Showing 90001 words to 93000 words out of 231169 words

Chapter 31 - Dr.BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Aug 2024

9692

neman wucewa sai ta dauki wayanta ta shiga kiranshi...yanata ringing bai dauka ba har tayi mishi 4 missed calls ba wanda yayi answering a ciki...nan kuma hankalinta ya fara tashi dan tasan lafia lau dai baza'a yima Bobby har 4 missed calls bai gani ba..sake kira tayi for the fifth time ganin still no answer saita dannawa Nur kira hoping ko basa tare yasan inda yake...Nur dake kan hanyan komawa gida yana ganin kiran nata yayi parking snn ya daga kafin yayi mgn Mummy tace"Nuru kuna tareda Bobby kuwa?.."girgiza kai Nur yayi kaman tana ganinshi yace"No mun rabu tun daxu Mummy..ai tun around 4 ya baro college saidai ko Hospital ya wuce"..Mummy tace"anya kuwa?..na kira wayanshi bai dauka ba and yau yacemin yana gama da college dawowa gida zaiyi ya huta bazaije ko inaba"..shiru Nur yayi yana tuna a halin da ya bar college din yasan zaiyi wuya yaje wani wurin idan ba gida dan haka yace"Mummy a duba flat dinshi dai..zai iya yiwuwa ya dawo yana ciki bai fito ba shiyasa baku san yana nan ba"..gyada kai Mummy keyi before tace"shknn let me check"..daga haka ta kashe wayar snn ta juya zuwa flat dinshi...tana tura kofan tajishi a bude tasan yana ciki knn dan haka direct ta wuce bedroom dinshi..a kwance can karshen gado ta hangoshi ya kudundune kanshi kanshi cikin duvet dukda haka kuma jikinshi bai bar rawa ba...karasawa tayi da hanzari ta yaye duvet din tana ganin yanda ya dunkule waje daya saida gabanta ya fadi dan Bobby ba mai yawan rashin lafia bane..yana dadewa baiyi ciwo ba amma duk ya tashi yi sai ya kusan mutuwa sbd wahalan da yakesha...zaunawa tayi nan kusa dashi hankalinta duk a tashe in igbo tace"Bobby meke damunka?..yaushe ma ka dawo gidan bamu sani ba?.."da kyar ya iya bude idanunshi ya zubasu a kanta sai kuma ya sake maida su ya lumshe sbd baison ganin tashin hankalin dake rubuce kan fuskata...hankali tashe ta sake fadin"ba mgn nakeyi ba?..meya sameka?.."daurewa ya mike zaune da kyar yanajin yanda sanyin dakin ke sake ratsa mashi jiki Mummy data lura da hakan tayi saurin mikewa ta kashe ac snn ta sake dawowa ta zauna tana dafa forehead dinshi tace"u look seriously sick Bobby..meke damunka?.."hannunta kawai ya iya kamawa yana zuba mata idonshi dake mata nuni da bayason ganin damuwar nan da takeyi shiyasa tun daxu yaso ya tashi yasha magani kafin ta shigo amma ko motsi kasawa yayi...ganin kaman bazai iya mgn ba ta dauki wayanta data shigo dashi kai tsaye ta sake dialing number din Nur tace"bari in kira Nuru yazo ya dubaka idan abun bai yiwu ba kawai mu wuce asibiti"..tun kafin ta rufe baki yaji wani new 6acin rai na diran mishi jin ta ambaci Nur sbd tunawa da iskancin da yayi mashi daxun yace"Mummy..dont..call him..plss"..Mummy tace"why zakace haka?..kaji yanda temperature dinka yayi rising kuwa?.."lumshe idonshi yayi dan baisan me zaice ba again...kafin Mummy ta kira Nur sai ga aunty sumy ta shigo dakin tan sanyeda dogon riga da hula itama duk a gigice tace"Mummy wai jikin nashi ne har yanxu?.."Mummy tace"wlh har yanxu sumayya..ungo wayan nan ki samu ki kira Nuru yazo ya dubashi wnn high temperature bana lafia bane"..da sauri aunty sumy ta amsa wayan da Mummy ke mika mata ta zauna tareda dialing number Bobby sbd takaici kawai ya zare hannunshi daga cikin na Mummy hade da komawa ya kwanta ya juya musu baya...hada ido sukayi kafin aunty sumy dake sake trying number Nur tace"ni ban ta6a ganin likita da baya qaunaf treatment ba irin Bobby..duk rashin lafia ya kamaka saika bamu wahala wajen zuwa asibiti ko kuma kiran doctor"..shidai baice mata komai ba sbd shi kadai yasan abunda yakeji...Nur na ganin kiran yayi picking tareda fadin"yauwa Mummy yana gidan kou?.."aunty sumy tace"yea yana nan amma fa bashida lafia..he's seriously sick inaga u should come forward ka duba jikin nashi"...da sauri Nur yace"ok gani nan zuwa yanxun nan"..daga haka ya kashe waya tareda juya kan motarshi zuwa airport road...aunty sumy na gama wayan itama komawa tayi ta zauna kusa dashi suka wani sanyashi tsakiya itada Mummy sai kace wanda ke fama da cutar ajali.😂
Ko cikakken 30 minutes baayi ba Nur ya karaso gidan..yana shiga ciki kai tsaye ya wuce flat din Bobby don bai samu kowa central parlor ba...saura kiris daria ya kufce mishi sbd ganin yanda sukayi wani tsuru tsuru suna kallonshi sai kace wanda akace musu ya mutu...karasawa yayi ciki yana kallonsu with smile yace"ya jikin nashi?.."Mummy ce ta mike daga inda take tana nuna Bobbyn da har yanxun ya juya musu baya tace"gashi nan dai..ka fara dubashi muga"...baiyi musu ba ya isa inda sphygmomanometer da stethoscope din Bobby ke ajiye ya daukosu snn ya dawo gefe gadon ya zauna ya ajiye kayan snn yakai hannu zai ta6a forehead dinshi ya wani daddage ya kwade mishi hannun aiko Nur ya fashe da daria sosai..bashi ba hatta su Mummy ya basu daria ganin yanda yakejin jiki amma har yanada energy din rigima haka...yana sake kai hannu Bobby ya kuma make hannun nan kuma Mummy ta daure fuskanta tace idan bai tsaya an dubashi ba zataci mutuncinshi..ba yanda ya iya haka ya mike zaune yana cika yana batsewa fuskan nan ba sarari kaman wanda aka aikoma sakon mutuwa...Nur bai damu da hade ranshi ba ya bude sphyg din ya zaro curf din ciki snn ya zurashi hannun Bobby yana tieing dinshi a hankali...bayan ya gama ya makale stethoscope dinshi a kunne tareda kama hannun nashi snn ya fara pumping...yana gamawa ya zare abun daga kunnenshi snn ya shiga kwance curf daya daura mashi yana duban su Mummy yace"Blood pressure dinshi is normal amma idan bai dena sa damuwa ba yana iya hawa nan gaba kadan"..Mummy ta gyada kai alaman ta fahimta shi kuma Nur ya mike zuwa first aid box dinshi ya dakko wasu drugs snn ya koma inda yake..Mummy tasa aunty sumy zuwa ta hado tea shima ya wani sake hade rai yace bazaisha ba saida Mummyn ta zauna da kanta itama ta daure nata fuskan snn aka samu ya sanyeshi tas ta amsa drugs din suma ta bala mashi yasha snn tace ya kwanta...ba musu ya sake juya musu baya ya kwanta yanajin yanda zuciyarshi keta harbawa sbd kular dashi da sukayi...bayan few minutes bacci ya daukeshi dan hadda maganin bacci aka hada mishi sai a lokcin suma suka fita daga dakin...kafin Nur ya tafi Mummy ta zaunar dashi tana tambayan ko wani abu ya hadashi da Bobbyn...Nur da har yanxu attitude din abokin nashi bai dena bashi daria ba yace"wlh ba wani abu Mummy love ne kawai yake dawainiya dashi kuma yaki admitting "..kallonshi Mummy keyi nan take kuma jikinta ya bata akan Lamido ne dan haka tace"u mean akan wnn yarinyar ne?.."Nur yace"a kanta ne wlh..kinsan halinshi da kafiya na fada mashi sonta yake yana maidani dan iska and the most funniest part of al'amarin shine azabar kishinta da yake wai amma har yanxun yaki accepting the fact that yana sonta..pics dinta fa kawai tayi posting a status shine yake wnn zazza6in"..gyada kai Mummy ta shigayi cikin ranta tace"lallai biri yayi kama da mutum"..a fili kuma sai tace"yanxu ya kake ganin za'ayi?..ni bansan irin Bobby ba wlh"..su Nur hadda gyara zama yace"nidai ina ganin dena mishi mgnrta kawai zamuyi..kuma idan kunayi ku dena nima daga yau ban kara fada mishi yana sonta..mu zuba mishi ido kawai na tabbata idan abun yafi karfinshi da kanshi zaizo ya fada"...shiru Mummy tayi tana nazari kafin tace"amma kana ga baza'a samu matsala ba?.."Nur yace"inshaAllah ba matsalan da za'a samu..a yanda halinshi yake indai za'a cigaba dayi mishi zancen yana sonta to ita kanta yarinyar zaiyita sauke mata masifanshi ne sbd zaiga kaman ita take janyo ana fada mishi haka..amma idan mukayi biris da al'amarin watarana da kanshi zaiyi admitting yana sonta"...gyada kai Mummy tayi tace"shknn Allah ya zaba mana mafi alkhairi..ni da zaka taimaka ka kawomin yarinyar ma in ganta"...yace"Kaii Mummy kinaso Bobby ya dena kulani knn?..a yanda yakeda kishin nan idan yaga na daukota a motata ai inaga kisan mutuwa zaiyi"..ya karasa mgn yana daria...aunty sumy da batsan da zancen ba sai yanxu tace"lallai Nur kasan kan abokin nan naka da yawa"...yace"ai aunty qanin naki ne kinsan zuma ne saida wuta"..daria suka saka kafin Nur yayi musu sallama ya wuce suma kowa ta nufi dakinta kafin a jima su sake zuwa ganin jikinshi.

Har gari ya waye Bobby bai denajin zafin da yakeji ba...ya samu dai headache da fevern sun sauka amma zuciyarshi dai tana nan a jagule yanda take tun jiya kuma duk kokarinshi na ganin yayi maganin hakan gagararshi yayi...ko yau da safe sau uku yana kiran numberta switch off hakan kuma ba karamin sake tunzurashi yayi ba..sbd batada hankali ta kwashi jiki ta tafi har kaduna biki sai kace bikin 'yar uwarta?..kuma yanada tabbacin a gidansu ba'a sani ba dan haka jira kwai yake ta dawo ya sauke mata nauyin dake cikin zuciyarshi.

A can kaduna kuwa Lamido tunda tasan yasan inda sukaje hankalinta bai sake kwanciya ba dan ko bikin ma dena enjoying dinshi tayi..tsoronta Allah tsoronta kada ya kira daddy ya fada masa tasan yana fada itakam ta gama yawo..da farko kin fadawa Billy da shi kanshi Sa'eed din tayi sbd tasan zasu dora mata laifi musamman Billy amma daga baya dole suka gane akwai abunda ke damunta dan haka ta fada musu exactly yanda sukayi dashi...hankalin Billy ya tashi matuka dan ko ita Lamidon bazata gaya mata shiga tashin hankali ba dama yanda kasan farar kura haka take wajen tsoro...basuyi niyyan barin kd ranan sunday ba amma haka Sa'eed ya tattarosu suka wuce sbd yana guje musu matsalan da zasu iya fuskanta wajen proprietor dama kuma biki ya kare tunda ankai amarya...haka suka tafi ko sallama basuje sunma amaryan ba...karfe uku da wani abu suka dauki hanyan kano and basu suka shigo birnin dabo ba sai around six..suna ganin an dauki hanyan FCNM hankalinsu ya sake tashi musamman Aysha da cikinta har wani juyawa yake sbd tashin hankali...har tsoron kunna wayanta take sbd tasan tana kunnawa zai kira and hakan na nufin masifa da bala'i dan kuwa tasan idonta idon Dr Bobby saiya cinye mata mutunci tas tunda dama ba yanxu ya saba ba..kawai tsoronta kada ya hadata da babanta amma dan ta masifarshi mai sauki ne dan idan da sabo yaci ace ta saba dukda cewa yanxu sam bai cika mata ihu ba..wani lokaci ko abu ya kama na fadan ne da idan baiyiba bazaiji dadi ba sai yayi mata shi a nutse kaman ba fada yakeyi ba amma yau kam tasan idan akwai abunda ya wuce ihu ma zaiyi shi tunda ta gama kular dashi...har suka isa hostel babu mai kwarin guiwar yin mgn cikinsu shi kanshi Sa'eed din addu'a yakeyi Allah yasa bazasu samu matsala sbd shi ba tunda shine wanda ya daukesu zuwa kadunan and Allah ya sani da yasan basuyi informing parents dinsu ba ba dalilinda zaisa ya kwashesu har kd saidai rashin sani...kafin su rabu ya sake kwantar musu da hankali tareda assuring dinsu cewa inshaAllah komai zai tafi normal..sukam gaba dayansu jinshi kawai sukeyi amma gani suke dole fa sai wani abu ya faru either big or small.

The next day sukayi shirin school kowa tasa uniform dinta suna jiran school bus saidai ba wanda takeda walwala a cikinsu...baa jimaba bus dinsu yazo ya kwashesu sukayi cikin makarantan...ana ajiyesu suka fice yau har rige rigen fita daga bus din suke a takaninsu sbd gudun haduwa dashi dukda ma sunsan monday ba ranan shigowarshi bane...daga nan direct class dinsu suka wuce basu sake fitowa ba har suka fara lectures.
Karfe tara daidai yayima Bobby a college din dukda cewa Monday ne ga kuma jikinshi da bai gama sauki ba amma ko hospital ya kasa zuwa sbd yanaso ya ganta...kai tsaye sama ya haura zuwa class dinsu don yasan idan yace har saiya sameta a waya to bazai taba samunta ba dan ba kunna wayan zatayi ba...wani lecturer ya samu a class din yana musu lectures dan haka kai tsaye ya fada class din fuskan nan a tamke kamar baisan menene daria ba...hannu ya mikawa lecturer din suka gaisa snn ya maida hannun aljihu yana baza idanu yanaso ya hangosu amma ko daya daga cikinsu bai gani ba...hankalinshi ya maida kan 'yan class din fuska ba fus yace"where is Lamido?.."da sauri suka nuna inda take can baya tana sunukuyar dakai..baice kala ba sai takawa da yayi har gaban seat din nata ya zuba mata idanunshi ko kadan bata sonsu snn a kausashe yace mata"mike.."ba musu ta mike tsaye kai a kasa..ya sake cewa"ina Bilkisu?.."da sauri itama ta nuna seat dinda Billy ke zaune itama kallon nata yayi tayi saurin dukar da nata kan snn ya juya still hands dinshi a aljihu yace musu"follow me"..sum sum suka bi bayanshi kaman marasa gaskia..yana gaba suna binshi dukda bai juyaba yanajin footsteps dinsu ta bayan nashi dan haka kai tsaye ya wuce office dinshi suna biye dashi..a hanya ya kusa cin karo da Nur ya wani wara ido yana kallonshi then su Lamido dake biye dashi sai kuma ya saki dan murmushi yana maida dubanshi gareshi yace"so ka warke knn?.."ko kallonshi Bobby baiyi ba ya wuce office dinshi...yana isa ya bude kofa da yake bai shigowa Monday so secretary dinshi bata zoba...shine ya fara shiga ciki snn sukabi bayanshi...a kan sofa ya zauna yana kallon yanda sukayi wani cirko cirko a gabanshi sai ya sauke idanunshi kan Billy da yake ganin kamar tafi hankali yace"Bilkisu hadda ke?.."da sauri Billy da kanta ke kasa tace"wlh sir ba laifina bane ba yanda banyi da ita akan mu fada a gida ba tace wai baza'a fada ba"..yace"then meya hanaki kirani ki fadamin?.."Billy da har ta fara hawaye tace"shima cewa tayi bazan fada ba wai sbd hanawa zakayi?..sir dan Allah kayi hakuri wlh bazai sake faruwa ba"..gyada kai yayi dan ya yadda da ita yace"next time kina ganin zatayi anything stupid just give me a call ai kinada number na"..gyada kai Billy tayi tace"inshaAllah sir"..yace"shknn u can leave"..Billy tayi godia snn ta juya zata fita Aysha tabi bayanta da sauri wai tunaninta ya sallamesu gaba daya amma sai taji cikin cunkushashen voice dinshi yace"who ask u to leave?.."juyowa tayi a hankali tana dubanshi kaman zatasa kuka tace"sir dan girman Allah in tafi"...ya sake hade rai yace"C'mon comeback here before i loose it with u"..juyawa tayi a hankali ta daw ciki idonta na cikowa da hawaye...kallon hawayen dake silalowa daga idon nata yayi nan take ya lumshe ido yanajin yanda hawayen ke sauka har cikin zuciyarshi...baisan meyasa these days ko tayi laifi tana fara kuka jikinshi ke mutuwa ba..so yake yayi mata masifa son ranshi amma yana ganin hawayen nan yaji zuciyrshi yayi waji weak...kujera ya nuna mata idanunshi a kanta yace"seat"...batayi musu ba ta zauna inda ya nuna mata tana hawaye na sake ambaliya akan face dinta...dafe goshi Bobby yayi hade da lumshe ido yanajin yanda takeso ta sake haddasa mishi ciwon kai da wnn kukan nata yace"For Gods sake me akayi makai na kuka ne wai?..nayi maki wani abun ne?.."girgiza mashi kai tayi still tana hawaye yace"then why are u crying?..nida kika haddasa ma rashin lafia banyi kuka ba saike zaki sani a gaba kinamin kuka?..kinama da hankali kuwa?.."turo baki tayi jin abunda ya fada wai ta haddasa masa rashin lafia..ta sake tale baki tana dan kallonshi ta gefen idonta tace"nidai dan Allah karka fadawa daddy plss"...kallonta yakeyi yace"naji I won't tell him amma inaso ki dena kukan nan muyi mgn dake"..ba musu takai hannunta ta goge hawayen duk yana kallonta snn tace"na goge"..gyara zama yayi still idonshi kanta yace"tambaya nakeso inyi maki and i want u to be fair to yourself..idan da a Gombe kike gaban parents dinki would u do what u where doing now?.."girgiza mishi kai tayi a hankali alaman bazatayi ba...yace"then why kikeyi a nan sbd ba gabansu kike ba?..tsakaninki da Allah da ace wani abu ya sameki a hanya what do u want me to tell ur dad daya bani amanarki?..ko sbd kina ganin baki ta6a yin wani abu na sanar dashi ba?.."girgiza kai ta shigayi da sauri tace"sir wlh ba haka bane..gani nayi Lubna friend dinmu ce sosai and ko sbd besty bai kamata muki zuw..."bata karasa ba ya katseta cikin karaji yace"in your entire life karki sake mentioning min besty idan muna mgn..ina ruwana da wani besty ni ke na sani bashi ba and idan bakiji abunda na fada ba kuma you will see the other side of me"..ya karasa mgn har wani huci yake kaman tsohon zaki...Lamido dai kallonshi kawai take tana mamakin yanda yake changing forms within minutes..yanxun nan fa yake mata mgn a nutse kmr bashi ba within a second kuma ya dawo mata asalin proprietor data sani...kauda kanta tayi tana turo baki ita gara ma ya dingayi mata masifan kmr yanda ya saba ba yasata a gaba yanayi mata mgnr dake sa jikinta yana mutuwa ba...ganin yanda itama ta hade rai tana turo mishi baki ya danyi kasa da voice dinshi yace"wai meyasa bakijin mgn ne ke kam?..meyasa fitinanki yayi yawa?.."sake turo baki tayi tana gunguni kuma akan idonshi kawai sai ya rufe idanu tareda jingina jikin kujera yana karanta innalillahi a cikin ranshi...kamar yanda ya fada ne idan baiyi wasa ba yarinyar nan saita haifar mishi da ciwon zucia sbd abunda yakeji kanta is beyond his control...kawai yana ganin Allah ne ke jarabtarshi da 'yar Gombe sbd tsananin kiyayyan da yakema 'yan Gomben.









Rano✨






Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
29
Kallonshi Aysha keyi ganin yanda ya dafe goshi ya lumshe ido aikuwa ta daddage ta maka masa wani harara sai gashi karaf ya bude idon nashi...ta wani zaro ido hadda dora hannu a bakinta tace"sir i swear bada kai nakeba"..bai iya cewa komai ba sai kallonta da yakeyi nan kuma tayi kasa da idanunta tanajin idanun nashi har cikin brain dinta...ta rasa meyasa har yanxun ta kasa sabawa da idanun mutumin nan..sam bata kaunar ya zuba mata su sbd

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login