Showing 210001 words to 213000 words out of 231169 words

Chapter 71 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9645

rasa nasaba da zullumi da kuma uban kukan da taci bane..ko baccin ma kasayi tayi don basu taba kwana separate room ba tunda sukayi aure sai yau..kuma ita tsoro takeji don ko a gida bata saba kwana ita kadai ba suna tareda Husna a school kuma tareda Billy so zata iya rantsewa ma ita bata taba kwana ita kadai a daki ba ko gidan aunty Fiddausi taje tareda Mufida suke kwana..tun kukan nata na fita tareda sound har ya koma zallar hawaye takeyi babu saurin komai sbd disashewa da muryanta yayi...har dare yayi nisa sosai bata samu bacci ba sbd zazzabin dake jikinta sai gabannin asuba ta samu baccin yayi gaba da ita shima kuma cikeda mafarkai marasu dadi.

Shima Bobby sbd rashin samun enough bacci har ya makara sallahn asubah dan lokacin da ya tashi an idar da sallah a masallaci..alwala ya shiga yayi snn ya gabatar da sallah yacigaba da zama nan yayi su azkhar da addu'o'i har saida gari yayi haske snn ya mike daga wurin ya fita direct to her bedroom dan tashinta tayi sallah..a nan kan sofa ya sameta kwance ta kudundune da hijab dinta..ya karasa a hankali ya zauna kusa da ita yana kallon yanda face dinta yayi jaa sbd kukan da kwana tanayi..lumshe ido yayi ya bude tareda kai hannu da nufin ya zare hijabin dake jikin nata sai yaji jikin ya dauki wani irin zafi kaman ana hura mata wuta..da sauri ya daga hijab din nata yana sake dora hannu jikinta yaji still temperature yayi rising baisan lokacinda ya dagata gaba daya ya cire mata hijabin ba..a firgice ta tashi taga baccin tana hada ido dashi ta mike zaune da sauri tana kwabe fuska tace"par..tner"..daure fuska yayi yana kallonta yace"what's wrong with u?.."kuka ta farayi tana cewa"partner dan Allah let me explain"..bai bari ta karasa ba ya dora finger dinshi akan bakin nata still fuskanshi daure yace"i said me yake damunki?.."kasa tayi da idanunta hawaye na sake cikowa cikinsu tace"fever.."yace"only fever?.."kai girgiza tana share hawayen tace"da ciwon kai"..dauke idonshi yayi daga kallonta dan yanda yaji kukan nata na neman karya mishi da zucia yace"kinyi sallah?.."Kai ta girgiza mashi alamar no yace"then shiga bathroom kiyo alwala"..kallonshi ta tsaya yi zatayi mgn ya dan daga murya yace"just go don't waste my time"..mikewa tayi da sauri ta shige bathroom tana shiga ta durkushe nan kasa ta fashe da matsanancin kuka..gaba daya gani tayi ya dawo mata asalin Dr Bobby data sani..gabanta har wani faduwa yakeyi duk ta kalleshi taga fuskan nan nashi a cunkushe..da kyar ta iya mikewa tayi easing kanta tayi brush snn ta daura alwalan ta fito tana takawa a hankali sbd zazza6i dake sake rufe mata jikinta..tana karasowa ya nuna mata inda ya shimfida mata praying carpet ya mika mata hijab dinta without looking at her yace"kiyi sallah"..ba musu ta amsa hijab din ta saka snn ta tsaya kan carpet ta tayar da sallah shi kuma ya mike zuwa kitchen don nema mata abunda zataci kafin ya bata drugs..hankalinshi ya tashi sosai da jin yanda temperature dinta yayi high hakan Sam bazai hanashi nuna mata girman laifinda ta aikata ba..takeaway din daya ajiye mata jiya a dinning yaga yana nan untouched meaning bataci abinci ba ta kwanta knn..duk sai ya sake jin jikinshi yayi sanyi kawai ya shiga kitchen yana tunanin abunda ya kamata yayi mata yanxu taci kafin ya bar gidan.. custard dinta ya gani inda ta ajiyeshi jiya dan haka ya dora ruwa a gas da sauri ya dama mata custard din ya zuba Madara da sugar snn ya koma dakin nata..a kwance ya sameta inda ta idar da sallah ta sake lullu6e kanta da hijab ya karasa ya ajiye custard din akan table snn ya mikar da ita tsaye bayan ya cire mata hijabin ya nuna mata custard din da hannunshi fuskan nan ba sarari yace"dauka Kisha"..kallon custard din tayi kafin ta dawo da kallon gareshi kmr zatasa wani kukan tace"na..koshi"..saida gabanta ya fadi da ganin yanda ya sake hade rai yana kallonta..murya a cunkushe yace mata"ina wasa dake ne?.."da sauri ta hau girgiza kai tana goge hawayen dake zubowa face dinta tace"ah..ah"..yace"then ki dauki custard din nan kisha idan baso kike kiga other side of me ba"..wani yawu ta hadiye mai daci snn takai hannu ta dauka custard din ta fara sha a hankali tana yatsine fuska kmr mai Shan magani..baifi spoon biyar tasha ba zata ajiye cup din yace"don't u dare..shanye shi zakiyi gaba daya"..haka tacigaba da danna custard din cikinta tana hawaye tana komai har Allah ya nufa ta gama shanyewa..dauka cup din yayi ya fita daga dakin can sai gashi ya dawo da drugs da goran ruwa a hannunshi..daga nan inda take ya tsaya ya 6alli drugs din ya mika mata tareda ruwan dake hannunshi yace"amsa Kisha"..nan ma ba musu ta amsa drugs din daga hannunshi ta fara zuba ruwan a bakinta snn ta watsa drugs din ta hadiyesu aikam tana hadiyewan taji wani irin amai ya taso mata tayi saurin mikewa tana toshe da bakin zata wuce bathroom saidai kafin ta karasa bathroom din ta durkushe nan kasa ta shiga kwarara aman a nan..Bobby na tsaye rungume da hannu yana kallonta..tausayinta yakeji sosai amma taurin kai da kuma zafin abunda tayi bazai bari ya nuna hakan ba..karasawa yayi shima ya durkusa nan inda take ya dagota jikinshi bayan ya fuskanci ta gama aman ya dauketa cak ya shiga bathroom da ita..ruwan zafi ya hada ya mata wanka da kanshi yanata wani daure dauren fuska shi a dole baiji wani abu ba har ya gama ya daura mata towel ya fito da ita..da kanshi ya shiryata yasa mata simple doguwan riga mara nauyi snn ya kwantar da ita kan gado ya fita daga dakin..tea ya sake hada mata da Milo kadai sai sugar snn ya hada da injection ya dawo dakin nata..wnn karon da kanshi ya bata tea din tasha snn ya shiga withdrawing alluran da zaiyi mata..tana ganin allura duk ta rikice tana kuka tana rokon yayi hakuri shidai baice mata komai ba har ya gama hada alluran sai kawai ya tsaya yana kallonta..duk wnn abun da yake Allah ya sani karfin hali ne kawai amma shi kadai yasan yanda yakeji a cikin ranshi..yasan halinta ne indai ba wuta wuta yayi mata ba bazata shiga hankalinta ba shiyasa zaiyi iya bakin kokarinshi yaga bai bar tausayinta da yakeji yayi tasiri a yanxun ba har saita fahimci kuskuren data aikata..zaunawa yayi kan gadon ya dagota yayi mata alluran tanata faman ihu amma bai saurara ba saida ya gama snn ya rungumeta a jikinshi yana patting bayanta a hankali..wnn zafin na jikinta har tsoro yake bata wlh..ji yake kaman yayi transferring ciwon daga jikinta zuwa nashi da kilan bazai dingajin yanda yakeji yanxu da ciwon yake a jikinta ba..karfin hali kawai yakeyi amma yana cikin damuwa sosai..bai ajiyeta ba saida bacci ya dauketa snnya kwantar da ita ya rufeta da duvet ya fita daga dakin..wanka yayi shima ya shirya snn ya sake komawa dakin nata ganin baccinta yayi nisa sosai yayi deciding ya dan leka hospital kona few hours ne ya dawo tunda yanada aiyuka a can..ko abincin shi baici ba ya karasa shiryawa ya bar gidan tareda driver dinshi..yau ko main house bai shiga ya gaida Mummy ba sbd baison ta tambayi abunda ke damunshi.














Rano✨





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
65
Har wajen 1 yana Hospital yanata duba patients ga kuma hankalinshi gaba daya yana kanta..so yake yaji halinda take ciki kuma yanata Kiran wayanta bata dauka dan haka yayi deciding ya kira Mummy tasa aje a duba mashi ita..bayan ya sallami patient din gabanshi bai sake Kiran wata ba yayi relaxing kan seat dinshi yana dialing number Mummy..tana dauka ko gaisawa bai bari sunyi ba yace"Mummy aje a dubamun Aysher plss..batada lafia and inata kiran wayanta bata picking"..da dan damuwa Mummy tace"subhanallah what's wrong with her?.."murya can kasa yace"fever da headache"..Mummy tace"amma kasan batada lafia shine baka zauna tareda ita ba Bobby?..yanxun idan wani abun ya sameta fa?.."a hankali yace"Mummy nothing will happen to her inshaAllah..ya kama dole ne fitan nima da bazan fito ba..yanxun dai ko Miemie ki tura taje ta ganomun halinda take ciki plss..i still have lots of patients ne da zuwa zanyi da kaina in ganta"..ajiyar zucia Mummy ta sauke kafin tace"don't worry yanxu zataje ta ganota..i will get back to u"..yace"alright Mummy.. nagode"..Mummy bata sake cewa komai ba tayi hanging Kiran..fitowa tayi da kanta tacema Miemie dake karatu sbd sun kusa fara waec taje ta duba mata Aysha wai bata da lafia..da sauri ta warware veil dinta data daura a kai ta yafashi snn ta fita daga gidan..ta main gate ta fita sbd taga kofan cikin kaman a kulle ne..tana zuwa ta kwankwasa mai gadi ya bude mata ta shiga cikin gidan kai tsaye..a bedroom dinta ta sameta tashinta daga bacci knn sai kuka take har lokacin kuma akwai fever sosai jikinta..hankali tashe ta kira Mummy ta fada mata halinda ta sameta a ciki don haka Mummy ta turo driver dinta tace ya daukesu kawai su wuce asibiti tunda Bobby yana can sai ya dubata..Miemie ta dauki hijab dinta tasa mata snn ta kamata suka fita compound inda driver je jiransu..suna shiga motar ya tadata suka fita daga gidan.

Suna shigowa hospital din Miemie ta fita da sauri zuwa office dinshi ta banka ta shiga ko sallama batayi ba ta fada mashi halinda ake ciki..yanda ya fito a rude har mutane saida sukayi mamaki dan lokaci daya yaji komai nashi yayi tsaye cak..da sauri ya karasa inda motar yake ya bude back seat nan ya ganta jingine jikin seat din idonta na fitar da hawaye..hannu yakai ya ta6a forehead dinta yaji still da zafi a jikin kawai sai ya dauketa a hannunshi ya fito da ita daga motar zuwa cikin asibitin..sauri kawai yakeyi ya karasa office dinshi bai ko damu da kallon da jama'a ke binshi dashi ba..yana shiga ya kwantar da ita kan gado snn ya cire mata hijabin jikinta kawai sai ya tsaya yana kallonta without saying anything..Miemie data shigo office din da sauri yace ta shiga bayi ta kawo mashi warm water da towel..ba musu tayi yanda yace ta kawo mashi yace taje driver ya maidata gida..shi kuma ya fara jika towel din yana shafa mata ruwan a jiki sbd temperature nata ya sauka..bayan ya gama ya fita zuwa pharmacy da kanshi ya kar6o drip da allurai snn ya koma office din nashi..tana ganin drip da allurai hannunshi ta fara kuka shidai bai iya ce mata komai ba ya samu ya lalla6a yasa mata drip din don yasan ba wani abinci zata iyaci ba..yana gamawa ya mata alluran da zaiyi saurin saukar mata da fever din snn yaja seat dinshi ya zauna nan kusada ita yana kallonta..Aysha na kuka sosai tace"partner am so sorry plss"..hannunta ya kama ya rike cikin nashi baidai ce mata komai ba..mikewa ta shiga kokarin yi shi kuma yayi saurin maidata yana nuna mata cannular dake hannunta yace"careful mana"..komawa tayi ta kwanta tanacigaba da kallonshi tana hawaye..shima kallonta yakeyi yanajin wnn abun da yazo ya tsaya mashi a throat dinshi tun jiya yasan indai ba mgn ya samu yayi da itaba wnn abun bazai fada ba dan haka ya dan runste eyes dinshi kafin a budesu a kanta voice dinshi kasa kasa yace"so da gangan kikayi hakan koh?.."da sauri ta hau girgiza kai tace"wlh coincidence ne..i never knew such thing will happen am sorry"..yace"but u even hugged him..why did u do that?.."tace"i thought it was u sbd eyes dina a kulle suke saida naji perfume dinshi ba irin naka ba nasan u are not the one..kayi hakuri ka yafemun dan Allah"..ta karasa mgnr tana kuka sosai..shiru kawai yayi yana kallonta yasan shima yayi over reacting jiyan nn amma it wasn't his fault..sake matsawa yayi yuana rikeda hands dinta yace"nima am sorry for reacting the way i did..i shouldn't have done that so kiyi hakuri"..kai kawai take gyada mishi..ganin yanda har jikinta na rawa sbd kukan da takeyi yace she should stop talking zasuyi mgn anjima..sosai ya sake bata hakuri yana cewa yasan bai kyauta ba..itama tace mishi ko dan gaba if wani abu irin wnn ya faru saurin fushi bayada amfani gwara su zauna suyi communicating that communication is a solution to any problem..shiru kawai Bobby yayi yana kallonta dan kunya yaji sosai wai itace take fada mashi what is right..sauka ajiyar zucia yayi yana ayyana idan fa bai dena wnn saurin fushi da zafin ran ba watarana zaiyi dana sani duk sai yaji jikinshi yayi sanyi yace inshaAllah zaiyi kokarin gyarawa kuwa..ita kuma tayi shirun bata sake mgn ba har drip din ya kare zuwa lokacin kuma fevern dake jikinta ya dan sauka shima sai a lokacin ya dan samu peace of mind..a hankali ya mike zuwa inda wayanshi keta ringing ya dauka snn ya samu wuri ya zauna bayan yayi picking call din..a daya bangaren Nur yace"hey are u at the office?.."kmr bazaice wani abu ba sai can yace"what?.."Nur yace"just answer me dan rainin wayo"..lumshe ido yayi yana kallon inda take kwance kafin a hankali yace"ina nan".. Nur yace"ohk gani nan zuwa"..daga haka ya ajiye wayar tareda mikewa zuwa inda take ya maida mata hijab dinta yana cewa"do u need anything?.."a hankali ta girgiza mashi kai alamar no..yace"bazaki ci komai ba?.."nan ma kan ta sake girgiza mashi yace"bari Nur yazo idan ya tafi sai in maidaki gida tunda zazza6in ya sauka"..kai kawai ta iya gyada mashi shi kuma ya fita daga office din..can parking space yaje ya tsaya tana jiran isowar Nur bai dade da tsaiwa ba kuma sai ga Nur din ya karaso..bai bari ya karaso nan inda yake ba ya nufi wurin motar shi..yana zuwa ya bude ya shiga tareda relaxing yana kallon Nur din a hankali yace"daga ina kake haka?.."maimakon ya bashi amsa sai cewa yayi"wai what's wrong with ne?..u look disturbed..ina Lamido?.."a hankali Bobby yace"she's inside"..Nur ya dan wara idanu yace"inside kuma?..yanxu wurin aikin ma saika taho da ita Bobby sbd gajen hakuri"..harara ya watsa mashi mai kyau tareda sakin wani tsaki yace"u are annoying wlh..to batada lafia kuma ni bana gidan shine aka kawota na dubata"..wani murmushi Nur ya saki yana shafa gemu yace"so meke damunta?.."Bobby yace"fever..amma nasa mata drip yanxu fevern ma ya sauka"..Nur na gyada kai yace"Allah bata lafia..amma why ba'a yi mata test ba?.."juyawa yayi ya kalleshi rai a dan 6ace ganin kmr neman zance kawai yakeyi yace"ban saniba".. Nur ya kwashe da daria yana kallon abokin nashi yace"kaga malam ka maida wukar ka ni bani na kar zomon ba..am only trying to be of help"..a dan fusace Bobby yace"to hell with u and ur help"..kallonshi kawai Nur yake har yanxu bai bar murmushi ba yace"ohk let me keep quiet tunda bakaso..dama cewa zanyi kasa ayi mata pt kilan she's pregnant"..da sauri Bobby ya juya yana kallonshi idanu a waje yace"what do u mean?.."Nur yace"Ina nufin kilan ciki ne da ita mana..kai ina ka taba ganin anyi haka kawai matarka ba lafia kazo ka wani farayi mata blind treatment baka tunanin ko karuwa ka samu"..wani irin diff Bobby yayi yana bin Nur da kallo kmr bai gane abunda yace ba..tunani ya tafi yi tabbas tunda akayi bikinsu bata ta6a period ba and idan ba wai manta lissafin yayi ba bikinsu saura 2 weeks tayi period and idan akayi adding two weeks to that shine ovulation period dinta kuma a daidai wnn time din akayi bikinsu so there is 90% possibility na zata iya samun cikin within wnn kwanakin sbd time din ovulation dinta ne..nan take fuskanshi ya washe da wani irin murmushi yana sake wara idanu akan Nur hannunshi dafe da bakinshi cikin tsananin farin ciki da kuma mamaki yace"oh my Goddess..why didn't i think of this?.."harara Nur ya watsa mashi yace"oho banza"..sake juyawa yayi yana kallon Nur da kyau yace"Nur ina kyauta zaton wnn mgnr naka gaskia ne..she might be pregnant oh Allah"..ya karasa mgnr full of excitement kaman an tabbatar mishi tana dauke da cikin already..shi gaba daya tunaninshi baizo nan wurin ba all he was thinking was incident daya faru jiya har ya kulle mashi kai ya kasa zargin cewa cikin ne da ita.."ikon Allah"..ya sake fada out of excitement Nur dai na zaune yana kallon ikon Allah at the same time yana mishi daria..shi kanshi zai so ace yau Lamido tanada ciki ko dan yayi kallon uban rawan kan da Bobby zaiyi akan cikin...bude motar yayi ya fita shima Bobby ya fito da sauri ya kama hanyan cikin asibitin yana fadin"we need to conduct this test now..i pray it turn out to be truth"..Nur dake bin bayanshi ya amsa da"Ameen"..har suka shiga cikin building din..direct office dinshi suka shiga lokacin tana kokarin mikewa tsaye Bobby yayi saurin karasawa inda take yana kallonta full of love and excitement yace"baby where are u going?.."a hankali tace"ruwa zansha"..ruwan ya dauko da sauri ya kawo mata yana cewa"here u go"..ta saki dan murmushi snn ta amsa ruwan tasha cikeda mamakin sudden change din nan nashi?.. it's like ya gama saukowa completely..saida ta gama Shan ruwan snn ta lura da Nur dake zaune kan sofa yana kallonsu..ta danyi kasa da kanta tace"sir Ina yini"..yace"lafia ya jikinki?.."tace"naji sauki"..yace"to Alhamdulillah".. Bobby dai drawer ya bude ya dauko duk wani abu da zaiyi amfani dashi snn ya koma wurinta ya shiga lallabata wai zai dauki blood sample..itadai batace komai ba ya dauki sample din snn yaba messenger bayan ya rubuta test din da za'ayi a paper yace ya kai lab yace yana jiran result yanxun nan.

Ana kawo result din Bobby yayi saurin karba daga hannun messenger daya kawo har ya fara budewa sai kuma yayi saurin maidata yanda take tareda juyawa yana kallon Aysha da har yanxu ke zaune tana kallonsu..juyawa yayi suka hada ido da Nur sai kuma ya sake juyowa gareta ya sakar mata murmushi.. Lamido data kasa gane what they are up to kawai sai ta sauka daga gadon a hankali tana kallonshi ta nuna bathroom dinshi tace"zanyi alwala"..da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login