Showing 75001 words to 78000 words out of 231169 words
cikin shopping da yayi mata daxun saici takeyi kaman ba gobe...Billy suka shigo dakin tareda wata ta karasa ta dauki iron dinsu dake ajiye ta bata snn ta juya ta fita ita kuma ta karasa kusada Lamido ta zauna tana murmushi tace"wai Lamido har yanxu fushin ne?.."murguda baki Aysha tayi batace komai ba...Billy ta kara sakin smile kafin tace"dama Ammi ne tace idan baki kulani ba in kirata in fada mata"..tun bata karasa ba Aysha ta juyo tana kallonta da mamaki sosai tace"yanxu zuwa kikayi kika hadani da Ammi Billy?..sai kace bakisan halin fadanta ba?.."daria Billy ta saka tana mikewa daga inda take tace"dama mgn nakeso kiyi kuma kinyi..ba wata Ammi dana fadawa"...pillow dake kusada ita Aysha ta dauka ta wurga mata shi kaman zatasa kuka tace"amma kin shiga haqqina wlh..kinsan irin tsoron da naji kuwa?.."daria kawai Billy keyi ta fara rage kayan jikinta ta shiga bathroom.
Zaune yake a parlonshi waya rike a hannunshi sai jujjuyashi yake kaman wanda yake tunani...tun daxun yake zaune nan wurin yanaso ya kira yaji ya jikinta yake amma wani zuciyan na hanashi wai idan ya kira zata iya misunderstanding dinshi...yayi kokarin kira kusan sau goma yana fasawa sbd zuciyarshi dake raya mishi cewa kar ya kira...tsaki ya saki yayi wurgi da wayan snn ya kwanta nan kan sofa da yake zaune yana wani daure fuska kaman Lamidon tana gabanshi yanxu haka...sam bayason yanda zuciyarshi ke saqa mishi abubuwa a kanta...ya rasa dalilinda yasa tun jiya ya kasa macewa da halin daya barta a ciki kiri kiri yana son kira kuma ya hana kanshi...har yanxun bai dena jin uban laushin gashinta a hannunshi ba kaman yanda bai ta6a mance cute face dinta dake tsaya mishi a rai ba...lumshe ido ya sakeyi cikin ranshi yana ayyana ko mutuwa zatayi bazai kirata ba..to meye ma ruwanshi da rashin lafiyarta da har zai bi ya damu kanshi?...juyi ya sakeyi yana dafe head dinshi duk a kokarinshi na ganin ya hana kanshi kiran nata saidai abunda bai saniba shine duk taurin kanshi heart dinshi bazai dauka ba sbd yafishi taurin kai don haka dole ne yayi mata abunda takeso idan har yana son zaman lafia...kasa daurewa yayi daga karshe ya sake mikewa zaune ya dauko wayan nashi...yayi dialing number dinta yana wani hade rai kaman tana ganinshi...tana kwance daki suna waya baby kiran nashi ya shigo sbd tsabar dadin hira ko noticing kiran nashi ma batayi ba...Bobby da yaji an buga masa wani abu kaman guduma a cikin heart dinshi sakamakon busy da yaji alaman tana waya...haka har ya gama ringing dinshi bata dauka ba hakan kuma ya mugun 6ata masa rai dan yasan da kyar idan bada namiji take wayan ba...sake kira yayi still bata dauka ba sai a na uku ne akayi sa'a taga shigowan call din dan haka tacema baby ya bata two minutes zata kirashi...picking call din tayi da sauri bayan tayi hanging wancan tana wani turo baki kaman tasan yanda ya hade ranshi shima...tana kokarin gaisheshi taji yace"dawa kike waya?.."murguda baki tayi cikin ranta tace"ina ruwanka?.."a fili kuma tace"Hamma na ne"..shiru yayi ba mgn as gaba daya ma mgnr baisan sanda ta fito ba..shi kanshi saida yaji wani iri daya tambayeta amma ba yanda zaiyi ne shiyasa ya tambaya...baisan meyasa abubuwa irin haka suke son su dinga faruwa dashi ba yanxu..shi da sam ba haka yake ba wlh...jin bai sake cewa komai ba tace"hello"...wani mgnr ne ya sake su6ucewa daga bakinshi ba tareda ya shirya ba yace"ya jikinki?.."ita kanta saida tayi mamaki jin tambayar amma bata nuna ba tace"naji sauki"..bai sake cewa komai ba ya kashe wayarshi yana dafe kanshi da yaji kaman zai rabu biyu sbd ciwo...da yasan abunda zai faru knn da bai kirata ba wlh...kawai yana zaman zamanshi ya janyoma kanshi 6acin rai..ko waye Hamman data fada ma oho..a iya saninshi dai idan ance Hamma ana nufin yaya namiji saida i baisan meyasa jikinshi ya kasa amincewa da yayanta take waya ba...sam yasan ba haka bane ta fada ne kawai don ta gujema fadanshi amma zaiyi wahala idan bada daya daga cikin boy friends dinta take wayar ba...wnn tunanin kadai ya sake dagula mishi lissafi.
Kwanakin da suka biyo baya shirye shirye sukeyi sosai na End of Year Presentation da suka saba gabatarwa duk end of session.
Bobby kuwa tun daga wnn ranan bai sake kiran Lamido a waya ba..ko a hanya suka hadu ko kallonta baiyi dan ko gaisheshi tayi bai amsawa wai duk a kokarinshi na ganin yayi yaki da abunda yake ganin bai kamata ace yanaji ba kuma a kanta...yau friday tun safe ya shigo college din sbd meeting da yake dashi da entire staff karfe 10...bayan sun fito Nur ya biyoshi har office dinshi yana mishi bayanin Presentation da za'ayi next week...ya gama sauraranshi tsaf snn ya bar office din shi kuma sai a lokacin wani tunani ya fado masa...yasan zaiyi wahala wnn abun ace ba'ayi selecting Lamido ba dukda dai kowane department voting sukeyi a tsakaninsu ko wanne class tun daga year 1,2 da 3 zasu bada mutum daya da suka yadda da brain dinshi sai a hadasu su ukun ayi masu test kowa akan gaba daya courses dinshi na shekarar duk wanda yayi winning a cikinsu shine zaiyi representing gaba daya department...baisan meyasa haka nan jikinshi ke bashi ita zatayi winning ba..kawai shidai baya sonta da wnn abubuwan ba don komai ba sai sbd shegen rawar kan daya lura tana dashi snn abune wanda a gaban mutane za'ayi shi hadda wanda ba daga makarantan suke ba..shi kuma yanxu baisan meyasa yaki jinin yaga tana wnn abubuwan ba..sam bai son yaga tanata wnn rawar kan nata a gaban mutane suna kallonta hakanba karamin 6ata mishi rai yake ba...sanin zaiyi wahala idan batayi din ba ya lalabo numberta ya danna mata kira don yayiwa tufkar hanci...shiganta class knn taga kiran nashi ta wani zare ido sosai tana sake kallon screen din to make sure ba idonta ke mata gizo ba...to me yake nema a wurinta yanxu kuma?..ta samu ta huta da masifarshi a yan kwanakin nn shine yanxu zai wani kama ya kirata salon ya wargaza mata jin dadi...ganin ya kusa tsinkewa ta daga tareda kai wayan kunne tana turo baki..kai tsaye yace"meet me now"...bai jira cewarta ba ya kashe wayar..ita kuma ta mike tana kwaikwayonshi"wani wai meet now...as if i am his child..inyamurin banza dan rainin hankali kawai"...mikewa tayi tanata sababi ta fita zuwa office din nashi...secretary dinshi na ganinta ta dauke kai bata kulata ba itama batabi ta kanta ba ta tura kofa ta shiga da sallama...yana zaune kan seat dinshi yana dan juyawa a hankali idanunshi kan kofa...kai a kasa ta karaso gabanshi ta tsaya snn ta gaisheshi still ba tareda ta dago idonta..shima bai damu da ta dago din ba ya nuna mata seat dake bayanta a nutse yace"seat.."dagowa tayi ta kalleshi da mamakin abunda ya fada dan bata ta6a zuwa office dinshi yayi mata tayin seat ba sai yau...janyo kujerar tayi a hankali ta zauna still idanunta a kasa tana wasa da fingers dinta...ba yabo ba fallasa yace"akwai end of year presentation da za'ayi next week nasan kin samu labari koh?.."gyada mishi kai tayi alaman ta sani...yace"then so nake koda anyi selecting dinki a cikin participants kice you won't do it"...sake dagowa tayi tana kallonshi da mamaki tace"but why sir?..already an riga anyi choosing dina and I can't say no because I don't want my department to loose"...kallonta kawai yakeyi yanda take wani explaining mishi bata san kome zata ce ba ganewa zaiyi ba...ya wani hade rai yace"i said you are not going to do it and that's final"...sake dagowa tayi tana kallonshi da mamaki shima kallon nata yakeyi wai ko zata fahimci abunda yakeji ta cikin idanunshi amma sai yaga ta kauda kanta tareda daure fuskanta itama tace"nidai I can't say no"...tun kafin ta rufe baki yace"haka kikace?.."shiru tayi tana kallonshi ya sake fadin"haka kikace kou?..fine..we shall see"..dan marairaicewa tayi tana mishi puppy eyes tace"yanxu sir fisabilillahi kawai sai inje ince musu bazanyi ba bayan an riga anyi selecting dina?.."cikin fushi yace"na fada maki baza kiyi ba and if u like go and do it kiga what will happened..just try me and see"...kallonshi kawai takeyi yanda yake mgn ita kam kome zaiyi saidai yayi wlh amma bazata fasa yin abunda tayi niyya ba..besides ko daddy zai fadama tasan bazai hanata ba tunda ba wani abun rashin kyau bane and sai tayi abunta wlh...ganin kallon da yake mata sai tayi kasa da idonta a hankali tace"shikenan zan fada musu su samu wani"...ajiyar zuciya ya sauke a 6oye dan wani irin relieve yaji ya samu jin abunda ta fada ita kuma ta sake dubanshi cikin nutsuwa tace"ina iya tafiya?.."baice komai ba sai kofa daya nuna mata alaman she can...mikewa tayi a hankali ta fita saga office din cikin ranta tace"in your widest dream ba..ai wlh sai nayi abuna saidai kawai ka ganni kan stage..shknn sai ince na fasa kilan aje a dauko wanda bata iyaba ta kayar da department dinmu..to bada A'i za'ayi wnn wautan ba..dan rainin hankali kawai".
Ranan Monday tana shigowa school ta wuce office din Nur da safe...yana zaune yana signing wasu papers ta karasa ciki ta zauna bayan sun gama gaisawa tace"Sir dama alfarma nazo nema wurinka"...Nur ya ajiye pen dake hannunshi yana kallonta sosai yace"ohk ina jinki"...tayi kasa da kai tana wasa da fingers dinta tace"Sir so nake dan Allah ko mgn zai hadaku da Proprietor kada ka nuna mishi ni zanyi representing midwifery a presentation din nan"...kallonta Nur yake da mamaki karara a face dinshi yace"amma why?.."tana turo baki tace"cewa yayi wai ko anyi choosing dina ince banyi and ni kuma inaso inyi shiyasa banaso ya sani saidai kawai ya ganni kan stage"...gyada kai Nur ya shigayi alaman gamsuwa before yace"no problem ur secret is safe with me..he won't know inshaAllah"..murmushi ta saki tareda mikewa tace"thank u sir"..yana mata murmushi yace"u are welcom"..daga haka tayi mishi sallama ta bar office din...Nur ya bita da kallo cikeda mamakin abunda ta fada...shi bai gane kan wani dalili Bobby zai hanata participating ba..dama these days ya lura kaman abu na damunshi and bai ta6a fada mashi ba..."ko dai son Lamido yake?.."ya fada a fili trying to figure it out amma ya kasa...daga karshe sharewa yayi kawai cikin ranshi yace"kilan idan tayi wari ni zan faraji"..da haka ya kaida tunanin daga zuciyarshi.
Bobby kam hankalinshi kwance yake sosai data ce mishi bazatayi ba...har wani nutsuwa yaji ya samu na musamman wnn dalilin yasa bai sake yunkurin nemanta sbd ya sake jaddada mata ba...ranan Thursday ya kama zaayi presentation din and tun safe Lamido suka shigo school sbd shirye shirye da ake...auditorium dinsu na nan a cike maqil da mutane participants kawai ake jira domin hatta malamai duk suna nan ciki...as usual Bobby da Nur tare suka shigo kowa ya samu wurinshi ya zauna...Nur ne ya danyi briefing jama'a yanda tsarin abun yake...kowane participant za'a rubuta sunan topics kaman guda uku cikin courses da sukayi a shekarar snnayi folding dinsu ya za6a and duk wanda ya dauka akanshi zaiyi presentation din...bayan dogon jawabi ya sake daidaita mike zuwa zaitin bakinshi yanda mgnrshi zai fito radau snn yace"and our two participants are Sa'eed Mukhtar Makarfi from Nursing department and Aysha Ahmad Lamido from Midifery department"...wani irin dammm Bobby yaji kaman saukan aradu a cikin heart dinshi...gaba daya saiya shiga rudani jin Nur ya ambaci Aysha Lamido and idan ba wai mancewa yayi ba da bakinshi ya ta6a fada mashi kta kadai take bearing da Lamido a college din...shi kuma yasan sunyi mgn da ita tace mishi bazatyi ba amma why zaizo ya kira sunanta kuma?..kodai watace mai suna irin nata bai saniba?...kafin ya samu amsan tambayanshi ya hangota ta taso daga inda take zaune zuwa seat da aka tanadar musu...sanye take cikin uniform dinta fari qal sai shinning yake sbd iron...dan hijab dinta daidai chest dinta sai gashin goshi da sajenta da suke nan waje as always...wani irin sanyi yaji yana lullu6eshi kaman fever zai kamashi...ya lumshe ido ya bude yana sake jin ciwon karyar da tayi mashi har cikin ranshi.
Rano✨
Wnn litafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a turo evidence of payment via 07063800556.
25
A hankali take takawa wanda Bobby kejin each taku kaman a kana zuciyarshi take yinshi...wani irin nauyi yaji zuciyar tayi mashi kaman wanda keda heart problems...sake juyawa yayi ya kalleta nan take kuma yaji wani abu ja sake tokare makoshinshi...ko baa fada ba yasan gaba daya mazan wurin nan kallonta suke...hakan kuma yasa yaji kaman ya harbi kanshi ya huta...finally ta karasa seat da aka tanada dominsu ta zauna kusada Sa'eed daya rigata karasawa...sake runtse ido Bobby yayi yanajin ciwon zama kusa dashi a tayi...ya ganeshi sarai shine yaronda tayi acting as his wife ranan da sukayi drama and shine the same yaron da ta bama ruwa ranar da akayi sports...yanxun nan din ma a rasa da wanda za'a hadata sai dashi?..kodai wani hu ke tsakaninsu dashi ne wai?...bayan sun zauna daya daga cikin malamansu mata ta taso da wani box a hannunta mai kyau ta kawo wurinsu tace Sa'eed ya dauki daya tunda shine first presenter...ba mus ya zura hannu cikin box din ya dauko paper daya cikin guda uku da suke ciki snn ya bude...sunan topic din ya gani a rubuce dan haka ya mike daga inda yake yana nuna mata ita kuma ta amsa daga hannunshi ta nunawa malamai then back to students snn ta koma wurinta ta zauna...dan matsawa yayi jikin white board dake ajiye nan wurin ya rubuta sunan topic din nashi snn ya fara presentation dinshi a tsanake...gaba daya hall din yayi tsit voice dinshi kawai akeji...Bobby dai na zaune kaman gunki sbd tsabar abubuwa da suka taru suka mashi yawa...yasan yanxu ko bindiga za'a zare ace ya fadi abunda yaron ke fada bazai iyaba as hankalinshi baya wurin gaba daya...kawai yanajin ciwon deceiving dinshi da tayi tace mishi bazatayi ba...ruwa dake ajiye gabanshi ya dauka yayi sipping ya ajiye tun yanxun yanajin haka idan ta fara nata kuma kilan zaucewa zaiyi...baisan meyasa Allah zai dora mashi wnn masifan a kanta ba...Sa'eed saida ya cinye 40 minutes da aka deba mishi snn yayi handing over mike din ya koma ya zauna anatayi mas tafi dan yayi kokari sosai ba kadan ba...bayan Nur ya gama praising dinshi snn ya sake kiran Aysha Ahmad Lamido data karaso tayi nata itama...kaman dazu wnn matarta mika mata box itama tayi picking one a cikin papers uku dake cikin box din snn ta mike a hankali zuwa inda board yake...kallonta kawai Bobby yake kaman bai ta6a ganinta ba sai yau...glasses data sa a idonta ya zauna daram shi sai yaga kaman ma bai ta6a ganin kyan da glass din yake mata ba sai yau...ya sake daga eyes dinshi zuwa goshinta da kusan rabin gashinta ke waje sbd ita ba gwanar sa dankwali ba hula bane..sam bata sonsu sbd suna takura mata shiyasa hijab kadai take zurawa ta tafi abunta...ciwo yakeji sosai yasan yau kaf wurin kowa saiya gama ganin gashinta..kowa kuma sai yaji voice dinta to his satisfaction...tunanin hakan yasa wani hadadde zafi ya kunno kai cikin sanyin da already ya faraji...lumshe ido kawai yayi ysna karanta duk addu'a da yazo bakinshi for he don't want to loose it kamar yanda yayi ranan festival...sam bayason a fara zargin ko da wani dalili yake aikata haka while baya da wani dalili kawai dai yarinya ce Allah ya jarabceshi da ita da ko kusa bata son ya zauna lafia...idanun nashi a rufe yaji ta fara presetation din cikin sweetes voice dinta...sake runste idon yayi yanaji kaman yaje ya toshe kunnen kowa dake wajen yanda ba wanda keda daman jin muryan nata sai shi kadai...kwata kwata baya fahimtan abunda take fada shidai kawai yasan mgn take in a sweet tone amma ko za'a kasheshi bai iya fadin ga abunda take cewa...tsoron bude idonshi yake sbd gudun abunda hakan zai haifar amma daga karshe kaman idon nashi sunfi karfinshi ne dan ji yayi sun bude kansu da kansu basu fada ko inaba kuma sai a kanta...nan kuma ya tsayar dasu a kanta yana kallon yanda take mgn tana demonstration da hands dinta...gashi sai dan matsawa take from one place to another hakan kuma yasa jikinta ke dan shaking as if she's doing it intensionally ga kuma gashinta koshi yana iya ganoshi daga inda yake...baisan lokacin daya rike kanshi da yayi mishi wani azababben sarawa ba...har wani jiri yaji yana daukanshi all of a sudden...addu'a kawai ya shiga jerowa dan samun sassauci amma abun kaman gaba ma yakeyi...ita kuwa Aysha presentation dinta take hankali kwance as ba wani sabon abu bane a wurinta...gaba daya tama manta da wani Bobby and his masifa abunda yake gabanta kawai takeyi...bayan ta cinye 40 mins dinta itama ta koma ta zauna anata aikin yi mata tafi wanda hakan ke kara ta'azzara yanayin da Bobby ke ciki...daya daga cikin malamansu ne ya amshi mike yayi 'yan jawabe jawabensa kafin a sake mika musu box kowa ya sake daukan paper daya this time around 20 mins zasuyi instead of 40...kaman daxu Sa'eed ne ya fara yin nashi yana gamawa itama ta mike ta fara...zuwa yanxu abunda Bobby keji ya ninka wanda yakeji daxu kusan sau uku...har wani gumi ke tsatsafo mishi sbd azaba don zazza6i sosai ya rufeshi kaman wanda yayi kwana da kwanaki yanayi...bai sake gigin bude idonshi ba har ta gama snn yaji hall din ya kaure da tafi...kafin ayi announcing wanda yayi winning a cikinsu wani babban mutumi daya saba halartan taron duk shekara yace a fadawa Lamido ya bata kyautan sabon MacBook hade da 50k a matsayin tukuici na burgeshi da tayi...aikuwa ana fada hall din ya sake kaurewa da ihu da tafi...masu jin dadi nayi masu rashin jin dadi ma duk sunayi...Bobby da yaji abunda mutumin ga fada kaman saukan aradu baisan time daya bude idonshi ba...daidai lokcin kuma Sa'eed ya dan kai bakinshi kusada kunnenta yace"congratulations besty..seems baby ya samu new rival"...da juyawa tayi tana kallonshi ta dan saki murmushi kafin itama ta matsar da nata bakin dab da