ya kamo hannunta yana cewa"ki nustu mgnr da zamuyi knn amma ki tsaida kukan nan first"..ba musu ta hadiye ragowar kukan tareda kai hannu tana goge hawayenta...saida ya tabbata ta dena kukan snn yace mata"haka kika tsaneni dama ban sani ba?.."da sauri ta hau girgiza tace"ni ban tsaneka bafa"..yace"idan ba tsanana kikayi ba meye wnn?.why kike bani attitude sbd ance zan aureki?.."langabar da kai tayi tana dubanshi a hankali tace"Allah ban tsaneka ba Hamma..kawai ban ta6a picturing kaina matsayin matarka ba..kallon dan uwa na jini nake maka Hamma ba kallon mijina ba"..sake kama hannayenta yayi ya rike shima yana dubanta da kyau yace"na sani Maama..hasali nima kallon qanwata nake maki ba kallon matar da zan iya aure ba amma ya zamuyi?..idan kaddaranmu yazo a haka dole haka zamuyi hakuri mu kar6eshi tunda bamuda yanda zamuyi"..hawaye na sake taruwa idanunta tace"kai bakada wadda kakeso ne?.."shiru yayi yana kallonta kmr bazaice komai ba sai can kuma yace"inada..akwai wadda nakeso Maama amma bankai ga sanar da ita ba wnn mgnr na Lamido ya 6ullo"..da sauri ta sake rike hannunshi tace"then muyi mgn da daddy plss..ka fada mashi kaima kanada wadda kakeso nasan inshaAlla bazai rasa yanda zaiyi ba"..hannu yakai yana goge mata hawaye yace"naji i will think about it amma yanxu ki bari mu shiga muyi dubiyan nan tukun..kada su Ammi su gama bamu je ba"..da sauri ta shiga gyada kai tana karasa hawayenta tace"toh na dena"..murmushi ya sakin mata tareda bude motar ya fita itama ta fita suka nufi cikin asibitin...saida ta kira Ammi ta fada mata room number snn suka isa zuwa dakin...Najeeb ne ya fara shiga snn itama ta shiga kai a kasa...Bobby idonshi ke kallon kofa tun daxu yana jiran shigowanta kasa dauke idanunshi yayi a kanta..yanajin zuciyarshi tayi wani tsalle ta dire sbd ganinta da yayi tareda wanda yasan shi zai aureta baisan lokacinda ya runtse ido yana salati sbd zafin da yaji ba..ba kowa dakin sai shi kadai don haka Hamma ya kara karasawa kusa dashi yana dubanshi da murmushi yace"sannu ya jikin"..kai kawai Bobby ya iya daga mash ba tareda ko bude idonshi yayi ba..a yanda yakeji yasan tsaf zai iya kasa controlling anger dinshi na ganinsh da yayi tareda ita shiyasa ko idan yaji budewa balle yayi mashi kallonda zai jefashi tunani...Najeeb bai kawo komai ba a tunaninshi ko jikin nashi ne shiyasa daya gama dubashi ya juya ya fita daga dakin...wani irin shiru dakin ya dauka har suna iyajin numfashin junansu...kallonshi kawai take ganin yanda ya kara haske ga dan rama da yayi sai taga kaman karo mishi kyau akai don sosai taga yau dai yayi mata kyau...shiko bude idanunshi yayi jin har yanxu batace komai ba sai gashi karaf idanunsu sun sarke cikin na juna..da sauri ta dauke nata tana zare ido sbd wani irin abu da taji ya shiga cikin idanun nata har zuwa zuciyarta..bata taba jin irin wnn game dashi ba tadai san for sure idonshi na sata jin wani iri amma ba irin wnn feeling din bane kwata kwata...lumshe idon ya sakeyi kafin ya budesu fes a kanta yanajin kmr ya mike ya sanyata a jikinshi ko zai samu saukin wnn ja'iban da yake ciki...idanunshi sun kada sunyi jajir ga zuciyarshi daketa faman bugawa da mugun sauri...ido ya sake lumshewa yanajin yanda gaba daya ganin nata ya dirar mishi da wani kasala na musamman...wani irin weird feeling yakeji irin wanda bai ta6a ji a kanta ba...addu'a ya shiga karantowa a ranshi wai ko feelings din zasu ragu amma kmr sake hankado mishi su akeyi...sun dauki kusan mintina biyar a haka kafin ta karasa kusa dashi a hankali har yanxu bata bar kallon face dinshi ba tace"ina yini"..bai bude idonsh ba kuma bai amsa ta ba..ta sake cewa"Sir ina yini"..still bai amsa ba sai takai hannu ta dora kan nashi da nufi ta jijjagashi wai ko bai jita bane aikuwa ya kama hannun nata da sauri kmr magnet ya damke cikin nashi...wara ido tayi tana kallonshi da mamaki ashe idonsa biyu dan rainin hankain...kokarin kwace hannunta ta shiga yi nan take yaji wani karfi yazo mishi kawai sai ya mike zaune yana dubanta da idonshi da ya bata tsoro sbd jajir din da yayi...kallonta yakeyi cikin ido eyes dinshi na shinning as a result of hawaye da cikoshi..tunda abun nan ya faru sai yanxun tears suka samu damar zuwa idanunshi amma jiya sai zafi da idon suke ba hawaye ko kadan...kallonshi itama take tana karantar abubuwa da dama cikin idanun nashi wanda bata ta6a tsaiwa ta karance su ba ada..abubuwa ne masu wuyar karantuwa snn kuma masu wuyar fassaruwa amma dukda haka taji ta kasa dauke idanunta a kanshi...hawayen dake idanuwanshi yayi kokarin maidawa kafin yace"can..i hug..u plss?.."wara ido tayi tana kallonshi without saying anything..voice dinshi na rawa ya sake cewa"for this once Aysher plss..mutuwa zanyi"...lokaci guda itama hawaye suka ciko idanunta ba tareda tasan dalilin su ba...ganin kallon da take mishi ya janyota jikinshi tareda wrapping dinta da hannayenshi ya saki ajiyar zucia mai karfin gaske...tana iya jiyo yanda heart dinshi yake bugawa da mugun sauri nan take hawayen dake idonta suka gangaro fuskanta...Bobby ko wani irin sanyi yaji yana ratsa tun daga kwakwalwarshi har zuwa tafin kafafunshi..idanuwasnhi rufe yayinda hawayen dake ciki suka wanke mishi fuska..ji yake inama zasu dawwama a haka shikam daya gama samun komai na dunia...a hankali yayi breaking hug din tareda kamo fuskanta da hannayenshi ya hada da nashi fuskan still idanunshi rufe saidai ba hawaye yakeyi ba yace mata"ina sonki sosai Aysher..morethan any other thing..you are my whole world..my whole heart..you are my.."kasa karasawa yayi ya sake runtse ido sbd wani abu da yaji ya tokare mishi wuya..sake manne face dinshi yayi da nata yana kallon cikin idonta yace"i will die without you.. i will die for sure"..ya karasa yana sake lumshe ido at the same time yana sauke numfashi...Lamido kuwa kuka ta fara wiwi kai kace uwa da ubanta ne suka rasu suka barta a doron kasa...ita kanta kuma bazata ce ga dalilin kukan ba amma for sure tasan akwai tausayinshi sosai a cikin ranta...ta kuma san da gaske yana sonta fiyeda komai kmr yanda yace...sake rungumeta yayi yana shafa bayanta yace"sorry i made u cry...i just feel like saying what i have in mind but am sorry"..girgiza kai ta shigayi alaman ba reason din kukanta knn ba tace"aure za'ai min"..yace"i know"..tace"Hammana zan aura"..nan ma kai ya sake gyadawa yace"i..know"..a hankali ta bude ido tana kallonshi cikin sigar lallashi tace"am sorry"..yace"u don't have to..i forgave u already"..kai ta shiga gyadawa tana sakin smile da wet face dinta tace"thank u..thanks for loving me"..kallonta kawai Bobby keyi yanajn wani abu na zagayawa cikin jininshi and he couldn't help it saida ya kai lips dinshi goshinta ya manna mata peck a wurin snn ya saketa tareda komawa kan gadon ya kwanta yana fadin"thank you"...kallonshi ta tsaya yi tanajin wani bakon abu na zagayawa cikin jikinta...karasawa tayi kusa dashi idonta akan fuskanshi tace"Allah ya baka lafia..zan tafi"..kai kawai ya iya daga mata tareda dan sakin murmushi wanda baikai zuci ba...saida ta juya zata tafi ya bude ido yana kallonta har ta fita daga dakin snn ya sake lumshe idon tareda kai hannu yana dafe saitin heart dinshi dashi.

Kwananshi biyu a asibiti aka sallameshi a ranar kuma ya dage sai sun wuce kano waziri yace bazasu tafi a ranar ba.. dole suka bari the next day shima kuma bada son waziri ya bari suka tafi ba..ba yanda zaiyi ne kawai sbd yanda yaga Bobby ya daga hankalinshi ne amma da bazai bari su tafi ba musamman daya kasance har yanxu ba gama warkewa yayi ba...shi kuma yayi hakan ne sbd yanaso ya nesanta kanshi da ita and hakan bazai yiwu ba don idan yana Gombe jin kanshi yake yana kusa da ita amma idan ya koma kano zai samu sauki ya sani...idan ta dawo college kuma tsaf zai iya dena shiga makarantan ma gaba daya balle watarana ya ganta abunda yake kokarin 6oyewa ya tona masa asiri...da wnn shawara na zuciyarshi yayi na'am ya kumayi tawakkali tareda mika lamuranshi ga Allan don yasan shi kadai yakeda ikon canxa al'amura a lokacinda yaso.

Kwana biyu da tafiyarsu Aunty Munubiya da bata koma tare dasu ba ta shirya ta tafi gidan Uncle Lukman wanda yake mazaunin babba cikin 'ya'yan waziri tunda shi yakebin mahaifinsu Bobby...bayan sun gaisa dashi ya shiga dubanta da alamar tambaya yace"Munubiya lafia kuwa naganki gidane irin wnn lokacin?.."cikeda damuwa tace"wlh ba lafia ba Yaya Lukman..mgn ce nazo da ita akan Bobby"..shiru yayi yana kallonta kafin yace"to meya faru?.."a nutse ta shiga koro mishi bayanin kaunar da yakema jinin Lamido da yanda sukaje tareda Waziri akan batun neman aurenta sai kuma sukaji Lamidon da bakinshi yace ya riga ya tsayar mata da miji...tunda ta fara bayani yayi shiru yana sauraronta baice komai ba saida ta kammala yace"to yanxu me kikeso ayi Munubiya?..da bakinki fa kikace Lamido ne yace ya mata miji kuma a yanda nasan Lamido dai zaiyi wahala yayi mgn ya canxa musamman mgnr aure"...yana rufe baki tace"na sani amma bai kamata mu nade hannu mu kasa yin komai matsayinmu na 'yan uwan mahaifinshi ba...so nake dan Allah yaya Lukman kaje ka samu mahaifin yarinyar nan in person ka nuna bakasan da waccan mgn ta Lamido ba kace nemawa Bobby auren yarinyar kazoyi wata kila zai iya cewa ya hadaka da Lamido..daga nan nasan shi kanshi Lamidon zai sake nazari musamman idan ya kasance yarinyar ba son wancan auren take ba..ko don alaqar dake tsakaninshi da Waziri nasan zai iya janye waccan mgn da yayi"...shiru Uncle Lukman ya sakeyi yana sauraronta...tabbas gaskia ta fada amma shin zai iya kuwa?..gani yake kmr zasu fahimci drama suka shirya musu tunda ai Lamido yasan Waziri yasan da mgnr amma meye abunyi?.Allah ya sani shi kanshi yaji yana son taimakon yaron ko don ya samu damar goge tarin laifukan daya aikata musu a baya ciki harda kin amincewa ya nemosu bayan rasuwar mahaifinsu...yayi nadama sosai yanxu ya kuma ji gaba daya ahalin Attahir sun shiga ranshi matuka ko don sbd yanda basu nuna wani alama na har yanxu suna rike dasu ba dukda yasan zaiyi wahala ace sun manta duk abubuwan da suka aikata masu a baya...ganin yanda yayi nisa cikn tunani Aunty Munubiya ta sake lankwasa murya tace"dan Allah yaya Lukman ka taimakawa yaron nan a matsayinka na qanin mahaifinshi...ko don zumunchi ka daure kayi hakan bakasan tarin ladan da zaka samu ba"...ajiyar zucia ya sauke kafin yace"shknn zanje inshaAllah..zan fara bincikawa inji yaushe Ahmad din yake gida sai inje in sameshi"..nan take Aunty Munubiya ta shiga washe baki tana cewa"Allah ya saka da alkhairi yaya..Allah kuma yasa muji alkhairi"..shima yana murmushi yace"Ameen..duk yanda mukayi dashi zakiji"..tace"to shknn yaya..bari inzo in tafi Allah ya saka da alkhairi"...ya amsa mata da Ameen snn tayi mishi sallama ta tafi..cikin gida ta shiga wurin matarshi itama tayi mata sallama snn ta koma gidan waziri don gobe take shirin komawa kano itama dama ga dalilinda ya tsayar da ita nan.

Washegari around 4:30 Uncle Lukman ya iso gidansu Aysha bayan sunyi mgn da daddy ya tabbatar mashi da cewa yana gida...daddy ya bude kofar parlonshi ta waje ya shiga dashi nan ciki suka fara gaisawa...bayan gaisuwa kai tsaye Uncle Lukman ya fadi mgnr dake tafe dashi saidai bai 6oye mashi komai ba har yanda Lamido sukayi da waziri kan batun aurenta da Najeeb da kuma yanda shi Bobbyn ya shiga wani hali sbd jin mgnr auren nata...bayani sosai yake mashi dalla dalla kaman yanda ya samu labari wurin Aunty Munubiya...daddy kuwa rsabar mamaki kasa kwakwaran mosti yayi a wurin...gaba daya kanshi ya kulle knn all these while yaron nan yana sonta bai ta6a nunawa ba?..tausayinshi yaji ya kamashi matuka yaji inama yanada hanyar dazai taimaka mashi da yayi haka..inama ikon bayar da aurenta a hannunshi yake da ya bashi ita ko bataso saidai mgn a hannun Lamido yake ba hannunshi ba...har Uncle Lukman ya gama bayani tareda rokon idan akwai taimakon da zai iyayi don a samu sauyin al'amura ya taimaka yayi ko don a ceto rayuwar yaron...hankalin daddy ya tashi sosai ya kumaji tausayinshi ya kamashi fiyeda tunaninshi...yasan yaron baida matsala sam and yanada duk wani quality da iyaye ya kamata su duba wajen za6ama yaransu miji kuma zaifi kowa son ace ya hada jini da Mentor dinshi Col Attahir saidai hakan da kmr wuya tunda bai zama lallai Lamido ya tankwaru ba...hakuri yaba Uncle Lukman sosai tareda alkawarin zaiyi bakin kokarinshi yaga abunda Allah zaiyi saidai suci gaba da addu'a...har ya tafi daddy bai dawo cikin hayyacinshi ba...mamaki kawai yakeyi da har yake mata so irin wnn kuma ya iya 6oyewa har na tsahon lokaci haka...sosai yaji yana son hada zuri'a dashi a daya bangaren kuma yana tunanin shima Najeeb din idan sonta yakeyi fa?..itama kuma Ayshan wanda takeso daban shikam ya zaiyi ya kwance wnn kullin ne?..ya zaiyi ya daidaita al'amuran nan?.."kira Najeeb din zakayi ka tambayi ko shima yanada wadda yakeso"..amsar da wani sashe na zuciyarshi ya bashi knn nan take kuma yayi na'am da ita dan haka ya dauki waya ya dannawa Najeeb din kira yace lallai lallai yanason ganinshi idan ya dawo daga office.














Rano✨





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata yafitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
45
Da dare misalin karfe takwas Najeeb yayi sallama parlon daddy kmr yanda yace yazo yana nemanshi...ya karaso ciki ya gaisheshi kafin a hankali ya kira sunanshi"Najeeb"..kai a kasa ya amsa da"Na'am"..daddy yace"tambaya ne nakeson yi maka amma inaso kayi alqawarin zaka fadamun gaskia"..still kanshi na kasa yace"nayi alqawari daddy"..daddy yace"so nake ka fadi tsakaninka da Allah kana son Aysha ko baka sonta?.."shiru Najeeb yayi kai a kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login