Showing 222001 words to 225000 words out of 231169 words

Chapter 75 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9659

tsohon ciki Aysha Ina ke ina zuwa Gombe a yanxu?..ki bari idan kika haihu lafia sai kizo amma dai yanxu bazai yiwu kizo har Gombe da tsohon ciki ba"..kmr zatasa kuka tace"Ammi ba tsoho bane it's just 6 months ai zan iya zuwa"..dan murmushi Ammi ta saki tana girgiza kai tace"6 months din ne bai tsufa ba?..kinfiso kizo kiyita yawo da ciki knn kowa yana kallonki".. tayi shiru batace komai ba Ammi ta sake cewa"idan ma kinzo yanxu nasan bazai fi kiyi one week ba amma idan kika bari kika haihu saiki dawo gida gaba daya idan kinyi 40 sai ki koma"..nan da nan ta washe baki jin abunda Ammi ta fada tace"to Ammi na bari"..Ammi da yanxu sosai suke shiri da yar tata dan a ganinta tayi hankali tace"yauwa ko kefa..Allah dai ya saukeki lafia"..tayi murmushi cikin ranta tace"Ameen"..daga haka sukayi sallama da Ammi ta ajiye wayar.
Ana kawo mata wainar flour ta tasa a gaba ta faraci tana hadawa da yaji kaman yanda ta saba..ga kuma sauran tamarind dinta na jiya da tasa a fridge shima tana korawa dashi..ita yanxu har ta mance yaushe rabonta da shan tea dan koda safe ko rana ko dare batada abunsha daya wuce tamarind..ko ruwa bata cika sha ba yanxu sbd batajin dadinshi a baki amma tamarind Kam yana mata dadi sbd wnn tsamin da yakeyi..saida taci tayi nak snn ta ture plate din tacigaba da kallonta time to time tana duba agogo ganin har rana ya farayi bai dawo ba..har ta gaji da kallon dayi bacci a nan cikin parlon kawai taji ana shafa cikinta ta bude ido da sauri tana ture hannunshi tace"meye haka?.."zaunawa yayi nan kusada ita yana kallonta da murmushi yace"ina mgn da babyna ne fa"..murguda baki tayi tana hararanshi shi kuma yayi pecking goshinta yana cewa"to am sorry"..banza tayi mishi batace komai ba shima bai sake mgn ba sbd kiran Nur daya shigo wayarshi..dauka yayi suka gama mgn snn ya janyota jikinshi yana gyara gashinta da bata gyarashi ba yace"what is it baby?..waya ta6amun ke?.."tale baki tayi kmr zatasa kuka tace"shine ka dade baka dawo ba"..yace"sorry naje hospital ne sai kuma Nur ya kirani wai da akwai emergency a college clinic so shine naje na dubata"..da sauri ta dago tana kallonshi jin ya ambaci college clinic tace"u mean college clinic kaje?.."gyada kai yayi yace"yes"..tace"kuma mara lafiyan da ka duba mace ce?.."yace"mace ce mana baby akwai wani problem ne?.."tun bai rufe baki ta hau girgiza kai tana hawaye tace"amma ka cuceni"..mikewa take kokarinyi yayi saurin dawo da ita jikinshi yana patting bayanta yace"subhanallah me nayi?.."tace"amma tun yaushe nake fada Maka banson kana zuwa clinic din nan..ni college din ma da inada dama wlh bazaka sake zuwa ba dan bakasan yanda mata suke kallonka bane"..wara ido yayi yana kallonta da murmushi yace"so kema kina kallona knn lokacin da kike makarantan?.."harara ta watsa mashi jin zai canxa mgn tace"don't change the topic"..kissing gashinta yayi yace"am not changing the topic baby i just want to know..kinsan dai dunia ya nade bazan so wata mace apart from u ba so ki kwantar da hankalinki"..sake turo baki tayi tace"how will ever kwantar da hankali bayan nasan yanda halin maza yake especially now that my body is Chang..."bai bari ta karasa ba yace"kome zaki zama ni ina sonki haka and ba abunda zai canxa hakan..i love u for who you are bawai dan kyawunki kadai nake sonki ba so stop saying your body is changing indai baso kike muyi fada ba..i love u and only you".. kallonshi tayi yanajin wani irin sanyi na mamaye zuciarta..wato she is so lucky to have found this guy..he is so amazing and she loves him so much..rungumeshi ta sakeyi tana sakin murmushi tace"to na dena..amma da gaske tsoron yammata nakeji"..hannu yakai yana shafa kanta yace"u don't have to baby..duk macen da zata kalleni saidai kallon kawai amma bazata iya dauke heart dina wajenki ba for i love u unconditionally"..smile ta Kara saki tana shakan kamshin perfume dinshi tace"nima i love u more partner..u are my world"..dago face dinta yayi yayi pecking forehead dinta yana cewa"now tell me are u among wayanda suke kallona lokacinda kina school?.."murmushi ta saki tana gyada kai tace"sosai ma amma kasan irin kallon da nake maka?.."girgiza kai yayi yana smiling yace"no"..tace"irin masifaffun inyamuran nan masu shegen taurin kai..har cewafa nake da kyar in baka cikin masu assasa yaki Biafra"..wara idanu Bobby yayi yana kallonta yana daria yace"so yanxu baby kallon mai son a raba Nigeria kikemun?.."kama hannunshi tayi tayi pecking tana cewa"it was then ai..amma yanxu i know better..nasan duk dunia za'a dade ba'a samu namiji kaman kai ba shiyasa nakesonka sosai"..murmushi shima ya saki yana rike da hannun nata yace"amma gaskia baby baki kyautamun ba..koda yake ba laifinki bane laifina ne dana sa maki ido ma takura maki"..murmushi take tana kallonshi as abubuwan da suka faru rush back to her tace"ai gaskia partner ba karamin wahala ka bani ba..ka takuramun a lokacin nan kullum saika mun masifa"..murmushin shima yakeyi yace"and believe baki kaini shan wahala ba..duk wnn abun da nake maki qi fadi ne kawai amma Allah kadai yasan halinda nake ciki a lokacin"..daria ta saki sosai ta rungumeshi yace"shiyasa idan kika haifamun babygirl kaman ki bazan yadda in kaita irin colleges din nan karatu ba sbd kar taje tarwatsa rayuwar proprietor kmr yanda kika tarwatsa nawa"..dukan chest dinshi tayi cikin shagwaba tace"tarwatsa rayuwarka ma nayi koh?.."ya sake rungumeta da hannunshi daya dayan hannun kuma ya dauko wani abu cikin pocket dinshi snn ya dagota yana cewa"now close ur eyes in nuna maki wani abu"..ba musu ta rufe eyes dinta shi kuma ya bude hannun nashi snn yace ta bude idon..tana budewa taci karo da zabunanta na gold guda biyu daya ta6a kwace mata a college aikam ta wara idanu sosai tana kallon rings din tace"oh my Godd..kasan gaba daya na mance dasu wlh"..kama hannunta yayi ya shiga kokarin zura mata su a fingers dinta yace"ai ni ban manta dasu ba"..tana daria tace"ai ranan haushinka naji bafa daka kwacemun su"..shima yana dariar yace"ni kaina a lokacin saida naji haushin kaina ta yanda har idanuna suka gano abunda ko Nur da yake mgn dake bai gani ba..a duk lokacin da muka hadu kokari nakeyi sosai na ganin ban kalleki ba amma bansan ya akeyi ba kawai saidai in tsinci kaina Ina kallonki kuma ba tareda na gaji ba especially idan kikasa wnn glasses din naki".. kallonshi kawai takeyi tana murmushi har ya gama saka mata rings din snn yakai hannun bakinshi yayi kissing yana cigaba da murmushi yace"ya kamata dai acigaba da samun glasses din nan a gida ina gani dan da gaske ji nake kaman in daukeki duk lokacinda na ganki dasu"..har yanxu murmushi take tace"da wnn tulelen cikin ne zan wani dinga da glasses?.."kissing cikin yayi yana cewa"itama zan siyo mata irin naki yanda idan kin haihu sai ku dinga sakamun Ina gani"..daria kawai ta saki tana girgiza kai shi Kuma ya sake janyota jikinshi ya dan rage muryanshi yace"kinsan fa ni mace nakeso ki haifa"..gyada kai tayi tace"i know..ni kuma nafison namiji"..kallonta kawai yake yana murmushi lokaci daya kuma ta fara ganin wasu abubuwa cikin idanunshi..a hankali yakai hannu yayi cupping fuskanta fasu snn ya dora forehead dinshi akan nata..kallon eyeballs dinshi takeyi kmr yanda shima yake kallon nata dan zuwa yanxu tana iya daukan lokaci tana kallon idonshi amma dukda ba kmr yanda shi yakeso ba..a hankali ya lumshe ido tareda dora lips dinshi akan nata murya can kasa yace"baby please..i missed us"..hannunta ta zagaya wuyanshi dashi snn tayi grabbing bakinshi shima nan da nan ya kama kaman magnet..daga haka kuma na baro musu parlon and ban sake dawowa ba sai bayan wata uku...lol😂

Bayan wata uku...











Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
69
Bayan wata uku...
Cikin Aysha ya shiga wata na tara knn cif and edd dinta baifi saura 3 days..gaba daya ta canxa daga Lamido da kuka sani a baya ta dawo wata irin salaha kmr dai ba itane ke ba iyayenta ciwon kai ba..sosai ta zama kalar tausayi dama ga cikin nata da girma sosai musamman yanxu da haihuwan ta kusa sai girman ya sake fitowa..ga kuma nauyinshi da takeji wani lokaci har cewa take kilan twins zata haifa maybe scanning machine dinsu ne baida kyau shiyasa bai nuna haka ba..duk ta Fadi haka saidai Bobby yayi daria dan yasan baby daya ne cikinta saidai girman kawai..ga masifa data koya da rashin hakuri Dan abu karami zata hau fada tana cewa ai dama dole ya dena sonta sbd yanxu tayi Muni shidai banda daria ba abunda yake mata..wani lokaci har video yake mata bata sani ba idan tana wnn sababin yasan idan ya nuna mata nan gaba daria zatayi..sai kuma fever da take yawan kwana dashi da ciwon baya wanda har yasa take cewa kilan mutuwa zatayi..sosai take daga hankalinshi duk tayi wnn mgnr amma bai taba nuna mata ba.. addu'a kawai yake mata tareda fatan Allah ya sauketa lafia..a bangaren mummy ma tana kulawa da ita sosai dan da dadewa itace ta dauki nauyin dafa mata duk abunda takeso tunda ba komai take ciba..yanda take lalla6ata ita har kunya ma takeji amma sai taga su ko ajikinsu..siyayya kuwa zuwa yanxu ba abunda basu gama siya ba tun daga kan kayan baby har zuwa ita kanta nata kayan..bedroom guda ya ware cikin nata yasa akayi renovating dinshi zuwa baby room mai kyau aka kuma cikashi da kayan yara iri iri tun daga kan furnitures har zuwa su toys da sauran kayan wasa na yara..tsakaninta da Amminta ma yanxu mutunci sukeyi sosai dan yanxu tayi hankali ta dena rashin kunya a cewar Ammi shiyasa suke dasawa abunsu..kusan kullum sai sunyi waya da ita dan ko ita Ayshan bata kira ba Ammi zata kirata taji ya jikinta..tana kuma turo mata addu'o'i tace taitayinsu daga nan har lokacin da Allah zai kawo haihuwar wai sai yazo mata da sauki..sosai itama take tausayawa 'yar tata sbd halin da take ciki shiyasa Husna na gama ssce daddy yace tazo ta zauna tareda ita ko ba sbd aiki ba at least zata dan dauke mata kewar gida da take fama dashi..zuwan Husnan kuma ya yayi mata dadi sosai dan kusan kullum suna tareda ita da Miemie a gidan su suke mata komai saidai mai aiki ta tayasu kawai..shima Bobby yana bakin kokarinshi kwarai wajen ganin batayi lacking wani abu daga gareshi ba including time dinshi da kuma caring..sosai yake tsayawa ya kulada ita don ko wurin aiki ma sai ya tabbatar ya gama mata komai snn yake wucewa hakan da yakeyi kuma ba karamin faranta mata rai yake ba..tana jin dadi sosai idan taga yanda daga shi har Mummy da siblings dinshi ke nuna tsantsar so da kula wa cikin nata har watarana takejin ta matsu ta haihu sbd taga irin kaunar da zasu nunama babyn..gani take kmr Mummy da Bobby sunfi ita kanta da babyn ke jikinta kaunarshi amma batasan ko dan riga yazo dunia bane..a halin yanxu dai duk wani fatanta bai wuce Allah ya sauketa lafia ba.

Yau Friday suna zaune parlor ita da Miemie da Husna suna kallon wani film Sab ya shigo gidan da sallama yana hararar Miemie da gaba daya hankalinta ke ga film da suke kallo..bayan ya karaso ciki ya zauna sai ya dan saki fuska yana duban Aysha da murmushi yace"sannu Aunty Aysha"..murmushi itama ta saki tana girgiza kai tace"bazaka dena cemun sannun nan ba koh?.."yana cigaba da daria yace"ai dole ace maki sannu matar Uncle Bobby..wnn babyn namu nasan da kyar idan baya baki wahala don da gani nasan fitina zaiyi wlh"..daria gaba daya suka saki har su Husna da hankalinsu ya dawo kan hiran nasu..Husna tace"wlh uncle Sab kmr kasan nima tunanin da nakeyi knn..na tabbata indai ya dauko halin Adda to wlh ba karamin fitinanne za'ayi ba"..ta karasa mgn tana daria Aysha Kuma tace mata"zanyi maganinki wlh..ki bari insamu time dinki"..Sab yace"ai idan ya dauko halin babanshi bayan fitina ma sai ya hada da masifa da rashin mutunchi..ta6 Uncle Bobby ai ba baya bane wajen wadan nn dabi'un"..da sauri Miemie tace"wlh kuwa uncle Sab..ni kaina gani nak..."bata karasa ba ya katseta ta cewa"C'mon keep quiet wayasa dake a wurin nan?.."turo baki tayi tana rungume hannunta tace"ai nima ba da kai nakeba"..kwafa yayi yace"kicigaba da murguda min bakin nn watarana saina karyashi wlh..badai ni kikaje kikama munafurci a wurin Mummy ba..zan kamaki ne"..sake daure fuska tayi tace"nidai gaskia na fada mata ai..kuma ba ruwanka dani Uncle Bobby yace ka dena shiga harkata"..ya bude baki zaiyi mgn Lamido tace"ya isa haka dan Allah..na rasa meyasa ku kullum cikin fada kuke kmr tom and Jerry".. Sab yace"yarinyar nan batada kunya bakisan halinta bane..wai har ni zataje tayima gulma a wajen Mummy"..Husna tace"ASP Uncle Sab da gaske ba gulma tayi Maka ba..a gabana Mummy ta tambayeta"..wani irin daria Sab yayi yana cewa"bazaki dena Asp Uncle Sab din nan ba koh?.."dariar itama takeyi tace"to ai Asp ne naga"..murmushi kawai yayi ya gyada kai kafin wani cikinsu ya sake mgn Bobby da Nur sun shigayi parlon a tare..da sauri Sab ya mike yana kallonsu da murmushi yace"sannunku da zuwa"..Bobby yace"kai baka zuwa sallahn jumu'a knn?.."Sab yace"yanxun na dawo ai..ask Aunty Zata fada maka ban jima da shigowa ba"..Bobby bai sake cewa komai ba suka karasa parlon suma suka zauna..Miemie da Husna suna gaishesu suka bar parlon shima Sab yana gama gaisawa dasu ya fita dan dama akwai inda zaije...kallon Aysha da har yanxu take zaune yayi kafin a hankali ya mike ya koma kusada ita ya zauna yayi mata side hug yana fadin"how is my baby doing?.."a dan kufule tace"ban sani ba"..yayi murmushi yana nuna cikin nata yace"bafa wnn babyn nake nufi ba wnn"..hannunshi ta ture daga jikinta tana duban inda Nur yake zaune tace"Sir Ina yini"..murmushi ya saki yana kallonta shima yace"lafia lau Lamido..ya jikinki?.."kanta a kasa tace"Alhamdulillah"..Bobby yace"baby bana hanaki kiranshi da Sir din nan ba..call him Nur mana ai sunanshi ne"..girgiza kai tayi tana dan murmushi tace"bazan iyaba"..tana rufe baki Nur yace"kinji mutumiyar kwarai..duk iskancinka dai haka zaka hakura ka barta tace bazata iyaba"..Bobby yayi daria kawai tareda dan rage murya yana kallonta yace"kinsan mene?.."kai ta girgiza mashi alamar bata sani ba..yace"zuwa mukayi dai yau mu fadawa Miemie cewa muna sonta"..dan wara ido tayi tana kallonshi tace"da gaske?.."yace"eh mana..nine ma zanyi masa zancen sbd a abokin Nur nazo yau ba Uncle Bobby ba"..murmushi kawai Aysha tayi tana girgiza kai tasan wnn mgnr wasa yake mata..mikewa zatayi yayi saurin kamata ya mikar da ita snn yace ta turo musu Miemie idan ta shiga..tana murmushi itadai ta wuce zuwa bedroom dinta ta tura musu Miemie kmr yanda suka bukata...tana zuwa ta nemi wuri ta zauna kasa Bobby yace ta koma kan kujera ta zauna..ba musu tayi hakan sai kuma duk sukayi dif aka rasa wanda zai fara mgn cikinsu..can Bobby ya nisa tareda Kiran sunanta..ta amsa kanta kasa dan har wani faduwar gaba taji tanayi ba gaira ba dalili..a nutse sosai ya fara mata bayani ta sigar da yasan zata fahimce shi sosai.. already dama Saida ya fara mgn da Mummy da parents din Miemie snn yazo gareta so ba tareda wani shakku yake mata bayani ba..itadai tsit tayi tana sauraran yanda yake koda mata abokinshi sai daga karshe kuma yace zai barta dashi ya karasa Mata sauran bayanin..bayan ya bar parlon Nur ya dora daga inda ya tsaya itadai kusan mutuwar zaune ma tayi jin wai da gaske Uncle Nur ne ke sonta..sosai ya kakkashe mata jiki da salon soyayyarshi wanda ita halin yanxu dai bazata iya gane shin tana sonshi ne ko kuma bata sonshi ba..shima baiyi gaggawa ba yace she should go and think about it idan ma tanada Wanda zatayi shawara dashi tayi idan ta gama yana jiran feedback dinshi..haka ta mike ta bar parlon jiki a sanyaye kmr kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Wnn knn...

Washegari bayan ta idar da sallahr asuba ta dade sosai zaune inda tayi sallahr tana ta addu'o'i bayan ta kammala azkhar dinta..Bobby kuma na masjid bai dawo ba..sosai take addu'a tana rokon Allah ya sauketa lafia ya kuma raya mata abunda zata haifa cikin tafarki madaidaici..saida gari ya fara haske snn ta shafa addu'an snn ta shiga kokarin mikewa amma sai me?..kugunta taji ya rike gam ta kasa ko kwakwkwaran motsi a wurin..ta kai hannayenta biyu ta dafe waist din dasu snn ta sake yunkurawa zata tashi sai kuma taji bayanta shima ya rike da sauri ta sake komawa ta zauna ta rintse ido tana maimaita innalillahi a cikin ranta..Saida taji ciwon ya dan lafa snn ta sake kokarin mikewa a karo na uku still taji bazata iyaba dan haka ta koma tacigaba da zama tana salatin annabi..Bobby daya dawo daga masjid direct kitchen ya shiga ya hado mata tea da shanshi ya zama mata constant duk ya dawo daga sallahn asubah dama saiya fara hada mata yake shiga daki..yana shiga ya ganta zaune nan inda tayi sallah ya ajiye mug din hannunshi kan table da sauri ya nufi inda take yana dagota yace"baby are u alright?.."a hankali ta dago ido tana kallonshi yaga eyes din are so red nan take hankalinshi ya tashi baisan sanda ya durkusa nan kusada ita ya kamo hannnuwanta yana tambayanta what's wrong ba..dan murmushi ta saki ganin har hankalinshi ya tashi tace"ba komai fa partner..kawai tashi zanyi naji bayana ya rike amma believe me yanxu banajin komai"..kamata yayi ya mikar da ita tsaye snn ya shiga kare mata kallo wai ko zaiga wani canji tattare da ita still yaga ba komai dan haka ya rike hannunta ya zaunar da ita kan sofa bayan ya zare hijabin dake jikinta..tea dinta ya dauka ya mika mata yace"to ga tea dinki Kisha"..murmushi tayi ta karba shi Kuma ya dauke carpet da tayi sallah dashi ya ajiyeshi inda ya dace snn ya sake dawowa ya zauna nan kusada ita yana kallonta tana shan tea din...bayan ta gama ya sake kamata suka kwanta kan gado ya rufesu da duvet cikin lokaci kankani kuma bacci yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login