Showing 21001 words to 24000 words out of 231169 words

Chapter 8 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9656

fadin haka ta ajiye wayan tayi gaba abunta...Yusra ta dauka tana murmushi suka fara mgn...duk abunda suke Hamm na zaune yana kallonsu...lokaci daya Aysha ta mance da wani 6acin ran proprietor sukaita hira da qanwarta...basu suka gama ba saida ya kar6e wayan da kanshi...sai a lokacin ta samu ta shiga toilet tayo wanka snn tazo ta shirya ta sake hayewa kan gadon ta kwanta sbd Billy bata dakin...tana kwanciya sai abubuwa da suka faru suka shiga dawo mata...ta tuna yanda ya daure fuska ya kuma tsareta da wnn shegun idanun nashi mai kama dana aljanu ta bakin na Billy...batasan wane irin magic ke gare idanun nashi ba da yana dora mata su taji kaman an tattaro duk wani rashin nustuwa da tashin hankali na duniyar nan an dora mata su akai...anya kuwa mutumin nan ba wani abu yakema idanunshi ba?..tana cikin tunanin Billy ta shigo dakin ta mika mata wayanta dake hannunta tace"kar6i ki ce masa ya dena kirana dan Allah..haba! tun daxun yaketa faman kira ko yanaso ya shanyemun caji ne?.."ba musu Aysha ta mike zaune tareda amsan wayan daga hannunta taga Lamido's bestie ke kira...dariya ta saki sosai dan har gobe bata dena dariyan wnn sunan da tayi saving number besty dashi..wai Lamido's bestie sai kace wani yace bestienta ne ita...har kiran ya katse wani ya sake shigowa bata dauka ba...Billy data kulu tace"malama idan bazaki dauka ba bani wayata dan Allah"..bata bata wayan ba tayi kokari ta tsayar da dariyan snn tayi picking tareda karawa a kunne...yanajin an dauka yace"Haba my Billy"..Aysha ta wani zaro ido jin abunda ya fada hadda toshe baki tace"besty ba ruwana wlh"..dan dariya shima yayi kafin yace"inata kiran wayanki bakya dauka itama kuma wnn 'yar rainin hankalin sai wani jamin class takeyi taki daukan wayan sai kace saurayinta"..yana rufe baki Billy da taji kaf abinda ya fada ta daga murya tace"Allah ya kiyaye na rasa dawa zanyi soyayya sai kai...kuma a kashe a bani wayana sai ka kira wayarta ku cigaba da shirmenku"..dariya yasa sosai Lamido na tayashi...saida sukayi me isarsu snn yace"besty wai an fasa zuwa saloon din ne?..kin ganni fa tun dazu a bakin gate dinku ina jiranku"..tana dan girgiza kai tace"anya zuwa saloon din nan zai yiwu kuwa besty?..i don't feel like going out"..tana rufe baki yace"kuma shine baki kira kin fadamin ba saida na baro gida nazo?..fadamin me yake damunki da zakice you don't feel like going out?..na sanki da son yawo fa besty"...tayi shiru tanajin yanda 6acin ran dazu ke son dawo mata sabo fil...shi kuma jin tayi shiru sai yace"alright ki fito waje sai muyi mgn..ina bakin gate"..bata ce komai ba ta kashe wayan snn ta mike ta zura hijab tace ma Billy"taso muje"..tayi mata wani kallo tace"je ina?.."tace"wajen besty mana bakiji yace yana bakin gate ba?.."tsaki ta saki tana kokarin hawa kan gadonta tace"sai kin daw.."bata gama mgnr ba ta shiga janta suka fita daga dakin tunda already da akwai hijab a jikinta...har suka fito waje bata dena jan hannunta ba itama kuma bata dena kokarin kwatan hannun nata ba har suka karasa inda yake...ya bude mota ya fito yana kallonsu one by one kafin ya danyi murmushi yace"to a bani labari menene ya faru?.."Bilkisu ta daure fuska tana kawar da kai Lamido kuma tace su fara samun wuri su zauna first... duk basuyi gardama ba suka karasa wani dan wuri da aka zagayeshi da flowers tsakiya kuma cement chairs ne suma aka zagaye wurin dasu suka zauna...suka danyi shiru na wani lokaci kafin Aysha ta bashi labarin duk yanda sukayi da proprietor daxun...shi kanshi baiji dadi ba kuma suma yaga yanda duk Mood dinsu ya sauya dan haka yace ko baza'a je saloon ba shi yanaso ya kaisu wani wuri...Bilkisu ce ta fara cewa bazataje ba kunsan mutumiyar taku😂sai da kyar suka samu suka lalla6ata ta amince ta bisu..daga nan basu koma ciki ba suka shiga motanshi suka wuce..kai tsaye Ten to Ten ya fara kaisu yayi musu ordern abinci mai kyau yace suci dan yasan yau da kyar idan sunyi lunch gaba dayansu...ba suyi musu ba kuwa sukaci dan da gaske ba abinda sukaci tun breakfast... suna barin nan ya kaisu park nan kuwa duk suka ware suna enjoying kansu...bayan sun bar park din suka shiga Ado Bayero Mall sukayi shopping snn sukai branching a gidan grandmother dinshi dake Tarauni...tana zaune parlor tanashan nono da fura suka shigo...ta dago tayi musu kallo daya tareda ta6e baki snn ta cigaba da shan furanta...saida suka karasa ciki suka zauna Sa'eed yace"Hajjaju baki ganni da mutanen naki bane?.."sake ta6e baki tayi ta kur6i furanta kafin tace"ai ni ba ruwana da mutanen nan yanxu...tsakani da Allah suna cikin garin nan yaushe rabon da naga kafafunsu cikin gidana?.."dan murmushi Billy tayi tace"Haba Hajiya kinaso Sa'eed yaji kanmu knn?.."tace"yo jin kai na nawa kuma Bilki?..ai saidai kar a kuma"...Aysha daketa murmushi itama tace"to munji mun dauki laifinmu Hajiya kuma mun bada hakuri inshaAllah baza'a sake ba..daga yanxu duk weekend sai bestie ya kawomu mun gaisheki"...harara mai kyau ta watsa mata tace"sarauniyar 'yan dadin baki..to na hakura dai ba dan halinku ba..ya kuke ya karatun?.."sukace"karatu Alhamdulillah Hajiya..ya gida"..tace"lafia lau..ya wajen iyayen naku?.."Sa'eed dai na zaune yana kallonsu..lokaci guda i hira ya 6arke a tsakaninsu dama hajiya ba daga nan ba akwai labari su din ma kuma ba baya bane...a takaice sai da sukai sallahn magrib suka bar gidan...kai tsaye ya maidasu Hostel kowacce rikeda kayan kwadayin da suka siyo a shoprite..duk wnn kunci da 6acin rai da suka shiga daxun yayi disappearing..besty kam yayi kokari.

Wahsegari sunday karfe 7 daidai Bobby ya dannawa Nuru kira...bai dauka ba sai a karo na biyu ya daga cikin magagin bacci...Bobby ya dan ta6e baki jin bacci ma yake yace"kana jina?..ka fadama students din naka zan shigo 8 muyi lectures din..and tell them duk wanda ta wuce 8 batazo ba batada C.A"...yana gama fadin haka bai tsaya jin me zai fada ba ya kashe wayanshi...da mamaki sosai Nur yabi wayan da kallo kafin ya sake danna masa kira...saida ya kusa katsewa snn ya dauka..da sauri Nur yace"Bobby me kake nufi ne wai?..i don't understand"..babu gardama ya sake repeating abunda ya fada daxun..Nur ya wani marairaice yace"amma Bobby ka duba time kuwa ka gani?..this is past 7 yanxu har yaushe aka kira aka sanar dasu su fito gashi yau weekend"..a takaice Bobby yace"that's non of my business.. ba kai kakeso inyi musu lectures ba?..to gashi nan zanyi and wallahi duk yarinyan da ta sake na rigata shiga class din nan tayi loosing c.a so kindly call and ask them to start coming tun kafin 8 din yayi"...still yana gama mgn ya kashe wayanshi...Nur ya girgiza ya shiga neman number Lamido ya samu ya kirata...yasan duk meyasa Bobby ke wnn abun sbd yayi amfani da Mummy ya tilastashi yin abunda baiso ba shine shima yakeso ya rama ta wnn hanyan...yana zuwa kan numberta yayi dialing amma har ya katse bata dauka ba..shi kuma bai hajura ba ya sake kira..yana dab da katsewa ta dauja cikin muryan bacci tace"good morning sir"...yace"Morning Lamido inaso ki sanar da duk 'yan class dinku su shigo college zuwa 8 an samu wanda zaiyi taking over reproductive health dinku"..da sauri ta kalli wall clock dake manne cikin dakin nasu kafin tace"but sir this is 7:15"..yace"i know just try your best..tell them duk wadda batayi attending ba tayi loosing c.a and i want yiu to be fast about it please"..a hankali tace mishi"ohk"..snn ya kashe wayan...Billy dake bacci ta fara tashi tayi mata bayani snn ta dauki wayanta ta kunna data tayi musu bayani ta voice note ta tura a group snn kuma ta dhiga kiran duk wanda tasan zai iya sanar da wasu tana sake fada musu...Billy kuma fita tayi tayi announcing wa 'yan class dinsu dake cikin hostel din...saida ta tabbata ta fadama kowa snn ta koma daki..itama Aysha daidai lokacin ta gama kiran duk wanda zata sanar ma...tana duba agogo tana 7:35 dan haka ta mike da sauri ta fada bathroom tayi wanka sharp sharp tana fitowa itama Billy ta shiga...karfe takwas saura mintina goma suka gama shiryawa..ita tana sanye cikin abaya sky blue tayi rolling mayafin rigan..Billy kuma dogon riga ta saka na atampa ta daura dankwali sai veil dinta a kafada...koda suka fita compound drivern school bus har ya fito dan haka suna gama fitowa suka shiga motan zuwa cikin makaranta...motan na gama parking duk suka fito suka nufi class dinsu makarantan yayi tsit sai few students dake shigowa karatu...mutum 8 kadai suka samu a class din sunzo idan aka hada dasu da suke cijin hostel su 15 sun zama 23 knn out of 38...hankakinta duk yabi ya tashi ta dauki waya tana kokarin sake kiran wasu kiran provost ya shigo wayan...tayi picking da sauri tace"Sir wlh har yanxu da yawa basu karaso ba..mu 23 ne kadai a class din"..yace"no problem ki fada musu suyi sauri suzo before 9 ni zanyi kokari in rike maku shi har zuwa 9 din"...tace"thank you sir"..snn ta katse wayan...group dinsu ta sake shiga tayi announcing cewa an kara musu 30 minutes dan haka kowa yayi sauri ya karaso.
Cikin ikon Allah kafin 9 din gaba daya sun hallara...shi kuwa Bobby yana office din Nur time to time yana duba agogo...9 din nayi daidai ya mike duka fito daga office din tareda Nurun...suna haurawa sama ta window ya hangosu zazzaune cikin class din kowa da kalar kayansa sai ya dan dakata da tafiyan yana duban Nur yace"and why are they not in uniform?.."Nur yace"dama lectures din weekend bada uniform suke zuwa ba gaskia..kuma kaima bakace ace musu su sa uniform ba ai"..bai sake cewa komai ba suka karasa class din hannayensu zube cikin aljihu.






Masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank..sai a tura evidence of payment ta 07063800556.









Rano✨






🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22


08


Suna shiga gaba daya class suka hada baki suna gaishesu..Nur ne kadai ya amsa musu da "morning class ya weekend?.." suka amsa da lafia yace"well as a result of maternity leave da malaman Reproductive Health dinku ta tafi nasan you people do miss alot a karatunku ga kuma exams dake approaching...Class Rep dinku tazo ta sameni da maganan and our Generous Proprietor here says he will assist you guys har kuyi covering syllabus dinku"..ya karasa mgn da wani killer smile a fuskanshi tareda dan juyawa ya kalli Bobby dake tsaye rungume da hannaye yana sauraronshi...lokaci daya Class din ya dauki tafi jin Proprietor da kanshi yace zaiyi assisting nasu nan kuwa basu san saida aka kai ruwa rana before ya amince ba...Lamido da Bilkisu kuwa kallo daya sukayi masa gaba daya sukayi kasa da idanunsu..Billy dai addu'a take kada Allah ya kawo dalilinda zaisa wnn shegun idanuwan nashi su sauka a kanta..ita kuma Aysha hararan gefen ido take binshi dashi cikin ranta tace"inyamurin banza inyamurin wofi"..daidai nan kuma Nuru ya dubi Bobby yace"to Dr.Bobby bismillah"..daga haka ya koma can karshen class din ya samu wani empty seat yayi zamanshi a wurin...shi kuma Bobby ya dan kalli class din har yanxun yana rungume da hannu thinking from where to start...saida yayi shirun amost 3 mins kafin yace"where do you guys stop?.."daya daga cikin 'yan class din ta fada mishi last topic da sukayi...yana dan gyada kai ya tambayi course outline nan ma suka bashi...saida ya gama studying course outline din snn ya ajiyeshi kan table dake gabanshi yace"well according to the course outline kunada remaining 5 topics to cover before the exams..now zamuyi kokari muyi covering 2 topics the ramaining ones kuma zakuyi dividing kanku into 3 groups..each group su dauki one topic suje suyi studying dinshi sosai zuwa ranan Thursday zakuyi presentation..do u get me?.."gaba daya suka amsa da sun gane...shi kuma ya juya ga board dinsu yaga akwai rubutu a jiki sai ya sake juyawa garesu yace"who's ur class rep?.."gaba daya suka nuna Lamido...shi kuma ya wani daure fuska ganin itace dan lokaci daya incident din jiya ya fado masa a rai...itama daure nata fuskan tayi snn ta mike kanta a kasa..dukda ba kallonshi take ba tanajin wnn shegun idanun nashi a kanta..."come and wipe the board"..ya fada still looking at her...batayi musu ba ta fito tayi wiping board din ta juya zata koma ya sake fadin"da fingers dina kikeso inyi maku rubutun?.."bata juyo ba ta karasa seat dinta ta bude locker dinta ta dakko wani pink marker ta kai mishi snn ta sake dawowa ta zauna...duk wnn abun dake faruwa Dr.Nuru na bayan class din yana kallonsu...murmushi kawai yake yana girgiza kai cikin ranshi yace"zamuga yanda za'ayi wnn lecture"...sunan topic din Bobby ya rubuta jikin white board snn ya juyo yana facing dinsu yace yanaso daya daga cikinsu ta danyi briefing dinsu about the topic before he starts...wajen mutum biyar ne suka daga hannu shi kuma ya shiga binsu da kallo daya bayan daya yanaso yayi choosing mutum daya a cikinsu karaf idonshi suka fada kan Lamido...ya dage gira yana kallonta da kyau hadda sakin wani dan iskan smile cikin ranshi yana ayyana ita zaiyi selecting dukda ba daga hannu tayi ba kawai dai yanaso yana brain dinta da kullum Nur ke cewa she's genius she's this she's that..yau yanaso ya kure brain din nata...daga nan inda yake tsaye yayi pointing dinta da finger dinshi yace"You.."da sauri ta dago idanunta saidai suna sauka cikin nashi ta sake mai dasu kasa...still yana duban inda take yace"fito kiyi briefing namu akan topic din ba kece class rep ba?.."ya karasa mgn still da wani killer smile a face dinshi...ita kuwa qala batace ba ta mike daga seat dinta ta fito...ta juya taga sunan topic daya rubuta snn ta sake juyawa tana facing class din making sure bata kalli inda yakeba don kada ma ya zuba mata wadan nan idanun nashi yasa ta kasa ta6uka komai...bayani ta shiga yi musu dalla dalla kaman ba briefing dinsu yace tayi ba...tunda ta fara dama ya jingina da wall ya wani lumshe ido yana sauraronta sam baiyi tunanin zata iya ba...a yanda take explaining ma sai yakega kaman koshi da yake certified gynaecologist bai zama lallai ya iya yanda tayi ba..sam baiji dadin hakan ba kuma dan so yayi ya kunyatata a gaban Nur da kullum yake kiranta genius...yanxu kam ko da bai yadda she's genius ba tabbas yasan she's brilliant tunda har ta iya explaining abunda ba'a koya mata ba haka..daga yanayin yanda take magana kuma ya fahimci kaman she's used to it dan babu wani alaman tsoro ko rashin sabo a tattare da ita...duk sai yaji ranshi ya fara 6aci all of a sudden...hada ido sukayi da Nur aikuwa ya dage gira irin ya kaga?..shi kuma ya dauke kanshi ba tareda ya kalleta ba yace ya isa haka ta koma ta zauna...6oyayyen ajiyan zuciya ta saki cikin ranta tace"Finally"..sa zahiri kuma batace qala ba ta wuce ta koma seat dinta..shi kuma ya dora daga inda ta tsaya...bayani yake musu sosai shima irin bayanin da bai ma ta6a zaton zaiyi musu ba..suma kuma class din suna participating sosai...nan take yaji ashe yin lectures dinma is not as bored as he thinks...a da kawai gani yake irin boring lectures zasuyi sai kuma yaga ba haka ba baisan ko sbd class din suna participating bane...yana karasa topic din data fara ya shiga yi musu dayan shima kuma suna understanding sosai...a takaice saida suka dauki almost 3 hours kafin su gama...bayan ya gama amsa tambayoyinsu ya sake jaddada musu mgnr presentation da zasuyi ran Thursday snn yayi musu sallama ya fita mai girma provost yabi bayanshi...har ya fara sauka stairs Nur ya bishi da sauri suka shiga sauka tare yace"ko baka fada ba nasan u enjoyed it"...harara kawai ya watsa mashi baidai ce komai ba...shi kuma ya saki wani smile tareda dan lowering voice dinshi yace"and ya kaga brain din Lamido?..hope you are now satisfied?.."tsaki kawai Bobby ya saki yaki kuma kulashi...saida suka fito yace mishi"zamuyi dropping dika ne?.."Nur yace"don't bother nazo da mota kawai dai dan Allah kace ina gaida su pretty idan kaje gida"...bai sakeyi mashi mgn ba ya shiga mota bayan driver ya bude mishi..shima drivern ya zaga ya shiga snn ya tayar da motar suka tafi...shi kuma Nur saida ya shiga office ya dauko wasu files snn ya shiga nashi motan shima ya wuce.

Da wuri suka fito daga Class din as a result of message data gani na Hammanta yana ce mata sun karaso...suna fitosa ta hango motanshi ai batasan sanda ta taka a guje zuwa wurin ba...Bilkisu ta shiga girgiza kai tana fadin"Allah nunamin randa zaki girma Lamido"...tun kafin ta karasa duk suka bude mota suka fito...Hamman nata ne da Yusra sai kuma Husna mai cewa ko zaizo bazata zo ba...kai tsaye tana isa ta wani d'ane jikinshi tana dariyan farin ciki...shi kuma ya rabata da jikin nashi yace"ke har yanxun bakisan kin girma ba koh?.."daria ta saki tareda dan kwa6e fuska tace"nidai ban wani girma ba"...murmushi kawai yayi ya girgiza kai yasan Maama will never change...ita kuma sai ta juya ta janyo Husna da Yusra ta rungumesu gaba daya kafin ta dago tana cewa Husna"kikace kuma bazaki zoba?.."murguda baki kawai Husna tayi batace komai ba...a daidai lokacin Billy ta karaso garesu aikam Husna na ganinta ta karasa gareta ta wani rungumeta kafin ta dago tace"nima ga yayata nan"...murmushi kawai Billy tayi tareda kama hannun Husna suka karasa ta fara gaida Hamma...bayan sun gama gaisawa tace ya kamata su karasa daga ciki...kaman jira suke kuwa duk suka shiga mota zuwa cikin Hostel...daidai inda ake parking yayi snn suka bude mota suka fito...yace su shiga ciki dasu Husna shi da akwai inda zaije ya dawo...su Aysha hadda wani marairaicewa akace"amma dai Hamma ba dadewa zakayi ba koh?.."ya saki murmushi ganin wnn shagwa6an nata da bai karewa yace"bazan dade ba Maamata...da wuri zan dawo muyi mgnr daya kawoni garin"..nan dai sukayi sallama dashi ya wuce su kuma suka shiga ciki...direct dakinsu Billy ta bude suka shiga Husna tayi wani irin tsalle ta dire akan gadon Billy tana fadin"nima dai ina candy FCNM din nan taku zance daddy ya kawoni...makarantan ba karamin burgeni take ba"...Aysha data kama Yusra suka zauna kan nata bed din tace"ba wani FCNM da zakiyi yarinya...ni kaina yanxu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login