Showing 129001 words to 132000 words out of 231169 words

Chapter 44 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9661

kan shoulder dinta yace"Mummy bazan taba aikata abunda kike tunani ba..a yanda nake kishinta bazan taba bari shaitan ya shiga tsakanina da ita kafin aure ba..kawai na kasa controlling feelings dina ne..Mummy ji nake idan yarinyar nan bata aureni ba bazan iya cigaba da rayuwa ba"..shafa kanshi Mummy ta shigayi without saying anything..bata ma san me zata fada ba..wnn wane irin so ne yakema yarinyar nan haka?..wane irin sone yake neman zautar mata da Bobby haka?..anya kuwa ya kamata tayi folding arms dinta tana gani yaronta ya shiga wani hali akan soyayya?..anya kuwa bai kamata tay making wani move da zai taimaka masa ba?..wnn tunane tunanen ne suka taru suka cika zuciyarta..zuwa yanxu ta gama tabbatar da yake cewa idan bai aureta ba mutuwa zaiyi...tsaf tasan hakan zai iya faruwa amma wane hanya ya kamata tabi don tayi preventing faruwar hakan?..duk brain dinta ya cunkushe tama rasa wane tunani ya kamata tayi...mikewa tayi da sauri tunawa da tayi lokacin iftar yayi itama ko ruwa bata sha ba tazo kiran Aysha shine ta iskeshi a dakin..kama hannunshi tayi tana kallonshi tace"yanzun ka tashi muje muyi iftar sai muyi mgn later"..baiyi mata musu ba ya mike don yasan idanma yace ya koshi Mummy ba rabuwa dashi zatayi ba dole sai yaci and shi kashi yanada buqatan yasha ko ruwa ne sbd yayi breaking fast dinshi...hannunshi na cikin nata suka fita daga dakin..a dinning suka samu Miemie da Sab har sun fara iftar dinsu sai aunty sumy da itama ta fito yanxu...Mummy taja mishi kujera ya zauna snn ta koma ciki don fitowa da Aysha..har lokacin tana bathroom bata fito ba saida Mummy tayi mgn taji voice dinta ne da gaske snn ta bude kofan..riganda ya wurgar a kasa Mummy ta dauka ta mika mata ta koma bathroom ta sakoshi abjikinta snn ta kama hannunta suka fita dinni g..da kanta taja mata seat ta zauna snn itamata zauna tayi serving dinsu..wurin sai yayi tsit banda karan spoons ba abunda ke tashi...daga Bobby har Lamido babu mai cin abincin kirki kowa tunanin da yake zuciyatshi daban..ita tsananin tsoro da kuma mamakin yanda har yakeda guts din da zai bude baki yayana sonta take yayinda shi kuma yaketa kallonta yana sauraran yanda zuciyarshi keyi mishi ihu tana sake jaddada mashi cewa matukar bai sameta ba mutiwa zaiyi..ya lumshe ido ya bude duk hankalinshi na kanta yaga a kasa cin komai a wurin banda jujjuyawa da take sai yaji sam hakan baiyi mishi dadi ba..ko kusa bayason ta kwana da yunwa especially not yanxu da ake azumi..Mummy yayi da ido yayi mata alama da tayi mata mgn..murmushi ta saki tareda juyawa tana dubanta tace"Aysha meyasa baki cin abincin ne?..idan kuma wani abun kikeso yamxu sai a shiga kitchen a dafa maki"..daukan yamballs tayo da sauri tana kaiwa bakinta tace"zanci"..daga haka ta shiga tunkuda yamballs din kmr an aikota..saida taci guda 4 snn ta dauki kunun gyada dake gabanta shima ta kafa a baki tanasha kmr mai shan magani...duk Bobby na lura da ita dan even for once bai dauke hankalinshi daga kanta ba..kawai jinshi yake yakai limit din da bazai iya cigaba da hiding feelings dinshi ba..idan kuma ya dage sai yayi hakan then definitely zuciyarshi zata samu matsala...Lamido kuwa dukda ba kallonshi take zata iya rantsewa taji pearcing idanun nan nashi a kanta..ajiyar zucia ta sauke har yanxu gabanta bai bar faduwa ba ta dauki drink dake gabanta tasha snn ta ajiye goran tareda mikewa zata bar wurin shima yayi saurin mikewa don ya koma daki Mummy tace"dawo ka zauna"..kallonta yayi da sauri yace"Mummy bafa binta zanyi ba"..bata bari ya karasa ba tace"i said sit"..bai sake mgn ba ya koma seat din da ya tashi ya zauna hade da dafe kanshi da hannu..Mummy da tasan yanda yakeji da batayi yunkurin hanashi tafia bawlh..shi ba wajenta zaije ba kawai yanaso ne yajishi a kwance ko zai samu saukin abunda yakeji.











Rano✨






Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
40
Tana shiga daki wayanta ta dauka ta sake dialing number Hamma amma bai shiga ba..ta kira na daddy shima bai shiga ba na Ammi ma bai shiga ba..duk hankalinta yabi ya tashi taji bata son zaman kanon ma gaba daya..ko ba yanxu zasu tafi Saudi ba itadai gara mata ta koma ko Bauchi ne gidan aunty fiddausi akan dai ta zauna gidansu wnn mutumin daya fara bata tsoro yanxu..gaba daya abubuwan da yayi mata sun kasa bajewa daga kwanyarta..yanda ya furta i love u din nan har yanxun bata denajin echo dinshi cikin ears dinta ba..kuma ta tabbata this time around da gaske yake..da gaske yake tunda har yanayinshi taga gaba daya ya sauya and she saw wani abu cikin idanunshi wanda ko kusa bata fatan sake ganin makamancinshi...ba Kano kadai ya fita daga ranta ba har FCNM din taji ta tsaneta da daddy zai yadda ya maidata Gombe da tafi kowa farin ciki da hakan amma tasan ko rasuwa zatayi daddy bazai canxa mata makaranta ba especially not yanxu da take dab da kammalawa...bayan sallah suna gama hutu zasu tafi Clinical posting daga nan kuma saura musu semester daya su gama ta huta da alakakai..duk ranan da akace ta gama FCNM kuwa tana tunanin bazata sake tako kafarata ta kawo Kano ba duk kuwa da tarin kaunar da takewa garin amma bazata iya da halin proprietor dinsu ba..she remember yanda Prof ya nace kan Bobby sonta yakeyi hakama Billy ita kuma tanata cewa ba sonta yakeyi ba ashe duk sun fita gaskia...abubuwa da dama sai yanxu suka shiga dawowa kwanyarta suna kuma sake tabbatar da lallai da gaske proprietor sonta yake saidai ita ko kusa ko alama bataji wai zata soshi ba saidai tausayi daya bata..kawai dai zaiyita wahalar da kanshi ne daga baya ya hakura tunda dai tasan da hankalinta da komai bazata fara zabanshi a matsahin miji ba bayan ba kalan bakin halinshi da bata sani ba.

Bayan duk sun kammala iftar dinsu suka mike zuwa parlor kafin sallahn isha..ya rage daga Mummy sai Bobby da har yanxun ke dafe da head dinshi a dinning din...kama hannunshi Mummy tayi cikin tsananin tausayinshi tace"dan Allah ka ragema kanka damuwan nan Bobby"..tana rufe baki ya dago jajayen eyes dinshi dake nan kaman ana hura musu wuta yace"bansan yanda zanyi in dena ba Mummy..ya zanyi plss?.."yana rufe baki tace"ka fawwalawa Allah komai..ka kuma yi imanin cewa idan Aysha matar ka ce zaka aureta likewise idan ba matarka bace duk wnn kunchi da damuwan bai isa yasa ka sameta ba"..dagowa yayi yana kokarin boye tarin damuwar dake kan fuskanshi yace"shikenan Mummy amma pls can i see her this once?..i just wanted to make sure bata tareda yunwa ne kinga azumi akeyi and ina kallo daxun ba wani abincin kirki taci ba"..mikewa Mummy tayi tana cewa"don't worry i will take care of that"..da sauri yace"Mummy please..idan ban ganta ba bazan iya bacci ba wlh"..kallonshi Mummy tayi kawai ta ksa mgn..tausayi yake bata sosai..da ganin yanda ya jigata za'a san dama abun ya dade yana cinshi a zuci yanxun ne kawai ya fito sbd kasa cigaba da boyewa da yayi..bata sake hanashi ba ta kama hannunshi suka nufi flat dinta...a tare suka shiga dakinda take tayi saurin mikewa daga kwancen da take tana kallonsu...Mummy ce tace mata"anya kin koshi da abincin nan kuwa Aysha?..idan kina son wani abu ki fada a kawo maki"..girgiza kai ta shigayi da sauri tana cewa"Allah na koshi Mummy"..kallonta Mummy tayi kmr zata sake mgn sai kuma ta saki hannun Bobby tareda juyawa ta fita daga dakin..tana fita ya karasa ciki da sauri yana dubanta a raunane yace"if sbd mgnr dana fada ne yasa kika kasa cin abinci am sorry.. ki fadi duk abunda kikeso i will go out in samo maki yanxun"..girgiza mishi kai kawai tayi tareda komawa ta kwanta murya can kasa tace"na koshi"..legs dinshi yaji sunyi wani irin sanyi kmr bazasu daukeshi ba..murya a hankali ya kira sunanta ta mike tana kallonshi kawai sai ya juya ya fita daga dakin yana jin kanshi na sarawa da karfi...magani kadai ya iya sha snn ya hau gado ya kwanta tareda lumshe ido yana addu'an Allah ya kawo bacci ya daukeshi ko zai samu saukin halinda yake ciki...dukda maganin da yasha baccin bai samu daukarshi da wuri ba sai can kuma ya daukeshi ba tareda saninshi ba...ana kiran sallahn isha ya farka tareda sake dauro alwala ya wuce masjid..bai dawo ba saida suka idar da taraweeh still ya sake komawa daki ya kwanta tun daga nan kuma bai sake tashi ba saida alarm din wayanshi ya buga alaman time din sahoor yayi knn...mikewa yayi da sauri ya sauka daga gadon tareda fadawa bathroom yayi brushing ya fito kai tsaye ya fita zuwa flat din Mummy...yau ko nafilar dare bai iya tashi yayi ba sbd maganin bacci da yasha..a parlor sukayi karo da ita tana ganinshi tace"yauwa ka tashi?.."yace"na tashi..Mummy kin tasheta?.."murmushi Mummy ta saki tana kama hannunshi tace"na tasar maka ita Bobby..nama kai mata abincinta can dakin saida ta fara ci na fito"..ajiyar zuciya ya sauke gamida lumshe idonshi yace"Mummy kar kina fita taki ci fa"..hannunshi Mummy ta kama suka fita daga parlon tana ce mishi"zataci inshaAllah..believe me"..kai kawai ya gyada mata har suka fita...nashi abincin shima ta hada ta kawo mashi snn itama ta zauna cin nata..shi kuwa kasa cin abincin ma yayi gaba daya hankalinshi ya tafi wurinta..bayan mintina kadan ya mike yace ma Mummy zaije yayi nafilah kafin time din subhi yayi..batayi masa musu ba barshi dukda tasan kafin yayi sallahn sai ya fara zuwa inda Aysha tukunna...ilai kuwa yana shiga direct dakin da take ya wuce...ya sameta da mug din tea a hannu tana sha baisan lokacinda ya sauke wani ajiyar zuciya ba..kallonta ya danyi for like 5 mins snn ya juya ya fita don yasan ko yayi mata mgn ma zaiy wahala ta amsa mashi hakan kuma yana iya sa zuciyarshi ta hauro yazo yana mata abunda bai kamata ba.

Karfe goma na safiyar ranar Aunty Munubiya tazo gidan tareda yaranta..gaba daya sun cika parlon Mummy suna labari har Aysha da Mummy tasa dole aka kirata ta fito itama ake labarin da ita..dukda ba wani abu take cewa ba tana sauraronsu tana murmushi..ga Miemie da Nusaiba da suka sanyata tsakiya sun cikata da surutu kmr ba azumi suke ba...dukda labarin da sukey hankalin Mummy na kanta taga yanda take dan smiling idan an fadi abun daria sai hankalinta ya dan kwanta at least dai bata cikin damuwa yanxu...Bobby na fitowa ta wani hade girar sama dana kasa kmr ba ita ke smiling a while ago ba.. ya karasa ciki ya zauna suna gaisawa da Aunty Munu kmr bazai ce mata komai ba shima nashi face din daure can kuma ya kasa hakura yace"come and speak to ur dad"..kallonshi tayi taga shima ya daure fuska saida gabanta ya fadi da ganin fuskan nashi...tayi kasa da kai kmr bata jishi ba shi kuma ya sake cewa"ba dake nake mgn bane?.."mikewa tayi a hankali tana turo baki shima ya mike maimakon ya hadata dashi din sai ya kama hanyar fita itama dole tabi bayanshi kafin ya zazzaga mata masifa kuma...Mummy da mamaki ta bishi da kallo ganin har yanxu bazai dena hade ma yarinyar nan rai ba bayan duk wahalan da yakesha kanta...yana fita kai tsaye motarshi ya nufa ya bude front seat yana kallonta har ta karaso ta shiga ya rufe kofar snn shima ya zagaya ya shiga tareda tayar da motar ya figeta da wani irin gudu suka fita daga gidan...cikin tashin hankali ta juya tana kallonshi taga fuskan nan ba sarari sai ma sake tamkeshi da yayi kmr namijin saniya..kasa cewa komai tayi ta dauke kai daga gareshi...gudu yakeyi sosai ba tareda yasan shi kanshi ina ya dosa ba..kawai haushi yakeji da zata dinga treating dinshi like this sbd yace yana sonta bayan ya tabbata ko bestynta baza tayi treating dinshi haka ba ballantana kuma ace wnn tsohon saurayin nata...ganin yanda yake tsere da motoci akan titi kawai ta fashe mishi da kuka..yanzu idan yaje ya zubar dasu ya zasuyi?..kuka takeyi wiwi yana jinta baice komai ba bai kuma dakata da gudun da yakeyi ba dukda yanda kukan nata ke neman karyar mishi da zucia amma haka ya dake...saida yaje can Arean Naibawa ya hau fly over yabi titinda zai maidashi hotoro snn ya samu silent area da ba motoci ke wucewa sosai ba yayi parking nan wurin yana kallonta...lumshe ido yayi jin kukan nan nata yake har cikin ranshi..duk wnn zafin da ya fito dashi sai ya nemeshi ya rasa kukan nan da takeyi duk ya wargaza su...a hankali yake dubanta murya a matukar raunane yace"do u want to kill me?..so kike kiga karshena koh?.."shiru batace komai ba..ya sake cewa"am asking u..kinaso kisamun ciwon zucia sbd kinga na damu dake ne?.."dagowa tayi tana wiping tears dinta ta girgiza masa kai alamar aah..yace"then why are u doing this?..why are u punishing me like this?..na fada maki if sbd abubuwanda na maki a baya ne u are free to punish me amma am begging u to stop giving me tough times haka nan..na wahala mana..ko a haka kika barni i've learnt my lessons and ko a mafarki bazan sake yunkurin hurting dinki ba plss"..kallonshi kawai take ba tareda tace komai ba..kamo hannunta yayi da sauri ya dora kan chest dinshi yace"feel my heartbeat kiji..bai sake bugawa normal ba tun daga ranan dana fara sonki"..dakatawa yayi tareda dora kanshi kan hannun data yace"Aysha help me plss..am about going crazy"..kallonshi kawai Aysha keyi gabanta na tsananta faduwa...for the very first time taji ya mugun bata tausayi yau..ta yadda da gaske son nata yakeyi amma ita fa tana sonshi?..hannunta taji ya fara sagewa sbd kanshi daya dora akai dan haka ta shiga kokarin kwatan hannun ya sake mata shi da sauri ya dago kai yana kokarin maida tashin hankalin dake fuskanshi yace" am sorry"..yarfa hannun ta shiga yi kafin a hankali tace"it's ohk"..shiru sukayi na wani lokaci kafin Bobby yace"zan baki enough time kije kiyi tunani akai..i promise bazan sake disturbing dinki da mgnr ba amma do help me plss..help me out of this whole mess"..kallonshi har yanxun takeyi tanajin zuciyarta na karyewa..tausayi yake bata fiyeda tunaninta amma ya zatayi?..tasan idan tayiwa baby haka bata mai adalci ba..koda tana son Bobby bai kamata ta wulakanta shi ba ballantana ba sonshi takeyi ba tausayi kawai yake bata...yana gama mgn ya gyara zamanshi snn ya dauki phone dinshi yayi dialing number daddy...yana fara ringing ya mika mata wayar ta amsa tareda karashi a kunne...tanajin yayi picking tayi saurin cewa"daddy ina kwana"..yace"lafia lau..meya samu wayarki ne Najeeb yace tun safe yake kira bai shiga ba"..a hankali tace"kilan network ne..nima tun jiya ina kira bana samunshi"..daddy yace"shknn..yanzu ki zama cikin shiri zuwa gobe flight dinku zai tashi inshaAllah..shima Najeeb din a gobe zai iso"..nan da nan face sinta ya washe da tsananin farin ciki tace"to daddy..Allah ya kawoshi lafia"..daddy yace"Ameen"..snn sukayi sallama..ta mika mashi wayarshi tana cigaba da murmushi tace"thank u"..kallonta kawai yayi bai iya cewa komai ba...ya amsa wayan ya ajiye snn ya tada motar suka cigaba da tafia...bakin wani mall taga yayi parking snn ya bude motar ya fita..after few minutes ya dawo da leda a hannunshi ya ajiye back seat snn ya shiga ya sake tada motar suka wuce..har yanxun babu mai cewa wani abu a cikinsu..shi gaba daya tunaninshi yanaga neman hanyar da zaibi don ya samu soyayyarta yayinda ita kuma nata tunanin ke ga tafiyar da zasuyi gobe zuwa saudi sai kuma asalin tausayinshi daya fara damunta...har suka isa gida ba wanda yayi mgn cikinsu..bayan ya gama parking ya dauko ledan da ya ajiye a baya ya mika mata ba tareda cewa komai ba..batayi gaddama ba ta amsa ta duba sai taga abaya ne a ciki da wani zundumemen hijab da ta tabbata sai yakai mata har kasa..da dan murmushi ta dubeshi tana fadin"thank u"..bude motar yayi ya fita ya saki dan guntun smile shima kafin yace"u are welcome"..daga haka ya wuce gaba tana binshi a baya har cikin gidan...har yanxu suna nan zaune a parlor ya karasa ciki ya zauna ita kuma Aysha gaishesu tayi snn ta wuce daki don Allah Allah takey ta kira Billy da besty ta sanar musu tafiyanta gobe ne...Aunty Munubiya ta bita da kallo har ta shiga flat din Mummy snn ta juya tana kallon Bobby dake zaune kusada ita..ya saki dan murmushi yana shafa kai baidai ce mata komai ba...itama bata ce komai din ba ta maida hankali ga hiran da suke wanda mostly na zuwa Gombe da zasuyi ne cikin sallah.

Lamido na shiga daki daukan waya tayi ta shiga kiran Billy ta fesa mata zancen tafiyarta saudi gobe suna gamawa ta kira besty shima ta fesa mishi..tana shirin kiran Hamma taji karfe nawa ne flight din nasu kiran Prof ya shigo wayarta...dagawa tayi sukasha labari abunsu shima ta sanar mishi zata tafi Umrah gobe amma koda wasa bata fada mishi cewa tana gidansu proprietor ba don tasan for sure hakan zai bata mishi rai...saida suka gama hiransu snn ta kira Hamma shima dai labari sukasha bayan sun gama ta dauki wayan nata ta koma parlour.

Washegari around 11 ta gama shirya kanta tsaf cikin dogon rigan daya siyo mata jiya blue black..tayi veiling da mayafin rigan ta dauki dan small bag daya hado mata dashi duk a jiyan tasa phone dinta a ciki da 'yan abubuwanta snn ta rataya bag din a shoulder dinta ta fito tanata baza kamshi...Aunty dake zaune tareda Mummy a parlor tana ganinta tace"fa tabarakallahu ah'sanul khaliqeen..sannu Aysha"..dan murmushi ta saki kanta kasa ta karaso cikin parlon tana gaishesu kowa na yaba irin kyawunda tayi yau din nan...Bobby da ya gama shiryawa shima yana fitowa daga flat dinshi idanunshi basu sauka ko inaba sai kanta..heart dinshi har wani irin tattarewa yayi ya koma can gefe guda ya cushe sbd tsabar kyau daya ga tayi..duk yanda yaso ya dauke idonshi a kanta kasawa yayi..tayi mishi kyai fiyeda duk tunanin mai tunani...lokaci daya kuma wani irin kishi ya lullu6eshi daya tuna jrgi zataje ta hau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login