Showing 66001 words to 69000 words out of 231169 words

Chapter 23 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9675

kome zai faru sai yayi mata mgn saidai idan taga dama misquoting din nashi he no longer cares..kawai haushi yakeji that gaba daya festival din ma ya fita daga kanshi kuma ya rasa wnn masifa da akan yarinya guda daya yana neman rasa sukuni da nutsuwarshi...suna isa dance floor aka sa musu waqan yoruba suka fara dancing...tafi da sowa kam sun shashi kaman ba gobe ga kuma ruwan kudi da suka samu daga mazauna wajen...lokacin da suka fito zasuyi na igbo Bobby kasa dauke ido yayi a kanta sai yaga kaman duk kayan da ta saka ba wanda yayi mata kyau kamansu...baisan ko don shi ya kasance igbo din ba amma kayan sun amsheta kaman itama igbo din ce...sai yaga kaman idon kowa na wurin a kanta yake sbd kyawunda tayi...bata sake bashi mamaki ba saida suka fara rawar...sunyi kokari matuka kaman dama inyamuran ne su...har yanxu kuma wnn zafin da yakeji yana nan wanda shine yasa gaba daya baya enjoying zaman wurin...Fulani dance shine na karshe and lokacinda suka shigo Bobby baki da hanci ya saki yana kallonta...tunda yake bai ta6a tsaywa ya kalleta irin na yau ba...tayi mishi kyau fiyeda yanda bakinshi zai iya fada..shi baima ta6a ganin kyanta kaman na yau ba tunda ya santa...haka akasa musu waqar fulani sukayi rawa sosai yanda ya kamata...and again an watsa musu naira snn wani babban mutumi dake wurin yayi musu kyautar kudi masu yawa...wani kuma daga cikin baqin shima yace ya bawa Aysha kyautan sabuwan waya Smsung Galaxy...farin ciki sosai takeyi har hakan ya kasa 6oyuwa dan sai murmushi takeyi Bobby kuma kamar bala'i idanunshi suna kanta yana ganin yanda dimples dinta ke fitowa as a result of smile da take...kasa cigaba da zaman wurin yayi kawai ya mike kaman wanda yakeda mutanen 6oye ya fita daga hall din kusan gaba daya mutane suka bishi da kallon mamaki...Nur ne ya mike da sauri yabishi a baya yana dab da shiga office dinshi ya iskeshi yace"Bob are u alright?..lafia naga ka tashi ana taro ko wani abun ya faru ne?.."juyawa yayi a fusace yana kallon Nur din snn ya nunashi yatsa yace"Fuck you"..daga hakaya bude office dinshi ya shiga ciki tareda bugo kofar da karfi...Nur mutuwan tsaye yayi a wurin yana kallonshi da mamaki...to meya sameshi haka?..kodai wani saga ciki guests din yayi mishi abu?..duk kokarinshi na yaga yayi pointing finger kan dalilin tasowarshi daga wurin ya kasa...baiyi yunkurin binshi cikin office dinba kawai ya juya tareda komawa can wurin still yana tunanin abunda akai mishi.

Bobby na shiga office din ya zauna tareda dora kanshi kam table yana sauke numfashi da sauri kaman wanda yayi race...ko kusa baya son wnn sabon al'amari dake kokarin kunnowa cikin rayuwarshi..bayaso sam...baisan kan wane dalili zai dinga jin haka akan yarinyar da bai hada komai da itaba...shi tunda yake ma bai ta6a samun kanshi cikin yanayi irin wnn ba sai yanxu...gaba daya yarinyar nema take ta zame mishi tauraruwa mai wutsiya...ciwo yakeji sosai na raye rayen da taje tayi a bainan nasi..kuma sbd rashin sanin darajar kai ko dan mayafi bata yafa ba ballantana ayi mgnr hijab..gaba daya ya kasa gane wace irin yarinyace ita?..duk sai yaji kaman bai kyautawa babanta daya damka amanarta a hannunshi ba...kaman wanda akama allura ya mike da sauri ya fita daga office din...can inda audit din yake ya nufa yana shiga premises din wurin yaga Billy ta fito daga ciki tana waya tana ganinshi tayi saurin kashe wayan da takeyi tana kallonshi a tsorace...voice dinshi a cunkushe yace mata"where is ur friend?.."da sauri ta nuna auditorium din tana cewa"tana..ciki"..."go and call her"..ya fada hands dinshi zube cikin aljihu...ba musu Billy ta juya da sauri ta koma ciki...can tsakiyar dance floor ta hangota bayan sun gama performance dinsu aka sakar musu kida suka fara rawa gaba dayansu...haka Billy ta kutsa ta cikin mutane zuwa inda take kawai sai ji tayi ta kamo hannunta ta shiga janta...Lamido ta kwace hannunta tana turo baki tace"Billy rawa nakeyi dan Allah"...harara me kyau Billy ta watsa mata before tace"to kicigaba da rawa ai ga Proprietor can yana nemanki"..bata rufe baki ba Aysha ta zaro idanu tana fadin"dan girman Allah da gaske?.."kama hannunta Billy tayi suka fita daga wurin snn tace"Allah da gaske nake..yana can a waje fuskan nan kaman bai ta6a daria ba dan wlh har tsorata nayi dana kalleshi"...nan take hankalin Aysha ya fara tashi tace"na shiga uku meyasa yake nemana kuma?.."Billy tace"indai kinsan bakiyi laifin komai ba ki kwantar da hankalinki..kiyi addu'a kije ki sameshi in Allah ya yadda ba abunda zai miki"...girgiza kai kawai Aysha keyi tace"zo muje ki rakani dan Allah"...Billy ta kwalo idanu waje tana fadin"Ni?...rufamin asiri Lamido in mutu maza su kaini ba mata ba...haka nan inje yayita zazzaro idanun nan nashi yasani sakin fitsari a wando"...dukda tashin hankalin da take ciki saida mgnr Billy ya sata daria...sai kuma ta marairaice fuskanta tace"na shiga uku tsoron zuwa nakeyi wlh...nasan yanxu abu karami yake jira ya hadani da daddy"...Billy tace"ba fada miki inshaAllah ba komai kedai kawai kije kiji mezai fada idan ba so kike ki kara wani laifin ba"...jiki a sanyaye ta gyara mayafinta snn ta fita daga wajen...bata sameshi nan waje ba dan haka ta wuce office dinshi...tana shiga ya dago fuskanshi da yayi murtuk kaman na marasu imani kawai ya mika mata hannunshi murya a cushe yace"bani wayarki"...mika masa wayar tayi da sauri tareda sunkuyar da kanta kasa tana wasa da fingers dinta...shi kuma yana amsan wayan yasa digits dinshi snn yayi dialing...wayanshi dake ajiye kan table dinshi yayi ringing alaman kiran ya shigo snn yayi quitting call din tareda ajiye wayan a kusada nashi...Aysha dai har yanxun kanta na kasa tana kwararo mishi addu'a cikin zuciyarta...tsoronta Allah tsoronta kada ace wani laifin tayi ya kira daddy ya fada masa...shi kuwa kallonta yakeyi yanajin tamkar ya kwada mata mari don haushi..dubi dai yanda ta wani nustu a gabanshi kaman mutumiyar kirki amma dazu taje ta gama bayyanar da jikinta wa mutane suka kalla...ko rantsuwa yayi yasan da kyar babu wanda bata burgeba a cikin wadanda suke wajen...kawai ciwo yakeji that a gaban idonshi abun ya faru and he couldn't do a thing...cikin muryan daya kusa sanyata fitsari yace"wato ke bakida hankali kou?..sbd bakisan ciwon kanki ba kikaje kina rawa gaban mutane kina musu tallan jikinki kou?.."dan dagowa tayi ta kalleshi kafin ta mayar da kan nata da sauri dan tsoro idanun ma suka bata...saida ta dan marairaice snn tace"tallan jikina kumah?.."a fusace yace"if u dare say another word a wurin saina kwada maki mari...tambayana ma kikeyi sbd bakida kunya kou?.."shiru tayi tana turo baki...yace"well let me call ur Father and tell him all you've been doing"..yana karasa mgnr ya dauki phone dinshi dake nan kan table ai batasan time din da ta kama hannun nashi ta rike gam ba sbd tsoro...cikeda tashin hankali tace"Sir dan Muhammadu rasulillahi kar ka kirashi..i beg of u please"..ta karasa mgnr hawaye ba zubowa kan cheeks dinta...Bobby dake kallon yanda ta rike mishi hannun yace"how dare you?.."sakin hannun nashi tayi da sauri tana cewa"am sorry...Sir dan girman Allah ka rufamin asiri karka fada wlh fada zaiyimin"...sake daukan wayan yayi yana searching contact din daddy yace"da kina tsoron fadan ai bazaki aikata abunda ba daidai ba"...wnn karon hannayenta ta hade waje daya in a pleading tone tace"Sir na rantse da Allah ban karawa kayi hakuri plss"...ajiye wayan yayi yana kallonta..dama baida intension din kira yayi haka ne kawai dan ya tsoratata tunda already yasan yanda take tsoron mahaifinta...idonshi a kanta yace"fadamin meyasa bakijin magana?.."tana cigaba da hawaye tace"am sorry"...yace"ba wnn na tambayeki ba..i said meyasa bakyajin mgn?..why kikeda fitina?.."shiru tayi tana goge hawayenta sai can kuma tace"nima ban saniba"...tsaki ya saki tareda daukan wayanta yana mika mata yace"leave my office immediately..and if u like gobema kizo kiyi abunda kikayi yau kiga idan ban sanar dashi ba"..kar6an wayan tayi tana turo baki ta juya ta ta fita daga office din..tana ganinta a waje ta sauke wani ajiyar zuciya a fili ta furta"kuma Allah ya isana wlh..inyamurin banza"...shi kuwa sai daga baya duk haushin kanshi yabi ya kamashi...wai ma ina ruwanshi da rayuwarta ne at the first place...mamakin kanshi yakeyi shi that ya tsani Fulani especially na Gombe amma wai shine har yake kokarin protecting yarinyar da yasan asalin 'yar Gombe ce?..baisan ko don sbd mutuncin mahaifinta da yake gani bane...abu guda daya sani shine dukda kasancewar babanta bafulatani kuma na Gombe yana matukar ganin kima da darajarshi and shine mutum na farko daya faraji ya kwanta mishi a rai bayan sanin cewa shi din bafulatanin Gombe ne...kilan sbd kyawawan maganganun da yayi kan Dad dinshi ne amma maganan gaskia mutumin yayi mishi dari bisa dari...itama kuma 'yar tashi yasan sbd mahaifinta yakejin abunda yakeji and nothing more.

The next day which is Wednesday ranan ne ake inviting mawaqa from different states suzo suyi performing a makarantan...Bobby na kwance tun safe a daki ko parlor ya kasa fitowa...kawai jin jikinshi yakeyi wani iri that har yake tunanin kilan hakura zaiyi da shiga college din nan kawai...dukda yayi mata mgn jiya and yanada tabbacin ta tsorata sai yakejin kaman yayi zamanshi a gida or better still ya tafi Hospital dinshi kawai ba sai yaje ba balle yaga abunda zai 6ata mishi rai...haka yayita kwance a daki bai fito ba saida Mummy ta aiko a kirashi...yana saukowa daga gado ya fada bayi yayi wanka snn ya fito ya shirya kanshi cikin wata armless shirt da wando three qtr snn ya nufi parlor...parlon Mummy ya samesu zaune gaba daya as aunty sumy na gida itama ranan bataje aiki ba Miemie ma bataje sch ba sbd fever data kwana dashi ita kuma ilham tun 1 aka tashesu...karasawa yayi ciki ya zauna da igbo ya gaida Mummy itama ta amsa da igbo snn tayi adding da"yau baka fita ne naga har yanxu baka shirya ba?.."dan ta6e baki yayi yace"i just don't feel like going out..i think zamana zanyi a gida in huta"...Aunty Sumy tace"aikam bai kamata kaki zuwa ba Bobby..remember it's a Festival week and abune wanda yake taking place once in a year sai nakega kaman bai dace kaki zuwa ba ko don sbd guests dinku"...Mummy ma na gyada kai tace"sumayya gaskia ta fada Bobby"..shiru yayi cikin ranshi yana ayyana bazaku gane bane...abun kaman hadin baki kawai sukaji sallamr Nur a parlon...Bobby ya kulle ido tareda fadin"the fool is here..nasan yanxu ko banida intention din fita saina fita ko don nacinshi"...daria Mummy sa aunty sumy suka saka jin abunda yace...Nur daya karaso ciki ya zauna ya shiga gaisawa dasu Mummy shima cikin igbo...aunty sumy tace"wlh har mantawa nake Nur yanajin igbo sbd bai cikayi ba unlike abokinshi da mgn daya biyu sai ansa igbo a ciki"...murmushi Nur yayi yana shafa kanshi yace"wlh ni kaina ina manta inajin yaren aunty...gaba daya hausawa sun janyeni"...daria suka sake yi Mummy tana ai dole hausawa su janyeshi tunda yake zaune a kano...bayan sun gama Nur ya juya yana kallon Bobby kafin yayi mgn Bobbyn ya mike yana cewa"ba saika 6ata bakinka ba nasan meya kawoka..ka bani just 5 mins zan shirya in fito"...daria gaba daya suka kara sawa Bobby ya wuce flat dinshi...aunty sumy tace"Nuru kai kadaine maganin Bobby gashi tun kafin kayi mgn an tafi shiryawa"...dariyan shima yasaka yace"kinsanshi baya son naci ai..ni kuma indai inason yayi abu bana barinshi har saina samu abunda nakeso"...bayan 5 mins ya fito a shirye kaman yanda ya fada...Nur na ganinshi ya mike yana sallama dasu Mummy Ilham tace"uncle bobby inaso inje plss"..kallonta bobby yayi sai kuma yace"no kiyi hakuri sai gobe kuje tareda su aunty kinji"..makale shoulder dinta tayi tana fadin"oh oh inaso inje yau"...kallonta kawai yakeyi totally speechless..shi ba son zuwan nan nasu yakeba wlh..ko gobe da aunty sumy tace zasuje suji lecture da za'ayi ba so yakeyi ba...Nur da yaga tana shirin sakin musu kuka yace"zamuje dake baby don't cry"...nan da nan ta washe bakinta tana tsallen murna..."uncle Nur"..yaji Miemie ta kira sunanshi...a hankali ta juya yana kallonta sai yaga tayi narai narai tana kallonshi...murmushi ya saki dan ya gane mgn take mishi a haka..so take taje itama and tana tsoron furtawa sbd Oga Bobby kada ya hana...saida ya dan saci kallon Bobbyn snn ya dubeta yace"kema zakije kou?.."daga mishi kai tayi da sauri..yace"to je dauko mayafinki"..da sauri ta mike zuwa dakinta ta dakko veil da phone dinta ta fito...Bobby da haushi ya isheshi ya bude baki zai fara masifa Mummy tace"don't say anything plss..kuje dasu su gani ai ba dadewa zaayi ba"..gum ya maida bakin nashi ya tsuke ba tareda ya fadi abunda yayi niyya ba...sallama sukayi musu suka fita Bobby ya shiga motanshi tareda driver da kuma ilham shi kuma Nur ya dauki Miemie a nashi motan suka tafi.

Tsaye take gaban mirror dinsu tanata kallon kanta kaman bata ta6a ganin mirror ba...straight gown ce a jikinta na wani lace mai kyau..dinkin yabi jikinta ya kwanta luf luf hakan kuma ya baiyanar da beautiful figure dinta...daurin dankwalinta Zara Buhari as usual gashinta ya leko ta karkashin daurin..gaba daya ranta ba dadi duk ma tasan ba jin dadin yau din zatayi ba sbd Bobby..duk ta tuna kashedin da yayi mata jiya na idan tayi wani abu zai hadata da daddy sai taji kaman tasa kuka wlh...yanxu haka yakeso taje tayi zaune a wurin tayita kallonsu knn ita bazatayi rawa ba...da yasan yanda take kaunar rawa da baiyi mata haka ba wlh..kawai rawan yakema bala'i jiya kaman zuwa tayi club ta kwana...Billy ta shigo dakin tana sanye cikin kayanta irin na Aysha sak har dinki da daurin dankwalinsu iri daya...batace mata komai ba ta karasa cikin dakin ta dauko veils dinsu da suke zube kan bed dinta ta hada da wayoyinsu snn taja hannun Aysha suka fita daga dakin...binta kawai takeyi har suka isa compound snn ta saketa ta mika mata veil da wayanta ba musu ta kar6a ta yafa itama Billy ta yafa nata snn tace"nasan in muka daka ta taki zamu iya kwana nan ciki baki gama kallon madubi ba..na fada maki idan kika kiyaye babu abunda ya isa ya maki amma har yanxun kinki kwantar da hankalinki"..juyawa Aysha tayi tana kallonta kaman zatasa kuka tace"yandu fisabilillahi saidai inje inyi zaune kaman gunki ni bazanyi abun arziki ba?..ai wnn rashin imani ne wlh"..ta karasa mgn hawaye na cikowa idonta...daria yaso kufcewa Billy amma ta gimtse suka fita daga wurin...inda Sa'eed ke tsaye suka nufa kafin su karaso ya bude musu mota Aysha ta shiga gaba Billy kuma baya snn shima ya shiga ya tayar da motar suka tafi...a hanya ya dubi bestyn tashi yaga fuskan nan cunkus sai ya kallo Billy ta mirror yace"waya ta6amin besty ta?.."daria Billy ta saki tace"akan mgnr jiya nefa"..dan murmushi shima ya saki yana kokarin controlling dariarshi yace"besty har yanxu mgnr rawan ne dai?.."a fusace ta juya tana kallonshi tace"malam ba ruwanka dani tunda biyewa Billy kake kunamin daria...kawai sai inje inyi zaune ni bazanyi rawa ba sbd rashin imani"...ta karasa mgn hawaye na sake ciko eyes dinta...wnn karon kasa 6oye dariar sukayi dan dagashi har Billyn basu san sanda ta fito ba...daria sukeyi sosai sai kace ta6a66u Aysha kuma ta shaqa iya shaqa kawai sai ta rufe fuska da hands dinta ta wani rushe da matsanancin kuka...ganin kukanda take sai darian ya sake zuwa musu aikam sukaita yinshi knr sabbin kamu saida sukayi me isarsu snn suka bari...Sa'eed ya dan juya yana kallonta with a little smile yace"besty dan Allah kiyi hakuri kinji..nifa bake nakewa daria ba"...yana rufe baki Billy ma tace"nima na ranste ba dake nake ba dan Allah ki bar kuka"...ai kaman ma sunce tacigaba don kara sautin kukan tayi hadda su buga kafafu a kasa ba shiri Sa'eed ya gangara gefen titi yayi parking...juyawa yayi yana kallonta ya wani marairaice yace"yanxu besty dan girman Allah bazakiyi shiru ba?..nace fa am sorry kuma da gaske ni ba dake nake ba"...banza tayi dashi tana cigaba da kukanta...yana mata ciwo idan ta tuna saidai kawai taje wurin a matsayin hoto bazatayi rawa ba...gashi ance hadda favorite mawaqinta aka dauko Ado Gwanja kuma ace bazatayi rawa ba ai wlh an cuceta...wayanta dake ajiye kan dashboard ne ya fara ringing Sa'eed yakai hannu ya dauka ganin yanda tayi banza da wayan...Baby boo ya gani kan screen din dan haka ya juya screen din yana nunawa Billy..da sauri tace"yauwa dauka kace masa yazo ya rarrashi kayarshi tunda mu taki ta sauraremu"...ba musu Sa'eed yayi sliding tareda sawa a speaker...on the other side Prof Ahmad yace"my baby girl"...hada ido Sa'eed sukayi da Billy suna kunshe daria kafin ya maze yana cewa"ahm ba ita bace sunana Sa'eed"...Prof yace"ai besty zaka cemin yanda zanfi ganewa"...Sa'eed ya kara sakin murmushi before yayi adding"besty ce dama tun daxu take kuka wlh kuma munyi iya bakin kokarinmu taki tayi shiru"...hankalinshi har ya fara tashi yace"wait voice dinta ne nakeji tana kuka yanxu?.."da sauri Sa'eed yace"itace wlh...mun rasa yanda zamuyi da ita"...Prof yace"bata waya muyi mgn"...ba musu Sa'eed ya ajiye wayan kan laps dinta...voice dinshi taji yana fadin"hello baby girl"...dan dakatar da kukan tayi tana goge tears dinta tace"umhum"..yace"why are u crying baby girl..waya ta6amin ke?.."saida ta sake goge tawagar hawaye da suka biyo fuskarta tace"ba komai"...yace"no ban yadda ba baby kodai inzo ne?.."girgiza kai tayi tace"aah.."yace"then promise me u will stop crying inba haka ba kuma am coming"...a hankali tace"I promise"...yace"yauwa my little baby girl i love u kinji?..and zanzo da daddare sakin fadamin wanda yasa babyna kuka"...kai take gyadawa kaman yana ganinta kafin tace"toh.."yace"ohk bye"...itama tace"bye.."snn ta ajiye wayar...Billy da Sa'eed hanci da baki suka saki suna kallon ikon Allah ganin har ta dea kukan kaman ba itane suke roki ta dena ba amma taki...bata kalli kowadaga cikinsu ba ta maida kanta jikin window...suma basuce mata komai ba as suna tsoron su sake mgn ta kuma langabe musu Sa'eed ya koma seat dinshi ya zauna snn tada motar suka karasa cikin makarantan.

Wucewa sukazo yi ta daidai inda suke tsaye da alama wani suke jira...Bobby rikeda hannun Ilham Miemie kuma na tsaye kusada Nur don ko kadan batason hada ido da Bobby data tabbatar haushinta yakeji for following them...Bilkisu da Sa'eed ne suka fara tahowa suna zuwa inda suke gaishesu snn suka wuce ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login