Showing 60001 words to 63000 words out of 231169 words

Chapter 21 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9670

hospital that ana buqatarshi da gaggawa haka ya fita ba don yanaso ba driver ya daukeshi zuwa hospital din...emergency theater suka shiga and basu suka fito ba sai around 1...sallah kawai ya tsaya yayi masjid dake nan asibitin snn ya shiga mota driver yaja suka dauki hanyan college.

Daya da mintina bakwai Motan daddy ya shigo cikin haraban makarantan...wani taro ne ya kawoshi kano shine yaga before ya wuce Gombe ya kamata yazo ya ganta dan ya kwana biyu bai zo ba..ko sanar da ita zuwanshi baiyi ba sbd yanaso yaga how she's doing a school din...dama duk zai zo bai ta6a sanar mata ba saidai kawai ta ganshi kwatsam yazo...dagashi sai driver dinshi da security guda daya...bayan sunyi parking yace da security yaje bakin gate ya tambayi masu gadi ko zasu santa dan yanata kiran wayanta bai shiga gashi kuma baiga student ko daya a premises din ba ba mamaki suna clesses dinsu...da hanzari security ya tafi bakin gate kamar yanda aka umarce shi ya tambaya ko sunsan Aysha nan sukace mai basu santa ba and abun bai sani ba shine idan zai shekara yana tambayan Aysha zasuce mishi basu santa ba because ba wanda ya santa da Aysha a cikinsu...ko yan class dinsu mantawa suke sunanta Aysha sbd yanda sunan ya 6ace 6att kowa yake kiranta da Lamido...komawa yayi ya sanar dashi sunce basu ganeta ba dan haka daddy ya bude mota ya fito yana karema premises din kallo still trying her number wai zaici saa ya sameta yanxu...daidai wnn lokacin motan Bobby ya shigo haraban school din...gefen motan daddy driver yayi parking nashi snn ya bude mishi mota ya fito...tun daga cikin mota yake kallon wnn mutumi that kana ganinshi zaka gane babban mutum ne kuma mai dattako yana tunanin me yazoyi college dinshi kuma?...har zai wuce office dinshi yaga kaman bai dace ba..bisa ga dukkan alamu mutumin wani yake nema duba da yanda yaga yanata kokarin kiran waya kuma bata shiga...juyawa yayi zuwa inda suke yana tafiya a nutse kaman yanda ya saba har ya karasa inda suke...fuska dauke da murmushi dan haka nan yaji mutumin ya mishi wani irin kwarjini yace"sorry to interrupt sir..are u looking for someone?.."murmushi daddy ya saki tareda mika mashi hannu alaman suyi musabiha yace"yarinyata nazo gani wlh kuma inata kiran wayanta baya shiga"...Bobby da yaji nauyin ya bashi hannu su gaisa yace"if babu damuwa mu karasa office dina sai insa a nemo maka ita"..daddy ya fadada smile dinshi lokaci daya yaji yaron ya kwanta mishi a rai yace"ba damuwa muje"...Bobby ya wuce gaba shi kuma yabishi baya..security dinshi zai biyosu yayi mishi alaman he should stay...suna zuwa office din ya bude suka shiga still yana murmushi ya nuna mishi sofa yace"Bismillah sir"..ba musu daddy ya zauna yana sakejin yaron na burgeshi sosai...shi kallon sani ma yake mishi sai yaga kaman ya ta6a ganinshi a wani waje...Bobby ya bude fridge ya dauko ruwa da lemo ya ajiye mishi kan table snn ya zagaya seat dinshi ya zauna ya dauki landline dinshi yace"ya sunan yarinyar da za'a kira sir?.."daddy bai maji me yace ba as hankalinshi gaba daya yana ga katon picture din Bobby dake manne a wall din office din...fuskanshi dauke da suprise look ya juya yana kallonshi yace"u mean kai son din Col Attahir ne?.."Bobby yayi shiru yana kallonshi da mamaki shima...daddy ya sake juyawa ya kalli pic din snn ya kuma juyowa gareshi har yanxun cikeda mamaki yace"ina nufin Col Attahir Waziri na Gombe..are u his son?.."a hankali Bobby ya gyada mishi kai alaman yes...wani irin bright smile ya gani shimfide kan fuskan daddy wanda ke nuni tsantsan farin cikin haduwa dashi...juyawa ya sakeyi ya kalli hoton then back to Bobby kafin yace"ikon Allah...kasan mahaifinka shine sanadiyyar matakin da nake kai a yanxu?..he was a very good and generous man..my mentor...har yanxun banida wani abun kwaikwayo kamanshi...he was a very kind hearted person..a very responsible person.."ya karasa mgnr da wnn bright smile kan face dinshi sai kuma eyes dinshi dake nuni da tsananin kewarshi da yaji sakamakon tunawa da mutuwarshi da yayi...Bobby dai mutuwan zaune yayi sai kallonshi kawai yakeyi kaman statue...wani irin qima yaji
mutumin ya sakeyi a idanunshi...kawai yaji yana sonshi sbd wnn maganganu da yayi kan dad dinshi...a rayuwa yanason ya hadu da mutumin da yasan babanshi ba don komai ba sai don kawai yayita bashi labarinshi yanajin dadi amma banda familyn dad din nashi...su wadan nan ko zasuyi me bazai iya yadda wani alaqa ya sake shiga tsakaninshi dasu ba...bayan few minutes of silence daddy yacigaba da cewa"no wonder tun a kallon farko da nayi maka naga kaman na sanka...its because kana kama da dad dinka sosai and ba iya kamanninshi kawai ka dauko ba harda halayenshi...kawai daga gani na kaji ya kamata ka taimakamin har ka kawoni office dinka without knowing who i am and wnn na daya daga cikin halayen mahaifinka...bai ta6a ganin wani na bukatar taimako bai taimaka mishi ba...ubangiji Allah ya jikanshi yasa yana aljannah"...Bobby ya lumshe ido sbd dadin addu'ar da yaji a hankali yace"Ameenn"...daddy ya zuba ruwa a cup yasha snn yace"kasan sa akwai alaqa ta sarauta tsakanin shi mahaifinmu Lamido da kakanka Waziri..wnn dalilin ne yasa dana fara aikin Custom aka hadani da mahaifin naka"...kallonshi kawai Bobby keyi yanajin dadin labarin...shi daddy yacigaba da fadin"kacigaba da irin wnn habit din yanada kyau kaji?..Allah ya maka albarka"...yana murmushi ya amsa da"Ameen..nagode sir"..daddy yace"no thanks a tsakaninmu...u are like a son to me"...sake murmusawa Bobby yayi yana shafa kanshi...tunda yake bai ta6a cin karo da mutumin da ya kwanta mishi a rai ba kaman wnn mutumin ba..da ganinshi mutumin kirki ne and he ha so much respect for him..baisan ko sbd yasan dad dinshi bane oho amma yaji yana ganin girmanshi sosai...saida ya sake daukan landline snn yace"Sir baka fadi sunan yarinyar ba"...murmushi daddy ya kuma saki yace"kaga har na manta da ita sbd tunowa da Mentor na da nayi...May his gentle soul continue resting in peace"..sake lumshe ido Bobby yayi tareda cewa"Ameen Ameen"..daddy yace"sunan yarinyar Lamido...Aysha Ahmad Lamido"...idanu a waje sosai Bobby ya dago yana kallonshi jin sunan daya ambata...he can't believe wnn responsible mutumin shine zai haifi wnn fitinanniyar yarinyar...ganin irin kallon da yake mishi daddy yace"do u know her in any way?.."da sauri ya shiga girgiza kai yace"ah no sir..bari insa a nemota"...daga haka ya kira secretary dinshi using the landline...tana dauka yace tazo yana son ganinta...bayan ta shigo yace mata"did u know a girl called Lamido?.."secretary ta danyi shiru for the mean time kafin tace"yea na santa sir..mai kukan allura kou?.."banza yayi kaman baiji me tace ba yace"kije midwifery section ki nemota..tell her that her father is here waiting for her"..secretary ta amsa da"ohk sir"..snn ta juya ta fita daga office din...daddy ya bita da kallon jin tace mai kukan allura...knn hakan na nufin Aysha har a nan dinma kukan alluran take?..kawar da tought din yayi ya juya ga Bobby yace"kanada sister sumayya koh?.."gyada kai Bobby yayi yace"yes my elder sis"...murmushi daddy ya kuma saki yace"a lokacin bazan manta ba inajin sunanta a bakinshi...yanaji da kids dinshi sosai dan koda yaushe cikin mgnrku yake...and kanada brother mai sunan Waziri kou?.."nan ma kai ya sake dagawa yace"Sabeer"...daddy na cigaba da murmushi as old memories rush back yace"ina tunawa da sunanku ai..he was man of the people shiyasa duk na kasa dashi suke sonshi sosai"...gyada kai kawai Bobby yake yana murmushi...he doesn't want the conversation to end.

Secretary na fita kai tsaye midwifery section ta nufa kaman yanda yace mata...duk wanda ta tambaya Lamido zaice baisan inda ta tafi ba...har class dinsu taje bata nan and gaba daya yan class din suna ciki suna lectures ita kuma ba wanda yasan inda take...gajiya tayi da neman nata ta sauka kasa ta sake dubawa nan inda classes din Nurses yake amma ba Aysha ba alamarta...tana fita daga wurin ta hangota can bakin gate ta shigo makarantan hannunta niki niki da ledoji kaman wadda taje kasuwa...da sauri ta karasa inda take tace"kece Lamido koh?.."kai tsaye ta gyada mata kai alaman eh...secretary tace"kizo office Dr.Bobby na nemanki"...Aysha ta wara idanu kaman taga abun tsoro tace"what!..ce mishi kikayi kin ganni?.."secretary bata sake cewa komai ba ta juya tace"nidai na fada miki..idan kuma inje ince mishi baki zuwa ne toh"...da sauri tabi bayanta tana turo baki tace"muje..ai dai duk abunshi bazai gutsuri naman jikina yayi pepper soup dinshi yaci ba..iyaka ya balbaleni da masifa wnn kuma shi ya sani"...secretary dai tafiyarta tayi bata ma jin abunda take fada sbd ciki ciki tayi mgnr...saida ta fara ajiye kayan dake hannunta nan kofar office din nashi snn ta tura kofar a nutse ta shiga bayan ta gama hade rai wai sbd kar ma yaga fuskanta a sake yace zai rana mata hankali...bayan ta shiga ciki ta juya tareda closing kofar tayi taking one step forward kafin idonta ya hango mata wanda ke zaune cikin office din...zare idanu sosai tayi looking at him kaman taga dodo dan har ga Allah ta dauka gizo yake mata...hannu takai ta murza idanunta sosai tana tunanin kodai sbd batasa glasses dinta bane ta fara gane gane kuma...bata tabbatar da gaske shine nan zaune ba saida taji voice dinshi na fadin"ni ne nan zaune ba daydreaming kike ba"...lokaci daya gabanta yayi wani irin faduwa irin wanda bai ta6a yin irinshi ba...juyawa tayi ta kalli Bobby taga shima idonshi a kanta snn ta sake juyowa ga daddy still shima kallonta yake fuska daure...nan take wani irin zufa ya fara keto mata...taya akai daddy yazo office din mutumin nan?..bata samu amsan tambayan ta ba ta sakejin daddy yace"ni kike jira in taso in gaisheki knn kou?.."da sauri ta karasa inda yake ta zube kan guiwoyinta murya a matukar nutse tace"daddy..barka da z..."bai bari ta karasa ba ya katseta da fadin"daga ina kike?.."wani yawu ta hadiye da kyar zufa na kara keto mata tayi qundunbala tace"da..daga class nake"kallonta yakeyi rungume da hands dinshi yace"really?..wato daga class kike?.."kai ta sake dagawa tareda cewa"eh.."sai kuma tayi saurin girgiza kan ganin irin kallon da yake mata tace"aah.."fuskanshi ba alamun wasa yace"kince eh kince aah..wanne zan dauka knn?.."hawaye na cikowa idonta tace"daddy wlh abinci naje na siyo"..yace"abinchi?..bakuda cafeteria ne cikin makarantan?.."tana girgiza kai tace"da akwai"...yace"then menen dalilinda zaisaki fita waje siyo abinci lokacinda students yan uwanki suke class..wato har yanxu baki dena irin wnn halayen ba koh Aysha?..kina ganin kaman tunda kina nesa damu you are free to do duk abunda kikaga dama kou?.."da sauri ta shiga girgiza kai tana hawaye sosai tace"daddy wlh ba haka bane...dan Allah kayi hakuri wlh Billy ce batada lafia tace in siyo mata shine na fita amma ba haka nakeyi ba wlh"...kallonta kawai daddy keyi baice komai ba...Bobby kam kusan suman zaune yayi sbd mamaki...bai ta6a tunanin haka takejin tsoron mahaifinta ba dan hasali ma shi kallon sangartatta yake mata ashe abun ba haka bane..ya tabbata da sangarta ta ake babu yanda zaayi ta shiga tashin hankali haka sbd ganin babanta...wnn kadai ya isa ya nuna cewar sam ba sangartata akeyi a gida ba kilan dai kawai halinta ne haka...amma kam albasa batai halin ruwa ba...jin kukanta ya fara cika office din daddy yace"ke denamin kuka a nana..ai bakisan da kukan ba kike aikata abunda kikaga dama sbd kinga bama ganinki kou?.."girgiza kai kawai takeyi tana kokari tsayar da kukan nata ko uffan ta kasa cewa...a dan fusace yace"bazakiyi shirun ba knn"...tun kafin ya rufe baki tayi diff kaman anyi ruwan sama an dauke...still fuskanshi a daure yace"ina Bilkisun take?.."da sauri tace"tana hostel.."yace"kun kaita asibiti ne?.."ta gyada kai tace"da safe muka kawota..an bata drugs da injections yace inshaAllah zuwa gobe zataji sauki"...gyada kanshi yayi alaman ya gamsu kafin ya sake dan hade ranshi yace"idan kin koma ki hadani da ita awaya and wlh wlh Aysha idan kika sake na gani ko naji labarin kin aikata abunda bashi kenan ba a cikin makarantan nan ko a waje Allah sai kinyi mamakin matakin da zan dauka a kanki tunda na fuskanci har yanxu akwai sauran rashin ji a tare dake..just dare me kiga abunda zai biyo baya"..kai a kasa taba matsar kwalla tace"inshaAllah zan kiyaye daddy..kayi hakuri"..baice mata komai ba ya juya yana kallon Bobby da yayi relaxing kan seat dinshi yana kallon su kaman movie..kawai mamakin yanda such a responsible and reasonable person kamanshi zai haifi tantiriyar yarinya kamar Lamido...ga dukkan alamu kuma yana iya bakin kokari kan tarbiyyarta kunnen qashi ne kawai Allah ya hore mata...muryan daddy ya dawo dashi daga duniar daya tafi da yace"son alfarma nake nema a wajenka"...wnn karon Aysha ce mai mamakin sbd sunan da taji daddy ya kirashi dashi"son dai?.."ta fada cikin ranta...murmushi Bobby ya saki cikeda girmamawa yace"ai babu alfarma tsakanimu sir..kawai ka fadi buqatarka"...shima daddy ya saki smile din jin dadi snn ya nuna Aysha da har yanxu ke zaune kan guiwoyinta yace"so nake kasamin ido a kanta plss..tanada fitina sosai..she is so stubborn that saida mahaifi na yasa baki before in amince ta taho karatu wani garin..batajin mgn sam kuma tun tana karamarta haka take...na yadda da tarbiyyarka shiyasa zan dora wnn responsibility din a kanka and inada tabbacin u can do it...i want u to put eyes on her idan kaga zata aikata abunda ba daidai ba kayi stopping dinta snn duk lokacinda kace tayi wani abu batayi ba just give me a call zakaga hukuncin da zanyi mata..i hope u can do that for me"...gyda kai Bobby yayi yace"inshaAllah sir"...murmushi daddy ya kara saki tareda mikewa ya isa gaban table dinshi ya mika mishi hannunshi yana cewa"thank u so much son..ubangiji Allah jikan mahaifinka"...Bobby da kunya ya hanashi mika nashi hannun yace"Ameen sir"...kamo hannun nashi dady yayi tareda shaking da nashi still smiling yace"we've already became family so meye na makale hannun?.."murmushin dai ya kara saki kanshi kasa ya kasa hada ido dashi...hakan da yayi ya sake burge daddy sosai ya kuma tabbatar da cewa ya damka amanar Aysha a hannun daya dace domin yasan har abada jinin Attahir bazai ta6a kasancewa bata gari ba..ya aminta da tarbiyyar yaron dari bisa dari...bayan ya saki hannun nashi ya zari card dinshi daga aljihu ya ajiey kan table dinshi tareda fadin"here is my card ka kirani da wuri sbd inyi saving numberka"..Bobby ya dauki card din yana fadin"InshaAllah sir..thank u so much"..daddy yace"always welcome son..will like to meet u again"...yace"inshaAllah Sir..Allah ya tsare"..daddy ya amsa da"Ameen"..kafin ya fita daga office din...hajia Aisha kuwa suma ne kawai batayi ba tsabar mamaki...har yanxu ta kasa fahimtan ta inda wnn sabon alaqa ya 6ullo tsakanin daddy da inyamurin mutumin nan..sam hakan bai gamsheta bane..dr Bobbyn da ba kaunarta yake ba shine yanxu zaa ba amanarta aikam tasan ta gama yawo..takura dai iri iri zata sha a wurinshi kuma batada bakin complain tunda umarnin mahaifinta ne...ficewa tayi itama yabi bayan daddy...yana dab da shiga mota ta cimmasa dan haka ya dakata tareda juyawa gareta ya zaro kudi masu yawa daga aljihun babban riganshi yayi dividing kudin into two tareda mika mata daya yace"ga naki"...ta amsa tana godia snn ya sake bata dayan yace"wnn kuma na Bilkisu..saura kuma ki bari inji labarin ya saki ko ya hanaki wani abun kinki yi zakiga yanda zanyi dake"...kasa cewa komai tayi kanta kasa...security dinshi dake tsaye ya nunama ya dauko mashi wani abu a mota nan da nan ya bude motan ya dauko wani bag mai kyau ya mika mashi...daddy ya amsa tareda mikawa Aysha dake tsaye kai a kasa yana cewa"take.."da sauri tasa hannu biyu ta karba tareda dan risinawa tace"Allah ya saka da alkhairi "..a hankali yace"Ameen"..snn ya shiga cikin mota...ta matsa jikin window tana dubanshi tace"daddy Allah ya kiyaye hanya..ina gaida su Ammi"..yace"zasuji inshaAllah..ki koma ciki"...a hankali tace"toh.."tareda barin wurin...tana kallo motan nashi har ya fita daga makarantan ta sauki ajiyar zuciya tareda dafe kirjinta da har yanxu bai dena bugawa ba...taso komawa ta dauko kayan data bari a kofar office dinshi amma bazata je ba haka kawai yayi ram da ita a wajen...yanda yake neman tan nan tasan ai idan suka hadu rashin mutunchi ne zata sashi musamman yanxu da daddy yace wai yasa mata ido...wucewa tayi class dinsu cikin ranta tana ayyana wai ita daddy zaice a sa mata ido sai kace wadda take aikata wani aikin ashsha.














Rano✨





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
21
Tun daga wnn ranan bata sake yadda ta hadu dashi ba har tsahon sati guda shima kuma bai nemeta ba...gashi duk sukayi waya da daddy sai jaddada mata tayi mishi biyayya and ta ringa zuwa tana gaisheshi time to time ta amsa mishi ai already tana zuwa...gaba daya haushi takeji that daddy zai dinga hadata da wnn mutumin...ko a inama ya sanshi har ya yadda dashi haka oho?.

Yau Thursday suna zaune class dinsu tana koya ma wasu assignment kiran daddy ya shigo wayanta...excusing kanta tayi tareda daukan wayan tana gaisheshi..bayan ya amsa yace mata"where are u now?.."tace"ina class daddy"..yace"kinje kin gaida Attahir?.."shiru tayi tanaso ta gane waye Attahir yace"ur proprietor"...da sauri tace"eh..aah banje ba..amma zanje sai mun tashi daga class"..yace"to idan kinje ki hadani dashi a waya"..bai jira cewarta ba taji ya kashe wayan...tabi wayan nata da kallo tana mamakin abunda yace..tadai san bai yiwuwa ace har yanxu Bobby bai kirashi don akan idonta ranar yace yanaso ya kirashi a wuri so dole yanada number dinshi amma why zaice ta hadasu a waya?.."so yake ya tabbatar da kina zuwa gaidashi ko bakiyi"..cewar wani 6angare na zuciyarta..ta kuwa yi na'am da haka don dai tasan zaiyi wahala ace kiran wayanshi yayi bai shiga ba...komawa tayi suka karasa assignment din kafin lecturer dinsu ya shigo ta nufi office dinshi don tasan idan bata hadasu kamar yanda daddyn yace ba then zasu samu matsala gagaruma...tana isa bakin office dinshi kafin ta shiga secretary dinshi ta bita da wani irin kallo tace"wai ke me kike zuwa yi office din nan ne?.."wani kallo Aysha tabita dashi irin na rainin hankali kafin taja tsaki ta wuce...da sauri ta mike daga inda take tana fadin"ki bari a fada sanar dashi zuwanki kafin ki shiga"...ai ko tsayawa sauraronta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login