Showing 108001 words to 111000 words out of 231169 words
sai daxu a jikinta..baisan lokacinda daria ya su6uce mishi ba daya tuna yanda ta gwalo idonta a lokacin..yasan she was shocked amma da yake tanada positive mind sai batayi thinking negative a kanshi ba sai ma yabonshi da tayi..shi tunda yake bai ta6a sanin haka mutum kejin dadi idan an yabeshi ba sai yau din nan kuma a kanta..lokacin data yabeshi sai yaji kaman duk dunia ko kowa bazai yabeshi ba nata kadai ya isheshi...nata kadai ya isa yasashi farin ciki...har ya gama wanka ya fito bai dena tunaninta yana sakin murmushi time to time ba...koda ya gama shiryawa sai yayi kwanciyarshi nan cikin dakin yaki fita sbd yasan kilan wadan nan mutanen suna nan basu tafi ba shi kuma baison haduwa dasu dan haka gwara yayi kwanciyarshi a daki...wayanshi ya dauki ya shiga gallery dinshi hoping inama zaiga pictures dinta amma babu..bayada pictures dinta ko daya amma yanada bukatar ya samu ko guda daya ne sbd irin wnn lokacin..kunna data dinshi yayi ya shiga whatsApp wai ko zai ganta online amma she's offline...ya duba status dinta nan ma batayi updating komai ba sai wani short video na wasan PSG da Manchester..dan ta6e baki yayi cikin ranshi yana ayyana dole ma ya rabata da kallon ball din nan wlh..shi bazai dauki ta wani dinga son 'yan ball tana supporting dinsu ba..hakan 6ata mishi rai yakeyi sosai...kashe data dinshi yayi ya ajiye wayar ganin har lokaci bata online...yana ajiyewa kuma kiran Nur ya shigo wayan dan haka yayi picking yasa a speaker yana sakin wani murmushi yace"Dr Nuruddeen Ugo"..daga daya 6angaren Nur ya wara idanu yana fadin"ah lallai abu ya tafi yanda ya kamata i don't even have to ask"...Bobby yace"of course..ka kayuta sosai daka kawomin ita thank u"..da sauri Nur yace"always welcomed angon Lamido..yanxu a bani labari in detail inji abunda ya faru"..murmushi Bobby ya kara saki yana shafa beard dinshi hadda su lumshe ido yace"ka bari kawai Nur..sai yanxu na fara yadda da mgnrka..tanada hankali sosai"..Nur ya fashe da dariya before yace"bana fada maka ba?..tanada hankali wlh kawai idan ba zama kayi da itaba bazaka fahimci hakan ba"..Bobby na gyada kai zai sake wani mgn Ilham ta shigo dakin tace mishi Mummy na nemanshi..sallama yayi da Nur snn ya janyota yana kallon yanda har yanxu bata gama maida jikinta sbd rashin lafiyan da tayi ba yace"mutanen nan sun tafi ko suna nan?.."ilham tace sun tafi dan haka ya mike rikeda hannunta suka fita parlor...Mummy kadai ya samu a parlon ya karasa ya zauna yana kokarin zaunar da Ilham kan laps dinshi Mummy tace"kyaleta taje wurin su Miemie mgn zamuyi ai"..ba musu ya saketa fa nufi parlon aunty...Mummy ta maida hankalinta gaba daya gareshi fuskanta ba yabo ba fallasa tace"ya mgnr zuwa duba Waziri?.."wani irin damm yaji gabanshi ya fadi amma bai bari ta lura ba yace"za..zamu..je mana Mummy..ba kince yana india ba?.."yana rufe baki tace"an dawo dashi jiya..yana nan a Abuja kuma wnn satin nakeso kuje ku duboshi"..Bobby ya hadiye wani irin yawu kafin ya tattaro abunda zai fada mata yace"kenan..Gombe zamuje..mu dubashi?.."kallonshi Mummy tayi rai a dan 6ace tace"bakaji nace yana Abuja bane?.."da sauri yace"yi hakuri Mummy banji ba..amma why not a bari next week sai muje"..tun kafin ya rufe baki Mummy tace"ban yadda ba wnn satin nakeso kuje ku dubashi..idan kuma kanaso ka nunama dunia ban isa dakai bane Bismillah"..kallonta kawai Bobby yake yana mamakin sudden change din nan nata..Mummy ba mace ce mai fada ba sam..zaiyi wahala kaga tana fada musamman ma shi amma yanxu gashi ta daure fuskanta tana mishi fadan akan mutanenda bai daukesu a bakin komai ba..mutanen da basu ta6a kaunarsu tsakani da Allah ba tun mahaifinsu ma yanada rai...yasan duk wnn abun tanayi ne sbd kar yayi mata gaddama kaman yanda ya sabayi a baya amma shidai har yanxu baiji zai iya zuwa wani duba waziri ba..Wazirin da shi kanshi ba kaunarsu yake ba...ganin yanda yayi shiru ya wani kafeta da ido tace"bazaka jeba knn?."da sauri yace"aah ba haka bane Mummy..zanje..amma in..."bata bari ya karasa ba ta dakatar dashi da fadin"kaje ka fara shiru this coming weekend zakuje gaba dayanku ku duboshi"..kallonta yake yace"gaba dayanmu kuma?..wai kina nufin hadda su Miemie?.."kai tsaye tace"ko su ba jininshi bane da baza suje dubashi ba?.."a hankali yace"amma Mummy su meye hadinsu da Waziri da zasuje duboshi"..kallonshi Mummy keyi cikeda takaici tace"kaidai idan bakayi wasa ba sai Allah ya kamaka da laifin yanke zumunta..su Miemien zakace meye hadinsu dashi sbd bakada hankali?.."shiru kawai yayi yana kawar da kai shidai harga Allah wnn abun da Mummy keson tursasa su suyi bai gamsheshi ba..kilan ma suna zuwa Wazirin yasa koresu yace bayaso ya sake ganinsu har abada...ita kuwa Mummy ganin idan tacigaba da zama tana mgn dashi 6ata mata rai kawai zaiyi sai ta mike bayan ta gama mgnrta ta wuce zuwa 6angarenta...sbd iskanci zai wani ce a bari ba yanxu ba sai azumi ya shigo knn yakeso suje dubiyan nashi ko sai bayan sallah?..ta rasa wane irin taurin kaine da Bobby da ko ita data haifeshi watarana bya tankwaruwa ta dadi a wajenta?...yana ganin ta shige ciki shima ya mike zuwa flat din aunty sumy..he need to talk to her about this ko zata iya lalla6a musu Mummy ta bari sai bayan sallah tunda yanxu dab ake da fara azumi...yana shiga kai tsaye bedroom dinta yaje ya kwankwasa kofa ta bashi izini snn ya bude kofar ya shiga...a zaune ya sameta tsakiyar gado tana aiki da system dinta..ya isa ciki ya zauna kusada ita yana dubanta a hankali yace"mgn nakesonyi daks aunty sumy"..ba tareda ta dago ba tace"to ina sauraronka Uncle Bobby"..dan 6ata rai yayi yana kallon kaman zaisa kuka yace"aunty plss be serious mana..please!.."ajiye system din tayi tana dubanshi da murmushi tace"to yi hakuri..ina jinka"..gyara zama yayi kafin yace"Mummy ce take mgnr zuwa dubiyan Waziri"..ajiyan zuciya ta saki kafin tace"kaima ta fada maka knn?.."yace"ta fadamin..yanxu ya kike ganin zamuyi?..nidai bana son zuwa inda suke kwata kwata..bana son ganinsu"..kallonshi aunty sumy keyi kafin ta sake sauke wani ajiyan zuciya tana cewa"na fuskanci wnn karon Mummy da gaske take kan mgnr nan..idan mukace zamuyi kokarin kaucewa umarninta muna iya samun matsala da ita"..shiru Bobby yayi yana nazari shi kanshi yaga alaman hakan zai faru amma ya zasuyi?..yace"yanxu knn kina nufin bamuda wani option dole sai munje?.."gyada kai tana cewa"gaskia dai kamar bamuda wani option din..kasan yanda Mummy take da damuwa Bobby idan bamuyi abunda takeso ba muna iya sawa ta samu wani matsalan kuma kasan yanda bp dinta yake..baason tana shiga damuwa da yawa"...shiru ya sakeyi yana nazari..tabbas mgnr data fada gaskia ne...yasan yanda ta kwallafa rai kan sai sunje din nan idan sukace zasuki zuwa tsaf zata iya sama kanta damuwa har jinin nata yazo yana hawa shi kuma abunda baiso knn har abada...ajiyar zuciya ya sauke tareda runtse ido yasan wnn karon kam bashida wani hanyan tsira..duk wani kauce kauce bazaiyi tasiri akan Mummy ba wnn karon tunda har tasama ranta sai sunje dole...haka nan zai hakura yaje domin mahaifiyarshi amma wlh ba donshi wazirin ko don wani daga cikin 'ya'yanshi ba...aunty sumy ta dafa hannunshi cikin sigan lallashi tace"haka nan zamu hakura muje wnn karon..koba komai zamu samu ladan da su bazasu ta6a samuba sbd kin nemanmu da sukayi na tsahon shekaru"..gyada kai kawai ya iyayi tareda mikewa ya fita daga dakin...tabbas zasuje amma ba don wani daga cikinsu ba sai domin Mummy..sbd gudun 6acin ranta daka iya haifar mata da matsala amma ba sbd su ba.
Bayan kwana biyar...
Da sallama ya shigo parlon Mummy ya sameta zaune tana answering call...karasawa ciki yayi ya zauna nan kusada ita saida ta gama wayan ya wani kwa6e fuska yana dubanta yace"Mummy am back..Mummy yunwa nakeji wlh ni yanxu duk kin deddena sona"...dan murmushi ta saki tana kallonshi..cikin 'yan kwanakin nan ta fahimci yana cikin farin ciki..batasan ko sun daidata da yarinyar ba amma she's happy seeing him like this...sake kwa6e fuska yayi yace"kuma Mummy ko ki tambayeni yanda mukayi da Lamido"..murmushi ta saki tana kama hannunshi tace"ai nasan tunda na ganka cikin farin ciki these days kilan kun gama daidaitawa da ita"..tana rufe baki yace"a ina?..we are still patching things up dai..kawai inaso tasoni koda baikai wanda nake mata ba"...sake damke hannunshi Mummy tayi tace"zata soka inshaAllah..just continue being a good guy"...murmushi ya saki mai kyau yana shafa lallausan gashin kanshi yace"Allahumma Ameen Mummy..I can't wait to see that"...dan rankwashi Mummy ta kai mashi a kai tana cewa"rashin kunya kou?.."dafe kan yayi yana dan saki kara yace"ouchh..Mummy da zafi fa"..dungure mishi kai tayi tana hararanshi tace"Comot for this place"..murmushi ya kara saki ya wani makale mata kafada...kallonshi kawai tacigaba dayi full of excitement..seeing him like this really gladdens her heart and she prays Allah yasa ya dore har karshen rayuwarshi...Allah ya mallaka mashi yarinyar nan idan har ta kasance alkhairi a gareshi...ganin yanda taketa kallonshi sai ya dan 6ata fuska yace"Mummy wnn kallon fa?.."murmushinta ta fadada tana fadin"am just suprised and impressed..My Bobby is in love i can't believe this"..murmushi shima ga kara saki yana cigaba da shafa gashin kanshi kaman zaisa kuka yace"Mummy manaaaaa..am shy plss"..daria ta saki sosai kafin tace"ba wani u are shy bayan har rowarta kake mana..tun yaushe nace maka ka sake kawo mana ita mu gaisa amma baka kawota ba"...yana cigaba da smiling yace"zan kawota Mummy inshaAllah..amma dan Allah idan tazo kar kice mata wani abun plss"..murmushi take tace"bakaso ta sani?.."gyada mata kai yayi tareda cewa"not now"..Mummy tace"dont worry she won't know anything..yanxun dai take these"..ta zaro wasu papers dake bayanta ta mika mashi...amsa yayi yana dubanta yace"Mummy meye su?.."a takaice tace"ur flight tickets"..kallonta yayi da sauri cikin mamakin abunda tace..kafin ma ya tambayi na meye ta sake cewa"to Abuja"..kallonta kawai yake full of surprise..a hankali yace"Mummy badai ke da kanki kikaje airport siyo mana tickets ba?.."harara ta watsa mishi tace"it's non of ur business..nasan ba son zuwa kuke ba ai shiyasa nayi maku haka..sai kuje ku fara shiri flight dinku is tomorrow by 4"..kallonta kawai yake kafin ya koma kallon tickets din...na gaba dayansu ne including Miemie da Ilham...sbd tsabar mamaki kasa ce mata komai yayi..shi wlh da yaji shiru ta dena mgnr ma yayi tunanin mantawa tayi ashe tana sane ido kawai ta zuba musu...numfashi ya sauke yana cigaba da duban tickets din shidai Allah ya sani ba son zuwa Abujan nan yake ba..sam baison tafiyan shi baima san ta ina zasu fara ba idan sukayi ido da ido da Wazirin shin gaisuwa za'a fara ko kuwa kallon kallo zasuyi a tsakaninsu...itadai Mummy mikewa tayi ta shiga bedroom dinta shima yaja jiki a hankali ya fita daga parlon nata..knn dai gobe i yanxu suna can Abuja tareda Waziri..what the heck shi baisan ma da wane ido zasu kallesu ba wlh..sam baisan ya haduwan nasu zai kasance ba.
Washegari ko fita baiyi ba dan Mummy hanawa tayi..haka ta tsaresu gaba daya kowa ya dauki kayanshi set daya tunda gobe zasu dawo...Bobby na fitowa daga Flat dinshi ta kalleshi from head to toe kafin ta mike zuwa insa yake tana cewa"koma kasa manyan kaya"...kwabe fuska yayi yace"manyan kaya kuma Mummy?.."tace"yes haka nace..hanga dalilinda zaisa ka tafi wajen grandpa dinka haka ba"...kallonta Bobby yake kaman zaisa kuka yace"Haba Mummy kaman wanda zaije wajen surkai?.."kama hannunshi tayi suka koma Flat din nashi tana fadin"komai abunka bazaka tafi a hakaba wlh..kuma idan ma kayan daka dauka na gobe irin wnn ne then ka sake wasu"...kasa cewa komai yayi suna shiga bedroom kawai ya shiga closet dinshi ya sako wani coffee yadi mai taushi ba tareda yasa hula ba ya fito yace"Mummy amma dan girman Allah ba saina sa hula ba koh?.."kallonshi tayi taga yanda yayi kyau saita saki smile kafin tace"da kasan yanda manyan kaya ke maka kyau da ka dena saka wnn suits din wlh..now wuce muje time na kurewa"..ba yanda ya iya haka ya wuce gaba Mummy tabiyoshi a baya...a central parlor suka tadda sauran suma gaba daya sun fito kowa ya gama shiryawa...haka ta hada kansu suka fita zatayi musu rakiya airport..aunty sumy da Mummy da kuma Miemie suna motan Mummy da driver ke tukawa..shi kuma Bobby yana tareda Ilham da Sab shima cikin nashi motan...duk ranshi a 6ace yake sbd tafiyar nan nunawa ne kawai baiyi sbd Mummy...bayan sun isa airport duk dukayi sallama da ita har zasu wuce Bobby ya sake dawowa inda take yana dubanta kaman wanda zaisa kuka yace"yanxu Mummy ke kadaifa zamu tafi mu bari a gidan..dan Allah ni in dawo su su tafi sbd kar a barki ke kadai"..girgiza kai Mummy tayi tana jan cheeks dinshi tace"nafa fada maka ba abunda zai faru ai akwai masu aiki a gidan"...turo baki yayi yace"nidai dukda haka u take care of yourself"..wnn karon rungumeshi tayi gamida manna mishi kiss a forehead dinshi tace"zan kula inshaAllah..Allah ya kaimin ku lafia ya dawo daku lafia"..a hankali ya amsa da Ameen..da sauri Sab ya matso kusa dasu yana cewa"Mummy nima bakiyi hugging dina ba"..bude mishi hannu Mummy tayi yace"come here dan autana"..da gudunshi kuwa ya fada jikinta kafin ta maida hannu ta rungumeshi snn ta dagoshi shima ta manna mishi kiss a goshinshi...daga nan kuma sai Miemie da Ilham suma duk suka dawo tayi musu aunty sumy dai ba tsaye tana kallonsu...Ilham ce ta kalli mamanta snn ta kalli Mummy tace"Mummy to saura aunty"..dungure mata kai Mummy tayi tace"wa yake ta wani aunty...auntyn da ta girma"..daria gaba daya suka saka nan kuma aka fara announcing passengers su zama ready jirgi ya kusa tashi..a gurguje suka sake sallama snn suka wuce itama Mummy ta shiga motanta driver yaja suka koma gida.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
34
Karfe biyar da wani abu jirginsu ya sauka Nanmdi Azikiwe International Airport Abuja...wani Friend dinshi mai suna Dr Fariq ne yazo ya daukesu daga airport din zuwa Freedom Medical College inda ya ware ma kanshi apartment guda sbd irin wnn lokacin...apartment din na dauke da babban parlor guda daya sai three bedrooms inda shi ya dauki daya Sab ya dauki daya su aunty sumy ma suka dauki daya...gaba dayansu ba wani mai cikakken walwala cikinsu kowa yake kawai yakeyi amma ta ciki na ciki...tunani da kuma zullumin yanda haduwarsu da 'yan uwan mahaifinsu zai kasance bayan kusan shekaru shidda suke...aunty sumy dai addu'a take Allah yasa karshen komai ke yazo while shi kuma Bobby jikinshi ke bashi ko sunje dinma Waziri ba accepting nasu zaiyi ba har yanxu..kawai ya riga ya sawa kanshi tunda baiyi kokarin sawa a nemosu har tsahon wnn lokacin kilan ba baya sonsu ne..ko kuma bai shirya kar6ansu a matsayin jikokinshi ba...Dr Fariq ne yayo musu takeaway na abinci ya kawo musu dukda basa tareda yunwa...Mummy dake can gida hankalinta gaba daya yana kansu ta kira Bobby tana tambayan ya suka sauka...yace sun sauka lafia sai sunyi sallahn magrib zasuje can asibitin da wazirin yake..dadi taji sosai tareda sa musu albarka..har tausayi yaji ta bashi sbd yanda take mgn..ya tabbata ita kanta tana cikin zullum ko waziri basan amince dasu ba...saida sukayi sallahn magrib kaman yanda yace snn gaba daya suka fito suka nufi asibitinda waziri yake cikin motan Dr Fariq da Bobby ya tuka da kanshi...koda suka shigo cikin asibitin saida gaban kowa ya fadi including Bobby da baisan dalilin faduwar gaban ba...bayan sun fito daga mota suka nufi cikin asibitin da yake nan kaman ba dare ba sbd hasken dake ta ko ina...daida suka tambayi wani sub staff room 105 yayi directing dinsu har zuwa can...a kofar dakin suka tsaya suna kallon kallo an rasa wanda zai fara karfin halin shiga a cikinsu..aunty sumy ce tayi murmushin yake tareda tura kofar a hankali ta shiga da sallama suma duk sai sukabi bayanta...yana kwance kan gado idanunshi a rufe da alama bacci yakeyi..sai wani dan matashi dake zaune kan kujera daga dam gefenshi...kallon kallo aka shigayi tsakaninsu da matashin shi yana musu kallon kamar ya sansu amma ya kasa tuna a ina suma suna mishi kallon saidai ya kasance jika a wajen waziri domin kaf yayanshi sun sansu amd bashida karamin yaro kamarshi...wuri ya nuna musu suka zauna yana kokarin dora murmushi kan fuskanshi yace"sannunku da zuwa"..aunty sumy ta amsa da"yauwa sannu..ya mai jiki?.."yace"Alhamdulillah ya samu sauki"..gyada kai kawai tayi kafin tace"Allah ya kara sauki"..daga nan kuma sai dakin yayi shiru ba wanda ya sake mgn cikinsu...a hankali Bobby ya daga ido yana kallon tsohon da a kallon farko za'a gane jininshi ne sbd kamanninshi daya dauko..mahaifinsu na kama da waziri sosai shima kuma Bobbyn sai ya dauko mahaifinshi...kallonshi kawai yake yana tuna duk abubuwanda suka faru a baya sai yaji ranshi na 6aci..da sauri ya dauke kanshi tareda mikewa tsaye da hannayenshi a aljihu yace"i think we should leave tunda bacci yakeyi da safe sai mu dawo"..babu wanda yayi masa musu cikinsu duk suka mike da nufin su fita sai kawai sukaji am turo kafar dakin wata mata ta shigo sanyeda katon hijab da glass a idanunta...tana dora idanu a kansu ta saki ledan dake hannunta tana zare idanu sosai a kansu bakinta yana motsi alaman she wants to say something...da sauri ta karasa inda suke ta shiga nunasu da finger dinta daya bayan daya har yanxu bakinta bai bar motswa ba amma ko kalma daya yaki fita daga bakin...ta tsayar da idanunta kan Bobby da shima yayi kasake yana kallonta kawai saita rungumeshi hawaye na saukowa fuskanta tace"Bobby is this realy you?..anya ba mafarki nake ba?.."hannunshi yakai shima ya zagayeta dasu snn a hankali yace mata"you are not dreaming"..dagowa tayi tana kallonshi har yanxu bata bar hawaye ba..takai hannayenta tayi cupping fuskanshi dasu tana cewa"my son..where have u been?..ina kuka shiga kuka 6oye nayita wahalar nemanku ban sameku ba?.."kafin yace wani abu ta sakeshi tareda matsawa inda Sabeer shima tayi hugging nashi tightly tana cewa"Sabeer..Sab kaine ka girma haka?..kaine ka zama saurayi haka?..zaka iya tuna ni?.."duk a lokaci daya ta jero mai wadan nan tambayoyin sbd tsabar shock data shiga na ganinsu..bata ta6a tsammanin ganinsu a nan ba..tayi wahalar nemansu na tsahon shekaru amma da yake ita mace ce kuma ba mazauniyar kano ba sai ta