Showing 84001 words to 87000 words out of 231169 words
knn sbd yana ganin kwata kwata bai cancanta yana jin wani abu makamancin haka a kanta ba..sam bai dace ba shiyasa shi kanshi yakejin haushin kanshi kuma dui kokarin na yaga yayi stopping abun kasawa yayi...saida suka dauki lokaci mai tsaho a haka kafin ya dago daga jikinta a hankali yana yin kasa da ido sbd kar ya hada idanu da ita..Mummy takai hannu ta dago idanun nashi tana dubanshi sosai tace"fadamin..what is the matter with u?.."hannunta ya kamo ya rike cikin nashi yana kallonta shima ya rasa abunda zai fada..kawai tunani yake me zaice mata yana damunshi dan dai da kunya yace mata kan yarinya karama yake wnn abun...shidai zuciyarshi batayi mashi adalci ba wlh...ganin kallon da ya zuba idanu yana mata ta sake kiran sunanshi...ya lumshe ido ya bude cikin ranshi yana addu'an Allah yasa ta bar zancen amma sam Mummy ta dage sai taji damuwanshi...ganin ba hakura zatayi ba ya tattaro duk wani karfin hali da dakiya irin nasu na maza kafin yace mata"dama..mummy..it's about a girl"...tun bai rufe baki ba Mummy ta wara idanu tana kallonshi tace"u mean kana son wata yarinya?.."girgiza kai ya shigayi da sauri yana wani ta6e baki jin abunda ta fada yace"Mummy Noo..wata yarinya ce kawai mahaifinta ya bani amanarta shine ita kuma take kokarin tasamin ciwon zuciya"...kallonshi Mummy keyi full of suprise don har yanxu bata fahimci inda zancenshi ya dosa ba..shima ganin kallon da take mishi sai ya shiga bata labarin tun haduwar da sukayi da daddy a college zuwa yanda ya gane shi son din Col Attahir ne da irin maganganun daya fada kan mahaifin nashi har zuwa yanda yace ga amanarta ban ya bashi yanaso ya kula da ita sbd batajin mgn...Mummy tayi shiru tana sauraronshi har ya gama kallonshi kawai takeyi dan she smells something cikin maganr nan nashi...tasan wanene shi sarai dan haka tafi kowa fahimtan halinda yake ciki fiyeda kowa a dunia and cikin maganganun daya fada ta tabbata ko ba son yarinyar yakeyi ba tabbas yanada interest akanta har tunda yake kishinta haka?..ita kuwa inama zataga wnn yarinya ta samu tayi mgn da ita?..inama Allah zai kar6i addu'anta ya zarginda takeyi ya zama gaskia?..inama zat...bata kai ga karasawa ba taji hannunshi a jikinta yana dubanta yake fadin"Mummy tunanin me kikeyi ne wai?.."dan murmushi ta saki tareda kama nashi hannun itama still tana smiling tace mishi"yama sunan yarinyar kace?.."hade rai yayi yana kallonta yace"Mummy me zakiyi da sunanta kuma?..yarinyar da ina fada maki tana kokarin halakani shine kikeso kiji sunanta?.."murmushi ta kara saki tace"nidai fadamin sunanta plss..watarana ma so nake ka kawomin ita mu gaisa"...da mamaki sosai ya tsaya yana kallonta jin abunda tace...shi bai gane me take nufi ba sam ya ya kawo mgnr da ya kamata ta tayashi jaje amma sai behaving take kaman wani abun celebration ne ya faru...daddagewa yayi ya kwa6e fuskanshi kaman zaisa kuka yace"Mummy manaa..meye haka kikeyi plss?.."daria sosai ta saki kafin ta dakatar dashi tana sake dubanshi tace"to yanxu tell me meya kamata muyi?.."gyara zama yayi yana dubanta in a serious tone yace"shine abunda ban saniba Mummy..na rasa wace irin yarinyace ita..wlh jiya ko bacci banyi ba sbd haushin data kunsamin shiyasa har yanxu kaina bai dena ciwo ba..na rasa meyasa na kasa mantawa da komai har zuwa yanxu"..sake kamo hannunta yayi ya rikesu gam idonshi na sake canxa launi yace"Mummy ya zanyi in manta plss...inaso in manta"...ajiyar zuciya ta sauke tana kallon yanda duk yanayinshi ya sake sauyawa dan haka ta kwantar da murya tace"karka damu watarana zaka manta inshaAllah..ni wnn damuwan naka ne banaso kaga har yanxun jikinka akwai fever..inaso ka nutu ka kwantar da hankalinka sosai snn kayima kanka treatment kuma ka dena damuwa dan idan baka denaba ko kayi treatment dinma a banza zai tashi..ko kanaso wani ciwon ya kamaka ne?.."girgiza kanshi yayi da sauri yace"definitely not because of that stupid girl"...Mummy tace"then ka dena damuwa..yanxu ga breakfast na kawo maka ka shiga kayo brush zanyi serving dinka"...baiyi musu ba ya mike tsaye da kyar snn ya shiga takawa a hankali zuwa bathroom dinshi...mummy tabishi da kallo tana tausaya mashi..cikin ranta tana addu'an Allah yasa dai ba soyayya ne zai wahalar dashi ba don a yanda taga alamunshi soyayya zaiyi matukar bashi wahala sbd yanda yake da riko da kuma sanya damuwa cikin ranshi.
Bayan sati daya...
Tun daga wnn rana Lamido bata shiga sabgarshi ba..dan gaisuwan ma da take mishi idan sun hadu a hanya ta dena snn idan zai shekara kiran wayanta bazata dauka ba...yau tsahon kwanaki uku knn dayake kiranta bata dauka..tana ganin wayan zaiyita ringing amma ko kallonshi bazatayi da sunan dagawa ba...yanayi mata ciwo duk ta tuna da kalmar daya jefeta dashi ranan..wai tana biye biyen maza bi ma'ana dai tana karuwanci..lokaci daya duk wnn tsoron nashi taji ya ragu dan cikin kashi dari tasan yanxu da kyar za'a samu kashi hamsin a cikinshi...su Billy kuwa saida suka dauki lokaci kai tsah suna bata hakuri snn suna saku ta hakura suka cigaba da gudanar da rayuwarsu...shirye shirye sukeyi ma na zuwa Kd bikin Lubna fa za'yi next week suna dawowa kuma ba dadewa zasu fara exams daga nan sai Clinical posting sai kuma su shiga level 3...tsakaninta da babynta kuwa sai sambarka dan soyayya sai kara karfi yakeyi kullum.
A hankali ya shigo parlon yana tafiya a hankali kaman mara lafia hannunshi rikeda briefcase dinshi sai dayan kuma rikeda suit dinshi...kallo daya zakayi mashi ka gane bashida lafia sbd dan karen raman da yayi kaman wanda yayi wata a kwance...ya kara wani irin haske da idan ba saninshi kayi ha u will think ko bleaching ya fara...Miemie da Sab ne kadai zaune a parlon suna labari kaman basune ke fada kaman suna ganin hanjin juna ba...he is so lost in thought that har ya kama hanyan Flat dinshi bai lira dasu a parlon ba...Sabeer da bai dade da dawowa ba ya dan daga muryanshi da igbo yace"uncle Bobby sannu da zuwa"..dakatawa yayi tareda juyawa a hankali yana kallonshi yace"yaushe ka dawo?.."Sab yace"ban dade da shigowa ba..ya aiki?.."a takaice yace dashi"fine"..snn ya juya yacigaba da tafiyarshi walking slowly..dagashi har Miemie dankallo suka bishi sbd yanda yake tafia da yanda sukaga damuwa karara kan face dinshi shows kodai wani ya 6ata mashi rai ko kuma yana cikin serious rashin lafia idan akayi laakari da raman da yayi...yana shiga Mummy ta fito daga parlonta tana dubansu tace"kaman muryan Bobby naji yanxu"...Sab ne yace"shine..amma Mummy kinganshi kuwa?..bashida lafia ne?.."Mummy bata iya cewa komaiba ta bishi zuwa part din nashi...yana zaune gefen gado yana kokarin cire takalman kafanshi ta shigo dakin...saida ta isa har ciki ta zauna nan kusada shi snn ta dubeshi da kyau kafin tace"yanxu Bobby bakaji duk fadan da nayi maka ba daxun koh?.."rausayar da kai yayi yana kallonta kaman zaisa mata kuka yace"Mummy to yanxu me nayi?.."tace"kaki ka kwantar da hankalinka ka dena sama kanka damuwa mana...yanxu kana tunanin wnn damuwar da kake zaiyi sorting things out ne?.."rai a 6ace yace"Mummy yarinyar ce ta rainamin hankali...har wace ita da zan dinga kira tana ignoring min call?..har rejecting calls dina fa ta farayi sbd taga ban hadata da babanta ba"...murmushi Mummy ta saki tana kallonshi tace"kenan dai idan na fahimceka ignoring calls dinka da take bai maka dadi ba..u want her to be answering ur calls koba haka ba?.."da sauri ya shiga girgiza kanshi yace"Mummy don't misinterpret me plss..that's not what i mean"...tace"then why all this damuwa idan abun bai dameka ba?..why ka kasa cire abun a ranka har yake saka rama haka?.."shiru kawai yayi baice komai ba as basan mezai fada mata ba..sam bashida abun fada..shi kanshi yana mamakin kanshi wai the whole him ne yake damuwa sbd wata can tana ignoring calls dinshi...abun ya dameshi sosai bai abunda bai ta6a tunanin faruwa dashi ba har abada...ganin yanda yayi kicin kicin da fuska Mummy ta kara sakin smile tana cewa"nidai i want u to take it easy on urself plss..i told u kana bata hakuri komai wucewa zaiyi amma baka yadda ba"...tun kafin Mummy ta rufe baki yayi spitting yana fadin"over my dead body"..murmushi har yanxu takeyi tana girgiza kai...wnn hakilon nashi karamin daria yake bata ba wlh..kiri kiri ga abu yana feeling amma dan banzan ego dinshi bazai bari yayi admitting ba...mikewa tayi ta fita daga dakin don kawo mishi abincinshi tunda da dadewa ya yayema kanshi cin abinci tare dasu.
Ranan Tuesday karfe biyu ya bar Hospital zuwa College sbd yanason mgn da Nur...tunda incident din nan ya faru basu sake haduwa ba...yasan tunda yaji shiru Nur ko a waya bai nemeshi ba fushi yakeyi dashi...da kanshi ma yayi driving sbd driver dinshi baida lafia...yana shiga cikin premises din bayan yayi parking ya nufi Office din Nur yanata baza ido wai ko zai ganta a nan waje amma ko mai kamada ita bai ganiba.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
27
Yana shiga ya iske Nur zaune kan office chair dinshi yana aiki da laptop yana ganinshi ya wani hade rai yanacigaba da aikin gabanshi ko kallon inda yake baiyi ba...Bobby ya karasa ciki ya zauna yana kallon yanda yake wani ciccin magani kawai saiya saki murmushi yana girgiza kai yace"Man how far?.."banza Nur yayi dashi yacigaba da aikinshi...Bobby ya sake cewa"Man meye haka ne plss?..stop acting like a kid"..tun bai rufe baki ba Nur ya dago yana kallonshi rai a 6ace yace"oh really?..wato I should stop acting like a kid sai kace kai ka manta wulakancin da kayimin harda korana office dinka ba"...saida ya barshi ya gama snn a nutse yace"I wasn't on my sense..I was furious kai kuma kazo kana so kayi adding to what i was going through shiyasa nayi reacting that way amma am sorry"...wani harara Nur ya dago ya watsa mashi snn yacigaba da aikinshi...Bobby ya dan dafe goshi yanajin kanshi na wani sarawa sbd wnn abunda Nur yake..baisan meya sameshi ba amma shi yanxu sam bayason hayaniya..sam baison matsala idan ba hakaba head dinshi yayita mishi ciwo knn kaman me hypertension...after like 3 mins ya sake dagowa yana dubanshi yace"yanxu bazaka hakura ba dai knn?.."ba tareda ya dago ya kalleshi ba yace"ba haka ake bada hakuri ba ai..kai kanka kasan abunda kayi is uncalled for amma ya zanyi dakai?.."dan murmushi Bobby ya saki yana shafa lallausan gashin kanshi yace"to nace am soryy shikenan?.."sai yanxu Nur ya dago yana dubanshi yace"to yanxu kam na hakura..amma on one condition"...kallonshi Bobby yayi sai kuma ya dauke kai alaman baison wani mgn again..yasan tambayan da zaiyi mishi shi kuma sam bashida amsan bashi...tunanin nashi bai dire ba Nur yace"tsakaninka da Allah meya 6ata maka rai ranan?.."shiru kawai Bobby yayi as bayason fada mishi abunda ya faru...shi kuma Nur dage shoulder dinshi yayi yacigaba da aikin gabanshi yace"idan tayi naji"..qala dai baice mishi ba ya mike hands dinshi a aljihu...Kallonshi Nur yayi yace"so wucewa zakayi?.."yace"yes dama abunda ya kawoni knn?.."Nur ya sake daga shoulder dinshi yace"alright sai Thursday..my regards to Mummy dasu pretty"...Bobby ya amsa da"zasuji"..snn ya fita a office din..Nur ya bishi da kallo yana murmushi yace"dan rainin hankali zama ka gama guje gujenka ka dawo kan hanya ne...waya fada maka Borno gabas take?.."yana gama fadan haka sai ya kwashe da daria hadda su buga table ya sake cewa"su Dr Bobby in love har na matsu naga karshen love story din nan..da yake novice ne shi har dan ramewa naga yayi sbd damuwa..kai amma Lamido ta hadu wlh..kin gama min komai tunda kika fara daidaita wnn dan iskan"..ya karasa yana ske rushewa da daria...shikam ko baa fada mishi ba yasan definitely son Lamido yake sbd abubuwan da yaga yanayi dama wanda ita kanta Lamidon ta fada mashi.
Yana fitowa yaci karo da ita ta fito daa office din Sir Abdool aikam tana ganinshi ta wani hade rai tayi wucewarta abunta ko kallon inda yake batayi ba...saida takai bakin kofa sai kuma ta juyo idonta a kasa tana sake daure fuska murya a ciki ciki tace"ina yini"..kallonta kawai Bobby keyi without blinking...wasu irin ramuka da baisan dasuba a cikin heart dinshi yaji suna ciccikowa just by seeing her...haka nan yaji ganin nata gladen his heart sai a wani 6angaren kuma yaji ciwon zuwa office din Abdool da tayi...idan bai manta ba da bakinta ta ta6a furta mashi Abdool din sonta yake kuma shine zata biyoshi har office dinshi sbd batada hankali...ganin ta gaisheshi bai amsa ba ta juya zata wuce yayi saurin dawowa hayyacinshi snn ya dan daa murya ya kira sunanta"Aysher"...juyowa tayi tana dubanshi da mamaki...this is the very first time da taji sunanta a bakinshi..ko Lamido bata ta6ajin ya kirata dashi ba balle kuma Aysha da dama ba kowa ke kira a college din ba...takawa ya shigayi a hankali zuwa inda take..ya juya tabbatar ba kowa inda suke kafin ya sake juyowa yana kallonta ba yabo ba fallasa ya nuna mata hanyar office dinshi yace"muje"...turo baki tayi tana sake cin kunu tace"sir nifa class nakeso in koma"...bai sake ce mata komai ba kawai ya zuba mata idanunshi da yasan bata isa ta sake mishi gardama idan har ta kallesu...lokaci daya ta wani hade rai ganin yana kokarin yasata yin abunda batayi niyya ba bayan duk wulakancin da yayi mata hadda kiranta karuwa shine yau zai wani zo yace mata muje kaman shi ya haifeta...kallon da taga bazata iya jurewa ba ta wuce zuwa office din nashi yana binta a baya...da kanshi ya bude office din ya shiga snn itama ta shigo ya maida kofan ya rufe..ya karasa kan sofa ya zauna itama ya nuna mata wanda ke opposite dinshi yace"seat"..rungume hannunta tayi tana sake hade ranta tace"am comfortable here"..baice qala ba ya mike daga nan inda yake ya karasa ya tsaya dab da ita har suna jin kamshin perfumes din juna ya rungume hannu idonshi na kanta yace"fushi kikeyi dani?.."da mamaki sosai ta dago tana kallonshi don batayi excepting such mgn daga bakinshi ba..shima kanshi Bobbyn baisan lokacin da mgnr yayi escaping lips dinshi ba..it's like mgnr ya fito direct from his heart bawai a baki kadai ya tsaya ba...ganin yanda suka hada ido kuma sai taji kunya ta sake yin kasa da kanta tana turo baki...shikam bai iya dauke idanunshi kanta ba ya sake cewa"say something mana..are u mad at me?.."sake kautar da kanta tayi tana cigaba da turo bakinta tace"cewa fa kayi ina karuwanchi"...wara idanu yayi cikeda mamaki yana kallonta yace"Nii?..when did i say that?.."wani irin bacin rai taji ya rufeta na ba gaira babu dalili kawai sai tayi kasa da idonta...Bobby da duk yaji hankalinshi na neman tashi cikin wani irin murya dashi kanshi baisan yana dashi ba yace mata"Aysher speak manaaa"...runste idanu Lamido tayi nan take taji hawaye na neman ciko idanunta...a take hankalin nashi kuwa ya karasa tashi cikin wani irin rauni da baisan daga ina yake fitowa ba yaji yana ce mata"dont cry plss..ki fadamin yaushe nace maki kina karuwanchi?.."hannu takai tana goge hawayen nata baki a tunzure tace"ba haka kace ina biye biyen maza ba..kuma ni ba biye biyen mazan da nakeyi ko Sir Abdool da ka ganni dashi shi yake sona bani nake sonshi ba"..baisan lokacinda bakinshi ya furta"shi kuma wnn dayan fa?.."dagowa tayi tana kallonshi dan bata gane wa yake nufi ba..ya wani hade ranshi kafin yace"that boy..wanda kikayi acting as his wife ranan da kukayi drama"...dan murmushi ta saki da wet face dinta jin wanda yake nufi tace"bestie na nefa"...kallonta kawai yake rai a 6ace ya rasa ma abunda zaice mata...ganin ta sake maida fuskanta ta dinkeshi tsaf kmr ba ita ta gama murmushi yanxu ba yace"is that why u are not picking my calls?.."tana turo bakinda ya zame mata sabo ta daga alaman eh..yace"then i am sorry...da nace kina biye biyen maza i never meant that kawai raina ne a 6ace..are we good now?.."shi kanshi yana mamakin kanshi yanda ya kwantar da murya yana mgn da ita...kai ta sake daga mishi alaman eh snn kuma tace"amma sir dan Allah ka denamin masif.."bata karasaba sai tayi saurin rufe bakinta tana kallonshi tace"sorry ina nufin fada..kuma ka dena kallona da idanunka yana bani tsoro"..murmushi kawai ya saki abunda ya mance yaushe rabonshi da yayi kawai ya koma kan sofa ya zauna yana cigaba da binta da ido..har wani ajiyan zuciya ya saki a 6oye sbd wani irin relieve da yaji just by patching things up with her..zuwa yanxu duk taurin kanshi yasan tabbas bazai iya daukan tana fushi dashi ba sbd ya fuskanci zuciyarshi bata san wnn karatun ba...ganin ya koma seat dinshi ya zauna itama ta dan kalleshi gamida kauda kai tace"sir zan tafi"...kallonta still yake yanajin kaman kar ya barta ta tafi...sam bai gaji da ganinta ba amma ko kusa yaki yin addmitting hakan..sbd ya karyata zuciyarshi da take ta mishi ihun cewa Lamido wani 6angare ce mai girma na cikinta kawai sai ya nuna mata kofa tareda fadin"u can leave"...yana rufe baki ta juya ta fita tana mamakin wai yau proprietor ne yayi mgn da ita haka ba wnn masifan nashi har yana bata hakuri..lallai kuwa za'ayi ruwa da qanqara...shi kuma Bobby sai yaji kaman an sauke mashi wani abu mai nauyi cikin zuciyarshi just by patching things up with her...baisan meyasa ba amma sai yajishi garau duk wnn damuwowi daya sanyama kanshi na kusan sati guda babu su...ranan har 'yan gidansu sun fahimci yana cikin nishadi don yanda yake murna da farin ciki says it all...Mummy dai sai binshi da kallo take cikin ranta tana"Allah dai ya tabbatar min da alkhairi"...nikuwa nace mata"Ameen Ameen Mummy".
Tun daga ranan sai suka koma mutunchi sosai da Proprietor dan yana daukan lokaci mai tsaho baiyi mata bala'i ba amma yanajin zancen saurayi ko something like that bai iya daurewa sai ya dan zazzaga mata yakejin dadi...yanxun ya koya mata duk ta shigo college da safe taje ta gaisheshi idan yana cikin makarantan..haka kuwa take zuwa ba don ranta naso ba..wani lokaci idan yana nemanta ko ta kashe waya ko bata shigo cikin makaranta dashi ba saidai kawai ta ganshi a class dinsu yazo ya wani hade rai yace yana nemanta..haka zatayita ture turen bakinta tabishi tana