Showing 63001 words to 66000 words out of 231169 words
batayi ba ta banka cikin office din itama tabita da sauri...tana shigowa secretary din itama ta shigo da surinta...Bobby dake zaune seat dinshi ya daga idanu yana kallonsu..ganin yanda kowacce ke huci yace"bakuda hankali ne?..why zaku shigomin office kai tsaye haka without my permission?.."da sauri secretary dinshi tace"Sir cewa nayi ta jira in fada maka idan kace ta shiga sai ta shigo shine taki tsayawa ta shigo ciki"..juyawa yayi yana kallon Aysha data wani hade rai yace"kan wane dalili zaki shigomin office kai tsaye?..are u mad?.."sake daure fuska tayi tana turo baki tace"raina min hankali zatayi shine kawai na shigo"...tsaki ya saki tareda juyawa ga secretary dinshi yace mata"u can leave"...ba musu ta juya ta fita daga office din...shi kuma ya maida dubanshi gareta fuskanshi cunkus yace"wato ke bazakiyi hankali ba kou?..duk wani abu da bai kamata ba bazaki dena yi ba kou?.."turo baki ta sakeyi tace"Sir ni me nayi?.."kallonta kawai yake yace"oh tambayana ma kike?..to bari na kira mahaifinki na sanar dashi shi sai kiyi masa bayani"...ai tun kafin ya karasa ta karasa kusa dashi da sauri tace"aa dan Allah kayi ban karawa"..harara ya watsa mata bai sake cewa komai ba...ita kuma taja kujera zata zauna yayi saurin katseta da fadin"who asked u to sit?.."ta wani marairaice tace"Sir dan Allah..daddy ne yace in hadaku a waya"...still bai sake cewa komai ba ita kuma ta zauna snn ta fiddo wayanta tayi dialing number daddy...yana fara ringing tasa a speaker snn ta mika mishi...ya kar6a ya wani 6alla mata harara tareda cirewa daga speaker snn yakai kunnenshi..tana ganin yanda har wani sunkuyar dakai yake yayinda suke gaisawa da daddyn...ta lura he have so much respect for him and hakan ko kadan bai burgeta ba don gani take duk ladabin kura ne...saida suka kammala wayan snn ya mika mata abarta yana hararanta yace"wato ce masa kikai kina zuwa gaisheni koh.."sake turo baki tayi tace"ai daga yanxu zan fara zuwa"...ya wani ta6e baki yace"kiyi zamanki bana bukata..now tashi ki bar min office"...mikewa tayi ta sake hade rai fa fita cikin ranta tana ayyana shegen son office inda kasan kanshi aka fara zaman office...komai sai ya wani ce office din,my office sai kace wani yace ba office dinshi bane...batafi 10 mins da fita ba Nur ya shigo office din...ya karasa ciki ya zauna yana duban abokin nashi yace"maza yane?.."Bobby yace"normal..kwana biyu..ya aikin"..yace"aiki fine yanxu ma mgnrshi ne ya kawoni"...Bobby yace"umhum inajinka"..."kan batun Festivities din nan ne"...gyara zama Bobby yayi before saying"ina sane dashi ai..next week za'a fara kou?.."Nur yace"yea and yanxun nayi receiving message daga social department that suna buqatar additional money for the preparations"...buda hannu Bobby yayi yace"then ka basu mana"...Nur yace"dama in fara mgn da kai ne..if kace a basu sai a basu"...wani kallo Bobby ya shiga binshi dashi kafin yace"seriously?..haka ka daukeni dama?..kenan har yanxun ban wuce wnn matsayin a wurinka ba?.."shafa kai Nur yayi yace"sam ba haka bane..kawai dai naga bai kamata in fara amsan kudi without permission dinka ba"..yana rufe baki Bobby yace"gaskia bakayi min adalci ba idan har yanxu baka bar irin wnn tunanin ba..now tashi ka bar min office"...dan murmushi Nur ya saki saying"abun hadda kora kuma?.."Bobby yace"yes tunda baka daukeni bakin komai ba ai banga amfanin zamanka nan ba so kindly leave"..gyara zama Nur yayi hade da fadin"to kayi hakuri ya wuce"...harara ya sake 6alla mishi shi kuma yasa daria yace"da gaske bazan karaba mana..sorry".
Ranan Friday akayi pasting result dinsu na first semester wurin ya cika fam da jama'a kowa na kokarin duba nashi wanda sukayi passing mata murna while masu resitting suna jimami...Aysha dai na kwance a hostel dan ko fitowa batayi ba sai Billy ce tayi kokarin duba musu da taimakon Sa'eed sbd turereniya akeyi sosai a wurin...bayan ta samu fitowa daga hayaniyar ta samu waje ta zauna tareda dialing number dinta...cikin muryan bacci ta daga da fadin"Hello"..Billy tace"so u are still sleeping"..tace"eh mana ban dade ma da kwanciya ba"...cikin excitement Billy tace"anyi pasting results yanxun nan and gues what?.."a hankali tace mata"what?.."da sauri Billy tace"as usual ke kikayi overall..and this time around bestynki ma yayi abun kirki"...daria ta saki dukda baccin dake idonta tace"kema dai kinsan my besty is always intelligent kece dai kawai baki ganin haka"...ta6e baki Billy tace"oho ku kuka sani..am hanging up now"..da sauri Aysha tace"wait..baki fadamin naki ba ai"...wani murmushin Billy ta saki kafin tace"congratulations to me..inada 4.55"..tun kafin ta rufe baki Aysha ta saki wani ihu tana fadin"are u serious Billy?..gaskia am very happy bari in kira besty this calls for celebration"...murmushi Billy ta kara saki tana jin yanda take farin ciki ko nata result din bataima wnn murnan ba koda yake idan da sabo ai ya kamata abun ya zaman mata jiki dan tun shigowarsu college din bata ta6a scoring below 5 points ba...kafin ma ta jira jin ta bakinta tayi hanging kiran and for sure tasan bestyn nata zata kira kamar yanda ta fada.
Bobby da bai samu shigowa college din da wuri ba sai after jumu'at prayer motanshi na shigowa ya hangi crowd din dake wajen sai ya tuna ashefa Nur ya fada mishi cewa yau zasu kafe result...daga dan gaban inda aka kafe result din ya hango katon banner da suke kafewa duk shekara na best students of the year kowa da grade dinshi da department sai kuma picture dinshi a jiki...driver bai karasa inda ya kamata yayi parking ba yace ya saukeshi nan wurin..ba musu yayi parking daga gefe kafin ma yazo bude mishi kofan ya bude ya fita...inda aka manna babban banner ya nufa...haka nan yaji yanason ganin da akwaita a jiki ko babu...aikam yana karasa yayi ido biyu da pic dinta tana sanye da uniform da glasses dinta a ido...qasan pic din nata ya kalla baisan time daya wara idanu yana sake kallon points din nata ba...gani yake kaman karya ne bazata iya scoring wnn points din on her own ba...hoton su biyu ne kadai a jikin banner daga ita sai Sa'eed da yayi overall a Nursing department...dukda baisan yaron ba amma ya jinjina mashi sosai dan points ba kadan ba shima yakeda...ita kuwa nata har yanxun bai gama yadda ita taciyoshi da kanta ba...bayan ya gama kallon ya shiga takawa a nutse zuwa office dinshi saidai kafin yakai office din kusan mutum uku sukazo suna gaisawa dashi snn suka nufi office din tare...deep down wani irin feeling yakeji...like gaba daya sai baiji dadin ganinta da yayi jikin banner ba...not because yana mata bakin ciki but because yana ganin yin hakan kaman talla ne akeyi da 'ya'yan mutane tunda yasan yanxu duk wanda ya shigo college din sai ya gani and hakan will make her popular da bai zama lallai parent inta su so haka ba..especially ita da dama ba wani cikakken nutsuwa gareta ba...ya fuskanci kanta na rawa shiyasa ko mahaifinta baya sassauta mata...har ya isa office dinshi bai bar tunanin ba and yanaso yayi ma Nur mgnr kuma yanajin tsoro kar yazo yayi misquoting dinshi amma seriously baiji dadi ba sam...sai yakejin kaman yaje ya yageta daga wurin amma ba hali...hakura yayi da yima Nur mgnr saidai ya kudirce a rai kafin next year zai samu yayi mgn dashi kawai a hakura da banner ma gaba daya...sam baiga amfanin yin hakan ba...dukda ba yanxu aka fara ba amma wnn karon kam abun baiyi mashi dadi ba.
Shirye shirye sukeyi sosai for the upcoming Annual Festival da ake gabatarwa cikin college din every year...shiri ba daga 6angaren students ba ba kuma daga 6angaren social department ba...week guda suke cinyewa suna abu guda and wnn year din ma kaman ko wacce shekara sun gama tsara duk yanda festivities din zasu kasance...ranan farko daya kama Monday zasu gabatar da dramas da wasu daga cikin students din zasu gabatar..da akwai English drama sai Hausa drama...rana na biyu kuma zasuyi cultural activities rana na uku ne ake inviting mawaqa daban daban suzo suyi performing a wurin sai rana na hudu wich is Thursday zasuyi Public Lecture and Fun Walk ma'ana za'ayi picking one among cututtuka da suke damun mutane a wnn lokacin sai daga cikin doctors da ake inviting zuwa wurin suyi fashin baqi akan cutan bayan an gama sai su fita fun walk dasu police bands da masu dj suna tafe suna waqa da rawa zasubi ta cikin gari har zuwa state road snn su dawo college din a qafa...ranan Friday wich is the last day of the festival sukeyin sport activities such football,volley ball,table tennis,snooker,basket ball dama sauran wasanni na maza dana mata.
Ranan Monday wich is the first day if the festival wurin 10 na safe auditorium dinsu na cike da students,doctors da kuma manya manyan baqi from every angle na kano da akayi inviting dinsu...kowa yana zaune a respective wurin da aka tanadar musu...mike na hannun mc yanata welcoming baqi tareda sanarwa cewan a jira wanda zasu gabatar da drama zasu bayyana in few minutes time...daga can waje masu yin draman ne a tsatsaye suna mgn da wani daga cikin organizers na festivals din...ba anko sukayi ba amma kowa cikin yayi kyau in his own way...saida ya gama musu karin bayani kan abunda zasuyi snn yace su shiga audit din...suka jera kansu a layi snn dj yasa musu waqa suka fara shiga wurin...Aysha na tsaye a gaba tana rikeda katon sign board da aka rubuta day 1 English and Hausa Drama...suna shigowa wurin ya kaure da sowa da tafi kowa sun burgeshi...Dr.Bobby dake zaune inda aka tanada domin shi a hankali ya dago idanunshi ya kallesu...as always idanunshi ita suka fara hango mishi...tana sanye cikin riga da straight skirt na atampa red da touches din black leaves a jiki...ta daura dankwalinta irin daurin da ake cewa Zara Buhari ta fito da gashinta ta qasan daurin snn ta kalmasheshi ya tsaya a wuyanta...daga bayan skirt din nata an dan tsagashi kadan ta kasa sbd yayi mata dadin tafia...takalmin kafanta flat ne sosai black sai veil dinta da tasa a kafadanta shima black...sai wrist watch da dankunnenta suma black...batasa sarqa ba dan haka fair wuyanta yana nan sai daukan ido yake...a hankali take takawa tana rikeda sign board a hannunta sai murmushi take dimples dinta na fitowa...wani irin abu yaji ya taso tun daga kwakwalwarshi yazo ya tokare mishi maqogaro shi bai tafi ba kuma shi matsa ya bashi sararin maqogaron ba...tunda yake bai ta6a tsintar kanshi cikin 6acin rai irin wnn ba..har wani zafi yaji yana rufeshi duk kuwa da sanyin ac dake wurin...lokaci daya kanshi yayi wani mugun sarawa kaman zai tarwatse..har yanxun kuma ya kasa dauke idonshi daga gareta har suka karasa suka zauna...lumshe idanunshi yayi yana karanta innalillahi a cikin ranshi wai ko zai samu sassauci...kai tsaye kuma yace ga abunda ke damunshi bazai iya ba dan shi kanshi bazaice ga dalilin wnn sudden change din nashi ba...sam baisan yaya zai misaltashi ba...kokari yayi sosai yayi kokarin danne abunda ke taso mishi ganin har za'a fara taron...yana kallo aka fara kiran sunan wanda zasuyi draman kawai ya runtse ido yana addu'a Allah yasa babu ita a ciki saidai kamar jiran addu'an nashi akeyi yaji mc na kiran "Aisha Ahmad Lamido"...sake runste idanun yayi yanajin wnn kuncin da yaketa kokarin 6oyewa yana sake neman hanyar dazai fito amma bai bashi dama ba dan kara dakewa yayi sosai wnn karon har yana dan muzurai snn ya bude idon...baisan ko shi yake kai idanunshi gareta ko kuma idanun ne ke kai kansu gareta ba dan yanxun ma ita ya sake gani bayan ya bude idon...karasawa sukayi suka zauna inda aka tanada domin yin draman...acting zasuyi itada Sa'eed matsayin mata da miji Billy kuma kishiyarta a cikin sauran kuma akwai yara snn akwai set of another couple da dai sauransu...cikin kwarewa da nutsuwa suka fara gabatar da draman nasu na English knn...wurin sai yayi tsit banda voices dinsu ba abunda akeji...gaba daya sun saki jiki suna acting dinsu sosai dan babu wanda zai gani yayi tunanin ba gaske bane sai wanda ya sani...dama kuma sunyi rehearsal sosai shiyasa basu samu wani problem ba...Bobby kuwa tunda yake bai ta6a sanin da akwai kunchi irin wnn yakeji a yanxu ba...kallon yanda suke acting itada Sa'eed kadai yasa yaji kaman zazzabi na neman kamashi...baisan meyasa yake feeling what he's feeling ba...baisan why zai damu da rayuwar yarinyar nan ba..."sbd amanarta da mahaifinta ya baka"..cewar wani sashe na zuciyarshi...babu wata wata kuwa yayi na'am da wnn amsa don yasan da gaske kuwa ba abunda ya hadashi da ita bayan wnn...da wnn amsa na zuciyarshi ya dan samu sauki kadan daga cikin abubuwanda ke damunshi...haka yacigaba da daurewa yana kallonsu har wani murmushin yake yakeyi sbd kar mutane su dago halin da yake ciki...draman nasu ya dauki kusan one hour kafin su gama...wanda zasu gabatar da na Hausa akace su zama ready kafin mc yacigaba da surutanshi...sauran kuwa tafi aka shigayi musu sosai dan ba wanda basu qayatar ba a wurin Bobby kam shi kadai yasan halinda yake ciki...bayan lokaci mai tsayi masu draman Hausa suka shigo and to his biggest suprise wnn karon ma da ita a ciki...lokaci guda face dinshi ya sauya yana kokarin mance jarumtar da yace zai nuna...wnn karon kuma matsayin budurwar wani ta fito hakan kuma ya 6ata masa rai fiyeda tunaninshi...haka nan ya sake daurewa ya kalla har suka gama amma fa kafin a gama ya saki tsaki yafi cikin carbi...6acin ranshi kuwa ya ninka na dazu ninki ba ninki...gaba daya yaji zaman wurin ya gallabeshi burinshi kawai a tashi ya samu yarinyar can ya zabga mata rashin mutunchi...kwata kwata baisan dalilinda yasa bayason ganinta cikin irin wadan nan abubuwan ba...bayan sun gama masu jawabi duk suka tayi sukayi kayansu...wanda zasu bada kyauta ma duk suka bayar and Lamido na daya daga cikin wanda suka samu kyautar 50k da wani attajirin mutumi ya bayar...ran Bobby idan sun kai dubu duk a 6ace suke...ji yake inama yanada hali ya kar6e kudin daga hannunta gaba daya sai yaga ta gidan uban da zatayi amfani dashi dan yaga sai wani fara'a take tana jujjuya ido ita bata yadda ba celebrity...InShot har aka tashi daga wajen Bobby baisan ina kanshi yakeba...a zafafe ya koma office dinshi ya dauki waya da niyyan kiran secretary dinshi tasa a nemo mashi ita nan take kuma wani tunani yazo masa..."to idan na kirta ince mata me?.."ya fada a fili kaman he's talking to someone...nan take kuma ya shiga girgiza kai yana fadin"no yanxu idan na fadi wani mgn tana iya misquoting dina ma tunda ba hankali gareta ba"...ya sake fadama kanshi...can kuma yace"amma ai sbd babanta zanyi hakan kou?.."yayi shiru kaman yana sauraran amsan da zuciyarshi zai bashi kafin yace"No I won't talk to her...wai ma ina ruwana da ita taje taita haukanta mana is not as if i care"...ya fada yana daddaure face dinshi kaman tana zaune nan kusa dashi...da wnn shawara yayi amfani don bai kiratan ba a cewarshi wai baison raini...haka yayi dakon bakin cikin daya kwasa ya kaishi gida su Mummy sukaita aikin fama.😹
The next day kasa fitama yayi da wuri sbd tunanin abunda zuwan nashi zai haifar...yadai san a yanda take da shegen rawar kai yanda tayi performing a komai na jiya yau din ma zaiyi wahala idan batayi performing ba..shi kuma baisan meyasa yakejin abunda yakeji ba and Allah ya sani bazai iya kiranta ya hanata ba sbd kar tayi tunanin wani abun daban...da yanada ikon hana kanshi jin abunda yakeji da ya aikata hakan wlh ko don ya samawa kanshi salama amma bayada damar hakan...wnn dalilin yasa bai samu fitowa ba har saida yaga Nur ya fara kiranshi a waya and yasannshi da shegen naci haka zaiyita jera mishi kira idan har ba fitan yayi ba.
Wani daki ne kusada auditorium dinsu inda daya wanda zasuyi performing suke ciki kowa yana karasa shiryawa...cultural dance suka shirya na Hausa,Fulani,igbo da kuma yoruba...and kowa daga cikinsu yana sanye cikin traditional attire na tribe da zaiyi representing...Lamido sarkin rawa zatay participating kusan gaba daya sbd ita koya musu rawar...da farko cewa tayi only Fulani da Yoruba zatayi sai hod na social department dinsu yace tayi participating gaba daya...Hausa Dance shine na farko dan haka koda mc ya kira iya wanda zasuyi hausa dance din ne suka fita daga dakin...as usual itace a gaba tana rikeda sign board kaman najiya saidai shi an rubuta day 2 cultural activities...wata kuma daga cikinsu ta rike wani da aka rubuta Hausa Dancers a jiki...waqa aka sakar musu ta hausa mai dadi yayinda suke shigowa cikin wurin...gaba dayansu suna sanye cikin normal dogon riga na atamparsu iri daya kowacce ta daura dankwalinta babu mai mayafai cikinsu...bayan sun karasa dance floor sun tsaya dj ya samo waqar hausa ta gargajiya yayi playing snn suka fara dancing...yau ma Bobby yana zaune mazauninshi na jiya and gaba daya tunda ya dora idonshi a kanta ya samu gagarumar matsala don komai nashi tsayawa yayi cak banda zafi ba abunda yakeji har cikin heart dinshi...lumshe idanunshi yayi yana salati dan abunda yake jin yaji jiya was nothing compared to what he is feeling right now...ji yake kaman yaje ya dauketa ya fita da ita daga wirin...haka nan yakejin ciwon kallon da mutanen wurin zasuyi mata tana rawa kamar batasan ciwon kanta ba.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
22
Ranshi bai sake 6aci ba saida yaji yanda gaba daya wurin ya kaure da tafi da sowa ana hailing dinsu..nan take yaji wani abu yazo ya tokare masa wuya...abun bai tsaya haka ba har liki mutanen da akayi inviting suka fara tasowa suna musu...bayan sun gama aka kara tafa musu sosai snn suka fita mc yacigaba da zance kafin next dancers su fito...dakin da suka shirya suka koma nan kuma suka fara arranging next dancers da zasu fita wato Yoruba Dancers...Lamido ce kadai tayi changing dress dinta zuwa na yoruba snn ta shiga cikin sauran suka koma ciki...suma dai da tafi da sowa akayi welcoming dinsu...Dr.Bobby yana zaune sam baiyi mamakin ganinta ba dan yasan dama hakan zai faru saidai bai saniba ko zai iya cigaba da jure abunda yakeji har su gama...yau dai ya rantse