Showing 42001 words to 45000 words out of 231169 words

Chapter 15 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9658

basu ta6a yunkurin nemanmu ba...su kuma su Ilham nasan ke da kanki kinsan meyasa banso suje inda mutanen nan sbd ba sonsu sukeyi ba"...hawaye suka shiga sauka fuskanta tace"duk abunda in the past bai kamata mu bari yayi affecting future dinmu ba...we are all Humans Bobby and we all make mistakes...nasan abunda da sukayi is uncalled for amma ya zamuyi?..dole haka zamuyi hakuri dasu tunda sunyi nadama...zumunchi ba karamin abu bane Bobby banaso Allah ya kamamu da laifin yanke zumunta a ranar gobe kiyama"...tana karasawa wasu tawagar hawaye suka sake biyo fuskanta Bobby baisan sanda ya matsa tareda rungumota jikinshi ba...kuka takeyi sosai da alama dama ta jima tana neman inda zatayi kukan...bai hanata ba saida ta dakata dan kanta snn yace"Mummy to kukan ya isa haka plss and we shouldn't talk about them again..am not angry anymore"...ta saki dan murmushi tana share hawayenta tace"then tashi muje kaci abinci"...baiyi musu ya mike ya koma kan sofa ya zauna snn ya janyo table data ajiye abincin akai ya fara cin kayanshi...itama mikewan tayi ta dawo kusa dashi ta zauna snn tace"and mgnr zuwa duba Waziri"...a takaice yace"yana nan Mummy..idan ya dawo zamuje gaba daya mu dubashi..are you happy now?.."sake gyada mishi kai tayi tana murmushi...shi kuma yacigaba da cin abincinshi amma deep down yasan abunda ya fada karya yake...ko kusa baijin zuciyarshi zai iya mance tarin munanan abubuwanda Waziri da iyalanshi suka aikata musu har yaje inda suke..sam hakan ba mai yiwuwa bane ya fada mata ne kawai dan ta dena damuwa amma baida intension din zuwa ko ina..shi a yanda yakeji mafa ko rasuwa waziri yayi saidai suje za'aziyya kawai su dawo amma ba wani zaman makoki da zasuyi tunda bai ta6a daukansu a matsayin Family ba.


Gombe...


Tsaye take a kitchen tana suyan Pancake fuskan nan a tamke kaman wanda aka aikoma da sakon mutuwa...daga gefe kuma Ammi ce tana kokarin hadama Daddy breakfast dinshi a kan tray sai kuma mai aikinsu dake juya pepper soup a kan gas...bayan ta gama hadawa ta dauki tray din kafin ta fita ta dubi Aysha dake faman tura baki tace"kuma wlh idan bakiyi sauri kin gama ba har Lamido ya fita bakuje kun gaisheshi ba zakiga yanda zanyi dake a gidan nan"..mai aikinsu mai suna Asabe tace"da kin barta hajia zan karasa wlh..ita taje tayi shiryawanta"...Ammi tace"bazan barta ba Asabe na lura tunda ta dawo gidan daga kallo sai chatting ta iya bata tsinana uwar komai ko dakinsu saidai Husna ta share..anjima ma ita zaku bawa suyan fried rice tayi ai ba bayi ta ajiye dan sunayi mata girki ba"...tana gama fadin haka ta fita daga kitchen din...ita dai Aysha na tsaye tana aikin gabanta ko juyawa batayi ba amma fuskan nan kaman zatasa kuka...ko Allah yasan ba mai son girki bace ita...gara a bata duk wani aikin gida zatayi amma ta tsani girki shiyasa ko a makaranta Billy keyi musu girki...Asabe na ganin Ammi ta fita ta kashe gas din gabanta snn ta matso inda Aysha take tana amsan spoon din hannunta tace"kawo in karasa kinji indo...ki tsaya daga nan ki huta idan mukaji zata dawo saiki kar6a kicigaba"...nan da nan kuwa ta sakin mata shi tareda matsawa gefe tace"nagode Baaba"...Asabe tacigaba da suyan Pancake ita kuma ta rungume hannu tana kallonta...wayanta dake aljihun jean dinta ne ya fara ringing...ta zaroshi da sauri tana sakin wani smile ganin Prof ke kira tasan yanxu zaiyi flushing wnn 6acin ran da take ciki...saida ta gama kwa6e fuskanta tayi readyn shagwa6a snn tayi picking...a daya 6angaren Professor yace"my baby girl"...ta wani cunno baki sai kace yana ganinta tace"umhhm"...yanajin yanda tayi replying yasan akwai matsala...if u see yanda ya gigice zakasha namaki...fadi yake"my baby please what happened...waya ta6amin ke?.."ta sake narkewa tana tale baki tace"baby Ammi ne"...yace"Subhanallah me Ammi tayi maki?..hope ba dukanki tayi ba?.."tace"cewa tayi sai nayi suyan Pancake...kuma ni baby banason girki fa"...tana iya jiyo sautin dariyarshi kafin yace"eyya sorry my baby gaskia Ammi bata kyautamin ba..why zata turamin mata kitchen?.."tana sake narkewa tace"shi na gani nima baby..aidai in munyi aure bazaka na sani girki ba koh?.."yace"wane ni in saka princess dina girki...duk abunda mukeso ordering zamu dingayi ko mu dauko chefs su dafa mana"...lokaci daya ta wage baki tana smiling tace"yauwa my Professor..my very own baby durling"...saida ya lumshe ido daga can inda yake ya wani dora hannu kan chest dinshi yace"ohhh that sounds sweet baby...i love u"...tace"i love u more baby"...mai aiki dai na aikinta tana sauraron yanda take zuba shagwa6a tana murmushi...ko su da suke aiki gidan sun san Aysha mai son shagwa6a ce duk kuwa da cewa iyayen nata ba shagwa6ata suke ba...haka taciga da wayanta har aka gama suyan Pancakes din snn ta dora wormern da aka zuba kan tray ta fita dashi parlor...dining ta karasa ta ajiye snn ta nufi parlorn daddy...as usual suna zaune dinning suna karyawa shida Ammi...ta karasa ciki bayan ta nutsu snn ta gaisheshi ta bar parlon...tana fita ta samu su Husna a dinning itama ta karasa ta zauna suka fara breakfast...Ammi da daddy suka fito tare bayan sun kammala suma...Ammi na rikeda briefcase dinshi zasuje gaida Lamido shi da yaran daga can kuma zai wuce Abuja wurin aikinshi...su Aysha na zaune parlor suma sun gama nasu breakfast din kowacce sanyeda katoton hijab sbd zaaje gaida Lamido...Daddy ya kalli yanda sukayi reras a parlon kowa tasha hijab kawai ya girgiza kai yasa daria...ya lura har wani nutsuwa na musamman sukeyi duk zasuje wajen Lamido snn kaf jikokinshi ba wadda take zuwa mishi ba tareda hijab ba dan fada yake sosai...bayan ya gama dariyan ya kallesu one by one yace"are we good to go?.."suka hada baki wajen fadin"yes daddy"..snn yace"to ku tashi muje"...gaba daya suka mike suka fita...shima suka fita tareda Ammi...har jikin mota ta rakashi ta bude mishi kofa da kanta ya shiga snn ta ajiye briefcase dinshi..suma su Aysha nasu motan suka shiga tana kallon Ammi tana sallama da mijinta cikin ranta tace" muma dai muzo muyi auren nan wlh..haka zanje inta yima babyna yana lalla6ani"...Yusra dake jikinta tace"Adda me kika ce?.."ta saki murmushi tana shafa kan Yusra tace"ba komai habibty...bance komai ba"...motan daddy ne ya fara fita daga gidan snn nasu.

Kofar gidan Lamido motocinsu sukayi parking...daddy ya fara fitowa suna biye dashi zuwa ciki...katoton parlon Lamido dake daukeda two sets of kujeru suka shiga...yana zaune kan one of kujerun sai wasu mutane biyu zaune a kasa suna gaisheshi...karasawa ciki sukayi daddy ya zauna kasa ta right side dinshi su kuma suka zauna his left side...kyakkyawan bafulatani da a kallon farko da kayi masa zaka gane attajiri ne snn kuma yanada dattako...kamanninsu daya da daddy saidai haske da daddy zai nuna masa shima ba sosai ba...bayan ya sallami mutum biyu dake zaune ya juya yana duban daddy yace"Ahmad har an fito?.."cikeda respect daddy yace"na samu fitowa Baffa...barka da safiya"..yace"barka dai ya iyalin?.."kai a kasa yace"suna nan lafia Baffa...tace a mika mata gaisuwa kafin ta shigo"..gyada kanshi yayi yace"to mashaAllah"...sai kuma ya juya ga su Aysha ya dan saki murmushi yace"mutanen Lamido"...da ladabi suma suka dukar da kai suka gaisheshi...ya amsa tareda tambayansu makaranta sukace Alhamdulillah...idonshi ya tsayar kan Aysha kafin yace"ke saura wata nawa ki gama karatun ne Aisha?.."tace"ba watanni bane Lamido saura shekara daya da rabi"..gyada kai yayi yace"to ba laifi Allah ya kaimu..Allah yasa a gama lafia"..sukace" Ameen Ameen"...sun dan jima suna hira har wani qanin daddy ya shigo shima da 'ya'yanshi...suka gaisa dashi snn daddy yayi salama da mahaifin nasa suka fita...kai tsaye ya shiga motanshi suma suka shiga nasu bayan ya sallamesu suka koma gida shi kuma suka fita daga Estate din.

Kwanci tashi abun ba wuya har sun cinye sati biyunsu cif sun fara shirin komawa makaranta...tunda satin komawa ya shigo Aysha take kunci tana baqin ciki sam batason komawa wlh especially idan ta tuna wnn dan rainin hankalin inyamurim Proprietorn nasu...sam bata kaunarshi wlh...neman hanyan da zata sanar da Ammi kawa take amma ta rasa dan haka ta tsiri 6ace 6acen rai sai ta zauna a parlor da gayya tayi tagumi wai tanaso Ammo ta tambayeta abunda ke damunta ta fada mata amma Ammi tayi biris da ita kaman batasan tanayi ba...abu daya dake dan yaye mata wnn damuwan shine Prof dinta...zuwa yanxu soyayya sukeyi sosai sai kace wanda sukayi shekara da shekaru a tare...yana mugun shagwa6ata kaman yanda takeso ita kuma tana sake falling mishi.

Kaman kullum yau ma tana zaune ta buga uban tagumi a parlor wai ko Allah zaisa Ammi ta tambeyi meke damunta saidai abunda bata sani ba shine Ammi ta rigada ta ganota tasan duk wnn attitude da take displaying kilan sbd komawa makaranta ne shi yasa taki kulata...Ammi ta shigo parlon waya kare a kunneta tana mgn da Aunty Fiddausi...bayan ta gama ta dauki remote tana kokarin kunna tv Aysha da taga still bazatayi mata mgn ba ta dan marairaice tana dubanta tace"Ammi.."ba tareda ta bata attension dinta ba tace"na'am"...sake narkewa tayi tace"Ammi bazaki tambayi meke damuna ba?.."dan juyawa Ammi tayi tana kallonta kafin yace"what's wrong..are u sick?.."sake marairaicewa tayi ta koma kalar tausayi tace"Ammi dan girman Allah ki cema daddy bazan koma makaranta ba plsss"...fuska daure Ammi tace"sbd me?.."tace"bana sonta wlh kuma yanxu ba wani karatu akeyi ba sai shegen takurawa mutane"...gyada kai Ammi ta shiga yi tace"dama nasan karshen zancen knn...kilan kinje kinyi laifi anyi miki fada shine zakizo kice mana bazaki komaba kuma kike tunanin zamu yadda dake kaman bamusan halinki ba koh?..to bari kiji in fada maki babu fashi komawa makarantanki gobe idan kuma kika sake kika sake min mgnr nan sai kinci ubanki wlh...daidai nake dake ai kinsani"...nan da nan ta fara hawaye tana cewa"nifa Ammi Allah na gaji da Kano inaso in dawo gida...kuma Proprietor dinmj inyamuri bashida mutunci wlh"...Ammi mikewa tayi zata bar parlon tace"ur problem not mine..nidai na gama mgn kuma Allah yasa kar ki dena kukan nan kiga yanda zanyi dake a gidan nan...shashasha kawai"...daga haka Ammi ta wuce dakinta...ita kuma hajia indo ta rungumi pillow tana sake rushewa da kuka.












Rano✨






Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
15
Yau Sunday tun around ten Hamma ya tafi maidasu bisa umarnin daddy ya maidasu da wuri shima ya samu ya dawo gida da wuri kafin dare...karfe daya a cikin Hostel yayi musu...Hamma bai tafi ba saida ya tabbatar ba abunda suke bukata snn ya musu sallama ya wuce su kuma suka shiga area classes don duba Posting dinsu...gida biyu akayi dividing class dinsu first 19 aka turasu Freedom sauran 19 din kuma aka turasu Kinana...gaba daya ran Aysha taji ya 6aci itadai Allah ya sani ba son Freedom din nan takeyi ba...tasan ko baa fada ba Dr.Bobby mugun takurawa mutane zaiyi sbd yana ganin Hospital dinshi ne...ita kuma harga Allah yanxu batason abunda zai sake shiga tsakaninta dashi yazo yana mata rashin mutunci tunda ta fuskanci dabi'arshi ne...kallon Billy tayi tace"Billy zo muje muyi mgn da provost ko zaisa baki a canxa mana posting din nan...na tsani zuwa Freedom wlh"...Billy tace"but why?..asibitin yanada kyau fa Lamido..besides ko kinje wajen provost ma i don't think zasu canxa maki cox ba'a ta6ayima mutum posting kuma daga baya a sake mishi ba..kawai ki hakura dashi nasan muna fara zuwa zakiji kina enjoying"...girgiza kai ta shigayi bayan Billy ta gama mgn tace"nidai dan Allah ko rakani ne kiyi plss...Allah bazan iya zuwa Hospital din nan ba haka nan da kayi small mistake Proprietor yace zaiyi maka rashin mutunchi"...daga kafada Billy tana cewa"Fine tunda bakiji shawara na ba...nima kuma babu inda zan rakaki sai kije ki dawo ina jiranki a nan"...hararanta tayi ganin itama zata mata wulakanci kawai ta juya ta tafi ita kadai...kafin ta shiga office din secretary dinshi tace baya nan amma yace idan anzo nemanshi ta kira ta sanar dashi dan haka tayi dialing number dinshi yana dagawa tace"Sir Lamido tazo nemanka"...daga other side din yace"kice ta sameni office din Dr.Bobby"..tana kashe wayan tace mata"yace kije office din Dr.Bobby yana can"...Aysha ta wani zaro ido jin ta ambaci Dr.Bobby tace"tsaya..waye Dr.Bobby?.."dan murmushi Secretary din tayi kafin tace"Proprietor mana"...wani irin diff tayi kaman wuta ya dauke mata...tabbas da tasan inda yake knn da bata bari an kirashi bama in the first place bare har yace taje can ta sameshi...itafa ta tsani abunda zai hadata da inyamurin nan ko kadan..sam batason hada sabga dashi sbd ta lura ba karamin mara mutunchi bane...gashi kuma Secretary ta ambaci sunanta da wlh bazata jeba sai tayi wucewarta ta dawo daga baya amma yanxun tunda yaji sunanta tasan zuwa ya zama mata dole ko don posting da takeso a sake mata tunda gobe zasuyi reporting...ganin tana 6ata lokaci a banza ta juya ta fita daga wurin tayi hanyar office dinshi tana sake sake cikin ranta sai kuma taji haushin kanta for tsoron wnn inyamurin...kawai ma gara taje inyaso ta dake ta fadi abunda ya kawota tasan duk tsiya dai bai isa yasa hannu a jikinta ba...da wnn sabon courage ta isa zuwa office din...bayan an bata permission din shigowa ta tura kofar a hankali ta shiga kai a kasa...yana zaune kan kujera yayinda Dr.Bobby shima ke zaune kan office chair dinshi...ta karasa ciki ta tsaya snn tacema Nur"good afternoon sir"...yace"Afternoon Lamido ya holidays" ...ta dan kakalo murmushi tace"Alhamdulillah"..yace"to bismillah zauna inji meke tafe dake?.."tace"thank u ba saina zauna ba Sir...akan mgnr posting ne dama"...yace"Posting?..meya faru?.."saida ta hadiyi saliva trying very hard not to look at Bobby da zata iya rantsewa taji wann shegun eyes din nashi a kanta tace"Sir...banason inda akayi posting dina shine nace in maka mgn ko zakasa a canxa min?.."Nur dake kallonta yace"No problem ina akayi posting dinki?.."ta sake hadiye wani yawun snn tayi qundunbala tace"Freedom"...da mamaki sosai Nur yake kallonta yace"amma why bakison Freedom din?..naga students da yawa har so sukeyi ayi posting dinsu can"...kai tsaye tace"Sir kawai nidai banaso"...saida ya danyi shiru na wani lokaci kafin yace"shknn kije zanyi mgn da Isaac sai muga yanda za'ayi"..nan da nan ta saki smile tana fadin"thank u so much Sir..nagode"..wani mamakin ya sake kamashi ganin how happy she is kawai sbd xaa canxa mata posting...lallai bata son Freedom din kuwa kaman yanda ta fada...Dr.Bobby yayi shiru yana kallonsu saida suka gama yace"ba wanda za'a canxama posting"...a tare Nur da ita suka juya suna kallonshi...ganin kallon da suke mishi ya sake tamke fuska yana cewa"don me za'a canxa mata posting bayan ba haka akeyi ba...who did she think she is?.."Nur yace"amma..."bai bari ya karasa ba ya katseshi da fadin"if she can't stay..she leaves"...mamaki sosai ya kama Nur kawai yayi sakato yana kallonshi...ita kuwa Aysha right now ji take kaman ta kwada masa mari...dan rainin hankali har ita zai wani ce she leaves?..wlh da daddynta zai amince da daga office din nan ko Hostel bazata koma ba zatayi gida saidai Bilkisu ta taho mata da kayanta amma she won't sbd tafi kowa sanin halin mahaifinta...rai a matukar 6ace ta juya zata fita yace"dawo.."tsayawa tayi cak da tafiyar ita bata juyo ba kuma bata cigaba da tafiya ba...shi kuma ganin ta wani yi tsaye ta juya musu baya saiya tuna ranar da sukaje Hostel dinsu ma haka tayi musu...a kausashe yace"i said come back here...are you deaf?.."juyawa tayi ta koma gaban table din fuska a tamke...Dr.Nur dai relaxing yayi yana kallon wnn rigima nasu...ya shiga binta da wnn kallon da bata kauna snn ya nuna hannunta da fingers dinshi yace"remove those things"...a rikice ta dago tana kallonshi sai kuma ta dauke kan da sauri jin wnn abun da batasonji duk ya kalleta..hannun nata ta kalla zobuna ne na gold guda biyu ajiki kwata kwata mantawa tayi bata ciresu kafin ga bar gida ba...ta dan rage murya tace"Sir..."kasa karasawa tayi sbd wnn idanun dai daya zuba mata...bata sake yunkurin mgn ba takai hannu ta zarosu daga fingers dinta snn ta ajiye kan table din ta juya a fusace ta fita daga office din..shi kuma ya daukosu daga inda ta ajiye ya bude wani drawer dake kusa dashi ya watsasu ciki ya rufe...duk abunda yake idanun Nur na kafe a kanshi yana kallon latest behavior dinshi...mamakin ta yanda har ya lura da akwai zobe hannunta yake dan koshi da suke mgn da ita bai lura akwaisu a hannunta ba saida ya fada...wani murmushi ya saki yana shafa beard dinshi yace"Dr.Bobby tell me plss..do u love this girl?.."wani kallo Bobby ya bishi dashi kafin yace"what the hell...are you insane?.."Nur ya daga shoulders dinshi yace"no am not..kawai dai inaso in san ta yanda akayi ka lura da akwai rings a hannunta bayan koni da nake mgn da ita ban lurada hakan ba"...tsabar haushi kasa mgn yayi sai ido kawai daya zuba mishi yana mishi kallon da shi kanshi yasan zaiji ajikinshi...ilai kuwa Nur din ya dan yatsine fuska yace"C'mon stopping looking at me that way plss?..sbd kasan tasirin idanunka shiyasa kakeso kayita tsatstsare mutane dasu don kasa sunajin somehow..nidai stop looking at me plss tunda mgnr ne bakaso an barshi"...murmushin cin nasara ya saki tareda komawa yayi relaxing kan kujeranshi...Nur yace"dole kayi smiling mana tunda ka cuceni"...baice mishi komai ba sai shoulder dinshi daya daga.

Washegari Monday kowa zaije yayi reporting a Hospital da aka kaishi...kaman kullum karfe 8 school bus dinsu ya kwashesu zuwa Freedom Specialist Hospital...daidai lokacinda suka isa Hospital din shima Dr.Bobby yazo..bayan bus dinsu yayi parking duk suka fito shi kuma bai fitoba sbd waya da aka kirashi...daga nan inda yake ya hangota suna mgn da Billy baidai san me suke cewa ba yaga sun nufi wurin wata mota...suna fitowa Aysha da tun shigowarsu taga motar babynta a parking space tace ma Billy"wlh Billy shine ba gizo yakemin ba..dama yace yau ko office bazai iya zuwa idan baizo ya ganni ba"...Billy da zuwa yanxun ta dan fara sakewa dashi tace"ikon Allah..kinga har ya rigamu zuwa"..Aysha daketa blushing tace"ai Allah kadai yasan tun yaushe yake a nan...zo muje kar ya gaji da jira"..ba musu Billy ta bita zuwa inda yake...tun kafin su karaso ya bude mota ya fito idanunshi kan Aysha yanajin kaman ya rungumeta ga jikinshi tsabar kewarta da yayi...suna karasowa Billy ta gaisheshi ya amsa da tambayan ya baby girl dinshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login