Showing 69001 words to 72000 words out of 231169 words

Chapter 24 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9690

kuma tana baya dan cewa tayi bazata jera dasu ba...ganinshi tsaye a wurin ta sake dinke fuskanta tsaf tana cigaba da tafiya kaman batasan suna wajen ba...kafin ta wuce Nur ya kira sunanta"Lamido"...a hankali ta juya tana kallonshi with a little smile kan face dinta tace"Sir good afternoon"..yace"afternoon ya gajia"...murmushi kawai tayi batace komai ba...Miemie da a kallon farko taji ta burgeta sbd kyanta itama ta gaisheta..Aysha ta amsa ta murmushi tana mamkin inda provost ya samo yarinyar me kyau haka...so tayi ta wuce batareda ta gaishe da Bobby ba amma sai taga bai dace ba kuma yana iya hadata da daddy dan haka ta dan juya tana kallonshi a kaikaice fuskan nan ba fus tace"ina yini"...ko kallon inda take baiyi ba balle ya amsa mata...ita kuma jin yayi shiru ta daga ido sai taga wayanshi ma yake dannawa aikuwa ta daddage ta murguda masa baki sai kuma karaf a idanunshi...idanunta na sauka cikin nashi tayi kasa da nata da sauri...kallonta yayi for like 2 minutes snn ya dauke kai...ita kuma juyawa tayi zata tafi Ilham da har yanxu ke rikeda hannunshi tace"Ehihie Oma"...juyawa Bobby yayi yana kallonta da mamaki jin tayi mata igbo..kafin yayi mgn Aysha data juyo itama tana kallonta with smile tace"hey I don't understand igbo...how are u"..ilham ta saki murmushi tace"am fine"...Aysha ta gyada kai dan yarinyar sosai ta burgeta sai ta ganta kaman Yusra don itama akwai surutu...tace"ya sunanki?.."da sauri ilham tace"sunana Nadia amma ilham ake cemin..mamana kuma sunanta Sumayya muna cemata aunty...wancan kuma sunan..."bata karasa ba Bobby ya toshe mata baki yana hararanta yace"and who asked u all these?.."turo baki tayi tace"Uncle Bobby let me finishi plss"...bai bari ta sake mgn ba ya kama hannunta suka bar wajen...Aysha ta bisu da kallo tana hararan bayanshi kaman idanun zasu fado...tsaki taja tacigaba da tafia itama...tana shiga inda hall din yake kafin ta karasa Bobby dake tsaye yana jiran shigowanta yace"come here"...juyawa tayi a tsorace tana kallonshi don batasan da mutum ba a wurin...ya wani hade rai yace"bazaki zoba?.."turo baki tayi ta wuce inda yake...tana karasawa ta rungume hanu tana ciccin magani and hakan bai dameshi ba ya nuna gashinta dake a waje fuska babu alamun wasa yace"maida wnn gashin da kika fito dashi"...dagowa tayi ta kalleshi hawaye har sun ciko idonta sbd haushi...har yanxu idan ta tuna batada daman yin rawa a wurin nan sai taji kaman ta shakeshi ya mutu...ganin yana mata wnn kallon da bata so takai hannu ta tura gashin nata ciki...ya bita da wani irin kallon kafin yace"now leave"...ba misu ta juya ta tafi daga wurin hawayen dake cikin idonta na gangarowa kasa...shima ya kama hannun ilham zasu shiga saiga Miemie da Nur sun shigo...Nur ya kalleshi da mamaki yace"wai dama baka shiga ba?..meka tsaya yi a nan toh?.."banza yayi dashi yaja ilham suka shiga ciki...shima shiga cikin sukayi yana mamakin abunda ya tsaidashi a waje bayan tun daxu ya shigo.














Rano✨





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
23
Suna nan zaune daya daga cikin mawaqan da sukazo ya fara performance dinshi...hajia Aysha na zaune tana kallo kaman tayi kuka...yana kammalawa favorite din nata ya shigo tareda ganguna da 'yan rawarshi aikuwa gaba daya hall din ya rude da sowa da tafi...kaman yasan halinda take ciki saida ya samo favorite dinta a cikin waqoqinshi nashi ma snn akayi playing ya fara miming...nan take hall din ya sake rudewa da muryan mata duk suna bin waqar wasu kuma suna zuwa suna mishi liki...itadai tana daga gaba gaba tana kallonsu tanajin ciwon da bata isa ko dan liki taje tayi ba...tana kallon su Billy sukaje sukayi liki snn suka dan taka rawa suka fito...hawaye taji suna ciko mata ido kawai saita rufe fuska da hannayenta tana kokarin mayar da hawayen...Bobby da tun daxun hankalinshi ke kanta daga inda yake yana ganin yanda ta rufe fuska fuska ya wani ta6e baki cikin ranshi yace"ko kukan jini zakiyi bazakiyi rawa a wurin nan ba wlh"...ita kuwa bata ma san yanayi ba saida ta gama goge tears din snn ta bude fuska...daga karshe ma mikewa tayi ta fita a wurin don bataga amfanin zamanta ba...duk akan idon Bobby da kona one second bai dauke idonshi kanta ba sbd yasan tsaf zata iya fakar idonshi ta shige cikin 'yan rawa idan taga baya kallonta...can waje ta fita ta samu wuri tayi zamanta tana jera masa Allah ya isa a cikin ranta kmr daga sama taji sallaman mutum a kanta..idonta ta lumshe tasan yanxu zuwa zaiyi ya kara mata kan abunda take ciki dan ko ba'a ba tasan shine...muryan kadai taji ta gane Sir Abdool ne...kallon yanda ta kulle idanu yake kafin a hankali yace"may i?.."kai ta gyada mishi ba tareda ta bude idon ba...zama yayi nan kusada ita yana sake kafa mata eyes dinshi yace"Lamido wai bakida tausayi dama?..ace duk tsahon lokacin nan inata faman baki hakuri amma kinki hakura"...bude idon tayi tana dan turo lips dinta tace"Sir nifa ba fushi nakeyi dakai ba"...tana rufe baki yace"idan ba fushi kikeyi dani ba meye wnn toh?..meyasa har yanxun bakya picking calls dina?.."dan juyawa tayi tana kallonshi tadan marairaice tace"da gaske ba fushi nakeyi ba"...yace"then fadamin idan sona ne bakyayi I won't force you"...sake narkewa tayi tana dubanshi tace"inada wanda zan aura ne"...hannu yakai ya dafe chest dinshi tared runste ido yace"that hurts"...a hankali tace"am sorry"...bude idon yayi yana kakalo murmushi yace mata"as i have said I won't force u to love me and congratulations to the lucky guy"...dan murmushi kawai tayi batace komai ba..she's happy yayi understanding dinta...muryanshi taji yana cewa"but akwai alfarma da zan nema wurinki"...tana gyada kanta tace mishi"inaji"..yace"if I can't be ur lover at least i will be glad to be ur friend"...bright smile ta saki tana dubanshi tace"then we're friends"...murmushin shima ya saki yace"yes we're friends..thanks for accepting my offer"...daria kawai takeyi tana kallonshi..taji dadin yanda ya fahimce ta har hakan yaso yawa ta manta baqin ciki hanata rawa da akayi...shima darian yakeyi yana kallonta deep down yanajin ciwon rashin samun soyayyanta amma ya ya ita tunda bata sonshi?..kaman ance ta daga ido sukayi ido hudu da Bobby daya wani hade rai yana binta da tsinannen kallon nan bata qauna...darian da takeyi ya tsaya cak itama ta hade rai tareda dauke idonta daga gareshi...shi kuma wucewa yayi zuwa office dinshi yanajin haushin yanda heart dinshi ke neman deceiving dinshi yana sashi jin abunda sam bai kamata ace yajishi akan jinin Fulani ba.

A takaice ranar haka aka tashi taron nan batayi rawa ba sbd tsoron kar ya fadawa daddy...haka suka koma hostel itada Billy tanata ciccin magani Billy batabi ta kanta ba ta shiga sabagar gabanta...sai dare da babynta yazo snn ta dan samu nutsuwa dan bai bar hostel dinba saida ya tabbata yayi flushing away wnn damuwan da take ciki.

The next day around 10 suka fita sbd da wuri ake fara lecture din...dress code dinsu na ranan white ne dan basuyi anko ba saidai ance everybody should wear white cloth...itada Billy black straight skirt suka saka da farar shirt sai farin kimono da suka dora akan kayan itama white da digi digon black a jiki suka yafa black veil...ita Billy tasa turban snn tayi veiling da mayafin while hajia indo batasa komai ba sai dan mayafin data yafa akanta...daidai sa bags da suka rike iri daya ne suma duk farare...suna shigowa cikin school kiran Husna ya shigo wayan Billy nan ta dubi Aysha da sauri tace"Lamido ina tunanin su Hamma fasun karaso kinga Husna na kirana"...Aysha tace"to mu karasa parking space muga ko suna can"..daga haka suka wuce zuwa parking lots din...tun daga nesa suka hango motanshi dan haka suka nufi inda take...Hamman nasu ya shiga binsu da kallo yana murmushi yace"lallai ashe gayunku kawai kukeyi a makarantan bamu saniba"..Aysha tace"kai Hamma meya wani gayu a nan"..yana kallon Billy yace"gayu ne mana..dan bakiga yanda kukayi kyau bane"...kafin Aysha tayi mgn Husna tace"Hamma mudai dan Allah mu karasa ciki kar a fara abun arzikin bamu shiga ba..nasan anjima nayi zaka fara cewa azo a tafi daddy yace kar ayi dare"...murmushi kawai yayi gamida girgiza kai snn suka dunguma zuwa hall din...da yake yau kusan kowa yana inviting family ko friends dinshi sai hall din ya cika yayi taf fiyeda sauran ranakun...wuri suka samu suka zazzauna daga gaba gaba yanda za'ayi komai akan idonsu snn suka cigaba da kwasan hira kaman sun shekara basu hadu ba...suna nan zaune gab da za'a fara Sa'eed shima ya shigo tareda lubna aikam suna ganinta suka mike zuwa inda take sukayi hugging dinta..shi kuma Sa'eed ya karas shna gaisawa da Hamma dasu Husna...bayan sun gama rungume rungumensu suka karasa suma suka zauna Lubna nata jadda musu sai sunzo kd bikinta nanda few weeks sukace zasuje inshaAllah...saida kowa ya gama shiga snn Proprietor,Provost da kuma manya manyan doctors da zasu gabatar da lecture suka fara shigowa...duk yawan jama'an dake wurin baisan meyasa idanunshi suka hango mishi ita zaune a tsakiyar wasu maza ba...ranshi yaji ya 6aci sosai yanxun duk space dake cikin hall din nan ta rasa inda zata zauna sai ta shiga cikin maza?..wai wace irin yarinyace ne wnn?..wane irin shegen rashin hankali gareta?..har suka isa high table da aka tanada dominsu suka zauna bai denajin ciwo ba...sai a lokacin Aunty Sumy dasu Miemie suka karaso...Nur ne ya amsa mike daga hannun mc yayi welcoming guests dinsu snn ya gabatar da sunan disease da za'ayi lecture a kanshi Sickle Cell Anaemia wanda akafi sani da Sickler...tafi wurin ya dauka kowa yana ganin dacewar gabatar da lecture akan Sickler sbd yanda masu ciwo irinshi suke facing challenges a rayuwarsu na yau da kullum...bayan hall din ya danyi tsit ya dora da fadin"and before i hand over the mike to our qualified doctor Olusola Bulus...i will like to invite Aisha Ahmad Lamido for a brief introduction of Sickle Cell Anaemia"...fuska daure Bobby ke kallon abokin nashi ko meye ma'anar hakan da yayi oho?..meye amfanin wani kiranta tayi bayani tunda ga doctor zaiyi lecture a barshi ya gabatar da abunshi mana...Aysha da taji sunanta unexpected kasa mikewa tayi daga inda take zaune...Hammanta ne ya sunkuya yayi mata mgn a kunnenta kan idon Bobby da idanunshi ke wurin...a hankali ta mike daga inda ta fito zuwa kan stage...tana isa ya ba ta mike dake hannunshi ta amsa ta fara da gaishe da manyan baqi da colleagues dinta dake wurin snn ta shiga yi musu brief introduction ko ince explanation na Sickle Cell Anaemi kaman yanda aka bukaceta...ta burge mutane da dama a wurin domin tun daga kan yanda take mgn with courage and confidence zaka san ba karamar mai kwanya bace...uwa uba kuma dressing dinta daya sake fito da ainihin kyawunta hatta yanda take mgn ma abun kallo ne...hall din yayi wani irin tsit ko tari babu sai sweek voice dinta dake tashi ta cikin speakers...bata shiga deep ba ta tsaya iya introduction kmr yanda akace tayi snn ta sake miqawa Nur mike din ta sauka daga wurin..tafi sosai aka shiga yi mata hatta doctors dake wurin saida suka jinjina mata dan tayi kokari sosai ba kadan ba...tana karasawa inda take Hammanta ya mika mata hannu suka tafa and again kan idanun Dr.Bobby da yabita da wani hadadden harara data sauka daga stage...kawai haushi yakeji and ya rasa dalili...gaba daya mutanen wurin ma haushinsu yaji yanaji for clapping mata da sukayi ballantana kuma Nur dashine wanda ya haddasa komai...aunty sumy dake zaune daga dan gaba itama kallonshi kawai take tana mamakin abunda aka mashi yake wnn cin kunu haka...ta lura ko noticing zuwansu ma baiyi ba hankalinshi na can wurinda batasan me yake kallo ba...text tayi typing a wayanta"what's wrong?..why are u frowning ur face?.."ta tura mashi...wayan na aljihunshi yanajin shigowan text bai duba ba..ta sake tura mashi"Bobbyyyy"...zaro wayan yayi cikeda haushin damunshi da akeyi zaisa a flight mode idonshi ya sauka kan sunanshi data kira...sender ya duba yaga itace sai ya bude message din da sauri shi sam ya mance sunyi mgn daxu tace mishi suna hanya...yana gama karantawa ya daga kai yana duban wurin wai ko zai hangota amma bai ganta ba...text ne ya sake shigowa wayan ya duba sai yaga tace"ba ganinmu zakayi ba kawai ka bar frowning face dinka haka kar guest dinka suyi tunanin wani abu"...ajiyar zuciya ya sauke yana sake wurga idonshi still bai gansu ba dan haka yayi typing"ohk na dena"shima ya tura mata...yana gama tafiya ya maida wayan aljihu yana kokarin daidaita face dinshi kmr yanda tace kar guest dinshi suyi tunanin wani abu...doctor Olusola ne ya fara bayani kan yanda Sickler yake..yanda yara ke samu ta hanyar iyayensu and hanyoyin daya kamata abi don ganin sun zauna cikin koshin lafia...saida ya dauki more than one hour yana abu daya kafin ya gama...bayanshi wani doctor Solomon shima yayi bayani stigmatization da suke fuskanta a society da kuma hanyoyin daya kamata abi don kiyaye wnn stigmatization din and lastly doctor Nuruddeen wato Provost yayi bayani kan hanyoyin da za'abi wajen preventing haihuwan yara masu sickler snn idan an haifesun hanyoyin da za'ayi taking proper care of them tun daga neonatal stage zuwa child har zuwa adolescent...daga nan kuma ya sake mika godia wa duk wanda suka halarci taron a matsayinshi na Provost na FCNM tareda fatan komawa gida lafia...daga nan kuma sai aka hau raba drinks da snacks each table aka ajiye musu nasu snn aka faraci...bayan sun gama Provost ya sake amsan mike yace yanaso su zama ready for the Fun Walk don in the next 10 minutes zasu fita...haka kuwa akayi duk mutane suka fara mikewa suna fita daga hall din...Bobby ma ya taso daga inda yake zuwa inda ya hango su aunty sumy zaune...tun kafin ya karasa Ilham ta mike tana rungumoshi..shi kuma yajata suka karasa wurin yana kokarin dora smile kan face dinshi yace"wai yaushe kukazo?..kinsan banga shigownku ba?.."aunty sumy tace"dama ya zaayi kaga shigowanmu hankalinka na wani wajen..wai mema kake kallo ne kam?..and meya 6ata maka rai da kaketa cin magani haka?.."dan shafa kanshi yayi yace"bafa wanda ya 6atamin rai kawai zaman wajen ne ya isheni..kuma zakuyi walk din ne ko bazakuyi ba"..mikewa aunty sumy tayi hannunta rikeda bag dinta tace"rufamin asiri da wnn tafiyar Bobby..komawa gida zamuyi dama lecture mukazo ji kuma an gama so we are going back home"...gyada kanshi yayi cikin jin dadin tafiyar da zasuyi yace"gara ku koma ai dan wnn walk din wahalar banza ne kawai"..aunty sumy ta wuce suka fara tafia tace"wnn karon ma bazakaje ba knn?.."yace"haba!.Allah ya kiyaye ai bazan iya wnn wahalar ba"..murmushi kawai ta sakeyi batace komai ba...saida ya rakasu har mota yaga sun shiga sun fita daga makarantan snn ya juya zuwa office din Nur don yasan da yawa daga guest din da basu tafi ba suna can...snacks ya samu sunaci da drinks dinsu sunata kwasan hira kaman basu ba...daidai lokacin da ya shiga yaji Gabriel na fadin"ni wlh yarinyar nan cema ta burgeni gaba daya tunda na ganta naji na gagara sukuni...yaya ma sunanta kace?.."yayi referring tambayar to Nur dake sauraronshi yana daria yace"kai wnn yarinyar tafi karfink wlh..Lamido matar manya ce ba yara irinku ba"..daria suka saka Gabriel din na cewa kodai shima Nur sonta yake Nuru yace ai babu mamaki ma idan yana son nata...Bobby dake tsaye jikin kofa yana sauraran conversation din nasu kasa karasawa ciki yayi..haka nan yaji wani irin faduwar gaba dajin abunda Nur ya fada..shi sam mgnr Gabriel bai daukeshi da wani abu kaman na Nur ba..da dadewa dama yana zargin Nur sonta yake and now ya tabbatar da zarginsa..dukda ba fitowa fili yayi ya furta yana sonta ba a iya mgnr daya fada ya fahimci da gaske son nata yakeyi...juyawa yayi ya bar office din yana sakin tsaki a fili ya furta"ko uban me Nur zaiyi da wnn yarinyar oho?.."shidai wlh wnn yarinyar yana ganin ko daura masa ita akayi a kafarsa zai kwance ya wurgar don baiga amfanin auren mace mai shegen rawar kai da kula samari ba..jiya ma ya ganta da Abdool and a yanayin da yaga suna mgn yasan da kyar idan shima ba saurayinta bane..daxun ma ya ganta zaune tsakiyar maza su dinma kuma ba abun mamaki bane idan ance samarinta ne shi kam me zaiyi da mace kaman wnn da take daukan maza kaman 'yan uwanta mata?..a fili ya sake furta"God forbid"..harda tsartar da saliva.😹

Bayan few minutes gaba daya wanda zasuyi walk din suka fita masu police band nata kida haka masu dj sunyi playing music sauran kuma ana tafe ana rawa kowa rikeda banner da akayi rubutu a jiki...dukda tafiyan akwai nisa ba karamin enjoying dinshi sukayi ba don suna tafe suna takawa hadda Aysha data gama dubanta tsaf bataga proprietor a wurin ba...duk inda suka wuce anata kallonsu sbd yawansu haka duk titin da suka hau suke rufeshi gaba daya saidai masu wucewa su nemi wani hanyan...suna tafe sunata daukan pics da videos abundai sai wanda ya gani...haka suka gama zagayensu suka dawo college din a kafa.

Suna shigowa college din can bayan classes dinsu dake nan kmr garden suka wuce kai tsaye suka shimfida manyan carpets a wurin snn suka fiddo abincin da sukazo dashi daga gida suka zazzauna nan sunaci sunata kwasan labari...idan kaga yanda suke hira zakayi zaton duk 'yan uwan juna ne irin wanda suka shaqu da juna sosai...Lubna da Aysha da Billy sunacin nasu tare..Hamma da Sa'eed suma sunacin nasu sai Husna da Yusra...Billy ce kadai ba 'yan uwanta kasancewar ita kadai ce mace a gidansu duk sauran siblings dinta maza ne...bayan sun gama ciye ciyen sai suka fara daukan pictures da videos Aysha nata ma Hammanta da bayason daukan hoto daria...a takaice basu suka bar FCNM ba sai after five...suka rakasu har mota suka tafi snn suka dawo ciki ya rage daga Aysha da Billy sai Sa'eed da Lubna...daga nan ya kwashesu zuwa hostel don Lubna cewa tayi ita sai dare zata koma gidan Hajia..hakan kuwa akayi don bai dawo ya dauketa ba sai around 9 na dare..haka suka rabu sunata zullumi kaman bazasu sake haduwa ba bayan ko gobe tace zata dawo kallon sports da zasuyi.

Washegari Friday basu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login