Showing 150001 words to 153000 words out of 231169 words

Chapter 51 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9668

aureta insha Allah sbd haka rashin lafia ya kare"..murmushi kawai yake saki yana gyada kai yama kasa bude baki yayi mgn...kawai mamakin yanda al'amari ya canxa yake..is this really happening ko kuma day dreaming yake?..a hankali ya zauna kan sofa dake nan kusa dashi bayan sunyi sallama da waziri ya sake lumshe ido yayi relaxing kan sofa din murya can kasa yace"i can't believe this?..Allah kasa ba mafarki nake ba"..Nur dake zaune yana kallonshi tasowa yayi daga inda yake ya karaso nan kusa dashi ya zauna yana dubanshi da murmushi shima yace"ba mafarki kake ba Dr Bobby..it's reality..Lamido dai ta kusa ta zama matarka congratulations to u"..tun kafin ya rufe baki Bobby yayi mishi wani runguma cikin excitement yace"i still can't believe this Nur..Anya ba mafarki nakeba?.."Nur yace"i told u ba mafarki kake ba da gaske ne..Allah ne ya amsa addu'anka"..dagowa yayi yana kallonshi har yanxu bakinshi kaman go at auduga yace"Allah Alhamdulillah..Alhamdulillah Rabbi am forever grateful"..yana gama fadan haka kuma ya mike tareda zura wayanshi a aljihunshi yace"lets get going I need to talk to Mummy about this"..Nur baice komai ya mike bayan ya day car key dinshi suka fita daga office din...Motan Nur suka shiga don dama da ita suka zo..kai tsaye ya kama hanyan gidansu kmr yanda Bobby yace..ko a hanya Bobby bai dena hamdala ba..kawai gani yake Allah yana matukar sonshi daya canxa mgnr aurenta a lokacin da ya gama giving up..gaskia ne da masu iya mgn suka ce duk wani tsananin yana tareda sauki kmr yanda duk mai hakuri yana tareda nasara...shidai yayi hakuri ya kuma fawwala Allah lamuranshi dai gashi ya kawo mashi canji a lokacin da bai ta6a tsammani ba..Lallai Allah abun godia...har suka isa gidansu bai dena godia wa wnn ni'ima ta ubangiji ba..gani yake an gama mashi komai a dunia saidai kuma yayi fatan gama wa lafia...ko parking Nur bai gama ba ya bude motar da sauri ya fita zuwa cikin gidan...Nur ya bishi da kallo yana girgiza kai yace"wa yaga ba sabon ba"..karasawa yayi ya gyara parking dinshi snn ya bude motar shima ya fita zuwa ciki...yana shiga yaci Karo da Mummy dake kokarin Shiga parlonta kawai sai ya rungumota ta baya yana cewa"Mummy I can't believe this..waziri yace wai ni zan aureta yanxu..am super excited Mummy Allah yasa ba mafarki nake ba"..juyawa Mummy tayi ta dagoshi daga jikinta tana kallonshi da murmushi a fuskanta itama tace"ba mafarki bane..duk wani da kaji a gaske yake faruwa ba mafarki ba..dama ba nace maka jikina na bani kai zaka aureta ba?.."da sauri ya shiga gyada kai kafin ya lumshe idanunshi ya sake rungume Mummy yace"Mummy nagode sosai..nagode da addu'arki gareni Allah ya saka da aljannah"...hannunshi Mummy ta kama suka karasa parlorn suka zauna tana dubanshi tace"Ameen..kaima Allah ya maka albarka..waziri yace mun gobe zasuje su samu Lamido tareda uncles dinka akan mgnr auren naku"..sake rungumeta Bobby yayi yama kasa cewa komai...Nur dake tsaye tun daxun yana kallonsu sai yanxu Mummy ta lura dashi tace"Nuru karaso ciki mana"..yana murmushi ya karasa cikin parlorn ya zauna yana gaishe da Mummy...kmr wanda ya tunada wani abu sukaga ya mike da sauri ya kama hanyar flat dinshi duk suka bishi da kallo suna daria..daidai lokacin Aunty Sumy ta shigo wayanta rike a hannunta tace"yanxun muka gama mgn da Aunty Munubiya tace tana nan zuwa gobe inshaAllah"..Mummy tace"to Allah kawota lafia".

Yana Shiga parlonshi ya zauna kan three seater tareda dialing number ta yana lumshe ido..har ya gama ringing bata dauka ba ya sake kira still no answer kawai sai ya ajiye wayar tareda mikewa ya shiga bedroom direct ya fada bathroom ya daura alwala ya fito ya shimfida carpet ya tayar da sallah don ya nuna godia wa ubangijinshi for such a blessing da yayi mashi na bashi auren Lamido...har azumi ya kamata yayi don nuna godiyarshi wa Allah...har dare ya tsala bai dena Kiran wayanta ba ita kuma bata dauka ba..ganin ba daga wa zatayi ba yayi sending mata"thank u..thanks for accepting me..I love you"..daga haka ya jiye wayar ya lumshe ido yana tuna duk moments da yayi spending da ita..kaman yayi tsuntsu yakai kanshi Gombe haka yakeji amma ba zaiyi wnn rashin kunyan ba matukar ba cewa akayi yazo ba..afterall saura baifi 4 days suyi resuming school ba so zai na samun daman ganinta duk time din da yaso..he prays Allah ya shirya mashi ita yasa bazata na aikata abubuwanda dole zaisa yayi mata masifa ba.

Gombe..

Tunda Lamido ta samu labarin yanda reshe ya juye da mujiya sai abun yazo mata a bazata sosai..wani irin sanyi taji jikinta yayi zuwa yanxun for sure tasan she does not hate him amma ya zatayi da Prof ne kam?..ba wai aurenta da Bobby ke 6ata mata rai ba..kawai yanda baby zai dauka kaman dama can yaudaranshi take shiyasa ta hanashi zuwa ga parents dinta da wuri..and shi kanshi proprietor nan ba sabawa tayi dashi ba..ita bata San ma ta ina zata fara zama da wnn mutumin as her hubby ba..tasan yana sonta da gaske amma har ga Allah itadai gani take kmr bayan auren zai sake rikidewa ya dawo asalin proprietor data sani a baya..gaba daya ranar yini tayi a daki tana faman kunchi ko abinci bataci ba kuma ba wanda yace mata don me...conference video call ta hada musu itada Billy da besty tana tuttura baki ta fada masu duk abunda ke faruwa ga mamakinta sai taga gaba daya sunyi farin ciki da mgnr don har lissafin biki suka fara kawai ta kashe wayarta tana huci..ita fa har yanxu bata ga ta inda ita da proprietor za'ace suyi aure ba..to ta inama za'a fara?..kawai gani take kmr abun ba mai yiwuwa bane..gashi tun jiya take kiran wayan Prof a kashe har zuwa yanxu kama a kashen yake ta rasa dalilinda yasashi kashe waya..so take ta sanar dashi an samu turn of events ya gwada turowa wai ko Lamido zai sauraresu amma bata samun wayan nashi..duk tabi ta zama wata iri ita ba mai lafia ba kuma ba mara lafia ba..tana gani tun daxun yake kiran wayanta taki dauka don batasan abunda zai fada mata ba kmr yanda itama batasan abunda zata fada mashi ba...kunayanshi ma taji tanaji wlh..tana nan kwance a daki har dare daddy ya turo Yusra ta kirata..ba musu ta mike tareda maida hulan kanta ta nufi parlon nashi..suna zaune tareda Ammi ta karasa ciki a nutse ta zauna a kasa..daddy yace"nasan kin samu labarin abunda ke faruwa wajen Amminki koh?.."ta daga kai alamar ta sani..daddy yacigaba"to inaso ki kwantar da hankalinki kiyi mana biyayya a wnn auren..a yanda yaron ke sonki nasan kema bazaiyi taking naki long time kafin ki fara sonshi ba..kuma ban yadda ki mashi wani rashin kirki ba Aisha..inaso ki girmamashi kmr yanda kikeyi a baya snn kar in sakeji ance kin hadu da wnn mutumin ko waya ban amince kiyi dashi ba..idan Allah ya kaimu gobe zasuzo a tsaida ranar aurenku..Allah yasa haka shine alkhairi a tare daku Allah kuma ya maku albarka baki daya"..a hankali ta gyada kai idonta a kasa..saida ta tabbata ya gama snn tace"daddy dan Allah ina son zuwa Bauchi gidan aunty fiddausi"..daddy yace"ba wnn sunday zakuyi resuming school ba?.."a hankali tace"eh amma kafin sunday din zan dawo..ko kuma a daukemu daga can tareda Billy kawai mu wuce"..shiru daddy yayi kmr bazaiyi mgn ba sai can yace mata"shknn saiki shirya gobe da safe a kaiki..Allah maki albarka"..ta amsa da"Ameen daddy"..snn ta mike ta fita daga parlon..Ammi ta bita da kallo bayan fitar nata tace"ikon Allah..wai Aysha ce tayi wnn nustuwa haka sbd mgnr aure ya 6ullo..wonders shall never end"..ta karasa mgn tana daria yayinda daddy ke girgiza kai shima yana murmushi..shi kanshi yaga wnn canjin tattare da ita fatanshi dai Allah yasa auren nasu shine alkhairi a tareda kowannensu.

Washegari da safe ta shirya kmr yanda daddy yace driver dinsu ya dauketa zuwa Bauchi..tana zuwa gidan ta fashewa small mom dinta da kuka wai za'a mata auren dole..Aunty Fiddausi nata aikin rarrashinta tace"ni banga abun tada hankali anan ba Aysha bayan kowa ya shaida irin son da akace yana maki"..tun kafin ta rufe baki tace"Aunty inyamuri ne fa..kuma wlh bashida mutunci masifaffe ne na bugawa a jarida..shknn ni sai a hadani dashi salon yayitama mutum masifa komai fa shi abun fada ne a wurinshi"...daria aunty fiddausi ta kunshe kafin tace"to kiyi hakuri ni da kaina zanyi masa fada ya dena maki masifa gaskia..kuma shi da yake jikan waziri ta ina ya zama inyamuri kuma?.."da sauri tace"babarshi inyamura ce kuma shima yanayin inyamurancin..kawai sai in haifi 'ya'ya a dinga koya musu igbo..wlh an cuceni"..daria sosai small mom dinta ke mata don ita bataga abun daga hankali a nan ba...idan ta fahimceta ba ma rashin auren wancan saurayin ne damuwarta ba kawai damuwarta an hadata dashi kuma wai masifaffe ne..ta lura iskanci ne kawai yasa take wnn abun amma ba kiyayya ba don bisa ga dukkan alamu itama tana sonshi kilan ganewa ne kawai batayi ba.

Sha biyu da wani abu tayi sallama da aunty fiddausi ta wuce gidansu Billy..ta iske Ummansu a parlor tareda sauran siblings din Billy maza..ta karasa ciki a hankali kaman wata mara lafia ta shiga gaisawa da Umma..Umma dake dubanta with smile tace"ashe kuma proprietor dinku zaki aura?..dazu Bilkisu ke fadamun..to Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana lokacin Aysha Allah yasa albarka"...juyawa tayi tana kallon Billy kmr zata fashe da kuka kafin ta sake juyowa ga Umma tace"Umma masifaffe ne fa"..daria Umma da sauran brothers din Billy suka sa jin abunda tace...Umma tace"banda abunki Aysha ai ba'a cika son namiji ya zama mara fada ba sbd raini"..turo baki kawai tayi bata sake mgn ba..wani elder brother din Billy mai suna Mubarak yace"naji ance jikan wazirin Gombe ne koh?.."mikewa tayi still tana turo bakinta tace"kuma babarshi inyamura ce"..daria suka kara saki Billy ta mike da sauri zuwa inda take ta kama hannunta tana kokarin kunshe dariar dake cinta itama tace"ki kyale Yaya best friend tsokanarki yake..yanxu mu shiga ciki ki bani labari in detail"..kwace hannunta ta shiga kokarin yi Billy bata sakeshi ba saida suka shiga dakinta..tana sakin hannun nata ta sake fashewa da daria har tana clapping hands dinta tace"wlh ba karamin dacewa kikayi dashi ba..dama garinku daya"..kallonta Aysha take har ta gama iskancinta snn ta karasa ciki ta zauna gefen gado tana duban Billy da wani murmushin mugunta tace"dadin abun dai kema naki yana nan zuwa..kwanan nan na samu labarin wani yana sonki har turowa ma zaiyi gidanku ayi mgn"..tsaki Billy ta saki tareda zama nan kusada ita tace"matsala na dake karya..uban wa ya baki wnn labarin?.."Aysha tace"ba labari aka bani ba kan idona komai ya faru..da gaske kema very soon zakiji ance an fidda maki miji sai ki zama cikin shiri"..kallonta Billy take kmr mai son gano gaskia..sake matsawa jikinta tayi tana marairaicewa tace"bani labari dan Allah..da gaske kike ko da wasa?.."Aysha tace"da gaske nake wlh..Hammana ne yake sonki"..wani kwalo idanu waje Billy tayi kmr taga abun tsoro tace"Lamido kiji tsoron Allah"..Aysha tace"Allah kinji na ranste maki da gaske nake..a gabana ya fadama Lamido ke yakeso shi kuma Lamido yace zaiyi mgn da grandpa dinku"..dakatawa tayi tareda kamo hannayenta tace"Billy i cant believe this wlh..abun yayi mun dadi wai ace Hamma na zai aureki..dan Allah Billy kema ki soshi kinji and kada kije ki fada masa na sanar dake dan cewa yayi bai yadda in fada maki ba"...murmushi Billy ta saki tareda zame hannunta daga nata tace"banza 'yar rainin hankali"..ta fashe da wani daria tana cewa"ni dake za'a ga dan rainin hankali a ciki..yarinya tanaso tana kaiwa kasuwa"..da sauri Billy tace"ai kema kina son proprietor kuma kina kaiwa kasuwa"...haka dai sukaita tsokanar junansu Aysha bata bar gidan ba sai dab da magrib tayi sallama dasu ta koma gidan aunt dinta.

Washegari Waziri da Uncles din Bobby biyu suka je nema mashi aurenta wajen Lamido...Waziri da kanshi ya bada kudin aure inda Lamido,daddy da uncles dinta suka karba tareda tabbatar musu da cewa an bashi ita halak malak..Lamido yasha godia wajen waziri kaman wani gagarumin abun yayi mashi..an tsayar da mgn kan baza'ayi biki ba sai ta gama makaranta amma zai iya zuwa duk time da yakeso yayi mgn da ita wnn kam an bashi izini batun aure ne dai akace sai ta kammala.
Washegarin ranar suma sukaje Bauchi nemawa Hamma auren Billy a hannun kakanta babu wasting of time suma suka amince suka kuma ce an bashi aurenta lokaci kadai ya rage a shafa fatiha.

Lokacinda labari ya iske Bobby ji yayi kaman yayi tsuntsu ya tafi Gombe sbd farin ciki..bai taba tunanin komai zai faru cikin sauki haka ba..matsala daya da yake fuskanta yanxu shine rashin samunta a waya..ba wai bai samun wayan nata bane aah yana shiga dauka ne kawai batayi wanda baisan dalilin haka ba..duk iya dauriyarshi kasa cigaba yayi sbd yanda take neman ta tarwatsa mashi dan farin cikin daya samu yanxu a dalilin aurenta da yasan an bashi...daukan wayanshi yayi ya kira waziri sukayi mgn dashi yace shidai yanaso yazo Gombe a gobe sbd ya samu ya ganta..Waziri bai hanashi ba yace babu damuwa yazo ya ganta ko don su fara fahimtar junansu.














Rano✨




Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba... masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
47
Da wuri ya gama shirinshi don ko breakfast bai fitoyi ba saida ya gama..flat din Mummy ya fara shiga ya sameta zaune tana mgn da waziri a waya..karasawa yayi ciki ya zauna kusada ita yana jira ta gama..sun dauki lokaci mai tsayi suna discussing kan mgnr da bai fahimci inda ya dosa ba kafin su gama..Mummy na ajiye wayanta ta jiya tana dubanshi tace"so ka gama shiryawa?.."yace"na gama Mummy..Nur kadai nake jira"...Mummy ta mike tace"to muje kayi breakfast kafin Nur din ya karaso"..mikewa yayi ya matairaice yace"Mummy am not hungry plss..kinsan idan zanyi tafia ba son cin abinci nake ba"..hannunshi ta kama zasu fita daga dakin tace"ko tea ne sai kasha in ba haka ba kuma u will not step out if this house"..bai sake yi mata musu ba yabita har dinning..aunty sumy itama daidai lokacin ta fito don da wuri zata fita aiki...su Miemie ne bai gani ba ya tambaya Mummy ta wani hade rai tace sun tafi gidan kakarsu..baice komai ba sbd yanda yaga ta hade rai..batasan ko bata hade rai ba ba mgn zaiyi ba sbd shima yanxu na gabanshi ya isheshi..Allah Allah yake ya ganshi a gaban yarinyar nan yaji dalilinta na ignoring calls dinshi..koma me zatayi dai daga baya ne tunda an rigada an bashi aurenta so duk ihu bayan hari takeyi ya sani..tea Mummy ta hada mashi ya dauka ya shiga sha cikin ranshi yana tunanin yanda zasu kwashe da ita...kafin ya gama sha Nur ya iso gidan dan haka ya mike da sauri bayan ya ajiye mug dake hannunshi yana duban Mummy yace"zamu wuce Mummy..tafiyan akwai nisa"..murmushi kawai Mummy tace"Allah ya kiyaye hanya..ina gaida 'yar tawa"..murmushi yayi tareda fadin"zataji"..snn ya koma zuwa flat dinshi don daukan keys..Nur kuma ya karasa yana gaisawa dasu Mummy..aunty sumy dake cin abincinta tace"wnn abokin naka zalamamme ne wlh..haka ake zuwa zance tun sassafe sbd rashin hakuri"..daria Nur yasa kafin yace"ai aunty kinsan qanin naki halinshi sai shi..ita kanta Lamidon fa wai haushinta yakeji bata daukan mishi waya..so nake muje dai inga iya inda fushin nashi zai kare"..daria itama aunty sumy tayi tana cewa"ai matar Bobby ta shiga uku da masifa..koda yake ita wnn yana sonta bazai iya mata masifan ba kila"..Nur yace"ina ya isa ya mata?..daidai dashi ya samu ai"..daria suka kara saki Mummy dai na jinsu tana murmushi..ita kanta wani lokaci takanyi tunanin yanda Bobby zai kare da matarshi da wnn temper din nashi..saurin hawa gareshi kmr farashi gashi kuma da wuyar sakkowa..amma ta bakin na Nur ta lura yarinyar daidai dashi ce snn kuma uwa uba soyayyan da yake mata wanda bazai barshi yanayi mata anyhow ba..sbd wnn fadan nashi yasa a kullum addu'arta Allah ya bashi macen da yake mutuwar so ba wadda ke mutuwar sonshi ba don idan ya auri macen da baiso matsala za'a samu gagaruma..Allah almusawwir kuma sai ya amsa addu'anta ya bashi wadda sonshi yafi nata..fitowa yayi daga dakinshi yanata baza kamshi..Nur ya kalleshi yana wani kashe ido yace"bakaga kyan da kayi ba wlh..manyan kaya na suiting dinka and da wnn wankan nasan dole Lamido ta ajiye ego dinta ta bada kai don zata fahimci kai din fa ba kmr kowa bane"..harara Bobby ya watsa mashi baice komai ba..yana karasowa yayima Mummy da aunty sumy sallama snn ya juya ya fita Nur yabi bayanshi yana kunshe daria...driver na ganin su ya karaso suka gaisa Bobby ya bashi key din motar da zasu fita yana sake trying number dinta bata dauka ba..driver ya kawo motar inda suke snn suka bude suka shiga shi kuma ya tayar da ita suka fita already dama ya sanar dashi cewa Gombe zai kaisu...ko a hanya saida ya sake trying number still no answer sbd tsabar haushi baisan sanda ya wurga wayan nan gefenshi yana fadin"to hell with you"..juyawa Nur yayi yana kallonshi then back to wayarshi dake yashe a tsakiyarsu...hannu yakai zai dauki wayan Bobby yayi saurin daukan kayarshi shima yace mishi"fuck you"..Nur ya kwashe da daria hadda kyakyatawa...Bobby ya kulu iya kuluwa amma baice komai ba..gaban driver dinshi zai dinga mashi irin wnn iskancin?..zaiyi maganin Nur wlh...bai sake ce mishi komai ba har shima ya gaji da daria don kanshi ya bari daga karshe ma baccinshi yayi hankali kwance..a kufule Bobby ke kallon yanda ya wani yi bacci a mota kmr karamin yaro..shiko tunanin dake ranshi ma bazai iya barinshi baccin ba..gani yake kaman ba tafia suke ba don Gomben yaga tayi nisa sosai baisan ko don sbd matsuwar da yayi ya hadu da ita bane...haka yayita sake sake har suka shigo Gombe around 11:45..saida ya fara zuwa suka gaisa da waziri snn suka wuce estate dinsu...suna zuwa bakin gate gabanshi ya fara faduwa da baisan dalilinshi ba...gidan Lamido suka sauka kmr yanda waziri yace daga nan kuma Lamido yasa aka rakasu har kofar gidansu..tun jiya da waziri ya sanar dashi zaizo dama yasa da sassafe akaje aka daukota

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login