Showing 99001 words to 102000 words out of 231169 words

Chapter 34 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9701

tsaya including breathe dinshi...nan take face dinshi ya sauka murya a dakile yace"sbd shi kike kuka knn?.."cigaba da kukanta take tace"tafiya fa zaiyi ya barmu...ba sun gama council ba"..a kufule ya mike zuwa inda ya ajiye wayoyinshi yace"sai ki bishi ai"...harara ta watsawa bayanshi tana turo baki...ya dauki wayoyinshi daya ajiye nan wurin snn ya kama hanya zai fita yace mata"fito mu tafi"...da kallo kawai ta bishi tana mamakinshi..har yanxu bata bar mamakin yanda he can change forms in a blink of an eye ba..he can be nice for a second and become annoying the other second...shiyasa kwata kwata bata gane mashi...mikewa tayi ta zura jilbab dinta snn ta fita daga office din..a bakin kofa ta sameshi yana ganin ta fito yayi locking office dinshi snn ya wuce parking space...motanshi ya bude ya shiga itama tana karasowa ta shiga sai turo baki take...bayan sun dauki hanya ta dan saci kallonshi ganin yana driving..tunda suke bata ta6a ganin ya tuka kanshi ba saidai yayi d'urum a baya mota ana driving dinshi yau kuma wane salon ne yasa shi driving din oho?...motan yayi tsit ba abunda kakeji sai sanyin ac dake tashi...wayanshi dake ajiye kan dashboard ne ya fara ringing...yayi connecting Bluetooth snn ya daga..daga daya 6angaren da igbo Mummy tace"Bobby where are u?.."shima da igbo din yace mata"ina kan hanya Mummy..what happened?.."tace"jikin yarinyar nan ne naga kaman gaba yakeyi wlh..ko asibitin zamu kawota?.."yace"aah Mummy gani nan zuwa gidan yanxu"..Mummy tace"to kayi sauri dan Allah"..yace"toh.."snn ta kashe kiran...Lamido data kasa kunne tana jinsu bata fahimci komai a zancen nasu ba tace"kilan mamarshi ce"...yaji abunda ta fada sarai kulata ne kawai baiyi don a yanda ta kular dashi tsaf zai iya kwada mata mari wlh...haka ta ringa baza ido tana kalle kalle har suka iso kafar gidansu...maimakon ya shiga da motar ciki sai yayi parking a nan waje ya bude motar ya fita ya wani sake hade ranshi yace"saura kuma ki fito daga ciki kiga me zanyi maki"...tabe baki tayi ta kauda kai shi kuma ya juya ya nufi gate..kwankwasawa yayi mai gadi na lekowa yaga shine ya bude mishi da sauri ya shige cikin gidan...Lamido na ganin ya shiga ta bude motar ta fito tana karema gidan nasu kallo tace"ai wlh saina fito na bawa idona abinci"..sake juyawa tayi tana kallon zabgegen mansion din tana girgiza kai tace"gaskia mutumin nan me kudi ne..ji gida kaman ba'a Naija ba ni Aisha"..karasawa tayi jikin gate din ta shiga lekawa ta wata 'yar karamar kofa kamar daga sama taji an danne mata horn ta bayanta...a rikice ta matsa daga wurin tana kallon motar dake kokarin shiga gidan sai tayi saurin komawa inda motarshi yake kafin ta shiga taji ance"yammata"..juyawa tayi tana kallon matar duk sai taji kunya ya kamata tana leka musu gida..ta shiga washe baki tace"ina..ina yini"..aunty sumy ta bude mota ta fito zuwa inda take tana kallonta da fara'a tace"lafia lau yammata..zaki shiga ciki ne?.."da sauri tace"aah tareda proprietor muke shine nake jiranshi"..ta karasa mgnr duka daburce kaman matsoraciya...aunty sumy ta saki smile jik tareda Bobby suke tace"to mu shiga daga ciki mana saiki jirashi a can"..tun kafin ta rufe baki Aysha tace"aa ba saina shiga ba wlh..yace kar in shiga"..dafa shoulder dinta aunty sumy tayi tace"karki damu bazaiyi maki komai bafa..aini nace ki shiga sbd haka muje plss"...narkewa tayi tana kallonta kafin tayi mgn aunty sumy ta sake fadin"please!.."haka nan ta bita suka cikin gidan ba don tanaso ba...mai gadi taba key ya shigo mata da motar snn suka wuce...matar ce tayi mata kwarjini wlh amma ita sam bata son shiga yazo yana wulakantata...suna shiga compound ta ware idonta tana kallon lafcecen compound din dake zube da uban motoci kaman na siyarwa..cikin ranta tace"babban burin inyamuri a dunia kenan..a danqara gida snn a hau motoci"..ganin bata daga kafa aunty sumy ta kama hannunta suka nufi entrance...basu samu kowa central parlor ba dan haka direct ta nufi parlon Mummy da ita...Mummy na zaune da Ilham akan cinyarta shi kuma yana rikeda hannun ilham din yanayi mata alluran jijiya..yarinyar tayi luf jikin Mummy sai sauke numfashi take...saida suka isa ciki aunty sumy ta saki hannunta tana doka wani uban murmushi tace"Mummy ga bakuwa na kawo maki"...dagowa Mummy tayi tana kallon yarinyar da kanta ke kasa kafin tace"to bismillah zauna kinji bakuwa"..karasawa tayi ta zauna a hankali har yanxun kanta yana kasa...Bobby da sai yanxun ya gama mata alluran yana dago kanshi yayi ido biyu da ita tana zaune kusada aunty sumy sai wani sussunne kai take...cikeda mamaki sosai yake kallonta yace"ke bakida hankali ne?..waya baki izinin shigowa gidan nan?.."juyawa Mummy tayi tana dubanshi tace"ka santa ne?.."dauke kai yayi yana huci ya kasa cewa komai...tambayoyin nan ne bai shirya amsawa ba shiyasa yace tayi zamanta cikin mota amma sbd tsabar rashin ji irin nata saida ta fito...yanxu shknn yasan ya shiga uku da tambayoyi a wurin su Mummy...ganin bazaice komai ba aunty sumy tace"ganinta nayi fa a cikin motarshi shine na tambayeta tace tare dashi suke amma yace ta zauna nan cikin mota karta fito"..juyawa Mummy ta sakeyi ta kalleshi sai taga ya sake hade rai yana muzurai sai ta maida dubanta ga Aysha da har yanxun kanta ke a kasa lokaci daya ta saki wani murmushi dan tasan zaiyi wuya idan ba itace Lamido ba dan haka tace"yammata meye sunanki?.."a hankali tace"Aysha"..Mummy ta shiga gyada kai tace"MashaAllah Aysha me babban suna ce ashe?.."daga kai kawai Lamido tayi tanajin kamar ta saki fitsari a wando sbd yanda takejin idanun Bobby nata kaiwa da kawowa a kanta..ko baa fada ba tasan kallonta yake...Miemie ce ta shigo parlon rikeda tea data hadoma Ilham..tana karasowa ta mikawa Mummy snn ta zauna tana kallon Aysha dake zaune tace"Mummy bakuwa mukayi?.."Mummy da har yanxu bata bar smiling ba tace"wlh bakuwa mukayi Miemie"..Miemie ta matsa kusada ita tace"sannu da zuwa ina yini?.."dan dagowa Aysha tayi ta kalleta kafin tace"lafia lau"..wara ido Miemie tayi da taga face dinta tace"laa Mummy ai na ta6a ganinta a FCNM wall..."bata samu karasawa ba sbd wani kallo da Bobby ya watsa mata ba shiri taja bakinta yai tsit..aunty sumy da tun daxu take kallonshi ganin yanda duk yabi ya takura kanshi kawai ta saki murmushi..ita bata ta6a ganin mai hali irin na Bobby ba wlh..kiri kiri ga abu kana sonshi amma wai kake kaiwa kasuwa?...mikewa Mummy tayi ta ba aunty sumy tea din Ilham tace"ki bata tasha"..snn ta karasa inda Malama A'ee take zaune ta kama hannunta ta mike tsaye snn ta jata zuwa dakinta tace"tashi muje mu gaisa 'yata"...daga haka suka shige bedroom din Mummy..Bobby yabisu da kallo kaman idanunshi zasu koma jikin kofar dakin...hankalinshi yaji ya tashi kardai Mummy taje ta fadama yarinyar nan abunda zaisa ta rainashi fa..gabanshi har wani faduwa yakeyi wlh...kaman wanda aka tsikara yabi bayansu zuwa dakin da sauri kamar zai tashi sama...





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
31
Yana shiga ya marairaicewa Mummy yace"Mummy dan girman Allah mu tafi..bama ta da lafia shine na kaita asibiti"...murmushi Mummy tayi kafin tace"to ka jiramu a waje yanxun nan zata fito"..da sauri ya canxa yare yace"Mummy me zaki fada mata?.."da yaren itama tace"akwai abunda kake 6oyewa wanda bakaso ta sani ne?.."girgiza kai yayi da sauri duk yabi uzzurawa kanshi babu gaira babu dalili...kofa Mummy ta nuna mishi alaman ya fita haka ya juya ya bar dakin yana sake sake...bayan fitarshi Mummy ta dawo da dubanta ga Aysha tace"zauna mana Aysha"..maimakon ta zauna saita risina har kasa tana kallon kasan tace"Ina yini"..Mummy ta amsa da"lafia lau..ya karatu?.."tace"Alhamdulillah"..Mummy tace"to dawo nan ki zauna tunda mun gama gaisawa"..ba musu ta mike ta zauna inda ta nuna mata...kallonta kawai Mummy keyi taji ta shiga ranta sosai...irin wnn kyau da take dashi ai ba Bobby ba kowane namiji ma yana iya samun matsala idan aka jarabceshi da qaunarta...tana cigaba da dubanta tace"da gaske bakida lafia?.."kai kawai ta iya dagawa...Mummy tace"to Allah ya baki lafia..yanxu bari a kawo maki abinci kici"..da sauri tace"wlh mama na koshi banajin yunwa"...Mummy ba girgiza kai tace"aah dole kici wani abu"..daga haka ta kwaloma Miemie kira...tana shiga Mummy tace"jeki kawo mata abinci"...kafin ta fita Aysha tace"wlh ban dade da cin abinci ba banajin yunwa"..Mummy tace"to shknn dukda haka dai ko tafiya sai kinyi dashi...Miemie ki samu abu ki zubo mata pepper chicken sai ki hada mata da lemo"..ba musu Miemie ta fita don yin yanda aka sata...suna nan zaune ta dawo da wani bag mai kyau datasa pepper chicken din a ciki...Mummy tace"to ki rike mata saiki rakata waje dashi"..a hankali tace"toh.."snn ta juya ta fita...mikewa Mummy tayi zuwa wadrobe dinta ta dauko wasu turaruka masu kyau guda biyu ta zuba mata su cikin dan karamin jaka mai kyau snn ta bude drawernta ta dauko two sets na sarkoki suma masu azabar kyau duk ta zubasu cikin jakan...hajia indo dai tana zaune kai a kasa kamar munafuka..hannunta Mummy ta kama suka fita daga dakin...Bobby daketa safa da marwa ya juya yana kallonsu kamar idonshi zasu fadi kasa..saida daria ya subucewa Mummy sbd ganin yanda duk yabi ya addabi kanshi ba gaira ba dalili..shi kuma ya wani kwabe fuska da igbo yace"Mummy me kike ce mata dan Allah?.."bayan ta staida dariyarta tace"gata nan ka maidata kuma wlh ban yadda kayi mata fada ba Bobby..idan kayi kuma zai dawo kunnena"..daure fuska kawai yayi baice komai ba...aunty sumy ma ta fito daga dakinta rikeda wani dan box mai kyau tana karasowa ta mikama Aysha tana murmushi tace"to ga wnn Aysha..i hope zaki sake kawo mana ziyara?.."murmushi kawai tayi bata iya amsawa ba duk sun sata jin wani iri wlh..sunada kirki sosai unlike Proprietor da sukayi hannun riga da kirki...ta amsa abun tayi godia..Mummy tace"ai zai sake kawota mu gaisa"..aunty sumy tace"kwarai kuwa..idan ma bai kawota Mummy da kaina zanje har hostel dinsu in dauko mana ita"..shidai yana fsaye fuskan nan a tamke baice musu kala ba...after long surutunsu finally ya samu aka bashi ita suka fita..Miemie ta rakata har mota da kayanta ta zuba mata su back seat snn ta zaga inda take da nufin tayi mata sallama Bobby dake cika yana batsewa ya wani 6alla mata harara tareda fadin"bar nan"..ba shiri ta koma ciki tana turo baki...tada motar yayi da wani irin gudu suka bar layin nasu..Ita dai a tsorace take sai rarraba idanu take...suna hanya wayanta ya fara ringing ganin wanda ke kira sai tayi silencing wayar taki dauka sbd gudun masifanshi...sake kira akayi ta kuma sawa a silent shi kuma ganin batada niyyar dagawa yakai dubanshi kan wayar dake cinyanta sai yaga baby boo kan screen aikuwa ya sake dinke fuskanshi tsaf yana sake figan motan a guje kmr zai tashi sama...gani take kaman tsoron dunian nan a kanta ya sauka wnn uban gudun da yake idan yaje ya watsar dasu fa?..bata dai ce masa komai ba har suka isa gate din hostel...ya cire mata lock ba tarefa ya kalleta ba yace"fita"..da sauri ta kama kofar zata bude sai kuma taji yace"bana hanaki kiramin wani besty idan muna mgn ba?..ke wato bakyajin mgn koh?.."da sauri tace"kayi hakuri"..yace"sbd kinga banaso shiyasa kike fada wato koma me zanyi inyi koh?.."ta dan lankwasa wuya tace"sir nace fa kayi hakuri"...dauke kanshi yayi daga gareta yace"fitamin daga mota"..ta sake langabewa tana kwabe fuskanta tace"sir i said am sorry mana..kayi hakuri bazan kara ba"...juyo da kanshi yayi yana kallonta yace"idan kika kara inyi maki me?.."hannu takai tana shafa cheeks dinta kafin a hankali tace"ka mareni"..murmushi kawai ya saki tareda jinginar da kanshi jikin kujera..dama yasan fushin ma ba wani iyawa zaiyi da ita ba..itama murmushin ta saki tace"sir kacigaba da smiling dan Allah..yana maka kyau"..bude idonshi yayi ya zubasu a kanta..wasu sabbin al'amura yakeji suna zagayawa cikin jini da tsokarshi...mikewa yayi daga inda ya jingina still yana dubanta ina serious note yace"da gaske banason jin wani besty ko waye a bakinki..banaso idan kuma kika sake kiramin shi muna mgn marinki zanyi kaman yanda kika fada"..murmushi take tace"bazan ma kara ba inshaAllah"..yace"shknn u can go..and make sure kinsha drugs dinshi akan lokaci kuma banda skipping idan ba haka ba kuma alluran da bakiso shi za'a kuma yi maki"...bude motar tayi ta fita still tana murmushi tace"aah banason allura zansha maganin..saida safe"..kanshi kawai ya iya daga mata snn ta juya ta tafi bayan ta kwashi kayanta dake baya...saida yaga shiganta ciki snn yaja motarshi ya kara gaba.

Tun daga wnn ranan suka sake dinkewa abunsu...tanajin magananshi sosai and hakan ba karamin farantawa Bobby yake ba..zuwa yanxu ya gama admitting ya kamu da soyayya..soyayya kuma na bafulatana data fito daga jihar Gombe..what a miracle..tunda yake bai ta6a tunanin zaiso wata mace ba ballantana 'yar Gombe amma ita sai yaga kaman turota akayi dan tazo ta wargaza duk wani tanadi da alqawura da yayima kanshi...shida yake shiga college only Thursdays da Fridays amma yanxu kusan kullum sai ya shiga sbd kawai ya samu ya ganta domin ganin nata shine kadai samun nustuwarshi...yanayi mata sonda shi kanshi bai tunanin yana yiwa kanshi amma har yanxu ya kasa nuna mata dukda yasan wani lokacin actions dinshi suna nunawa sbd kasa controlling kanshi da yake amma ita kota fahimta bata ta6a nuna mishi ba...abu biyu dake damunshi sune na farko amanarta da mahaifinta ya bashi yana gudun kada mgnr sonda yake mata ya fita shi kuma mahaifinta yaga kamar bai rike mashi amana ba tunda har shi da kanshi zaice yana sonta..sai na biyun kuma shine Gombe..bayan kasancewarta 'yar Gombe muma tazo a bafulatana..har yanxu bai mance yanda 'yan uwan dad dinsu fulani sukayi treating Mummy ba..shima yana tsoron kada yaje neman aurenta ace dan inyamura ne shi baza'a bashi ba..ga kuma su kansu 'yan uwan daddyn da matukar zaiyi aure dole saiya nemi inda suke sbd su shige mishi gaba kan mgnr saidai sam baiji zai iya zuwa ya samesu ba..har yanxu yana nan akan bakanshi na babushi babusu amma kuma tayaya zai samu auren Lamido ba tareda sa hannunsu ba?..gaba daya ya zama wani iri yanxu ko abincin kirki baici..aiyukan nashi ka neman tsaywa suke cak sbd damuwar da yake ciki..har dan ramewa yayi sbd tunani..Mummy tayi tayi dashi ya sanar mata abunda ke damunshi amma kullum mgnrshi daya shine babu komai...ganin yana neman rasa nutsuwarshi yau dai ya yanke shawaran zaije ya samu Nur suyi mgn ko yanada solution da zai bashi...gashi itama yarinyar wahalar dashi takeyi these days baisan laifin da yayi ba duk ya kirata a waya bata dauka...hankalinshi ba karamin tashi yayi ba yau kusan 5 days knn baiji muryanta ba kuma bai ganta ba dan haka yake jin kanshi kaman mara lafia..baisan meyasa take mishi irin wnn ba..haka nan babu laifin zaune babu na tsaye saita dauke mishi wuta sai yayita binta yana lallashi snn zai samu kanta amma this time around yace bazai ske nemanta ba inyaso sonta yayi ajalinshi shima sai ya samu ya huta.

Yana shigowa College zuwa office din Nur da yace mashi yana jiranshi a ciki...da sallama ya shiga yana takawa da kyar sbd matsaloli da suka taru suka cika mashi brain...Nur na ganinshi ya mike ya koma kan sofa shima karasawa yayi ya zauna nan kusa dashi tareda jingina da jikin kujeran yana lumshe ido...Nur yace"kace zamuyi mgn i hope dai lafia?.."girgiza kai Bobby ya shigayi tareda bude idanunshi yace"ba lafia ba Nur..ina cikin damuwa"..gyara zama Nur yayi yace"to inajinka"..ajiyar zuciya Bobby ya sauke yana shakar iska da kyar yace"it's about Lamido..i think..i think i've fallen for her"...dukda Nur ya dade da sanin yana sonta yayi mamaki sosai jin a yanayin daya fada mashi...kamo hannunshi Bobby yayi yana kallonshi da idanunshi da suka sauya kala muryanshi cikin raunin da Nur zai iya rantswa bai ta6ajinshi a ciki ba yace"i am in a serious mess Nur..na rasa nustuwata gaba daya..komai bayamun dadi..komai banajin dadinshi abu daya da yake keeping dina company shine tunaninta..zuciyata ta cuceni duk iya kokarina na ganin na kaucewa abunda nakeji abun yafi karfina Nur..bansan meya kamata inyi ba nasan yarinyar nan bazata ta6a sona ba"..yana rufe baki Nur da yaji asalin tausayinshi na ratsashi ya dafa shoulder dinshi yace"Man take it easy plss..idan kana wnn damuwan kana iya samun problem ka sani..nayi maka alqawarin i'll help you in anyway possible dan inga ka samu soyayyarta..wnn matsalan nake guje maka shiyasa tun farko naso ayima tufkar hanci baka bani dama ba"..sake damke hannunshi yayi yace"yanxu na baka do your best plss..ka taimakeni before i loose my sanity..inajin zafi sosai duk lokacinda na ganta da wani..yanxu haka da nake mka mgn ko wayana bata dauka kuma bansan laifinda nayi mata..nasan kilan Allah yanaso yayi punishing dina ne kan abubuwanda nayi mata a baya amma wlh bada son raina bane..bansan meyasa ina ganinta raina yake 6aci har yasa nayi mata abubuwanda nayi ba"..rungumeshi Nur yayi cikeda tausayinshi sosai yace"it was all the love Bobby ganewa ne bakayi ba..tun daga ranan da tacemin kace baza tayi presentation ba nasan da akwai wani abu a ranka gameda ita..Lamido is a good girl..tanada hankali sosai and am sure ko bata soka yanxu ba watarana zata soka"...dagowa yayi daga jikinshi yana kallonshi with a wide smile jin abunda ya fada yace"nagode sosai Nur..thank u..kasan a da nayi tunanin sonta kake sai kuma daga baya naga ba haka bane"...Nur yace"well a gaskia bazan boye maka ba i once had a crush on her amma tunda ja fahimci kana sonta saina hakura sbd nasan sonda kake mata yafi wanda zan mata..kuma dakai tafi dacewa bada ni ba and inshaAllah i will do my possible best inga na hada wnn soyayyan..ba karamin matching couple zaayi ba kai da Lamido"...murmushi sosai Bobby yake wanda ya manta when last yajishi so lively haka...maganganun da Nur ya fada sai yajisu tamkar diamond da gold sbd tsananin dadinsu da yaji...cikin murmushin da yaki bajewa fuskanshi yace"thank u so much friend..u are really a friend indeed"...shafa kai Nur ya fara yana wani murmushin shakiyanci yace"gaskia ya kamata ayi saluting Lamido data canxaka haka?..yau Dr Bobby ne da godia haka ba kakkautawa?.."murmushin shima ya kara saki shi kanshi ya dade yana mamakin kanshi..ya dade yana mamakin yanda ya canxa ta 6angarori da dama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login