Showing 39001 words to 42000 words out of 231169 words

Chapter 14 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9716

tace"au yanxu har daman zuwa zance ma kika bashi mutumin da bakisan halinshi ba Lamido?..ba gara Sir Abdool din ba tunda shi munsan wayeshi?.."Aysha ta ta6e baki tace"ba dama ayi mgnr arziki sai kice Sir Abdool...nidai dan Allah ki taimaka ki roki Ammi kice zan rakaki gida sai muje tare plss"...a kufule Billy tace"bazanyi ba"..tace"C'mon Billy dan Allah fa nace?.."Billy tayi mata banza bata kulata ba.

Da yake event din ranar na dare ne basu suka fara shiri ba sai after magrib...yauma kaman jiya har gida make up artist tazo tayi musu wnn karon hadda Billy...Lace ne a jikinsu yellow da black flowers a jiki sai aka daura musu black head dinkin straight gown daya zauna jikin kowaccen su...karfe takwas da wani abu Hamma Najeeb ya kwashesu zuwa hall da zaayi event din...wurin yayi kyau sosai hakama Amarya da maids dinta tamkar a sacesu a gudu sbd kyau...Amminsu ma yau ba'a barta a baya ba dan make up akayi mata light wanda baikai nasu ba sai ta fito tayi das abunsa kamar yammata...biki dai yayi biki domin anci ansha anyi ruwan kudi snn an dirki rawa kaman ba gobe...su Aysha basu koma gidaba sai after twelve..wanka kawai sukayi suka kwanta bacci.

The next day ringing din wayanya ya tadata daga bacci...ta mike zaune a hankali tana murza ido takai hannu ta dakko wayan nata..Prof taga ke kira kaman yanda tayi saving dinshi..ta saki smile sai a lokacin ta lura duk su Billy ashe sun rigata tashi sun ma fita daga dakin...tayi picking da sallama..a daya 6angaren yace"my beautiful baby girl..hope bani ma tasheki a bacci ba"..ta wani narke tace"ka tasheni mana"..yace"eyya am sorry baby pardon me plss..am eager inji voice dinki ne that's why amma am sorry kinji?.."tana murmushi tace"baka laifi ai"..cikin excitement yace"Really?.."tace"Sure.."yace"baby gaskia inason ganinki sosai..i feel like coming to Gombe right now"..tayi kasa da murya sosai tace"no ka bari yanda muka tsara plss..anjima kadan zamu wuce Bauchi inshaAllah"..yace"shknn sai anjima..i have to barki kiyi wanka kiyi breakfast koh?.."tace"yea..ba bye"..shima yace"bye"..snn suka ajiye waya...ta sauka daga gadon tana sakin murmushi one after the other ta shiga bathroom...brush kadai tayi snn ta fita zuwa parlor...a dinning ta iskesu gaba daya suna breakfast except daddy da Ammi da normally sukafi yin breakfast dinsu a parlon daddyn...karasawa tayi taja kujera ta zauna tace"shine duk kuka fita baku tasheni ba"...Billy tace"yo kina can kin wurgar da bakinki akan me zamu tasheki?.."Husna tasa daria tace"kai Adda Billy meye wurgar da baki kuma?.."Billy tace"mutum ya kwanta yana bacci mana"...Husna ta sake sa daria...itadai Aysha bata kulasu ba ta fara serving kanta...saida suka gama Hamma Najeeb ya shigo yace suyi serving dinshi...Husna ce tayi serving su kuma sauran suka koma parlor.

karfe hudu da mintina aka fito da amarya zaa kaita gidanta dake Bauchi...hajia Aysha dai ta samu da kyar da sidin goshi Ammi ta barta zuwa kai amaryan tace daga nan ma ta biya gidan Fiddausi ta duba mata jikin Mufid idan tazo gobe saisu dawo tare...murna wurinta kaman bata ta6a zuwa Bauchi ba har saida Ammi tayi zaton ko wani abun zai kaita sai kuma ta waske tacema Ammin ba komai...basubi motan kai amarya ba Ammi ta hadasu da driver ya tafi dasu...kai tsaye gidan aunty Fiddausi ta nufa ko hanyan gidan amarya basu nema ba...lokacin karfe biyar ya kusa...suna shiga ciki suka gaisa da Auntyn nata dake nan mai kamada Ammi sak snn Aysha tayi mata bayanin zatayi bako dan yanxu haka ma yana kan hanya...kallonta ta shiga yi tace"Adda bata saniba koh?.."da sauri Aysha tace"Aunty kinsan idan na fada mata bazata barni inzo ba..tama ce gobe idan tazo duba Mufid sai mu wuce tare..Aunty ya jikin nashi kuwa?.."tace"yaji sauki dama malaria ne yake fama dashi amma yanxu ya warke yana ciki yana bacci"..tace"to Allah kara sauki amma ya banga Mufida ba".."Mufida na islamiyya..yanxu me za'a dafama bakon naki?.."Aunty ta tambayeta kai tsaye...ta danyi shiru tana nazari kafin tace"kawai Aunty a dafa mishi koma menene..nasan ya kusa karasowa yanxu haka"..mikewa auntyn tayi ta nufi kitchen tace"to bari in fada musu suyi mishi abu mai sauri tunda lokaci ya kure"...cikin jin dadi tace"yauwa Aunty na"...Billy dai na sauraranta ko uffan batace ba as haushinta takeji for accepting wnn mutumin kuma wai harda bashi dama yazo su hadu...da farko ma cewa tayi ita gida zata tafi sai da kyar ta samu ta shawo kanta kan ta bari su tafi tare gobe.

Prof bai samu shigowa Bauchi ba sai after five...yabi address data tura mishi sai gashi kofar gidan Aunty Fiddausi...ya kirata a waya yace mata ya iso ita kuma tacema nai gadi ya bude mishi ya shigo...tana tsaye jikin window tana ganin shigowanshi...da kanta ta fito cikin black abaya da yayi nata kya sosai ta shiga dashi dakin baqi...ko zama ya kasayi kallonta kawai yake yanajin tamkar ya dagata yayita juyi da ita cikib parlon sbd tsabar kyau da tayi mashi...duk yasa ta farajin wani iri wlh..da kyar ta samu ya zauna itama ta zauna suja fara gaisawa...ya kasa dauke idonshi daga kanta kona second daya...mikewa tayi ta shiga ciki ta kawo mishi drinks da snacks kafin a gama abinci...har ta zuba lemo ta mika mashi bai bar kallonta ba..ta dan daure face tana turo baki tace"Prof mana...banason kallon nan wlh"..a hankali ya dauke idonshi yana sauke wani gwauron ajiyan zuciya yace"na dena my baby..just know that i love u so much"...dan murmushi ta saki for the first time itama tac mishi"i love u too"...ya wara idanu sosai yana kallonta full of excitement yace"Really?..da gaske kina sona baby?..thank u so much baby Allah ya miki albarka"...ta wani sake karya muryanta tace"Ameen Ameen my Baby Boo"...wani irin dadi yaji ya sake lullu6eshi...shikam baisan inda zaisa kanshi ba duk ranan da akace ya mallaki wnn zandadediyar yarinya..she's like 100 percent kaman ita tayi kanta..she's like a complete package da kowane namiji zaiso samunta as his wife...hira sosai suka shigayi irin na masoya inda mutumiyarku keta zu6a shagwa6a shi kuma yana tarairayarta...bayan an gama girki Billy ta kawo mishi snn ta zauna suka gaisa...Aysha tayi introducing nata as her best friend shima tayi introducing nashi as her baby boo...wani takaici Bilky taji ya isheta jin wai wnn tsohon take kirada baby boo..bata wani jima suna hira ba tayi excusing kanta ta fita su kuma suka dora daga inda suka tsaya...har akai sallahn magrib basu gajiba yaje sallah ya dawo suka cigaba da gashi...in short Professor bai bar gidan nan ba sai da aka kira sallahn isha..ta rakoshi har mota suna jin kaman bazasu rabu ba sukayi sallama ta kima ciki shi kuma ya tada mota ya wuce yasan kwanan Bauchi ya kamashi dole tunda dare yayi saidai da safe ya koma...a labarin da sujayi ne ya sanar da ita bashida mata domin tun bayan rasuwar matarshi tsahon 3 years bai sake aure ba amma yanada yara uku mata biyu namiji daya...babbar macen tana aure a Abuja with a son mai binta kyma ba'a dade da bikinta ba ita kuma tana kd sai karamin cikinsu Muslim yana karatu a Malaysia.

Washegari wajen 10 suka tafi gidansu Billy kafin Ammi ta karaso...ta gaisa da Ummansu Billy da abbansu sai wajen 12 ta koma gidan Aunty...lokacin kuma su Ammi sun jima da zuwa tareda Yusra da Husna...nan suka zauna sunata faman hira amma koda wasa Aunty Fiddausi batayi mentioning zuwan bakon Aysha wa yayar tata ba dan tasan idan ta sani har ita kanta zata hada ta wankesu tatas shiyasa tayi shiru da bakinta..wnn dalilin yasa kullum Ammin ke cewa bakinsu daya da Aysha dan nasu yazo daya sosai zaiyi wahala aji kansu snn kuma Aysha bata ta6a zuwa hutu ta koma ba tareda tazo Bauchi gidan Auntyn nata ba...suna shiri sosai da ita unlike Husna da basa jituwa kwata kwata...saida sukayi sallahn asr snn suka nata sallama suja tafi...Aysha duk sai tajita wani iri ita dama su barta ko sati ne tayi a Bauchin.


Kano...


Yana kwance cikin dakinshi yayi wani coiling a kan gado yana bacci Ilham ta shigo...tun daya gama gymming dinshi yayi wanka ya kwanta shine har yanxun bai tashi ba don sai yamma zai shiga Hospital...ta karasa kan gadon tana hargitsa uban gashin kanshi mai santsi takai bakinta saitin kunnenshi tace"Uncle Bobby wake up"...a hankali ya bude ido snn ya sake maidasu ya rufe...Ilham ta sake hargitsa gashin nashi tace"Uncle Bobby wake up mana..Mummy said i should call u"..wnn karon gaba daya ya bude idanun nashi yana kallonta...sai kuma ya mike zaune yana gyara gashinshi data hargitsa yace"Ilham bakida hankali kou?.."tace"Sorry Uncle Bobby Mummy tace a kiraka"..sauka yayi daga gadon snn yace mata"kice am coming"..Ilham bata sake mgn ba ta mike ta fita..shi kuma ya shiga bathroom yana jin haushin katse mishi bacci da akayi...ya tabbata da ba Ilham din suka turo ba duk wanda yazo ya tadashi a baccin nan sai anji kansu dashi amma Ilham favorite dinshi ce shiyasa ko fada bai fiye yi mata ba...brush yayi ya wanko face dinshi ya fito don bai dade da yin wanka ba...ya dauki wayanshi kan mirror snn ya fita...a Central parlor ya samesu zazzaune...Mummy ce da Aunty Sumy sai wata mata da bai gane wace ba...ya karasa kusada Mummy ya zauna snn yace"Mummy gani...lafia dai koh?.."da igbo tace mishi"lafia ka gane wnn?.."ta nuna matar dake zaune...ya girgiza kai alaman aah...tace"Sunanta Hafsa kuma qanwar Isma'il ce"..ai tun kafin ta rufe baki ya wara ido sosai yana kallonta fuskanshi har ya sauya sbd 6acin rai...bata damu da sauyin face din nashi ba tacigaba"zuwa tayi tanaso ta tafi dasu Miemie su dubo grandmum dinsu da batada lafia"...bata rufe baki ba cikin zafin rai still da igbo yace"babu inda zasuje Mummy...basu bukatan wayan nan mutanen a rayuwarsu"...shiru Mummy tana ganin yanda yakeson kunyata ta gaban baiwar Allahn nan..dukda bada hausa yayi mgn ba tasan zata iya fahimta sbd yanda ranshi ya 6aci all of a sudden...Aunty Sumy kam dama she expect this to happen shiyasa she's not surprised...ita kuma bakuwa Hafsa kanta na kasa tana sauraronsu...dukda bata gane me yake cewa ba har ga Allah ko hanata daukan yaran sukayi bazatayi blaming dinsu ba tunda tasan duk wulakancin da sukama uwar yaran har ma dasu kansu yaran a baya so bazataji haushinsu ba ko kadan...Bobby da yaji zuciyarshi na kara haurowa sama mikewa kawai yayi ya fita daga parlon cox idan yaci gaba da zama zai iya causing scene din da he might end up regretting dan haka yake ganin it's better he leaves...Mummy da taji kunyan abunda ya fada ta bishi da kallo kawai har ya shige flat dinshi snn ta dawo da kallonta ga Hafsa tace"don't mind him Hafsa inshaAllah tare zaki tafi dasu..amma ayi kokari a dawo dasu gobe sbd kar suyi missing school"...da sauri Hafsa tace"in Allah yadda za'a dawo dasu Mummy...nagode sosai Allah ya saka da alkhairi"...Mummy ta amsa da Ameen snn ta juya ga Aunty Sumy da ita kanta bataji dadin hukuncin da Mummyn ta yanke ba tace taje ta hada kayan Ilham ta kawo itama Miemie ace ta shirya nata kayan ta fito...haka ta mike jiki ba dadi ta shiga flat dinta...dakin Miemie ta fara tsayawa ta fada mata ta dauki kaya set daya zasuje gidan grandma dinsu da Aunty Hafsa...itama ranta baiso ba amma ba yanda ta iya ta dauki set dayan kaman yanda tace ta saka a jaka snn ta fita...itama Aunty ta fito da na Ilham a hannunta.


















Rano✨





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 sai a tura evidence of payment via 07063800556.
14
Miemie ta amsa kayan ilham din ta hadashi da nata cikin bag din data dauko snn ta samu wuri ta zauna...Hafsa ta mike tana duban Mummy tace"Mummy to bari muje in Allah ya kaimu gobe da kaina zan dawo dasu..nagode sosai da sasai Allah ya saka da alkhairi ya kara girma"...Mummy tace"ba komai Hafsa Allah ya bata lafia"..ta amsa da Ameen snn ta rike hannun Ilham zasu fita Mummy tace"Ilham ba sallama?.."juyowa tayi tana murmushi tace"ba bye Mummy mun tafi yawo"...murmushi na daria tace"to a dawo lafia"..daga haka suka fita Aunty Sumy da Miemie sukabi bayansu...kafin su karaso har ta bude mota sun shiga..suna zuwa Miemie ma ta bude ta shiga ita kuma Aunty Sumy tace"to shknn Hafsa sai goben koh?.."Hafsa tace"eh inshaAllah...ina godia fa Maman Miemie Allah ya bar zumunci"..Aunty Sumy tace"Ameen"..snn ta dagama ilham hannu alama bye itama ta daga mata...Miemie dai na zaune back seat duk rai a 6ace..sam batason zuwan inda matar nan wlh..dukda ba wani girma gareta ba time din she can still remember yanda sukayi treating nasu kaman ba family dinsu ba...bayan sun gama sallama Hafsa taja mota ta tafi ita kuma Aunty Sumy ta koma gida.

Basu zarce ko ina ba sai gidan kakarsu dake Kabuga...tana gama parking ta bude motar ta fita tareda kama hannunsu gaba daya su biyun suka shiga cikin gidan a haka...kakarsu na kwance parlor tana jiran karasowarsu...tana ganinsu ta mike zaune da kyar ta kama hannayensu kawai sai ta rushe da kuka..ba ita kadai ba hatta Hafsa saida ta tayata kukan...ko baa fada ba tasan tanajin ciwon raba Sumayya da Isma'il tunda gashi nan tun bayan rabuwarsu ta kasa gane kan danta...matar data aura mishi ma bai dade da rabuwa da Sumayyan ba ya saketa shi kuma ya tattara ya koma London da zama sbd baqin cikin rashin Sumy...kuka takeyi sosai tana cewa su taimaka su yafe mata snn su roki mamansu ma ta yafe mata...Ilham dai tayi tsuru as kwata kwata bata san inda zancen ya dosa ba...Miemie kuwa sarai ta fahimci me take nufi amma tayi gum da bakinta dan bataji zata iya yafewa ba itadai...ta dauki tsohon lokaci tana kuka tana su yafe mata ganin kamar numfashinta zai dauke suka rabata da hannuwan yaran da kyar snn suka dauketa suka maidata daki itada autarsu mai suna Safiyya...Hafsa na fitowa daga dakin ta dannama dan uwanta video call don yace tana daukosu ta kirashi vid call yanaso ya gansu...yana ganin kiran nata ya dauka tana murmushi tace mishi"to Yaya ga 'ya'yanka dai yau na kawosu wajen Umma"...yace"kin kyauta sosai Hafsa..dan banisu mu gaisa plss"...ba musu ta mika musu wayan tace"speak to ur Dad"..Miemie ta wani hade rai snn ta karbi wayan...kallonsu ya shigayi sosai idonshi na cikowa da hawaye...it's been six long years rabonshi da ganinsu..yanxun kuma daya gansu sai yakejin wani irin kewa da sonsu na sake shiganshi...murya can kasa yace"Mamana"...Miemie ta dan tsuke baki kafin tace"na'am ina yini"...yace"lafia mamana ya school?.."a takaice tace dashi"fine.."kallonshi ya maida ga Ilham da tayi tsit tana kallonshi dan ba saninshi tayi ba...shima saida yaji wani kuka ya taho mishi da yaga kallon da take masa...ko ba'a faa ba yasan kallon rashin sani ne wnn..wai ace yana matsayin mahaifinta amma ta tashi bata sanshi ba...shi kam ina zaikai zunubin yaran nan dana uwarsu?..itama murya a sarke yace mata"Maman Aunty"...ta sake yin zuru tana kallonshi dan bata gane me yake nufi ba..Miemie dai ta gane don bazata manta ba lokacin tana jaririya haka yake kiranta Maman Aunty ita kuma Miemien ya kirata da Mamana..itama Aunty tacema Miemie Maman daddy snn tacema Ilham Mamana...yayi kokari ya maida hawayen dake idonshi yace"baki sanni ba right?.."da sauri ta daga mishi kai...yace"i am ur father"..yarinyar ta wara ido sosai hadda su rufe baki tace"Uncle Bobby ne babanmu ai"...yace"yea he is ur dad but ni na haifeku"...idon ta sake budewa cikeda mamakin abunda ya fada tace" dama maza suna haihuwa ne?.."diff yayi kamar ruwa ya cinyeshi..sai can kuma yace"sunayi mana kinga ni din nan nine babanku..shi kuma Uncle Bobby uncle dinku ne shiyasa kuke kiranshi da uncle"...kafin Ilham ta sake mgn Miemie tace"sai anjima"...tana kokarin kashe kiran yace"don't hang up plss..i missed u guys alot ko ganinku bazaki bari nayi ba?.."tayi shiru ba mgn shi kuma yace"ya Mamanku?.."ta sake cewa"she is fine.."shima ya danyi shiru na tsahon lokaci kafin yace"i know u are upset with me Miemie but believe me wlh nayi regretting komai dana aikata dan haka please inaso ki yafemin snn ki tayani rokon mamanki ma ta yafemin"...kallonshi Miemie tayi for like two minutes snn tace"toh.."daga haka bata jira me zaice ba ta kashe kiran..sam ta gaji da jin wnn maganganun nashi...ita har taso ta manta kamanninshi ma wlh..ilham kuwa dama bata sanshi ba so bata dauki abunda ya fada serious ba...haka suka kwana gidan duk basu wani sakewa dasu duk kuwa da yanda yan gidan suke kokarin jansu a jiki kin sakewa sukayi.

A can gida kuwa Bobby baisan tare dasu Hafsa ta tafi ba saida ya dawo daga Hospital around 9 na dare ya tambayesu Aunty Sumy tace sun tafi da Hafsa...wani hadadden kunchi yaji yana sauko mashi..yanxu knn Mummy saida ta tura yaran nan suka tafi?..bayan duk abubuwan da suka aikata a baya still take kokarin patching things up dasu?..ranshi gaba daya yaji ya 6aci..kawai ya wuce Flat dinshi...karfe goma da wani abu Mummy ta zuba abinci ta dauka da kanta ta nufi Flat din nashi...yana kwancen can kuryar gado ya juyama kofa baya..ta karasa ta ajiye abincin hannunta kan table snn ta isa gefen gadon nashi ta zauna...a hankali takai hannu ta zare hannunshi daya rufe fuskanshi dashi...ha dago yana kallonta snn ya mike zaune da kyar kaman mara lafia...sake kama hannun nashi tayi ta rike tana kallonshi da igbo tace mishi"so u are upset with me right?.."a hankali ya girgiza kai alaman aah...tace"you are lying nasan fushi kakeyi...kana jin haushi sbd na bari Hafsa ta tafi dasu koh?."kasa yayi da kanshi baice komai ba...Mummy tace"Bobby you won't understand..bansan ya zanyi maka bayani ba..kawai dai banaso ka nesantasu da yan uwan mahaifinsu kaman yanda ka nesanta mu da gaba daya yan uwan mahaifinku..ni kadai nasan how am feeling duk na tuna cewa grandfather dinku na nan da rai amma baisan inda kukeba tsawon shekara biyar...inaji a jikina bamu kyauta ba sam kuma nasan Allah bazai yafe mana..."bata karasa ba ya rufe bakinta tareda matsowa sosai ya rike hannayenta...idan ya bari tacigaba da magan nn tsaf zata kashe mishi jiki tasa ya farajin kaman shima bai kyauta din ba...ga kuma jininta da zai iya hawa idan bata bar wnn damuwan ba...yana kallon cikin idonta yace"Mummy ba laifi bane...ba laifinmu bane...laifinsu ne da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login