Showing 177001 words to 180000 words out of 231169 words

Chapter 60 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9699

a gaba da fada bayan ba laifin komai tayi ba"..murmushi Ammi tayi tareda mikewa daga kan gadon da take zaune tace"Adda bakisan halinta bane idan ba haka nayi mata kunya zatazo tana bani a gaban jama'a..shegen rawar kai gareta kmr ba bafulatana ba".

Suna bar gidan direct gidan uncle dinta suka wuce da kafa tunda ba wani nisa ke tsakaninshinda nasu gidan ba..suna shiga ta hadu da wata cousin dinta ta 6angaren Ammi mai suna Walida da taba dade da zuwa ba..aikam suna ganinta suka rungume juna suna murnan zuwanta..abinci kadai sukaci bayan sallahn la'asar wanda zatayi musu red henna tazo tunda gobe iya black za'ayi a wajen henna party..daga ita sai Jessy da gajeren wando ta zauna aka fara mata lallen yayinda Billy da Walida keta faman dirkan hira kaman wanda suka shekara da sanin junansu..kafin a gama mata wasu daga cikin cousins dinta dake nan cikin estate din suma duk sun karaso dan haka sukayi reras sunata hira da labari abunsu sai tsokanar amarya suke Billy na tare mata...bayan ita suma duk sauran wanda suke son red din akayi musu ciki harda su Hajia Bilkisu kirjin biki da kuma wasu daga cousins dinta na wurin...har matar gidan saida mai lallen tayima daga nan kuma Ammi ta turo aka dauketa zuwa can gidan nasu don tayi musu nasu lallen suma.

Henna Party...

Tun safe mutane keta shirin tafia henna party da za'ayi a makeken compound din gidan wani uncle dinta dake nan cikin estate din..anyi decorating wajen in a traditional way wurin yayi kyau sosai da gani traditional event za'ayi a wurin...masu kidan kwarya tuni sun fara aikinsu yayinda wasu da suka fara zuwa wurin suketa tikar rawa.
Amarya Aysha bata iso wurin ba sai around 5 tayi matukar kyau cikin wani saqi army green kasancewarta fara sai duhun kayan ya sake fito da ainihin hasken skin dinta..dinkin straight gown akai mata da head dinta da aka daura ya tashi sosai kmr dai na amare..tun daga kan shoes har purse dinta duk sunyi matching da kayan jikinta...tayi kyau sosai da light make up dinta daya sake fito da kyan nata..su Billy da sauran cousins dinta sai few friends dinta ne sukayo mata rakiya har zuwa wurin event din...kafin su shiga da ita ciki Billy dake sanye da ankonsu na bridesmaids tayi kyau sosai itama kasancewarta best friend din amarya ta matso kusada ita da sauri tana daga musu hannu tace"you people should wait inyi video din shigan nan in turama angonta don da gaske idan bai ga wankan nan ba yau da kyar zai iya bacci"..daria gaba daya suka saka itadai Billy ta dauko wayanta ta shiga yi mata pictures da videos saida ta gama snn ta maida wayarta cikin jaka daga nan Kuma suka sake jeruwa suka shigo da ita ciki bayan an sakar musu kida na musamman domin shigo da amarya..bayan sun kaita inda aka tanadar mata ta zauna sai suka koma tsakiyar fili suka dan taka rawa daga nan kuma kowa ta nemi wuri ta zauna..su Billy table guda suka cika na yan FCNM da suka zamu zuwa bikin kowacce tayi shar da ita exactly yanda qawayen amarya keyi idan ana bikin qawar su..each table yana cike da kayan ciye ciye iri iri na gargajia bayan sun gama ciye ciyen henna artists da sukazo suka fara aikinsu...lalle sosai akeyi musu baqi kusan duk Wanda tazo wurin babu wanda hannunta ba lalle a jiki..amarya dai na zaune inda aka ajiyeta duk zaman wurin ma ya isheta kafin a gama nata lallen...tun kafin a gama photographers keta aikinsu..masu daukan pictures nayi masu video coverage suna suna nasu..a takaice har akayi sallahn magrib suna abu daya..dakatawa akayi sukai sallah bayan sun dawo Kuma aka sake sakar musu kida suka cigaba da rawa wnn karon har amarya Lamido kasa cigaba da zama tayi don haka ta taso ta shiga cikin qawayenta sukaita rawa suna nishadinsu a cewarta dai Ammi ba zuwa zatayi wurin ba...bayan wani lokaci su Aunty Fiddausi da sauran aunties da mata uncles dinta suka zo wurin nan ma kida aka sake sa musu sukaita rawa suna 6arar da kudi kmr basu sa zafin nemansu..Aunty Fiddausi ta kama hannun Aysha sukaita rawa abunsu kmr wasu qawaye aikuwa yan uwan Ammi sukayi caa a kansu suna watsa musu kudi..inshort dai basu suka tashi taron ba sai after 8..zuwa lokacin kowa jiki yayi liqis don rawar da sukayi a wurin bana wasa bane..motoci aka kawo musu suka dauki amarya da friends dinta zuwa gidan uncle dinta yayinda su Aunty Fiddausi suma suka nashi motocin da sukazo dasu suka wuce.

Suna komawa gida Aysha ta cire kayan jikinta ta shiga wanka don yanda takejin kayan duk sun takura mata..tana fitowa ta dauki sabon jessy dinta na Man u as usual ta saka ta hada da gajeren wandon rigan snn ta zura katon hijab ta tayar da sallah..tana idarwa ta cire hijabin kanta ko hula babu ta dauki waya ta fita parlor inda qawayenta suke sunata maida zance suna daria...gaba dayansu suma sun canxa shiga zuwa na bacci kowa kuma ta gabatar da sallahn da ake binta kafin su zauna..tsakiyarsu ta shiga ta zauna Billy dake kallon wayarta tace"Lamido kinsan ya mukayi da mijinki kuwa?.."girgiza kai tayi tana kallonta meaning bata sani ba..Billy tace"hmm ai Ina tura masa videos din nan na daxu ya kirani wai amma bamuyi masa adalci ba..nace sir rashin adalcin me mukayi wai da muka bar masa ke kika fita a haka nace dole fa yayi mana hakuri har a gama bikin nan"..daria gaba daya suka saka suna tsokanarta ita dai tayi gum babu bakin mgn.. kmr kuwa yasan mgnrshi sukeyi sai ga kiranshi ya shigo..ta mike da sauri ta fada daki hadda su rufe kofa snn ta zauna kan gado ta dauki wayar..ko sallama baiyi ba yace mata"lets video call"..tace"ohk"..shi Kuma ya kaste Kiran sai gashi ya kirata video call..dauka tayi tana kallon screen sai ta ganshi zaune a bedroom dinshi yana sanye da white shirt da three quarter fuskan nn nashi a shagwabe kmr zaisa mata kuka..kallon yanda yayi da face dinshi tayi sai ta saki smile tana karema beard dinshi da yayi mata kyau sosai sbd gyaran fuska da akai mashi kallo..kawai sai taji dama kusa da ita yake yaudai takai hannu ta taba wnn sajen nashi da take ganin kmr duk dunia babu wanda gemu da saje kema kyau kamarshi..lumshe ido tayi tana sake fadada smile dinta..yayinda take kallonshi shima kallon nata yakeyi ganin jessy a jikinta ya dan bata ranshi yace"love meye wnn kike wearing?.."kallon jikinta tayi kafin ta maida kallon gareshi tace"riga ne mana partner"..tana rufe baki"of all rigunan da kike dasu ki rasa Wanda zaki sa sai na 'yan ball..what is wrong with you?.."kallonshi ta tsaya yi har ya gama mgn snn tace"ka cika rigima wlh..riga ne fa kawai ba wani abu ba"..tana rufe baki yace"nidai banasonki da kayan Manchester din nan seriously"..gyada kai tayi tana cewa"to na dena sawa daga yau..are u happy now?.."girgiza mata kanshi yayi yana turo baki yace"Kuma gashinki a bude"..murmushi tayi tareda mikewa ta ajiye wayar jikin mirror yanda zai na kallota daga nan tace"to bari in dauko hula in sa"..daga haka ta juya zuwa wardrobe ta shiga neman hula ko dankwali da zata rufe gashin nata dashi..tana juyawa ya bita da kallo ganin dan wandon dake jikinta ya lumshe ido jin gabanshi har faduwa saida yayi..wandon ya kamata ne sosai gashi kuma gajere baifi iya guiwarta ba..sake bude idon yayi daidai lokacinda tayi bending tana kokarin zaro hula daga cikin kayan Billy kawai sai ya kashe kiran da sauri yana sauke numfashi..tana gama daukan hulan ta juya tana kallon wayan sai taga ya kashe dan haka ta saka hulan a kanta da sauri snn ta sake kiranshi video call din amma har ya katse bai dauka ba..sake kira tayi still no answer tana shirin sake kira sai kuma kiranshi ya shigo amma voice call ba video call..picking tayi ta Kai kunnenta kafin tayi mgn yace"let's not video call again plss..matsala za'a samu"..wara idanunta tayi tace"matsala kuma partner"..gyada kanshi yayi tareda fadin"yes ko a yanxu nasan na gama samun matsala..Allah yasa dai ba haka kike fita kowa yana kallonki ba"..sauke ajiyar zucia tayi kafin tace"da hijab nake fita..amma what's wrong naji kace ka samu matsala"..shiru yayi kmr bazaice komai ba sai can yayi kasa da murya ya shiga furta mata mgnr da tunda suke dashi bata ta6ajin such words daga bakinshi ba..ai da sauri ta kashe wayar tana kwalo idanu waje kmr munafuka..har wani seizing taji numfashinta nayi kmr zai dauke..wai meyake damunshi ne these days?..gaba daya ya canxa mata wlh..sai yayita furta mata duk abunda yazo bakinshi shi ko kunya bai dashi...Billy ce ta shigo dakin taga yanda take kwalo idanu waje tace"what?.."girgiza mata kai tayi alamar ba komai..Billy ta saki smile tareda karasawa ta dauki charger dinta ta juya kafin ta bar dakin tace"yarinya ta kusa jin mazaaa..wlh har tausayi kike bani Lamido"..harara ta Maka mata mai kyau tana wani daure fuska tace"kinga banason irin haka Billy..meye wani na kusa naji maza sai kace yar iska"..juyowa Billy tayi tana kallonta da wani dan iskan murmushi a fuskanta tace"wnn mijin naki dai da gani ba hakuri zaiyi ba yaseen..Proprietor da ko kallonki yakeyi sai an fahimci wani abu..yarinya idan ma zaki shirya ki shirya don aiki ne gagarumi yake tunkaroki"..tana gama fadin haka ta fice daga dakin tana kyalkyala mata daria ita Kuma Aysha komawa da baya tayi ta zauna gefen gadon tareda dafe chest dinta idanu a waje sosai tace"na shiga uku ni Aisha..anya kuwa ba fasawa zanyi ba?.."















Rano✨





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
55
Cocktail Party...
Karfe shidda da wani abu aka gama wa amarya make up dinta..tana sanye cikin gown na wani sky blue material..head dinta ma da akayi mata turban style blue sai su earrings da rings silver likewise takalmi da purse dinta..light simple make up da akayi mata ba karamin amsanta yayi ba dama ga lalle tasha red and black da suka sake haska pure white skin dinta...Billy ce ta shigo dakinda take cikin ankon da sukayi na dark blue material itama tayi kyau har ta gaji da haduwa..wayanta ne ya fara ringing ta koma gefen gado ta zauna ganin besty ke kira..daukan wayan tayi tana wani daure fuska kmr yana gabanta tace"besty what is it again?..why are u disturbing me?.."daga daya 6angaren Sa'eed ya saki murmushi yana shafa kanshi yace mata"wai yanxu besty har yanxun mgn bai wuce bane?..nace maki fa gobe zan taho inshaAllah"..sake 6ata rai tayi tana turo baki tace"amma ai ba gobe mukayi dakai zakazo ba yau kacemun zakazo"..yace"to nidai dan Allah kiyi hakuri..i promise idan nazo gobe bazan dawo kd ba har sai an kaiki gidan Proprietor".. murguda baki tayi tana cewa"dole kace haka dama ai..kuma idan bakazo gobe ba dena kulaka zanyi wlh"tana rufe baki yace"bazai ma kaimu ga haka ba Hajia besty amaryar Proprietor"..dan murmushi ta saki kafin suyi sallama abd jiranta da aka fara yi..tana gamawa ta mike make up artist ta sake gyara mata face dinta snn ta fito daga dakin hannunta rikeda purse dinta..qawayen ta dake zazzaune parlor suna ganin fitowarta suka saki ihu suna yaba irin kyawun da tayi..banda murmushi ba abunda take musu ganin kusan kowaccensu ta fito da waya tana daukan pictures..suna cikin daukan pics din Husna ta shigo parlon itama taci ado har ta gaji da haduwa..kallo daya zakayi mata ka gane sister din amarya ce sbd tsabar kyau da tayi..ta karaso ciki tana duban yanda suka wani baibayeta suna hotuna tace"Adda jiranku akeyi fa tun daxu..ga motoci can a waje duk ku suke jira"..da sauri suka karasa pictures dinsu suka fita..ko a wajen ma duk wanda ya kalli amarya saiya furta MashaAllah sbd tsabar haduwan da tayi..mota aka bude mata ta shiga sauran friends dinta ma suka shiga aka kwashesu zuwa hall da za'ayi event din..tun suna hanya Bobby ke kiranta tana gani bata dauka ba dan da gaske ita dai tsoro yake bata yanxun..haka nan ta dauki wayanshi yazo yana kunyatata a gaban qawayenta.

Yau ma dai kamar jiya event yayi kyau sosai Kuma ya qayatar da mutane..idan kaga yanda Aysha ta dirki rawa bazakayi zaton she's the bride ba..da yake babu manya Kuma ba maza daga ita sai qawayenta sukasha sha'aninsu..pictures da video coverage yau ma sunyi su kmr ba gobe..inda Billy tana gama daukan nata ta turama Bobby da tun daxun yake sake jaddada mata ta turo mishi hoton amaryarshi ya gani...event yayi dadi sosai sunci sunsha Kuma sunyi rawa kmr yanda sukeso..Lamido ji take ko event din jiya bai Kai na yau yi mata dadi ba..sunsha sha'aninsu ne itada friends dinta abun ba'a cewa komai...a takaice basu bar wurin ba sai around 9 o'clock..kai tsaye ana daukansu gida aka wuce dasu kowacce jiki yayi laushi sbd rawan da sukayi.
Yauma kmr jiya suna komawa gida ta sake yin wanka ta saka sleeping dress suma su Billy duk sun sauya kaya zuwa na bacci Wanda zasuyi wanka sunyi wanda baza suyi ba kuma sun wanke make up dinsu bayan sun rama sallolin da ake binsu..ta jona wayarta caji snn ta fita parlor inda sauran suke nan sukaita maida yanda akayi suna darawa abunsu...kusan raba dare sukayi suna labari a parlor sai wajen 1 suka mike kowa ta nemi makwancinta...tana daukan wayanta ta zare Ido ganin missed calls dinshi kusan 20 a wayar..komawa kan gado tayi da sauri ta zauna tana dialing number nashi..har ya kaste bai dauka ba tana shirin sake dialing kuma sai gashi ya kira..tana dauka tun ma tayi mgn ya shiga tambayarta inda taje ta bar wayarta haka..hakuri ta bashi tareda mishi bayanin ta fita parlor wayan kuma ta barshi daki yana caji..hira sosai suka shigayi irin na masoya Billy na kwance tana jinsu har bacci ya dauketa basu dena wayan nan ba inda yawanci hiran nasu bai wuce akan tahowa shima da zasuyi a gobe ba don dashi za'ayi Mother's Eve..daga nan zasu kwana Saturday bayan daurin aure zaa wuce mishi da amaryarshi..sosai yake farin cikin hakan sbd abunda yake hange daga nesa ne yake dab da karasowa kusa dashi...ga su Mummy suma da suketa faman shiri wai zasuyi traditional event dinsu na Igbo ranan da aka kawota..shi gaba daya ba son harkan events din nan yake ba wlh..a takaice Bobby bai kashe wayarshi ba saida yaji ta fara bacci snn ya saki smile tareda kashe wayar cikin ranshi yana ayyana very soon shima zata fara bacci a kusa dashi kilan ma a jikinshi..tunanin hakan da yayi saida yasa ya saki wani murmushi na musamman yana shafa gashin kanshi.

Mother's Eve...

Misalin karfe 12 da wani abu Mummy da jama'arta gaba daya suka sauka garin Gombe..gida guda Waziri yasa aka ware musu ita da 'yan uwanta da kuma sauran mutanenta..Aunty Sumy ma gayya guda tayi na kanta abunka da babbar yayar ango.

A 6angaren oga Bobby kuma gida suma Waziri ya bashi ya sauka tareda abokanshi..duk yanda yaso Waziri ya bari suje hotel hanawa yayi yace dole saidai su zauna gidan daya basu tunda yanada girma zai daukesu gaba daya shi kuma basu gane ba hayaniya ne baiso shiyasa yaso suyi lodging a hotel tunda kowa separate room za'a kama mishi so babu wanda zai dameshi amma nan ko bai hada daki da kowa ba yasan dole zai hada da Nur da yakeda shegen tsokana da rawar kai kmr shine angon..shi duk randa akace yau ana auren Nur baisan irin giggiwar da zaiyi a matsayinshi na groom ba..gaskia idan haka ne Miemie ta shiga uku..kawai sai ya saki murmushi yana girgiza kai.

Karfe shidda da wani abu suka gama shiryawa duk suka shiga motocinsu wasu suka fara tafia hall da za'ayi event din shi Kuma ango da some of friends dinshi irin su Nur suka tsaya gidan da zasuyi picking amarya..dama tun kafin zuwansu an kammala mata shirinta tayi kyau sosai cikin coffee lace dinta daketa walwali..daurinta yayi daidai dana amarya ga kuma gashin goshinta da aka sa musu gel akayi wani coiling dinsu suka kwanta luf a goshin nata..fuskanta na rufe da wani net da ake iya hango fuskan nata daga ciki..Billy ce ta fito da ita tareda walida cousin dinta..ita tana daga baya tana dage nata gown dinta dake jan kasa walida kuma na daga side dinta suna tafia a tare...tun daga cikin mota Bobby ke kallonta gabanshi har wani faduwa yayi sbd kyau da yaga tayi..she looks extremely gorgeous har baisan da wane kalma ma ya kamata ya danganta kyawun da tayi dashi ba..relaxing yana cigaba da kallonta hannunshi daya dafe da saitin heart dinshi da yaji fitowa zaiyi daga kirjinshi sbd mugun bugawar da yake...Nur dake zaune driver seat yana ganin sun fito ya fita daga motar da sauri yana kallonsu baki a washe yake fadin"MashaAllah Tabarakallah..Lamido kece kuwa?.."murmushi tayi tana sunne kai daidai lokacinda suka karaso wurin..Nur da kanshi ya bude mata baya inda Bobby ke zaune har yanxun yana dafe da zucia ta karasa a hankali ta shiga cikin motar kafin ya kulle kofa shima ya koma driver seat..Walida da Billy suka shiga motar Hamma Najeeb da bai dade da zuwa ba suka farayin gaba kafin shima Nur ya tada nashi motan su tafi...wani irin tsit cikin motar yayi yanda kasan babu wani abu mai rai da motsi a ciki..ga kuma kamshin perfumes dinsu da ya baibaye ko ina a cikin motar..ta mirror Nur ya kallesu yaga yanda har yanxun Bobby ke jingine jikin kujera ya wani lumshe ido ita kuma tayi kasa da kai tana wasa da purse dinta..murmushi ya saki yana girgiza kai cikin ranshi yace"strange couple"...har suka isa hall din babu wanda yayi mgn cikinsu..shidai Nur yana gama parking ya bude motar ya fita don ya basu space su dan tattauna before azo a shiga dasu ciki kuma..kmr abunda Bobby ke jira knn ya bude idon a hankali tareda karkatawa gaba daya yana kallonta...dagowa itama tayi ta kalleshi sai kuma ta saki murmushi tareda dauke kanta..a hankali ya matsa kusada ita tareda kai hannu ya yaye net da aka rufe face dinta dashi..nan take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login